Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 74

Tarko complete novel - Chapter 74

Tarko complete novel Chapter 74: Tarko complete novel Chapter 74. Koda muka isa dare yayi a lokacin amma ba wani sai ba don haka direct masauki ya wuce…

3,208 words

Koda muka isa dare yayi a lokacin amma ba wani sai ba don haka direct masauki ya wuce dani, Wai a cewan shi nagaji sosai kuma ba wai ba a gaskiya ranan nagaji sosai din don na dade banyi zama irin wanan din ba, Nai wanka nayi sallah, inda aka kawo muna abinci lafiyayye a cikin kuloli masu kyau, Ganin kyawon kulolin yasani zargin cewa daga gidan su Fatima wanan abincin ya fito, Ina cikin tunanen naji takun shigowan yaya Abubakar wanda yadan fita da dadewa, yashigo dakin , Gurin da abinci yaje a cikin basket ya kalla da sauri ganin ban taba ba yasa shi saurin kalloni, May yasa baki ci abincin ba har yanzun nan haka gashi kin san cewa bake kadai bace, Murmushi nayi ina cewa abincin ne ban san daga ina aka kawo muna ba, Kai tsaye yake ceea mahaifitar Fatima ce ta hada muna shi don tasan zamu zo, Nima kai tsaye na ce mai ai ni da kai duk muna da mahaifa kuma sun san cewa zamu zo yau din, Don haka ni ba zanci abincin gidan kowa ba tunda ba bakuwa nake ba agarin, Mamaki sosai yaji don shi sam baiga abin cewa wani abu a nan ba don kawai an kawo muna abinci, Ban tsaya jiran komai, ba nafara kokarin gyarawa na hau gado na kwanta, don dama agajiye nake lokacin, Ido ya zuba min da mamaki don ganin iyakar gaskiyana ke nan zan kwanta da yunwa, Nikan har na kai kwance don yasan bazanci abincin ba ke nan tunda har na kwanta, A hankali na lumshe idona sai wani irin takaici dake dibana don dama nasan cewa zan iya cinkaro da irin haka ko daga Aliyu ne, Murya yaya ji yana kiran yaya Mustaph wai yazo mai da kaji da drinks nace a raina da yafi dai, Muryan shi naji daga bayana yana cewa, zaki dai ci kazan ko ? Da kyat na iya amsawa dacewa ummmumm cikin bacin rai, Idona a runtse yayin da Yaya ya shiga wanka, ina tunanen cewa ai a sashen Baba na yake cin abinci tun yana samartakan shi, Sai yanzune zata tsiro wani tsurku cewa wai daga gidan ta za,a kawo muna abinci,

Shima yaya, a lokacin yana bayi sai tunanen wanan irin rashin jittuwan dake a tsakanin kowacen mu da Fatima yake yi, Amma duk ace gaba dayan mu babu wace zata sha da dadi daga gare ta, Yace kai itama Fatima akwaita da son iyayi ne in bashiba ai tasan muna da gida may na cewa a dafo mai abinci daga gidan su, Hakana yafito rai abace saboda sai ya rasa may ke mai dadi a lokavin kawai rayuwan shi yaji ya baci gashi kuma yana jin yun wa don tin karyawan da yayi ne da zaifito daga gida ke cikin shi, Yana gama shiryawa yaya Mustapha ya bugo mai waya gashi waje a lokacin, Baidadeba yadawo dauke da ledoji a hannuwan shi yana cewa ki tashi kici tun bai yi sanyi ba fa, Bamusu don dama ina jin yunwa sosai don bazan iya barciba banci abinci yadda nake ji, Sosai na ci abincin hankali na a kwance, na gama na samu guri na Kwanta don inyi barci,, Sai can zuwa dare naji bin da Yaya ke min abinda yasani bude idona kenan, a hankali tare da dan sauke numfashina a hankali,,,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL-MUBDI

Meenatu, kinfini sanin halin mutanen gidan mu a yanzu don haka nake bukatan shawaran ki akan kowan su, Shiru nayi tare da,sauke ajiyan zuciya don jin abinda yace, Dan nazari na shiga yi a lokacin don jin may yace don haka sai nayi kokarin dan zare jikina daga nashi na nufi bakin gado na zauna saboda ban iya dogon tsayuwa yanzu kamar da, Shima a bakin gadon ya zauna yana mai kura min idon shi yana saurare na, Na dago kaina a hankali nace Yaya malam tsoho dai ya kamata a ce an,gyara mai wanan majalisar tashi yakoma na zamani, Murmushi nagani a fuskan,Yayana tare da dan rausaya kan shi da yayi yana dukan ahannuwan shi guda a cikin guda a hankali, Ganin irin murmushin da ya keyi yasani dakatar da zance na, Yace ya kikai shiru go on ina sauraron ki ai don dama nasan cewa da masoyinki zaki fara gashi kuma keep n fara din, Nima murmushi nayi nace Yaya ai kaima malam babban masoyin ka ne, Amma kuma ban kaiki ba ke sarkin fadar shi ko don kowa yasan hakan,

Sai da na murmusa nace sai Baban makaranta ina nufin Baba Buhari ke nan, Da shi da mama idan da hali Yaya ai saudiya ya kamata a kai su ko ? Ko wanan karon murmusawa yayi min irin ta manya murmushi irin na iya fuska kadan, Ya ce ina da niyan hakan amma sai nan gaba kadan insha Allah, Nace to Yaya ba sai ka gyara,ma su part din su ba ya koma irin na zamani kaga idan mun tafi mu samu gurin zama mu dan wala, Yace malam yace nayi gina a,bayan dakun su Baba, dama, Nace ok, yanzu dai a takaice abinda ya kamata gaba dayan su sauran sai ka basu dan abinda zasu kara ga jarin sana,an su ko ? Ka naga yana jijigawa a hankali tare da lumshe idon shi , Sai yai wani irin jan iska tare da fesarwa, a hankali,, Yace a daidai lokacin da yake mikewa tsaye daga yanzu idan zamu yi shawara a kan iyayyen mu, Ban so kina ware min Baban makaranta daban Babana daban, Don kowa yasan cewa, Baba Samaila ba karamin kokari yayi ga ala,amari na ba duk da dai za ace ba,wani mugun girma sukayi ba amma ya kyautata min sosai a,rayuwan na, Don haka ni ban mantawa da, alheri a rayuwa na, Daga haka ya shige bathroom don yin wanka a gurin da ya barni zaune ban daga ba ina gurin zaune har wani dan lokaci ina tunane, duniya, Zuwa can na mike zuwa bakin wardrobe din shi na ciro mai kayan da zai sa tare da feshe su da turare, Da sauri na na kara gyara inda ya kamata a dakin badon komai ba fa don dai kawai na burge shi, Kunsan abu ga mai kishiya duk abin da zakiyi wanda ita batayi zaki kokarta kiyiwa mijin don kawai kiyi galaba akan ta, To nima sai nake gani ai bankai ajin da zan kara a tsakanin Sadiya da Salawatu, don haka ne na dinga yin aiyukan da karfin jiki na, Abinda ban sani ba a lokacin shine ashe badaga haka ba shi na miji shi ne yasan jarumar sa a ransa ke dai naki shi kada ki bari a barki baya ko ta halin kaka, Bayan fitowan Yaya daga bathroom ya shirya acikin kayan da na fitar mai a tare muka sauko ni dashi, Inda muka zauna don a dining space, don ya ci abincin shi abincin da ya sha gadi wirin Ramatu don gudun a zuba wani abu kamar yadda take tuhuma, A hankali na bude kulan abincin inda naga tuwon farar shinkafa kulle a,leda ledan ya dauki zafi ya dan sake ma tuwan fashion kama ado Kulan miyan ganye tayi watau miyar taushe, yaji alaihu da sure sai nama da agusi, tai amfani, Gaba dayan mu munji dadin tuwon don sai da na cinye ledan da na dauka tare da Salawatu mukaci don tace wai mu take jira, Gab da zamu kare ne Anty Ramatu tafito daga dakin ta da gani daga barci ta tashi a lokacin, Ganin mu mu uku yasa ta canza fuskan ta ta,wani daure fuska tamau, Kishi, sosai ya baiyyana a fuskan ta amma sai ta dan kauda kan ta batare da taiwa kowa magana ba ta ja kujera ta zauna har ta fara ci bata cewa kowa komai ba, Babu wanda ya tanka mata sai kowa ya shiga yin abinda ke gaban sa, Mun kai dan wani lokaci a gurin sanan muka koma daga ciki, A ranan yadda Yaya Abubakar ya gwada min tankar, ranan ce ya fara sani na a matsayin diya mace, saboda wani irin mahaukacin soyayyan da ya nuns min wanda ban taba sanin cewa ya na iya yi wa mace,irin, sa ba, Sai dare sosai na samu Yaya ya sarara min ya nata fadar wai yaji na canza mai sosai tankar bani bace,abin ya kara rikita shi, Tun wanan lokacin da na koma girki banda shakat da Yayana don koda yaushe yana manne dani don bai jin na gundire shi, Hakan yasa bini,bini Yaya Abubakar yana a tare dani, sai ma na manta da zancen bed rest, Nayi warkewan dole saboda irin yadda yake gwada min dole na jajirce wa zuciyana na daure kada aga gazawa na, Duk da yana iya kokarin wurin ganin cewa gaba dayan mu yabawa kowa hakkin ta, Abinda ban sani ba ashe tun lokacin da mukai zancen taimakawa yan gidan mu da Yaya Abubakar tun a lokacin ya yi duk yadda nace ayi don har an gama gyarawa malam tsoho part din shi,,,

****** ********** ****** Yau a gajiye ya dawo gida kaman kullun irin yadda ya saba dawo wa cikin gajiya, Nice da girki don haka ya shigo tun a kofan falo na karbi jakar kayan shi na ahiga gaba yana,bina baya, Wani irin tunane ne yazo mai a ranshi fon ganin yadda komai nawa ya sauya, a idon shi, Muna hawan sama yana tuna hiran da Baba Wadda yai mai na gorin haihuwan da akai wa Baba Buhari akan shi cikin shiyan mu, Shiyasa yanzu ma da yai wanan tunane da idon shi ke maigizo a kaina yadda siffana yayi kamar na mace mai ciki, Yai saurin kawas da zancen da cewa subbahanallahi yana mai lumshe idon shi, Da wanan tunanen muka isa dakin inda a tsakiyan dakin yajawoni ya manna a jikin shi, Na lumshe idona saboda irin yanayin da na shiga ajiyan zuciya naji ya sauke daidai saitin kunne na, Saman gado muka fada atare inda yadan shiga aika min da sako, Hannun shi a saman cikina ya kai, abinda ya haddasa wa abin cikin cikina yin motsi bul,bul wani irin suka naji shima Yaya da sauri ya mike zaune yana cewa ,Ya Allah Zuciya baki da kyau, wai tunane na har ya kawo min imagination din ciki ajikin ki, Tausayi maganan da najiya fada ya bani sai naji tankar a lokacin infada mai gaskiyan zancen, Ya mike zaune yai shiru yana mai dafe kamshi da alaman yana cikin wani irin yanayi,, Ganin yadda jikin shi yasake yai sanyi yasana yanke shawaran yau da dare zan sanar dashi insha Allah, Nadan kamo hannuwan shi na kwantas da kaina a saman kan kafadan shi, Sai naji shi acikin ya nayi yake, a hankali na bude bakina nace mai, Ya yaka tashi kayi wanka ga ruwan zafi can yana jiran ka a bathroom, tun dazun, Nace abinci kuma yana ready a falo kai kawai muke jira, Maimakon ya tashi sai ya kara kaiwa kwance ya dan rike min kwankwaso yana cewa waima kuwa zan iya tashi wankan yanzu kuwa, Saida nai kokarin mikewa amma sai yajawo min hannuwa nadawo na zauna tare da dan rankwafo mai, cikin wani irin murya nace, Haba dai Yaya dan Allah dai ka tashi mana kada mutanen gida su jiramu, Wani irin kallo ya kama yi mun tare da lumshe idon shi Yace Meenat wallahi na gajine yau sosai, yau nayi over work ne Da kyat na lalaba Yaya Abubakar ya mike zuwa yin wanka, Kafin yafito na koma kasa na kara gyara kwalliyana, A haka rayuwan gidan mu yai ta gudana kowa na boye halinsa saboda azauna lafiya,

Yau ma a Zaune muke gaba dayan mu muna hira a falo duk da ba wani hira bane kawai dai kowa na nashi tsabgan ne Wayan Yaya Abubakar tai kara ya dauka ganin wace ta kira layin shi, Mama Ladi ce take, kiran shi a cikin girmamawa tankar tana a kusa da shi, Bayan sun gaisa ne take ce mai Ànty, Nafisa tana asibiti ance CS za ai mata idan bata haihu ba nan da yan awowi, Da karfi naji yana cewa subbahanallahi ita Nafisa, tun yaushe ne tafara rashin lafiyan, Jin su nan wace ya ambata yasani saurin dago kai na ina fuskantar shi, kallo na son karin bayani nake mai, Ansa da Mama ta bashi ne ban ji ba don wayan ba a hands free yake ba, A take hankalina yai mugun tashi don nasan zancen haihuwan ta ne akeyi, Wani asibiti ne kukai kai ta mama ta bada amsa da cewa Sir Yahaya ne aka kai ta, Yace idan bazasu iya ba ne a dauke ta a mayar da ita FMC yanzun nan mana,, Gaba daya duk hankalina na tattara gareshi don jin abin da suke fadi, Ya kare da cewa barin turo maku Aliyu yanzun nan yaga halinda su ke ciki, Yana kashe wayan mama ya fara kokarin duba nomban Aliyu nake ce mai Yaya anty Samira ce , ba lafiya ? Ya ce cikin dan yanayin damuwa wai yau, kwana biyu tana wanan abin, na haihuwa har yanzu kuma bata haihu ba, Innalillahi wa,ina alaihim,raji,um abinda na fadi ke nan a lokacin da nake mikewa,a rude nace, Ya Allah ka tausaya muna ka sauke muna masu cikakkan mu lafiya, Salawatu ta ansa da fadar ameen, Amma Anty Sadiya bata ce muna uffan ba sai dai gyaran yatsunta take yi kawai, A cikin damuwa muke zaune gaba dayan mu, sai faman waya Yaya Abubakar keyi da jama,an gidan mu, Jikina da kayan cikina sai ka rantse cewa ba a jikina yake ba,, Don wani irin kaduwa da nake ji saboda jin cewa yar uwata tana acikkn wani hali, Shi kanshi Yaya Abubakar din a rude yake don ya kasa zaune ya kasa tsaye,, saboda damuwa, Ita ko Salawatu sai faman binsa da ido takeyi duk inda yabi a lokacin, Shiga daki nayi na dauki wayana na kira mamana don inji yaya ake ciki, Mamana ta dauka tana cewa tun da rana nake son kiranki yae Baba , Na gaishe ta sai nake tambayan ta ashe Anty Nafisa ta a gurfane ne tace ai shine nake son kiranki in fada maki, Nan mama take sheda min halinda ake ciki akan wai aiki za,ai mata don dan yayi girma da yawa bazata iya haihuwa ba Nace mama da sauki dai ko don naji Mama Ladi ta bugowa Yaya waya tana fada mai abinda ake cikki, Mama na dai ta kwantar min da hankali yadda taga duk nadamu sai ma take tambayana ya jikin nawa nasamu lafiya yanzu ko ? Mun dan dauki lokaci muna hira da ita cewan ina yan kanne na su ke da kuma tambayan lafiyan su, Jiki ba kwari muka watse ranan don bace da girki ba don haka ban wani dauki lokaci mai tsawo ba a falon, A haka gari ya waye muna mu na cikin sauraren zancen haihuwan Anty daga birnin Kebbi, Sai da nagama shirina tsab na fito falo don na gaida Yaya saboda bazan iya jurewa ba har ya shigo dakina, Idan ma ai har na bari ban kyautaba don ban nuna mai damuwar yar uwar shi ba ke nan duk da dai nima yar uwatace amma ai ya fi kusa da ita shi,,,,, Yadda na samu Yayana zaune a falo da waya a hannusa yana saye da jallabiyar sa ta zaman gida mai launin ruwan madara,, Kallon da nai mai kawai yabani tausayi, sosai don nasan damuwan dake damun shi, Ina kwana na fara yi mashi tare da tambayan shi ya labarin mai jiki, Cikin dauriya ya dan gyara zaman shi yace min, Yanzun nan mukai waya da Aliyu yake ce min an shiga da ita tiyata, kuma wai ba lalaine a samu jaririn ba nace wayyo Allah na ,,, Allah dai yasa a samu rayayye Allah kuma yafito da su lafiya, Ina daga tsaye a bayan kujera Salawatu ta iso gurin tana cewa Yaya Abubakar ka dawo, Ya amsa mata a hankali da cewa eh nadawo tace to ya maijikin da sauki ko,? Nan takai zaune tana cewa gaskiya dama asibitin garin nan aka kawo ta ma da zai fi ai , Nace, aiko can akwai asibiti kawai dai akasi aka samu saboda rashin kaita asibiti da wuri, Sai lokacin Yaya na yadago ido ya dube ni yake cewa agida ke nan suka barta ko ? Na ce ance wai a gida aka barta don akwai wata malaman asibiti a kusa da su, Ita ce ke cewa wai da sauran time juyi ne kawai har ta kai ga galabaita, Yaya Abubakar yai tsuki yana cewa yanzu ashe ma duk sune suka ja mata wanan problem din ashe ? Daga gurin da nake tsaye amma duke saman makarin kujera nace haka dai Allah ya kawo al,amarin kawai, Muna gurin Ramatu tazo tana wa Yaya Abubakar jaje da fatan Allah ya raba lafiya, Munan dai kowa na fadin albarkacin bakin sa batare da ya tanka muna ba, shi sai can mu kaji yaja wani dan guntun tsuki,,, da karfi ya ce, Wai Sadiya may takeyine a cikin dakin nan please,? Gaba dayan mu mukayi tsit babu wanda ya tanka masa, Hanyan part din ta yakai idon shi tare da yin wani iri numfashi yana cewa Allah ya shirya halin wanan matar, kawai, Gurin da Ramatu take a tsaye ya ke kallo yace kira min Sadiya please ? Baba Ramatu kan tunda tadawo take ce mai tana zuwa, wai, ta juya abinta zuwa kitchen don bata tsaya ba, Can sai gata tafito da alaman barci takeyi aka tashe ta, Juyaqa yayi yakalli yanayin ta yace may kike aciki ne ke kowa na nan, Sai kuma ya kafeta da ido bai ce komai ba, Zaune takai tana cewa may yafaru ne wai nagan ku nan tunda safen nan haka,? Nace a,a muna dai zancen Anty Samira ce da ke fama da jiki can gida,,, Tambaya tayi cikin muryan ta tsatsaye tana cewa, tahaihune to ? Kagin wani ya bata ansa wayan Yaya yai kara ya dauka yana cewa Salamu Alaikum, Aliyu ya dai an yi aikin ne ? Shiru yayi yana sauraren abinda Aliyu ke fada mai ida muma duk mu kayi tsit, gaba dayan mu muna sauraren shi, Sai da yace to ita Samira din fa anfito da ita ne ko kuwa, Bai kuma yi magana ba sai ci gaba da sauraren bayanin Aliyu da yakeyi kawai, Yakare da cewa duk dai abinda ya kamata anyi kayi don Allah zan shigo next tomorrow insha Allah, Ya kashe wayan ya maida kanshi bayan makarin kujera yana mai da numfashi a hankali guda guda, Gaba dayan mu an rasa wace zata fara tambayan shi ko may ke faruwa, Sai Anty Sadiya ce tai karfin halin cewa may ake cikine yanzu wai, Yace a cikin tubure fuska an mata aiki anfitar da diya mace, Carfa na ce tana da rai baby din kuwa ? Kai yagyada min da alama yana tare da bacin rai sai dai babu halin mu tambaya,, Nikan jin cewa Baby din is alive yasani yin murna da farin cikin jin tana lafiya an samu rayayya,, Daki na koma ina mai farin cikin jin cewa Anty tasamu rayayyan baby bisa ga yadda ake ganin cewa da farko zata rasa baby din

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull