Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 68

Tarko complete novel - Chapter 68

Tarko complete novel Chapter 68: Tarko complete novel Chapter 68. ****** ********** ****** Bayan wayan su da Uncle dina inda Uncle ke sheda mai cewa an…

3,166 words

****** ********** ****** Bayan wayan su da Uncle dina inda Uncle ke sheda mai cewa an bugo mai waya ana neman mu next week a school, Hakan ne ya dan sashi rage fushin shi akan cewa ba don kar na bishi ba nace hakan, Badon rashi ya so ba Allah ya kwace ni daga fushin shi, Ranan da zasu wuce ina , part din mu ban fito ba ,shima kan shi bai iso gidan da wuri ba sai zuwa wani lokaci, Yan abubuwan da na saya don akaiwa Baba Ramatu, da Fattu tare da,Antyn Saloon nabawa Baba Hamza shi da Baba Wadda, Ganin cewa ana ta hada,hadan sallaman su ni ban fito ba yashi shiga pary din mu, Ina zaune ina cin, dan wake da mai da yaji, da fura a kwanon sha mai sanyi a gefe na, Idon shi suka sauka ga abinda na keyi a kwanon , Sai naga ya kada kai alaman yayi sun gaisa da Mama na acikin mutunci da girmamawa, Yake tambayan ban san cewa suna shirin tafiya bane ban fito ba, Nai kwal da idona na duka don ban da abin cewa a lokacin, Ina ganin yana kokarin saka hannuwan shi a aljihun rigar shi, na kauda kai gefe guda, Muryan shi naji yana cewa, idan zaki tafi sokoto mun yi magana da Aliyu cewa zai zo ya kai ki don ban son shiga motan haya don ganganci, So da zaran ki shirya ki bugo min sai na turo maki shi, Ki tabbatar da cewa kina zuwa awo saboda tsaron lafiyan ko dana Baby, Duk da na so ace mun koma tare sai muje gurin wanan doctor naki inji dalili rufe min zancen cikin ki da yayi alhalin ina mijinki na sunna, Kaina na dukar kasa azuci nace dama nasan shirun da yaya yayi don muna a gida ne ba wai ya fita zancen bane, Amma Allah ya kwace ni da ga tarkon shi don da ban san irin hukuncin da zai zarta min ba, Yamiko min kudi yana cewa idan da wani abu sai ki fada min na turo maki Aliyu da,shi, Idan yace Aliyu a da ban jin haushi amma a yanzu sai naji wani irin takaici ya turnu ko min a zuciya ta, Nakarba ina cewa nagode yace Baba ya hada muna tsaraba masu yawa naso na samay shi a gida kafin ya fita in mai godiya, Sai a lokacin na dago kai na ce Babana, ? Cikin mamaki ya bani ansa da cewa wa yasan cewa Baban ki ne shi tunda mutane da baban Sadauki suka san shi, Abinda yasani murmushi ke nan tun shigowa wan shi don nasan nima dai maganar tazo min ne amma ai gaskiya ya fada, Massage ce ta shigo a wayan shi abinda ya dauke mai hankali ke nan yana karantawa yana dan murmushi,gefen fuska, A take na gane cewa duk yadda akayi wasu kalaman soyayya ne yake karantawa hakan, Kafin ya kai ga karshen karatun shi na jefo mai tambaya da cewa , Sai ka dawo ne za ,a daura auren naku ko ,? Ba tare da ya daina karatun da yakeyi ba yadan sake murmushi mai sauti daga fuskan shi, A hankali ya dago daga karatun da yakeyi a wayan shi yana cewa ko tsoron haka ya hanaki tafiya da mu, ? Saida na dauki dan wake da tsinke na saka a mai da yaji na kai ga bakina na fara taunawa san, nan ce, Ba tsoro ya hani bin ku ba yaya , ai da ma sai na bika don ba zan so wata ta shivo ta kwace min Yaya ba don ita ma din ai yayan ta, Kawai dai don kada in samu matsalane a karatun tun da saura kiris ya rage in gama, Murmushi yayi yana cewa, ban san munafukin da ya fada maku wanan zancen ba, Nace babu wanda ya fada muna kawai dai yadda ake kokarin sace zuciyar mijin mu a lokaci guda yasa mu fahinta, Baiyi magana ba sai mikewa da yayi yana cewa zamu tafi ki kula da kan ki kuma zamuyi waya naji yaushe ne zaki dawo, Na lumshe idona a hankali tare da kokarin mikewa tsaye, don nai masu rakiya, Muryan Yaya Abubakar ce ta shigo kunne na idan yake magana tankar mai rada yana cewa miss you , Don kin san bada son raina zan barki a gida ba yanzu haka don ina bukatar iyalaina a kusa dani, Murmushi kawai nayi mai batare da cewa komai ba don nasan abinda ya fada gaskiyane,

Part din Mama Ladi na shiga na samu Anty Sadiya tana zaune kusa da Anty Samira wace aka sallamo daga asibiti, Mun gaisa da su inda Samira ke cewa ashe ke muna nan da ke ba tare zaku koma ba, Murmushi nayi ina kokarin kaiwa zaune samira takara cewa Meenatu wanan cikin naki fa da alaman yai nisa sosai, Da sauri Ànty Sadiya ta juyo tana kallo na acikin mamaki idon ta ya sauka a dan cikina da ya turo gaban zani na, Damm, dammm gaban ta ya bayar cikin wani irin mamaki ta furta a fili tace, Meenatu cikin shin akgare ki haka bamu sani ba shin ? Anty samira tace wai kuna bani mamaki da za,a ce duk wai har mai gidan ku ba ku gane wannan cikin da har ya zama katon baby yanzu, A take duk wani annurin fuskan Sadiya ya gushe a lokaci guda, Fuskanta ya matse ya koma na bacin rai mun fahinci hakan gaba dayan mu amma sai muka basar da ita tankar bamu fahince ta ba, Muna tsaye a bakin kofan gidan mu suka bar gari alokacin naji wani iri a zuciyata, Take kewan mijina ya fara shiga zuciyata son shi da kaunar shi yana ratsa sassan jikina ta ko ina, A hankali naji wani irin kasala yana mamaye man sassan jikina ta ko ina,, Yan uwan Sadiya basu kara shiga ciki ba daga na sukayi muna sallama suka tafi inda Habbi sister din anty sadiya ta ke cewa wai ban zo gidan ta ba, Nai murmushi tare da bata hakkuri nace zan zo insha Allah mu kai masu sallama suka tafi,abin su, Suna bada baya Aisha tace min da kin mutu idan kin je gidan su wayan nan mayun masu mugun abu azuciya,, Najuya daga tafiyan da na fara nace haba dai Anty Aisha may yai zafi haka kike masu wanan zarin haka,? Cikin mamaki suke hada baki suna cewa ke baki san cewa mahaifiyar su ta kawo hari nan gidan ba malam tsoho ya tona mata asiri, Labarin da Baba Wadda ya bamu shine ya fado min arai suke kara gaya min harda wanda Baba Wadda bai fada min ba,, Mamaki sosai naji don zancen ya tabbata ke nan da gaske, Part din mu na fara shiga gurin mamana nasamay ta tana kwashe abinci, Take tambayana har sun tafine nace mata eh sun tafi , Ganin da Mamana tai min jikina a sanyaye tun shigowa na sai take zaton don tafiyan mijina ne nakoma hakan, Kin fara da kin sani ki bisu ne ko ? Da sauri na girgiza kai tare da cewa haba dai kai Mama, Ina dai tunanen duniya ne yanzu su Anty Aishe ke fada min zance akan mahaifiyar su Sadiya, Mama tace ai wanan tsohon zancen ne nima a lokacin da abin yafaru hankalina ya tashi kwarai amma daga baya sai na bar wa Allah komai nasan insha Allah bazata iya komai da ke ba, Nace tare da nisawa cikin damuwa Allah ya kyauta Mama,

****** ********** ****** A zaune gurin da sadiya take a gefen shi tana kallon yadda suke waya da Fatima wace kusan duk minti talati sai ta kirashi, Tambaya Sadiya ta jefo mashi cewa, harda kai cikin rufe min zancen cikin Meenatu Abubakar ? A bazata tambayan tazo mashi tankar bada shi takeyin magana ba don tankar bai jita ba ma Sai da ya dauki yan min tuna sannan yake cewa, yadda kika tsunci zancen a nan haka nima na tsunce shi anan din, Tace kana nufin cewa kaima baka san cewa tana dauke da ciki har ya girma haka ba, Ya zanyi in sani tunda ni ba likita bane kuma ni ba mace bace balle na gane hakan, Ya dan lumshe idon shi tare da lashe labben sa ya furza iska sannan yace, Malam tsoho naji yana zancen haihuwanta abinda yasani sani ke nan da saidai kawai naji haihuwan ta kwasam, A wani jahilcin ta,wai tana jin kunya fada min cewa tana da ciki, Wai ita azaton ta zangani a idona , yayazan yi in san ciki wanda ko bari ba,a taba yi a gidan sa ba yagani, Wani irin abu ne ya kara sukan zuciyar Sadiya don tasan cewa da ita yake ke nan, Juyawa tayi tana mai kallon window motar tace a cikin bacin rai yanzu aga haihuwa nan za,a ma a gida sai kasan yadda yake ko tunda ba,a taba ma bari ba a gida, Murmushi ya kara yi tare da dan shafa fuskan shi a cikin takaici yace, Niba jahili bane nasan cewa Allah ne ke bayarwa ga wanda yaso kuma ahike hanawa a inda yaso don haka kada ki canza min zance please,, Daga haka babu wanda ya kara cewa uffan acikin su, sai karan gudun mota kawai kakeji yana tashi Wanan karon wayan shi tayi wani sabon sauti again suna a cikin gari ne kiran Salawatu ya shigo wace, tana son jin ko yana ina ne a lokacin don ta dawo daga gurin da ta tafi ansan kayan gyaran jikin mata, Wanan halinta ne sosai haka takeyi idan tasan baya gida ko gari sai ta kirashi tankar kiran soyayya tana wani kashe murya tana cewa hello, sweet Oga ,, Kana hanya ne yanzu shi kuma da yake na miji ne, bai san cewa tako bane ta hada mai sai ya bata amsa da cewa ya na guri kaza ai, A hakan sai ta samu daman fita duk inda take so ko kuma ta karasa ayin abinda ta fita yi waje, alokacin, Yauma hakane yana fama fadawa Salawatu cewa yanzu suke shigowa Abuja , Yakashe kiran ke nan zai aje wayan kiran Fatima ya shigo itama yake mata cewa ai sun shigo gari yanzun nan sai dai basu kai gida ba,, Daga gefen da take ta sake wani irin tsuki mai karfi tare da dan gyara zaman ta saboda takaicin da take gani da ji a gaban, ta, Yau Abubakar din tane mata ke ta tawanda da shi kaman wani kwallo, a gaban ta, Duk da tasan cewa yanzu akwai canji sosai a tare da shi ba kamar da can baya ba da yake nata ita kadai, Amma ai so da kaunan da take mai yana nan bai gushe ba, kuma tana kishin abinta, Tunda shima duk da samun wasu matan da yayi ai fita batun taba yana dan lalabata a hankali, Da farko bata jin zafin abinda take ganin ya na yi da wasu matan shi, Saidai kuma yanzu zancen Fatima yasa tana jin zafi da kishin mijin ta don sanin da tayi na kowaye Fatiman tun farko, Har suka karaso gida hankalin ta baya a jikin ta sam jin sun iso yasata daukan hand bag din ta zuwa cikin gidan, batare da ta tsaya jiran wani abu ba, Da murna Baba Ramatu tazo ta tare ta tana raraba ido taga shigowa na daga baya, Sai daga baya ne ta fahinci cewa badani aka dawo ba a falo suka yada zangon su inda salawatu tafito tariyan maigida cikin rangwada da kararairaya , Ruwan da Baba Ramatu takawo wa Anty sadiya shi take sha a hankali tare da sauke ajiyan zuciya, Idon ta yana akan Salawatu wace kamar zata shige mai ajiki don mannewa da take mai, Azuciyar Sadiya tace zaki ji jiki ai fon badan goyo bane wanan, din da kike gani, Batakai karashen tunanen taba taji wayan Fatima ya shigo wsi tana mashi a huta gajiyan hanya,, Yadda Salawatu ta hankalta da yadda yake kashe ido yana lumshe su tare da kwantar da kai yasa ta gane cewa akwai sabon kulli, don jin da tayi yana cewa agaida, Baby, Daga ida Sadiya take zaune take kallon reaction din Salawatu dariya yaso kamata, amma sai ta cije tace kema kiji yadda kowa yaji, azuciyan ta, Daga haka ta mike zuwa dakinta gyalen ta hannu rabi yana jan kasa dayan hannunta dauke da hand bag din ta, Sai a lokacin bayan ya gama wayan da Fatima ya fahinci Salawatu ta dan tsargu ga yanayin ta yadda ya nuna ,, Don haka sai ya sake mata wani killing smile tare da dan jawo ta zuwa jikin shi,, Don ta tabbatar da zargin ta sai ta daure tana cewa ina Meenatu may yasa bata dawo ba, Murmushi yayi tare dan kokarin dagawa daga man,newar da sukayi da Salawatu yana cewa zata koma school ne shiyasa ta tsaya, Tace taufa, kamar tace dawa kake waya sai kuma taga rashin da cewan hakan sai take cewa ayya ashe zamu sha kewan ta, Yana kokarin hawa sama,ne yake cewa kila ma sai ta haihu zata dawo garin nan, Amma zan so tazo kafin ta haihu wai,don mu ga likita da take gani,, Pardon Sir kana nufin cewa ciki ne ga Meenatu ko waye kake zancen haihuwan ta, ne wai, Saida ya hau stairs din yadan juyo inda ya barta tsaye yana cewa, Zancen Meenatu muke yi da ke ko yanzu ko baki ji bane, , A hankali ta koma saman kujeran da ta tashi tana maimaita maganar shi ciki fa ? As how har wanan karamar yarinyar ta dauki ciki ita tana jiran may ?

****** ********** ****** Tun bayan wucewan su ba muyi waya dashi ba bawai na manta ba ,a,a kawai dai ban kira bane, Don nima ina son in dan gwada jan aji irin na mata saboda nima in san ko ina da star a zuciyar shi, Har dare karfe tara ina shirin kwantawa mama na daga gefena a zaune tana gyaran Wani sarkan ta, A lokacin ne wayana yai kara alaman kira na shigo min ke nan, Banyi saurin daga wayan ba abinda ya sa mamana dago kai ta dan dubeni a hankali Ganin hakan ya sani mika hannu na dauki wayan na danna received a hankali tare da manna wayan a kunne na ina cewa, Assalamu Alaikum naji muryan Yaya Abubakar shima yana karba min, Gaishe shi nafara yi naji ya karba min a dadare, nace a hankali ya hanya, Ya ce ai baki damu da sanin ya hanyar ta mu ta kasance ba tunda baki kirakiji ba, Watau ke kin samu mutanen gida kin manta da kowa ke nan tun da kina ganin ki a gida, Nadan lumshe idona tare da dan gyara kwanciyana nace, sau biyu ina kira ana cewa not reachable, Sai naji yadan ce hmm din da ya saba fada, yace ya kuke, ya kuma kowa agida ? Nace lafiya ina su anty Sadiya da Salawatu da Baba Ramatu,, Murmushi naji yayi tare da sauke ajiyan zuciya yace suna nan suna fushi dake dani, Da sauri nace dani kuma Yaya may nai madu suke fushi dani, Mamata ce naga ta dan kalloni a gurin da take zaune don haka sai na dan rage sautin muryana, Yaya Abubakar yace zancen cikin dake a jikin ki da kika boyewa kowan su, Da sauri nace to suyi hakkuri ba laifina bane nima ban san hakan ba, Amma harda Salawatu ta sanine na tambaya a gagauce, Yabani ansa da cewa ta sani mana nina fada mata dazun da na dawo, Ban san lokacin da na lumshe idona ba ina cewa a zuciyata da tun farko na fada mai da haka zai fada maxu zancen, Suko su sani da abincikin vikina agaba da suraitai barkatai, Muryan shine naji ya katseni yanacewa cikin wani yanayi Anya Meenatu zan ya iya barinki ki koma school kuwa saboda ina bukantan ku a kusa dani don ki dinga ziyartan asibiti a nan Don haka sai ki shirya nan da kwana biyu zan dawo na dauke ki kidawo, Ban san lokacin dana ce cikin dan marairaice murya haba sadauki yaushe har naje school nagama abinda nakeyi na fara lectures ? Ok bazaki dawo ba ke nan ko ? Zance mai ba haka nake nufi ba naji ya kashe wayan dip,,,, Daga gurin da mamana take zaune ta kalleni cikin natsuwa tace so yake ki dawo ko ? Na daga mata kai a hankali tare da cewa Ummm don raina ya riga da ya baci ko a lokacin, Mama tace dama ai babanki ya fadi cewa baiso yatafi yabarki ba a yadda ya nuna mai , Shiru mu kayi gaba dayan mu dakin kowa da abinda yake sakawa azuciyar shi, Ida mama na taci gaba da abinda takeyi batare da ce min kala ba kuma, Azuciya ta nace gaskiya ni bazan koma ba sai dai na hada shi da malam tsoho ko Baba Buhari, Muryan mahaifiya na ce yadawo dani daga abinda nake sakawa tana cewa Tunda ya kashe a cikin fushi ki kirashi ki fada mai cewa yabari kije sokoton ki gani idan ba wani matsala zaki bugo mashi ,, Kinga hakan zai saya san cewa bawai da son ranki kika tsaya ba kema, Naji dadin shawaran mahaifiyata don shine ake son zama da manya a kusa, Tace kin daiga kunzo a tare dadi dadi kowa yana sha,awan hakan, don haka kada ki rusa hanyar goben ki, Nace to mama a hankali tare da kara lalabo wayana na kira shi, Wayan tana ta ringing azatona ba zai daga ba tunda ya kashe,, Gab da wayan zai tsinke naji ya daga yana cewa ya akayi kuma tunda kince bazaki dawo ba, Nace cikin marairaice murya ba hakana bane Sadauki, Idon shi ya lumshe tare da hade wasu yawu don jin sunan da na kirashi dashi, Nace ainima bada son raina na tsaya ba zancen zuwa screening din nan ne kawai ya tsaidani don ina son dawowa tare daku ko don lafiya ta Yace abinda nake maki duba ke nan nima don kada ki samu sauyin magani, Nace to kayi hakkuri idan ranka ya baci dani please ? Murmushi naji yayi ta wayan sai naji ya kira suna a hankali ya ce Meenatu na amsa na,am, Yace mama tana kusa dake kenan ko, kai tsaye na bashi amsa da cewa eh,, Sai naji yace nikan nasani don indon take ce bazaki kara kirana ba hakan, Shiru nayi don banda ta cewa a lokacin banda sauraren shi, Muryan shi naji yana cewa Meenatu gidan naji yaimin wani irin girma da baki,a gidan, Don haka ina bukatanku a kusa dani ke da baby na don na ji dumin ku a tare dani, Baiyyananen Murmushi zancen shi yasani nace insha Allah da zaran natafi zanbugoma kaji abinda ake ciki, Yabani amsa da cewa kin kyauta sai na jiki ki gayar min da mama da sauran mutanen gida, Na amsa dacewa zasuji insha Allah nagode a,huta gajiya daga haka muka kashe wayan,,,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 7⃣8⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL WA,AHID

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull