Tarko complete novel - Chapter 55
Tarko complete novel Chapter 55: Tarko complete novel Chapter 55. ****** ********** ****** Da safiya suka tashi da shirin son kama hanya don dawo wa Abuja,…
3,763 words
****** ********** ****** Da safiya suka tashi da shirin son kama hanya don dawo wa Abuja, Duk yadda suka so su gane mahaifana acikin gidan mu basu gane ba saboda yawa, Amma sai Salawatu tace wa Anty Mariya akai su su gaida Mama na don basu ganta ba, Anty Mariya tace ai itace wace ta kawo maku abincin da kukaci jiya da dare, Saurin kallon junan su suka yi suna cewa da turo ranci wai kada fa ayi charming din su ? Sai kuma suka murmusa a tsakanin su, sun samu mamana tana gyara ko ina sai kamshin mangyadan da soya wanda zata zubawa shinkafa da waken da ta dafa masu nagida don a karya dashi, Saboda Baba na shi tun da,safe ake mai abinci da zaici kafin ya fita zuwa gurin neman kudin shi, Idan dan abin kwadaine kuma sai a saka mashia kula,yatafi dashi, Cikin mutunci da sakin fuska mama saratu take masu sannu da zuwa, Sai wani yatsune yatsunen fuska su keyi kaman masu jin wari, Babana ya fito daga daki yana masu sannu da zuwa tare da tambaya sauran abokan zama, Basu wani dadewa ba suka fito don dama gulmane ya kai su, Mama Ladi daga gurin da take a zaune take cewa wai shin ku gidan ku har yanzu shiru babu wanda ta motsa Sai dai aita kawo maku kuna ci kuna zubawa a masai, In ta tagidan nan da ake ta faman karerayin wai tayi bari tayi bari, Suka hada ido acikin murmushi Lubuna tace Mama babu fa wani bari da tayi wanan wani salon kissane irin na wanan Yarinya, Mama Ladi mai nema a duhu tace ai ni dama nasani sun daiyi plan ne kawai don ace hakana din, Nan suka shiga,kushe ni da,suka agurin Mama Ladi suna cewa wai duk Yaya Abubakar hankalin shi na gurin na, Ta fara fada tana cewa ai dama nasani wanan mugun irin da aka hada shi da ita bazai gane komai ba balle ku na tare dashi, Maganganu dai suka dauki lokaci suna yi akaina tare da su, Suka bata kudi ita da Baba Buhari amma sai Baba yace su bar shi kawai ya gode, Sunyi wa malam tsoho sallama wanda yakeyi tankar bai fahince su ba, Bayan tafiyan sune gida ya dauki zance cewa aiko Meenatu tashiga uku don wanan matar ai kilama ta girmi Mamana nisa ba kusa ba, Wasu suce ai wanan badai ta haihu ba sai dai don kawai a zauna kawai, Irin wanan zancen ne har yai ta yawo a kwakwalwan Mama Ladi duk hankalin ta ya tashi jin da ta yi , Hankalin ta duk ya daga tana ta tunane kala,kala don fa agaskiya ya kamata ace yanzu anfara haihuwa agidan maisunan malam mata har uku amma shiru haka, Don haka ta dauki waya takira Yaya Abubakar Mariya sarkin fadan ta tana zaune daga gefe guda tana sauraren su, Bayan su gaisa take cewa ta bugo mai don taji ko may ke faruwa agidan shi haka shiru, Cikin rashin fahinta yace ban fahinta ba fa Mama ? Tace ina nufin har yanzu ace matan ka babu wace ko tai batan wata, ne wai daga cikin su, ya yi dan murmushi yace Mama ba Meenatu ta yi wanan ba yan kwanakin da suka wuce, Rufe min bakin ka kajiya narasa ko may kake tsinta gurin wanan yar karamar Yarinya haka, Wai ace yarinya kamar Meenatu tana juya ka kaman dan karamin yaro Murmushi yayi don ya san ina zancen ya fito har Mama ke mai wanan korafin, murmushi kawai yakeyi na takaici tare da girgiza kan shi, Suna gama waya da Mama yace Salawatu hmmm bazai ki canza ba ke nan, Sai kuma tunanen zancen cikin da Salawatu tace mai tanaa shi ya fado mai a rai, To Mama ba,taga Salawat da ciki bane da har ta fada mai haka ? Lalai akwai magana don bai taba jin zancen ba kuma tun ranan da take ce mai tana ganin kaman tana da ciki ajikin ta,, Meenatu ce ta fado mai a rai sai ya tuna irin yadda ta kwana adaren jiya,, Don haka ya kira layin waya na yana tambayana ko nasha magani na, Nake ce mai nasha saura na dare in Allah ya kai mu zan sha, Ya tambaya babu wani matsala ko wani wuri dake min ciwo, Na bashi amsa da a,a babu komai naji sauki sosai yanzu yace alright,,, Mu kayi sallama ya kashe wayan ita ma Sadiya ya kirata yana tambayan ta na ta jikin yadda yake , a cikin muryan ta mara marmari take cewa da sauki,
****** ********** ****** Washegari bayan fitan Yaya Abubakar gurin aiki ba ai wani dadewa ba sai ga Salawatu da su Lubuna sun shigo gidan , Batare da sun yiwa kowa magana ba, suka shige dakin ta, kida suka kunna suk kure karan shi kamar gidan disco,,, Barci na keyi saboda rashin barcin da ban samun yi dadare yanzu sai nake ji kamar mafarkin kida, har dai nakai ga bude idona, Kida ne sosai kamar gidan zai tsage ina son yun kurawa in tashi ne sai ga Ramatu ta shigo dakin dauke da kayan da ta wanke min, Tace Hajiya kin tashi ba ai dole don wanan haukan ai yai yawa, matar wacan dakin ne ta dawo shinesuka saka wanan irin kidan haka, Cikin murmushi nace au Salawatu ta dawo tace eh dazun nan bayan futan Alhaji, Nace barin tafi in gaida ita da dawo wa, Ramatu tace min haba Uwar dakina ai ba,ayin haka, Ko kin manta da cewa da sunan ki tabargidan nan ne wai, Yanzu abinda za,ayi shine kawai duk wani addu,an neman tsari da kika iya sai ki hau fadan shi ga bakin ki kafinkuyi arba da ita, Saboda duk wani sheri da ta kullo tazo dashi ya koma mata, Ramatu tace furzawa yar banza tabbatiyada ta bayan hannuwa ta bare da ita daduk sherin ta, Dariya Ramatu tabani don ganin yadda ta hakikan ce da zance, Takai zaune saman center carpet dina tana cewa wallahi uwar dakina yanzu zama da mutane ya koma sai da dubaru, Kada ki raina zance na juya bayan hannuwani ki tofe yar banza sai ki fure duk wani bakar aniyarta y koma mata, Kin ga kin mata kai kayi koma kan mashekiya ke nan, Baki ta Ramatu ba tunda su manyan matane nayi kamar yadda tace min din tace to madallah yanzu ko zaku hadu duk wani mugun nufinta bazai yi tasiri a kan ki ba, Nace nagode sai ma naji fitan ya fita fin arai kawai nagyara kwanciya na tare da taimakon Ramatu ban fita yin komai a wajen falon gidan ba inda zan iya haduwa dasu, Har suka gama ihuce ihuce su sukabar gidan suna wani irin shewa da tafawa irin na goggagun matan bariki, Muna daki da Ramatu ina shan Faten waken da nace tai min , Ramatu tace yan iska ta Allah ba taku ba tsofin banza kawai wai su yanbariki, Nace kai Ramatu don Allah ki daina kulasu don ba su ko a gabana ni, Tace amma ke kina agaban su ai har ita wacan din mara marmarin, Murmushi nakarayi batare da na tanka mata ba don na fahinci tana masifan jin haushin su, Kada na biye mu shagala shedan ya rude mu muma akan su,
ZEEE MAKAWA YELWA,,
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 6⃣8⃣ ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH - AL -HAMEED
Barkan mu da ganin wanan ranan mai albarka ranan da ta kasance Jumma,an karshe acikin wanan shekaran ta kalandar musulunci, Ya Alkah ka sadamu tarin alherorin dake acikin wanan shekaran, Ya Allah ka kare mu ka yafe muna dukkan kura,kuren da muka tabka wanda muka sani da wanda bamu sani acikin wanan shekaran, Allah kasa muna daga cikin yantattun bayin ka Allahuma Ameen,
Kira gareku yan uwana musulmai abokan zaman median na zauren beibei isah kamar yadda muka sahircewa junan mu Ina maikara baku hakkuri da mudinga hakuri da junan mu akan rashin fahintar juna dafatan zamu kara yafe wa junan mu, Nagode kwarai sa fahintar junan da mukayi saboda gaba dayan mu ba laifin mubane,,, Nagode nagode nagode kwarai,,,,
Yinin Ranan barci nai tayi abina batare da na fito wajen gidan ba, Ganin Salawatu zatai girki a kitchen din yasa Ramatu tatara duk wasu abubuwan da tasan ina bukatan su ta adana, Ta dawo dakina ta zauna tankar wace take gadi na, Bayan sallah la,asar kadan na farka a firgice tunanen banyi sallah ba fa ya fara zo min, a rai, Idona ya kai ga agogon bangon dake manne a dakin naga hudu da sha tara, Zubur na mike da,salati a bakina ban san cewa Ramatu tana dakin ba sai ji nayi tana cewa, Yi a hankali uwar daki na kin san fa bake kadai bace don haka ki dinga yi a hankali don Allah, Har zan shiga bayi sai na dakata najuyo da sauri ina kallon ta a cikin mamaki, Nace Ramatun ban fahinci ki ba nacewa bani kadai bace da kikace, Tai murmushi tace hmm uwar dakina aiko makaho ya lalaba yagan ki haka ya san akwai tsiron Allah a tare dake, Ga shi ko ina naki ya nuna hakan a fili, jikin nawa da tace ya nuna nakai wa kallo ko ina ni banga wani canji da ta tace yayi ba sam, Sai na kallo ta nai murmushi na shige bayi kawai batare da nai magana ba, Awala nakeyi amma ina ta tunanen zancen Ramatu har nafito na tada sallah, Ramatu bata dakin a lokacin da na idar ina zaune ina jan casbi ta shigo dakin dauke da cup din ruwan zafi tana cewa naga ruwan shayi kawai kike so shine na hado maki , Kamar tasan yuwa nake ji ban bata lokaci ba na karba nai bissimillah na dan fara kurbawa ahankali, Nakai rabin cup din sai na dakata na dubi Ramatu nace Ramatu bakinki don Allah don kin san yadda gidan nan yake hakan yasa ko maigidan ban fada mai ba sai in har abin ya tabbata, Tana kads kai tana cewa wanan gaskiyane uwar dakina, Hakika kinyi gaskiya wallahi sosai da wanan dabara taki don rashin imani zai iya sa akawo hari ko kuma mugun baki ya har kai ga yaro tun yana cikki, Nace ashe kin gane tace niko na gane tunda ni, na san abinda baki sani ba, Naci gaba da kurban ruwan Lipton dina ina tajin dadin shan sa, Ramatu ta tashi tana gyara gado da yan goge gogen abubuwa, Ina gamawa na mike don zuwa duba Anty Sadiya, Baki yana mai fadar addu,oin tsarin da na sani nasa kai na fita, A tsakiyan falo mu kayi kicibis da Salawatu wace ta ramay tayi baki, Tana gani na naga tayi wani irin shock kamar ta juya sai kuma ta dan tsaya taci gaba da tafiyan ta, Murmushi nayi tare da ce sannu da zuwa, Kamar bazata amsa ba sai kuma naji tace, Ya gida ? Na amsa da fadar Alhamdullahi, kawai na wuce abina, Da sallama na shiga dakin ta tana tsaye tana kokarin gyara zani gadon ta, Sai na ce mata ina wuni anty ta ansa min a dasashe kamar bata son ansawan nace ya karfin jikin tace taji sauki, taci gaba da abinda takeyi, Sai a lokacin na fahinci cewa fushi fa anty sadiya ke yi dani, Ina tafe ina tunanen ko may ye dalili sai na tuna zancen Ramatu ko ? To ai don zance Ramatu ce Ramatu dai tun farko gurina aka kawo ta ba ta dalilin ta nasan ta ba, So don na rike ta yanzu ba wani abin jin haushi bane inda ba da wani magana a kasa bane,
****** ********** ****** Yana zaune office sai tunanen yadda suka kwashe da Mama yau yake yi, Don yasan sherin Salawatu ne ba kowa yakai sukan gurin mama ba sai ita, Zai ko yi maganin ta don ba zai lamunci mace ta hada shi da mahaifiyan shi ba ko yan uwan shi, To wai ma har may nakewa Meenatu da Salawatu ke ganin wai nafi kulata, Ita Salawatu da ba kwana biyu cif batai request din abu a wurin shi ba, Kuma ko ya bata babu godiya, sai dai takarba ma tana korafin bazasu ishe ta ba, Amma daga Meenatu har sadiya babu wace ke rokan sa kudi indai bashi ya dauka ya bata ba, Asalima ita Sadiya ko dinki bata iya tiwa kanta sai dai idan shi ya dinko mata, su,, Kuma bata sawa don zata iya wuni saye da rigar barci a jikin ta har wani daren, Shi dai yasan abu guda shine ita Meenatu zancen ta duk bai wuce na yan gidan su ba, Zance mutanen gida kuma ai nashine shima don shi take gyarawa hanya, To wanan ne so din da ake nufin yafi gwada mata ko ko may, Yasan cewa Salawatu koda baya tare da Meenatu bazata bar Sadiya ta wala ba agidan don ya riga da ya karanci halayen ta ko, Ita arayuwan ta kanta kawai ta sani kuma inhar son samu ne ta maida shi shanun tatsa, Sallaman malam Abdullahi ne ya katse mashi tunanen da yakeyi yake sheda mai ga hajiya Jummai Dubai nan ta zo, Ya ce ace ta shivo tashigo tana cewa gaskiya kanina naga ka ramay fa ko dai sarakan nawa suna maka rowane, Yaya yai murmushi kasancewar matar suna dan shiri dashi sosai don itace mai kawo masu kaya suna saye a ma,aikatar su, Itama ba wai irin shashashun matan nan bane tana da kamun kai sosai, Shiyasa yadan sake jiki da ita har yake fada mata cewa yana da bukatan ta hada mai kayan irin na lefe,, Take tambayan ko aure zai yi yake ce mata, a ina da mata wace na aura ban mata laife ba sai yake bata dan labarin auren mu, Matar tace gaskiya ya kamata ya hada min tunda ita Salawatu ta karbi kudin tane maimakon lefe, Yau ma da tazo abinda wanda yasaba hutda da mutane kallo guda taiwa Yaya Abubakar tagane yanayin sa na damuwa, Yaya yai murmushi yace Hajiya ai basu bari azauna lafiya, Tai dariyan manya tace, ai dama mai mata sai ya kai ga wanan stage din, Ya ce hajiya yau wanan fitina gobe wacen ciwon ni wallahi abin har ya fara kwance min lissafi na, Sun dan dauki lokaci da ita tana bashi shawaran akan halin kowan mu , Sanna ta gabatar mai da kayan da ta sayo mai tare fada mai kudaden su, Sosai Yaya Abubakar yaji dadin shawaran Hajiya Jumai Dubai, Sunyi sallama inda yasa malam Abdullahi da malam mudi su kwashe kayan zuwa motar shi Yaya Abubakar ya dawo gida da akwatina lates model, Har guda shidda da kit din su Allah ya taimaka har su Baba Hamza da Baba Wadda suka shigo dasu dakina kamar yadda mai gidan ya umurce su da yi, Salawatu ko Anty Sadiya babu kowan su a waje basu masan anyi ba, Anty Sadiya babu kowan su a waje basu masan anyi ba, Tun daga waje kafin ya shigo gidan ya gane cewa Salawatu tana a cikin gidan shi, Yaja ya dan tsaya da mamaki karfin hali irin na Salawatu din, A take zuciyar shi ta fara buguwa atake ya karanto adduan neman tsari daga Allah, Ya karaso cikin gidan a hankali bai ga kowa a waje ba don haka ya nufi dakin Meenatu don yaga lafiyan jikin na ta, Tun da kofa yake jin murnan mu ni da Ramatu wace ke cewa kodai Alhaji yasan da zancen ne yayo wanan kayan haka Ya bude labulen dakin ya gan mu mun a zaune akwatunan suna daga gefe aje, inda aka jera su, Sannu da zuwa mukayi mashi ya ansa adan gajiye yace yawwa, Ramatu ta mike don ta fita daga dakin amma sai Yaya ya dakatar da ita, da hannu yana cewa, No zauna abinki ba tsayawa zanyi ba ai zan fita ne yanzu,, Nadago kai na dube shi ido cikin ido nace Yaya wanan kayan fa haka ? Yaya Abubakar yadan dubecni shi ma sai kuma ya dubi kayan yace lefen ki ke nan ya iso yau, Wani irin duban mamaki nai mai na bude baki kamar zanyi magana sai kuma na kasa yi, Na noke kaina acikin filon dake a kusa dani saboda kunya, Yace sai a kira Anty Amarya a sanar mata yau ba bashin yar ta akai na da akai min tuni ko ? Wani irin kunyan ne ya kara kamani ban san sanda na ce Yaya duk wanan kayan masu yawa haka, Yai murmushi tare da dan lumshe idon shi yana cewa ai,kin fi haka agurina Meenat, Ya juya ya bar dakin cikin nuna jin dadin yadda na karbi kayan acikkn farin ciki da murna ga godiya danayi ba,adadi, Ya na fitowa daga part dina a daidai tsakiyan falo su kayi kicibis da Salawatu ta dauko flask din ruwan zafin shan tea din yaya Abubakar zuwa kitchen, Wani kallo ne ya watsa mata yai saurin kauda kan shi gefe guda, tankar bai ganta ba, Kamar yadda mu kayi da ita hakan ne sai duk ta daburce don ganin irin kallon da yai mata, Dakin Anty Sadiya ya shige abin shi batare da ya karba ma ta gaisuwan ta ba, Yadan jima adakin gutin Sadiya yafito ya shige dakin shi don ya dan rage kayan jikin shi, Ya fara balle maballin rigar shi ke nan Salawatu ta shigo dakin, Ta bayan shi ta karaso tana kokarin taya shi balle aninin rigar, ta shi, Cikin wani murya yace mata stop it please, kada ki fara ki taba min jiki, Waya baki izinin dawowa gidan nan da kika dawo yau din, Kallon shi take ti a cikin mamaki sai taga ya kara mata wani irin kwarjini a fuskan ta, Kuka ta sake a lokaci guda tana cewa, don Allah dai Oga kayi. hakkuri, Bazan iya kara jure rashin kaba atare dani don haka kayi hakkuri ka yafe min bazan sake tayar ma da hankali a gida ba, Kallon ta yaya yayi ido da ido yace Salawa ban san may yasa kike son kawo min matsala da fitina ba a rayuwan gida, Tun sati hudu da kika tafi gidana ya koma min normal babu wani matsala a tsakanin iyalina, Idan har zaki amin ce da duk wani fokan da zansaka maki a yanzu to a shirye nake da nabarki a dakin ki, Cikin sauri Salawatu ke ce wa zan kiyayen insha Allah kuma zaka samay ni kamar yadda kake bukata, agidan nan, Dadi yaji a zuciyar shi ganin yadda ta horu don jikin ta har rawa yakeyi, don kaduwa, da fargaba, Nan Yaya ya dinga kidaya mata dokokin shi tana cewa ta dauka yayi hakkuri da ita please, Tausayi ta bashi daga karshe saboda irin son da take mashi, Amma sai dai ya boye mata ya nuna mata cewa har yanzu fa yana da fushin ta akai, A hankali ta dago kan ta tana kallon Yaya Abubakar tana duban shi hawaye na tsiyaya mata aido, Tana cewa, Sweet Oga ka yarda dani har a cikin zuciya na gaskiya nake fada maka, Yaya Abubakar yadaga idon shi da suke nuna fushi da tsana a gare ta ya kalle ta, da su, Yace mata Idan da hakan ne ai da baki kai sukan wani ba agurin Mama ko,? Kince sai abinda Meenatu tace nakeyi a gidan nan ban ganin kowa idan ba ita ba, Yanzu ke idan ace ki ratse abinda kika fada gaskiyane zaki iya rantsewa,? Ta hada hannayen ta biyu guri guda tana cewa wanan sherin shedan ne amma irin yadda kake tsan manin ba haka bane gaskiya, zamana adakina yafi min zama a gida, Ido yadan tsura mata tankar mai nazarin son gano gaskiya daga gare ta, Ya wuce ta gefen ta batare, da ya kara cewa uffan ba again, Ido Salawatu tabi bayan shi da shi tana kallon shi cikin wani irin yanayi, Wanka ya fada ya fito ya samu ta aje mai kayan da zai canza tare da takalman zama gida, Wanan ranan bamu ga Yaya Abubakar ba a part din mu yazo muna sai da safe ba, Sai washe gari muka gan shi zaune a falo yana kurba shayi a hankali shi kadai saman dining table, Ni kuma na fito don zuwa kitchen gurin Ramatu a lokacin, Kallon guda nai mashi na ga yanayin shi a cikin annuri yake, Ban karaso ba don nasan rayuwan Salawatu bata bukatan mutum ya je kusa da Yaya Abubakar idan tana tare da shi, Don haka, daga inda nake na tsaya nace ina kwana Yaya ? Ya dago ido a cikin annuri yana cewa lafiya kalai Meenat ya kuka kwana, Na amsa da fadar Alhamdullaj na juya abina zuwa kitchen, A lokacin Salawatu ta iso gurin shi a cikin wani ado da kwalliyan da ta caba, A take fuskan ta ya canza yanayi ganin da tai min da Yaya Abubakar duk da banzo kusa dashi din ba Ta daure fuskan ta daga yar annurin da ta fito dashi daga dakin ta, Nagane nufin ta amma sai na nuna tankar ban fahinta ba, Don ita fa haka take saboda duk cikin mu tanawa Yaya Abubakar wani itin mugun so, Wanda ke haddasa mata mugun kinshi sa idan tagan shi a tare da wata daga cikin mu,, Ban fito ba don ma kada in katse masu jin dadin su duk da naga cewa shi kan shi yaya akwai dan canjin yanayi a tare da shi, tsakanin daren jiya zuwa safiyan yau,,, Ban kara gaskanta zargina ba sai da na tsinkayo muryan Salawatu tanawa yaya Abubakar adawo lafiya, Abinda Yaya bai taba yi muna tun dan zamana dashi ya fita bai muna sai ya dawo ba,, Abinci nake ci a kitchen din don da yunwa na kwana ranan, Hakan yasa na kasa hakkuri har Ramatu ta kawo min, Daga inda Ramatu take a tsaye tana tsiya min ruwa ta hango Salawatu tana murmushin keta, ita kadai tana kada kai, alaman tayi nasara, Gurin da nake tsaye ina kai spoon din indomie a bakina da zafin shi Ramatu ta kalla tace min Uwar dakina mu tafi daki ki karasa acan don nan din a tsaye kike, Ban faye musu ba nabi zancen Ramatu muka koma daga daki alokacin Salawatu ta dan shiga dakin ta, Ramatu tsohuwar yar hannu ce don haka tasan makircin kishiya kamar may fa, Zama tayi ta dinga jana da hira har naci nai kat na sha ruwa tare da magani na, Ban dauki wani lokaci ba mai tsawo barci ya kwashe ni ta yi murmushi ta mike daga gurin da take zaune Ta fara gyara min ko ina taja min kofan dakin ta rufe don gudun kada tana daga waje ashiga min dakin,