Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 75

Tarko complete novel - Chapter 75

Tarko complete novel Chapter 75: Tarko complete novel Chapter 75. Wanka nashiga idan bayan fitowana dafa dan kwantawa barci ya kwashe mai nauyi sosai, Yaya…

3,206 words

Wanka nashiga idan bayan fitowana dafa dan kwantawa barci ya kwashe mai nauyi sosai, Yaya Abubakar yashigo daki ya samay ni ina barci na hankalina a kwance, Hakan yasa shigane cewa daren jiya banyi barci ba ke nan, saboda tunanen halinda yar uwana ke ciki, Sai zuwa karfe daya na farka ko shi yunwane ya ta da ni daga barcin da na keyi,, Ina bude idona kai a agogon dakin inda yanuna min time nadan yi guntun tsuki alokacin da nake kokarin mikewa zaune, Baba Ramatu ta shigo dakin dauke da kulan abinci abinda yasani dan murmusawa ke nan, Tace uwar dakina kin tashi ke nan ko namurmusa na kai zaune da kyau nace na tashi Baba, Ashe nayi barcine sosai haka dai kuma baima isheni ba fa yunwane ya tadani, Tace Alhaji ya shigo har sau biyu kina barci zan tadake yace wai na barki kiyi barcin ki,, Murmushi nayi daidai lokacin da nake kokarin mikewa tsaye nace, yana gida ko ya fita,? Tace bai wani dade da fita ba ai kika farka don ina ganin tare da Baba Wadda da baba Hamz suka fita , Alwala na dauro na fara gabatar da sallah kafin na zauna cin abinci, Nakai wani lokaci ina cin abinci na hankalina akwance sai dai ina ta tuna halinda Añty Samira take cikki yanzu, Waya na dauka na fara fadawa Fattu zancen haihuwan Anty Samira inda ta jajan ta muna akan zacen Cs din, Ina gamawa na fito zuwa waje, don indan taka Anty Saloon ce tazo tare da wata dadtijuwa gajera mai jiki , Natare su haba haba a main falo muka yadda zango dasu naje na dauko masu ruwan sha tare da drink's nakawo masu, alokacin da nake aje wa agaban yar dattijiwan Anty Saloon ke cemin mamace fa tazo Da sauri nadaga kaina ina kallon mahaifiyar nata inda nakara gaishe da Mama cikin Ladabi ta dan yi kokarin rusun na min itama, Nace a,a a Mama anice dai zan durkusa maki bake ba, Hira sosai mu keyi dasu takawo tsaraban da akazo muna dashi irin kayan amfani na gargajiya wanda babu shi a nan sosai, Naji dadi wanan karamcin wanda hakan yakara sani tabbatar da zance Anty Saloon a kaina da take yawan cewa tana dauka na takar kaunata ce ta jini, Anan take ce min ai maigidan tane ya kawo su don tun da safe su ke son zuwa amma sai yafita, Nake tambayan ta shago tace tunda mama tazo bata faye shiga ba yara ke zama yanzu ai, Salawatu ta fito ta gan su amma sai tai tankar bata gansu ba, zata wuce amma sai Maman tace mata, Ina wuni ? Sai lokacin ta juyo ta kalli Anty Saloon wace bata ko kallon gefen ta ma, A wani iri tace wa yar tsohuwar yawa sannu ko ? Sai banji dadi hakana din ba sai nake ganin ai babba babba ne ko , Amma ba laifi ai cin tuwon kishiya ranko ne don zamu hadu ai, Don ai naji yadda su kayi da Anty Sadiya akan friends din ta da sukazo suna shaye shaye a gidan, Da zasu tafi naba Mama turmin zani lafiyayye da turare mai kamshi, tai muna taji dadi tana samin albarka da hausa da kuma yaren nufawa,, A kofa na raka su sai ga Yaya Abubakar ya dawo yar dadtijuwar matar tai mai gaisuwan mutunci sosai, Daga inda nake a tsaye ta cikin get nake cewa mahaifiyar Antyn Saloon ce tazo daga Bidda, Yace ok ya juya yana mai sa hannuwan shi a cikin aljihun shi yaciro kudi yazo gab da ni ya miko min yana cewa ga shi ki bata kice mun gode, da zuwan ta,,, Na bata tabi bayan shi,har kasa takai tana mai godiya, ya juyo yace no ba komai mun gode,, Sai da naga wucewan su na shigo ciki a daidai da lokacin da su Baba Wadda suke ta kokarin shivowa da ledojin da suka dawo dashi, A falo su kai ta aje kayan shima azaune maigidan yake a falo Salawatu ta kawo mai goran ruwan sha, agaban shi, Sannu na karayi mai ina kokarin wuce, sai naji muryan shi yana cewa, ki kiramin Sadiya kuzo please ya fada a dan gajiye,, Gaba dayan mu ,muna zaune a falon muyi tsit kamar ruwa ya ci mu,, Ledojin ya cewa Salawatu ta jera su a kamar yadda yake mata kwatance, Sai yake cewa Sadiya ki dauka kamar bazata dauka ba tamike tana wani yatsune yatsune fuska ta ja kashi guda, Ya juyo gurinda nake a zaune yace ke kuma dauki guda itama ta dauki guda, Kowan mu ledan gaban ta taja yana mai kura muna ido har kowan mu ta koma mazaunin ta, Dayan ledan wanda shikadai ne daga ciki kuma bai kai sauran cika ba ya dan dubi gurin da nake yace, Dauki wance kibawa Ramatu ko, Na dan mika na jawo shi ina cewa mun gode Allah ya kara rufa asiri Yace zuwa banda gobe zamu tafi Birnin Kebbi, da ke Sadiya da Meenatu, don mu dubo Samira da jiki da sauran mutanen gida Saboda kunga azumi ya gabato yanzu,, Ya juya gurin Salawatu yace zamu barki da Ramatu dan ku zauna tare har mu dawo, Tace a sanyaye cikin nuna rashin jindadin ta amma ai da nima an tafi dani ko, Fuska adaure yace ke yaushe kika dawo daga can da zaki ce a tafi dake kuma, Ya cigaba dacewa duk da na duba store naga akwai koma na karo abubuwa da dama daga ciki,,, Sai yai shiru ya koma ya kara kwantawa saman kujera yana mai lumshe idon shi a hankali yana hamma kamar mai jin barci Muna zaune gaba dayan mu munyi shirun mu kayi don bamu da say daga gare mu Yace yanzu abinda za,ayi duk wace ke da abin yi zuwa gobe sai ta je tayi, don tunda asuba zamu bar garin nan insha Allah,,, Ina kokarin mikewa tsaye ne na ji muryan Anty Sadiya ta na fadin cewa, Meenatu idan zaki shiga gurin wanke kaine sai mu tafi tare, Fuska a sake har a zuciya na ba matsala nace to Allah ya kai mu anty sai mu tafi da guri don kada layi yai yawa, Na kwashi kayan mu nida Ramatu nabar gurin saboda nagane cewa Salawatu bata acikin good moode, zaune kawai take tana yake, Baba Ramatu ta kasa rufe baki sai ikon Allah take fada, Tace kai jama,a gaskiya wanan irin alherin ban san may zan fada ba, Nace aiko sai kiyi maza kije godiya kafin ya shige don nasan da wuya ki gan shi sai kila da safe, Da sauri ta nufi falo don tai mai godiya daga shi sai Salawa sai dai da alaman ba a cikin dadin rai suke ba, Ta na zuwa gab dasu taji yana cewa na fada maki cewa bazaki ba period bazan canza magana na ba don ki ji,,, Ramatu ta karaso zuwa gurin su ta tsuguna har kasa tana cewa Alhaji nagode Allah ya kara rufa asiri, Hannu ya daga mata yana cewa no ba wani abu ki tafi kawai ,,, Salawa tabi bayan Ramatu da wani irin uwar harara har ta bace ma ganin su,,

****** ********** ****** Kitso kawai anty Sadiya tayi wai bazata iya zaman gyaran kafa ba dan haka akai mata kitso wanda ya fitar mata da da kkyau fuskan ta a fili,, Nikan anyi min kitso an,wanke min kafa da yatsun hannu na an rangada min kumshi a kafa, da hannaye na, tsab kafin a gama min Anty Sadiya duk ta matsu ta koma gida dole na kira Baba Hamza yazo ya tafi da ita,

Sosai,nake shirin kayana tsab a dan karamin trolley daga gurin da nake zaune ni da Ramatu ne a dakin nawa, Ita ce ke ta faman shirya min kayan da na harhada zan tafi da su tsaraba, Ina kallon lokacin da mike ta nufi drower dina na mirror ta debo magani na ta cusa min a jakata , Dariya ta bani don ta san cewa idan don tani ce bazan sha ba kuma zan tafi za su ba, Tace aida ina da nomban mama da sai nace ta sakaki a gaba kina sha, Nace yanzu ai tunda kin sa aidole na sha Baba amma ni sai nake ganin cewa naji sauki ko, Tsab komai da nake bukatar tafiya dashi ya hadu inda Ramatu ke ce min gaskiya Uwar dakina da Alhaji zai yarda in koma gida har zuwa lokacin da kuka dawo,, Nace a cikin murmushi au, bazaki zauna da Salawatu ba ke nan kike nufi, Sai da tayi kamar ta leka kofa don kada wani yaji may zatace sai ta juyo tana ce, min, Ina tsoron abokan ta mashaya kada su shigo suyi min dukan tsiya a gidan nan babu kowa boni ya ci ni, Dariya sosai ta sakani harda kwalla tace ai tun ranan da tace wa Uwargida kada takara saka mata ido ga al,amarin ta kuma ta bugawa Alhaji waya a take, take sheda mai cewa aiwa Uwargida kashedi a kan ta, Yaya Abubakar wanda ke tsaye daga kofan dakin yai gyaran muryan alaman yana gurin a tsaye, Ramatu tai saurin kama bakin ta batare da ta kara cewa kala ba, a lokacin, Tamike tabar muna dakin don tasan cewa Yaya Abubakar yana son gani na ne. Ramatu na fita ya karasa shigowa dakin yana ce min ya kamata ace duk wani abinda zaku tafi dashi an saka a mota tun yau nace amma Yaya ni sai anyi suna zan dawo ko ? Yace OK idan hakan kike so sai ki shirya ke nan don dai ni ba zan tsaya nawani lokaci mai tsawo ba a can,,,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH- AL- MUQADIR

Yan uwa muslmai, fatan alheri gare ku, a koda yaushe, kaunar ku da addu,an ku a gareni tankar wani taki ne, mai kara min girma da albarka ga al,amarina, Nagode nagode nagode kwarai da irin kulawan da kuke gwada min,,,,,,

Fuskan Yaya Abubakar yana dauke da murmushi har barci ya kwashe shi a haka, yana tunanen irin bawai war da Allah yai ma wanan yarinyar haka, Natsuwa gamsuwa da kwanciyar hankali inganttaciya sai idan ya kasance da Meenatu, Gashi kuma yau yaji ta kara canza mai a fiye da kullum da yasan ta, Duk da cikin ta ya tsufa amma sai ya samu gam suwa ta daban daga gare ta wanda ya sa shi farin ciki da annashuwa, Ya tambayi kamshi da kamshi cewa kenan wanan yanayin ya mayar da Meenatu haka ko ya dai, Nikam ban san may ya ke ciki ba sai kwance nake ina barci na a hankalina kwance, Sai jin hannuwan shi nayi ya kara rungumoni zuwa jikin shi yayi da naji ya sauke wani irin ajiyan zuciya da karfi, Tare da kara rungumo ni zuwa jikin shi ya dan matse ne a hankali yana sauke numfashi a hankali, Abinda ya dan sani bude idona a hankali daga barcin da yadan fara dauka na saboda duk a gajiye nake a lokacin, Kiss naji yakai min a daidai kumci na alaman godiya da sai da safe ,

Washe gari mun tashi duk a gajiye ban san ya akayi ba ina ganin ankawo breakfast a gidan su Fatima, Amma sai naji yana cewa a fita da shi, aba yan ma,aikatan gurin masaukin, Ina ganin haka nace a raina tare da wani irin lumshe idona ina cewa yan raini hankali kawai, Naso na koma barci amma sai kuma cikina dake bukatan na sa mai wani abu saboda wani irin yunwa da nake ji, Don haka sai ban tsaya ba na mike na kara shiga wanka ida na fito na fara shiryawa, Yaya Abubakar, ya shigo dakin yana min kallon mamaki ganin cewa ina shirin fita, Ina kokarin rolling a kaina nake cewa cikin dan bata fuska wallahi yaya gida zan tafi yunwa nake ji sosai, Dariya naso bashi ganin irin yadda har jikina yake rawa a lokacin, Inda nake tsaye ya kara yayin da ya tallafo cikin nawa a hankali yana cewa Oh, I am,so sorry dear, laifin Daddy ne ko yasa ka wahala last night,? Murmushi nayi don jin may Yaya Abubakar ke cewa, Nace a hankali ai, baby bai fushi da Daddy, shi, kawai dai yunwa muke ji, Dariya yayi mai kama da yake don shi ba muyltum bane mai washe baki a gurin dariya, Yana cewa an kawo maku abinci kun ce bazaku ci ba ,,

Mun shiga gidan mu lokacin rana yadan tasa mutane sai hada,hada dan su, su keyi na yau da kullun wanda haka al,adan rayuwan dan Adam yake, Saida na shiga part din mahaifana inda na aje handbag dina, na nufi sauran part din gidan namu, Mutane sai sannu da zuwa suke min da kara yi min kallon kurullah, A part din su Mama Ladi gurin gwago Sa,a kishiyar ta na fara zuwa gaida ita, Daga baya na dawo gurin Mama Ladi, inda na samu har yaya Abubakar ya shigo suna zaune tare da ita, Tun da ta hangoni naga ta daure fuskan ta tamau daga yar fara,ar da takeyi da farko, Saida na dafa dan kujeran dake dakin ta wanda Yaya, Abubakar yake zaune, akai, Na samu na kai zaune saman tabarman dake shimfide akasa dakin Nai mata ina kwana da mun samay su lafiya ? Yau abinda mamaki don na samu amsawan kwarai daga gare ta ba kamar kullun ba, Amma sai na dan ganta hakan da cewa ko don dan ta ya na zaune a gurin ne, zato dai (zunubi ne, ) Muryan ta naji tana cewa kamar da gaske amma dai, yanzu ke kusa hauhuwa ko ? Ban amsa mata ba don amsawa rashin kunya ne ga manya don haka sai nai shiru kawai, Yaya Abubakar ne wando idon shi yana ga wayan dake hannun shi ke cewa insha Allahu kila kafin mu tafi ta haihu, Wani irin naga Mama Ladi tayi tana cewa, to aiko gara in haihu tun kafin su wuce din, Nidai ban ce komai ba sai dan wasa da gefen tabarman da nake zaune na keyi,kawai, Dashi da mahaifiyar shi ce kawai suke tahiran su suna magana akan Safiya da mijin ta yanzu bai aikin komai kamar da can baya, A hankali na yunkura na mike don komawa part din mu gurin Mama Yaya Abubakar ya bini da ido a hankali, yana cewa, ina kuma,zaki Nace cikin dan ya mutsa fuska gurin Mama sare zanje ko da fura a fridge na sha, Ok kawai yace sai bayan fitanane mama tai wani irin ta dubi dan nata tana cewa Allah mai iko yanzu ni jikana na farko da zangani a gurin ka ta wa yan nan munafukan mutanen zai fito min, Mutanen da ko mutun yafi aula dubura baya taba gane cikin su sun iya, kisisina kamar yunwar cikin su, Dubi yadda take wani karairaya kamar diyan wani da wata can sai mutum yace ba diyar Samaila da Saratu bane tallakan banza da wofi, Haba haba Mama wanan ba kyau fa ina dai yarinyar nan diyar ki ce itama, A,a wallah, mi add hadin kifi da kaska Babu abinda na hada dasu don dai ni wallahi tallahi kaina kadai naga kana ra,ayin zama da wagga diyan in bashi ba da tuni na kakabe ta cikin kayana, Mi akai da babbakun iri irin diyan Fuldenu masu gaje guri yazam nasu,, Yaya Abubakar wanda zari ya ishe shi yace, waima ina son ganin Safiya don mu san abin yi a kan zancen haihuwan Meenatu, Da sauri Mama tace mi zakayi har wani shiri na zakayi su mi aggaresu da zasuyi wanda har za,a kashe masu garali irin haka, Ya mike tsaye yana cewa mama ni ban damu da zancen suna da shi ko ba su dashi ba, Meenatu dai ko banza kaunata ce ita, ina da ikon yi mata irin yadda zanyiwa Safiya ko Samira, a rayuwa, Don haka ni bance sai sunyi min wani dawainiya ba mai yawa can,, Sannan kuma abinda ke cikin cikin ta ai dana ne jinane jininki ne kema don haka babu zancen yi dole, Daga haka yasa kai yana cewa hello, hello a cikin wayar shi,

****** ********** ****** Zaune ni da mahaifiyata itama babu zancen da take min sai na yadda za,ayi fitar kunyar haihuwana, Nace mama shin wai har mi da dami zaki na fada maki don Allah kada kuyi wani dawai niya mai yawa, Mama tace ina wagga zance ai dashi mahaifinki ka kwana da shi yaka tashi, Har adashe naji yasa akan zancen amma sai dai basu jittu ba da masu adashen don sun kai shi nesa kwara, Tambaya nayi nace halan har nawana kwasa Mama, ? Tace wai dubu saba,in na sun kasa kwasa shina yashiga ga kuma zancen tafiyan su ya taso shina yace in abin ya tabbata shi yaron ga sai ta kama fita da mota tai zuwa jigila don a samu kudin kashi,dana zubi, Duk wanan lokacin da mama tafara bayanin ta hannuna yana a cikin jakata, a lokacin, Na zaro sabbin yan dubu guda da dari biyar biyae na ajesu a gaban ta ina cewa tau Mama ni dai ke ga abinda anhannuna don haka sai a fara amfani da suwa, Zancen kuma ace wai yaya Ibrahim ya dinga amfani da motar Baba ni dai ban yarda ba mama abar mashi motar shi idan ya dawo sai yaci gaba da amfani da abin shi, Tace min mi zamu ci idan ya tafi halan yar baba Ina gyara mike kafana nake cewa akwai Allah mama kuma shi wanda ya kai su ai bazai bar ku hakana ba, Sai lokacin taga gudin dana zube a gabanta take cewa,cikin mamaki, Ina kin ka samo wanga kudi masu yawa haka yar baba, cikin mamaki tare min wani irin kallon Mama kudin da Yaya yake yawan bamune sune naita tarawa a guri na don wanan laluran, Tace tau Allah shi kyauta Allah yai maku albarka yabaku diya masu rama maku alherin ku, Kullun ina jin dadin irin kalaman Mama a gare mu don kalamanta suna sanyaya min zuciya ta akoda yaushe, Mamana mutum ce wace bata shiga harkan kowa agidan mu hakan yasa su Mama Ladi ke ce masu wai masu zurfin ciki, Don bazaka taba jin halin da take ciki ba sai dai kagan ta acikin rufin asirin Allah, A nan Mama na take kara ja min kunne akan zance auren da Yaya Abubakar yakara a lokacin, Mama tace min kada ki yarda da hadin kan kishiya domin kishiya duk sunan ta kishiya, Ki yi al,amarin ki gwargwado da kowan su tsakani da Allah, Tace balle yanzu idan Allah ya saukeki lafiya kin samu abokin hira idan ma mace ce abokiyar shawara kika samu, Nai murmushi nace Mama Allah dai yasa macen ce wallahi, Tace idan mace ce shikenan haka tsayuwar ki da rayuwar ki za su tsaya, Amma idan namiji ne kika fara samu zaki kara tsawo kadan bisa ga yadda kike, Sannan kuma wani irin hankali da natsuwa zasu ziyarci rayuwan ki sosai, sai dai idan mutum ba mai rabo bane daga Allah to ba zai daina aikin shirmay ba, Daga gurin da nake zaune nace tau fa ashe haka zancen yake ke nan , Aiko ban taba sani ba ni wallahi tace yar Baba har yaushe kike da zaki san abubuwan rayuwa, haka,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull