Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 66

Tarko complete novel - Chapter 66

Tarko complete novel Chapter 66: Tarko complete novel Chapter 66. Lokacin da naji abinda Yaya Abubakar ya fada sai nagane nufin, Shiru nayi ina tunanen yau…

2,601 words

Lokacin da naji abinda Yaya Abubakar ya fada sai nagane nufin, Shiru nayi ina tunanen yau may ya faru da bai tafi da Anty Sadiya ba, ne, Don tare su na zuwa tare don ni banda lafiya tun zuwan mu, Amma kuma don may kuma yau zai tsiro cewa wai tare zamu tafi da shi, Abinda ban sani ba shine har Anty Sadiya ne zamuyi tafiyan tare don zamu wasu gurare gaida mutane, Sai da na fito ne gane cewa tafiyan harda ita,ne za, ayi shi a lokacin,, Saboda na samay su a mota gaba dayan su, su uku azaune, suna jirana, Yaya Abubakar da Aliyu zaune a gaba sai Anty Sadiya zaune a baya ita kadai, Na bude bayan motan na zauna tare da yi masu sallama, Na gaishe su a cikin ladabi cikin girmamawa da ladabi, Kowa ya amsa min ba laifi don haka Aliyu ya ja motan shi muka fara tafiya, saida tun a lokocin da na shiga motan na gan su zaune a cikin motan Rayuwana ya bani cewa da akwai gurin da zamu tafi kila,, Ni dai azaune nake batare da na cewa kowa komai ba, sai kallon motocin da ke ta moving a saman titin , Muryan Aliyu ne naji yana cewa, ya dai tsohuwa asai maki gyada dafafa ne ko masara mai zafi,? Murmushi naji Yaya Abubakar yayi daga gaban motan da yake a zaune ya dan gyara zaman shi ka dan yace, Ai kawai kasaya mata don ba ita ba har muma din nan ci zamuyi ai, A gaban wasu mata masu gasa masara a saman hanya ya tsayar da motar shi yana cewa, yanzu dai bari mu saya mugani, Zace suke tayi sai dai ni hankalina baya a tare da ni lokacin ina can ina tunanen duniya,, Sai ledan abu mai zafi naji Yaya Abubakar yana miko min yana cewa karbi nan. Kamshi gasassan masara ne ya daki hanci na tare gyada, dafafa , Ban san lokacin da na lumshe idona ba a hankali don dadin da naji, A zatona mu biyu ne dashi shi sai naga Anty Sadiya da nata a gaban ta, ita ma, Gidan wani mutum wanda na sani da dadewa tun ina yarinya muke zuwa da kafa daga gidan mu a lokacin bukin sallah ,,ana cewa wai wan Mama Ladi ne can mu ka fara zuwa,, Mun samu dadtijon a kofan gidan sa zaune saman kujerar katako yana kallon titi, Bai gane cewa mune ba sai da yaga Abubakar ya fito daga cikin motan ya nufo shi a cikin girmamawa ya gaishe shi, a ladabce sunan da diyan Mama Ladi ke kiran shi, dashi kawu,Manu,, Sai lokacin dattijon ke fadin a,a Sadauki ne, yau a gidan nan Sunan da na tuna cewa mafi yawan yan uwan Mama a da haka suke kiran Yaya Abubakar da shi, Mun, gaishe, shi a cikin mutunci da girmamawa inda yake muna iso cewa mu shiga cikin gida gurin iyalin shi, Gidan gina ne irin na mutanen garin birnin kebbi na da can, Ginan dakin laka wanda za a yabe ko ina har saman ginan da laka, yai kyau baka jin sanyi a cikin sa kusan muma agidan mu tsofin gina a haka suke sai dai ire,iren part din mu ne da ba,a dade da yin su sosai ba ake da dan bugun kwano, Matan duk da ba su san mu ba sun tare mu a cikin mutunci inda na gane su , Sune dai tun nada can baya da muke zuwa tun muna yara kanana, ita ta karshe da idan mun tafi muke yawan zama a dakin ta muna kwalliya don tana yawan shafa janbaki da powder, don shi kawai ranan da babu islamiya sai mu ce Anty Samira tace zamu tafi gaida kawu manu, Shikuma sai ya bamu naira,naira idan zamu dawo gida munyi kwalliya, Kallo guda nai mata sai naga matar ta girma sosai don kanta har ya fara furfura, Sun shimfida mina tabar man kaba sabuwa yasha turi mai kyau a jikin shi , Sai ruwan randar kasa mai sanyi da aka tsiyayo muna a cikin wani kwanon silver mai marfi, Anty Sadiya aka,fara bawa sai tace a,a a barshi ta gode na mika hannuwa na nakarba don wani irin kwadayin shi naji a lokacin, Don haka na kafa kai na na kwankwadi ruwan sosai na rufe kwano nace na gode, Daga gurin da Uwargidan take zaune take cewa gashi ko basu gane mu ba , Murmushi nayi nace masu matan Sadauki ne saudaukin Ladin shiyan sarakuna,,, A tare suke cewa a,a a shin kuna ? Sannun ku da zuwa an taho lafiya yaya yara ya jama nice dai mai ansawa don Anty Sadiya sai wani ya mutse fuska take yi, Shatu, ce tace shin ko keta wadda anka ba shi gidan su, Nai murmushi na ce ni ta ke dai, mun samay ku lafiya, ko ta amsa da fadin walle lafiya lau A,a kaji arziki ba aiko mungode da zumunci wallahi ina sadauki din, Ya na a kofan gidan tare da kawu , Nace ina su yar Asama, sai da suka danyi dariya su kace ashe baki manta da su ba ke nan ko,? A lokacin ne su Yaya Abubakar su ka shigo gidan tare da mai gidan a lokaci guda, Shima wani tarbama aka dauko mai kyau aka shimfida mai ya zauna Muna daga gefe suna hira da kawu Manu, na abubuwan dake faruwa acikin,dangi da kuma wurin Mama,, Da zamu tafine ya ba kawu kudi tare da mai alkawarin cewa zai dawo insha Allah kamar yadda kawu yai mai nasihan kula da zumunci, Da zamu tafi na bude yar post dina na ciro dubu biyu na basu sai fatan alheri suke min, Daga gidan kawu Manu muka wuce gidan, yayar Anty Sadiya, Tun shigan mu gidan matan gidan ke muna sannu da zuwa sama sama mu ka gaida su mu ka fito na basu kyautan kudi, suma nace su sai wa yara Sweet, Gidan wani yayan Baba na da suka hada zumunci ta gurin uwayen su wanda ke zumunci sosai da mahaifina duk cikin yan uwa nasu yafi zuwa daya, Shima mun mai kyauta muka fito zuwa gidan gwagwanin mu su biyu duk mun gaida su, Gidan karshe ne ban san ko gidan waye zamu tafi ba saidai da muka tsaya, a bayan gidan sarki gidan yake, Sadiya ce naga ta fàra hade fuskan ta tamau tana magana ciki ciki a lokacin da zamu fita daga motan, Mun shiga duk da ba musan kowa ba antare mu dai ba laifi zamu ce, Wata bakar matashiya mace yar gaye na gani ta fito daga daki, tana rike da hannun yarinyar yar kimanin shekara, uku, Ta zauna gab da kujeran da dattijuwar gidan ke zaune tana cewa sannuku da zuwa cikin dan wani yauki da yanga takira wata mace mai masu aiki tace akawo muna ruwan sha, Ganin yadda take yasa ban ko dauki ruwa guda nasha ba, Duk da ko ina jin kishin ruwa a lokacin, ba wai ban ji ba, Shigowan su Yaya Abubakar ne gidan yasa naga abin mamaki don a take a gaban mu naga wani irin sallo da yanga agaban su, Sun gaisa ana wani haba haba dashi kamar wani sarki a gaban su lokacin, Sai dattijuwar matar ke cewa matan ka ke nan a she ? Murmushi kawai yayi ba tare da yai wani magana ba, Haka kawai irin yadda na lura da mutanen gidan sai na ji ba su kwanta min a raiba, Sai daga baya,ne na fahinci ashe gidan su Aliyu abokin shi mu ke, A take na tuna cewa ai mijin Fatima wace Yaya Abubakar yai nema da farko yarasu kuma a tare muka tafi gaisuwa da yaya wanda a lokacin duk ta sake, Shin ko dai ita ce ma wanan din a zaune gaban mu yanzu , Sai a lokacin ne nai saurin dago kaina na dubu gurin da da take zaune a gefen idona, Ai,kuwa abinda na gani yasa gabana faduwa saboda irin manyataccen kallon da takewa Yaya Abubakar a lokacin, A take naji wani irin kishi wanda ban taba sanin cewa ina dashi ba ya turnike ni, a lokaci guda, Anty Sadiya wace duk ta kasa sukuni a zaune kawai take a gurin duk dan tsawon lokacin,da muka dauka azaune, Tsam ta mike daga tsaye ta kokarin gyara gyalen da ta yafa a jikita, A hankali su ka bi ta da idanuwan su falon suna kallon ta, Ina daga waje tace idan kun gama ganin ta fitane yasani nima mikewa tare da cewa sai anjiman ku, Yaya Abubakar daga gurin da yake zaune yaji wani irin nauyi da kunya sun lulube shi a lokaci guda, Murmushi ya dan sake tare da dan lumshe idanuwan shi, Abakin mota suka samay mu tsaye bayan sun dan dauki lokaci kafin su fito, Motan tayi tsit baka jin komai sai FM radio da ke aiki suna wani talla akan zazzabin cizon sauro, Daga gurin da nake zaune a bayan mota na jiyo muryan Aliyu a hankali ya na tambayan ina muka nufa kuma sai Yaya Abubakar ya bashi ansa a hankali da cewa Asibiti, Asibiti mun samu yan gidan, mijin Anty Samira da yawa sun,zo gaida su don haka ba muyi wani dadewa ba a ciki, Yaya Abubakar ya cewa Aliyu ya,wuce da mu masaukin shi direct gaba dayan mu,, Muna shiga na wuce don in gabatar da Awala kayan Anty sadiya naganiba dakin wanda hakan yasa ni sanin cewa a nan sadiya take zaune yanzu, Nafito na tada sallah na kawai ba tare da na tsaya jiran wani abuba,, Bayan na idar na dade a gurin zaune ba tare da na mike ko naiwa wata magana ba , Shiru shiru yaya Abubakar bai shigo dakin ba ya sani daukan waya na buga mai wayan tana ringing bai dauka ba, Mamakin hakan naji sosai don nasan cewa idan na kirashi wani lokaci ma shi ke kashe wayan sai ya kirani ta layinsa, Daga gurin da Anty Sadiya take zaune tana dan,ne danen wayan ta, Ji nayi tsuki sai ce min tayi yau ai bazai jiki ba Meenatu tunda yana kallon ana mai wanan kissan, Murmushin jin abinda ta fadi na yi nace, kai haba Anty wani kalar murmushi ne bai gani ba a duniyan nan, Text nai mai ina sheda mai cewa lokacin shan magani na ya dan wuce, Baidade ba sai gashi fuskan shi still a daure nasan cewa hakan nada nasaba da fitowan da mukayi daga gidan su Fatima, Ki tashi a mai dake yace min don haka ban tsaya jiran komai ba na mike tsaye inawa Anty saida safe cikin murmushi nabar dakin hotel din, A mota dagani sai shine zaune sai a lokacin naga ledan masarana da gyada wanda suka saya muna dazun, Tun shiga na ba wanda yai magana daga cikiin mu nidashi, Mun danyi nisa kadan a hankali cikin natsuwa ba tare da ya juyo gurin da nake zaune ba ya kalle ni ba, yace, Don kuyi min wullakanci ne yasa dazun kuka tashi, daga gidan su Aliyu ba tare da umurni na ba, ? Saida na gyara zamana batare da juya ba nima cikin rashin sake fuska don ko banza a gajiye nake lokacin guri kawai nake son samu in kwanta, Nace aa yar siririyar murya da cewa, ni ban bar gidan ko falon ba sai dai kawai na fitane, saboda na gaji sosai, aikawa ne, Murmushi naji ya sake tare da cewa amma dai ai kinsan ko wacece Fatima ko ? Sai a lokacin na juyo gare shi nace Fatiman diyar Gwago? Dariya na dan bashi sai cewa yayi bai ma san wace nake zance ba shi Daga haka na daure fuskana batare da,nakara cewa komai ba kuma, daga lokacin, Na juya fuska na ina fuskantar window din motan Yar boyayyan dariya na bashi saboda ya fahinci ban son jin zancen ke nan, Mun isa gida ya tsayarda mota ina kokarin bude kofan motan ina cewa saida safe , Yace ki shirya don zuwa sundaya zamu bar garin nan insha Allah, Tau kawai na ce tare Allah ya kai mu lafiya nasa kai na bar motan, Ban,jira tashin sa ba na shige gida abina batare da na tsaya jiran wani abuba, Zuciyata sai harbawa take a kan abinda nake hasashe daga gare shi shida Fatima, Mamana na samu a tsakar gidan mu tana yan aikace, aikacen ta take ce min mundawo, na amsa mata da tare da mata sannu da gida, Daga haka na shige daki jikina duk ba kwari a lokacin, Tufafin jikina na fara sauyawa tukun tare da son in watsa ruwa a jikina, Ina kokarin mikewa ne wani irin yunwa ya ziyarce ban jira komai ba na fara cusa abinci a cikina , Saidai badon dadi nake cin sa ba cusawa kawai nake yin don ceton kaina, daga yuwan da nake ji a lokacin,,

****** ********** ****** Yana shirin kwanciya ne yaji wayan shi ta dauki ringing alamar kira ya shigo mai, Sadiya wace ke kwance a gefen shi tankar ta na barci ta kara lafewa, Da,farko wani irin shu,umin murmushi taji ya sauke murya kasa, kasa yake cewa Aiko min dadewa bazan manta da muryan da ya fara yawo a kwakwalwana da farko, Sai ake tambayan shi ya muka dawo daga ziyaran da muka kai dazun, Kafin ya bada ansa saida ya dan juya, gurin da take a kwance yaga still tana nan yadda take da farko, Sai yaci gaba da,wayan shi yana cewa, lafiya kalau muka dawo, Tambaya ta jefo mai da cewa tana fatan har yanzu akwai kaunar ta a zuciyar shi kamar farko don taga yanzu ya zama dan madubin mata, Dariya sosai zancen ta ya bata tare da cewa a cikin dariyar shi wanda yasa shi mikewa zuwa dan wani wajen shan iska dake adakin ta gefe, guda, Yace mata aikema kin san cewa har in na zama dan madubin mata tokece ai ta farkon dauka ki duba ko ? Taji dadin wanan zancen don hakan ya tabbatar mata da cewa ta samu karbuwa sosai daga gare shi, Tace amma ai kasan yanzu da can baya ba daya bane akwai yan banbanci sosai, Murmushi yayi tare da cewa ke ce ke wanan tunanen don ni a gareni duk daya ne babu wani canji a hakan ma, Allah ne ya kyauta don Sadiya ji tayi tankar ta kuwata saboda abinda kunnuwanta ya jiyo mata, Sun dauki lokaci suna wayan sannan su kayi sallama tare yi ma juna kalaman soyayyan sai da safe, Bathroom ya shiga yadan kara kimtsa jikin shi kafin ya kwanta, Ya dan dauki hannuwan shi ya dora a jikin Sadiya wace tai saurin kauda jikin ta daga gare shi, Yai mamaki kwarai da ganin ashe ba barci takeyi ba don alama bai nuna cewa idon ta biyu ba, Duk da baiji dadin yadda taji shi yana soyewa awaya ba gaban ta, Amma da yake na mijin duniya ne sai kawai ya dake kamar babu komai yana kokarin cin ma burin shi gare ta, Malam da kayi hakkuri har ka jira wace tafi kowa tazo ma tukun ina ga zaifi ma sauki, Murmushin kasaita ya sake tare da cewa ai ba wani dadewa zatayi ba tashigo kawai da abinda nake jira ne, Daga haka ya gyara kwanciyar shi ya juya mata baya batare da ya nemi wani abu daga gare ta ba don yasan cewa ya riga ya bata wanan daren nashi ko yau, Ita ko Sadiya kamar ta hade zuciyar ta take ji a lokacin don barci ma gaba daya yaki zuwa mata ranan, Sai zuwa dare sosai bayan zuciyar ta yai ta mata sake ,sake kala kala akan zaman gidan Abubakar,,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull