Tarko complete novel - Chapter 84
Tarko complete novel Chapter 84: Tarko complete novel Chapter 84. ****** ********** ****** Matafiya sun isa gida lafiya sai dai duk a gajiye suke saboda…
2,956 words
****** ********** ****** Matafiya sun isa gida lafiya sai dai duk a gajiye suke saboda nisan hanya da suka sha, Don haka kowa kokari yake yaga cewa ya samu gurin hutawa, Sun samu gida angyara ko ina anyi masu girki lafiyayye sai kamshi ke tashi ta ko ina a gidan, Fatima tana zaune a falo tasha kwalliya sai kamshi takeyi da kyalli, Idon ta kyam a kofan shigowa falon wanda basai an fadawa mutum ba yasan cewa shigowan maigida ne kawai take dako, Matan ne har da Ramatu suka fara shigowa gidan a cikin gajiya tare da su, Sai da ya dan dauki lokaci kafin ya shigo gidan, Yana saye da rigar shadda mai ruwan brown colour tayi sequsing a lamar cewa ya sha zaman mota da su, Waya yake a lokacin da ya shigo gidan Fatima tana ganin shi ta mike tsaye daga gurin da take zaune, Ta nufe shi cikin wani irin tako da ka saita tana wani rangwada tana karasowa gurin shi, ta rungumay shi, zuwa jikin ta, Bai daina wayan da yake yi ba sai dai dan bubuga mata baya da yayi kadan yayin da take cewa cikin wani irin murya miss you sweet Bukar, Kai ya daga mata ya na mata alaman cewa yaji dadi amna baidaina wayan ba, Salawatu wace ta fito, daga dakin ta don shiga kitchen ta dauko ruwan sha, Sai take ganin irin abinda Fatima keyi ma maigidan wani irin bacin raine ya sauka mata lokaci guda, Da sauri ta kawatlr da kanta a gefe guda tare da fadawa kitchen tana maida numfashin ta, guda guda don kishi, Har ta koma daki Fatima tana lake a jikin Abubakar da yake wayan shi hankali kwance, Bab ta fada sanan gadon ta da karfi tana mai sauke numfashi a hankali idon ta ya kada yai ja, A irin wanan halin itama sadiya ta riske su amma sai ta kawar da kanta duk da taji wani mugun zafi da kishi sosai itama,, Yana gama wayan yadan juya yana ce mata ya kuke ya gida daga haka yasa kai zuwa sama abin shi, Mamakine sosai ya kama Fatima yayin da tabi bayan shi da kallo har zuwa lokacin da ya bace mata dagani, A gurin da take tsaye ta hade wasu miyau masu zafi da suka sulalo mata da ga bakin ta, Hakan yasa tasan cewa akwai magana ke nan a tare da, ita, don Bukar, din ta is not normal Batai fushi ba inda tabi bayan shi zuwa dakin ta samay shi har ya cire rigar jikin shi yana son shiga wanka, singlet ce kawai a jikin shi sai wando, Wanka zakayi tace yayin da take karasowa gare shi cikin wani tako na jan hankali, Ummh yace mata tare da kokarin karasa cire kayan shi, da yakeyi , Ta karaso gab da shi cikin jan ra,ayi take cewa duk gajiya ya wahal min dai kai ko,? Murmushi yayi don yagane nufinta sai cewa yayi barin watsa ruwa ko zanji dadi, Ya shige bathroom yayin da ta dan kara binshi da kallo har ya shige,wankan, Falo ta dawo ta kara gyara ko ina don gurin ya kara yin kyau, Ta kara feshe gurin da turare masu kyau don ya kara daukan idon maigidan da duk wanda ya gani,
Fitowan shi wanka kenan na kira layin shi don naji saukan su gida lafiya, Yadauki wayan a cikin farin ciki mu ke gaisawa inda yake cewa yanzunan nan nake son na kiraki ai naji ya kuke, Murmushi nayi nace kun isa ke nan tun dazun ko, ? Yace ar kasalance don har ina jin alaman zaman shi a bakin gado ta wayan, Maman Boy ya muka barku ina Boy, ? Wani dadi ne ya mamaye min zuciyata saboda kasan cewa tare da shi, Acikin wani sallon murya nace cikin lumshe idona ga boy a kwance yana kewan Baban shi yau, Hmmm naji yace tare da cewa gaskiya ban so ace nima na barku can ba naso ace na dawo tare da ku, Sai dai kuma wanan zancen na tafiyan mu ce yasa na bar ku a can, Cikin yar dariyar zolaya nace ai malam ba zai bari ba na biyo ka a hakan, May ye a cikin don nace zan dawo da iyalina, mu tafo tare, nan, shine zai min fitina, Nan Fatima ta shigo dakin taja ta tsaya daga bakin kofa tana mai wani irin kallon tuhuma saboda yadda taga yana zance a cikin shauki, A hankali ta, tako zuwa gare shi tana takowa tana wani hade yawu masu zafi don takaici,, Zaunawa tayi daga gefen shi inda idanuwan ta suke kallon center carpet din dake a tsakiyan dakin, Har zuwa, lokacin da mukayi sallama dashi tana zaune sai sake sake takeyi a zuciyar ta, Ya dai, ina son nayi sallah, ne ? Cikin wani irin sarkewan murya take cewa dama abinci nazo na ce maka, is ready, Idan nai sallah zan fito muci ai ko sauran sun fito ne su don mu ci, Take fuskan ta ya matse don ita azaton ta daga ita sai shi za su ci abincin,, Amma babu yadda ta iya dole ta shirya abincin muttun hudu,, Ganin ya mike tsaye zai gabatar da sallah, hakan yasa ta mikewa don fita daga dakin, , Yau ta san cewa akwai aiki gurin maigidan yana rike da ita kan zancen wayan su,, Kai kai ashe akwai jan aiki kenan a gaban ta don kawai tai, magana akan meenatu da dan ta, Gaskiya wanan Meenatun ta girma Azuciya Bukar da a kwai jan aiki a gaban ta sosai,. Don ta dauki alwashin, cewa sai ta ga bayan wanan Meenatun a rayuwan Bukar din ta, Batai fushi ba domin yau fushi ba nata bane saboda tana son ta shawo kan dan Bukar din ta, Ta hanyar abubuwa da dama sai faman sake sake take yi a zuciyar ta, Duk yadda ta so ya sauko a ranan ba ta samu sa,an hakaba daga gare shi don gaba daya ya daure mata ta rasa gane kan shi,,
****** ********** ****** Ba,ayan kamar kwana hudu da tafiyan su tafiyan mahajjata yataso don haka duk gida ya rude zancen tafiya saboda da yawan su basu tabbatar da zancen tafiyan mahaifina da Mama Ladi tace bata yarda, yatafi ba, Saidai wani dan uwanta ya tafi a madadin mahaifina don baza tayarda ba da hakan, Saida Baba Buhari yai mata kaca kaca amma bai sa ta janye kudirinta ba gare shi, Sun shirya sunyi bankwana da mutane yan uwa da abokan arziki aka raka su hajji camp har zuwa lokacin Mama sai jidali takeyi, A waya mu kayi Allah ya kai lafiya da su Anty Sadiya tare da Salawatu, don shi maigidan da jirgin yawo zai tafi sabod yanayin aikin su, Fatima ce akabar wa gida inda ta dauko yaranta dukkan su biyu wai zasu zauna da ita su debe mata kewa, har matafiya su dawo, Ba karamin dadi daji ba ganin diyan ta sun dawo gurin ta lafiya, batare da wani hayaniya ba daga dangin mahaifin su da kuma fanin mijin ta, Hakan yasa ta bude wani sabon rayuwa na cinkaren ta babu babbabaka ita da diyan ta Ramatu ta roki maigidan da tabarta ta koma gidan ta har zuwa lokacin da zasu dawo daga saudiya, Haka Fatima da diyan ta suka sakata suna wallawan su gida ya zama na su, sai yadda suka ga dama abin su, Kafin mahaifina ya tafi sai da Yaya Abubakar ya bawa yaya Ibrahim dina kudi yai masu sayayyan komai da zasu bukata na dangin kayan abinci da sauran a bin bukata, Sai dan kudin da zasu a je, domin ,wasu, bukatocin su dashi, Hakan yasa bamu sha,wani wahala ba saboda kasan,cewan samun komai a tare da mu, Gashi kuma sauran iyayyen mu suna bamu kulawa na musan man wada ba mu da wani damuwa, atare damu, saidai kewa kawai, dake damun mu, A nawa fanin kulawa ta musan man nake samu a gurin malam, saboda haka hankalina a kwance,. Jego ya karbe ni dagani har yarona duk munyu bul,bul damu munyi fresh, Yaro na dan sati uku yayi bulbul dashi yana wani kara haske irin na mahaifin shi, Yana samu duk wani taimako da jariri ke bukata daga matan kakana wa yanda ke bamu Kulawa ta musan man daga dangin ruwan zafi ganyen wanka, irin ta yan gargajiya, Harda wani ganye wai lemon daji wanda idan uwa ta bawa yaron ta zai zama mai hazaka da kuzari, Idan Allah ya raya shi baya zama raggo duk inda hazikki yakai insha Allahu sai yaro ya kai gurin, Wanan ganyen lemon Dajin shine Mama Abu take yawan dafawa, take bashi ya sha kuma tai mashi tausa da ruwan, Inda na fara notices din ganyen shi tun yaron yana dan jariri idan ya danki nono sai nayi ihu saboda yadda yake damkan nono,
****** ********** ****** Zan iya cewa wanan tafiyan na mahajjata tankar basu tafi ba don a kullun mu lake da waya da yayana ko Babana , Shi Baba na nice mai yawan kiran shi don kada ya kashe kudin shi, amma yaya Abubakar shi da kan shi yake kirana Musan man ma idan zai sayi wani, abu zai bugo min waya yana tambaya na akan wanan abin,, Zamu iya daukan tsawo lokaci muna kan layi dashi muna hira , Saidai idan naji shiru nasan cewa yana gurin ibada ke nan babu halin na ji kira, Abubuwa masu muhinmanci na ci gaban rayuwa sun faru dani dan wanan zaman gidan da nayi saboda hakan ya dan kawo min shakuwa a tsakanin yan uwa na da ada can baya Kiyayya da ada can baya Mama Ladi ta cusawa mutanen gidan mu a kan mu yanzu a hankali yake wankewa saboda gaskiya dake baiyyana a yanzu, Samarin gidan mu wayanda suke a matsayin yayyena sukan dan zagayo gurina suce sun zo duba Baba karami, Sai su dan dinga wasa da yaron a hanakali idan sun faki idon mutane sai suce, Meenatu don Allah kina da canji na hau yar Vesper banda canji zan tafi wuri kaza Wasu kuma sai su ce min Meenatu kina da canji na dan sayo abu kaza, Ire iren hakan ke saka su kara sona kunsan dama ance idan kana son shiri da uwa to kaso Dan ta zaka ga sakin fuska daga gida,. Yan matan gidan mu duk nai masu gwajon kayan sakawa na wanda Anty Amarya tai min na amarcina, Badon sun tsufa ko su yi wani abuba na basuba a,a kawai dai don ganin cewa, dai yanzu Allah ya hore min wasu saboda haka nabawa mabukata su ma, tunda yanzu nafisu samu, Ba karamin farin jini wanan alherin ya jawo min ba daga cikin yan uwana Kayan dakina na da wanda yaya yacire ya saka muna wasu Baba Wadda ya kwaso min su a tare da wayan anan kayan da na rabawa yan uwana, A dakin mahaifiyana na kafa wanan kayan yayin da na dakin ta muka mayar a dakin mahaifina, Tsab mu ka gyara mai dakin shi kafin ya dawo daga saudiya,,
Ina zaune a gurin dana idar da sallah waya ta dake gefe tai kara hakan yasani gane cewa Yaya Abubakar ne yake kiran Kafin na dauka sai wayan ya katse a lokacin don haka saina rike wayan a hannuwana, Ba,a wani dade ba ya kara kiran layin nawa na dauka acikin wata murya mai saka kasala ina cewa Yayana ni kadai bada kowa ba, Hmmm yace tare da jefomin tambaya da cewa ina kika shigene haka waya nata ringing baki daga ba, Nace wallahi salla nakeyi yaya ina idarwa yana katsewa, Tambayana yakarayi da cewa Meenat har kin fara sallah ne ? Na dan yi dum batare da na bashi amsa ba da sauri, Kara tambayana yayi kamar na farko Nace ai na kwana biyu ina yin sallah Sai naji ya sauke ajiyar zuciya yana cewa ashe tunda kun warke da na dawo sai ku dawo, A take rudani ya kamani don nasan cewa zai iya yin haka ba wasa ba, Kasa magana nayi sai dan inda inda nakeyi din jin muryan shi da nayi yana cewa ko bazaki dawo bane idan na dawo, Subbahanallahi nace yayin da nake tunanen cewa, aiko idan nace zan koma yanzu da nawa ya samay ni ke nan, Muryan shi naji yana cewa yaya ina maki magana baki bani amsa ba Koko so kike sai idan nazo kice bazaki dawo ba har malam ya saka baki, Ajiyan zuciya na sauke tare da kokarin tattaro miyauna guri guda don inji dadin magana, Nace ai sai munyi wata uku kasan kafin mu ce zamu dawo, Stop that please, kin kuwa san irin halin da nake ciki da har zaki ce hakan, Kasa cewa wani abu nayi saboda mamaki don har wani irin hali na tsuci kaina, Mutum mai mata har uku za,a ce wai yana zumudin dawowan na da jegona, Naji yana cewa, look,Meenat dubi fa yadda na lalace na ramay nai wani irin baki, saboda kewan ku, Ke ba kya tausayin nane wai Maman Boy, duk fa rashin kune ya ja min hakan, Shiru nayi ina sauraren shi yayin da naji yana cewa, cikin dan kara tausa murya, Meenatu Watan ki fa kusan shidda bakya a gidana so kike har sai an shekara daya ba kya gidan, Cikin yar siriri yar murya, nake cewa Yaya kayi hakkuri lalura ne, ya kawo hakan, don nima ai ba dadina bane na nisan ta da kai, Amma kin san cewa akwai hakki na akanki daiko, ? Shiru nayi batare dana bashi ansa ba saboda jin irin yadda yake maganan shi, Na rasa may zan ce mai sai kawai naji hawaye suna dan silalo min a lokaci guda, Saboda abinda naji yace wai hakkin shi a kaina abin sai ya sakar min mutuwar jiki, Ban san ya akayi ba ya gane cewa ina hawaye a lokacin don sai ji nayi, yana cewa don nafada maki gaskiya kike hawaye ko, ? Idan nace ban yafe maki ba kin san dai kina da kaya a kanki, Ko so kike sai na zubar da mutuncina nazo da kaina nace zan tafi dake, Ya sallam na furta a zuciyata don sai nake ganin zancen kamar almara yakeyin shi, Mutum kamar Yaya Abubakar cikkaken namiji dan boko mai ilimi kamala da zati ne zai dinga fada min wanan kalman haka, Ga mata manyan mata a gidan shi har uku suna kara kaina a tsakanin su amma shine zai buge da fada min wanan zancen har yana cewa wai na dauki alhakin shi saboda ban tsaya a Abuja ba tsawon wani lokaci, Ranan ba wani hiran arziki da mukayi haka na muka rabu jiki ba kwari don ko dan shi bai tambaya ba, Nai nadama kwarai na fada mashi cewa sallah nakeyi da duk hakan bai faru a tsakanin mu ba, Hakana nake jiki duk yai min sanyi hardare duk na sakawa kaina damuwa, Sai daga baya naiwa kaina fada na cire duk wani damuwa dake tare da ni,
****** ********** ****** Duniya ba kyau wanan tafiyan da Yaya Abubakar yayi yasa wasu daga cikin yan ma,aikatan su kai sukan cewa wai ya kamata a bincike shi, Saboda irin yadda yake abubuwan shi cikin waddata da walwala akoda yaushe, Ba bata lokaci aka shiga binciken al,amura akan yaya Abubakar din wanda bai kasan yana maka gurin sauke farali, Malam Abdullahi masinja ne ya buga ma Yaya waya yana sheda mai cewa an shigo mai office ana bin cike wai Murmushi yayi a lokacin yana Haram yana zaune saman carpet sai murmushine kawai ya sake yana cewa kabar su suyi ikin su kawai akwai Allah,
ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 8⃣9⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL BATIN
JUMMA,AT MUBARAK YA JAMA,ATUL MUSULUMIN WISHING YOU BEST OF LUCK OF THESE BLESSING DAY,,,
Komai izuwa yanzu ya yi kyau a gidan mu don sai kara samun hadin kai mu keyi a tsakanin parents dina, Wanan kuma ya samu asali daga tsohon gidan wanda ke ta kokarin ganin cewa kafin ya kaura yabar duniya ya samu hadin kai a tsakani zuri,ar shi, har abada, Yanzu tsakanin wanan part din da wancan an rage yawan hamaiyya a tsakani sosai, Lokaci guda jikokin gida sun fara kafa zaman lafiya a gidan fiye da tsanmanin shi, Don haka yake wa Allah godiya yau da safe da ya fito ya fito ya samu Baba musa a zaune tare da Baba Hamza suna shawara, Saida ya fito ya samu guri ya zauna a mazaunin shi, tare da dan gyara yan abubuwan da basu zauna daidai ba a gurin, Lokacin ne suka samay shi zaune sukai mai barka da asuba tare da ankwana lafiya,, Nan suke fada mashi cewa suna magana ne akan zance yaron wurin Baba Hamza wanda ke gudun karatu yanzu ya kuma fara bin miyagun a bokai yawo, Malam ya furzar da ruwanda ya gunda a bakin shi don ya kurkure goro yana cewa, Subbahanallahi assha tir, jam, Allah ya tsare ya kare yaushe har haka ya faru baku fada min ba, Duk kan su shiru sukayi saboda basu san may zasu ce mai ba akai, Cikin daurewa Baba musa ke cewa nima jiyane shi Hamzan ya samay ni da zancen, Wai da cewa malamin su ne yazo har gida yana fada mashi irin halin da yaron ke ciki, Shiru malam yayi tare da dan jijiga kan shi a hankali yana mai lumshe ido yace Alkah ya kaimu gobe akwai abinda zanyi, Su kayi wa tsohon sallama suka nufi, wurin al,amuran su na yau da kullun, Wanan maganar ta tsaya wa malam a rai sosai don bai tsan mani samun yaro maratarbiya irin haka ba a gidan shi , Badon komai ba sai kasancewar shi, mai ba da tarbiya a,cikin shiya saboda akasarin yaran uguwar mu a gurin malam suke saukan Al,Quran mai girma,