Tarko complete novel - Chapter 83
Tarko complete novel Chapter 83: Tarko complete novel Chapter 83. ****** ********** ****** Tsab yake sauraren abinda Fatima ke fadi ta wayan a cikkin kuka…
3,150 words
****** ********** ****** Tsab yake sauraren abinda Fatima ke fadi ta wayan a cikkin kuka sai dan sheshekan kuka takeyi, Sai da tagama zancen ta tsaba sai yace hmmm tare da sauke gajeren murmushi, yace, Fatima kin gama maganar ki dai ko ? Fatima tace eh cikin shagwaba, da murya mai hana natsuwa, Yace duk wanda ya baki wanan labarin cewa na kashe wa Meenatu da dan da ta haifa kudade masu yawa ina gani ya rage maki zancen bai fada maki gaskiya ba gaba daya, Yace ina dai kudina ne ba nakiba dai ko,? Ashe dama can, munafunci kike min cewa ya kamata na baku kudi kuyi masu sayayya abinda ya kamata, daga bangaren ku, "Da na da matata na kashewa ba wasu can daban ba, Ko ke yau kika haihu idan ina da halin yi zan iya maki fiye da hakan, Domin ko wani da da arzikin shi yake zuwa duniya dama, Tace to amma aiko bamu hauhu ba zaka iya kyautata muna, kwatan kwacin yadda kai mata ko,? Look Fatima wai shin tare da ke nake neman arzikina ko kuwa kece ki ka bani jari,? Ke har yaushe kika shigo rayuwa ta da zaki kafa min doka haka,? To ki kama kanki don ban son raini kuma kin bani mamaki ke lokacin dana aure ki may ye ban maki ba waye yace wani abu daga cikin su, Tace haka zakace min Sweet Bukar ,? Ko kina ganin cewa kin fisu ne a gareni ko Sadiya wace na dade da ita bazatai min irin wanan shamakin ba balle ke, Au gori ma zakai min don kayi mi dawainiya da zamuyi aure shine har zakai min fade, haka, Yace an maki tunda shi kike son ai maki, Tace ai yanzu dai ina cikin iyalin ka don haka ina da right din da zan wa kaina inci, Ke yace cikin daka tsawa ban son rashin kunya fa kin san halina Don haka ki kama kanki, kada na saba maki wallahi, Allah ya baka hakkuri indon na fadi gaskiya yasa kake cewa haka, Rai bace ya kashe layi tare da jan tsuki mai tsawo kamar tana a gaban shi Idon shi da suka kada sukayi ja yadan lumshe tare da lashe busassun laben shi, Yasa hannuwan shi ya dafe kan shi tare da furzo iskan takaici Yace why kowa problem kowa na son kan shi idan hakane ashe dole ya gyarawa kowace zaman ta, don sam bazai lamunci wanan halin ba a gidan shi, A haka Aliyu da Lawal da su ka fita tare zuwa wurin gyaran mota suka dawo suka samay shi rai a bace, Anty Safiya ta bugo mai waya tana sheda mai cewa wai, Mama ta tayar masu da hankali, Wai don may za,a raba nama batare da ankawo mata su gaba daya gurin ta ba ta duba, Gaba daya ya kashe waiyan nashi don bai son yawan damuwa haka, Aliyu yaidan murmushi tana cewa yanzu mara hankalin nan ta bugo min waya tana cewa wai, wanan dayar matar taka yar Abuja ta buga mata waya tana sheda mata irin shagalin da akayi na suna, Rai bace yace cikin wani irin murya mai nuna takaici tabugo min waya ai yanzun nan, Aliyu yace ashe Fatima bata da wayo ban sani ba lailaima kuwa zata gane kurenta sosai, No ka kyaleta Yaya Abubakar yacewa Aliyu cikin daga hannu tare da dago rinannun idanuwan shi da sukai ja,
Fatima tun bayan gama wayan su da shi taji irin ansan da ya bata sai hankalinta ya daga, Take natsuwa yazo mata da nadama saboda bai,dace ba ta fito fili ta, nuna mashi cewa tayi bankin ciki da haihuwan da akai mai, A hankali ta rutse idon ta saboda takaicin da take ji a cikin zuciyar ta ida Sakawatu bata bugo mata waya ba da batasan yadda duk akayi ba acan, Dole tasan mafita kafin yadawo don kada ya dauki zancen da zafi har yakai ga mata mugun fassara, Cikin tashin hankali ta kira mahaifiyarta tana fada mata abinda yafaru tsakanin su da shi akan zancen suna, Uwar tace ashe baki da wayo Fati, ashe hankali bai ishe kiba, Yanzu da kishiya zakiyi wanan hadin kan haka Fati ? Ita tana can da miji gurin tafiya zata bugo maki waya ta kara tunzuraki, Maza wallahi ki san yadda zaki gyara tsakanin ku kafin ya dawo ya dauki mataki a kan ki, Gashi kince za,a kawo maki yaranga can suyi maki hutu , Gashi ke kina nuna mai bakin ciki akan dan shi tilo daya da Allah ya bashi, Wani irin karfafan ajiyan zuciya ta sauke tana cewa walleh nayi kuskure kwarai mama,, Bayan sunyi sallama da mahaifiyar ta, taita kokarin kiran layin shi amma a kashe wayan yake, Tsoro da fargaba ne ya kamata kada yace shima bai yarda da zancen zuwan yaranta gidan shi ba suyi hutu, Don tasan halin maza yanzu sosai basu yarda da rikon dan wani, Don haka ta zauna ta rubuto mashi guntun text a waya kamar haka ta yadda da ya bude wayan shi sakon nata zai shigo mashi My Sweet Bukar dan Allah kayi hakkuri da abinda na aikata maka, Son ka da na ke yi maka, da yawa yasa min jin zazzafan kishinka haka, Amma daga baya da nai tunane sai naga cewa ban kyauta maka ba ban maka adalci ba sanin irin kyaqan halaiyan ka da nayi har nai ma wanan mumunan fahintar haka, Dafatan zaka fahince ni ka yafe min batare da rayuwanka ya kara baci ba a kan zance, Taka har kullun abin kaunar da alfahari Fatima Musa, Amaryan ka, Bata kyaleshi haka ba saida ta yaudare shi da wasu daddan kalamai wanda sirin su ne hakan, shida ita, Tasan cewa duk lokacin da ya bude waya har ya karanta wanan sako zai sauko daga fushin da yake ciki,
****** ********** ****** Muna zaune a daki tare da bakina da sukazo min suna kowace anbata nata gift din bukin sai farinciki takeyi, Nan ne Anty Saloon take fada muna cewa taji Salawatu tana waya da, Fatima suna zance akan wai maigida yazo yana wa yan uwan shi da matan shi barin kudi,haka Saboda haihuwa nan har zai kashe kudi irin haka, Ànty Amarya wace ke zaune a gefe ta dawo daga rakiyan bakinta da zasu koma gida yau Don ita zata kwana biyu tare da mu kafinta koma, gida, tace, Ita ma Fatima munafukata aiduk tasan yadda mukeyi nan kasan kuma ai hakan ba wani sabon abuna ba garemu, Hali daine irin na kishi kuma akan su zai karewa don dai, walle, Meenatu tafi karfin su ,, Ta Allah ba tasu ba don tariga da tai masu tazar ba yau ba ta ko ina, Fattu tace da kyau, Anty wallahi haka nake son ji don wallahi da ace wa yan nan matan sunfi karfin mu ai da mun shige su don da ba za mu iya zama da su ba ia,, Nan hira irin na mata ya kaure a tsakani kowa tana fadin irin nata halaiyan zama cikin kishiyoyi, Ramatu takara muna bayanin irin yadda yanzu zaman gidan yaya Abubakar yake, Da zancen hadin kan da aka kulla tsakanin Salawatu da Fatima saboda a hadewa Sadiya kai, Anty Amarya tace Allah ya bamu rai da lafiya kusha kallo don baza,a kai ko ina ba don badon Allah akayi shi ba, Shigowan malam tsoho ne cikin gida ya katse muna hiran mu ta hanyar kiran sunana yana cewa, Meenatu ashe dama aikin kudi su Abu su kai maki ban sani ba , Don wanga irin hidima haka walle yai yawa kafin in bashi ansa sai muryan Anty Amarya naji tana cewa haba dai malam tsoho, Dan waga abin da aka basu ai ba komai bane, tunda sunfi karan fin haka gare ta,, Amma dai gaskiya hakan yai yawa tunda akwai mutane da yawa ai malam tsohone ke fadin hakana, Inda Anty taita bashi magana har dai ya yarda ya shiga jero muna addu,oi tare da neman tsari, Ina zaune daga gefe muna sauraren su, don a lokacin duk a gajiye nake, Duk wani part dake cikin gidan mu saida Anty Amarya ta, aika masu da kayan buki gift din robobi sabulan wanki da omo clean, Hakan yasa su jin dadi tare da kara muna yin addu,oi masu ma,ana,,,
Washegari duk mun tashi agajiye amma haka na daure tare da tsula ado inda na yafa gyale na fara shiga parts din gidan mu, Ina masu ya gajiyan buki wanda na koma wata yar mulmulmul dani sai sheki nake zubawa don kyau, Nasamu yan uwan haihuwan mahaifina agida sai godiya suke min suna cewa Meenatu duk wadda akai kunyi keda mijin ki don kun gwada muna cewa, kudiya ne masu albarka don wanga hadin auren da malam yayi munga alfanun shi tun ba aje ko ina ba, Don da ace ke wata bare ce can daban ya aura da duk wanan abin sai dai muji labari nai, Amma yanzu kinga hikimar tsoho duk abinan ya dawo gida a hannuwan mu, Baba musa yace amma yanzu kinga sai yarda mukayi da abin mu, Matsalar mu guda yanzu shi na Ladi ta gane gaskiya, ta dawo ga hanya, Don wanga irin hauka da takai banga ranan da zatabar shi ba tunda hassadace ke cin ta,, Murmushi nayi tare da mikewa don bari part din Baba Musa kada ya ja min wani sabon matsala don da nace tak yanzu ji mama zatayi, Don ma aini maganar bata shafeni ba zancen su ne na manya, Har sabon part din mu na shiga gurin su Anty Sadiya wace tun case din mahaifiyar ta da akayi bata sake jiki ba har yanzu, Don ko jiya gurin yinin taron suna suna dakin ta da yan uwan ta suna ta tattaunawa a kan zancen mahaifiyar su,, Wanan ne karona na farko dana shiga wanan sabon, part din namu, Kofan dakin Salawa a rufe yake don haka sai na tsaya a tsakar gidan ina kwada sallama, Fattu ce tafi daga dakin da suka sauka wanda nake ganin shine a matsayin nawa dakin, Tace a,a maijego kece da kanko kika taso na dan murmusa kawai tare da cewa wanne dakin Anty a ciki ta nuna min wanda nake tuhuma din shine nata dama, Da sallama na karasa bakin kofan kafin ta dan leko tana cewa, Meenatu ke ce kika shigo nace eh, Take ce min shigo mana yayanki ma ai yana a cikin daki, Da sallama na shiga, dakin inda na hango yayana daga can gefe, Na samay shi kwance yana barci a saman wani katon katifa dan tsale, dake gefen guda na dakin wanda ya sha ties sai walkiya yakeyi, Jin sallamana yasa shi a hankali ya dago kan shi daga kwanciyar da yake, Bai amsa sallamata ba bai amsa gaisuwata ba sai cewa yayi ina Baba din yake, Saida na dan murmusa sanan nake ce mai, yana can a bayan Dije yana barci, Gaishe shi na kara yi tare da tambayar shi gajiyan jama,a ya amsa min da cewa Alhamdullahi, ya kuka kwana ya jama,a yace min a lokacin da yake kokarin dagowa zaune daga kwance, Tambayana yayi dacewa kun bawa wa yan,nan bakin komai da ya kamata ko don asubanci zamuyi gobe asubanci zamuyi, Idan akwai abinda za,a kara saya masu sai kiyi min magana a sayo masu kafin su tafi, A hankali nace ina ga kamar ai babu komai da za,a sai masu inba dai kara masu za,ayi ba, Yace ok zan duba anjima nagani idan da,a kwai din sai ai masu don sunyi kokari sosai wallahi, Daga haka ya mike ya shiga bathroom din dake manne a gefe gudan dakin,, Shigan shi yasa dan sauke numfashi ina cewa jiya ankawo wa su Anty nasu kayan bukin kuwa, Tace ankawo Meenatu mun,gode, mamace dai bata basu ba, Murmushi nayi gami da mikewa ina cewa barin gaida Salawatu sai na tafi na karasa gaida sauran mutanen gida, Na dan dauki lokaci ina sallama kofan Salawatu dake rufe sai waka nakeji daga wayan ta yana tashi, Nakara nocking sai a lokacin ne ta bude min kofan saidai ta tsaya daga kofa bata bani hanyar shiga daga ciki ba, Nagane mai take nufi bata son na shiga sai wani kallon kurulla take min tun daga kafana har samana Da kyat ta iya bude bakin ta ta karba min ciki ciki tana cewa kun tashi lafiya ya ? Acikin sakin fuska nake amsa mata ina cewa lafiya kalau ya gajiyan jama,a da tafiya,? Vikin ya mutse fuska take ce min lafiya kalau sannu ko ? Nace Allah bamu wuni lafiya a huta gajiya sai anjima, Dakin bakina mai suna nawa wanda ke a tsakiyan dakunan su na shiga, Shima kamar sauran yake saidai katifa biyu da karami nagani acikin sa duk sabbi kamar sauran a nan na zauna muna gaisawa dasu cikin so da kauna, Matar Abdullahi masijan Yaya Abubakar wace bata faye yawan magana ba, Nace Suwaiba ya zafin Kebbi tai dan murmushi tace aida sauki amarya tunda kuna da wutan Nepa, ko yaushe, Aida ban san ya zanyi da wanan zafin ba wallahi don sam ban son zafi arayuwa na, Anty Saloon dake kwance saman dayan katifan tace kai kaunata sai fawani shining kike karawa, Murmushinayi mata tare dacewa kai haba anty duk wanan ruwan zafin da mama Dije ke gasani da shi, Muryan Yayana naji yana kirana cikin muryan nan nashi da ya ke rikitar da ni, Natashi zuwa amsa mai kiran nashi na samay shi yana saka kaya ajikin shi Kallo guda nai ma shi na kawar da kaina gefe guda nace gani yaya, sai yake ce min na fadawa su Fattu su shirya a shiga da su kasuwa , Yaciro kudi yace na ba kowar su ta sai abinda take so idan sun tafi, Zanyi godiya yadaga min hannu yace ki bawa kowar su kawai, Lokacin da zan fitone naga sisters dina sun shigo da kayan break fast acikin kuloli manya, Wanda hakan yasani gane cewa daga part din mu ake kawo masu abin karyawa, Dama Maman Biu acan take zaune tare da mamana da yan uwana, Sosai sukayi farin ciki da wanan sakon suna cewa gaskiya baza mu iyacewa maigida komai ba don ai la lura muka kawo mai nan
A part din Mama Ladi na shiga kafin na shiga namu Na samay su anty duk a gida wanda hakan ya nuna min cewa a gida suka kwana gaba dayan su, Nan na kai har kasa ina gaida Mama Ladi kamar yadda na tsan mana haka din ne don fuska a daure ta karba min gaisuwan, Mundan taba hira da yan uwana namike zuwa part din iyayyena wanda tun haihuwana sai yau naga Mamana Mundauki lokaci da su kafin na koma partdin malam tsoho inda nake zama,
Washegari baki suka koma suka bar mu cike da kewan su,
ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣8⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AZ ZAAHIR
Bayan tafiyan su duk sai naji ba dadi a rai na don ji nake tankar na bisu a lokacin, Dan saukin da na samu gurin kewan su shine Anty Amarya bata tafi ba ta na nan sai mun gama komai zata koma , Mun shirya komai yadda ya kama inda na umurci Anty da ta dauki duk wani abin da take bukata daga cikin kayan, Amma sai ta nuna min cewa wai bata bukatan komai daga cikin kayan, Har saida nai mata hawaye ta dauki turmim zani guda amma nace sam bazan yarda ba, Dole ta hada da dinkakkun redemaide da waturmi again, Muna zauna muna hira take ce min Meenatu dama ina son nai maki magana gaskiya idan zaku koma dole mu sake wani sabon shiri fiye da na farko, Da sauri na juyo ina kallon anty don jin may tace min, Ta kada kai tana cewa akan yadda nake ta jin zan cen wanan kishiyar ta ku da alaman sai tayi makirci sosai, Don haka duk wani abinda kikaji ance tanayiwa wayance to ki shirya a kan shi don ke ma naki na tafe, A jiyan zuciya na sauke mai karfi tare da cewa nima ai tunanen da nakeyi ke nan, Nace ni dama Yaya zai barni na zauna nan garin ba sai na koma can tare dasu ba da yafi ,min wallahi, Aiko da bakin ciki ya ci ki Meenatu akan wata can zaki zauna a nan , Nace cikin dan marairaice murya gaskiya anty ni sai nake ga kamar hakan zaifi min sauki, Bazaki zauna ba Meenat ai zuwa tayi ta samay ki a gidan a kan may zaki bar mata guri, Hmmm nace tare da kara sauke numfashina nace Anty yanzu fa ina da yaro yaya zanyi a cikin su,, Kada na kara jin kin fadi hakan da zaran lokacin komawan ki yayi zanzo mu shirya komawan ki, Tau Anty nace, tare da dan kada kaina alaman to sai dai a can kasan zuciya na ina tunanen abubuwa da dama, akan komawar mu, Kafin muce wani abu saiga wasu mata sun zo barka daga Gese wai basu san cewa har anyi suna ba, Bayan fitan matan bada wani dadewa ba sai mu ka jiyo muryan mahaufina, Baba na ya shigo gida cikin farin ciki yake cewa Amaryan Nafiu dama ina son jin gaskiyan wanan al,amarin da kukayi, daga gareki, Don hankalina bai kwantaba saboda ina gudun magana, Kowan mu da mamaki yake kallon Baba saboda ba mu fahince shi ba mu san akan may yake son karin haske, Yace zance ko ina akan irin yàdda kukayi harkokinku cikin wadata haka, Murmushi tayi tana cewa har hankalina ya daga don ina ce ko wani zance ne can na daban, , Nan ta kwashe duk yadda al,amari yake ta fada mai da kudin dana bata da wanda suka bata sai kuma Uncle dina wanda ban san may zan mai ba na sakaiyya, saboda irin alherin da yake min, tun tasowa na Sai jijiga kai Baba keyi cikin mamaki yana cewa lalai kun kai yan zamani wa,yanga diya, Yanzu ashe kifina kun ka gasa da ruwan shi har ankaci, Lalai Ladi ta hadu da yan zamani sun sa ta kwana in takamar ga fitina, Baba yace to in har shi mai sunan malam yaga kayan yagane su fa, Anty tace may zaice Baba tunda rufa mai asiri ne mu kayi da ace mu ji kunya ai gara ace mai munyi irin haka , Balle namiji maishi ba ruwan shi da yawan binciken matan shi, Hakane inji mahaifina yace gaskiya Amarya ban mu da abinda zamu ce maki saidai addu,a Wadda kun kayi, muna ke da mijin ki Allah ya mayar maku da shi alheri Allah yasa wa diyan ku albarka, Sai amin muke cewa irin addu,an da mahaifina ke ta kwararo wa uncle da Anty Amarya na alheri, Kamar yadda mama bata dawo muna da kayan goyon mu ba haka muma ba muyi mata magana ba sai fa da ta tabbatar da cewa Anty Amarya tabar gari sanan ta yarda cewa ai ba kayan aro bane,