Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 64

Tarko complete novel - Chapter 64

Tarko complete novel Chapter 64: Tarko complete novel Chapter 64. Anty Sadiya zaune a dakin yar uwar ta Habiba an cika mata gaban ta da kayan lashe, lashe…

3,610 words

Anty Sadiya zaune a dakin yar uwar ta Habiba an cika mata gaban ta da kayan lashe, lashe da tandetande, Yar uwan nata ne ta shigo dakin bakinta dauke da sallama ta samu guri a bakin gadon ta ta zauna suna fuskan tar juna, Tambayan da tafa jefo mata shine Innan mu tasan cewa zaki zo gurina ne yanzu haka ko daga gidan mijinki ka zo nan ? Anty Sadiya wace ke daukan goran kunan Aya mai sanyi da zaki tace ba ta sani ba gaskiya, Sao Habiba tai ajiyan zuciya tai shiru tana mai kurawa yar uwanta ido wace ke kwankwadan kunun Ayayan ta hankali kwance, Sunan Sadiya ta kira cikin nunawa a fuskan ta tana son suyi maganan serious da ita, Habiba tace Sadiya ina son ki kwantar da hankalin ki ki saurare ni da kyau da kunnen basira, Ke dai ba yarinya,bace, yanzu ya kamata ki san ciwon kan ki, Ganin serious matter ne zasu yi magana akai yasa Anty Sadiya ta mai da hankalinta ga yar uwar ta, Habiba tace kada kiji gawani ko wata wanga zance da zan fada maki ki ji shi ga bakina maman mu MANYA ta (Witch) Da sauri Sadiya ta dago kai ta dubi yar uwar ta cikin bacin rai Tace a fussace Habiba ke ma kin tafi gurin malam zamani sun hada ki da uwar ki ko, Habiba wace idon ta ya kawo hawaye a lokaci guda ta dan share hawayen ta hade wasu yawun bakin ciki, tace,, Kada ki manta cewa nima mahaifiyata ce ba ke kadai ta haifa ba, Don haka idan kinga zaki iya saurare na ki kwantar da hankalinki in maki bayani, Sadiya taga babu wasa fa ko wani wargi, a harkan dole ta kurawa yar uwar ta ido, Habiba tace, mutane sun dade suna zargin Innan mu, Amma abinka da Da da mahaifi sai sam ban yarda ba, cewa gaskiya ne, Ina gida akace min ga Innan mu can ta tafigidan surukan ki wai matan gidan iskan su ya yatashi daga ciki harda Mariya, A fusace na taho daga gidan mu naga taton mutane, dafifi a kofan gidan, Sai gata tafito a wullakance daga cikin gidan na tare ina fada ina cewa Ni sai nayi karan su duk da akwai mutunci a tsakanin mu dasu amma sukai muna wanan cin fuskan haka, Zan sa abata ruwan maita ihar tana dashi kowa yasani in bata dashi kuma a fitar da ita daga zargin bakin duniya, Ta yi shiru tare da hade fuska ta hade wani irin takaici tukun tace hmmm, Sadiya sai Inna mu tace min idan na kara zancen zuwa shan ruwan maita, sai ta yanke min kauna, Dole ina ji ina gani na kyale duk inda tabi ana gudun ta cikin shiya mata dayara har ma da maza, Sai watarana na zo gaishe ta kafin in shiva gidan sai naji na taka wani abu, ina cikin dubawa sai nake jin muryan. innan mu tana cewa, Wai yanzu mugun tsohon ga duk yasa Dodon ta cikin wani yanayi gashi abinda yake samowa da yanzu ko kwatan shi bai samowa, Don haka ita wallahi duk yadda zatayi ta rama abinda akai mata sai tarama, Hakadai ta iya hakuri akan yaranta tabada mahaifan su balle wani katon bazan ya kawo mata chikas a vikin al amarin ta don ana bakin ciki da ita, Halan in ta mutu suwana zata barwa arzikin ba diyan taba suci tare da mazajen su, Tace walle Sadiya faduwa daina banyi ba agurin da nake tsaye sai dai naji kukan wani abu nadan leka don in ga ko minana,? Ke wasu irin halittana kaman maciji gashinan dai ban san yadda zan kwatanta maki su ba, Suna ta warki a tsakar gidan, har hawan jikin ta sukai bata damu ba, Amma da na dan taka don in koma bayan sai kawai wa yan nan halittun sun ka bace kamar walkiya ban gan su ba, Kafin Habiba taci gaba da zancen ta sai Sadiya tasa kuka kuka irin mai tsuma rai, Gaba dayan su su ka taru suna kuka cikin tashin hankali, babu mai rarashin wani daga cikin su, Sai Sadiya ce tai karfin halin cewa lalai na yarda da zancen ki, Nan ta kwashe labarin irin abinda ya tashi shige mata a a gaban ta har tai ciwo kamar zata mutu da yadda ya hannayen ta yanzu suka koma kaman sun lankwashe basu mikewa, Kuka sosai Habiba tayi tashi shine basu samu labari ba Sadiya tace, sai daga baya nake jin cewa wai Innar muce tace ina ruwan ta a lokacin da aka bugo mata waya, Nan dai ta kwashe labari tafadawa yar uwar ta kaf, Cikin kuka Habiba tace to wa yai jinyar ki haka Sadiya ? Tace wallahi Meenatu ce tai jinya ta sai daga baya tasamo min wata mata yar aiki ta dinga taimaka min,, Habib tace amma ko wagga diya tayi maki mutun ci gaskiya don wace kishiya zaki samu yanzu tai maki hakan, Sadiya tace amma dai kin san kishiya batai ma abu don Allah don haka ta dai yi ne don wani manufan ta kawai, Habiba tace haba dai Sadiya irin wana kokarin haka har mutum zai yi don sheri, Sadiya tace aiko sai tayi don sherin don mji yace ita ta Allah ce , Haba Sadiya aiko ma may ye tadai yi ita dayan matar tayi maki ne halan ,? Sadiya takara tabe bakin ta ce, wanan yar iskan wake zamcen ta ko sannu ban samu ba daga gare ta tunda tasan sherin da tayi min, Wani sheri kuma Sadiya tace wai turo min mugun abu inba ita ba kowa wani, Ai ba yau muke nake da mijina ba wani Abu bai taba samuna ba sai yanzu, Habi tace ke Sadiya kada ki daukan wa kanki wahalan zato wakike zaton cewa tai maki hakan a cikin su tace kada ki jawa kanki zunubi ga banza Allah,, Nan dai su kayi ta hiran a tsakanin su suna tatauna yadda, al,amuran suke masu, Dakuma mafita ita habiba take wa yar uwarta nasihan akan zaman duniya,,,

****** ********** ****** Har waye wan gari bamu hadu da Yaya Abubakar ba wanda tun, jiya da mama tai muna cin mutunci ya fita, bai shigo part din mu ba, sai wayan daya bugo min sama sama yana cewa nasha magani na kuwa,,,,, Ina bashi ansa naji ya kashe wayan batare da cewa komai ba, Sai yanzu nakira layin shi na sheda mai cewa ina son in tafi garin KALGO gurin gwagona don in dubota saboda ta samu kariya a hannuwan ta, Muryan shi ya tabbatar min da cewa, yana barci ne a lokacin, saidai na daure na fada mai, ina son zuwa, A takaice yabani amsa da cewa inbari zai zo mu tafi tare, ban so hakan ba don yini naso nayi a kalgon don sai yamma zamu dawo, Yaya Abubakar sai zuwa sha biyun rana ya shigo gidan mu cikin shiga na mutunci da kamal ,, Part din mahaifiyar shi ya wuce direct, don su gaisai, Mama Ladi tana daga zaune a kofan dakin ta fuskan da gani tana a cikin damuwa a lokacin don haka , Ya zauna saman tabarman kaban da yagani shimfide, Sai lokacin take cewa wai ya tashi a shimfida mai tabar man rubo saman wanan na kaba din, Ya ce No abarshi kawai don ba zama zanyi indade ba zamu tafi Kalgo ne gaida gwago Habib, Wayyo yau ina wuta Mama ta saka Yaya Abubakar wanda take ganin ya zama sallamamay a gareta, Yanzu mai sunan malam baka tafi kagaida yan uwa na ba amma shine wai har zaka tafi gaida yar uwar matan ka,? Ya dago kai cikin mamaki yace yanzu kuma gwago Habib ta zama yar uwar matata ke nan, ? Yar uwan mahaifina ce fa ita bawai dagin matana ba idan da yar uwar mama Saratu ce shine zakice dangin matata ce ita, Ko wacecen ka inda Habib ce baka zuwa ko ina Ya mike tsaye yana cewa, zan fita dama akwai abinda nake son zuwa yi Zauro don haka bari kawai na tafi, Sai kuma yai murmushi yana cewa saidai kuma,su Baba gaba dayan su suna kofan gida da malam tsoho Nasan cewa da nafita tambayana zasuyi ina nabaro ita Meenatun kuma, Kace masu kana zuwa ka dowa mana, ba shike nan ba,sai dai ka tahiyyan ka inda zaka, na, Ya,Ce haba Mama mi zaisa in masu karya cewa dai zanyi ke ce ta tai ita kadai, don zan tafi nawa tsabgan , Yau Allah ya gwada min Da yanzu ashe halin nan naka na rashin boye gaskiya na nan, To yaya kaka zama da matan ka don dai duk mai mata biyu bashi shuka gaskiya, Dariya maganar ta yaba Yaya Abubakar don dai yasan yadda tun yana yaro su ke kwasa da ita kan karya ,, Yace na tafi sai nadawo nika son mu zauna kafin in tafi, Nikan tunda Yaya Abubakar ya tura cewa ace in fito mutai ban tsaya jiran komai don dama da yan kanne na ne zamu sai kuma yaran Baba musa , du biyu fon haka su biyar sunka matse a bayan mota, Nafito saye da wata dogon riga baka tasha kwaliya mai kyau daga cikin kayan lefen da yaya ya sayo min yake, Mun dauki tsaraban da nazo wa gwago na dashi da sauran sayayan da nai mata anan, Kafin motan mu ya daga har yan gulma sun tafi fadawa Mama ko, , Ba wasu bane CID din Mama sai diyan Anty mariya da take riko har su biyu, mace da namiji,, Ni da Yaya Abubakar muke gaban mota sai su sisters dina, zaune a baya motan kowan cen su ta,fito da na kasan akwatin ta ta saka, Mai makon mu mike hanyan mu sai naga ya juya akalar motar shi zuwa cikin gari, Alairu quarter's mu ka nufa hankan yasani gane cewa gidan Anty Safiya zamu, Ba karamin dadi naji ba saboda na gane cewa Yaya Abubakar zai cika min alkawarin kai ni gidan dangi da kan shi, Don haka wani murmushin dadi na sake tare da lumshe idona, a hankali,,,,, Sai lokacin da muka bar unguwar mune na dan juyo ina cewa Yaya na Ina kwana, Sai da ya karya kwana tare da gyara tukin shi yake ce min Yaya kuka kwana, ya baby na ? Na, ansa a hankali da cewa lafiya kalau ya bakunta da hakkuri, Hmm kawai yace batare da ya kara cewa komai sai kwatance hanyan gidan Anty da muke mai, shi dai baice muna kala,ba har muka kai kofan gidan Anty Safiya, Mijin ta muka fara gani a kofan gidan su inda ya fara yin wasa kamar yadda yake min da can baya, Amma sai nai murmushi kawai ban bashi ansa ba, nace mai ina wuni ya aiki, yace da godiya, Ya juya gurin yaya Abubakar yana mai gashe shi cikin girmamawa, Yace matan manya kinga addu,ana ya zama gaskiya ko, Inna ce maki matar manya ce ke sai kice ina maki adduan auren tsoho, Nace kai Baban Dule baka mantawa ko nai murmushi na shige cikin gidan, su , anan muka barsu shi da Yaya Abubakar,,, Sosai Anty Safiya take murnan ganin mu gidan ta duk ta rasa abinda zatayi don murna, Yaya Abubakar suka,shigo gidan dashi da Babab Dule suna dan hira sama sama, Babu kujeran kirki a falon ta ga gidan irin na quarter's amma ba kyau gani sam don ba tsari, Mun dan taba hira da ita inda mukai mata sallama kudi masu yawa ya ba maigidan ta wanda muke cewa Baban Dule,, Tun fitan mu gidan naga duk yanagin shi ya canza sosai murmushi nayi a raina don nasan TARKO na ya soma aiki kenan, Mun dauki hanyan da zai kaimu garin Kalgo Yaya Abubakar ke tambayana cewa babban sister din shi wace ita a kauye take aure nake cewa kauyen su yana nan Masama, Sam Yaya bai san gidan Gwago Habi ba sai da muka gwada mai abinda yasani gane cewa baisan gidan kowa ce mace yar Family din mu ba, Allah Sarki Gwago Habbi gidan tsoho gida ne sosai duk ruwan sama ya darje ginan gidan, Muka fifita daga motan tana zaune acikin wani dan rumfar kara a gefen dakin ta, Kanta da wani kitso soro shidda yai makal,makal dashi tankar anyi shekara ba ai kitso ba, Kofan dakin duk ya kwakware sosai don daga dan inda ya zurma zaka iya hango cikin dakin, Sai murna takeyi da lalai mar habbiñ din ganin mu don har Yaya Abubakar saida muka shigidan dashi, Nida kaina na shiga dakin Gwago fon dauko shimfida, Daga inda take zaune take cewa in duba bayan kofa tabarma sabuwa yanan in dauko, Kayan tsaraban ta muka zube mata su a kofan dakin ta tun shigowan mu, Gaba,dayan mu muka hau saman tabarman saboda babbane sosai, Nan suka shiga gaisawa dashi acikin girmamawa sai kallon gidan yakeyi yana girgiza kai kawai, Bayan sun gaisa da shi Gwago tajuyo gurin da nake zaune kafa a tankwashe tana cewa, Tubarkallah Meenatu karuwa na munka samu haka shin ? To Allah shi jissuwa lafiya yan kuda na kwana, Car sai yar kaunata (sister) karama ta karba da cewa Ameen ,, Abin dariya yaba Yaya Abubakar don sai naga ya dan jawota zuwa jikin shi ya lakuta mata kumatu acikin wasa yake cewa, ashe kin san addua ko ? Can Yaya ya mike tsaye yafita yana waya hakan ne ya bamu daman kara gaisawa da gwago na mu kai mata yay jikin ta, Mikewa nayi na cire Hijab dina muka fara gyarawa gwago gidan ta da yai kaca kaca, Na bude jakata na ciro kudi nace su fita bakin hanya su sayo muna abubuwan abinci saboda mu dafa don naji Yaya ya tada motar shi hakan ya tabbatar min da cewa yatafi, Tsab har ban daki muka gyara wa gwago na mun sha albarka yafi dubu a ranan, Mun yi girki mun zuba a katon ture muna ci nida yan uwa sai dadin kasancewa a haka mu keyi, Muna tsakiya da cin abinci mukaji dirar mota a kofan gidan wanda kuma yai daidai da dawo wan maigidan Gwago daga kasuwa gurin sai da kayan miya, Katuwar katiface mukaji sallaman wasu matasa mutum biyu suna shigowa gidan dashi, Yaya Abubakar daga bayan su shida Baba Wadda da bakon mu Baba Hamza,, Suna dauke da buhun shikafa da su mai da sauran su, Yai mamakin ganin mun gyara ko ina mun share mun tara karare guri guda mun cin na musu wuta suna konewa ,. Ga kuma abinci da muke ci nida yan uwa a cikin katon ture a gaban mu,, Sai sannun ku da zuwa muke ta masu suna karbawa Baba Wadda ne ya jagoran kutsawa da katifan dakin Gwago bayan an kara rage kayan da muka gyara dazun, Daga girin da nake zaune muka dan hada ido da Yaya Abubakar ya sakar min wani lalausar murmushi tare da min signal wai na faye ci Murmushi nayi tare da dan dukar da kai acikin kunya ina cewa su Baba Hamza' a debo masu abinci ne, ? Baba Wadda yace kamar kin san muna jin shi kuwa don muna gurin gantali aka kira mu, Kaunata Zinatu ce ta mike tazubo musu abinci a wani kwanon silver mai fadi, Sai kuma ta dauko wa mijin Gwago nashi da muka saka mai tun gamawan mu, Makwabtan gidan gwago da yan garin sai zuwa gaida mu sukeyi suna cewa masha Allah Habbi ashe kina da iyali haka, Sai kuma ashiga dakin a leka ana kallon katifan da a,kasayo wa gwago, A can gefe guda kuma mijin Gwago ne da Yaya Abubakar, zaune suna tataunawa, Zamu iya gane zancen su kamar suna magana ne akan zagaye gidan su, Gwago da jama,an ta sai murna da fatan alheri suke muna, Zuwa dan wani lokaci Yaya yamike yana cewa mu shirya mu tafi gida, Ba don munso ba muka fara shirin tafiya gida sai godiya,gwagona keyi har da hawayen ta,, Muka fito gaba dayan mu idon mutane akan mu caaa suna fadar albarkacin bakinsu karya da gaskiya, Muka kama hanya misalin karfe hudu da wani abu na yamma zuwa gida, Saida muka yada zango gurin Anty Samira asibiti muka gaida ita tana tajin dadin ganin mu, Tana min korafin wai naki zuwa in, zauna muyi hira tunda nazo nake ce mata wallahi banjin dadin warin asibitin ne shi yasa,,, Dariya ta saka min tana cewa ai nikan nasan cewa za,a rina wallahi tun ranan da nagan ki, Haba Anty Samira yanzu wani canzawa nayi da zaki ce min wai wani abu zamuyi magana yaya yashigo shida su Baba Wadda da Hamza, Muna daga gefe su ka isa gurin ta suna gaishe ta tare da tambayan ta karfin jikin ta, Mun dan jima har gab da sallah magrib sannan muka nufi gida acikin jin dadi duk da agajiye muke amma bamu jin komai saboda mun tafi gurin yan uwa, Muryan yan rakiya da suke shewan jin dadi mun tafi kalgo tare yasa mutanen gida gane cewa mundawo a lokacin , Ina shiga part din mune mama take muna sannu da zuwa nace wanka zanyi ko zanji dadin jiki na, Mama tace min inyi maza kafin almuru ya sauka don koda ba cikki gareni ba ba,a son yin wanka a wanan lokacin, Dasauri don dai ina son yin wanka na nufi bathroom na watsa ruwan kawai ban tsaya sa sabulu ba, Nafito nai alawala nashiga daki sai naji wayana yana ruri cewa, kira ya shigo tsuki naja ina cewa waye mai kirana, a wanan lokacin, Sunan Baba Ramatu ne nagani rubuce, da sauri na dauka ina cewa ai nayi fushi Baba, Ramatu, Amma sai naji muryan ta tana cewa uwar dakina yanzu, nan matar gidan nan tazo wai na bata key din dakin ki zata dauki wani abu acikki, Da sauri nace innalillahi kin batane Ramatu, ? Ramatu tace haba dai uwar dakina ai nasan halin ta don haka nace mata ai da shi kika tafi, Don dama ban taba bude kofan ba bayan tafiyan ku, Wani irin mamakine naji nake cewa Ramatu wani sheri zatai min a dakin kuma , Tace nima tunanen da nake tayi ke nan tun dazun nima, Nace cabdi ashe akwai magana don duk tai gigi bude min daki wallahi bazan kyale taba niko Ramaru take ce min yanzu an samu mai gadi kullun sai ta fita tai masifa dashi wai yaki bari abokan ta su shigo gurin ta,, Murmushi nayi ina cewa kyale ta kawai ba zai yarda ba ai don maigidan ya kafa mai doka, sosai, Ramatu tace wallahi baki ga yadda tadinga min masifa ba don nace key bai hannu na , Dama tunda naga tana son jana ajiki nafara shan jini na da ita ina kaucewa, Don nasan cewa ba alheri zata shuka ba, sheri take son kullamin, Da zaran na gama aiyukana sai kawai na shige ciki abina batare da na tsaya jiran ta ba, Allah ya kyautana ce tare da ce mata sai anjima zanyi sallah saboda an fara kiran sallah ko, Ina idar da sallah nake jin muryan Anty mariya a part din mu tashigo tana cewa waiko Meenatu na gidan nan, Nafito daga ciki ina cewa ina nan anty ina wuni ta amsa min wani iri, ciki ciki Wai tambayana take yi dana tafi da su zinatu anguwa may yasa nabar yaran ta ban dauke su ba naje dasu, Nace anty koda muka shirya tafiyan mu basu kusa lokacin yaran Baba MUSA ne kawai a guri kuma tare muka tafi da su Meenatu kada kijawo raba daya biyu fa ki ce zaki nuna muna banbanci, Ai suma wa yannan yaran da kike gani ai yaranki ko banza Don na dauka cewa diyanki ne suma tunda kaunata kike, Amna wai kina ganin su kikasa yan uwanki a gaba kuka wuce kuka bar min su, Amma kuyi abinku don wuri kuka samu shiya don dama hakan ne akeso ayi ai Ta juya fuuu suka hadu da Baba mu a hanya yana shigowa gida don dawowan shi ke nan, Irin yanayin da ya ga tafita dashi yasa shi gane cewa ba lafiya ba, ke nan, Tun daga nesa yake tambayan Mama Saratu lafiya ta tsaya mai wani inda inda yadaka mata tsawa bashiri ta shiga fada mai abinda ya faru, Baba bai tsaya ba sai sashen Mama Ladi ya samay su suna raba abinci zasu ci Anty Sadiya tana daga gefe tana kallon yanayin su, Babu sallama ba yashigo yana cewa wai ina Ladi ne, Yau abinku ya isheni agidan nan wallahi ke da kin san ku ya xa ya kamata to da ko ance ki shuka min nida zuria ta rashi mutunci da bazakiyi ba, Amma da yake ke butuluce shiyasa al,amarin ki bai bani mamaki kwata kwata, Yau hatta takai iya iskancin ku ya kai mariya sashena don cin mutunci, Auren daki dai ne aka yata ko ? Tau yau zai kare yadda kike so sai ki zauna da wa yanda kike son ya zauna dasu ko, Ai,ko Baba ya haukace yai ta masifa yace sai Yaya Abubakar ya sake don shi agaji da wanan masifan, Kafin ace may maza suka shigo ta ko ina gidan ya cika fan da jama,a Amma ina sam.Baba sai cewa yakeyi sai fa Yaya Abubakar yasakeni kowa ya huta, zaifi,,,, Aiko hida ya rikice da jidali wanda hankane yasa Baba Buhari cikiin hasala ya tako har kofan Mama ya daga ashabarin da aka rufe part din da su Ya ce to Ladi sai ki tashi ki fito daga ke har wanan yar taki da diyan ta wallahi baku kwana min agida yau, Hakan ya isheni ya isheni sosai daga yau ya kare don ya ta zata dawo gida ke kuma sai ki koma naku gidan,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull