Tarko complete novel - Chapter 67
Tarko complete novel Chapter 67: Tarko complete novel Chapter 67. ****** ********** ****** Waya muke da Anty Amarya tana sheda min cewa, an na neman mu a…
2,723 words
****** ********** ****** Waya muke da Anty Amarya tana sheda min cewa, an na neman mu a school muyi summiting din evaluation form din mu, Nan muka fara hiran rayuwa da ita kamar kullun take tambayana yaushe ne zamu koma, nace ban san time ba amna dai ina ganin kamar nan da weekend ne don wai hutu ya dauka yace, Amna kuma ni ina son a barni don ayi sunan Anty Samira dani kafin na wuce, Tace ke ma kin san da wuya ya barki nan din don ba zai yarda ba, Nace ai yanzu ina da excuse don zan tsaya batun summiting din form dina, Sai kuma nace ai ni Anty bama zan bishi ba saboda idan son samune in zauna abina a gida, Cikin garaje tace min ke kada ki fara shi idan bai bari ba kawai ki bishi ku tafi don auren ki yafi maki wanan karatun, Shiru nayi ina sauraren ta har ta kare min fada da fadakarwa akan muhinmancin rayuwar aure, Nace cikin sanyin murya Anty Yaya Abubakar fa da alaman wani auren ne zai jajibo kuma again, Da karfi tace what ? Wai wasa ko da gaske Meenatu ? Nace wallahi ko Anty ina matar da mijin ta ya rasu wace ya kaini mukai gaisuwa a sokoto lokacin da muka dawo daga Niger, Tace kwarai kuwa anyi haka Meenatu, don Allah bari zancen nan Meenat, Nace to ni dai abinda nake ji a jikina ke nan Anty don dai ma naga alama, Nake fada mata yadda akayi ya kaimu gidan su Fatima din da action din da suke yiwa junan su, Abin mamako sai naji anty ta kwashe da wani irin mahaukacin dariya a cikin waya, tace, Na Mijin Duniya ke nan shi watau ma ba cikin mazan zamanin nan yake ba ke nan ? Dan tsuki nayi nace wallahi Anty wata yar duniyace fa haka da ita sai wasu matsatsun kaya take sakawa ajikin ta, Dariya anty tayi min tace wata sabuwar zance ke nan kuma amma dai bawai dagaske ba dai ko ? Kune dai ke ganin hakan ko ? Nace anty ni dai haka zuciya take nunamin, tace to ina ruwanki tunda ba akanki zata zauna ba, Ai kowa da halinta take zama da miji sannan hakan kuma ba haramun bane ai, Don haka koma da zaiyi ne yaje yai tayi shiyasani don babu abinda ya damay ki, Kawai tunda kinga shi mutum ne mai son raya sunna to ki dai yi kokarin gyara fannin ki kawai, Sai ki kara kwantar da hankalin ki kiga may ya fi bukata ga mace a rayuwan shi, Daga fannin abinci, tsabta, kwalliya, kwanciya da sauran su, Daga gurin da nake kwance a saman gadon Mamana, nadan lumshe idona don jin bayanan da Anty tai min, Sai naga cewa wani ne daga ciki ban yiwa Yayana Abubakar da har zai sashi ganin wata ta waje can, Gwargwdo gaba dayan mu kowacen mu tana kyautata mai sosai ta ko wani fanni, Muryan Anty ne yakatseni da take cewa su maza da kike ganin su Meenatu idan suyi niyar yin abu babu fashi sai suncin ma gurin su, Don haka bawai zaki ce zaki ci gaba da yadda kike da farko bane yanzu kuma sai mu canza mai wani salon idan mun fahinci ko yaya dabi,un ta yake, Don fa kin san cewa kowa da kalar ta, ta makircin balle ita wanan da ta taba zaman gidan miji tun farko kinga zata fiku iya badakala, ga maza, Don kin ga ai yanzu mun fahinci ko wacece Salawatu ko ? Na ce hmmm kawai don ko ita aiban gama fahintar taba ai, don kishiyace fa, yau dadi gobe daci,,, Bawai anty ta kare zancen ta bane wayan ya katse a lokacin, Don haka sai na fahinci cewa kudin wayantane ya kare kila, Nisawa nayi tare da kokarin gyara kwanciya na, don inji dadin tunane, Mahaifiyatace na gani a tsaye tana gyara kayan dake saman kujera,, Sai a lokacin nasan da cewa tana dakin don ganin yawan kayan da ta nade a gefen ta, Kafin inyi wani tunane ta jefo min tabaya da cewa, Wacece yake nema ? A hankali na furta mata da cewa wanan Fatiman ce kaunan Aliyu da yaso aure da farko Tace ta gidan zabarmawa hayi na ce ita ce Mama , Tace to sai may yar Baba idan zai aure ta aiba akanki zata zauna ba ko kuma ba ke ce zai kawo wa kishiya ba ai, Azuciya ta nace Mama ke nan ai kowan mu ya shafa wanan zancen mutanen da ne ke cewa hakan , Yanzu ai kishiya kowa take kaiwa hari ba wai sai wace take biwa ba, Mama tace kibi a hankali kamar yadda Anty n ki ta fada maki don kinga kina a cikin lalura yanzu kada kijawa kanki wani wahala , Shi namiji babu ruwan shi tunda har kikaji ya furta to yi zai yi balle yana jin aljihun shi da yan canji, Kuma ma don mai sunan malam ya ce zai kara aure aiba abin mamaki bane idan kikayi la,akari da kalaman iyayyen shi a gare shi, Don komai girman ka bakin iyayye zai iya kama ka don dai tun lokacin auren ku da mama taita masifan cewa, Malam yayiwa Sadiyar yar ta kishiya to kema sai mai sunan malam yai maki kinji yadda Sadiyan taji zafi, Idona na rutse don takaicin mama Ladi ina maiyin tir da wanan kalamin nata da ta lakakawa Dan ta, Mamana tace yanzun dai ki kwantar da hankaliki duk abunda zai yi kada ki fara inji sunan ki acikin wani zance mara dadi, Ki sawa kanki hakkuri tunda ba,a kanki zata zauna ba kuma ma wai zaki iya jayayya da hukuncin Allah ne shim,? Don haka ko kadan kada ki sawa kanki wani fitina mai wahal da ke daga baya, Kai na gyada tare da amsawa da bakina nace to mama insha Allahu zan tsare, Ta juya tafita ban san lokacin da wasu hawayen takaici su ka biyu idona ba tare da malolon bakin ciki, Mutum yai ta cika gida da kulakan mata kaman wanda zai kai su kurmi, sayar wa, Idan kaga yaya Abubakar sai kace idan an saka mai yatsa a baki bazai ciza ba, ma, Duk da nasan cewa shi gwarzo ne sosai ga matan shi yana da kokarin biya masu bukatun su ta ko wani fanni, Amma da wuya ace ansamu mutum a wanan zamanin yana koyi da sunnan irin haka,
****** ********** ****** Yau har kusan karfe dayan rana wayana yana a kashe ban kunna ba don gaba daya nakashe wayan saboda ban son surutu, Wayan malam tsoho ne yabayar wai a kawo min ana magana dani ta layin shi, Tun ban karba ba nasan cewa Yaya Abubakar ne a layin don haka na karbi wayan ban tsan mani a kunne take ba sai muryan shi naji yana cewa, Ya akayi tun safe yau wayanki yake a kashe ba,a samun ki, Nace ba komai just dai akashe take tun safe, Yace saboda baki damu da kiji lafiyan dan uwan ki ba ko dan kina agaban malam tsoho yanzu, Idan da dane daya fadi hakan da murmushi zanyi amma sai yaji sabanin hakan don shiru nayi saboda wani irin takaicin shi nake ji a lokacin, Shirun da yaji nayi yasashi tambayana cewa lagiya kike kuwa yau, Meenatu, ? Nabashi amsa da cewa lafiya kalau nake kawai dai daga barci nake, Yace to yaya kuke ya baby I hope yau yana kicking fiye da kullun ko ? Nan ma ban taka mai basai dai kawai hmmm da nace mai, tare da yin shiru, Hakan ya sashi fahintar cewa akwai matsala ke nan don da yaji na bashi ansa, Don haka sai kawai na,ji yace ok sai anjima ke nan, zan shigo,, Wayan na bi da hararan takaici tankar shi ne Sadaukin mazan, a gabana,
Dakaina namike zuwa gurin malam tsoho don na mayar mai da wayan shi, da ya aiko min na karba kira, Babu mutane gurin shi a lokacin don haka na samu daman sakewa dashi, Tunda na nufoshi yake murmushi yana cewa yau ina kika shige mijin ki ke neman ki, Murmushi nayi mai kawau nace ina nana gefe guda ina hutawa malam barci nayi yau sosai don jiya mun sha yawo, Malam tsoho yace min maigidan naki ya ce min zaku koma gobe ko jibi wai aiki ya taso mai a ma,iakatar su ,, Nace, tau gaskiya banda labari malam saboda bai fada min ba kuma ma ai ina ganin bazan koma ba saboda makarantar mu suna son ganin mu nan da wani sati mai zuwa,, Ya amsa da cew na,am gaskiya 8dan hakane tafiyan zai zama maki biyu ke nan , Malam yace Meenatu dama ina son ganin ki tun zuwan,ku garin nan sai dai bamu samu lokacin hakan ba saboda yan matsalolin da aka samu, Nai maza nace mashi to malam gani ai yanzu ko yace to samu guri ki zauna da kyau sai kiji may zan fada maki, Kamar yadda malam ya umurceni hakan na gyara na fuskance shi a cikin natsuwa ina sauraren shi, Yace Aminatu ba komai bane yasa na zaunar dake sai akan zaman ki da mutanen duniya musan man ma abokan zaman ki da kuma yanuwan haihuwanku watau yan uwan haihuwan mijikin wa yanda yanzu sun zama kamar dangin miji a gareki, Mafi yawan su zasu manta da irin alakar dake tsakanin ki dasu kiga suna maki wasu abubuwa tankar ba,a tsatso guda kuka fito da su ba, Hakan shima maigidan naki duk da nasan cewa ya rike amanar da muka bashi bakamar sauran maza da ake hada alakar zumunci su watsar ba, saboda ba su san muhinmancin yin hakan ba, To mudai gaskiya Alhamdullahi don zance mai suna na yai muna bazata gurin rike amana da gaskiya, Abinda malam ya fada gaskiyane don haka nai murmushi nadukar da kaina na kasa don nasan cewa yayi kamar yadda malam din yace din,,,,,, Afuwan please 👏👏
Jumma,atu mubark to all Muslims ummah,,,, ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 7⃣7⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH - AL - MA,AJID
Malam tsoho yaci gaba da cewa, cikin natsuwa don in fahince shi, Don haka ko,ba a fada mun san cewa wanan kyautatawan ya fito daga gare ki ne, Don haka hakan zakici gaba da gyara rayuwan ki da kowa a koda yaushe,, Yadda kika gyara a tsakanin ki da mijin ki tun farko har ya fahince ki to ko yanzu ma haka ,zakiyi da sauran abokan zaman ki, Duk da nasan kinayi din don haka sai ki kara zage damtsen ki gurin kyautatawa, Don haka kiyi ta addu,oin da na baki tun farko babu abinda zai samay ki da yardan Allah, Ita kuma diyar wanan muguwar da kuke zama atare da ita, barta can da mugun abinsu duk sherin uwar ta ce ke koma mata, Babu abinda zai samay ki dayardan Allah don Allah yana tare da mai tsarkaken zuciya akoda yaushe , Banda wani shakka akan ki Aminatu ko mata nawa mai suna zai yi don na riga da na haka mai TARKON da ba zai iya kurcewa daga cikin sa ba tun farko, Don haka ke je kiyi tawa mijin ki biyayya yadda zaki kara shiga zuciyar shi akoda yaushe, A hankali na dan runtse idanuwa na saboda ni dai a gani na banga wani TARKON da aka dana wanda ke aiki ba akan mutumin da ya maida mata kamar wata sana,a , Ina cikin wanan tuna nen ne naji muryan malam tsoho yana cewa, Naso ace a gaban mu zaki haihu don akwai abubuwan ada ya kamata ai maki yayin da cikin ki ya tasan ma haihuwa, Saidai mai gidan naki san boko ne baida ra,ayin dawowan ki gida nake gani, A hankali na dago kaina a sanyayye na ce malam idan har ka bukacin hakan ai zai yarda da hakan shima, Malam yace idan mutum ya kasance mai hakkuri to kada ka yawaita matsa mashi akan al,amuran shi, don kada yaga gazawan ka, Murmushi nayi a hankali nace malam nasan cewa ba za,a samu wani matsala ba insha Allah, Yace yanzu dai kafin ki tafi akwai abubuwan da zan baki kki kula da kyau kiyi amfani dasu don Allah, Nace mai nagode saidai kuma muka dauko hiran yadda rayuwa yake guda a yanzu da gidan mu da kuma duniya, ma gaba daya, Ina zaune tare da malam Yaya Abubakar ya aje motan shi nisa kadan damu, Ban motsa ba don nasan cewa zai hangeni idan nace zan shige daga ciki, Ganin da yai muna zaune tare da malam yasa shi kuro muna ido tun daga nesa cikin mamaki, Ya karaso da sallama dauke a bakin shi malam ne ya karba mai a fili nikan azuciya na karba mai, Gaisawa suka fara yi da malam tsoho yayin,da idon shi ke a kaina, Ya sauke su a saman dan ciki,nada ya turo zanin dake a,jikina, Ganin haka yasa ni mikewa, tsam da nufin shiga gida a lokacin idon shi ya daga ya na mai bina da kallo, Lokacin na ke masa ina kwana da kuma tambayan lafiyan shi, Saida ya lumshe idanun shi cikin bajinta da iya jan aji, ya karba da cewa lafiya, Gaba na yai mugun faduwa don a lokacin naso na fada mai zancen neman da ake min school din mu, Ya Abubakar ya dan rage fara,an dake dauke a fuskan shi yayin da ya fuskance ni, Tambaya ya jefo min da cewa yau may yasa wayan ki yake a kashene tun safe, Na rasa amsan da zan bashi in wanke kai na don zargi, Can nace wayan tawa ce ba caji a cikin don jiya a gajiye nake hakan yasani mantawa na sakata caji,, Ya ce ai wanan ba dabiar alheri bace ace tun safe mutum waya a kashe haka, Yace daman ina son na sheda maki cewa ki shirya zuwa gobe ko jibi zamu koma insha Allah, Duk da naji wani iri amma sai na dake ina cewa gashi kuma wai ana neman mu a school next week mukai evaluation form din mu, Yace cikin wani irin murya bazaki koma tare da mu din ba ke nan ko ? A hankali na koma na zauna gurin da nake zaune da farko nace, A,a ba wai bazan koma sa ku bane gani nayi dai cewa tafiyan zai min yawa in tafi gobe next week kuma na dawo Ok you can go a head duk lokacin da kika gama sai ki dawo, Malam tsoho wanda ke sauraren zancen mu ya ce abinda zata tsaya yi makarantan ba mai muhin, manci bane sosai ko, No, ni ban san komai ba akai kawai ta tsaya din ai ba komai idan ta gama sai ta dawo, Malam tsoho yadago kai yana dubana a take na bata raina don ban son ya tillas,ta ni bin shi don kada nai missing din karatuna, Ganin haka yasa shi dan yin murmushi yace jeki ciki Meenatu zan nemay ki anjima, Ina shigewa ya juya gurin Yaya Abubakar yace amma dai kasan cewa tana karatu tun farko ko ? Ya dago idon shi da atake suka rine sun canza kalla alaman ran shi ya baci, Yace, anzu ni may nace ta tsaya har ta gama karatun ta ai zaifi, A,a mai suna may yai zafi haka idan har baka yarda ba ai sai ta biku ku koma tare ba shi ke nan ba, Amma kunzo dadi, dadi sai kuma gurin koma bacin rai ya shigo, Yanzu ai bincikawa zakayi kaji idan abin ba mai muhin manci bane kaga sai ku tafi, Sai a lokacin ya dan sake ran shi, yace zan kira na bincika, Kawai dai bata son komawa ne ba don komai ba sai don kishi da suka sawa kan su duk kan su, Dariya malam yayi yace kishi kuma ashe kasan kayi laifine, Ya gyara zaman shi yana cewa gaba dayan su basu san halina bane don haka zan gyarawa kowar su zama, don ta shiga hankalin ta, Idan ma aure zanyi ai ba wace ta isa ta hanani yi daga cikin su, Da sauri mai sunan malam ya juyo yana kallon Abubakar, a cikin mamaki, yace aure ka mai suna,? Yaushe kuma a ina zakayi shi, ? Ya bawa kakan ansa da cewa, anan garin ne ina gani, Malam tsoho wanda mamaki da imani sukai mai yawa sai girgiza kai kawai ya ke ta yi, lokacin,