Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 80

Tarko complete novel - Chapter 80

Tarko complete novel Chapter 80: Tarko complete novel Chapter 80. ****** ********** ****** Abin duniya ya taru yai ma ko wacen su yawa zuwa yanzu don sam…

2,926 words

****** ********** ****** Abin duniya ya taru yai ma ko wacen su yawa zuwa yanzu don sam basu gane kan maigidan ba, Don ko suna zaune ne zakaji ya buga waya yana cewa idan sun gaisa da mutun ko cikin hausa ko turanci yana cewa wife din shi ta haihu ya samu baby boy, Sai kaji ana mai murna yana wani irin kwasan dariyan jin dadi afili ba tare da ya iya boye farin cikin shi ba, Yau, ma irin haka ne ke faruwa don suna daga gefe a zaune suna sauraren irin yadda yake kwasan dariya da wani abokin shi da suke wayan, Daga gurin da Salawatu take zaune tana faman dakila wayan ta sai dai zuciyar tankar ya fashe a lokacin don takaici, Fatima wace ta hankal ta da irin yadda Salawatu ke cika tana batsewa a lokacin sai tai kokarin controlling din nata fushin, Cikin iya kissan tsofin mata tace mai bayan taga ya gama wayan wai, Sweet Bukar ya masu jegone suna lafiya ko ? Cike da kwarewa a fanin kissa da shagwaba ta fadi wanan maganan, Da sauri salawatu ta dago kai a hankali tana mata kallon mamaki, Cikin murmushi da jin dadi ya ke ce, mata, lafiya kalau suke wallahi munyi waya da su bada dewa ba Tawani ce Allah sarki tana can da wanan zafin tana fama da ruwan zafi don tsaron lafiya, Wanan zancen natane yashi dan lumshe idon shi saboda tunawan da yayi da irin artabun da akayi dani gurin ba wa yaro nono, Can cikin cikin Fatima wani irin takaicin shi taji don irin yadda yake nuna jin dadin shi a fili, A ran ta tace anya wanan Meenatun batai min mugun tazara ba fiye da yadda nake zato, Kai gaskiya dole ne na kira mama ta don ta san abinyi kafin na makara, Sa kuma a fili tadan kakaro murmushi tana ci gaba da bugun cikin shi da cewa, Amma dai nasan cewa yanzu acan za ai duk wani program muba zamu samu ganiba, kenan muna nan,,,,

, ZEEE MAKAWA YELWA,

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣5⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL MUAKHKHIR

Gwagona Habbi ta iso washegari wace saukan ta rabi tana tare dani rabi kuma suna tare da mahaifana a na ta yan sha war warin yadda za a kayya, Yaran Mama Ladi irin su Anty Mariya da Anty maimuna wace tun haihuwana da safe ta iso gidan, Kullun a gida suke wuni ana ta aikin saka ido da kuma kullawa da warwarewa, akan abin yi kamar yadda ake yi idan an haihu, Duk yawan masifan Mama bai hana a aiwatar da abinda akeyi a bisa ga al,ada ba , Don ko da mama tace kada ayi abu kaza idan Anty Safiya tazo sai ta lalaba ta fadawa Baba sai ya shigo a tsakar part din Mama yake tsayawa da farko ya fara cewa , Bayan duk sunyi mashi sannu da zuwa da kuma gaishe da jama,a, Sai yaje cewa Safiya wai ko ankai kayan wanke fitsar a gurin masu jego, Yana nufin su Clean da sabulu da icce, da kayan yaji da gero Take fuskan Mama ya matse don bata so hakan ba sam saboda tasan cewa magana ce kawai ya kawo shi, Anty Safiya wace dama plan suka hada da Baba tafito daga daki tana daura dan kwali tana fadin Baba shine yanzu muke kokarin hadawa mukai, Yace idan an hada sai ku kirani na gani, ko mama bata ce komai ba sai wani bata fuska da tayi ta wani hade rai kamar ra kurma ihu, Sai bayan wucewar shi tace ai shina ya kamata yayi su tunda haihuwan fari ne dan shi yayi, Sai Anty maimuna tace a,a to tunda Allah ya hutar da shi har 'Dan shi ya samu halin da zaiwa kan shi may zai sa shi kuma wahal da rayuwan shi, yanzu, Takaicin zancen ta bai bar Mama tace komai ba saboda wani irin takaicin da take ji a rayuwan ta, Mama tana gani a gaban ta a ka hada kayan Kauri daga dangin kayan yaji buhun gero, sabulun wanki, da su omo clean, Sai kan shanu da kafafun shi, chew gun da kwalayen Sweets, Tsaye take sai masifa da take tun tanayi a zuciyar ta har ta fara a fili, tana cewa wanan ai rashin sanin ciwon kai ne, Mutanen da ko alaman yin nasu kaurin baku gani ba shine ku zaku kwashi kaya haka kukai masu indai zurian su Fuldeni ne aikuwa kuna da shan kunya don dai ko kwara basu da niyar yi su, Baba Buhari wanda ke tsaye yana jiran yaga fitan kayan daga part din Mama Wanda ya jagula mata lissafin ta, akan abinda ta shirya Don da ita nufin ta duk ta zabge kayan ta mika dan kadan kawai, Niki, niki a ka kai wanan kayan part din Baba Hamza wanda yake madaurin aure na, saboda kara, Jama,a sai farin ciki da sa albarka su keyi amma sai Baba Hamza yace a mayar da kayan a part din Baba Musa wanda yake gaba dashi don girmamawa, Kafin wani lokaci zance har makwabtan gidan mu ya kai don an fara shigowa kallon kayan kauri, Sam Mama Ladi bata san da cewa za,a kawo komai daga fanin iyayye na ba, Saboda irin yadda taga babu wani shiri da akeyi daga part din mahaifan nawa, Sai bayan sallah la,asar ne aka shigo da kulolin kunun kanwa da aka dama daga can gidan wan mahaifiyana, dake uguwar Badariya, bayan Abdullahi Fodio, Kula biyu na kunun kawa da sugar a cikin wani plastic bucket fari mai marfi, Sai kamshin kayan yaji ke tashi daga cikin kuloli, da kuma ruwan zubawa na sabon dakan garin gero abin gwanin ban sha,awa, Haba take kuma sai guri ya kara rudewa aka shiga rabo ana aikawa makwabta, da yan uwa da abokan arziki, Mama Ladi sai kuma aka fara dan kamay kamay tsegumi tana cewa shi kunnun ma saboda iya kisisina baza,a dama shi nan ba sai ankai, har wani uguwa, yi nai, Anty Maimuna tace hey Innar mu badai har sunyi sun kawo ba to may ya rage kuma don Allah,,, Tace naga na Samira cewa kikayi baza,a dama masu su sha banza ba, duk sa Samira ta sai geron ta har kwano, ashirin, Mama Ladi tace cikin masifa wai shin ke da kike wanga zance kina wani tare magana kada a fadi nawa kin ka kawo, Murmushi kawai Anty maimuna tayi don inda sabo ta saba da irin gorin mahaifiyar nata yanzu,

****** ********** ****** Sosai yake ta hada hadan hada komai da ya kamata yayi ta fannin shi, Batare da iyalin gidan shi sun san may yake shiryawa ba, a zahiri, don Hajiya Jummai Dubai ta riga da ta hado mai komai kamar yadda ya bukata, Ganin bai wani shirin akan bukin yasa uwar iya, bugun ciki kokarin bugun cikin shi da tambayar bata ga fa yana wani shiri a kan sunan dake tafe ba, ko da yake ku yan dangi ne kai da maijegon, Murmushi yayi batare da ya dakata daga daura agogon hannun shi da ya ke yi ba Sai da ya daura a gogon shi, tsab san,nan ya karasa gurin da turaren shi suke ya na cewa,, Shirin may zanyi, ? Da mamakin jin abinda ya,fada take kallon shi sai wani dadi da ya kumay ta cikin ranta lokaci guda,, Amma sai tace kai ko dai, Sweet Bukar shirin suna mana wanda zakayi a matsayin ka na uba, Murmushi yayi a daidai lokacin da ya isa gurin aje takalmomin sa, yana cewa a yayin da yake saka takalma a kafan shi, Ba a kwai mutane a gida ba, su za su gabatar da komai basai nayi ba ni, ko kina son ace dan fari bana kunyan shi ya fada a cikkn zolaya, Taji wani irin dadi ya kumay mata zuciya, sai cewa tayi to amma ai ya kamata ace mu a nan fannin mu munyi wani abu dai ko aje dashi, Yace OK to ai ku iyayyen yaro ne dama sai kuyi shawara akai kuga may za,ayi ko kafin in tafi don kila zuwa gobe ko jib zan tafi, Bari na fita idan na dawo sai muyi magana akai,muga, yadda ya dace, ayi ko, Tace cikin kissa tau Sweet Bukar nagode sai in kadawo din asan abinda za,a yi ke nan, Don dai gaskiya dole ne ayi shiri daga nan badon komai basai don ana zaton cewa muna a birni, Murmushi yayi yayin da yasa kai ya fita daga dakin fuskan shi dauke da murmshin mamaki,

Tafe yake a motar shi sai mamakin halin irin na mata ya keyi don idan badon kunnuwan shi sun ji mai abinda ya tsura Fatima tana fadi a waya ba Da babu abinda zai hana shi cewa tsakani da Allah take zancen ta, da shi a yanzu, Yadda abin ya,faru kuwa shine, ya shigo gida kamar yadda yasaba idan ya dawo daga gurin aiki, Ka,ida ce sai ya ziyarci dakin, ko wace mace ya dubi lafiyan yinin ta, sai dai ba wai dole kullun yake wanan zagayen ba sai ranan da ya dawo da wuri daga gurin aikin, Hakan yasa yau ya fara shiga gurin Fatima don itace wace tai girkin rana, a ranan, Daga gurinta ya nufi gurin sadiya wace zata karbi girkin dare a ranan a dakin Salawatu ce last din shigan shi ranan, Sai ya tuna cewa bai fadawa Fatima cewa yana son ta hado mai zobo wanda zuwa yanzu yazama mai abinsha, Zai saka kafa shiga dakin na,ta ne yaji muryan ta tana waya tana cewa ai kawai barshi, Asiya sai na bugi cikin shi inji irin abinda zai kashe mata Mai makon ya shiga sai ya tsaya daga baki kofa a lokaci guda yana jin kalaman ta sai yai wani irin zufa ya fara zubo mai da yaji tana cewa Bakiga yadda ya wani susuceba, ne shi a,dole matar shi ta haihu, ya samu yaro, Ni wallahi har mamaki yake bani wai fa akan Meenatu Bukar ke wanan rawan kafan, haka Yar yarinyar da duk a cikin yan uwanta a lokacin itace karaman su, Cak ya tsaya ba tare da ya karasa daga second cotton din dakin ba don haka sai kawai ya, Yara tafiya don ya bar gurin saboda kada ta san yana gurin, Juyawan yai niyan yi sai yaji tana cewa na fada maki dama ai Yaya Aliyu ya,fada min cewa yana son Meenatu sosai cikin matan shi,, Amma sai na mussanta mai nace ance bai damu da ita ba don auren hadine auren gida, Yana kaiwa nan yai yar murmushi tare da murda sitiyarin motar shi, zuwa gidan hajiya Jummai don ya gane wa idon shi irin kayan da ta shigo mai da su, Don Fatima yana ganin tafi duk sauran matan zafi don irin yanayinta yanzu ba wanda ya santa da shi bane da can baya, Yana tafiya yana cewa a ranshi ashe shiyasa itama Meenatu bata ra,ayin zancen da ya shafi Fatima duk gautan ja ce kawai, indai mace ce, Ya isa gidan Kayan sunyi mashi kyau sosai don yasan cewa za,a yaba da su don haka yasa a parker su a mayar a cikin akwatinan su kawai, Ya fada mata cewa Baba Hamza da Baba Wadda zasu shigo su dauka idan zasu tafi kawai dai ta rufe mai su da kyau,

Da dare kowa yana falon zaune yai shiru yana sauraren abinda mai gidan zaice akan zancen da suka kulla na cewa su karbi wani abu a gurin shi, Idan yaso sai su sai dan abu kalilan su bayar suce mashi ya isa hakana, su dai kawai su samu na su rabon daga ciki, Sadiya ce bata yarda da wanan hadin kan kishayan ba da za,ayi wanda ba na Allah bane, Don ko fuska Fatima yar iyayi bata gani ba a gurin Sadiya balle ta, tun kare ta da zance, Da farko ita ma Salawatu taso ta bijire mata amma da taji zancen yagar kudi ne sai kawai ta kawo nata gudun mawan ta yadda za su samu galaba, akan shi, Sai da ya gama abinda ya keyi a cikin computer dake gaban shi sannan ya dago kai tare da sauke numfashi yana cewa, Ok dama akan zancen zuwa gurin sunane yasa na kira ku nan yana magana yana kallon Sadiya, Ya,ce don inji ko da wace ce zamu tafi don dole mu bar wata a gida bazamu kwasa mu tafi ba gaba dayan mu ,, , Akwai motan Bus ta ma,aikatan mu da na dauka saboda matan Lawals da sauran mutane masu son zuwa,, Su har can zasu tafi basu jin nisan wanan tafiyan da akeyi ? Salawatu ce tai wanan maganan batare da tai la,akarin komai ba, Hakan yasa shi gane cewa bata da niyan zuwa gurin sunan ke nan don haka yace a ran shi zanyi maganin ki, Ya ce da farko zanbawa kowacen ku dubu ashirin don babu kudi kunga ga tafiya agaban mu da zamuyi, Don haka kowa yasai abinda yake son saya dashi, don laluran haihuwan, Ya, dauki waya ya kira Baba Wadda yace ya cewa Hamza ya duba a mota ya shigo da ledojin dake cikin motan, shi,,, Yaci gaba da cewa ke sadiya da Salawatu sai ku shirya mu tafi tare mu,bar ita Fatima a gida sai idan Allah ya dawo damu lafiya idan zan tafi gaida, su sai mu tafi tare,da ita ta gane su, Gurin gaba daya yai tsit ba wani mai motsi don plan din kowan, su ya rushe ke nan a hakan,, Hamza ya kawo ledojin ida ya mikawa kowan su nata a tamface da lace yace su samu na shiga buki saboda ba kudi, Fatima wace sai faman jujuya kayan take yi da hannun ta duk da kayan suna da kyau sosai ga kuma daukan ido ga lace din, Amma duk wanan kyau din kayan basu gaban ta don akwa abinda take son yi idan ta tafi BK din don tana son zuwa kangiwa,, Dole ba yadda ta iya ta hakkura da zancen zuwa dole itace zata tsaya a gida,

****** ********** ****** Mutanen gidan mu kowa sai aiyu kan shi ya keyi na yau da kullun idan gari ya waye Hakan yasa akabar ni a daki dagani sai dan jaririn dake barci, shi a gefena hankali kwace, Don haka ni tunda yan hira basu, zoba kowa tana can tana rage aiyukan gaban ta ,yasani nima kokarin kwantawa don na huta,wa raina, A hankali nakai kwance tare da sauke ajiyan zuciya yayin da na dan lumshe idanuwa na da niyar yin barci, Waya tace tai kara alaman kira ya shigo min duk da na fara lumshe idona alamar barci bai hanani bude idona ba a lokacin, Yaya Abubakar ne a layin yake kira na duk da nasan cewa shi ba mutum bane mai,kiran waya da safe saboda yana office a lokacin,,, Kafin wayan ta tsike nadaga kira dauke da sallama irin ta musulinci a bakina, A hankali naji yakira sunana cikin wata irin murya mai cike da kasala da birkita lissafin mutum wanda ma,auratane kawai suka san irin wanan yanayi,, A,take wani irin kasala ya sauka min tare da kewan mijina wanda na manta tsawon lokacin dana dauka banji irin hakan ba a tare dani Wani irin ajiyan zuciya na saki wanda shi kan shi Yaya Abubakar sai da yaji shi har cikin ran shi, daga bangaren shi, Hmm naji yace tare da cewa maijego kin sha zafi, ya kuke Meenat ya Baby na, ? Murmushi na sake a hankali tare da cewa cikin wani irin murya, Muna lafiya kalau insha Allah, ya amsa tare da cewa masha, Allah Yace insha Allah gobe zamu taso gaba dayan mu don saboda nisa Domin idan mun ta so mu samu mu huta kafin mu koma, Saboda haka idan akwai abinda za,a zo maki da shi sai ki fadi kafin mu taso din, Sai yanzu na dan sauke ajiyan zuciya tun lokacin da ya fara min bayani, Nace Yaya na babu abinda nake bukata daga can sai dai idan da guri kuzo muna da Irish da manja kawai, Yace cikin nuna alaman murmusawa, su kawai za, a zo dasu nace eh su ma din wa mutanen gida don amfani, su, Yaya Abubakar yace cikin kasalaliyar murya ina fatan uwar 'ya'yana ta daina fushin da takeyi da uban 'ya'yan ta, Sai da na lumshe idona saboda jin dadin jin sunan da ya kirani da shi na uwar yayan shi Cikin lumshe ido na naçe haba dai Yayana akan may zanyi fushi da dan uwana rabin raina, Yace amma badon zamu saudiya ba ai da nazo kawai sai na tayar wa malam da su Baba hankali cewa nida iyalina zan koma Abuja, A hankali na sake wani dan murmushi mai sauti nace aiko da kakawo fitina don malam gaba zai saka mu, ni da kai, yace mun kawo mai sabon fitina, Dariya naji Yaya yayi sosai tare da cewa zai koyi fitina yabar mu, Yace ba komai duk fitinan da za suyi indai zan dawo da ku ai bazan damu ba ni, Na ce haba yaya sai kace wanda baida mata agida da zakace mu dawo tun yanzun, da jegon mu, Murmushi mai nuna ma,ana naji ya sake tare da canza akalar hiran na mu, Ida yake sheda min cewa su Fattu da Anty Saloon za su zo su ma, tare da sauran jama,a Murna nayi sosai tare da nuna farin cikina a fili don jin cewa mutanen arzikina za su zo gari wagari tun daga Abuja har KB, Mundan jima muna hira da Yaya Abubakar wanda mun jima ba muyi hiran arziki irin hakaba dashi, tun kafin auren Fatima, da shi

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull