Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 76

Tarko complete novel - Chapter 76

Tarko complete novel Chapter 76: Tarko complete novel Chapter 76. ****** ********* ****** Kwanan mu biyu a Birnin Kebbi mukai shirin komawa washegari,…

3,165 words

****** ********* ****** Kwanan mu biyu a Birnin Kebbi mukai shirin komawa washegari, Malam tsoho da na shiga gayarwa a sashen shi yake cewa, maman biyu ina ce ko kinzo haihuwan ne ai, nai murmushi nace ba, yanzu ba malam, Sai naji yace min kaiyya Aminatu naso ace kin haihu anan kusa da mu wallahi, Shiru nayi ina sauraren shi don irin yadda yai magana nasan cewa da wata ma,ana acikin ta sosai, Wani murmushi naji ya sake, yana cewa to bari dai na dan saki a hanya don ki gane, Ya ce haihuwar ki a hannun mu yana da babban amfani sosai bisa ga irin yadda rayuwar yau da kullum ta koma wa mutane, Da farko kin sannirin rikici da faman da mukai tayi da mahaifiyar kishiyar ki, Sai a lokacin gabana ya fadi don sam na manta da zancen wata wai Hajja, Malam yace kinga kuma yadda uwar mijin ki take har yanzu ba wai hankali gare ta ba zata iya cewa idan a can kika haihu zata biku can ayii buki da ita, Nandai ya dinga kawo min musalai masu amfani sosai yadda har jikina yai sanyi don da duk ban kawo su a kai ba, ni, Zance Hajja tafi tsaya min arai amma sai kuma na yi amfani da kalman malam na karshe da yake cewa ai duk sherita batai Allah ba don Allah da ya baki ya na tare da ke, Lafiya kalau zaki haihu insha Allahu, babu abinda zai faru dake har dan cikin naki, Nabar wajen malam tare da yi mashi sallama jikina duk ba kwari akai, Na samu mahaifina a part din mu nan muka zauna tare da shi muka dan taba hira dashi yana ta yi min nasiha akan rayuwar duniya, Kafin mu dawo naiwa Yaya Abubakar magana akan ya samu abinda yabar wa su Baba wanda zasu barwa iyalin su a gida yace ba matsala a hakan zai duba yasan yadda akayi, Tafiya saura sati uku zuwa hudu su tashi yanzu don haka a cikin shiri suke gaba dayan su, Baba yai min nasiha akan inyi kokari indawo gida kafin haihuwana yazo inda nake ce mai ba matsala da na koma insha Allahu zan shirya indawo, Mun iso sokoto misalin shabiyun rana tun a mota na sheda mai cewa zan dawo BK badadewa ba, Saboda yadda Baba ya umurce ni dayi kenan kada na tsaya sokoto in haihu a gidan uncle dina, Yake ce min idan na shirya zai ce Aliyu yazo ya daukeni, Da sauri na ce mai a,a gaskiya bazan bishi ba don kada ma ya fara, wanan zancen ne ya bata mai rai, Fada ya keyi cewa, shi mai nake son mayarda Aliyu ne don ya ga ina kokarin bata masu alakar su da Aliyun, Bayin magana ba sai dai hade rai danayi nai shiru yana zuba min maganganu wai tsakanin shi da Aliyu ya wuce yarda nake tsanmani don haka na shiga hankalina, Shiru,nayi har ya gaji da zancen shi ni dai bance uffan ba a lokacin don bazan iya bashi amsa ba, Nadai sa a raina cewa Aliyu dai ne ban bi kamar yadda yake so, kafin mu isa yadan sake ranshi yana cewa, idan ya samu time zai dawo kafin su wuce zuwa saudiya, Mun isa mu kayi sallama dashi na shiga gidan mu sai dai har lokacin rayuwana babu dadi, Mun dan yi hiran rayuwa da anty na kwanta don na huta saboda jikina duk ban jin dadin shi a lokacin,

****** ********** ****** Ya Abubakar ya isa gidan shi a gajiye inda ya samu iyalin shi lafiya suna zuwa daya bayan daya suna mai sannu da zuwa, Nan ya haye sama part din shi don ya dan watsa ma jikin shi, ruwa yayi alwala don yai sallah, Ya dauki lokaci kafin ya fito yana saye da wandon tree quarter a jikin shi, Sau yar riga mara hannuwa da yasaka tare da feshe jikin shi da kamshi mai dadin shaka, A hankali ya kai zaune tare da, dan daukan remote ya kunna tv, don ya saurari, network, news, Fatima ce tafara shigowa falon tana saye da dogon rigar atamfa a jikin ta wanda yai fitar mata da surar jikin ta da da kyau, ta samu guri ta zauna daga gefen shi Bata kai minti biyu ba ko uku da shigowa sai ga Salawatu ta shigo ita kuma buje da rigar lace ke saye a jikin ta, ya matse ta tsab ta ko ina, Nan suka zauna kowa tana gwada wa maigida nata irin bajin tar daga zaune a cikin tako, Can sai ga Sadiya tafito ita ma jikin ta saye da dogon rigar jallabiya brown colour, Ta zaune tare da yi mai ya gajitan hanya da ja,aman gida ya karba acikin dan lumshe idon shi, Salawatu ce take cemai saboda son jin kwan, ka koga Meenatu, Yana kokarin rage volume din tv yake ce mata na ganta mana ai muna tare don tare muka tafi BK da ita, Gaba,dayan su yana cewa hakan sai da rayukan su ya dan sosu saboda, kishin da ya ziyarci zukatan su, Anty Sadiya ce tai karfin halin cewa ayya yanzun kan ai ta yi nauyi da yawa, Bai bata amsa ba kamar yadda tasan cewa ba lalai ne ta samu ansa daga gare shi ba, Yana ta dan,ne dan,nen tashoshin a tv bai tankawa ko wacer su ba su ma ko,wace da irin abinda take sakawa a zuciyar ta,, Fatima ba karamin dadi taji, ba da Abubakar ya kyale, Sadiya, akan zancen Meenatu da ta tambaya, Sai da ya dauki kamar minti, biyar zuwa sama sanan ya dan juya gurin Sadiya, Yace cikin furzar da dan iska mai zafi daga sama yace ai ina ga bata,da nisa,da haihuwa, kila, Salawatu tace cikin dan tabe fuska da baki shi cikin har ya girma ne ake zancen haihuwar shi,, Daga gurin da Fatima take zaune tana kallon fuskan Salawatu yadda ta tabe shi sai cewa tayi, a ranta ita wanan ke nan kowa kishin shin ta takeyi, Sarai ya fahinci irin yanatin ko wacen su amma sai ya nuna tankar bai fahinci, may suke nufi ba a hakan da su keyi, din, Bayan ko wace ta gama nata irin takon zuwa wani dan lokaci da guda, guda suka watse kowa ta kama gaban ta, Yayin da maigidan ya mike a hankali zuwa nashi part din don ya huta,

****** ********** ****** Sati guda bayan dawowan mu muka shirya Anty Amarya da wata yar uwar ta su ka rakani gida acikin motan Uncle dina, Malam tsoho wanda ya kasa boye, farin ciki sosai a lokacin da ya gane mu, Sun,zo da abubuwan da duk Anty Amarya tasan cewa zan bukata, a zamana tun daga dangin kayan amfanin jiki da na ci da sha, duk anzo min da su, A bakin Mama Ladi Yaya Abubakar ya samu labarin dawowa na gida haihuwa, Inda ta bugo waya tana mai korafin cewa ya kashe min kudi haka masu yawa saboda kawai zan zo gida haihuwa zai kashe kudi irin haka. ? Kuma ace idan na haihu sai ya kara sayen wani abin yakara kawo muna ai wan,nan ya zama kasuwanci ke nan, Da mamaki Yaya Abubakar ke tambayan Mama Ladi cewa Meenatu ta dawo gidane, ? Mama tace kana nufin cewa kai baka da labarin cewa, andawo da ita dazun da rana, da matan kawun ta, Mamaki sosai ya Abubakar yayi a lokacin da yaji abinda Mama tace mai Abinda ya fara zo mashi a rai shine, cewan da nayi ban yarda da Aliyu yazo ya dauke ni ba, Watau abinda nake nufi kada in fada mashi ya turo min Aliyu shiyasa naki fada mai ke nan ko, Cikin taushin murya yace Mama gaskiya ban da labarin zancen dawowan ta gida, Wani irin nauyi da kunya ne ya kama Mama don tayi fadan karya bata sani ba, Mamaki takara yi don jin cewa bai, masan da zancen ba gashi kuma taga irin yawan abubuwan da nazo dashi gida, Nan take fada ma Yaya cewa kada ya ko ce zai wahal da rayuwan shi gurin yi min wani da wainiya tunda dan uwan mahaifiyana yai min, Yaya Abubakar yace haba Mama ai baza ai haka ba tunda tana da hakki a kaina, Nan dai ya samu ya lalashi mama Ladi don dai, kawai ta kwantar da hankalinta kada ta sa wa kanta damuwa, Saidai kuma a zuciyar shi fam yake da fushi akan may zan koma gida batare da ya sani ba, Don haka sai kawai ya share ni batare da ya ce min uffan ba akan zancen, Waya ma sai bai bugo min ba kamar yadda ya,saba yi min duk dare na mu kwana lafiya, Da farko na dan sa damuwa don rashin jin kiran shi da baiyi min ba ga ranan,, Amma daga baya sai na fitar da damuwan tun da nasan cewa a gida nake zaune yanzu Sosai nake samun kulawa daga gurin mahaifiyata, da mahaifina wanda sai haba, haba su keyi dani, A kasarin zaman nawa a part din malam tsoho na ke yin shi don in samu natsuwa saboda babu yara a part din da yawa, wanan abin da nayi yasa matan malam tsoho sun ji dadin yin hakan a ransu sosai, Mahaifina ya bawa mahaifiyata shawaran cewa na koma daya daga cikin dakin matan malam tsoho da zama gaba daya, Hakan yasa ni komawa dakin mahaifigar Baba Wadda wace ita ce take yawan sake min fuska tun farko,, A cikin dare Mama Sare taba kan,nena kayan amfanina suka kawo min part din yan tsofaffin Kafin kayan su zo tana cewa na tashi na koma part din mu kada dare yayi sosai sai murmushi nayi kawai nace ai a tare zamu kwanta a saman gadon nan naki na karfe, Dariya tayi tana cewa haba yar nan ina zaki iya kwana saman wanan karfen ai sai mu, Sallaman yaran ne ya katse ta suna cewa ina zamu kai maki kayan Anty Meena, Nace ku shiga dashi dakin Dije mamaki sosai ya kamata tana cewa yanzu dama da gaske a nan din zaki kwana, Kai amma dai naji dadin hakan sosai wallahi ashe nice mai wanan masaukin bakin, Allah ubangiji ya jissheki lafiya yasa yan kuda suna kwana a lokacin, Kamar yadda na nace haka na haye dan gadon karfen dake cikin dakin Mama Dije, na kwanta barci, Kafin barci ya dauke ni inajin Mama Dije da uwargidan ta tana sheda wa malam tsoho cewa ai ina nan part din su, anan zan zauna Sai da ya kurkure bakin shi da ya cika da ruwa kafin ya ce au,to ku ce min ina da bakuwa a shiyan nawa ke nan, Mama Dije wacce itace mahaifiyar Baba Wadda tace ai ina ga tayi barci Don da alaman bata da nisa sosai don yau, tun da rana ina hankalce da ita Saboda duk wani alama na haihuwa ba nisa ya baiyyana a gare ta, Daga gurin da nake nai murmushi na, ce kai Mama Dije hoo, Bayan asibiti sun auna ni sun ce da sauran lokaci zaki ce min hakan wai kin ga an kusa haihuwa, Nidai tun ina jin su har barci ya zo ya kwasheni ban sake jin zancen su, ba kuma,

****** ********** ****** Tun da mutanen gidan mu su,ka fahinci cewa a part din malam tsoho na ke zaune ba part din iyayyen mu ba sai wani sabon gulma ya fara fitowa a cikin gidan, cewa Mahaifana sunyi hakane don sun,ga cewa zan haihu basu aje komai da zasu min na fita kunya ba, Zance iri iri suka dinga sakewa akaina badon komai ba sai don duk diyan gidan mu dake dawowa haihuwa babu wace aka taba kaiwa gurin matan malam din don zaman shan ruwan zafi, Niko iyaygena suna da hadi da fulani sun san kunya sosai, don A gare su tunda suna da magabata a gida bai, dace su zauna dani a cikin part din mu ba,

Mama Ladi tafi kowa daukan zafin zancen don da tasha zuga sai kawai ta hau yada magana tana cewa, Ita fa bazata yarda a mayar mata da Dan, ta shanun tatsaba a dinga fakewa ana ci mai dukiya, Malam tsoho shine ya jawa mahaina kunne akan cewa kada ya yarda ya kulla da zancen Mama tun da bata da tunane ita, Kauna ta (Sister) dina, itace ta shigo part din malam da safe muka gyara komai nawa yadda ya kamata muyi, Abin gwanin ban sha,awa idan ka gani da kaina na fito na,fara gyaran tsakar gidan malam din duk da su Mama Dije sun hana ni yi komai amma saida na gyara ko ina tsab, Abincin da sukayi sai suke ganin cewa wai bazan iya ci ba sai gani su kayi kawai na ci tuwon masra da miyan busassan kubewa yaji kifi da man shanu, Hakan ya kara sa,susakin zucitar dani suka kara sakani a jikin su, Su ko mutanen sassan gidan muna sai shige da fice su keyi wai don kawai su kara tunzura Mama Ladi, Ni ba mai yawan son hiraba bace ko hayaniya tun farko, don haka koda zasu shigo don ganin abin da na keyi sai su samay ni a cikin daki abina,, Sai ku ma a koma ana gulman cewa ban aikin komai sai kwanciya kawai na ke,yi ban motsa jiki irin na masu ciki wai, Matan malam tsoho sune masu mai da martani a cikin magana a dunkule, Ni nawa dariya ne kawai don nasan cewa rashin na yine ya kawo hakan wa mutane,

Yau kwanana uku da zuwa Birnin Kebbi Yaya Abubakar bai bugo min waya ba kamar yadda ya saba, Don haka, na kau da girman kai irin na muna matan hausawa a zuciyana nace bari ni na kira shi, Sai dai wayan wai switch off, hakan yasa ni gane cewa yana, cikin meeting ko kuma busy a office a lokacin, Don haka sai na kira Anty Amarya mu kadan gaisa da ita sama sama don wani irin abu da naji a can kasan marata tankar ansa min allura an tsikare ni, Nai mata sai anjima ina cewa zan dan ke waya bayi ne please har tana min sheri wai ko a bin ne yazo ta taso, Dariyan karfin hali nayi a cikin yar shagwaba nace aini Anty a gurin ki naso na haihu na sha gata tace aiko a nan din ma da kike Meenatu za ai maki gata, Nace sosai ma tace to ai kinga ba matsala ke nan nace dashi don a nan fa anty ruwa masu mugun zafi ake wa mutum amfani da shi Dariya sosai tayi tace ai yanzu nagane wayon ki watau gurin Anty asha ruwan sanyi ko nace wallahi ko, Hiran duk yadda naso muyi shi baiyi ba don irin abinda naji yanzu yafi na dazun ciwo sosai, Don haka ban san lokacin da na kashe wayan ba na kai durkushe, tare da murde baki idona yana wani fitowa waje gaba daya, Nakai kusan minti uku a hakan kafin a bin ya sake ni, inda da kyat na samu na rarafa na hau gado azatona hakan zanfi dan samun sauki, Ai kamar an kara min tsananin abin ne irin yadda nake ji a lokacin Tunda nake duniya ban taba sani cewa akwai ciwo maka mancin wanan, ba, sai yau, Ni kadai a daki cikin dauriya da karfin hali irin nawa, nake ta gumurzu a dakin Mama Dije, wace a lokacin tana can gurin da suke yin yar dawo, na shan gida,, Ina daga duke a bakin gado na kifa kaina a saman gadon dakin yar dattijuwar matar kakan nawa, Naji muryan maidakin tana cewa subbahanallahi yaya ankayi Meenatu, Ban iya magana, ba sai dan kara dukar da kaina cikin cinyoyi na da nayi, don azaban da na keji a lokacin yafi karfin a fadi, A hankali ta tako gareni a rude tana cewa cikin dan tausa murya kamar wace bata bukatan wani yaji , Yaya kike ji Meenatu ko dai in fadi ne mu tafi asibiti, yanzu, Daidai lokacin abin da nakeji ya fada min a nadago kai na da goshina da yai zufa don azaba nace wai Dije marata ce ke min wani irin mugun murdawan da ban taba jin irin shi ba, Tace sannu sannu kinji Allah dai ya raba ku lafiya sam yau ko a zuciyar da nake amsawa ban,iya amsa wa ba, Da sauri mama,Dije naji muryan ta a waje tana cewa yaro aje gurin malam ace ya rubuto masu suratul Maryam, Sai kuma naga ta dauko wani dan abu mai kama za an dunkule hannaye tana kokarin daurayewa daga bisani ta jika shi a cup,da ruwa mai yawa, Suna tsaye a kaina daga ita har abokiyar zaman ta sai faman sannu, sannu yar nan su ke min, Kafin wani dan lokaci wanan abin da Mama Dije ta jika a ruwa har ya wani babbaje a cikin ruwa ya bude kamar abin sihiri ta koma kamar yatsu, Sai naji tana cewa ai yatsu Fatima da aka jika hae ya jiku alamar haihuwa yazo ke nan, Gabana ya fadi da naji ta ambaci cewa haihuwa ya zo kenan watau ana nufin haihuwa zanyi ko may, Wata zuciya tace min kai wanan shirmayn Mama Dije ce take ta faman kira min haihu da sauran time, Yaro yazo da wanan rubutun da aka aika akawo daga gurin malam, Yace wai ancd na shaye dukka a lokaci guda na kuma sha da Bissimillah idan zan sha, Na karba bayan wancan ruwan Yatsun Nana Fatima da na,sha da farko, na kara kinkiman wani ruwan rubutun, a cikina,, Wanan karon tun shan wanan ayan danayi na babu sauki ga al,amarin sosai nakuda ya taso man, Duk da malam yasan cewa idan har mace zata haihu da yardan Allah da zaran an rubuta mata suratul Maryam, insha Allahu, zata, haihu aranan da yardan ubangiji bada dadewa ba, Wani wani rubutun ya kara aikowa dashi wanda ya rubuta Bismillahi kafa 21 ya wanke da ruwan ganyen gwandan gida, yace na yi sha daya ko biyu zuwa uku gaba dayan shi , a gani, Sosai hankalin mutane gida duk ya tashi kowa na part din malam tsoho da namu part din parents dina hankalin su yana tashe, Yaya Ibrahim din na ya matsawa malam tsoho da cewa a fito dani zuwa asibiti tunda yanzu waye wan kaine, Don may za,a ce a barni a cikin gida ana ta dura min rubutu kala, kala haka. Motar makwabcin mu aka samu wanda bai dade da dawowa daga aiki ba, Abin tsofafin mata Mama Dije wace tasan kan haihu sai cewa sukeyi ai dadai ayi hakkuri agani zuwa dan wani lokaci kadan ko zan haihu, Ya Ibrahim yace don Alkah ku kamota mu tafi kada a tsaya wani tunane can, Leda mama Dije tafara sakawa gurin da zan zauna a motan sanan na shiga tare da taimakon su,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL MUQATADRI

JUMMA,AT MUBARAK YAN UWA MUSULMAI ALLOVER THE WORLD ALLAH YASA MU DACE SAI KU TAYINI ADDU,AN AL,AMURORI PLEASE, ALLAH YA RUFA MUNA ASIRI DUNIYA DA LAFIRA ALLAHUMA AMEEN👏👏

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull