Tarko complete novel - Chapter 73
Tarko complete novel Chapter 73: Tarko complete novel Chapter 73. Alokacin da,yadawo daga Birnin Kebbi ranan ina lectures a wanan time din don haka ba mu…
3,356 words
Alokacin da,yadawo daga Birnin Kebbi ranan ina lectures a wanan time din don haka ba mu samu ganin juna ba da shi, har suka wuce, Nayi hakan ne kuma da gangan don a ranan bar shiya haduwan mu ba, da shi , Sai bayan su isa ne mu kai waya dashi inda nake masu sannu da hanya, da a huta gajiya, Ina kokarin kashe wayan ne naji ya kira sunana da wani karamin murya, Nima din a hakan na amsa mai tare da dan marairaicewa nace na,am, Amma dai da wani manufa kika kashe wayoyin ki yau, din, ko, shiru nayi ina sauraren shi, Sai can nà kara jin muryan shi yana kara tambayana, Cikin dan ma rairaicewa nake cewa ba hakana bane yaya duk lecture din da nake da su yau top one dole ne yasani fita, A karshe dai na ce nima ban so hakan ba don naso na ganshi inbada sako aikaiwa Baba Ramatu, Bai amsa min ba sai cewan da yayi munyi magana da Anty Amarya don tace bazaku dade ba zaku samu hutu a school, Nace amma hutun baida yawa ai sosai, ya karashe da cewa don haka bazaki zo nan ba ke nan tunda ba yawa hutun ko, Shiru nayi ina magana kasa kasa can nake cewa, ni ba haka nake nufi ba, Kawai dai naga hutun bawani mai yawa bane sosai, gashi kuma akwai dan nisa sosai daga nan zuwa abuja, Murmushin a takaice naji yayi yana cewa ba matsala kiyi zaman ki, Nace azuciyana ai ba wani matsala bane tunda kana da matan ka agida dayawa, Sai ji nayi yace ai na gansu nace ki dawo gida kiyi hutu anan, don muna shirin tafiya ne, Sai a lokacin na tuna cewa zasu tafi saudiya har da su Baba na, Murya a sanyaye nace, Allah ya kai mu lokaci lafiya, Bai bari nakai karshen maganata ba yace mata na da kike cewa sunanan ai suna,nan, don nasan da zaman kowacen su, Da sauri na ke cewa ni bawai wani abu yasa nace hakaba fa don naga dai ai da mutane a,,,,, Ban kai karshe ba yace don na kara aure ko kema kina kishin ke nan irin na sauran ko,? Murmushi nayi nace kowa ba kishi takeyi ba gani dai mu kayi duk muna iya kokarin mu da kai ai, Ai saboda kokarin na kune yasani, sha,awan karawa don kukara kaimi akai, Murmushi zancencen shi ya bani maimakon, takaici don ma maganar tashi ta zama zolaya Nace aiko sai asha amarci lafiya don ni dai ina a nan, Dariya naji yayi tare da cewa next week da zaran an gama hina zata tare ai kinga koda zaki zo zaki samu amarya agida, ke nan, Dariyan yake nayi nace ai kawai sai nai zamana gurin uwata anan , Don ko nazo ba batun mu akeyi ba ana zancen zukakan amare har biyu haka,, Dariya sosai na bashi dan injin yadda ya kwashe da dariyan a cikin raha wanda abin yabani mamaki azuciyata nace namiji mugu ke nan, Munyi sallama dashi yana ta faman jaddada min cewa na tabbatar da cewa na shirya kafin ya turo dauka na, Sai bayan mun kashe wayan ne kishin zancen tarewan Fatima ya turnuko min a zuciyata, Shigowan Anty gurin mu ne nake ce mata ashe wai next week Fatima zata tare Abuja, Fuska a daure tace kinji halin maza ke nan ya tafi an masa dandane haukace, Yadawo yana santin buje agida ko idan ba shi ke da keda tsohon ciki ina shi ina fada maki wanan zancen kuma, Baki na tabe na Oho dai wallahi gashi kuma ya matsa da cewa wai sai naje can nayi hutu, Ido a waje tace kije ina a hakan ke da keda wanan tsohon cikin haka wai,? Idan zuwa lokacin kin haihu fa ba sai muga tsiyar naci ba kuma, Dan yatsina nayi nace ai sai yasha amarci har yafita ranshi kafin ya gan,ni a gidan nan,
****** ********** ****** Zagayen aikin ginan shi keyi don tun da ya dawo agajiye yake, Saboda ba,a gidan suke zaune ba suna a wani dan karamin gidane a kusa da mu, mai Tree bedroom, nan suke zaune yanzu, Ya fitanan ya fada can yana kallo yana ya bawa aikin da akayi, har yazo nawa part din da mamaki yai wani juyowa yana kallon Lawal, Shi kan Lawal bai fahinci may yake nufi ba, don haka sai bai damu da kallon ba, Cikin wani irin kakausar murya yake cewa Lawal wanan kuma part din ya akayi ya samu karin wanan extra room din, Shima lawal din a cikin mamaki yake kallon shi yace ai ina ce ko kai kace ayi shi ko Don ranan na yi ma magana naga bakace min komai ba sai daga baya da nadawo na samu sun fitar da plan din, Nan ko idon shi ya kankance yafara masifa kan cewa akira mai, engineer din, Nan yaiwa mutumin masifa kan cewa don may zai fifita dayan part din fiye dana kowa, haka, Shikuma engineer din yace gani yayi cewa wanan filin idan an fitar da plan din a haka zaifi yin kyau, da abar filin abanza, Daga karshe dai yaba yaya Abubakar akan kuskuren dayayi don yaga rayuwan shi ya baci sosai a lokacin, Iya bacin rai yaya Abubakar yayi shi a ranan don sam bai so ace wanan part din ya fita daban da na sauran ba, Haka ya isa gida rai bace yana huci idon shi sun rine sunyi ja don bacin rai, Duk wace taji motsin shi a falo sai tazo yi mai sannu da zuwa a lokacin ganin yanayin shi, yasa hankalin su dagawa, Hakan yasa su fitowa dan karamin falon gidan da suke a cikin sa, Anty Sadiya ce tai karfin halin fara tambayan shi wai may ke faruwa ne duk taga ya canza, Yai tsuki yana cewa, banda wanan banzan engineer din wanda nasa ya fitar min da plan, din ginan gidan can wai sai kawai yai min karin wani extra room a dayan part din, na Meenatu, Salawatu tace akan may zaiyi haka shi kuma bayan ga yadda mai abu yace ayi ma shi,da abinshi, Yai tsuki tare da kawar da kai yana cewa daki har uku a part guda haka har may mace zata saka acikin shi, Ya dago jajayen idanun shi da suka rine sukai ja,ya dubu gurin da Sadiya take zaune yana cewa sai ki koma wanan part din ke, Itama da sauri ta dago kai tana duban shi tace wani , Yace ke man da wa nake nufi inbake ba, da sauri take ce mai don Allah a barni part dina, Takarshe zancen harda daga hannuwan ta alamar a,a bazata koma ba, Salawatu tace ni part dina saboda wanan corner din da nace ai min ne in bashi ba dani sai in koma a ciki, Sadiya tace a,a bazaki koma ba kawai abarwa Meenatu abinta tunda dama part din ta ne can din,, Salawatu tace gaskiya da abar ma wata kawai abarwa Meenatu part din nata ta zauna hakana, Sadiya tace to ai ni banga wani abin bata rai ba anan da har rayuwanka zai baci haka, Jajjayen idanuwan shi ya sauke mata yana cewa idan mutane suka ga rashin adalci na agare kufa tun akan gina dakunan ku, Salawatu tace wanan ai mun san cewa bawai ra,ayinka bane mistake ne akasamu don haka baza mu maidashi wani abin fitina ba can, Sai a lokacin ne hankalin Yaya Abubakar yadan kwanta saboda fahintar junan da ya samu daga matan shi amna a gaskiya bai so ace hakan ya kasance ba sam, Hannuwan shi dafe da goshin shi ya sauke ajiyan zuciya, tare da furzar da iska mai zafi yanisa tare da mayar da bayan shi ga makarin kujeran da yake zaune akai, Yadan lumshe idanuwan shi a hankali yake tunanen cewa wai ita wanan yariyar haka Allah yayi ta da sa,a arayuwan ta ne, Komai nata na daban ne zaka ganta a cikin nasara, watau abin daga Allah ne kawai, Muryan Salawatu ce take sheda mai cewa kayan gadajen su da suka sayo ance zasu shigo next weeek insha Allahu, Sai a lokacin ne ya dan bude idon shi da suke a lumshe yana cewa ai na kira masu decoration din gida sunce zasu shigo su duba, Sadiya tana zaune daga gefe tana rike da habanta da yan yatsun hannun ta tana kallon su, Tace a rayuwan ta shi ke nan duk Yaya Abubakar yanzu rayuwar shi ta canza a lokaci guda, Mutumin da da can baya ko sutura bai damu da dinkawa ba, Amma yanzu ga kudi suna shigo mai kamar hauka, ga kuma buri yana karuwa mai, Rayuwa kenan haka zamani ke tafiya da rayuwan mutane the more suke samu the more bukatocin su yana karuwa,
****** ********** ****** Sai Amarya Fatima aka shirya tafiyanta Abuja gurin sauran abokan zaman ta, Duk da maigidan yace mata,baya bukatan komai tazo daga ita sai kayan ta, Ta samu rakiya mata mutum shidda inda suka samu gida fiye da tsanmanin su, Suna shiga part din ta taga irin yadda aka gyara daki ta kware muna fukin mayafin da ta yafa a jikin ta, Tare da sauke numfashin ta a hankali wani irin shewa ta sake tare da sauran yan rakiyae ta, A nan tafara raraba idanu tane cewa ai ita kan gaba wanan auren ya kai ta yaushe ta taba tsan manin irin wanan ratuwar haka,, Nan suka shega dube duben part din gidan lungu lungu sako sako suna yaba kyaun shi, Sunci sun sha daga daulan Baba Ramatu wace tai ta faman yin da wai,niyar girka masu abinci, Kwanan su uku, suka juyo dawowa gida birnin kebbi cike da abin arziki Amarya Fatima ta shigo da irin nata sallon a gidan don, Maigida ya samu kyakyawan taro daga amaryan shi ida duk kan su suka debi takaicin amarci, Salawatu wace zuwa lokacin takai,ka, mar ta kama da wuta saboda kishi, Duk da dai babu abinda maigidan ya rage su dashi yana dan kokarin kaman tawa, Suna zaune a falo yayin da Fatima wace tana tsaye a gaban maigidan da jug din drinks din gargajiya da ta hada mai a hannun ta, Sai wani juye juye take keyi tana rausaya a gaban maigidan, Bayan ta sai shocking yake yi tana wani mazayawa don kawai ta tayar wa maigida da hankalin shi, Daidai lokacin da ta dauki cup zata tsiyaya mai drinks din ne Salawatu ta shigo Falon , Tun daga kofa tace ke, ke ke kada ki fara don munan da kika samu ba wai bamu iya irin wanan kissan naki bane, Fatima tai wani irin juyowa tare da watsa wa Salawatu wani irin hararan ke kuma fa, A gagauce ta karaso gaban su tana cewa amma dai kin san cewa yau bake ce da girki ba a gidan nan ko ? Da sauri yadago idon shi yana duban Salawatu tare da nazarin abin da tace,, Ya saurin juyawa gurin Fatima yana cewa may na tambaye ki da safen nan, Tace cikin daure fuska, kwana hudu bazawara keyi yau kuma biyu nayi a gidan nan, Ya daga kai ya dubi Salawatu wace ke tsaye a kan su cikin masifa, Salawatu tace wancan kwana biyu da ya tafi yai maki a kwana garin ku na may ye shi, Nufin ki kin samu garori zaki juya su yadda kike so ko may kike nufi da hakan, Cikin tsawa yace masu da karfi enough please ban son fita a ratuwata, don haka ku tausasa harshen ku a fahinci juna, Salawatu ta mika hannu ta dauke cup din da Fatima, ta cika shi da drinks acikin sa ,da ta aje a gaban shi,, Ta kai shi can nesa kadan da ida shi ke zaune hakan yadan sa shi lumshe idon shi a hankali, Yace yanzu dai ke nan ranakun girkin ki sun kare ke nan Fatima, Nan ta juya ta watsa wa Salawtu harara tana cewa inji wanan muguwae tsohuwar ba, Salawatu a cikin bacin rai tace muguwar tsohuwan tana can ai kin barta a baya tana sauraren ki, Tana nufin wai mahaifiyar Fatima na gidan tana jiran jin bayani daga gurin yar ta, Fatima tace ke wallahi,banda mutunci da kika gane ni gurin nan, Salawatu tace ai irin ki nake bukata dama amma wanan girkin yau ba ke ce dashi ba, Anty Sadiya ta shigo falon fuska a daure tana kallon su wani irin cikin mamaki, Ta samu guri a can gefe ta zauna yayin da ya dago jajayen idon shi ya sauke a gare ta, Yace yauwa Sadiya yaya wanan zancen yake ne wai don Salawatu tazo da cewa ba Fatima ce da girki ba yau ai, Anty Sadiya ta watsawa Fatima harara tace ai itama tasan cewa ba ita bace da girki yau, Kwana hudu tati tana girki wanda a kaida kwana uku ne idan bazawara ce, Da sauri Fatima ta kalli gurin da Sadiyan take a zaune tace wai kuna nufin cewa kun hada min kai ke nan, ko, Sadiya tace hadin kai sam, sam sam ni bani hadin kai ai da kishiya sam, Kawai dai magana ce ta gaskiya sahihiyar ta domin ai ke ba yarinya bace, don kin san komai, Cikin wani irin harara Fatima ta ce, ki ce nice uwar matan duniya baki daya, karewar ta, kenan,, Ya isah haka please tunda har bata lissafi akayi kuma kuma kun gyara kuskuren bashi ke nan sai mai girki ta dora inda aka tsaya, Da wani irin mamaki Fatima take kallon maigidan dashi don ba tai tsanmanin jin hakan ba daga bakin shi, Sai duban shi take yi a cikin mamaki tare da dan jijiga kai tace a ziciyar ta lalai namiji abarshi kawai, Inda ya kara bata tsoro shine ganin ya mike tsaye yana kallon fuskokin su a cikin bacin rai,yana, kara fuskantar ta yayin da ta sauke mai,firgitattun idanun ta da suka nuna kankanci,ya na cewa, daga haka bana son inkara jin muryan kowa again, daga haka ya shige part din shi, Jiki a sabule Fatima ta dauki, jug din drinks din ta zuwa part din ta, Inda rayuwan ta yayi dubu ya baci a ranan saboda bata mata tsari da Salawatu tayi, Ita kuma Sadiya ai dama sun saba kar tasan kar tun suna gida, Tun wanan lokacin bata fito waje ba tana dakin ta tana waya da yaranta, don zuciyar ta ya kwanta, Salawatu, ce ya kamata tai taking over, din duty ranan, don dama itace zatayi, Amma sai tace wa Sadiya ta dauka don abin ya dawo ma su normal according to tsarin shigar su gidan,
****** ********** ****** Zuwa yanzu nayi nauyi sosai na zama wata irin cikakkan mace Cikin jikina ya zauna min das a jikina yayi wani irin turowa sosai, Ni dai nakan ga anty takawo min ruwan abubuwa wai insha, na rage zaki, Bana mussawa nake karba nashanye shi a duk lokacin da ta bani din, Sai adduan lahaula, da nakeyi kullun a cup kafa goma sha bakwai na shanye, Ina zaune a gaban mirror muna waya da Baba Ramatu wace ta bugo min don mu gaisa, Ban taba tambayar ta may ke faruwa a gidan mu ba a baya na, Haka itama Baba Ramatun bata taba fada min komai daga zancen zaman su ba, Tambayana tayi da cewa wai uwar dakina yaushe ne zaki dawo, Murmushi mai sauti na yi mata ina cewa Ramatu ai ni da garin ku sai idan Allah ya sauke ni lafiya, Ramatu tace kai haba dai uwar dakina naji Alhaji nacewa ai kina tafe kwanan nan , Nace gaskiya Ramatu ni bazan je ko ina ba don bazasu dade ba zasu wuce zuwa saudiya ne, Ramatu ce aiko dai ga gida nan yasha gyara kowa ta shige a cikin nata, Nai saurin katseta da cewa ai idan da rabon in shiga komai dadewa zan samu nawa na jirana, Mun dan dade da Ramatu muna waya tana bani labarin diyan ta, da irin cigaban da ta samu yanzu,
Duk irin yadda Yaya Abubakar yaso nazo Abuja hakan baiyi ba saboda dan zazzabin da nayi yayin da mukai hutu, Dole ba don ya so ba yabar ni a gida don babu yadda zaiyi, Don hakane ma ya shirya zuwa dubana tare da zuwa gida. Fatima taso ace ta biyo shi su zo tare amma saiyake ce matabai zuwa da kowadaga cikin su, ayan yazo yaga irin yadda a lokaci kan kani na wani zama big madam sai da ya tausaya min, Wanan ganin da yai min yasa shi ya sauko da fushin da yakeyi da farko, Don yana ganin cewa, dan ban son zuwane kawai na kirkiro wa kaina ciwo, Duk yadda yaga kafafuna sun kumbura da kuma jikina yadda ya koma min duk na wani hakewa, Bai, so ya wuce zuwa Birnin Kebbi a ranan saboda yadda yaso ya kasance dani, Ina saye a cikin dogon riga baki dan kasan Jordan, ya kara sani yin kyaun masu ciki idan na bada baya yana nuna mazauna na irin yadda suka ciko min, Na shiga daga ciki don in dauko mai takardan asibiti na ya gani saboda yace sam bai yarda da cewa na tafi asibiti ba. Ina juyawa yabi bayana da kallon sha,awa yayin da yadan lumshe kyawawan idanuwan shi a hankali, A hankali idon shi a dan lumshe ya furta sunana da cewa Hmmm MEENAT, Ya dan furza iskan da ya gunda a bakinshi ya na cewa a cikin ran shi, Kunya natsuwa kamun kai, rikon addini, ga sanin ya kamata,, Meenatu kin samu tarbiya ingantattace wanda ya sa maki zama kamilar mace a rayuwan ki, Babu kwadayin komai a tare da zaman ta da ni babu zancen cewa bani nasai kaza ,zanje gurin abu kaza , Baikai ga karshen zancen zucin shi ba na dawo daga ciki hannuna dauke da farar takardan asibiti, Har na karaso gurin da yake zaune idon shi yana akaina na mika mai a cikin ladabi, Inda yakarba naji yana sauke ajiyan zuciya a hankali, Gefen hannun kujeran da yake a zaune na samu gefe guda na zauna, da kyat tare da cije baki, Yayi daidai da ya dago kai zai tambayeni zancen waya biya kudin maganin don yaga suna da yawa, Ganin yanayi na sai yaji wani irin tausayi na ya kama shi a zuciya, yace a hankali may ke faruwa kuma cikin nuna concern din shi gare ni, Saida nadan kara ya muta fuska don a gaskiya bana jin dadi sam, Nake cewa, a hankali bakomai kawai dai ban jin dadin jikin nawa har yanzu, Ya rasa may zaice min sai dai dogon ajiyan zuciyar da yayi yake cewa in daure mu tafi Birnin Kebbi a ranan, Ban kai ga magana ba Anty Amarya tashigo falon bakin ta dauke da sallama, Sun dan kara gaisawa dashi inda take cewa asibiti sun bata, Edd, cewa nan da two week ko kafin shi zata iya haihuwa, Da sauri ya juyo gurin da nake zaune yayin da zancen su yadan sakani jin kunya sai wasa nakeyi da yan tsun hannu na, a hankali, Dan jingina yayi da kujera yayin da yake jin wani irin zafi yana fita mai daga jikin shi, Yace ina ganin ni zan fasa tafiyan nan don dai kada sai mun tafi kuma ta haihu ba ma nan, Duk kan mu da Anty abin ya bamu dariya amma sai na dan sake murmushi mai sauti, Anty ce tai karfin halin cewa ai da kana nan da baka nan duk Allah ne mai yin komai, Allah dai ya kaiku lafiya, ku dawo lafiya ka samu bako ko bakuwa acikin yan taron ka da ti maka sannu da zuwa, A hankali ya murmusa tare da sa hannu a cikin aljihun shi ya ciro, dan kyallen shi na goge fuska, Yana cewa da yau naso mu tafi tare Birnin Kebbi da ita to amma kuma sai nake ga zata ma iya zuwa a hakan, naso taje suyi sallama da Baba ne wai, Gurin da nake Anty ta duba tana cewa zaki iya zuwa, mana Meenatu kuyi bye, bye da su, Nace zan iya a hankali don haka dole tafiyan ta kama dani ke nan, Ban dauki wasu kaya masu yawa ba don nasan kwana biyu kila zamu yi,