Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 63

Tarko complete novel - Chapter 63

Tarko complete novel Chapter 63: Tarko complete novel Chapter 63. ****** ********** ****** Inna shiga na samu Baba da Baba Buhari Baba musa da Baba Wadda a…

3,180 words

****** ********** ****** Inna shiga na samu Baba da Baba Buhari Baba musa da Baba Wadda a part din na mu da alaman kayan tsara ban da mu kazo da su ne su ke rabawa, Don ina jin Baba Buhari na cewa ai Wadda ka kyauta da ka kawo kayan nan, nan don da sun shiga hannun Ladi babu wanda ya isa ya raba shi sai dai su lalace tana kallon su,, Kasa na gurfana ina gaishe su a cikin ladabi baba musa ke cewa masha Allah Aminatu ashe karuwa mun,ka samu haka Allah ya raba ku lafiya ke ji,, Na mike kawai na shige daki abina ina jin Baba Buhari yana cewa, amma abin ya bani mamaki don dai ni ji nayi kwanaki ana cewa tayi barin cikin ko? Kafin wani yai magana daga cikin su Yaya Abubakar ne ya shigo part din mu sai dai kuma ganin su Baba su na ciki ana kasafi sai kawai hakan ya kare mai ahurin abinda yazo dashi,, Dole ya dan tsaya gurin su ,suna gaisawa da su tare da mai godiya,irin alherin da yake aiko masu, Yaya ya kalli Baba na yaga duk wahala tasa wani tsufan dole ya taso mai, tausayin sa ne yaji sosai a cikin ran shi ,, Bayan sun gama gaisawa da Mama na naji yana cewa maryam kaunata ki fadawa Meenat tazo mu tafi asibiti gurin Samira, Gaba na ya fadi don wani irin nauyi da kunya ne ga tsoro su ka rufeni a lokaci guda, Mama tashigo dakin tana cewa tashi ki shirya ga mijin ki a kofa yace kifito kutafi ganin maijiki asibiti, Ganin yanayi nane ta koma sakwarkwatai tace may ya faru kuma ? Ta jefo min tambaya daga tsayen, da take tana mai kallo na a cikin damuwa, Nace cikin kokarin kakaro murmushin dole na ce, babu komai Mama, Amsa tabani da cewa mijinki ya sani Yanzun ko ? Na gyada mata kai alaman eh ya sani gaskiya tace ai nasan agidan nan dama dole ne yaji Na ce mata malam tsoho ne ya fada mai, ai, Kada ki tsaya musayan komai kawai ki bashi hakuri akan kinyi kuskure, Kuma ke bakisan yadda zaki fada mai bane shiyasa ki kai shiru idan ya gani azaton ki zai gane ne, da kan shi, Nace wa Mama to nagode sosai, Muryan Baba na ne ke cewa wai ina Aminatun ga mijin ta yana jiran ta, a waje, fa kun shige daki, Malam shiryawa na takai shiyassa, ga ta nan tafe, ai, Mamana tabashi amsa da hakan Nafito saye da hijab dina na ce wa su Baba na sai mun dawo, Sukan hankalin su yana gurin rabo don haka basu kula da yanayin da nake ciki ba, a lokaci, Uwa uwace kawai ta gane damuwar yar ta a wanan lokacin

****** ********** ****** Yaya Abubakar ne na samu a mota shi kadai hakan yasa nagane cewa shi ne zai jamu zuwa asibitin, Tun daga nesa fuskan shi babu annuri a tare da shi sam ya daure fuskan shi, Jiki ba kwari na tako har zuwa bakin motar da yake zaune a cikki na bude a hankali na shiga, Mutanen dake kofa gidan malam a zaune duk idon su yana a kan mu, Ina shiga naji ya fisgi mota da karfi muka bar gurin, Lumshe idona na yi tare da dan hade yawu masu zafi don jiran sababi da zai min kawai nake yi, Ba lai fi don bai ce min komai ba mu,ka shiga asibitin gurin Anty Samira mun samay ta tana barci ga Baby a gefenta tana barci itama, Mun gaida dangin mijin ta da ke gurin inda Yaya Abubakar yabasu dubu goma da zamu tafi, Yace idan ta tashi anjima zamu dawo mu gaida ita,. Muna kokarin barin gurin ne sai Anty ta farka daga barcin da takeyi Idon ta na ganina tai kokarin mikewa zaune tana cewa Meenatu ke ta ? Sai kuma ta kalli gurin da Yaya Abubakar yake tsaye yana kallon yar Baby da ke barci tace, yayin da take kokarin mikewa Ina kwana Yaya , Ya gajiyan hanya ya fama da jama,a ya amsa atakaice da lafiya kalau, Ina kokarin zama gefen gadon da Anty take . x kwance naji muryan Yaya yana cewa mu tafi anjima sai ki dawo, Banda zabi dole na mike ina ce mata sai nadawo anjima insha Allah, Zan fara tafiya ne naji muryan Anty Samira tana cewa Meenatu ya jikin naki ? Na amsa da cewa, Alhamdullahi naji sauki ai Anty tace madallah, Daidai kan junction din da zai fitar damu asibitin FMC ne naji muryan Yaya Abubakar a cikin wani irin yanayi mai ban tausayi ya na cewa Meenatu may nayi maki zaki cuce ni haka kisani acikin garari, Ki jefa zuciya ta acikin maraici ki sa na zama abin zunde ga mutane mara tawakkali ga ubangiji, Why Meenatu why zaki min haka ki haramta min jin farin cikin da Allah ya alfarkace ni da jin sa na tsawon wani lokaci, Ban iya tsayawa ya karasa ba sai kawai na saka mashi kuka wiwi a cikin motan ina fadin cewa don Allah Yaya Abubakar ka gafarce banayi haka bane da wani manufa, Shout,up my friend I don't want to hear from you,,,, Just keep your mouth off, Shiru nayi ban iya cewa komai ba don firgita da yanayin sa da na yi,,,,,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 7⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH - AL -MUMEET,,,,

Yan uwa musulmai yar uwar mu musulma Anty HAFSAT ALIYU tana baran adduan ku gare ta za ai mata aiki gobe ko jibi don Allah kusata ga addu an ku,,,,👏👏👏

Bai tanka min ba sai ci gaba da tukin motan da yaci gaba dayi kawai , Sunan gurin da naga ya Parker motar shi yasani sanin cewa masaukin shi ne mu kazo an rubutawa gurin Land Of Equity guests in, Kaina yana a duke sai ruwan hawaye nake yi da sheshekan kuka, Tsawa ya daka min da cewa malam dan Allah ki rufa min baki kinji kada mutane su zaci cewa sato ki nayi nazo nan, Da sauri na bi command din shi don kada na kara wani laifi again, Ya bude marfin motan yafito ina ciki zaune ban fito ba tunda ba,a bani command na fita ba, Naga ya zagayo ta kofan da nake zaune ya bude min marfin motan a hankali, Ya bani umurni da in fito daga motan ba musu nafito yana gaba ina baya har muka kai dakin da ya sauka, a sama, Shigar mu akin naga ya fada saman gado ta baya ya dafe goshin shi da hannayen shi , Idonun shi a rufe lub da su tankar mai barci idan ka gan shi, Daga grin da nake tsaye na hango kujerar zama a dakin don ba,zan iya tsayuwa mai yawa ba, Don haka na nufi gurin kujeran a hankali ina kokarin zama, Muryan shi naji cikin tsawa yace zo nan ina zaki zauna kuma can, Na taka a hankali zuwa gare shi kamar mai sarsarfa, Cikin ki wata nawa yanzu ? Idona ya ciciko da kwalla nai shiru ban bashi ansa ba ina dai tsaye guri guda, Bake nake tambaya ba yace yayin da yake cire hannuwan shi daga fuskan shi, Ya kuru min jajayen idon shi da suka kada suka canza kalla don yanayi, Na langabe kaina kamar zan kara fashewa da kuka nace nima ban sani ba Yaya, Maganar ta doke shi sosai har cikin ran shi ya ji haushi cewan da nayi nima ban sani ba, Zaune ya mike da ga kwanciyar da yake, yana mai kura min ido kaman wanda ke son tantance watan cikin daga kallon da yake min, Cire kayan ki in gani yabani umurni daga gurin da yake kwance, Ido na fitar cikin mamaki nake kallon shi don jin abinda yace min, Tsawa yadaka min yace ko bakyajinane abinda na ce ki yi, Na langabe kaina nace don Allah Yaya kayi hakkuri bazan sake ba, Hannu yadaga min yana cewa imin shiru please ban son yawan surutu na fada maki, Wani irin kunya ne ya lulubeni don dole badon naso ba na fara cire tufafina a hankali, Naga ya kauda fuskan shi gefe guda kaman yasa abinda nake tunane, Yarage daga ni sai breazear da dan pant din da na saka, a jikina, Ya juyo a lokacin da ya jini shiru, idon shi ya sauka a dan cikina dai turu dan kui dashi, Cire skirt din nan na jikin ki kafin inzo gurin nan yace, a lokacin da yake mikewa tsaye, Da sauri na sabule dan farin skirt din da ke ajikina dagani sai dan pant da rigar nono kawai na rage, Ya tako a hankali zuwa gurin da nake tsaye ganin ya nufoni yasani dan runtse idona don fargaban abinda zai min,,, Yana karasowa yakai tsugune yana mai dukar da kunnuwan shi daidai saitin cikina, Wani irin kunyane ya lulubeni, don jin shi danayi ya manna kan shi a cikina sai kaqai naji shi yasake wani irin kuka mai dan sauti kadan, Ban san lokacin da na daga hannuwana ba cikin tausayawa na cusa su a kan Yaya Abubakar ina mai cewa don Allah Yaya kayi hakkuri ban san yadda zan fadama bane azatona ka sani ne , Girgiza kanshi yayi yana mai shafan ciki naji abin cikin nawa yana motsi a hankali wanda dama tun jiya da nai ta amai rabona da inji motsin shi,, Da sauri naga Yaya ya dago kai yana kallo na alaman cewa nima naji motsin da yaji, Kai na kada mai tare da daga fuskana da ya cabe da hawaye a lokacin,

Meenatu may yasa kika hanani gaisawa da baby na farin,ciki alfahari na, Da kyat na iya bude bakina a hankali nace ban hanaka ba ya ai kullun kuna gaisawa da shi, don ina zuwa gaida kai, Ya mike tsaye tare da tallabo kaina ya hada da goshin shi ya na cewa , Ban ji dadin boye min da zakiyi ba don kin san cewa shine burina shine farin ciki, na shine kuma kamalan zamana mutum,, Wani kukane ya subbce min wanda ban san dalilin yin saba a lokacin, Dani dashi duk an rasa wanda zai dakatar da wanin mu Tsam ya daga ni daga kasa ya nufi saman gado dani kaina yana tsune a kirjin shi, A tsakiyan gado ya direni tare da yi min kawa da girjin shi kiss ya fara kai min tun daga kafana har saman kai,na,, A hankali na runtse idona yayin da Yayana ya dinga aika min da sakon nai ta ko ina, Sam Yayana yaki barina in huta saida ya tabbatarda cewa dagani har shi kowan mu ya gamsu da dan uwan shi san,nan ya sarara min, A take barci mai nauyi ya daukeni daga gurin da nake a kwance, Murmushine ya fito daga fuskan Yaya don ganin yadda na galabaita, Ya tsura min ido nawani dan lokaci sai nabashi tausayi don ganin yau nice nai barci da janaba ajikina, Abinda yasan cewa koda wasa ban yarda na kwanta da shi, saboda cewan da nayi ban san ta Allah ya zai kasance dani ba, Saboda haan ne sam ban yarda inyi barci jikina babu tsarki a tare dani, Kuma ma ai yin tsarkin zai kara dawo min da sabon sha,awan mijina ne, Amma yau sai gani ina barci don wahala da gajiyan da nayi, Zaune yake a gurin daya sallamay sallah nafila Hannayen shi yadaga sama ya wa ubangijin mu sarki Allah godiyan wanan baiwar da kyauta da yai mai na bazata, Bakaramin dadi yaji ba samun tsatso daga mafificiyar matar shi wace keda ilimin addini asali na kwarai da kuma sanin ya kamata,,, Shima barcin ya kwanta yayi wanda mu muna can muna barcin jin dadi ga kuma jama,a masu zuwa yi mai sannu da zuwa suna can sun cika kofan gidan malam tsoho, Kamar yadda kusan yanzu al,adan hausawa ya koma kamar ta maroko, Mutum har mutum amma sai ya kama bin kofan gidan masu dan hannu da shuni yana maula, Aliyu yayi kiran wayan Yayana bai samay shi ba ance switch, up don haka yafara bawa mutane hakkuri cewa yana can yana barci don bai jin dadin jikin shi, Mama Ladi tayi aiken yara sashen mi don agani ko ina nan, Wasu sai suce mata ban nan wasu kuma suce mata ai ina nan ina ma barci ne a dakin mamana, Mahaifiyata ta fahinci may ke kawo yaran don haka sai ta sake labulen dakin kawai,, Shigowan Anty Safiya gaidani ne tagane cewa ban gida don Mama ta fada mata cewa mun fita da Yaya Abubakar tun da safe bamu dawo ba,. Tana shiga part din Mama Ladi tana kokarin cire hijab din tane take cewa Na biya in,gaida Meenatu ance sun fita da Yaya Abubakar tun safe, ashe, Mama Ladi tace nikan nasani nasan dama yana can tare da jarababban yarinyar nan mai gadon jarabar tsiya , Duk ta halaka shi ta kona shi bai ganin kowa a fuskan shi sai ita, Ni Ladi Allah ya hada ni da bakar iri baka zuri,a bakar jaraba, Yadda uwar ta ta mallake uban ta haka take so itama ta mallake min da, To ta Allah ba tasu ba don ni nawa dan ya,fi duk wani karfin sihirin su, Anty Safiya ta tace, haba dai Innar mu gaskiya hakan bai dace ba , Don dai yanzu ai ankara zama guda tunda ance Meenatu ciki gare ta, Ke inji Mama Ladi ta dakawa yar nata wani irin tsawa, Safiya kikiyayyeni wallahi don ina ganin ke da samira tankar bani ce mahaifiyar ku ba, Ke wata irin sakariyar yarinya ce da har zaki hada jinin mu da wa yance masu kama da yunwar Niger, Hmmm inji Anty Safiya tace tare da kauda kai tace, ai yanzu sai ki zubar da cikin, Tamike tabar part din zuwa wani part na gidan don ta sarara saboda nasu da Mama sam baizo daya ba, Sai bayan fitar tane taita sababi ta na ta masifa da zage zage, Daga gefen mama hafsi kishiyar Mama Ladi wace dan katanga ne ya raba su da juna take cewa a cikin daga murya, Yarinya kin yi daidai wallahi lalai Saratu kin iya haihuwa, Don kin samu, yar da ta kwaso ki kuma tafada inda yadace da ita, Ta mallake dan da yafi kowa agidan nan don haka dole ko uwar da naso ko bata so dole ne tabi ku yanzu kan, Don kun gama komai tunda kun nasa kwai a tare dasu, Ance daka haifi gwauna gara ka haifi matar gwauna yanzu,, Don ta mallako muku gwauna har kofan dakin ka kana kwance, Aiyurirrrrrr yau na sheda hakan don abinda ake muna kuri dashi sai gashi yau muna ganin an raba komai a tare da mu daidai wadaita agidan nan, Aikuwa sai Mama Ladi tahau masifa da zage zage tana cewa, tana cewa inko hakane lalai yau sai ta gwadawa kowa cewa ita dan ta har yanzu a hannun ta yake, Labari yakai kofan gidan wajen maza har Baba Buhari zai shiga gida sai malam tsoho ya tsaidashi, Yace yi zaman ka don babu abinda zata iyayi yanzu saboda abin ya wuce tunanen ta,

****** ********** ****** Anty Sadiya ce zaune tare da mahaifiyar ta da yan uwan ta tana basu labarin abinda yafaru da ita, take basu, Hajja wace duk ta tsure kan jin abinda Sadiya ke fadi hankalin ta ya tashi sosai, Lailai hasashen ta yau yatabbata yar tace ta nakasa mata Dodon ta da hannun ta, Wanda tun lokacin yake ta fama da massasara baida issasan wallawala sam da zai mata aiki yadda ya kamata, Habiba yar Sadiya wacce ta dade da zargin mahaifiyar su a kan abubuwa da dama, Tambayan Sadiya tayi da cewa, yaushe zaku komane sadiya,? Tai wani tabe fuska cikin muryan nan na tana rashin marmari tace, kila gobe zamu koma, Habiba tace haba dai Sadiya daga zuwankin zaki ce zaki koma Waiko Sadiya kinsan ciwon kanki kuwa mutum ace babu ruwan shi da yan uwan shi sam, Babu wanda ya san halinda kike ciki ke dai gakinan kawai, Daga cikin daki Hajja tana jin su tace wai Habiba ina ruwanki ne may kike so gare ta da zakice bata kula kowa, Ni banson irin hakana gaskiya kibarta tayi yadda ta saba Mamaki sosai ya kama Habiba don zaton ta da alaman gaskiya yanzu ,, Bai wani dadewa ba tace zata tafisai taga Sadiya kafin ta wuce tace tunda kikai aure ina ganin baki san dakina ba, Don ko kinzo ba zuwa ki keyi ba sadiya tace ma yarta ta dibi tsaraban da suka shigo dashi ta tafi dashi,,, Sunyi sallama tana cewa Sadiya tazo fa kafin ta wuce lokacin da taga idon mahaifiyae su bai a kanta, Ta kuma cewa Sadiya kada ta yarda takai Sallah magriba a gidan nan ta koma gidan kafin lokacin, Abin yabawa Sadiya mamaki taso ta tambayi mahaifiyar ta Hajja may yar nata Habiba ke nufin da haka , Amma sai ta manta saboda zancen da mahaifiyar nasu ke tambayan ta na mijin su cewa har yanzu dai ba wace ta samu ciki daga cikin su ko ? Sun yi sallama da Hajja tare da cewa zata dawo kafin su tafi,

****** ********* ****** Karan wayan Salawatu dake ta kiran shi yasa mu farkawa, daga dadaden barcin da mu keyi, A hankali Yaya Abubakar ya mika hannuwan shi ya dauko wayar dake ta ruri a kar kashin filon shi, Ya dauki wayan ganin wace ke kiran shi yasa shi sake tsuki, A hankali na bude ido na dake cike da barci a hankali, Sai yanzu na tuna cewa a dakin guests inn nake kwance, ashe, Sai lokacin na tuna irin yanayin da nake cikki kwance, Namike a hankali zaune don gyara jikina sai a lokacin abinda ya faru sai naji muryan Yayana ya na cewa kun tashi ko, Murmushi nayi don jin cewan da yayi wai mun tashi,? Can na hango kayana a saman kujeran dakin yaya ya gyara min su, guri guda, Towels, ya nuna min da hannun shi yayin da yake sallama a wayan, Nawuce zuwa bathroom abina na kyale shi batare da na tsaya jin may yake cewa ba, Wanka nayi tare da dauro alwala nafito daure da towel iya gwiwa da daurin gaba, Idon Yaya Abubakar yana akaina har na zo gurin da tufafina suke ajiye, Na warware zani na na daura tare da aza hijab dina asama na mara allah bisa sallahyan da nagani a shimfide gefe guda, Ina idarwa na dan kwantar da kaina a gefen kujeran dake kusa da ni, Waya yake harzuwa yanzu na fahinci cewa fada suke da Salawatu ta waya, Inda ta fara mashi korafi cewa wai ankawo mata sabon maigadi yana shuka mata rashin mutun ci agida Yace shi yaba da command din duk wani abinda ya faru, Nace a hankali yadda zaiji yunwa nake ji Yaya da sauri naga ya juyo gurin da nake, Yanacewa sai anjima

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 7⃣4⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-HAIY

Fatan Alheri gare ku masoyana Alherin Allah yasamay ku a duk inda kuke, Godiya maitarin yawa Gareki marubuciyar, HAWA,U ABDULLAHI SARKI nagode kwarai da kaunar ki gareni,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull