Tarko complete novel - Chapter 79
Tarko complete novel Chapter 79: Tarko complete novel Chapter 79. Zaune suke gaba dayan su a dakin mahaifiyan su sai hira suke yi kowa da abinda yake fadi,…
3,809 words
Zaune suke gaba dayan su a dakin mahaifiyan su sai hira suke yi kowa da abinda yake fadi, Anty Safiya wace fitowan ta ke nan daga part din malam tsoho gurin mu, tazo ta samu yan uwanta a dakin mahaifiyan su, Nan ta shiga yabon irin kaman da jariri yayi da mahaifin shi take ran Mama Ladi ya baci da tsawa ta katse Safiya da cewa, To uwar yan tsurku kowa ya tai yagani babu wanda yace kallallahu sai ke fadi ba antambaye ki ba, Mama saboda kawai na fadin gaskiya ai don naga kaman su ya baci ne da yaya Abubakar shi nassa na fadi,, Idon ki dai ya gwada maki hakan amma in ba ke ba nikan banji wanda yace hakana ba, Sai babban yarta ke cewa aiko gaskiyan Safiya na walle kamar su yai yawa da mai sunan malam, Dama ba wani fada ke ga yaya maimuna ba gurin mama kasancewar ta yar fari kuma bata da komai a kauye take aure ita, Walle kada in karajin wanga zance har wani ya jiya yaji dadin fadin haka agaban su, To ke Innan mu hallan mi ki ka nufi wai,? Naga dai wanga Da dan Yaya Abubakar na shi yai ciki nai to mi yakawo wani zancen cewa abar danganta shi da shiya ? Ke walle a hir din ki ban son maganar banza maganar wofi ace maku banda hankalina , Meenatu wace ar zaune sokoto shiko shina can Abuja, Salati anty Safiya tasa tare da saurin duban hanyan shigowa part din sai kuma ta leka part din Mama Sa,a taji ko tana kusa, Cikin tausa murya tace Innan mu walle bari bari ka da wagga magana tafita ko nan da can wallahi, Don wanga zance na kawo muna bacin rai gaba dayan mu don ko shi uban Dan wallahi tallahi ana jinku dashi Inna, Jinin ki ? jinikiza wa sheri irin haka acikin babban gida irin wanga walle abar zancen ga anan tun rayuka basu baci ba, Za tai magana Anty Mariya ta katse da cewa Innan mu na fada maki tun wuri in rai ya baci hankali ka bido shi, Bacin rai yasa ki barna wa jiniki suna ga banza cikin dubun dubada har gari ya dauka dan Allah dai Inna ki bari kawai, Ganin duk yaranta basu goyi bayanta ba kuma sun bata rashin gaskiya yasa ta yin shiru, Anty mariya tace ai naso in kawo shi Dije tace min wai malam yace kada a fita dashi ko ina sai anyi suna, Hakan ya kara tunzura Mama ta fara yin sababi da jidalin cewa ita da dan ta amma ana gwada mata fin karfi ga al,amarin shi, Duk wani abin mai sunan malam sai ai ta shige mata gaba a kan shi ita yanzu ta gaji da hakkurin hakan bazata kara yarda ba, Anty Samira tashigo goye da goyon ta a baya tana cewa ashe duk kun rigani ganin Baby kai amma wanan yaro kamar Yaya Abubakar yai kaki ke har yan yatsun shi walle duk na ubanai na, Wani irin tubure fusks Mama Ladi tayi don inda tana iyawa da ta ci masu mutunci don kada su kara, fadin haka a gaban ta, Kafin ai wani zance sai ga wayan Yaya Abubakar a wayan Anty Safiya cikin murna ta dauka tana cewa Baban jego Baban jego hoo, Ya ce hmm Safiya ya kuke ya gida da jama,a tace duk lafita kalau yayana, Yace dama na kiraki ne ince duk abinda ya kamata ayi yadda akeyi a al,ada sai ki fada min munyi magana da Mustapha jiya da dare yace yau idan kin shigo zai gan ki , kuyi magana akai,, Ta ce yanzu haka ma ina cikin gidan mu gamunan gaba dayan mu har Innan mu zaune, Yace OK kina kusa da Mama ke nan ko ta ce gata yayin da take mikawa Mama Ladi waya a hannun ta, Ta karba tare da wani yatsune fuska tankar Abubakar din yana a gaban ta, Sama, sama suka gaisa dashi batare da wani dogon magana ba, Ganin cewa ita batai mai murna ba ya sa,shi gane cewa, batai farin ciki ba da wanan haihuwan da akai mai, Yace Mama barkan mu fa da haihuwan Meenatu Allah ya raya yasa dadin musulmi ne, Amin tace cikin wani irin murya kasa kasa babu nuna farin ciki a tare da ita,, Yace abawa Safiya waya bayan ya gaisa da duk kan yan uwan shi sun mashi barka abinda ya wanke mai bacin ran mahaifiyar shi ke nan tun da yaji yan uwan shi nata murna suna mai raha cikin jin dadi da so da kauna, irin ta yan uwan taka, Bayan ta karbi wayan ne yake ce mata duk shawaran da ya dace suyi kafin taga yaya Mustapha din, Bayan ta kashe waya take kara masu bayinin yadda sukayi da yaya Abubakar akan zancen abinda ya kamata, su yi,, Anty mariya ce ta fara magana da cewa, gaskiya icce ya kamata ace ankawo tun da safe tunda shina jego, Zubur mama tace wani irin Ice kuma ba gidana ba dukka sai ankawo wani ice can kuma , Har suna hada baki wurin cewa haba Mama ko gida na fa ai hakin shina ya kawo ice, Safiya tace sai gero da kayan yaji ko, da sukari da kayan shayi tunda yana da halin su, Samira wace ke tsaye tana jijiga dan ta dake goye a baya yana mutseniya tace sai abin kauri ko in anyi kwana uku, Aiko acikin masifa Mama tayo kanta da fada tana cewa tunda baku san ciwon kanku ba shine har zakuyi irin wanan lissafin haka ga dan uwan ku, Inna mu amma naga ko mu munka haihu ana kawo maki irin wagga abubuwan da munka lissafa ko, Tace don kun haihu ankawo min fa ita ba gida bana dole na ankace sai anyi su, Mafarin akashe masu jiki su mi aggare su mi zasu kawo wa iya ka cewa zasuyi aiduk gidana ba sai anyi komai ba, , Ikon Allah inji Ànty maimuna wace duk zancen da akeyi bata ce komai ba don tasan bata da wani power gurin mahaifiyan nasu tun da bata da komai ita,, Tace haba inna wanga abu fa duk yiwa kaine da Meenatu dashi mai sunan malam duk gudana ai ko ? Haba ina wuta Mama ta saka wanan boyar Allah, da ta fadi haka cewa duk guda muke nida yayana, Nan ta shiga sake magana a cikin masifa da jidali tana wa diyan ta cewa ita fa bata yarda azo a kashe, ma wa yan nan matsiyatan mutanen kudi Su zo komai ba su kashe, wa mutane ba don tun yanzu banga komai da su ka aje wanda zasu fitan wa mutane kunya ta na su bangaren, Mama duk yadda an,kai muna ko ita sai an mata tunda duk guda na muke Shin wai wa zai bada kudin da za ai hidiman ba uban Dan na ba, Yaya Abubakar zai bayar, kuma shina ya haifi dan shi, don ya kashe ma danshi kudi, Don Allah ku, komai kada ku rage ga duk abinda yaje so ai ma iyalin shi, daga haka, ta sa kai zuwa waje abinta tana dan jijiga goyon ta Samirace mai wanan maganan, To issasa ai sai ki taho kiyi wadda kika so tunda ubanki na ya bada kudin Daga ida take waje tace a,a wallah uba Da dai na yaba da kudin ai mai kashin kunya, Aiko Mama tashiga surfa ma Samira zagin fitan arziki har sai da Safiya ta dagawa Samira hannu da cewa tayi shiru, Daga haka tabar part din mahaifiyar nasu zuwa part din mu, cikin bacin rai,
****** ********** ****** Malam tsoho ne ya shigo dakin Mama Dije inda nake jego, daga gurin da nake a kwance ga kaskon garwashin wuta a gefe guda sai dumama dakin yakeyi, Ina ganin shi nai saurin mikewa zaune da ga kwanciyar da nayi, ina cewa sannu malam, Cikin murmushi yake ce min Meenatu kun tashi lafiya yaya dare ina fatan babu matsalan komai ko ? Kai ya na kasa cikin dan murmushi ina wasa da yatsun hannu na nake cewa ba komai malam ya dawai niya damu, Yace waya fada maki ina dawainiya dake bayan kin ce baki son tsoho, Dariya mukayi gaba daya daki sai Mama Dije ke cewa wai har yanzu baka bar wa takwaran naka ba yace yanzu kan ai dole na hakkuri su je su karata can birni taraiya tare, Aka kara sa dariya adakin, alaman ganin zai zauna ga yar kujeran dakin yasa, ni, saurin cewa bari a gyara maka guri mana malam ya daga min hannu cikin dakatarwa yana cewa, nan ma ai ya isa Meenatu, Yana zama yacewa matar shi miko min yaron nan Dije da sauri ta gyara shi cikin dan farin showel da yake ta miko mashi shi, Idon ya kura,wa yaro zakace ko kallon shi ya ke yi amna idan ka lura da kyau, addu,a yake maron, tsayin wani lokaci ya dago kai yana kallo na tare da cewa wanan yaron tankar lokacin da mahaifin shi yake kaman shi sak, Murmushi kawai nadan yi ba tare da na ce wani abuba sai Mama Dije ce ke cewa ai da shi kowa ke cewa yai kama amma ance Ladi tace wai sam abar fadan haka ? Da sauri na dago kaina na dubi Mama Dije a cikin mamaki don jin Mama Ladi har da gudan jinin ta tana bakin ciki kuma, Muryan malam ne ke cewa ai al,amari Ladi sai Allah kawai don abin nata bana kai sake bane, Mama Dije tacd hassada ne kawai da bakin ciki mutum tun yana sheri har yai wa kan shi yanzu ai ita ake ji don kowa ya dawo daga rakiyan ta, Murmushi naga malam yayi tare da kokarin mikewa tsaye yana fuskantar gurin da nake zauns yace, Ameenatu zan sa akawo maki wani ruwan rubutu ki shanye shigaba daya Allah ya sa agama wanka lafiya , A hankali na, amsa mashi da cewa Ameen yaci gaba da cewa na tura Sahabi ya debo ganyen da zasuyi wanka dashi saboda yanzu ba a samun shi nan kusa don duk anyi gine gine a guraren, Bayan fitan malam ne Mama Dije ke cewa ai dole na Meenatu kuga irin wanga abu don miyagu (muggai) sun,yi yawa yanzu, Tace cikin ma dai ai Allah ne yanufa ki samu inba,shiba irin mugun daurin da macuciyar ga tayi aida ba hakan ba, Da sauri na dago kaina ina cewa wacece macuciya kuma da har zata hana ai abinda Allah ya tashiyi, Tace kaiyya Meenatu ke yarinyace baki san komai ba sai gaba zaki gane ke dai zancen ki, dutse da kikace Allah yanufa sai ko anyi komai wahala nai, Amma baku san irin takai din da dan tsohon ga yasha ba kafin a kai ga hakan da sannu dai ai gaskiya zai baiyyana kowa ya sani, Nace kai Mama Dije don Alkah bari qagga camfin haka wani ya isa yai wani abu batare da sani Allah ba na, Tace to ko mijin ki da add, rikeken dan izala yanzu dole ya zubar da wanan kaihin nashi ya san gaskiya don ya gane cewa da kulli tare da shi, Murmushi nayi mata ba,tare da nai mata wani magana ba again don nasan ba yarda zatayi da ni ba, Kofan shigowa dakin ta naga ta dan leka a hankali kamar mai son dubawa ko akwai mai shigowa daga waje, Tace con n tausa muryan ta uwar kishiyar ki ta saku a gaba ko wanan yaron ma da kika haifa kokarin ganin bayan sa takeyi, Ai shiyasa kikaga malam da mijin ki duk hankalin su a tashe yake, saboda su san abin yi, Amma insha Allahu bazata iya komai dashi ba don Allah ba zai bata iko ba, akan hakan, Hajja ai takai macuci don ita abin nata bai tsaya ga yart ba kawai har saida ta hada da diyan mutane, Yanzu kinga badon Allah yasa malam masanin bane acikin alkur,ani maigirma da sai kawai taita barna acikin ku ba,a gane cewa itace, Don kinga kowa yasan da cewa ta na da Dodon sihiri a gidan ta wanda ke kawo mata kudi, kashi, Sai dai abin takaici kuma ba kashin kudin takeyi ba don kudin sihirine basu ciyuwa mata yadda take so, tunda bata hanyar halas aka samay su ba,, Mama daki dauke shi ku fita waje sai na dan kwanta da sauri tace min rufamin asiri yar nan aiko nan da kofan daki baza mu fita dashi ba sai anyi suna saboda dokan malam, Zataci gaba da magana sai ga Samira tayi sallama, dakin inda fuskanta kawai zai nunawa mutum tana a cikin bacin rai, Ganin Samira bai sa Mama Dije ta daina maganar da take yi ba sai cewa tayi ai yanzu saura kiris ya rage asirinta ya tonu tunda mutanen shiya gaba daya sunyi meeting a kanta, Samira wace shigowanta ke nan a lokacin take cewa ita waye saura kirs asirinta ya tonuwai ? Don a zaton ta da mahaifiyarta ake zancd don tana tsan manin aji irin surutun da take sakewa akan zancen haihuwan, Amma sai Dije tace mata, Hajja mana bakar muguwa yar lahani, Samira ta, ce wanan ai sunan ta yai kauri a gari don yanzu ko wani shiya cikin gari sai labarinta akai, tatara dukiya kamar ya kashe ta, A hankali takai hannuwanta saman fuskan dan jaririn da ke kwance a gefen gado yana barci, Ta,ce sai faman barci, ake tayi yayin da ta juta gurin da Mama Dije take tana cewa, yana bari ayi barci da dare ko, Mama Dije tace gaskiya baida matsala duk da dai jiya jiyane haihuwan amma gaskiya baida fitina sam, A hankali takai zaune bakin gadon tana cewa Meenat yanzu kan kin san duniya don duk macen da bata haihuba bata san maynene duniya ba, Murmushi kawai nayi tare da dan kokarin gyara zamana, don itama taji dadin zama daga inda take zaune a gefena, A hankali muka soma hira da ita wanda duk yawancin hiran namu akan zance haihuwan tane don ni ban yarda na fadi komai ba akai don na san yanzu matsayi biyu take dashi a gurina, Bawai lalai ne tasan komai nawa ba kamar da can baya da muke zumuncin mu, da ita, Dan Jaririn wanda ke kwance can bayan yai motsi koda wasa ban juya don na kalle shi ba badon komai ba sai don irin karamin da naga ga Mama Dije da Anty Samira duk hankalin su gaba daya ya koma a gare shi, A hankali yaron ya fara dan yi kuka wanda, Mama Dije ke bashi ruwan zamzam, a hankali tare da kokarin lasa mai garin dabino da zuma a bankin shi a hankali,, Sai dan wanan kukan ba kamar na wanda yayi da safe ba ne yanzu kan a hankali yake kara sautin muryan shi, Muryan Mama Dije ce naji tana cewa Meenatu ki gyara a bashi nono yanzu kan, Gabana ya fadi damm don jin may tace don sam na mance cewa yanzu na zama feeding Mama, Jin shirun da Mama Dije tayi don gani ko gezau ban yiba daga ida nake kwanci ba bawani alaman motsin zan gyara in bada nono a lokacin, Sai tsala ihu yaron ke faman yi a lokacin Anty Samira tace gyara mana Meenatu ki bashi nono ya sha, Na gyara juya masu baya tankar banji su ba may yasa haka Meena inji Anty Samira a cikin yar hasala take magana, Wanan ai zalunci ne a ce yaro na son abincin sa amma ki hana mashi ana magana kinyi wani biris da mutane,, don kada ki shayar dashi, Mama Abu ce ta shigo dakin dauke da ruwan dumi a cikin wani roba mai fadi, Tana cewa zauna da kyau a wanke nonon ko ? Ya fara sha ai yayi kokari hakana, Binta nayi da ido ina kallon ta sai naga gadangadan ta haroni da roban ruwan daje hannun ta, Yaron ya rike a hannun Dije wace ke tsaye a kaina tana dan jijiga shi a hankali, Ita ko Ànty Samira sai cewa take kaji muguwa zata bar muna yaro da yunwa ya tsulance gashi tubarkallah masha Allah, Al,ajabi gami da mamakine suka rufeni a lokaci guda duk da ina kokarin bude zip din rigana da ya matse ni don naji dadin bude nonon, Na kasa furta ko mai sai mamakin Anty Samira nakeyi wace ta nuna cewa jaririn ne dan bangarenta har ta manta da nawa bangaren yadda muke da ita, Ban fargaba sai ji nayi Mama Abu ta sa hannuwa ta ta jawo nonuwa na ta fara wanke wa, A tsorace na juyo da sauri daga kallon mamakin da nake ma Anty Samira din, Nonon nawa sun dan wani canza kama a cikin dan kwana gudan da mukayi sun wani fara cikowa, fan A hankali ta miko min yaron tare da gyara mai kwanciya a saman cinyana tana mai kama mashi nonon yadda zaiji dadin sha da kyau, Jan farko da yayi ban san lokacin da na tsala ihu ba don zafin da naji dariyan keta anty Samira ta sake min tana cewa, Yaro ka zuki abinka da kyau Allah ya sa kasha masu albarka duk da dai kayi wa yayana ritaya a gurin hutawan shi, Wani irin harara na kara sake ma Antyn nawa wace yau ta rikide min ta koma dangin miji,, Na bude baki da zuman nai magana nakara jin wani irin dankan nonon da yaron yayi ai ban san lokacin da hawaye suka silalomin a idona ba saboda zafi, da azaban da naji, A daidai wanan lokacin ne kuma wayata dake daga gefen filona yai kara, Har kiran ya katse ban daukaba muna ta faman daga da shan nono da su Dije,da mama Abu, Shigowan wani kirane again hakan yasa Anty Samira tadauki wayan don taga mai kirana, Yaya Love, tagani hakan yasa ta gane cewa yaya Abubakar ne a layin ke kirana, don haka sai ta dauka don su gaisai, Tana cewa salamu alaikum yana cewa Mama Baby ina nawa ruwan zafin yake, Tace yaya ina wuni Samirata Meenatu ga tanan ana bawa yaro nono ne shiyassa, Cikin dan dakewan murya yace OK Samira kuna lafiya ko ya duke, Tace Alhamdullahi duk lafiya lau mu ke yaya, yaya su Anty sadiya ya amsa atakaice da cewa lafiya, tace mai barin baka Meenatu din, A hankali ta karamin waya a kunnuwa na ina jin shi ya sauke ajiyan zuciya, Abin sai yazama min biyu a lokaci guda zafin shan nono da nake fuskan ta ga kuma muryan yaya Abubakar da nake ji, A hankali naji ya kira sunana cikin wani irin shauki da kuma kulawa, inda na amsa mashi da naam, Ya kuke kuna dai lafiya ko ? Nace lafiya a takaice tare da murda baki don zafin da nake ji na kama nonon, I hope ba wani matsala a tare da ku ko don na kira dazun wayan tana a rufe lokacin, Kan na amsa mai maganar shi yaron wanda yaji dadin jan nono yakara tsuke bakin shi gurin shan nono, Ai ban san lokacin da nai wanikaraba sai na saka kuka kawai hankan yasa har nai cilli da wayan gefe guda, Nan yake jin irin takai din da mukeyi da matan kakan namu alokacin don nace bazan karaba yaro nono sai hawaye nakeyi, don zafin wahala dama can ni matsoraciya ce,ban son abinda ya taba min lafiyan jikina, Duk draman da mukeyi a kunnuwan yaya Abubakar mukeyin shi tsaba, Kashe wayan yayi a bangaren shi tare da jin haushin kin ba yaro nonon da yaji ina yi, a zaton shi da gangan ne nake hakan, Anty Amarya ce ya kira, yana mata korafi wai saboda kawai akwai dan matsala a tsakanin mu da shi shine nace bazan bawa yaro nono ba ya sha, Ita kuma rayuwan ta ya baci ta bugo min waya a hasale tana fada cewa may yaro yai man da zan dauki fansa a kanshi, Shiru nayi ina sauraren ta hakan yasa jikin ta yin sanyi ni ko sai mamaki abinda take fadi nakeyi, Sai da na bari ta idar nake cewa Anty shi ya fada maki hakan, Tace kwarai kuwa, don yanzu ina kitchen ya kirani yana sheda min abinda ke faruwa, Nan nake bata labarin abinda yafaru har yake zargin hakan sai take tambayana to dama akwai wani abu a tsakanin ki da shi ne can baya, Boyewa mata nayi nace babu komai anty abinda kawai akayi ke nan, Allah ya kyauta tace tare da, tambayan lafiyan mu cikin kulawa, da damuwa, Nan dai mu ka dan yi hira sama sama da ita, saboda tace a kitchen take a lokacin tana aiki, inda tai min alkawarin idan ta rarage aikin da takeyi zata kira ni don a kwai maganan da take son muyi akai, Don haka muna gama magana da ita na sake wani irin ajiyan zuciya tare da kokarin kai kaina saman filo don na kwanta da kyau, inji dadin nazari, Muryan Mama Dije ce ke cewa kin kwanta ne da kin tashi kin sha kunun kanwa da aka dama maki dayani, Ba musu duk da ban so ba haka na mike zaune ina kokarin saukowa saman, gado don na zauna a kasa,saboda nasha kunun, Yayi Kore yayi kyau sai, kamshin kayan yaji ke shi daga cikin shi yayin da take dan motsawa, Cikke a wani cup ta turo min a gabana tana cewa yi ki sauri ki shanye kafin yai sanyi, Ba musu, nadauka nafara kaiwa a baki na da sauri na cire cup din daga bakin saboda mugun zafin da kunun yayi a lokacin ga yaji yana cin harshe, Dije wace ban san ta na tsaye tana kallona ba tai saurin cewa, yaya akayi ne Meenatu, ki daure ki, shanye da sauri don Allah dai, Na daga kai na ina cewa acikin dan bata fuska akwai zafine fa sosai Dije, Baki bude tace a, Meenatu dama mai sanyi kike son sha ke ? ba mai zafi ba, Badon naso ba nadauka acikin bata rai ina dan kurbawa a hankali a hankali, Yayin da nake ji tankar harshe na duk ya sale saboda zugin da yake min, Sai wani irin zuba ke tsiyayo min tun daga cikin kaina har zuwa, duk wani sassan jikina,, Sai kokarin gogewa na keyi a hannuwa saboda irin yadda nake jin zafi yana fita min daga jikina Shigowan kaunata a dakin taga irin yadda nake ta yarfan zufa wani na tsiyayowa, Tace Anty Meenat wanan irin zufan haka kamar kin shiga oven haka, Gurin gado ta isa ta zauna ana dan wasa da kumatun baby dake barci abin shi kamar nace tabari kada ya farka saboda ina tsoron ya tashi yace zai sha nono, Niko yanzu in akwai a binda nake tsoro ko gudu shine, ya farka daga barci yace kuma nono, Ai ban kai ga karshen tunane na ba sai kawai na ga yadan fara motsi da kafan shi a hankali alaman yana son tashi daga barcin,