Tarko complete novel - Chapter 62
Tarko complete novel Chapter 62: Tarko complete novel Chapter 62. Kai tsaye part din mu su ka nufa shida Aliyu, sun samu su Mama tsatsaye akaina, Har dakin…
4,596 words
Kai tsaye part din mu su ka nufa shida Aliyu, sun samu su Mama tsatsaye akaina, Har dakin suka shiga duk kan su ganin yadda nake a kwance tun daga kofa yake min wani irin kallo, Ganin su Yasa su mamana wani dan kamay kamay cikin jin kunya suke gaisawa da shi, Shima yana gaishe ta da cewa mun samay ku lafiya ya mutanen gida, Hankalin shi yana gurina don haka bai damu da cewa suna dakin ba sai kokarin dan rankwafowa yakeyi gareni yana cewa May ke damun ki ne yanzu wai ? Nace ba komai kawai dai ina son dan hutawa ne ko zan daina ganin juwan da nake ji, Ki samu abinda kikaci idan bai bari ba sai mu tafi asibiti ke nan, Tare da yaya Ibrahim suke don haka yafita dakin yana cewa mamana ta samo min abinda zanci yanzu, Daga gurin da nake kwance nace kamu zansha, Kamu, kuma nace eh kunun koko nake son sha, yanzu, Yaya ya kara sheda min cewa naci abinci aga yaya jikin nawa yake sai asan abinyi, Daga haka su ka fita daga part din mu zuwa cikin gida inda mutane keta yi mai sannu da zuwa, Bayan nasha kunu tare da hade magani na sai wani barci ya dan kwasheni, Ban farkaba har sai bayan sallah magrib sanan na tashi, Mama da sauran yan uwana suke ta faman yi min sannu da jiki na samu nakai zaune da kyat daga gurin da nake kwance, Muryan Babana ne naji daga kofan mama yana tambayan cewa na tashin, Nace na tashi Baba mun samay ku lafiya ko ? Yayin da shi kuma Baba yake cewa Yaya jikin naki meenatu na ansa da cewa Alhamdullahi Baba naji sauki, Mikewa nayi zuwa ban daki nai alwala tare da zuwa tadda sallah A gefen barandan dakin babana na hango kayan tsaraban mu an jibga su agurin, Mamakin ganin su a gurin nayi don ni a zatona ai part din Mama Ladi za a kai su, Na fito muka kara gaisawa da babana wanda yake ta nuna jin dadi gani Sai tambayana bayan rabuwan mu yakeyi tare da tambayana labarin mutanen gida Uncle dina,mun dauki lokaci da mahaifi na muna hira, sai na Namike tsaye na jawo mayafina ina sabawa akaina nacewa yar kaunar ta, tazo ta rakani cikin gida in,gaida mutanen gida, Baba yace baki bari har zuwa safe idan kinji sauki sai kije ku gaisa da su, A,lokacin guda ni da mamana har muna hada baki gurin cewa bari dai in tafi ingaida Mama Ladi don gudun laifi,, A cikin wani murya a hasale don jin haushi da takaici Baba na yace Ladin may can inji babana ya fadi acikin fada bata da lafiya dole ne, sai ta tafi gaida ita a hakan, Mama tace ance tun dazun fada takeyi wai yar Baba taki zuwa gaida ita, Ita ta dade bata kai safe tana fada ba inji baba ni dai bance komai ba jiki ba kwari na kama hanya,,, Ina jin Mama na nacewa duk fa wanda yazo dubata sai yace ashe ma jikin sosai ne shine, Mama ke cewa ta can kwance don ta zama yar mulki yanzu wai har wullakancin da nake wa Yayana shine zan kawo gare ta, Nidai murmushi kawai nayi don jin may mama ke fada wa Baba abinda mama ladi ke fadi,
Tun daga nesa na gane cewa akwai mutane a part din na, mama Ladi saboda hayaniyan da na keji na mutane, Tun daga farko shiga part din nake ta faman kwada sallama amma sai hayaniya suke yi ba sa jin na,, Da Sallama na shiga har kofan dakin wanda tun kafin na kaiga karasowa nagane cewa ita da diyan tane adakin, lokacin, Sakon kamshin dana aika masu ne ya daki hancinan su a lokaci guda duk sai suka juyo kofan dakin, su na kallo na, Na kutsa kai dakin bakina dauke da sallama a cikin sa,tare da jefa masu kalman shahada, Gaba dayan su idon su yana akaina sunyo min caaa dashi daga uwan har yayan suna kokarin ganin ya nake, ? Wasu kuma suna son ganin suturan dake ajikina halinsu ba bako bane gareni don haka sai ban damu ba, A can saman gadon dakin mama na hango Ànty Sadiya kwance ta basu baya tana waya, Na gaida su inda wasuke min ya jikina sai dai ita mama ban tsanmani ta karba min gaisuwan ba ma, A,a Meenatu ta shin Meenatu mutan Abuja ke tashi? Ace kina can kwance jikin ya tabu maki tun hanya ? Murmushi nakwyi yayin da nakai gurfane a saman tabarman da suke zaune akai na gyara zama a gefe guda, Sai nashiga gaisawa da su duk da na fahinci irin mugun kallon kurullah da suke min, Na jajanta masu akan abinda yafaru da anty tare da fatan Allah ya bata lafiya, Daga gurin da mama take takecewa ai abin farin cikina don karuwa tasamu gashi ta aje min yar jikayan Mijin ta bai ciyar da ita ga banza ba aitunda yaci riba zama da ita, Bata zauna tai ta raruma nai ba tana aikowa iyayyen ta dasuwa, Wayana dake a hannu na yai kara gaba dayan su suka kara zubo min idonuwan su ,,suna saurare na, Don su gane wanda nake magana dashi yasa ban fita daga dakin ba , Muryan Yayana ne yake magana, Tambayana yayi cewa ina ina ne nace gani nan nazo gaida mama, Sai yake tambayan naji saukine dana fito sai cewa nayi naji sauki yadan lafa min yace inzo yana part din malam tsoho a sanyaye na amsa mashi da fadar to ,, Ina gama wayan anty Mariya tace Meenatu sai kace mai laluran ciki, haka, ? Mama ba nauyi ko kunya tace ciki ina matan kwarai ma basu yi ba balle,, Ai sai dai ai takaryan shi amma karyan mutun yace zai hada dani ban gaiyyace shi a cikin zuria na ba, Haba haba mama ina wanan zancen kuma yafito daga bakin ki inji anty , dake kokarin dauke plate da alaman wanda su anty Sadiya su kaci abinci ne dasu, Murmushi kawai nayi daga gurin da nake tsaye ban nuna ma dani take zancen , ba Ganin da mama taga nayi na mike da alaman fita zanyi a lokacin, yasa ta cewa,, Ke Sadiya ai gara ki shirya ki bi mijin ki ku tai zuwa masauki, Don kin san iya duniyanci na iyasa a tafi abarki a nan, don ba kunya anka gada ba Murmushi kawai nake yi tankar bada ni Mama kezancen ta ba , Nai masu sai da safe nafito daga dakin jiki a sanyaye saboda irin kalaman mama agareni Ina tafiya ina tunanen yaushe wanan kiyayyan zai gushe a tsakanina da ita,, A iya tunane na ni dai banga abinda muke mata ba wanda yai zafi haka, Gashi kuma Allah da ikon shi har zamu hada jini da ita yadda bata so,, Har na kai part din malam tsoho ban kai karshen tunane na ba nan na fara gaisawa da matan malam tsoho ida n su ke min sannu da zuwa da kuma yaya jiki don zuwa yanzu kowa nagidan yasan nazo ba lafiya Nasamu gefen tabarman dasuke zaune nazauna ina mai kara gaida malam tsoho shima anan yake min ya karfin jikin na,ansa acikin kamala dacewa naji sauki, Tausayin yaddanake malam ke ji don haka yake cewa Yayana kutashi ku tafi don ta huta ,,, Yace wa Yaya Abubakar Kasan irin yanayin da take ciki may yasa ka zo da ita ai da sai ka barta gida, ku kuzo kawai, Tafiya da mace mai ciki irin haka ai hatsarine sosai, Cikin mamaki Yaya Abubakar ya yace ciki malam tare da daga kai ya dubeni, Ni kuma sai nai saurin dukar da kaina kasa tare dan wasa da gefen tabar da nake a zaune,,,,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 7⃣2⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL MU,HYI,,
A cikin tausaya murya da marairaicewa, nake cewa Yaya Abubakar, don Allah su tafi da Anty subar ni in dan gana da mahaifana, har zuwa gobe idan naji sauki,, Sai da ya dan zubo min ido wanda duk da a cikin duhu ne amma sai da nasha jinin jikina sosai, don tsoron may zaice, Sai can naji yace OK hakan kuma fa yana da kyau don haka mu zamu tafi , Malam tsoho wanda ke daga gefen mu tankar baya jin may muke cewa saboda yadda muke maganan ba lalai ne yajimu ba,, Cikin mikewaa irin yanayi na wanda ya gaji yake cewa yayin da yake mikewa, Tau malam ni zan tafi masauki ke nan sai dai da safe idan Allah ya kaimu zan shigo, Malam ya amsa mai da cewa to maisuna Allah ya,bamu alheri a huta gajiyan hanya ko,,. Zuba mai ido nayi daga gurin da nake zaune saman tabar man malam, Malam tsoho ne ke cewa ita anan zata tsaya ko don naga bata tashi ba, Yaya Abubakar yace bazata ba zata tsaya su gana da yan uwane, Nima mikewa nayi don in taka mai daga nan nashige part din mu, Kamar yadda ko wani babba gida irin na hausawa yake sassa daban daban wani akewaye wani kuma a bude haka gidan mu yake don yawa sassa shima, Saboda nazo ban jin dadin jikina yasa ban leka kowani sashe ba sai namu dana Mama Ladi, kawai ko ita daurewa nayi don gudun fitinan ta, Sai kuma yanzu da na shigo na malam tsoho don ansa kiran mijina, A hankali nake bin shi a baya a lokacin da yake tafiya,, Saida safe iyalan malam ke muna a lokacin don sanin cewa tare zamu tafi, azaton su, Mun kai kwanar da zai shigar da ni sashen mu Yaya ya ja ya tsaya tare dan juyowa yana cewa tau kikoma ki kwanta nasan cewa yanzu Baba ya dawo amma bazan shigaba saida safe idan Allah ya kai mu,, Nace zan fada mai insha Allah saida safe ke nan, in Allah ya kaimu, Nikan daga haka na shige abina part din mu idan na samay su zaune suna kallon TV a yar varander sashen mu, Nai masu sannu na shige dakin Mama a zaton su zan fito ne ayi fira amma sai naji sanyi nakeji don haka kawai saina samu guri na kwanta kawai, Idona biyu amma zakace barci nakeyi nan ko tunane na keyi yadda malam tsoho ya fahinci cewa ina da cikki wai, Muryan mamana naji a dakin tana cewa, bazaki kara cin komai bane kuma, Na bude idona da su ke a lumshe nace ban jin yunwa yanzu Mama kila sai zuwa dare, kadan,, Yanzu banjin ci komai a raina ,zama naga mama tayi kusa dani tana mai tsura min ido abinda yasani kokarin kai wa daga zaune ke nan, Kwanta abinki nima fita zanyi Mama tace min sai kuma naga tadan maida yanayin fuskan ta a dan daure tace, Yar Baba yanzu cikin ki wata nawa ke, nan ? Da sauri na dan juyo na kalli Mamana sai kuma nai saurin dukar da kaina kasa, Bance komaiba sai itace ke ce min ya kai wata biyar ga yadda nagan ki ko ? A hankali na daga mata kai na bude bakina da kyat nace a sanyaye kila zai kai haka din , ko yafi, Kamar zata wuce sai kuma ta dawo ta tsaya ta jefo min tambayan cewa, Ya akayi kowa bai san zancen cikin ba don banji a na maganan hakan ba in ba da ki ka zo kowa ya gani ba,,, Da kyat na bude bakina nace ni ban fadawa kowa ba cewa ina dashi, Da sauri mama tace har da shi mai sunan malam din baki fada mai ba kike nufi, koko shima ya boye muna ne kamar yadda kika boye ke, Nadan marairaice murya a hankali nace mama ni ban san yadda zan gaya mashi bane ai, na fada tare da dan turo bakin shagwaba,,,, Ido na ga ta tsura min kamar zatayi magana sai kuma tai shiru yayin da tafara tafiya tace Allah ya Rabaku lafiya, Ban ansa a fili ba mama taji ,,amma a can cikin zuciya na na ansa da cewa Ameen ya Allah, Na koma a hankali na kwanta zuciyana cike da tunane da kuma fargaba, Don nasan cewa kafin mu koma sai Yaya Abubakar ya samu labari kilaa, Aikuwa ban san yadda zan kalleshi ba don gaskiya, ban san abinda zan ce mai ba, Da irin wanan tunanen barci yai awon gaba dani ban sani ba sai kusan asuba na farka da wani irin yunwa a tare da ni, A hankali na bude idona inda na fara raraban ido a cikin dakin , Wanda hakan ne ya sani tuna cewa, a gidanake kuma a dakin mahaifiyana, Hankali na dan yunkura nakai zaune, tare da lalubo wayana na kunna don inga haske a lokacin, Flask ne nagani a kusa dani da bread da sauran kayan hada tea, har da cup, da ruwa leda biyu, Na sauko a hankali na fara kurkure bakina sannan na zauna na hada tea din, Zan fara sha ke nan naji muryan mahaifina ta window dakin mu yana cewa kin tashi Meenatu ya jikin naki nace naji sauki ba, Yace to ki sha tea din sai ki kwanta kinji Allah ya sauwaka, Nace Ameen Baba nagode, Yana wuce, wa na sauke, ajiyan zuciya Baba na ya bani tausayi don Alama ya nuna min cewa ya kwana yana gadina ke nan, Mamana ce ta shigo dakin a lokacin jikin ta yana saye da hijab har kasa, Tace kin farka yar Baba kin hada tea din ne ko nace a hankali eh Mama nagode, Tace ai kamar Baban Baban ki ya sani cewa zaki bukaci shayin fiye da abinci da dare shine yace a sayo maki, , Na kai cup din tea a bakina na dan kurba a hankali, sannan nace haka nake a gida wallahi, Ko naci abinci bana koshi sai wani irin yunwa ya dinga damuna tankar banci komai ba, Cikin murmushi Mama tace badole kici abinci ba tunda bake kadai bace, Sai na maida kallona a gurin Mama na don jin may tace, Sai kuma naji tace gaskiya yar Baba banji dadin rashin fadawa mijinki zance juna biyun ki ba, Idan har zaki samu abin alheri haka baki fada mai ba towa kike ganin cewa zaki fadawa, Fuskana acikin yanayin damuwa nace mama ni bawai naki fada mai don wani abu bane sai kawai don irin mutanen da nake zaune da su, Sam mama wallahi babu yarda a tsakani na da su, Idona ya kawo kwalla na ci gaba da cewa, mama duk irin halarcin da nake kokarin yi masu sai sam babu yarda a tsakani na dasu, Murmushi naji tayi tare da zama a gefen gadon da nake tace, Laila kurciya, ke da har kike ganin cewa zasu yarda da ke, Ai kamar yadda kikasan cewa babu yarda a tsakanin ki da su To hakanen ma suma babu yarda a tsakanin su dake don duk abinda kikayi masu na alheri sai su dauka cewa da munakissa kikai masu shi badon Allah bane, Tace Allah dai kawai ya kare muna ke daga duk wani sheri mutum ko aljan Mama tace balle irin yadda naga mijin ku yana nunawa abinsa kanki babu ko boyo a cikin sa, Tsaraban da kukazo dashi fa dazun duk gaba daya cewa yayi wai a kawo nan na ki ne wai don shi bai zo da tsaraba ba tunda ba mace yake ba, Kin san halin Mama Ladi wurin fitina ance tsaye tayi tanacewa wai akawo komai a part din ta shi kuma yace tunda bashi ya sayo maki ba dole a nan za,a kawo, Wadda dayake shima ya fita iya fitina yace baza a kawo mata ba tunda an fada mata mai su, Dole tana gani Wadda ya sa yara suga shigo muna dashi nan a katara su kin gan acan kofan dakin babaki a ajiye, Ga shi ba ke kadai ce yazo dake ba balle yace akawo maki a nan, ai ko tunda da uwargidan shi yazo ita kuma din yar gari ce ai, Kinga hakan ne yasa surutu duk ya zagaye gidan nan da daren nan cewa wai kece yar gaban goshi sa ke nan, Nace indai Yaya ne kowa ar gaban goshin sa ce akwai dai wani dalilin da yasa yai hakan Na kurbi tea na nace Mama ni azatona ai akwatina kawai za,a kawo min nan din, Ai da da,fa yanzu ance Mama Ladi tace wai ai don sheri ki ka ki sauka a dakin ta daga yanzu a dakin ta zaki dinga sauka, Murmushi nayi nace ai babu damuwa dama uwatace ai, Mama tace zancen mu yazo daya da ke ke nan don nima hakan nace Mama tace, dama ta daine cewa bata son zaman shi da ke don dai ga shi kuma Allah ya kawo alheri a tsakani sai muga yadda zatayi, Don har gobe tana bakan ta na cewa wai sai ya sako muna ke, kin dawo, gida, da takarda Naga mama na ta sake wani dan guntun murmushi tace da farko har shedan yaso yasa mu biye mata dagani har mahaifinki, Amma tunda malam yai muna nasiha akan cewa mubar wa Allah al,amarinsa, Kinga ashe da mun bi ta kan,ta da duk mun zama shedanu akan hukuncin ubangijin mu, Don wanan rabon da yaya zamuyi da alhakinsa tunda har akwaishi, Murmushi nayi don jin may mama tace don nasan tadai fadi ne ina Yaya Abubakar zai iya sakoni, Gashi kuma da ga baya duk irin kaunar da mijin ki ke maki duk yana a kunnuwan mu, Bamuba ma duk wani wanda ke gidan nan yanzu ya fahinci, hakan don kinga ai da can mai sunan malam bai damu da kowa ba, daga cikin iyayyen sa, Amma yanzu gaskiya kowa agidan nan yana alfahari da shi babba da yaro, Don yanzu haka baifi sati uku ba da ya turowa kowa da dubu dariri wai su sayi abinci, Kinga shi mahaifinki da hamsi yabashi,aiko kinga dole su san cewa kin zamo wata babban hakankan TARKO agare su,, Sai naji tayi shiru tare da girgizan kan ta acikin takaici, Tace Yar Baba nida mahaifinki ka dai sai gwagon ki muka san irin halinda muka shiga a lokacin auren ki, Nayi kuka sosai akan wanan hadin da malam yayi a tsakanin ku, da mai sunan shi, Ba,don komai ba sai don sanin cewa mai sunan malan dan matar da bata kaunar mune a gidan nan, ne Hakan yasa tun da malam ya bamu magana na fawalla wa raina hakkuri da kai kukana ga Allah nai ta rokon Allah ya kawo mana alheri ga ala,amarin Kinga kuwa Allah ya karba muna don yau mu dai Alhamdullahi don kin zama abin alfaharin mu, bamu kawai ba har ma kowa sai dai makiyan Allah, zai ce bai gode ba, Don har yanzu nasan akwai wa yanda basu kaunar auren ku a gidan nan, Don basu da aiki sai zuga mama Ladi kawai da su keyi don ta dinga hauka abanza tana cin mutunci Don dai babu yadda zata yi da ikon Allah don ya riga da ya hada zuri,a a tsakanin ku ko Shiru nayi ina sauraron mama a lokacin da take cewa yanzu gashi har da rabo wanda Allah kadai yasan iyakar sa,,, Shiyasa aka horemu da cewa duk abinda kagani yazo maka arayuwa to ka rungumi wanan abin maikyau ko mara kyau, Mutum dai ya roki Allah ya mayar maida shi alheri, Na amsa wa Mama da kada kai tare da cewa a çikin natsuwa hakane Mama, Muryan Baba mu kaji yana cewa yau dai Saratu bazaki bari yarinyar nan tai barci ta huta ba, Gashi dama jikin nata ba lafiya amma kin tsare ta da surutu haka, Nace Baba nayi barcin ne har ya fita min a ido ai shiyasa, Yace to ta dai barki ki huta don Allah saboda kina bukatan hutu sosai kada kuma ajawo maki wani sabon ciwo, Daga ni har mama mun bi umurnin Baba inda ita Mama ta tafi ta daura alwala, don yin Sallah nafila, Daga gurin da nake a kwance na ji ladanin massalacin kofan gidan mu ya fara, kiran Sallah, Shedan sai kuma yaso ya samu sa,ata don sai a lokacin na fara jin barci a idona, Muryan Mamana naji tana cewa ke yar Baba ki tashi kada kiyi barci sallah asuba ya wuce ki, Badon naso ba idona tab da barci na mike zuwa yin alawala don in bi jam,i, Bayan na idar da salla na koma na kwanta don indan hantse,kadan, Sai gashi nayi barci mai nauyi har zuwa karfe goma na safe, Ina tashi na nufi bandaki inda ina tace min ankai min ruwan wanka nayi, Ban dau lokaci ba na shirya acikin wani koriyar atampan super wax sabon dinki wanda akaiwa dinkin redemaid kuma ban taba sakawa ba ajikina, Dinkin wanan kayan yasa dan cikina fitowa filli dan dagwas ya zauna min , Mayafin da na tanadar wa kayan na yafa tare da saka plat shoes a kafana, Na samu Mama da yaranta da, da suka kwana gida da ita, don nisa basu koma gidajen su ba saboda ganin dan uwan su yazo,, Tun shiga ake min wani irin kallon don dama jiya ganin dare su kai min niko ko ajiki na dai gaidasu a mutunce, da girmamawa, ban wani dade da shiga ba part din Sai ga bread mai yawa, Yaya Abubakar ya sayo yace a kawo a hada wa kowa breakfast, di shi, Ina jin lokacin da suke tambayan Mama ko a diban ma mutanen, gida ne ? Amma sai mama tace wai a,a ahada shayin gaba daya abawa kowa, Abinda mama bata sani ba shi ne duk part din gidan nan ranan ba wanda Baba Wadda bai kaiwa bread da kayan tea ba, Sai bayan ta hada aka jawo wani tsoho cup duk datti yai mai kanta aka zuba min wai ga nawa, nai murmushi nace na koshi Baba, ya sayo abun kari mun karya ko, Sam hankalina baikai ga Anty Sadiya wace ta nade a cikin tulin kayan dake saman gadon mama ba tana barcin ta, Sai gab da zan fita naji Anty Mariya na cewa wai atada Sadiya ta karya ne ko ? Sai wanan lokacin na farga da cewa tana cikin dakin ashe bata bi yaya Abubakar masaukin shi ba,,,, A part din Baba musa na samu su gwago da matan shi a zaune, suna raba bread din da aka kawo masu, Don ita gwago ita ce ke zama da Anty Samira asibiti, tare suke kwana sai da safe take dawowa gida, Da murna gwago tarbe ni tana cewa ashe na kusa zuwa zaman abuja, banda labari, Aminatu kin tsufa ne haka ? Matan Baba musa ce ke tambayan gwago ko may,za ta yi acan gwago tace idan Allah ya sauke muna Aminatu lafiya mana, Da sauri suka juyo gaba dayan su suna kallona a cikin mamaki sai a lokacin ne suka hankalta da cikin dake a jikina , Nidai ban wani zauna ba na juya na nufi sauran sasssan gidan don na gaida su sai faman ya jiki suke min da kallon kurullah,, Anty Aisha da Anty Nafisa da sauran yan uwana sai farin ciki mu ke da ganin junan mu ida suke kallo na acikin sha,awa,, Na dade sosai a gurin malam tsoho muna hira idan yake bani labaran yan uwan shi, Da irin yadda suka bashi baya don baida hali shi a cikin su, Malam yace duk hakan bai sa na damu ba Aminatu sai ma karamin karfin imani da haka yayi saboda nasan cewa Allah bai manta da mu ba, alokacin ina zaune da albarkan arzikin haihuwan da Allah yai min,, Yanzu sai gashi Allah bai nufi in gyara gaban gidana da kaina ba, Bai kuma ba wani daga cikin diyana halin da zasu iya yimin hakan ba , Yau sai gashi alkawarin Allah ya cika jikana yazo yasa an,buge a cikin yan kwanaki a gama komai lokaci guda, gida ya koma kaman ba gidan malam Manya ba, May zanyi ni inba in godewa Allah ubangiji Subbanahu wata,ala ba dawanan nan ni,iman da yai min, na samun jikoki masu albarka kamar ku, Na ansa dacewa kwarai malam gaskiya hakana ne imani da tawakkalin bawa bai tabewa a banza insha Allah,, A nan part din malam gwago damu takara samuna zaune da malam ya bani Masa da zuma ina dan ci a hankali, Bata ko kaiga zama ba sai ga su Yaya Abubakar shida Aliyu da Baba Hamza' ya take mai baya, sun shigo har ciki gaida malam, Duk a gurin suka samay ni zaune ganin su yasa na dan juya ban wani fuskantar su sosai, ina dan dangwala zuma a hankali ina lasa, Acikin gaisawa gwago ke cewa kai Aminatu zaki ko ? Sai gurin haihuwa ki ya bawa aya zaki, ? Kaina aduke nai murmushi kawai bance komai ba, Sai malam tsoho ne yace mata ai zuma baiwa mace mai ciki komai illa ma ai ana son su shashi sosai duk safe kiyi bissimillah kafa uku ki lasa, Saboda samun wankewan kwakwalwan yaro da mahaifan mace, Yaya Abubakar shi sai dariya suke bashi don ya dauka zance ne irin na mutanen mu kawai Don su hausawa da anyi aure sai zancen haihuwa kuma, da anga ankwana biyu babu ciki anfara zancen ke nan, Don wata ko bashi auren da akaci ba,a biya sai kuma ashiga na haihuwa, Gwago Damu tace maisunan malam ashe yar tawa ta tsufane haka ai,dazu nake cewa nice zan tafi zama can birnin taraiyan don kula da maijego da jaririn ta, Sai lokacin ne malam yace ni ai banso ace yadda Aminatu take haka ba ya biyo hanya da ita ba Ai da barinta kayi har in zata haihu sai kuzo tare zaifi,,, Gaban Yaya Abubakar ne ya ba da wani irin a lokaci guda don haka da sauri ya,daga kan shi ya dube gefen da nake zaune, Kamar gizo ya fani a idon shi don inba dai idon shi ke mai gizo ba to lalai kam Cikine kuwa girke zama das a jiki, sai yake ji tankar mafarki yake yi na wanan zancen, Kai na yana kasa don sai nake jin wani irin kunya ya rufe ni sosai a gurin,, Ya Abubakar ya watso min wani irin kallon mamaki wanda ya ma kasa iya boyewa mutane irin kallon, da yake min, Muryan gwago Damu ce ke cewa, ni dai malam idan za,a zama nice mai zuwa Don nasan yanzu nuna min baranci za,ayi, ace bani ce zan tafi ba, Malam yace ai dama du ku huta don kinga dai bata da wani nisa a hakan don haka nasan ba lalai bane ko ta koma ko kuma ba adauki lokaci ba ya dawo da ita gida don dai gaskiya bazan so ace tayi haihuwan farko ba,a birni, Gaskiya kuma malam inji gwago tace don dai ma anan gida zaifi dadi, Gaza zama nayi saboda abinda nagani a idon Yayana a lokacin don haka tun bai fashe ba na mike ina cewa Baba Hamza ya bakunta da kewan Maman Bi,u,,, Malam wanda ya ga na mike nabar Masan da nake ci ya daga kai ya kalleni, Yace ina kuma zaki tafi baki kare cin Masan ba zaki bar shi a nan nai murmushi kadan nace na koshi ne, Malam ya ce ja ira ke dai kice kunya kawai don kinga mijinki gurin bazaki ci ba ko Ina nan tun cikin waya kika damay ni da zancen Masa da zuma kike son ci,,, Barin sa a biyo ki dashi shiyan ku ai kyaci a can idan kin tafi,, Ya kira daya daga cikin yaran da ake tayar wa a shiyan shi yace tabini da kula masan sashen mu,,,