Tarko complete novel - Chapter 54
Tarko complete novel Chapter 54: Tarko complete novel Chapter 54. ****** ********** ****** Dining ya fara zuwa inda ya bude kulan abinci yaga cewa babu…
2,624 words
****** ********** ****** Dining ya fara zuwa inda ya bude kulan abinci yaga cewa babu wanda ya ci abinci a lokacin, Sai ya rufe ya nufi part din anty Sadiya ya samu suna shafa magani sai faman cewa takeyi wa Ramatu kada fa ki danna min kwarai don da sauran zafi a gurin, Yai masu sannu tare da tambayan ko sun shafa maikama da man shafin da aka bayar ta dinga shafawa idan zata kwanta, Anty Sadiya acikin dan daure fuska tace ai na fadama bazan kara amfani da abinda ya bayar yanzu ba, Don na gane cuta ya shiga cikkin harkan nashi saboda son kudin dan adam, Yaya Abubakar yace duk da na fada maki cewa, kiyi amfani dashi tunda wanda ya bamu da farko munga amfanin sa ina ruwanki da sherin sa ke, badai lafiyan ki akajawa ba kawai, Tace ai nace bazan yi ba don ban mason inji zancen shi sam wallahi, Ramatu ta jefa masu baki a zancen su da cewa haba hajiya kiyi hakkuri da kiyi amfani dashi kamar yadda ya umurce ki da kiyi, Wani tsawa ta dakawa Ramatu inda cikin murya kamar fada take cewa ke Ramatu kada ki soma kice zaki tsoma min bakin ki ga zancen mu, nida mijina, Allah ya baki hakkuri Hajiya dama don naga yana cewa ashafa maki ne shiyasa nace kiyi hakkuri ki bari a shafa maki din,, Ke Ramatu naga fa al,amarinki irin na munafukaine don haka ni ban yarda da ke ba ma sam, wallahi, Innalillahi wa,ina alaihim raji,um, Hajiya mai yai zafi haka har da wanan shedan haka subbahanallah inji Ramatu sai hawaye, masu zafi shar, shar shar, suka zo mata, Ganin haka Yaya Abubakar acikin bacin rai yabar dakin na Sadiya rai a bace batare da yw kara cewa uffan ba kuma, Ina kwance a lokacin ina jin wani irin tashin zuciya na damuna kamar amai zai zo min, Jin shigowan shi a dakina yasa ni gane cewa shine ya shigo a wanan lokacin, Ganin irin yanayin kwanciyan danayi yasa shi, cewa tun kan ya karaso May ke damun ki kuma haka Meenat ? Gab da zai iso gare ni na mike da sauri jikina har yana ciri na nufi bandaki, Na dinga kwarara amai tankar zan shude, a lokacin don sai nake gani kaman zan amaye komai na cikina, Na mike tsaye bayan na dan wanke baki na daniyar in koma daki, Sai na ji wani iri jiwa ya kara kwasa na kan zan fadi,, Ban san cewa Yaya yana tsaye a bayana ba duk aman nan da na keyi sai da nai kamar zan fadi naji ya riko ni ta baya, Dauka na yayi cak a cikin damuwa zuwa saman gado na, Yana jin yadda nake cewa wayyo Allah wai wai ina dafe kaina, Yana tsaye ya tsura min ido yana kallo na a cikin mamaki, Bai min magana basai naga ya juya yafita ya bar dakin ina ta kai na don haka ban tsaya mamaki ba, Bai wani dade ba ya shigo dakin ya na ce min ina card din da kike zuwa asibiti, Duk da ciwon da nake ji sai da gabana ya fadi don nasan yau asirina zai tonu ke nan, Ba musu dole na dauko katin acikin hand bag dina na bashi ya kama min hannuwa na tare da rufo min kofan daki muka fita, Daidai zamu bar get din gidan mu su Baba Wadda dasu Baba Hamza suna zaune suna hira, Suka ga fitowan mu hakan ne ya nuna masu ba lafiya don sun san cewa shi bai fitan dare, Duk suka taso zuwa gurin motan mu suna cewa lafiya dai ko ? Cikin rashin sake fuska kamar yadda ya ke ce masu bata jin dadin jikin tane , zamu tafi asibiti ne Baba Hamza' yace asha Bari mu tafi tare ya bude motan shi da Baba Wadda muka wuto da su zuwa asibitin, Kafin mu bar uguwan Hamza ke cewa Usman don Allah ka kai muna kayan mu cikin gida ko, Yace to yayi yanzu zan kwashe ashiga ma ka da su don muma zamu tashi ke nan, Wayan Yaya Abubakar tai kara ya dauka sunan wace ya gani yaso ya share amma kuma yadda wayan ke ta kuka yana neman agaji yasa shi dauka acikin muryan dakilan ci yace, Hello,, Ta amsa da cewa hello sweet Oga gamu nan tare da Old man zaune, Ki bashi phone din ya ce acikin mamaki,, Sai yaji muryan malam tsoho yana cewa maisuna muna zaune sai ga baki mun gani bamu da labarin zuwan su, A dan dadare yace eh tafiyan nata babu shirine shiyasa baku sani ba, Malam tsoho yace to madallah nan yake cewa Nagode sai ayi ta hakkuri da jama,a da iyali Yaya Abubakar yace ba komai, Salawatu ta karbi wayan tana cewa ok sai mun dawo ke nan, Bai bata amsa ba sai cewa da yayi Ok kawai, ya fara kashe wayan ta bangaren shi kanfin ta kashe, Dan tsuki yaja tare da cewa a lokacin da yake karya kwana, shiga asibitin da zamu Baba Wadda Salawatu ce, ta tafi Birnin Kebbi yau yanzu haka tana can suna tare da malam, Baba Wadda yace may ta,tafiyi haka har can Birnin Kebbi, Ina jin Yaya yai murmushin takaici yana cewa yar rashin mutunci ce nace sai ta roki malam gafarane, Don ce mashi da tayi mugun tsoho shine don bata da hankali ashe ta tafi bashi hakkurin, da nace din, Wanan matar taka mai sunan malam sai kai don daini gaskiya bamu shiri da ita , Cikin magagin ciwon dake damuna nace tunda har ta tafi don ALLAH Yaya kayi hakkuri please,,, Bai tanka ba sai ci gaba da tukin motar da yayi tare da shafan fuskan shi da hannuwan shi yana mai sauke, ajiyan zuciya,
****** ********** ****** Muna zaune a gaban likita bayan yadan duba file dina yai rubutu akai ya dago idon shi yana kallo na yace, Madam na fada maki sai kin bi jikin ki a sannu fa saboda ki samu lafiya shi wanan aman da kike yi ba komai bane don zai zo ya tsaya nan da dan wani lokaci saboda haka sai ki dan kara tsare bed rest din ki, please Nace to doctor na gode yace ba matsala Allah ya sauwaka yanzu , ku sayi wanan maganin don wanan aman da ke yawan damun ki,, Sai dai zakiyi ta barci sosai don maganin yana sa barci ne idan ansha, Ina ganin fitan mu office din doctor na sauke ajiyan zuciya tare da Hamdala na godewa Allah na ,da doctor bai tona min asiri ba, Mun sayi maganin muka juyo zuwa gida inda Yaya ke tambayana cewa, Ko akwai abinda na ke son a saya min sai da na tofar da yawu a tissue nace kaza mai zafi da Ice cream Bayan mun dawo na kara watsa ma jikina ruwa ko zanji sanyi don zafi nake ji sosai, a lokacin, Ina zaune a bakin mirror na ina dan kokarin shafa ma jikina dan mai sama sama, Yaya Abubakar ya shigo dakin yana kallona wani irin canzawa ya ga nai mashi ko ina nawa ya wani cicikowa na kara zama wata fresh, Har ya iso inda nake zaune yana tambayana cewa kin ci naman kin sha magani, kuwa ? Najawo Hijab dina ina sakawa nace yanzu zan sha Yaya, kazar kuma duk ta fita rai na wallahi, Yace sai mai kuma to zaki ci ga abinci can baki taba ba ,na bare, magani nasha na kora da ruwa, Ina kokarin hawa gado ne saboda duk na rasa may ke min dadi shiko yaya yana tsaye yana min kallon tuhuma, ganin yadda na canza a lokaci guda, Da ga inda nake kwance Na gyara juyawa tare da lumshe idona nace O Allah na ,cikin wani irin murya mai ban tausayi, Naji yaya ya kashe minfitilar dakin tare da rufo min kofan dakin dake a bude, Azato na ya wuce ne amma sai naji shi yana hawowa saman gadon inda naji ya rungumoni ta bayan shi cikin sauke ajiyan zuciya, Meenat jikin ki da zafi sosai mana nace cikin dan lumshe Ido, Ban jin dadin jikin nawane yaya duk wani iri nake ji,, Ina rugumay a jikin shi ina mai da numfashi guda guda har barci ya kwashe ni, A cikin barci naji wasu abubuwa da Yaya Abubakar ke min wanda ya haddasa min bude ido na, Jin da yayi cewa na farka daga barcin da nakeyi yasa shi rada min a kunne na da cewa relax, Meenat ba komai zan maki ba, Dole na lafe kamar yadda yace din ina sauraren shi, har wani barcin ya kara kwasa na, Barci shima ya dauke shi can cikin barcin yaji ina ta sheka amai a bayi inda ya tashi da sauri zuwa gurin da nake Mun dawo saman gado naji duk banjin dadin kwanci à saman gadon kasa nake son kwanciya, Gashi kuma na kasa tashi ga wani itin barci da nake ji, Na dora kai na saman jikin Yaya Abubakar yaji jikina duk dumine ya ce subbahanallah sannu Meenat, Na mike da ket don zuwa kasan tie's in kwanta amma na kasa Yaya ne yake tambayana ina zan tafine na nu mai kasa yace ok yadan kamani na sauka kasan yasamin filo nace ya barshi , Ina ta nushi guda guda har barci ya dauke msi karfi wanda shima hakan ya samu ya dan kwanta a bakin gado tun yana kallo na har barcin ya dauke shi,
****** ********** ****** Washegari cikin ikon Allah na tashi babu wanan amman sai dai yawan barci da nake yawan yi, Da kyat na tashi, nai wanka na dan kara jin dadin jikina nafito, zuwa kitchen don in samu dan abinda zanci, Mu kayi kicibis da Ramatu wace, take dauke da ledan kayanta Cikin kokarin kakaro murmushin karfin hali, take cewa Hajiya barka da safiya, Na amsa mata da kyat cikin dan sakin fuska nace barka dai Ramatu anfito tace eh, Idona ya kai ga yar kar kayan ta dake rike a hanuwan ta, Nace sai ina zuwa kuma haka da safe Ramatu ? Ta dan gyara rike jakar hannuwan ta tace Hajiya Meena gida zan koma wanan aikin ya ishe ni gaskiya,. Subbahanallahi may ya sa Ramatu may yafaru ne haka har zaki bar mu,? Bayan kuma ba haka mukayi alkawari da ke ba da farko, Kafintace wani abu Yaya Abubakar yasauko daga saman dakin shi da alama fita zauyi, Hankalin shi bawai a gurin mu yake ba don hannun shi gudayana saye a aljihun wandon shi guda kuma yana waya dashi, Ina kwana mukai mashi abinda yasa shi jiyuwa gare mu ke nan ya dakata daga tafiyan da yakeyi, Mu naji yai sallama da wanda yake wayan sai ya juyo gare mu gaisuwan Ramatu ya fara karbawa , Sannan ya kalle ni cikin wani dan yanayi yace ya jin yai sauki ko kai na daga mashi kawai alaman eh da sauki, Kinci abinci kisha maganin ki na ce yanzu dai zan dafa don yau Ramatu bata samu yi ba Inda Ramatu take tsaye rike da jakar kayan ta ya duba, Sai ga hawaye sharr a idon Ramatu tana kokarin taresu da hannun ta na hagu, May ke faruwa ne Ramatu ? Tambayan da Yaya Abubakar ya mata ke nan acikin muryan shi mai kama da ta rowa, Tace cikin hade yawun takaici, Alhaji tun zancen shafa maganin da kukayi da ita jiya shine har gari ya waye take cewa nabar mata gida Wai kilama har dani aka hada baki don aciwa mahaifiyar ta mutunci, Tsuki naji yayi tare da juyawa da karfi zuwa dakin Anty Sadiya, Ina a tsaye nace mata ta kawo jakan don babu inda zata tafi in ma har tace hakane ai a gurina aka kawo ki ba gurin ta ba ko ?
****** ********** ****** Magana yake mata amma sai take tankar bata ji may yake tambayar ta ba a lokacin, Wani tsawa ya daka mata wanda ya nuna mata cewa ba wasa, azancen sa, Ta san halin shi sarai don takan dade tana bata mai rai yai ta hakkuri Amma duk ranan da taga cewa yana mata tsawa to dole ne ta shiga taitayin ta, Don idan har bata natsuba zata gane kuren ta sosai daga gare shi, Shi mutum ne mai hakkuri sosai a yadda ta san shi, Yanzu ne ma da su kayi yawa har take jin zancen shi akai akai, Saboda can jin yanayi da gidan nasu ya samu na kowace da irin nata halin, Don haka tun wanan tsawan da ya daka mata yasa ta juyowa don tasan cewa ta kai karshen shi, Yace, tambayan ki nake yi mai wanan matar mai tai maka maki tayi maki da har zaki koreta, Cikin dakiya badon taso ba ta bude baki tace haka kawai naga bana bukatan ta atare da ni, Ya ce good amma wallahi ki sani babu wace zata kara wani wahala dake a gidan nan ke har kina ganin cewa kin samu lafiya ke nan da zakiwa wanan matar irin wanan wulakancin haka, To bara ki ji ni bani wulakanta dan adam a rayuwa na , Sanan ban a,zawa mutum laifin da ba nashi ba don haka bazata bar gida ba don ke, Asalima ai ba gurin ki aka kawota ba ko don haka zata zaunada wace tazo gidan domin ta, Tace kana nufin zata zauna da Meenatu wani kallon banza ya watsa mata, tare da juyawa ya bar dakin Sai kuma ya dakata ya juyo a fusace yana cewa zancen kuma da har kike kokarin yadawa ma duniya da kan ki, ke ki sani don idai ni ne bamu maijin wanan zancen a bakina, Don in mahar da gaske ne wallahi nabar mutum da Allah don ni Allah yana tare da ni , Daga haka ya sa kai ya bar dakin a cikin fushi batare da ya juyo ba Muna kitchen yasamay mu tare da Ramatu yace ke daga yau wanan zata dinga zama a gidan nan a matsayin mai gyara ko ina da kuma kula da wasu abubuwa, Don haka sai kisa a kwashe kayan dake wancan dakin na kusa dake, ta zauna tare dake, Godiya Ramatu tafara mashi, tare da kwararo mashi addu,a, Yafara tafiya yake cewa ki tabbatar da cewa kin sha maganin ki a lokaci idan har jikin bai bari ba ki kirani mu koma wani asibiti, Na amsa da cewa to Yaya Allah ya bada sa,a Allah ya tsare ya kare yace amin ciki,ciki, Na juya gurin da Ramatu take tsaye tana share hawaye nace dan Allah dai kiyi hakkuri ko ita ma Anty Sadiya din zata zo ta huce ai, Ramatu tace wallahi hajiya badon ke da maigidan ku da kuke min mutunci ba haka da babu abinda zai sani, tsayawa akan wanan matar, Jiya fa kwana tayi tana surfa min bala,i a kai,, Wai ance, kawai a shafa mata maganin da bata son ashafa mata ajikin ta, Cikin murmushi nace mata yi hakkuri Ramatu bacin rai ne yasa tai maki hakan, Baba Hamza nasa su gyara mata dakin tare da kara tsabtace shi tsab, Tare mukayi girki da ita inda na dauki na Anty Sadiya na kai mata nata daki, Nasan cewa idon ta biyu amma sai ta, lafe tankar mai barci don kada ta amsa min , Nasamu guri na aje mata nafito abina batare da na tsaya wani rigima ba, Ina fita ta bude idon tare da saukowa daga kan gadon ta don ta yi break fast saboda yunwa take ji bata karya ba ita ma, Tun a lokacin tafara data sanin rashin Ramatu a kusa da ita don gashi tana son a daurayo mata cup amma ba halin hakan, Ramatu ce na samu tagyara min ko ina nagida tare da yi muna girki, dare da rana,