Tarko complete novel - Chapter 65
Tarko complete novel Chapter 65: Tarko complete novel Chapter 65. ZEEE MAKAWA YELWA
3,203 words
ZEEE MAKAWA YELWA
๐ธ๐ธ๐ธTARKO๐ธ๐ธ๐ธ ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ 7โฃ5โฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH- AL- QAYYUM,,,,
Gida gaba daya ya rikice da fitina wasu na ganin laifin Mama Ladi wasu kuma suna jin takaici na da iyayyena, Sai dai masu jin takaicin mu basu da yawa sosai don kowa ya san su ,,, Irin yadda Baba ya nuna rashin mutunci ranan hankalin kowa ya tashi a gidan, Tsaye yayi yana cewa sai an kashe auren yau kowa ya huta, Dole Mama Ladi da taga cewa wanan fitinan yafi karfin ta tashiga hankalin ta, Ga Baba Buhari shikuma yayi rantsuwa cewa yau Mama bazata kwana mai gida ba, Dakin mu na,shige csn kuryan gadon Mama na ina wani irin kuka mai tsuma rai, Haka ita ma mahaifiyata tana zaune waje daga kofan ta idon ta sai tsiyayan hawaye yakeyi, Baba Wadda ne ya daga waya yana kiran Yaya Abubakar wanda ke can gidan su Aliyu Abokin shi,,, A,gagauce ya iso gidan inda ya samu fitinar bai kare ba alokacin, don ga,Baba tsaye a kofan part din Mama yana jiran tabar maigidan shi, Wani irin bacin rai ne ya ziyarci zuciyar shi a lokacin don yasan cewa yau ran Baba ya,baci ne sosai, don a gaskiya Baba Buhari mutum ne mai hakkuri sosai,,, Juyawa yayi zuwa part din mu inda yake jin muryan Baba Samaila daga can baya gurin Baba Musa, Gaida Mama yayi a mutunce saiyake tambayan Meenatu fa, Murya irin ta,wanda yai kuka sosai take ce mai tana ciki, Tausayin mama yaji don dai yasan cewa idan ta ita ce baza,a taba fada ba agidan mu, Kamshin turaren shi yasani gane cewa ya shigo dakin namu a lokacin,, Wai may, ki kewa kukane haka ? Kada fa kijawa kanki ciwon kai a kan wanan zancen don babu abinda ya shafe ki a cikin sa magana ce ta manya ba tamu ba, Abinda ya fada naji wanda hakan yai saurin sani duban shi, Don mamaki sosai ya bani don a kan mu ne fa ake wanan zancen amma sai ya cewai, akan may nake kuka, Na ce a hankali cikin muryan kuka Yaya baka ji may ake yi a gidan nan ba duk akan zancen mu, Yai murmushi mai daci tare da kara harde hannayen shi guri guda, Ya na kallo na tare da sake min murmushi ya jefo min tambayan cewa, Bakya son araba auren na mu ne ke ? Da sauri na dukar da kaina ina mai cigaba da zubar da hawaye,ina dan goge hawayena da bayan hannuwa, na ,,, A hankali ya kai zaune daga tsayen da yake ya kai zaune gefena kadan, Ya kira su nana a hankali yace ki fara shiri mu koma don bazan iya tsaya cikin wanan tashin hankalin haka ba, Na dan dago na kalle shi fuska da fuska na ce baza mu tsaya ayi suna damu ba ke nan, Ya mike don dama ba zama sosai yayi ba yafara tafiya yana cewa gaskiya bazan iya kai wani lokaci a nan ba haka ? Don haka idan zaki koma ki shirya idan kuma baki tashi ba sai ki tsaya har ki gama abinda kikeyi,,, Ya sa kai ya fita daga dakin yayin da nabi bayansa da kallon mamaki Na tambayi kaina da kaina nace wai kodai ma baiji abinda Baba ya ce bane,
******* ********** ****** Daga dark n gurin malam tsoho ya nufa idan ya samu tsohon a cikin bacin rai sai dai babu wanda zai iya fadawa, Zuwan yaya Abubakar gurin shi ne yasa shi dan jin dama, dama, abinda yake ji, a zuciyar shi, Zama yaya Abubakar din yayi tare sa ba malam baya kadan ya dukar da kan shi a tsakan kanin kafafuwan shi, Malam ne ya jefe shi da tambayan yaushe ne zaku koma, Ya Abubakar wanda ya dago kai da idon shi da sukayi jawur ya bude bakin shi da kyat yace, Ina ganin gobe zamu bar nan don bazanci gaba da zam irin wanan matsalalolin suna bulowa ba saboda mu, Dama wanan ra,ayin Meenatu ce don ita a zaton ta ban son yawan kula yan uwa, Yace malam tun farko, idan naima wani alheri abin yana zama fitina be sosai irin haka, Shiyasa nasawa kaina massalaha kan ban damu da kowa ba kuma ban shiga harkan kowa, Malam tsoho yace na fi kowa sanin wanan ba yau ba shi yasa ma nai kokarin yin wanan hadin a tsakanin ku,,, Yaya Abubakar yace Meenatu yarinya ce mai hankali malam, Abubuwa da dama da na manta dasu da farko itace a yanzu take yawan tunatar da ni, akan su, Munyi magana da ita a kwanan baya wanda taban shawaran da ya kamata, Tun wanan lokacin ne abubuwa da dama da su ka tsaya min arai,, Wannan daman ne nai amfani dashi a wanan haihuwan na Samira na dauki hutu don inzo in duba wasu abubuwa,, Malam yace jeka masaukin ka ka huta gobe karfe takwas na samu mu hadu a nan sashen nawa,
****** ********** ****** Washegari gaba dayan su diyan malam tsoho, duk kan su suna har Baba Wadda suna zaune a gaban mahaifin su, Wanda yake saye da farar tabarau a idon shi yana daga kwance kishingide yana karatun a cikin muwadda,malik, Hankalin shi naga karatun da yake yi tankar bai san da su ba agurin, Shigowan Yaya Abubakar a cikin sune yasa gaba daya hankalinsu na gurin shi,, Nan Yaya Abubakar ya tsugunna ya fara gaida su daya bayan daya a cikin girmamawa, Sai a lokacin ne dan tsoho ya dakatar da karatun shi ya rufe da shafawa, Sallama yai masu yayin da suke ta mika gaisuwan su gareshi ta ina kwana, Malam wanda yai gyaran murya don yaga cewa sun natsu don suyi abinda ya kawo su gurin kowa,ya tafi neman na abincin sa, Baba Buhari ne ya fara kallo yana cewa da fatan mai dakin naka ta dawo gida iyanzu ko ? Baba Buhari wanda yaji nauyin magananya dan yi kokarin gyara, zaman shi da kyau yana mai dukar da kan shi kasa, Sai kuma ya juya gurin mahaifina wanda tun malam din baiyi magana ba yai saurin dukar da kan sa kasa,, Yace mai 'ya ga mijin nata a gaban ka sai ka karbi takardan nata ko? Babana ya kara dukar da kanshi kasa cikin jin nauyi da ka sa daga fuskan, shi, Gurin Baba Musa ya juya yana cewa Musa may yasa har zuwa yanzu ka kasa gane halaiyar Ladi a gidan nan, Yanzu da ace kun kyale ta kamar yadda shi dan da ta haifa ya sa mata ido yana bida ita acikin dubara ai sai na ga zaifi ko ? Yanzu gashi diyan naku da,suka zo maku hutu sun yanke shawara komawa indal,su ka fito yau din nan, Gaba daya duk wanda ke wurin sai ya dago kai yana kallon gurin da Yaya Abubakar yake zaune, Malam ya,ce wanan ke nan, yanzu abinda nake son ku sani shine ni a gida na ba saki, Don haka daga yau ban son in kara jin zance kalman saki a cikin gida koda kuwa a bayan raina ne, A hankali suke furta cewa insha Allahu malam baza ayi haka ba, Malam yai murmushin takaici yace gaba dayan ku na zata zuwa yanzu zaku gane manufan hada auren nan da nayi, Iyanzu zaku gane cewa auren nan na yaran nan wani babban TARKO ne a gare mu baki dayan mu, har su, Yanzu wanan abubuwan da suke yi wa yan uwa musali watace can bare ya aura kuna ganin cewa zaku samu wanan alherin haka daga gare shi a koda yaushe, Yaya Abubakar wanda ke daga gefe yadago kai yana kallon malam malam yace kwarai da gaske hakane, mana, Ada can baya kafin ka auri yar uwar ka, matar ka da yan uwanta kawai ka,sani, Cikin jin nauyi Yaya ya dukar da kanshi kasa malam yace amma yanzu duk abinda zai yi a na gida ne zai fi yin sa, Ya girgiza kai tare da lumshe idanun shi yace ita Ladi da kuke gani bata da tunane ne ko kadan , Idan ba haka da bazatayi irin wanan haukan da takeyi wa mutane ba agida, Abin alfahari ne agareta ace ta samu suruka irin Meenatu daga tsatson ta gashi har Allah ya kawo rabo a cikin al,amarin, Ina yaushe, yaushe ne aka kashe wutan an mata gorin cewa takwara na wai bai haihuwa, Allah da ba azzalumin kowa bane ba gashi yanzu yabada rabo ba ta gurin da ma ba,a zata ba, Don haka daga yau irin wanan rigingimun ban son in kara jin shi a gidan nan Ai wanan abin kunyane kuke jawo min ace a gidana ake fadan hada zuria, aure, Yace akwai abinda yafi haka alfahari ace daga garesu ma,auratan babu wani matsalan komai a wajen su sun dace kuma da auren junan su wai sai a wurin ku, ku, Ita fa Ladi bawai Meenatu ba ko ma diyar waye daga cikin ku haka zatayi da mai shi, Don kunga ita fa ko diyan ta bata bari ba balle na wasu don haka sai kuyi hakkuri don kowa ma da halinsa ake zama dashi, Malam, Ya dan kada kai tare da lumshe idon shi yace Allah ya kyauta Allah ya tsare gaba wanan ya zama farko ya zama karshe ita ma Ladin zan zauna da ita ai mu tattauna akai, Gaba daya gurin shiru su kayi suna mai nazarin maganan dan tsohon cikin rayukan su, Baba Musa ne daga cikin su ya fara magana da cewa, A gaskiya malam zancen ka ni kan ba yau ba na riga da na san da kasan cewan yaran nan a tare wani babban alheri gare mu, Don idan anyi la,akari da irin yadda a yanzu muke samun kulawa daga maisunaka wanda mu yanzu bamu da abin cewa sai dai mu, yi maka fatan alheri a rayuwanka irin yadda kake muna Allah ya baka zuria masu albarka suyi maku fiye da wanda kai muna, Gaba daya gurin suka karba da Ameen ya Allah kowa ya shiga fadar albarkacin bakin sa, kuma, Yaya na yana daga gefe yana sauraren su, yana mai lumshe ido daga zancen su Yasan cewa yayi babban kuskure abaya so sai duk da dai a lokacin ba wai yana da wadata, (hali ) irin yanzu bane,,, Shirun da wurin yayine yasa shi dan dagowa ya dube gurin da malam din yake zaune ya ce, Ina son,wanan shekaran ta bana Baba da Mama su sauke farali a tare dani, Da naso in tafi da matana dukka amma sai gashi ita Meenatu tana da lalura don haka tagiyanta atare da mu bazai yi ba shiyasa na yanke shawa cewa a tsakanin shi Baba Samaila da Mama Saratu sai guda ya tafi, a madadin ta,, Ai,ko take guri ya dauki kabbara da murnan jindadi, Duk yan uwan Baba suka ce sai dai shi ya tafi don bai yiyu mama ta tafi shi baije ba, Yaya Abubakar ya dago kai ya dubi malam tsoho wanda,duk murna da farincikki ya kashe shi, ya ce,,, Sai kuma kai malam don naga cewa barinka gurin nan ba karamin matsala bane don haka ta International zaku tafi kai da Baba Wadda,, Yace ina son kafin mu tafi sai a dauke ku photo saidai kuma bansan ko zaku so zuwa ta Abuja ko tanan Kebbi,,, Baba musa yai saurin cewa ta nan Kebbi dai zai fi nake gani, Yace ba matsala zanga Aliyu sai a san yadda za, ayi aksi yace zai fita saboda zancen tafiyan su, Baba musa yace maisunan malam ina malam ya kashe wan nan zancen tafiyan ko, Tsayawa zakayi atare damu har zuwa lokacin da ka debona komawan ka daga hutunka, Murmushi yayi tare da cewa tau Baba ba matsala nagode da fatan zaku taya ni ba Baba Samaila hakkuri ya barni da matata please ,,, Dariya aka kwashe dashi tare da dan kara tatauna wasu al,amurorin akan harkan gidan,, Kafin wani lokaci zancen tafiyan su Mama Ladi makka ya kewaye ko ina cewa an biya masu makka hadda Baba na Samaila, za,a tafi,, Wanan zancen duk sai ya gushe da batun maganganun da ajetayi na fitina agidan mu, Sabon zance kuma ya shigowa mutanen gida da na waje,
****** ********** ****** Wanan zuwan da mukayi ya kara sawa sunan Yaya ya dan yi fice kamar yadda da zaran mutum yana gurin samu atake da tayi wani abin bajinta zakaji gari ya dauki ciri, To shima wanan karon hakane abin ya kasance , agare shi on mutane sai zance su ke yi a, gari cewa ai dan gidan malam tsoho yana nan ya,samu babban guri a Abuja,, Abubuwan business sosai su,ke kafawa a gari shi da Aliyu wanan zuwan, Yau daga wani unguwa sukd sai Aliyu ke cewa yana son zuwa ya duba mahaifiyar su a gidan su don haka Yaya Samaila yace su tagi tare don ya gaisa da ita shima, Kai tsaye suka shiga gidan yana nan kamar yadda ya san shi da farko a baya, , Hajiya tayi murna kwarai da ganin Abubakar a gidan su don tadade bata ganshi a idon taba., sai dai yakan aiko mata da sako wasu lokuta can ba,a rasa ba, Yar dattijuwan mai zubin kamala zaune a saman daya daga cikin kujerun da ke dakin nata, Take cewa Abubakar ka yanke zumunci ko ko sau daya baka taba kawo min iyalinka nagansu ba, Aliyu daga gefe yace gashi wanan zuwa dukkan su yan Birnin Kebbi sukazo yar Abuja ce kai suka bari tsaron gida, Murmushi Yaya Abubakar yayi kasa kasa yace anyi kuskure mama za a gyara insha Allah, Sai kuma tace yaran shi nawa yanzu sai kuma ta runa tace aff iji ance har yanzu babu rabo a gidan ka, Gashi ko kaga ikon Allah ita Fatima yaran ta uku fa inda badon ma maigidan nata yarasu ba aida kila yanzu takai hudu ko, Aliyu daga gefe ke cewa ai ya,zo hargidan lokacin rasuwan yai mata gaisuwa, ta ce Allah sarki aiko kaga banji ba fa, Aliyu yace a,a mama kindai manta don tun bai tafi ba ma na fada maki, cewa gashi yazo da matar shi gaisuwa, Tace Allah sarki gaskiya na manta da hakan wallahi, Wai ma ina Fatiman take tazo su gaisa mana ina tashiga ne wai, Sai ta fara kiran sunan Fatima, Fatima can kuma tace ke yar ma,aiki ina kikashige, Fatima wace ke daga dayan dakin dake hade da falon ta amsa tafito Tana saye da wani dinkin buje da riga na atamfa, sun dan matse mata jiki, sun sa bazaka iya gane cewa tayi haihuwa har uku ba, A hankali ta karaso cikin falon bakin ta dauke da sallama, Tana wani rausaya don ita mace ce mai son jan aji da yanga, Suna hada ido dashi sai yaji wani irin yarr a zuciyar shi, A bayan kushin din da mahaifiyarta take akai ta dan zauna a hannun kujeran tana cewa sannu da zuwa , Yace Fatima kina lafiya yaya yaran da karin hakkuri ta dan lumshe ido tace Alhamdullahi na godewa Allah, Sai akai dan shiru falon kowa na nazarin abubuwa a cikin zuciyar shi, Aliyu ne ke tambayan ta ina yaran ta su ke tace a yangace wai yanzun nan suka tafi gidan sister din ta maimuna, Yace ok ok Yayana yana daga gefe duk yana sauraren su wayar shi da tai kara yadauka yadan fara magana da mai kiran wani abokin aikin shine ya kirashi sun dan kai yan mintina suna waya da mutumin ya kashe baka jin komai sai kiran miliyoyi da sukeyi ga turancin shi gwanin sha,awa sai kace ai a turai aka haife shi ma, Yana kashe wanan kiran kuma sai ga wani kiran yashigo mai kiran Salawatu ce tana mai tambayan shi acikin shagwaba yaushe ne za su dawo , Ya mike a hankali daga gurin da yake zaune zuwa waje, Fatima wace tabishi da ido daga gurin da take zaune ta dan lumshe idon ta tare da shakan kamshin turaren shi, Wanda tun shigowan shi falon nasu ya gaurareye da kamshin sa ta ko ina, Itama mahaifiyan su Aliyu daga gurin da take a zaune zuciyar ta ya kiyasta mata wani abin daban Shikan Aliyu bin bayan abokin nashi kuma boss dinshi a yanzu yayi zuwa waje, Yana fita mahaifiyan su Aliyu tace ikon Allah yaron nan ya samu lafiya sosai ke nan, Allah mai iko, ke nan dubi yadda su ka tashi da Aliyu,, Muryan Fatima ce daga bayan ta take cewa mama ance matan shi biyu ko, Mahaifiyan nasuu tace anya kuwa basu fi biyu ba bakiji abinda yayanki ya fada ba yanzu, Tace wai har mata uku amna kuwa ni da can ce min ya keyi shi mace guda ta ishe shi a rayuwan shi,,, Tace abinda Allah ya rubuto mai ai sai yayi su don abin daga Allah ne fa, Tana son mi kewa zuwa cikin sai gasu sun dawo ciki shida Aliyu ya koma saman carpet inda ya zauna da farko, Yasa hannu a aljihun shi yaciro kudi ya aje su agaban mama ya mike tsaye, tare da mikawa Fatima wasu kudin yana cewa, ta sai wa yara alawa su sha yana gaishe su, Maman su Aliyu sai gidiya takeyi da fatan alheri akai, (Jama,a mudinga aikata alheri muna samun addu,an yan uwa musulmai a rayuwar mu don Allah kadai yasan wanda zai ma addu,aya kama ka a rayuwa) Ya dade da fita daga gidan amma kamar yana a zaune a gurin saboda fitinanen kamshin sa da ke ta shia falon gaba daya ma gidan kamshi ya keyi,, Suna fitane Aliyu shike tuki wanan karon da kanshi don Bado driver ya koma ko,, Sai za,a koma maigidan zai kirashi yazo su tafi tare dashi, Ban fito ba sai zuwa yamma nafito zuwa part din Mama babu kowa daga รงikin yaranta yan jikokin ta kuma suna kofan gida gurin karatu , Da sallama na shiga part din nata tana zaune tana yanka ganyen miya da alaman itace da girki, Na gaida ita acikin girmamawa ba yabo ba fallasa ta amsa min da alaman cewa malam yai mata nasiha, akai, Nace ta kawo yankan ganyen in kama mata amma sai ta kiya na dauki tsintsiya na share mata ko ina a part din tare da kwashewa nasa yara suka zubar, Nadauko muciya na zauna saman dan kujeran ta na mata yar (tsugono) na tuka tuwon ya tuku sosai, gwanin ban sha,awa kafin tafito har na hada, mata miya, sai dai tana fitowa naga ranta baiso hakan ba amma sai na dake kawai,, Tambaya dai nasha shi gurin mama cewa kesa abu kaza kesa abu kaza, nabata amsa da cewa nasa komai duk abinda ta ke tambaya din daga dangin maggi daddawa kayan yaji,, Nikan ina gamawa nabar part din nata batare da na tsaya komai ba zuwa namu part din, Nan ma ban zauna ba aiki mukayi tare da mama na, kafin dare mun gama komai nai wanka ina zaune a gurin da nayi sallah kira yashigo a wayana Yaya Abubakar a layin yake cemin in zauna da,shiri zamu tafi asibiti guri Anty Samira tare ,,,,
ZEEE MAKAWA YELWA
๐ธ๐ธ๐ธTARKO๐ธ๐ธ๐ธ ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ 7โฃ6โฃ
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH -AL-WA,AJID,,,
FATAN ALHERI GAREKU YAR UWA RABIN JIKI ABIN ALFAHARI NA A,KO,DA YAUSHE ANTYNA NAFISAT HARZAMI TARE DA DUK SAURAN MEMBERS NA FAMILY DIN HARZAMI GABA DAYAN SU MAZA DA MATA,,,