Tarko complete novel - Chapter 78
Tarko complete novel Chapter 78: Tarko complete novel Chapter 78. ****** ********** ****** Kowacen su ta caba kwaliya kamar masu zuwa gurin gasar fitar da…
3,135 words
****** ********** ****** Kowacen su ta caba kwaliya kamar masu zuwa gurin gasar fitar da gwanan kyau, Yanzu abinda suka gane shine kafin duk ace Yaya Abubakar ya fito duk kan su suna zaune kowace sai ta shiga yin nata irin iyayin, don burgewa, Ànty Sadiya ce, wace bata damu da irin wanan abubuwan da sukeyi ba tankar za su maida mijin a ciki don so, Yau ma kamar kullun Fatima ce tai nasara samun fitowa da wuri yau tana saye cikin wani Swiss lace mai shining, an,mai, wrapper mai kyau, dinkin shi half gown, Don haka ta na fitowa ta samu, guri daidai gurin da maigidan zai zauna ta zauna kasancewan ita,ce da girki, a ranan, Ba tafi ko da minti biyar ba da zama sai ga salawatu tafito cikin wasu material sky colour masu flowers farare, dinkin skirt da riga, kan,ta ya sha kitsoh attache, sai sheki ya keyi,,, A hankali yake takowa daga matakalar benen wanda ya sha ties sai sheki yakeyi don goguwa,da yasha daga sabuwar yar aikin su, da take masu gyaran gida, ita da Ramatu, Ganin shi tafe yasa ko wacen su ta fara dan kimkimtsawa cikin style, batare da yar uwa ta sani ba,, Sannu da fitowa su,ke mai yayin da yake zama akan kujeran three seaters dake falon, Sai amsa gaisuwan su yakeyi tare da dan yiwa kowacen su na ta jinjinan a cikin style irin na maza, Fatima mai girki a ranan tafara gabatar mai da abinci tare da dan kashe murya tana cewa yallabai abinci fa yana jiranka, a dinning, Bai tanka mata ba sai kokarin neman layin waya na ya keyi a lokacin sai dai wayan is switch off a lokacin Dan guntun tsuki yasake tare da fara neman layin malam tsoho a lokacin, Abinci fa yana dining nace maka Yallabai kada dare yayi, baka ci ba, Ina zuwa mana yace ba tare da ya dago kanshi daga abinda ya keyi ba, a lokacin, Sai ji su kayi ya fara cewa Hello malam barka da wuni yaya kuke, yakuma kaji da bakon ka, ? Jin sunan wanda ya ambata a wayan yasa ko wanin su kiran malam tsoho da sunan da suke kiran shi dashi wai ya ishe su, Anty Sadiya tafito jikinta saye da atamfan super wax mai ruwan brown colour yasha dinki mai aikin design din wuta a gaban rigan,, Ta zauna tare da yar makalalan sallama dauke a bakinta tana cewa ka dawo, Bai tankaba don waya ya keyi a lokacin saboda haka yake cewa a cikin waya, Nakiran nombanta ban samay taba yanzun nan ko watan baya kusa da itane Jin abinda yace yasa su gaba daya maida hankalin su gareshi saboda sun fahinci cewa akan mace yake zance, Malam tsoho ya ce mai na shiga gurin su yanzun nan da na shigo na samu sunyi barci ko tun dazun, Shidai, jaririn ne na samu idon shi biyu yana kallon kwan fitilla a sama,, Hmm kawai Yaya Abubakar ya iya cewa don jin may malam tsoho yace mai a lokacin, Ya tambaya da cewa, ita Meenatu babu abinda ke damun ta dai ko ? Don kasab anan kafinta tafi tana da likitan da ke dubata duk da dai acan ma sokoton sunce tana zuwa asibiti check up, Hakan yasa yazun ma da ta haihu nake son a duba lafiyan ta a gani idan babu matsala, Malam ya ce insha Allah gobe da safe za,a kai su a duba lafiyan su din kamar yadda ya dace, Gaba daya fuskokin su ya sauya izuwa mamaki don sambabu wace tai zaton cewa cikin jikin Meenatu ya isa haihuwa a lokacin Yayin da zukatan su ya shiga wani rudani a lokaci guda kowace da irin abinda take kiyastawa a cikin rayuwan ta, Yayin da hankali kwance maigidan yaci gaba da wayan shi batare da duban yanayin su ba, Jin call na shigo mashine a lokacin yasa shi yin sallama da malam tsoho wanda, ke ta bashi labari a qaya, Sai a lokacin da yake kokarin daukan kiran yaya Mustapha ne yake dan duban su yana cewa daidai face din Sadiya, Meenatu ta haihu yau dazun nan da marance aka bugo min, waya ana fada min, Bakin a tare Salawatu da Fatima gurin tambayan shi cewa mai ta haifa, Tankar baiji su ba yaci gaba da wayan shi da dan uwan shi inda a cikin wayan ne suka fahinci cewa Meenatu fa Da namiji ta haifa, Don sunji yana cewa dan uwa kagane Mustapha don Allah gobe a kaisu asibiti a tabbatar da cewa lafiyan ta da na yaron is normal, Sai kuma cewan da yayi zankiraka Mustapha zuwa anjima akwai abinda nake son yau din nan kai min insha Allah, Suna sallama da Yaya, Mustapha kiran yan uwa da abokan arziki ya fara shigowa daga wayan shi, Wanda haka yasa shi daukan lokaci mai tsawo yana waya da jama,a a lokacin, Sai da ya dan rarage Sadiya tana batun mikewa don ita har yanzu al,amarinta sai a hankali, Yake cewa, idan Ramatu ta fito sai ki fada mata cewa, an haifu don taji, tafadawa matar Lawal, da sauran mutane, Daga gurin da Fatima take zaune wani irin haushi da takaicin masoyin nata take ji yau watau saboda ya samu haihuwa shine zai mata haka Duk lokacin ta data bata a gurin girka mashi abinci sai ya share ta haka sai faman waya ya keyi abin sa, yana annashuwar an mashi haihuwa abin shi, Aikuwa yau zasu hadu don za ta gwada mai cewa ita fa mace ce maijan aji don bata daukan raini agaban kishiya ita Muryan shi taji ya na cewa tea nake son sha yau kawai bazan iya cin abinci ba, Da sauri a cikin mamaki Salawatu da tun dazun tai zaman suma a zaune ta dago kai ta dube shi a cikin mamakin jin yau ko abinci bazai iya ciba ,, Tirkashi, ashe a kwai magana ke nan a gidan nan don, dole ta mike tsaye tasan abinyi kafin taga takaici, Jaririn da aka haifa yau, yau shine har ya shiga ran maigidan haka tun ba akai ko ina ba baiga yaron ba, amma yake irin wanan dokin haka Wata kilama baby ba wani kyau gani gare shi ba yake irin wanan haukan haka, Kai amma dai abin da da mahaifi duk yadda yake zakaga ai baidamu ba aran shi,yana son abinshi hakana best solution shine, ita ma kawai ta turza ta samu ciki a gidan nan, Zaune take sai tunane take tayi kala kala a gurin don abin ya bala,in girgiza mata zuciya ace wai har Meenatu tai ciki ta haihu haka, ?
****** ********** ****** Acikin barci wanda ban san lokacin da ya kwashe ni ba nake jin muryan Yaya Mustapha sama,sama suna magana da Mama Dije, A hankali na bude idona sai nake jin muryan shi yana cewa ita Meenatu barci takeyi ne ? Tace ai dole tayi barcin gajiya yau Allah ya sauketa lafiya, zama da ciki ba wasa bane, Yace gashi ko Abubakar ya turo ni naiwa wanan yaron addu,a kamar yadda ya umurceni, A hankali na kara bude idona nace cikin muryan mai sanyi ina wuni Yaya, ya amsa da cewa kin tashi Meena, Barkan mu da arziki fa kuna dai lafiya ko bakya jin komai, na amsa a hankali da cewa Alhamdullahi yaya, Daidai lokacin da ake mika mashi dan yake cewa tare dan juyowa gurin da nake kwance yana ce min, Abubakar yace nazo nai ma yaron nan addu,a yau din nan kafin gobe hakan yasani shigowa yanzu, Dan lumshe ido nayi tare da cewa kai haba Yaya ni ina ruwana da zancen ku, Yayin da na juya na basu baya ida Yaya Mustapha ya fara yiwa yaron addu,a kamar haka, ( Huduban Bismillahi) Fatiha) Bismillahi Rahamanin Rahim, Allahumma,inni as, aluka Bissirin fatihatu , wafalalu, li Fatihatu wabarkatu Fatihatu, wama anzawah Fatihatu, wama unzillatu, Alaihin Fatihatu, Ataftaha Alayya, Hairun Dunya wa la Lahiratun Innaka ala, kulli,Shain Kadir,,,, Yana wanan adduan adaidai kunuwan dama na dan jaririn ta yadda nake iya jiyu shi daga gurin da nake a kwance, Yana idarwa ya mikawa Mama Dije yaron yana cewa Allah ya raya muna yashirya muna yasa albarka duniya da lahira Allah yasa dadin musulmi ne, Inajin Mama Dije tana cewa amin a lokacin da nima na karba da fadan amin din a cikin raina, Yace wa Mama Dije idan Allah ya kaimu gobe zan dawo insha Allahu akwai abinda zanyi mai, Yai muna sai da safe tare da dan taba barkwanci wa yan tsofin matan da ake wasan jika da su, Yana fita abinda yafara fado min arai shine rabuwan mu na karshe da Yaya Abubakar inda cikin rikicin mu nake ce mai idan ma har wani abu yake so ai mai ai kamata yayi ya umurci Yaya Mustapha ko ya Suleiman ko Ya Sa,adu duk diyan gidan mu ne kuma magidantane ba wai wani bare sabba ba can daban wai Aliyu, Ina ganin shine dalilin da yasa yau ya umurci yaya Mustapha da yazo yaiwa yaron wanan adduan da kan shi, Dan murmushi na sake a fuskana ina cewa, ai naka sai na gurin wuya don Aliyu da yake gani akwai inda bazai dace ace komai shi zai aiwatar ba akan mu, Ko ada can bayama da babu aure a tsakanin shi da Fatima balle yanzu da take zaman kishiya a gare mu, Don yasan cewa idan shi yaturo bazan yarda ba ya taba yaron nan irin yadda yake ganin take takena akan Aliyu,, A take naji wani irin son mijina ya shigeni lokaci guda badon komai sai don duk irin shaaran da zan bashi idan har yai naziri yaga cewa ta alheri ce to zai bi wanan shawaran, Gashi yau da kanshi ya umarci, Yaya Mustapha, dayazo yai wa dan shi huduba, Mutumin da da can baya babu ko ga maciji a tsakanin su saboda akidan iyayyen su da suke bi zakace ba kaka guda ta haifi iyayyen su ba, Ajiyan zuciya na sauke tare da yin hamdalla don ganin cewa wanan gaban dake a tsakanin iyayyen mu diyan su, sun fara kawar dashi, A haka har barci ya kwashe ni ban sani ba said ai kuma zuwa dare can sai barci ya kauracewa idona ,, Dole ina ganin Mama Dije wace taja dan jaririn a kusa da jikinta suna ta kwasan barci abinsu,,,
****** ********** ****** Muryan malam tsoho yadan fakal dani daga barcin da ya kwasheni da asubah, Naji yana cewa Mama Dije yaya dare ya kuka kwana tace lafiya lau malam babu matsalan komai, A raina nace, ai dole kice haka tunda ke kin samu barcin ki akalahe, babu ko farkawa, Wanka nayi tun da dan sauran duhu acewan Mama Dije wai a wanan lokacin yafi dadi, Bayan nafito na samu ankawo min kunu mai zafi a wani cup din silver sai suraci ya keyi, Mama ce mai cewa ki kafa kai da sauri ki shanye wanan kunun dukka Meenatu, Cikin sauri nadago kai na dubi kunun na dubeta ita ma wanan kunun mai yawa haka za,a ce wai na shaye shi dukka a cikina, Ina saka riga na zauna a bakin yar kujeran dakin na dauki cup din kamar yaddaMama Sa,a ta umurce ni na kafa kai don tace min wai ba,a sha da ludayi, don zai yi sanyi, Ina sha ina runtse idona tare da tausayin kaina da kaina gazafi ga dan yaji duk a bakina ina konewa, dole kuma nake daurewa ina ci gaba da sha, hakanan, Ina gama shan kunu sai ga Mama Abudauke da wani kwanan silver sabo ta shigo dakin, sai faman sannu da aiki ake mata, Tana cewa Mama Dije idan na gama ga miya nan wanda zan diga sha, Maganar Anty Amarya,ne ya fado min a rai na zancen miyan da tai min ida aka shigo dauke da kwanon tuwo again, Banda daman in mussa cewa na koshi dole ina kallo aka jawo plate aka zuba min a cikin shi , Ganin yadda ake ta zuba min abinci da yawa wai duk ni zanci ban san lokacin da nace don Allah abarshi haka wallahi ko yanzu a koshe nake,, Wanan dan abinci zaki ce kin koshi Meenat ai kawai bude ciki zakiyi ki ta zubawa,
ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL MUQADDIM,
Zaune suke gaba dayan su a dakin mahaifiyan su sai hira suke yi kowa da abinda yake fadi, Anty Safiya wace fitowan ta ke nan daga part din malam tsoho gurin mu, tazo ta samu yan uwanta a dakin mahaifiyan su, Nan ta shiga yabon irin kaman da jariri yayi da mahaifin shi take ran Mama Ladi ya baci da tsawa ta katse Safiya da cewa, To uwar yan tsurku kowa ya tai yagani babu wanda yace kallallahu sai ke fadi ba antambaye ki ba, Mama saboda kawai na fadin gaskiya ai don naga kaman su ya baci ne da yaya Abubakar shi nassa na fadi,, Idon ki dai ya gwada maki hakan amma in ba ke ba nikan banji wanda yace hakana ba, Sai babban yarta ke cewa aiko gaskiyan Safiya na walle kamar su yai yawa da mai sunan malam, Dama ba wani fada ke ga yaya maimuna ba gurin mama kasancewar ta yar fari kuma bata da komai a kauye take aure ita, Walle kada in karajin wanga zance har wani ya jiya yaji dadin fadin haka agaban su, To ke Innan mu hallan mi ki ka nufi wai,? Naga dai wanga Da dan Yaya Abubakar na shi yai ciki nai to mi yakawo wani zancen cewa abar danganta shi da shiya ? Ke walle a hir din ki ban son maganar banza maganar wofi ace maku banda hankalina , Meenatu wace ar zaune sokoto shiko shina can Abuja, Salati anty Safiya tasa tare da saurin duban hanyan shigowa part din sai kuma ta leka part din Mama Sa,a taji ko tana kusa, Cikin tausa murya tace Innan mu walle bari bari ka da wagga magana tafita ko nan da can wallahi, Don wanga zance na kawo muna bacin rai gaba dayan mu don ko shi uban Dan wallahi tallahi ana jinku dashi Inna, Jinin ki ? jinikiza wa sheri irin haka acikin babban gida irin wanga walle abar zancen ga anan tun rayuka basu baci ba, Za tai magana Anty Mariya ta katse da cewa Innan mu na fada maki tun wuri in rai ya baci hankali ka bido shi, Bacin rai yasa ki barna wa jiniki suna ga banza cikin dubun dubada har gari ya dauka dan Allah dai Inna ki bari kawai, Ganin duk yaranta basu goyi bayanta ba kuma sun bata rashin gaskiya yasa ta yin shiru, Anty mariya tace ai naso in kawo shi Dije tace min wai malam yace kada a fita dashi ko ina sai anyi suna, Hakan ya kara tunzura Mama ta fara yin sababi da jidalin cewa ita da dan ta amma ana gwada mata fin karfi ga al,amarin shi, Duk wani abin mai sunan malam sai ai ta shige mata gaba a kan shi ita yanzu ta gaji da hakkurin hakan bazata kara yarda ba, Anty Samira tashigo goye da goyon ta a baya tana cewa ashe duk kun rigani ganin Baby kai amma wanan yaro kamar Yaya Abubakar yai kaki ke har yan yatsun shi walle duk na ubanai na, Wani irin tubure fusks Mama Ladi tayi don inda tana iyawa da ta ci masu mutunci don kada su kara, fadin haka a gaban ta, Kafin ai wani zance sai ga wayan Yaya Abubakar a wayan Anty Safiya cikin murna ta dauka tana cewa Baban jego Baban jego hoo, Ya ce hmm Safiya ya kuke ya gida da jama,a tace duk lafita kalau yayana, Yace dama na kiraki ne ince duk abinda ya kamata ayi yadda akeyi a al,ada sai ki fada min munyi magana da Mustapha jiya da dare yace yau idan kin shigo zai gan ki , kuyi magana akai,, Ta ce yanzu haka ma ina cikin gidan mu gamunan gaba dayan mu har Innan mu zaune, Yace OK kina kusa da Mama ke nan ko ta ce gata yayin da take mikawa Mama Ladi waya a hannun ta, Ta karba tare da wani yatsune fuska tankar Abubakar din yana a gaban ta, Sama, sama suka gaisa dashi batare da wani dogon magana ba, Ganin cewa ita batai mai murna ba ya sa,shi gane cewa, batai farin ciki ba da wanan haihuwan da akai mai, Yace Mama barkan mu fa da haihuwan Meenatu Allah ya raya yasa dadin musulmi ne, Amin tace cikin wani irin murya kasa kasa babu nuna farin ciki a tare da ita,, Yace abawa Safiya waya bayan ya gaisa da duk kan yan uwan shi sun mashi barka abinda ya wanke mai bacin ran mahaifiyar shi ke nan tun da yaji yan uwan shi nata murna suna mai raha cikin jin dadi da so da kauna, irin ta yan uwan taka, Bayan ta karbi wayan ne yake ce mata duk shawaran da ya dace suyi kafin taga yaya Mustapha din, Bayan ta kashe waya take kara masu bayinin yadda sukayi da yaya Abubakar akan zancen abinda ya kamata, su yi,, Anty mariya ce ta fara magana da cewa, gaskiya icce ya kamata ace ankawo tun da safe tunda shina jego, Zubur mama tace wani irin Ice kuma ba gidana ba dukka sai ankawo wani ice can kuma , Har suna hada baki wurin cewa haba Mama ko gida na fa ai hakin shina ya kawo ice, Safiya tace sai gero da kayan yaji ko, da sukari da kayan shayi tunda yana da halin su, Samira wace ke tsaye tana jijiga dan ta dake goye a baya yana mutseniya tace sai abin kauri ko in anyi kwana uku, Aiko acikin masifa Mama tayo kanta da fada tana cewa tunda baku san ciwon kanku ba shine har zakuyi irin wanan lissafin haka ga dan uwan ku, Inna mu amma naga ko mu munka haihu ana kawo maki irin wagga abubuwan da munka lissafa ko, Tace don kun haihu ankawo min fa ita ba gida bana dole na ankace sai anyi su, Mafarin akashe masu jiki su mi aggare su mi zasu kawo wa iya ka cewa zasuyi aiduk gidana ba sai anyi komai ba, , Ikon Allah inji Ànty maimuna wace duk zancen da akeyi bata ce komai ba don tasan bata da wani power gurin mahaifiyan nasu tun da bata da komai ita,, Tace haba inna wanga abu fa duk yiwa kaine da Meenatu dashi mai sunan malam duk gudana ai ko ? Haba ina wuta ta saka boyar
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣4⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL MUQADDIM,
Ina mai baku hakkurin rashin jina kwana biyu da bakuyi ba wanan yafarune ga yan matsalolin rayuwa da fatan za ai min afuwan kamar yadda kuka saba,,, Wanan cigaban labarin danaturo guntunshi ne shekaran jiya bissa ga kuskure,