Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 81

Tarko complete novel - Chapter 81

Tarko complete novel Chapter 81: Tarko complete novel Chapter 81. ****** ********** ****** Gida kowa gyaran jikine daga dangin kitso kunshi siffa, da…

2,728 words

****** ********** ****** Gida kowa gyaran jikine daga dangin kitso kunshi siffa, da sauran su, Sai kuma dan kus,kus din da ke yawo cewa, Mahaifana ba su aje komai ba don babu komai a part din mu wanda zai nuna alaman cewa akwai, wani hidiman, suna agaban su ba, Don haka tun mutane ba su dauka har suka, fàra yarda da zancen ta Akai,ta suka na da mahaifana suna cewa wai ina zaune da mai hali amma naki tara komai muyi lalura, Suke fadi kuma haka za,a kwaso jiki a zo a fada min ni da iyayyena duk abin da suka ce a can din , Idan na fada ma anty Amarya zancen da mama keyi sai tace dallah rabu da wanan Mata da batasan ciwon kanta ba, sam Haka abubuwa su kai ta gudana kamar kowani gidan haihuwa yadda ake badakala, da jama,a,,,, A fanin iyayyena su ma sai shirin suna sukeyi a bin su a hankali, Amma mutane sai suke ganin tun da har, izuwa yanzu ba suga wani motsin kwarai ba daga sashen mu hakan ya nuna cewa maganan Mama Ladi akan mu gaskiya ne, Mama Ladi yaran ta a sashen su sai shawara sukeyi suna kullawa yadda za suyi al,amurorin shagalin sunan su, Anty Safiya da Anty Samira suka kaqo shawaran yadda za ai bawa mutanen gida abubuwan su, Amma sai mamata kekashe kasa tace bazata bawa kowani part ba iyaka dai wanda ya shigo a dan bashi a leda kawai, Basu son wanan shawaran na Mama amma kuma dole su bi shawaran mahaifiyar ta su, Sai ana gobe suna mahaifiyar Fatima ta shigo barka ita da wasu mata mutum uku, sai wani kallon kurulla take min tankar itace kishiyar tawa, Inda ta kawo, min turmin zani da sabulan wanka acikin wani farin leda, Sai da dare mutanen Abuja suka iso gaba dayan su inda gida ya kaure da murnan ganin bakin mu,, Sabon part din da Yaya Abubakar, ya gina don saukan mu idan munzo anan a ka sauke bakin mu da sukazo, Daga cikin su harda Baba Ramatu, matar malam Abdullahi masinja, Antyn Saloon Fattu da Maman Biu, sai matan wani abokin aikin su Yaya Abubakar su biyu, Haba murna da farin ciki ba,a maganan on muka baje a dakin dije da bakin nawa duk da an ma su masauki a can part din, Mukai wani lokaci zaune tare da su muna ta yaushe bayan robo , Inda gaba dayan su ,sun yaba da kyawondan jaririn dake kwance yana barci, Sun tafi masaukin su don su dan kimtsa a lokacin ne yaya Abubakar ya shigo sashen da malam tsoho, Daga cikin daki gurin da nake zaune ina iya hango shi cikin annuri, Fuskan shi sai sheki yakeyi yana annuri baiwan cikar zatin shi ya baiyyana a fioli, Ina jin muryan shi mai rikita may saurarenta tare da shiga yanayi ,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH AL AWWAL,,,,

Sai da ya gama barkwanci da matan malam tsoho a lokacin ina daga ciki zaune sai dan murmusawan jin dadi nake yi zuciya ta tayi fes saboda farin ciki, Da Sallama ya dago labulen dakin da nake a ciki zaune, gefe guda a kasa saman tabarman kaba, ta saka mai launi kala, kala a jikin ta, Jug ne a gefe guda na tab da kunun kanwa a cikin shi, sai wani roba dake shake da kayan yaji yaji daddawa da maggi da su tafarnuwa, acikin sa, sai sugar daga dayan gefen Dakin sai kamshin jego ya keyi duk da kamshin turaren wuta yaso, ya rinjaye shi, Idon shi kem a kan, dan jaririn da ke kwance cikin wasu zannuwa da aka dunkule a guri daya, Sai kuma ya juyo gurin da nake zaune, ina wani dan noke noken kai kamar mai jin kunyan shi, A hankali ya karaso bakin gadon inda yadan rankwafo jikin shi ya rage tsawon shi, Bude jikin yaron dake nade a cikin showel yayi har zuwa kafafuwan shi kamar mai son ganin wani abu a jikin yaron, Ajiyan zuciya naji ya sake a hankali tare da dan, juyowa gurin da nake yana cewa, Sannu Meenatu gaskiya kinyi kokari wanan yaron babba haka kamar ba kece kika haifo shi ba, Murmushi nayi kawai tare da dan kifta ido kamar mai marmada su nace cikin irin murya na, Sannu da zuwa Yaya ya hanya ya aiki ya sauke ajiyan zuciya tare da kokarin kaiwa zaune yana cewa Meenatu barka da arziki, haka, Ya kuke ya ruwan zafi da kuma kokari ? Sai na rasa may zance kawai sai nake cewa ance da su Anty Sadiya kuka shigo garin ko, Cikin mamaki yace basu shigo bane tun dazun da muka iso nace kila suna dan hutawa ne, Yace kawai basu da hankali don banga amfanin zuwa dasu ba , Ace sun zo basu zo sun dubi wanan yaron ba to may suke a can uban wa suka zo yi a garin ? Nasan yau ran maza ya baci tunda har da zagi naji daga bakin shi, akan bacin rai, Waya yadaga yana tambayan su suna ina ne wai, gashi a part din da nake baigan su ba, Muna nan gurin su mama inji Salawatu ta bashi amsa kai tsaye, Ok kawai yace batare da ya furta wani abuba a gain don canzawan idon shi kawai ya isar min da sakon zuciyar shi, Tafiya har da su Ramatu ashe da matan malam Abdullahi sai lokacin naji ya dan sake rai tare da ajiyan zuciyan tunanen da yake yi, Yace Ramatu a ko da yaushe tana yawan tambaya na da cewa yau she ne uwar dakina zata dawo, Hakan yasa nace ta shirya azo da ita ta gan ku ko hankalinta zai kwanta ita da maman Biu, Murmushi nayi don jin dadi nace ai nagode kwarai wallahi, Kafin nai magana sai naga jaririn yana dan wani wutsil,niya da kafan shi alaman zau farka daga barcin da yakeyi ke nan, Ido na kura mai daga gurin da nake zaune ba tare da nayi kokarin mikewa na duba shi ba, A hankali Yaya Abubakar wanda ke hankalta da abinda nakeyi ya mike tare da kai hannun shi da niyar ya dan jijiga shi, Aiko kaman ance ya tsala ihu sai ko ya barke da kuka wiwi, Daga waje Mama Dije ke cewa Meenatu, bakyajin kukan da dan bawan Allah ke yi ne, Cak Yaya ya dauko shi tare da dangware min shi a saman jikina yana cewa wanan ai daukan alhakaki ne ko yaro na kuka gaki zaune kina kallon shi, Cikin dan marairaicewa nace, yaya ai ina batun tashine dama shine ka miko min shi , A hankali nake kokarin bude nono na don nabawa yaron yayin da Yaya Abubakar ya tsure ni da idon nan nashi mai rikitarwa, Kunya duk ya rufe duk nashiga rudu na rasa yadda zanyi naba yaro nono a gaban shi, Muryan shi naji ya kira suna na a hankali yayin da na dago kaina na dan dube shi, cikin kunya ina kuma kokarin gyarawa, Yace an darajan Allah da Annabin sa, ki taimaka min ki tallafi yaron nan amana,kamar yadda muma iyayyen mu suka tallafe mu, A hankali nace yaya ai ina bashi nono kawai yau don dai, ka na gurin ne, Ya girgiza kanshi cikin lumshe idanuwan shi tare da dan jingina jikin shi saman filo, yana mai kara lumshe idanuwan shi saboda sha,awan mu da ya kama shi, Na turawa yaron nonon a baki yayin da ya cafke da sauri ya fara zuka, Shiru dakin yayi tankar babu kowa a cikin dakin a lokacin sai dan jaririn ne ke yar ajiyan zuciyan kukan da yayi, Zuba muna ido yayi yana kallon mu, cikin mamakin yadda nake dan rutse idona saboda zafin da nake ji yasa shi jin tausayina, A gogon dake daure a hannuwan shi ya dan kalla tare da gyara zaman shi yana ma muna kallon tsab, ni,da baby, muryan shi na ji, Yace to yaya zancen komawa tare da mu ina fatan yana nan dai ko ? Ajiyan zuciya na sauke, tare da dan dago kai daga duken da nake, Murmushi nayi mai sauti tare da cewa ai da malam ya saka mu gaba don ko yanzu ba,a fita da yaron nan ko kofan dakin nan, Nima wanka a cikin wanan dayan dakin da ba,a karasa ba yace a dinga yi min, har a yi sati guda, Iska ya furzo daga bakin shi irin mai fitar da takaici di nan yace badon komai ba ne sai don wasu yan dalili da suka faru Amma ai hakan yayi don badon Allah ya sa mun fargaba da wuri ba da an muna sakiya, da baruwa, Wanan yaro Meenatu Allah ya kara tsare muna shi dashi da duk wani wanda ke a cikin matsala iri na mu, A sanyaye na amsa da cewa Ameen Jikina nane yai sanyi sosai, don jin may yaya Abubakar ya fada hakan ya sani gane cewa akwai magana babba a kasa, Wayan shi ce da tai kara yasa shi dan dagowa daga dukawan da yayi gab da dan jaririn yana cewa, Ok ka iso ke nan ko ? Sai na gane cewa da Aliyu yake waya a lokacin, saboda, muryan shi dana dan tsinkayo a wayan, Da wuya na shigo nan again may be sai zuwa safe idan Allah ya kai mu don zamu tafi Kalgo ne yanzun nan, Nace Allah ya tsare hanya a dawo lafiya tare da dan r ausaya kaina wanda yasha kitso sai sheki yakeyi, ga kumshi dana, sha,a hannu da kafa, Tun zaman shi a gaban mu nake kallon irin yadda yake wani kashe Idon shi a gabana, Ya mike fuskan shi dauke da murmushi, tare da cewa OK kukula da kan ku saboda taron mutane,, Har ya fara tafiya sai kuma yaja ya tsaya ba tare da ya juyo ba naji ya sauke wani sanyayan ajiyan zuciya tare da cewa, Ban son naji matsalan komai daga ko wani bangare duk abinda za,ayi kuyi hakkuri akai, A hankali na gyada kaina alaman to tare da cewa insha Allah,, A hankali yadan rakwafo ya mika hannuwan shi a kumatun dan jaririn wanda ke rugumay a jikina yana shan nono a hankali, Yakara mika hannayen shi ya shafo gashin kan yaron mai laushi a hankali tare da sauke a jiyan zuciya mai dan sauti, Allah ya raya muna kai ya furta a hankali tare da sauke dan ajiyan zuciya daga gurin da nake na amsa a hankali da cewa Ameen summa ameen, Daga haka ya sa kai yabar dakin yayin da nabi bayan shi da kallo irin na so da kauna, wanda iyanzu so biyu ke tsakanin mu ñida shi, Gana zumuncin da muke da shi gana aurataiyan da yanzu ya shiga tsakani na dashi,, A hankali na dan rutse idona tare da rugumay dan jaririn dake makale a hannuwa na yana ahan nono, Wani irin son yaron ne naji yana shiga kowani sassan jikina a hankali yana ratsani a hankali, Tun haihuwan yaron ban samu lokacin da nai mai irin wanan rikon ba saboda a koda yaushe akwai jama,a a tare da mu a dakin, Nakara kai idona a hankali ina mai kara mashi kallon tsab nake ganin kamar shi da mahaifin shi tankar kaki, Wani dadi naji ya kumay min zuciya, na a hankali nake jin son mijina da dana yana shigana,,, Shiko yaron sai shan nonon shi yake ta sha batare da ya nuna koshi ba, a hankali na aza hannuna a kan shi ina dan sauke ajiyan zuciya, Jin a shigo dakin yasani saurin bude idona da suke a lumshe ina kallon mai shigowan, Anty Sadiya ce da Salawatu idon ko wacen su ya na a kan dan jaririn dake rungumay a jikina, Sannu ku da zuwa nake masu tare da kokarin nuna masu gurin zama,don su zauna, A,a, dadi ga hannu ana shan nono ne haka, inji anty Sadiya tana kokarin zaunawa, a bank n gadon dakin Dije, Salawatu sai bin dakin take da kallo kamar wace ke son ta kwankwance komai na dakin a lokaci guda, Cikin hausan nan nata take cewa ashe, a nan kuke zaune, ai ina ce ko a can part din su parents dinki kike zaune, Duk da banji dadin zancen ta ba sai nadake ina dan yake fuska kamae da gaske, Ina cewa, ai muna nan gurin malam tsoho muna shan dadin mu abin mu, Tace cikin hausan ta da ba pure ba, ai sai ku mu kan idan mune ai baza mu sha wanan dadin ba gurin wanan tsohon mai nuna wariya, Abinda bazan yarda ba dashi ke nan na juyo ina ce mata, amma wanan ki dai fadi ne don ko muna fuki bazaice hakan ba a kan malam, Kafin tai magana Anty Sadiya wace ke kokarin gyara dan jaririn a hannu ta, tace wai Meenatu wanan katon baby haka, Gaskiya kinyi kokari sosai, kuma ance ba,a asibiti kika haihu, ba, murmushi kawai nai mara sai muka ci gaba da dan hiran mu sama sama, Salawatu tana daga gefe sai wani basarwa takeyi kamar zata fashe, ban san may ta gani ba take hakan, Muryan ta mu kaji tana cewa kina nan ne zan tafi in dan huta, don dama nayi zaton cewa, wanan mai masifan yana nan ne, Ganin ta mike zata tafi ba tare da ta dauki yaron ba nace mata, baki dauki dan nakiba zaki tafi,,, Ta wani dan yatsune fuska tana cewa ai muna gari idan na dawo zan dauke shi, Nace, haba, Maman boy kada yai fushi dake fa yai maki kuka, kin ki daukan shi, Dije ce ta shigo dakin tana cewa Meenatu baki fa aha ruwan zafi ba tun dazu,ina lura da ke, Dukawa tayi tana kokarin zuba ruwan zafin da kunun kawa a cup din, Gaba dayan su hankalin su yana gurin ta daga gurin da Anty Sadiya take zaune take cewa aikina fama da shan ruwan zafi haka, Fitan Salawatu Anty Sadiya tace, rabu da ita bazata dauki yaron ba, don tana da wani manufa a ranta Yanzu haka kafin shigo nan ina jin suna waya kin san mun samu wata sabuwar yar iya a gidan,, Mama Dije ta dago da roban ruwan zafinda zan sha a hannun ta tana cewa , Sai dai su mutu amma basu iya komai da jinin malam, Dama nasan ita yar gidan zabarmawa ba son Allah da Annabi takewa maisunan malam ba, Anty Sadiya tace ina ma kika sani Dije ai sai kin zayna da ita zaki fahintan ta sosai, Nan Dije ta shiga zage zage nidai ina kurban ruwan zafina zafi yakai min ko ina kuma dan sauraren firan su a hankali, Nan na fahince wasu halaiyan Fatima daga gurin anty don haka nasha alwashin yadda zan zauna da ita, idan na koma,, Aiko Dije tana fita tafara aibanta Salawatu ce wa tana kishi har taki daukan jariri, Abinkada yan uwa sai ran yan gidan mu ya baci suka shiga sakewa Salawatu habaici da bakar magana, Nan da nan ta tsargu ta daina wani iskanci da tai niyar yi akan mu,

Su Baba Wadda da Baba Hamza motar suce shigowar karshe don haka suna shigowa suka wuce gidan Anty Safiya suka sauke kayayyanki da aka umurce su, sukai gidan ta, Sun iso gidan mu da dare sosai amma duk da haka sai da suka shigo cikin gida don suga Baby, Murna gurin mahaufiyar Baba Wadda ba,a magana ganin irun yadda dan ta ya sake a lokaci guda, Sunyi murna sosai da ganin mu kamar yadda nima nai farin ciki sosai da ganin su, Suna cin abinci suna min hiran irin abinda ke wakana agidan mu yanzu,, Suna sheda min yadda ake kwasa tsakanin Salawatu da Fatima amarya, Hamza yace, Wallahi Amarya duk na matsu ki dawo gidan duk ya koma ba dadin shiga, yanzu, Murmushi nayi ina cewa gaskiya ba yanzu ba saboda, sai munyi wata uku a gida muna shan ruwan zafi, Duk basu ji dadin abinda nace masu ba saboda su a zaton su da anyi suna tare zamu koma dasu, A dakin Baba Ramatu ta samay su tana masu sannu da zuwa, nan ta zauna muka dan taba hira dasu sukai min sai da safe, Baba Ramatu tace a dakin da nake zata kwana saboda haka ta gyara kasa wai a nan zata kwanta, Ranan zuwanta dakin yai muna dadi don mun samu barci sosai itako tana ta fama da dan jaririn mai kukan dare,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull