Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 53

Tarko complete novel - Chapter 53

Tarko complete novel Chapter 53: Tarko complete novel Chapter 53. ****** ********** ****** Tsaye nake a gaban mirror ina kara zaman gyale na, dana yafa wa…

2,906 words

****** ********** ****** Tsaye nake a gaban mirror ina kara zaman gyale na, dana yafa wa jikina, Na tabbatar da cewa babu sauran guri ko kadan, da zai baiyyana a jikina, Sai wani dan haske danaga nakara a fuskana tare da dan ramay , Sai da na tabbatar da cewa na kashe kayan wutan dake daki na sai na jawo kofa na nasa mai key , Dakin Anty, Sadiya na inda na samay ta tanawa Ramatu sababi wai ta zubar da ruwan da ta shafa mata magani a kasa, Gurin da ake cewa wai ruwan ya zube na fara kai idona sai naga baifi ko spoon biyu ba ma yawan shi, Sai kawai naji banji dadin irin yadda na samu ta na zazaga mata masifa a kai ba, A hankali na ce Anty don Allah kiyi hakkuri kila acikin rashin sanine ta zuba mata ruwan, Sai cewa Anty Sadiya tayi a hassale ita makauniyace da bata, gani, Shiru nayi saboda abin bai min dadi ba wallahi don dai a gaskiya Ramatu mutunce mai dadin zama, Gata bata da keta, tana aikin ta yadda ya kamata don ma harda wanda ma ba,a sa ta ba tanayi, Sanan ita anty yanzu idan Ramatu tai fushi ta wuce wa zai dinga mata irin wanan da wainiyar, Na juya gurin Anty Sadiya nace zan fita tare da Fattu zuwa gaida wata yar uwar ta da ke asibiti, Allah ya sauwaka kawai tace min batare da takara tankawa ba, ta ma kauda da kan ta gefe cikin bacin rai, Ita ma Ramatu nai mata sai na dawo sai take, ce min ai itama gida zata tafi ta dan zagayo, Sai zuwa dare zata dawo saboda yau Anty tace, mata zata tafi anguwa,,, Nace to Allah ya dawo da ita lafiya ni kan nasa kai na fita abina,, Mundan kai dan lokaci a gidan Fattu tana kimtsa gidan ta, Nai mamaki kwara ganin motar da Yaya Abubakar ya bayar akai mu Baban motar shi da yake fita da ita idan zai fita zuwa wani muhin min guri, ita ce nagani Hamza ya jawo ya Parker a kofan gidan su, Daidai fitowan mu ne zamu bar gidan su Fattu sai,ga Ramatu, ita ma tafito, daga gidan mu tana tafiya zuwa inda zata samu Napep, Na cewa su Baba Wadda mu dan dakata mu dauke ta idan sun aje mu sai su kaita gida, Ramatu tana ta zabga muna godiya tare da cewa Fattu tana gaida mai jiki, Wani asibiti da ganin sa na kudine muka nufa har ciki su Baba Wadda suka kai mu A kusan tara mu ka shiga da motar likitan asibitin inda yabi motar mu da kallo har zuwa inda muka tsaya muna fita , Na ciro dubu biyu a post dina na ba Ramatu nace ta sai wa yara tsaraba, Ta fara jero min addu,oi yadda har kai na ya dau zafi, don yadda, take cewa Allah ya kara rufa maki asiri hajiya Allah ya baki zuria mai albarka, Allah ya haushe ki sherin makiya gida dawaje Na amsa da fadin amin ya Allah Ramatu, na gode sai kin dawo ke nan, Na bude kofan mota nafita don Fattu ta riga da har tafita ko a lokacin, Ina fita sukai ribas suka bar gurin zuwa kai Ramatu kamar yadda na umurce su da yi, Baba Hamza ne yafara magana bayan sun dan fita daga get din asibitin, Gaskiya Hajiya Meenat tayi a rayuwa wallahi, babu ruwan ta ita Don inda ace watace ita da wallahi bazata ko baki lift ba balle har ta ce a kai ki gida cikin wanan zunguren motar tasu, Motar may gidan ne fa da yake yawan shigan ta idan zai fita, Ramatu tace ai al,amarin Hajiya Meena a kwai sha,awa don sam bata da matsala, Baba Wadda ya ce ai duk uwar ta ce ta kwaso, don haka mahaifiyar ta take a gidan mu babu ruwan ta don babba da yaro a gidan duk nata ne, Har zuwa lokacin da suka aje Ramatu a dan gidan su a cikin Garki village,,,

****** ********** ****** Kamar yadda muka ce haka muka fara yi muka shiga gaida wata yar yaren su Fattu, dake asibitin, Sai muka fito muka yanki kati, Allah ya tai make mu babu mutane da yawa a gurin sosai a lokacin, Ba muyi wani dadewa ba sai kawai ga layi yazo a kan mu, Fattu tace in shiga ni kadai don ba,a shiga mutum biyu, aciki, Naiwa likitan bayani wanda naga kamar yana min kallon sani, sai yace ai min photo, gwaji a gani,, Ciki ne dan wata kusan uku, a kwance cikin mahaifana, Sai aka rubuto min result na dawo wa likita da shi don ya duba, Nan yake min murna ya na kara nanata min,cewa , ciki ne na wata uku, don haka sai na bishi a sannu saboda ina bukatan bed rest zuwa wani dan lokaci, Wani irin dadi ne naji ya ratsa min zuciya abinda ya sa har na dan rutse idona a hankali don jin dadi,, Na fadawa doctor zancen miscarriage din da akace nayi a kwanan baya, Ya ce duk wanda yace miscarriage ne karya ne cikin dai ya dan so ya tabu a lokacin amma ai bai fita ba ,, Ya rubuta min magani yace in kula da zancen bed rest din don kada a samu matsala, Fitowa na yai daidai da dawo wan su Baba Wadda daga gurin kai Ramatu da su ka tafi,, Kafin su iso gurin da mu ke ne, nake wa Fattu bayani abinda, likita ya ce da kuma abinda zan kiyayye, Fattu tace cafdi, ashe kuwa za a samu matsala da maigidan ki don dai idan har kince, bazai sani ba da farko, Yanzu yaya ke nan za a yi Fattu don ban san may zance ba ma, Kawai ki fada mai zaifi don ni wallahi, banga abin rufewa ba acikin abin farin ciki, Na dan nisa nace Fattu ai ba wai, ina boyewa ko rufewa bane. A,a kawai dai irin yadda naga rashin imani a fili a gurin Salawatu shi yake bani tsoro, May zata iya yi maki wanda Allah bai tashi yi maki ba Meena, ? Kawai ki fadawa Yaya mukan mu ga irin farin cikin da zai yi yau, Nace sai dai na kira Anty inji abinda zata fada min, kinga naga kamar hakan zai fi, Tace eh gaskiya ki fada mata di, Muji may zata ce akai, nace OK ,, Mu ka dan taka zuwa gurin motar mu, ida su Baba wada ke ciki suna shan kida, Tun wanan lokacin sai na ke jin wani kasala yana rufe min ido na a hankali, Mun biya gurin Anty mai saloon mun gan ta muka dawo, a gajiye gida inda nai sa,a har lokacin Anty Sadiya tana gida basu tafi kauyen da zasu ba,, A gagajiye na is dakina jikina

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL- WALI,,,,

Ni kai na wanan bed rest din da na samu ba karamin dadin jikina naji ba saboda a koda yaushe ina a daki na kwance ban, komai, Ramatu ce na samu take tai maka min da komai, na fannin aiyukan gida, da na keyi, Matsalata guda yanzu shine Yayana Abubakar wanda na ke ganin ya kusa gaza hakkurin shi gare ni, Duk da ina ta kokarin ganin bai shiga bacin rai da ni ba, saboda hakan, Sai ma period din karya da na shiga yi nakan ta cewa ai yazo yadawo, Har nace zan tafi asibiti inga wanan matar inda Yaya ya nuna bai yarda ba sai dai mu tafi tare, Banyi musu ba sai kuma ko may yagani sai cewa yayi mu fara zuwa da Fattu muji may za, ace muna don shi yana da meeting din safe, Wanan daman na samu na tafi, awo saboda lokacin da doctor yace in zo awo yayi, Likita ya tabbatar min da cewa normal abin cikin cikin nawa yake yabani magani da zan dinga sha, tare da kara jaddada min in dan kara samun bed rest din wasu yan kwana ki agai har zuwa lokacin da zan kai four months, Takardan asibiti da maganin da akabani su na yi dubaran gwadawa Yayana Abubakar don ya gani, Abinka da wanda bai saba ba bai san kai ba sai bai gane cewa ai magani karin kuzari ne na masu ciki akabani ba, Shi dai ina nuna mai sai bai karbi takardan ba ma tun da ya gane dai cewa na tafi asibitin har ga sheda, Allah ya saika yai min tare da jadda da min cewa in kula da shan magani na please, Tare da kula da jikina kamar yadda aka umurce ni da yi asibitin Nai hamdallah ga Allah don bai sa Yayana ya fahinci plan di na ba, Abu guda nake dan fahinta irin yadda na ke ganin kaman cewa akwai matsala a tsakanin Yayana da Sadiya, Saboda irin yadda take mai abubuwa da bai dace ba, agidan, Ni dai sai nake ta kokarin nuna cewa ban fahinci komai ba akai,

****** ********** ****** Tsuki taja tare da kauda kai gefen window da take a zaune inda driver sai faman sharara gudu yake da su a titi, Lubuna tace gaskiya Salawatu inda nasan haka gurin nan yake da nisa sosai da banzo wallahi sai dai kizo ke kadai, Ita ma Salawatu a cikin nuna gajiya a fuskan ta tace, ban taba zaton cewa gurin yana da nisa haka ba wallahi, Lubuna tace ni wallahi mamaki kike bani Salawa ace kamar ki duk kin tsaya kin susuce a kan namiji guda haka wai har ya ke ta juya ki irin yadda ya so,, Ki duba fa har aikin da kike yi yanzu kin daina gaba daya da sunan ki na hutun aure har yanzu banga kin fito ba, Kina gida kina ta kwasan masifa da karamar Yarinya, inda ace kin koma ga aikin ki ne ai da duk wanan fitinan bakiyi shi ba, Yaushe ma kike da time din tsayawa wani fitina irin haka ? Murmushi kawai Salawatu tai mata tare da lumshe ido irin na takaici, Ta ce adaidai lokacin da take kokarin gyara zaman ta daga gajiyan da tayi da zama, Cikin murya mai kasala tare da lumshe idon ta a hankali, Lubuna shi fa Oga habit din shi is different from the others,, Dariya Lubuna tayi tare da itama gyara zaman ta acikin gajiya yana kokarin jawo gyalen ta da ta zauna akai, Ke dai kawai kin mutu wa wanan guy din bakya ganin laifin shi ko kadan Murmushi Salawatu tayi mata cikin jin zafin irin son da takewa mijin nata, Sai bayan Sallah la,asar lis suka isa garin birnin Kebbi, agajiye suke gaba dayan su har driver su, Mai yar mashin suka samu suka bukaci da yai masu jagora zuwa Shiyan Sarakuna, Har cikin shiyan mai yar mashin ya kaisu suka bashi dubu daya yana ta godiya da mamakin su, Kwatancen da Bado driver yai madu shi suka inda suka kai har kofan gidan mu driver ya kawo su, Tun suna zaune a cikin mota su ka hango, bawan Allah malam tsoho zaune tare da dattijan suna karatu, Yana saye da farar shadda anyi mai babban riga da yar cikin sa, Kanshi da hulla wanda hullan a daura mai rawani akai, Ksan duk wanda ke a kofan gidan ya na kallon motar don suga wanda zaifito daga cikin motar, Banda malam tsoho wandai baima san da tsayuwar motar ba agurin Sai biyawa wani dan matashin saurayi karatu yakeyi hannun shi yana rike da bulalan fata, Lubuna tace see the wicked old man , No,Wander ashe babban malami ne shiya sa duk abin da mukayi bai kama shegu, Salawatu tace I beg make we, live dis place first before you talk, You know he's witch man, Daga haka suka fifito daga cikin motan inda ake ta mamakin ko wurin wa wayan nan matan kabilan sukazo haka, Wasu yan mata da ke kokarin barin gurin karatun don an tada su suka biyo suna kallon su Salawatu , Lubuna ce tace sannun ku yan mata don Allah muna tambaya ne please , Sai yaran dukkan su su biyu suka dan tsaya daga nesa su na kallon su, Lubuna tace muna son ku kai mu part din mahaifiyar Abubakar wanda ke aiki a Abuja Sai Yarinya tace mijin Meenat din gidan ga ? Duk da maganan ya soshi ran Salawatu amma sai suka daure suka amsa mata da cewa Eh shi din, Su ka ce zo mu kai ku, ba bata lokai su kafara tafiyw su Salawa sukabi bayan su Babu wani mayafin kirki mai nuna cewa akwai macen aure daga cikin su, Hankalin mazan gurin duk ya gare su ganin zasu shige basu gaida kowa ba yasa Baba Buhari dakawa yan matan dake masu jagora tsawa da cewa Ke ina zaku kai su ? Kun san su na halan ? Yarinyan ciin dan rawa murya tace ,a, a cewa sun kayi wai mu nuna masu inda Mama Ladi, Baba Buhati ya kara nanatawa da cewa Ladin shin su suwa na shim ? Walle baba bamu san su ba mudai abinda dai sunka tambaye mu ke nan, Cikin mamaki Baba Buhari yace, daga ina kuke tafe ne ? Lubuna ce cikin karfin hali take cewa, muna neman Mama ce, Matar Abubakar, ce daga, Abuja, ke tafe yanzun nan, Wani, irin kallon ke din a haka din ? Sai da duk suka ji wani irin nauyin kallon da Baba Buhari yai masu,, Shiko Baba wani irin bacin rai ne yaji a lokacin ganin wanan macen wai ita ce matsayin sarakuwar shi matar mai sunan malam, Ganin yadda ya dawo gurin su rai a bace yasa kowa ke tambayan shin su wana ? Cikin wani irin murya ya juta ya na daukan buta don yin alawala ya ce wai ita ta amaryan maisunan malam, Baba Samaila daga gurin da yake ya zaune yana kallon duk abinda ke guda na, tun farko, Yace ke ku tai ki kaisu sashen Ladi din kice bakina, tayi daga gurin mai Sunan malam, Sannu,ku da zuwa sannun ku da hayan a,a kuna tafe, ? Ko,wa yabi su da kallon, mamaki, Yau anyi baki a gidan malam da har zasu wuce, malam zaune a kofa ba su gaida shi ba Lailai ko zamani ya zo da canji sosai, da har an samu sarakuwa agidan malam da bazata iya tsayawa ba ta gaida shi,, Sai faman haraman sallah magrib suke yi a lokacin don, lokaci ya gabato,,

****** ********** ****** Sarama Alaikum, cikin hausan yaren da addini bai wani zauna a zuciyar su ba, Wa ka wanga irin sallaman haka inji Anty Mariya wace tazo gaida mama Ladi, Ganin yan matan nan suna cewa ga sashen nata mu,mun tafi suka juya din wucewa, Lubuna ta ce su tsaya tabasu five hundreds naira, tace su raba, Sai suka ,a a wallah ki bar shi don dai mun gwada maku sashen Mama zaku bamu kudi ? Suka wuce abin su batare da,sun karbi kudin ba da aka ba su, Sallama suka karayi daidai suna shiga cikin part din na Mama Ladi Anty mariya ce tagane su tace kamar Amaryan mai sunan malam, Mama Ladi wace ta dawo daga ban daki tana kokarin zama saman wani dutse da take alawala akai,, Tace suna shin kin kace ? Har kasa Salawatu takai gwiwoyin ta tana cewa Mama sannu da gida mun samay ku lafiya, Tabarma Anty Mariya ta dauko masu daga cikin daki tana masu sannu da zuwa, ta shim fida masu a kofan dakin Mama Ladin, Ta wuce da gudu zuwa sashen baba Hamza don sayo masu ruwan sanyi su sha, Sai wani kalle kalle sukeyi suna wani mayde baki kamar masu jin kazanta ko wari, Anty Mariya wace ta shiga sashen Baba Hamza a rude tana cewa matar maisunan malam ce suka zo yanzu, Matan Baba Hamza su kace wace tace ta karshen mana wanan ma,aikaciyan, Da sauri ta karbi ruwan leda tabar part din zuwa na Mama Ladi, Kafin wani lokaci duk labari ya karade gida cewa matan Yaya Abubakar amaryan shi babban ma,akaciya tazo, Sai tururuwan zuwa gaida su akeyi da kuma ganin kwam irin na mutanen babban gida, Mamakin irin yawan gidan mu, suka farayi shi babban gidane, Sai dai suna ta kokarin gane ko wacece mahaifiyana daga cikin su, Mamana batazo ba saida kwanonin abincin da ta kwashe wanda tasawa Baba shi ta sa a wani sabon kula ta kai masu, Amma basu gane ta ba don duk basu yi tsan manin cewa mama ce ta haifeni ba, Sai da sukayi alawala su kayi sallah kamar kowa, Sannan suka dan zauna cin a binci sai bayan wani dan lokaci maza suka fara zuwa gaida su suna masu sannu da zuwa, Kowa sai kallon mamaki akewa Salawatu don sun ce ta girmay yaya Abubakar nisa ba kusa ba,, Salawatu tace tana son ai masu iso su gaida malam don gobe tun da safe zasu koma insha Allah, Daidai malam din ya shigo gidane aika masu iso gurin shi, Yana zaune ya gaman cin abincin dare tare da matan shi, Suka iso sai wani irin kamahi da karnin man bleaching ke tashi, Bayan sun gaisa ne Salawatu take,cewa dama Yaya Abubakar ne yace tazo ta gaida shi takuma ga yan uwan shi, Daga cikin duhu gurin da malam din yake zaune suka kura mai ido inda suke kallon irin kaman da tsohon yayi da Yaya Abubakar sosai, Waya ta jawo tafara kiran layin Yaya Abubakar din don ta sheda mai ta iso,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull