Tarko complete novel - Chapter 82
Tarko complete novel Chapter 82: Tarko complete novel Chapter 82. ****** ********** ****** Dakin Mama Ladi yau tab yake da jama,a sai kace ranan ne suna,…
3,076 words
****** ********** ****** Dakin Mama Ladi yau tab yake da jama,a sai kace ranan ne suna, saboda irin yadda gidan ya cika, A gurin da suke zaune sai ga dan sakon Hajja ya shigo dauke da gallon din manshanu da shinkafa a cikin kwanon kaya, Dakin shiru yayi saboda jin wace ta aiko da sakon don haka sai Anty mai mumunace tai karfin halin karban kayan tana cewa Kai du dukka inji Inna Hajja tace a kawo a Kara a sha,anin buki aiko walle angode, Yaune rana na farko da Mama Ladi taji wani irin tsarguwa akan wanan sakon da, Hajja tai ma, Duk wanan irin abubuwan bata yarda cewa Hajja zata iya cutar da ita, Sai gashi yau zuciyar ta ya nasa mata zargi akan kayan sakon da Hajja ta aiko mata da suwa, Amba yaro naira dari tukwici, ya wuce yana murna, tare da godiya, Dakin da take tara shirgin kayan aikin ta wanda ba,a kwana acikin shi tace a kai a aje, Abin gidan waya labari kus,kus har ya fada kunnwn malam tsoho hakali a tashe ya shigo har part din Mama Ladi da kan shi, A lokacin bayan sallah la,asar ne, ganin shi yasa kowa maida hankalin shi gare shi, Yace Ladi ina kayan da Hajja ta aiko dashi gidan nan suke samm Mama ta manta da zancen kayan sai yanzu da malam ya tambaya, Dark n aka shiga don a dauko kayan aiko sai ga Anty Mariya da gudu ta baya tafuto waje daga dakin tana cewa Innalillahi Innalillahi, Innar mu ba man shanu bane cikin gallon jine ne da tsutsoci ba shimLkafa bane tsutsoci ne, Daga gurin da malam yake a tsaye yai murmushi yace kun kuru da kunci shi da kunci bala,i sosai, Da kan shi ya shiga dakin ya fiddo da kayan waje kafin ace haka jama,a sun cika guri aciki harda Sadiya wace ta fashe da kuka a lokaci guda, Mutane kowa yagani sai hankalin shi ya tashi don tsoro take masu iska suka fara hawan iska gida ya rude a lokacin muna daki ni da baki, na Wanan labarin ya samay mu aiko duk suka tsorace, suna, ta addu,an neman tsari, Mama Dije ta shigo dakin a rude tana cewa kada kifita ko nan da kofa Meenatu yau gidan ba lafiya, nan ta kwashe duk yadda akayi ta fada muna, Tace aiga malam can da tawagan shi har da mai uguwar shiyan mu sun tafi gidan nata da kayan, Anty Sadiya tashigo gidan gurin yae uwarta da kuka nan suka labe a dakin sadiya can sabon part din mu da yaya yagina wanda a nan suka sauka, gaba dayan su suna dan tataunawa, yadda za,su yi, Nan akaci gaba da shagulgulan buki kowa ya fita batun zancen don dama ai kowa yasan cewa muguwa ce, Sosai maigari yai mata kashedi da gidan mu ida akace idan aka kara jin wani abu ya shiga tsakanin ta da mu sai andaureta, Shiko yaya Abubakar cewa yayi duk wani abu ya samu iyalin shi wallahi itama sai ya kashe ta Wai ita wace irin muguwae mace ce haka da nacin tsiya ro wallahi sai asirin ta ya tonu tunda tashiga gonan shi haka, Andai, tatausa maganan akace abar zancen tunda yarta tana a cikin gidan don haka abar maganar har a gama zancen suna tukun, Kunya da tsarguwa duk suka taru suka rufe Sadiya saboda irin abin kunyan da mahaifiyan ta taja mata a gidan auren ta,, Kamar yadda malam ya umurci kowa akan a share zancen aci gaba da sha,anin bukin suna hakan ne ya faru kowa na harkan gaban shi,, Mama Ladi wace taga har dare Anty Amarya bata zo garin ba yasa ta yin magana, Tana zaune gurin da ta idar da sallah magaribba take cewa karyan banza aidama nasan cewa baza,a iya fida sufe wuta ba , Ita wanan macen mai gwada min wai ita wata tsiya ta gashi shiru bata ko zo sunan ba, Mariya tace ina ko zata yarda tazo, ta kashe kuddin ta ga banza tunda wa yanda ma sunka haifita banga sunyi komai da za,aci a bangaren su ba, Koda yake haka sunkayi na kunun kauri gani shi dasu dai munkayi, miyan kan kauri na dai sunka dafa cikin gidan ga, Hira sukai tayi suna aibanta min iyayyena wai sai munyi kunya don komai bamu aje ba na fita kunya, a mahaifina kullun sai fita da gwangwaraman motar shi wai bidan kudi amma komai ba aje ba, Wasu suce wai don sunga anyi aure na basu kashe kudi ba shiyasa yanzuma suka sake jikin su ai masu,
****** ********** ****** Zanen suna akayi, irin na mutanen da abisa umurnin malam tsoho, antaru kamar yadda ba taruwa bukin yan dangi Yaro yaci sunan Shi Mohammad Buhari, inda mutane suka ji dadin wanan sunan da akasakawa yaron, Anfito da abincin liyafa jama,a sunci sun sha sun koshi Masa dafa duk kowani da nama a cikin shi, ga abinsha hade da ruwan gora, Mutane sai ci da sha sukeyi suna jin dadin su yan uwan mahaifiya na suyi kokari maza don da su aka zana suna tunda safe suna garin, Hakan yasa aka ware masu nasu acan cikin wani rufa daga gefe guda na kofan gidan mu, Sosai a ka karrama su da nau,in nau,in abinci tare da abin sha masu tsada, sunji dadin hakan da akai masu, sosai, Shanu da raguna biyu aka yanke wanda hakan ba wani bakon al,amari bane don haka al,adan yan kasan birnin kebbi da kewaye yake, Amma duk da haka al,adan yake saida Mama Ladi tai fadan cewa don zai yanka harda shanu, ai raguna biyu kawai sun isa basai ya hada da shanu ba, Tai ta mita wai yanzu duk mutanen gida kwashewa za suyi a cinye Da ta kirashi tana mai fada cewa don mai zaiyi hakan a cinye naman a banza , Sai cewa yayi haba mama dama ai don aci na yanka don kowa ya samu in ma bai isaba sai akara wani mana kowa ya samu,, Wanan maganan yasa ran Mama ya kara baci sosai, don haka a hasale tace wai ko mai sunan malam kana tanadi kuwa, ? Dariya sosai da mamaki Mama ta bashi don har yanzu dauka yaro karami take mai,, Bai iya cewa komai, ba yasa kai kawai yafita, abinshi yana mamakin irin rayuwan mahaifiyar shi,
Wani dogon rigan nasaka a jikina din half atamfa half material yaji stones agaban shi, Tsayawa bada labari irin yadda nai kyau, bata bakine, saboda duk wanda yaganin sai ya ce tirkasa, Labari ya kai ga yan uwan Yaya na cewa nasa wasu irin hadadun kaya a jikina, Daya bayan daya suke shigowa part din malam tsoho don ganewa idon su irin shigar tawa Jeloup din shikafa sukayi da kuma masa da miya, suna ba mutane da makwabta da yara, Anty Samira ce tace, wa yan uwan ta a samu abu a dan diba akai muna ni da iyayye na, Aiko sauran sukayo cikin ta tankar za su cinye ta danya a lokacin Anty Safiya bata dakin dole taja bakinta tai shiru, Bini, bini Mama Ladi tana turawa wai a je part din mu a duba mata ko may muke ciki, Zuwa karfe goman Safe motocin yan uwan mu suka iso unguwar motace bus har guda biyar sai kananin motoci, guda hudu take gida ya rude da ihun murna,,, Nan aka shiga fito da kulolin abinci kala kala da aka dafo daga sokoto gidan uncle dina, Tuwon semo tuwon Amala, tuwon shimkafa, masa fara kal, sai shimkafa da miya yaji corsole iri iri, nama kaman ba,a san zafin kudi ba don shanu dan madaidaici ne aka yanka akai hidima dashi, Mata yan uwan Anty Amarya da kuma kawayen ta da makwabta duk sun biyo ta acewan ta wai bukin First Born din tane ni, Gida yakara rudewa inda Yaya Abubakar da Aliyu tare da Lawal mijin Fattu suka nufi Bindawa plaza suka kwaso masu kayan sanyi masu tsada, Katon Katon aka jibge su a part din mahaifana sai a lokacin Anty Amarya wace ta tsaya saida taga duk bakin su sun samu gurin zama sannan tasa matan togo da tazo dasu su shiga raba abinci, Wasu manya kuloli da ta tana tare da mukarraban ta suka nufi part din Mama Ladi da su sukace ga abincin Daki na na yar kuryan daki da suka dafa aka debo mata nata share din, Duk wace ta bude kulla taga irin abinda ke ciki sai kaga an rufe a na kada kai don mamaki, Suna fita Anty mariya tace tirka sa ba,ayi ba yanzu za,a yi innan mu kin koga wa nan garalin haka, Vikin muryan nata mai kamar i,iniya tace duk burgan banzata anyi ne dai don mugani yanzu haka kila nasu wanda zasu cci babu komai ciki duk lami na, Sai wata mata saga cikin yan uwan Mama tace walle ko na yaran da aka zuba kamar duk namana zallah, Mutanen kebbi kowa ya san su da son nama kaman kuraye saboda zama da mutanen zuru, Don haka kowa zancen nama kawai yakeyi irin yadda aka gwada shi kamar banza, Duk part din gidan mu saida aka kai masu abincin da akazo dasu kala kala kowa ya lasa, Munkai wani lokaci da Anty na muna dan tataunawa kan al,amura ida na rasa irin godiyan da zan masu ita da Uncle dina da mahaifa , Bakina yan Abuja sunci sun sha sun kula na zuwa gida har sun gaji, Haka masoya Meenatu da Abubakar suka dinga shigowa gidan ban ko san su ba suna min barka da ma bani gift, Nayi shiga ta alfarma har saida hankalin Salawatu da Ànty Sadiya ya tashi tun suna gulma a waya da Fatima har tagaji ta shige dakin ta ta ki fitowa don ta kaici, Taiturawa akira mata Yaya Abubakar amma bai samu zuwa ba don haka tai mashi text da cewa, Macuci dancin amana wanda ranan lahira zai tashi da part guda, Wanan sakon yashi shivo cikin gida da idonshi da suka kada sukayi jajir, Yasamay ta kwance dakinta tana kuka yana shiga yace wani irin text ne kika turo min dashi, Ganin irin yadda idanuwan shi suka rikide yasa ta shiga hankali ta cikin kukan kissa tace yanzu Sweet Oga kasan cewa Meenatu zatai irin wanan shigan haka kaki fada muna muzo da shirin mu sai kawai muzo ana muna kallon wulakantattu haka, Bai fahinci maganan ta ba don haka yadakatar da ita cikin masifa yace wallahi kada ta kawo mashi tashin hakali yanzu sai yayi maganin ta, da taga da gaske yakeyi sai ta shiga hankalin ta nacewa yi hakkuri please rudin shadani ne dama, Yace ba shedani ba ko shedaniyace yanzu zanyi maganin ku ne ni, Haba wanan wani irn masifane mutum yana fama da jama,a kuma a tayar mai da hankali, haka, Yafita rai bace duk wanda yagan shi yasan cewa sunyi fitina adakin,
Mama wace ta matsu a fitar da kayan goyo akai, muna don kawai taga yadda zamuyi, Sam bata zaci irin kaya haka Yaya Abubakar dan baiwa sadaukin Meenatu ikon Allah, yayi ba, Duk da dai kayan baby sufi yawa kuma Ànty Safiya da Samira sun hurhura wasu daga cikin kayan sosai amma hakan bai hana mutane su rude ba, don yawan kayan,, Sai surutu akan kayan mutane keyi, wai an kashe garali, sosai, Mama Ladi ana ta fadi ana sake zance wai Su sun gaji arziki tako ina, gaba da baya,, Mutanen mu suna ji suka kyale ta ba wanda ya taka masu saboda tun wurin abuncin da ta hanawa mutanen gida sai duk girmanta ya kara zubewa, Sai musalin karfe biyun, rana matan Gwandu su ka shirya komai tsab kamar yadda Anty Amarya ta shirya komai, Robobin kayan su cicin da dubbla suwa su tsatsafa da takalmin uwar diya, roba har guda goma sha biyar,cikin sabbin roba fil, Sai akwatinan kayan goyo da sauran takarce da su mangyada da sauran abubuwa abin gwanin ban sha,awa, Daga haka aka kwasa zuwa part din Mama Ladi dasuwa, a lokacin sunyi kaca kaca suna cin abincin da aka kawo masu daga gurin mu,, Rana bata karya sai dai uwar diya ta kunya amma idan ta aje kunya sai dai ajishi ga yan kallo, Sai rangada guda sukeyi suna sake magana suna cewa aiko inda babu bamu gani balle muga babu a kayan mu, Yan Gwandu a ganku a kauce, don mu kunya gare mu badai tsoro ba, Haka sukai ta shigowa da kaya kalakala suna direwa a tsakar gidan Mama Ladi, Turururu mutane yan suna aka biyo don fitar da kyayan ido kowa nason gani, da idon shi, Ana bude kayan soyaye soye aka saka guda ayyurririiii, Ana zuwa na akwatina sai guri ya dauk guda da ihu mata na cewa tubar kalla masha Allah, Agani a zahiri shi ne arziki ba jiga baki ba Allah ya raya muna waga da Muhammad Buhari dan Albarka, Mama Ladi wace nauyi da kunya duk sun isheta sai yake takeyi na hakora ana cewa agausheku agaishe ku angode, Akwatin Turmin kanani wax aka fara budewa nan aka shiga ki dayawa, turmi arbain da hudu, zokaji magana, Sai dayan akwatin,turmi super wax ne guda goma sha biyar sai lace, da materials guda goma goma, Dayan akwatin ana budewa aka kara saka guda kayan uban jaririne har kala homa shadda Gezena da ghalila masu kyaun gani, Na kayan baby ne ba ayi da yawaba sosai take guri ya rude da murna da farin ciki, Nan suka juya suka bar ma Mama Ladi kayan a part din ta, Kunya ina kasa Mama ta shige don a tarihin gidan mu ba,a taba irin wanan abin arzikin ba, Take kyashi da hassada ya rufe Mama da wasu diyan ta suka shiga sake magana, Duk abinda ke wakana a cikin gida yana kunnen mazan kofan gida sai dadi suke ji yadda abin yazo
ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣7⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL AKHIRU
Sosai Anty Amarya ta girgiza mama Ladi don bata taba zaton cewa ko kwatan haka zata gani daga gare mu ba Gaba da su Anty Safiya suka zauna suna lissafa mata kudaden ko wani zani da suka fitar, Ai take hankalin ta ya kara tashi, sosai tace cikin bacin rai wanan duk makircin wanan yar banzar yarinyar nan ce Summaiya Amaryan kanin Saratu, Duk abinda tayi da gaiyya tai min shi don dai ta gwada min cewa su yan zamani na, Bata san cewa nagane sherin su sun tafi sun aro kaya shago sunzo su gwada min cewa, wai su sun ka saye su, Ai babu ida za,a da kayan ga cewa zanyi su barshi nan sai kayan zun kwana biyu hannuwa na na gwada ma mutane na, Safiya tace a,a Innar mu ina ruwanki da kayan su ko wanda dan ki yayi yanzu baki da iko a kan su tunda, sun shiga hannun su, Abinda nai niya shi zanyi don babu wanda ya isa ya hanani yi nai, Shiru yaran nata sukayi tare da nazarin samun mafita, Bayan duk anyi shiru sai kuma Mama tace, wai ma yanzu duk wa yan nan zannuwan a Meenatu za a barwa su gaba daya, Gaskiya sai dai in rage wasu daga ciki don dai sunyi masu yawa wallahi, Gaba dayan su suke hada baki gurin cewa a,a Innar mu, gaskiya hakan ba zai yuyuba gaskiya, Don dai ba,a taba yin irin haka ba uwar miji ta rage kayan goyon gidan uwayen mai jego, Ganin babu wanda ya goyi bayan ta yasa ta yin shiru tana mai kurawa akwatinan dake gaban ta ido, Can tace wai yaya ankayi da zance Nama ne don naji shiru, banji ance komai tun dazun ba,,, Safiya wace ke kokarin gyara kayayyaki dake tsakar dakin, Tace naman raguna ai ankai su gurin gashi guda na maijegone guda kuma namu na mutanen gida, Sai naman shanu wanda yana can ana rabawa yadda ya dace, Tambaya tayi kamar yaya ana rabawa kina nufin cewa wake rabawa tace, su Baba, Musa da Baba Hamza, gaba dayan su, Mikewa tayi fuuu ta dauki zanin ta ta yafa sai waje gurin da ake rabon naman, Tana zuwa ta hango an kasa, ko ina sai cewa tayi yaya ankayi haka nan za,a fara mata bayi Baba musa yace an kasa ankwashe ma kowa nashi Aiko mama ta hau sababi tana cewa ita don an maida ita haka sai adinga mata abu yadda aka ga dama a gida a kuma hana tayi magana, 'Da dai ita haifi anbinta babu mai shige mata gaba a kan al,amarin shi Inda take shiga banan take fita ba sai faman sake magana takeyi yadda ta so,,,
Mutanen gida, sai aka shiga surutu kowa da irin abinda yake fadi, akai, Saboda yadda Mama ta so tasawa mutane fita saida Baba Buhari yayi mata yankan kauna sannan ta shiga hankalin ta, talafa daga fitinan da take ta yi,, Andawo muna da duk wani kaya da muka samu wanda yasha surutu a gurin mutanen gida da na waje har ma da bakin mu, Ni kaina gani irin yawan kayan da aka tara muna saida hankalina ya tashi, Saidai kuma wanan ba wani abin mamaki bane idan akai la,akari da irin yadda muke bukukuwan mu a hausa, Sosai na yaba da irin hikimar Anty Amarya wace tafitar da mu daga cikin kunyan idon jamma,a, Mun fitar da manyan turamay a cikin akwatina daban muka parker su inda muka cire yan madaidaita tare, da na kasa da su, Daga ciki na cirewa matan malam tsoho turamay aka hada masu da sabulai da nama da kayan flower wanda aka soya masu yawa sai kudi da aka aza masu sama wai kudin dinki, Da farko da suka ga kayan sai suka bijire cewa bazasu karba don kayan sunyi yawa, Anty Amarya tare da gwagona Habbi da suka kawo masu kayan sukace haba ai in sunyi haka basu kyautaba don ba,a mayar da hannu alheri baya, Mama Dije tace ai kamar badon Allah mukayi ba idan mun karba, don gaskiya abin yai yawa, Haba Mama Idan kunya haka baku nuna muna ana tare ba ke nan, Ku tuna cewa abin Meenatu fa naku don may zata baku dan wanan abin har ku tsaya musuntawa, Anty Amarya ce ke masu wanan magana a cikin nuna damuwan ta a fuskan ta, Gaskiya zamu karba amma idan malam yazo mun gwada mashi yace mu mayar to zamu dawo dashi ne, Insha Allah ba ma zai ce ku mayar ba tunda yasan cewa Allah ne ya kaishi ga dadi ganin, dan jika, ai sai yawancin rai,