Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 96

Tarko complete novel - Chapter 96

Tarko complete novel Chapter 96: Tarko complete novel Chapter 96. ****** ********** ****** Dakin babu kowa aciki kuma gashi tana son juyawa sai dai bazata…

3,426 words

****** ********** ****** Dakin babu kowa aciki kuma gashi tana son juyawa sai dai bazata iya ba, Don haka a gurin da take kwance tasake, fitsari don matsuwan da tayi , saboda, hannun ta akwai, drip,, Yaya Abubakar ya shigo dakin shida Lawal, mijin Fattu, zarnin fitsari ne ya daki hanncin su, a lokaci guda,, Ga Anty Mariya bata a dakin basu san inda ta nufa ba, a lokacin,, Babu hali a matsayin su na maza su taimaka mata, surabata da wanan kayan na jikin ta da sauran su, Cikin ikon Allah sai gani na iso dauke da kayan su da naje dasu gida na wanke, A bakin kofa na samay tsatsaye ganin yanayin su ya tayar min da hankali don sai nake tsan manin ko wani abune ya faru da Mama din, Tambayan su nake a gagauce ko lafiya cikin dan bata rai yake ce min, Mama duk jikin ta ya baci gashi kuma Mariya bata dakin, Subbahanallahi, da sauri na fada dakin inda na samay ta duk ta bata jikinta kace, kace, Ba bata lokaci na shiga gyara mata jiki ta ko ina, duk sai da na gyaro na kuma ciro turare daga hand bag dina na fesa ko ina na dakin take gurin ya canza, kamar bashi ke wari ba dazun, Mama da duk jikin ta babu lakka sai bina da idanuwa take har na gama gyara ta, tsab, Nafito da kayan da ta bata daniyar naje na wanke su a lokacin Anty Mariya ta dawo tana cewa ashe kun zo ne wallahi ina can ina kallon wasu da sukayi hatsari aka kawo su wancan dakin, Cikin bacin rai Yaya Abubakar yace haba Mariya may ranan zaman ki a nan da har zaki tafi kibar mara lafiya acikin wani irin yanayi na naiman taimako, Irin halin da muka samay ta a ciki ba don Allah ya kawo muna Meenatu ba da ya zamuyi da ita, Gurin da nake ta ke kallo tana kallon kayan da na debo zan tafi na wanke, a famfo, Ki aje kayan ta wanke su, Yaya Abubakar ne ke fada min haka, Cikin ladabi nace a,a Yaya bari kawai na wanke ta dan huta yau, Baiso hakan ba amma sanin cewa nima yata ce Anty Mariya yasa shi yin shiru, Dakin suka koma yayin da na wuce don wanke kayan kazantan da mama ta bata, Sun samu, dakin tankar ba shi ba saboda yadda na tsabtace ko ina na dakin cikin dan kankanin lokaci, Mariya ce tace ikon Allah lalai Meenatu tasha aiki dakin gane ya koma haka tsab, Tunda nadawo daga wanke kayan nasamu tabarman dake a gefe na zauna, ina waya da Anty idon Yaya Abubakar yana a kaina, duk na dago idona sai munyi arba dashi ban san may yake kallo a jikina ba, Stil ina kara daga ido muka kara hado ido da Yaya Abubakar, naga ya sakar min wani tsadaden murmushi, wanda yasani dan lumshe idanuwa na, Kaina na kawar gefe guda cike da mamakin wanan kallon kurullah da Yaya Abubakar ke min, Kamar may rada yace min kibawa Lawal key din motar ki zaikai ai maki service, Kaina na gyada alaman toh ina kokarin ciro key din motan daga jakata, Ba musu na mika ma Lawal din keys din motana yafita kamar yadda aka umurce shi dayi, Dakin ya rage dani dashi da Mama da take daga kwance,saman gadon asibitin fuskanta yana kallon saman dakin, Dan yunkurawa tayi kamar zata mike sai kuma ga amai yazo mata da sauri na mike nazo gaban ta tare da tara mata kwanon asibiti don tayi ciki, Amai sosai Mama tayi duk ta galabaita zaban tausayi sai sannu muke mata, Yaya Abubakar suka shigo tare da likita inda yadan duduba ta daga karshe yace muna ai reaction ne na alluran da ake mata, Ranan bamu bar asibiti sai bayan sallah isha i ga Fatima wace ke ta faman kiran shi a waya tana cewa wai yana ina ne, Bai bata amsa ba sai tsukin da yaja kawai, tare da cewa Polish woman, kawai mara hankali da tunane, Wacece wai Anty Mariya ce ke tambayan shi, tankar ba da shi take ba don ko kallon inda take baiyi ba balle ya bata amsa,, Muna a zaune munyi shiru ba mai cewa komai daga cikin mu, Bayana na jingina a bangon dakin don naji dadin zama da kyau, idona yana a kan Mama wace ke barci a hankali take maida numfashi, Dan motsawa Mama tayi kadan naga ya mike zuwa bakin gadon yana dan duban ta, Ya juyo inda nake zaune fuskan shi babu walwala acikin ta ko kadan yace, muje na saukeki gida kada Amir yayi kukan nono, Kala bance ba nafara shirin mikewa, don tafiya kamar yadda yace, din, Yace wa Anty Mariya mu zamu tafi amma kila zandawo anjima, Anty Mariya tace, ai dama ka zauna abinka tunda Mama ta samu lafiya,, Mu kai masu sai da safe muka barsu a dakin ba tare da mun so tafiya ba,

****** ********** ****** Mun fara tafiya naji Yaya Abubakar ya da hura iska daga bakin shi, yace, cikin kasala, akwai abinda kuke bukatane a part din ku, Nace cikin dan rausaya eh to gaskiya kayan tea mu ya kusa karewa, da kuma spices din mu, Motar ya karkata zuwa shopping plaza don mu sayi abinda bamu, dashi a gida, Sayayya sosai mu kayi, a wanan plaza din muka fito zuwa, gida duk a gajiye, mu ke, A falo muka samu matan gidan namu gaba dayan su a zaune Kallo guda zakai masu kagane cewa rayukan su a bace yake a lokacin, Sam ban damu da su ba tunda babu wace tai min an dawo lafiya daga cikin su, sautin takalman kafana da ya cika ties din fallon da kara yasa aka dinga watso min harara Ledojin da mu kayo sayayya su Aminu friends din su baba Hamza suka kwaso zuwa part dina, Ina shigewa shima maigidan ya shigo a gajiye, bai tsaya ta kan su ba sai ko karin hayewa sama yake abinshi ba, tare da ya tsaya, ta kan su ba,, Fuuuu Fatima ta tashi tabi bayan shi atare suka shiga dakin nashi, Inda take cewa ashe kana can tare da Meenat shine nake ta kiran waya ka ka kyaleni , Na kyaleki ne don banga amfani daukan wayan da zanyi ba naki tunda har kinsan inada mara lafiya a assibiti, Tunda ba mahaifiyarki bace may zai sa ki damu da rashin lafiyan ba, ai,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 9⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH,MAALIK UL-MULK

Na kyaleki ne don banga amfani amsa maki call din ki ba , don amsawa ai ba dole bane ko tsaye tayi sororo tana kallon ikon Allah, Yace a hasale da ace mahaifiyar ki ce a asibiti ai da yanzu baki zauna ba, ina ranan cewa akayi bata jin dadi amma yini kikayi kina waya a gidan nan, Gani maganan shi in serious yakeyin ta idan tace zara bijiro mai da zancen fita da Meenatu zaita sa zancen yakai wani high level , Don haka dole badon taso ba ta ja bakin ta tai shiru, don gudun bacin ran miji, Amma tana fitowa daga part din shi muka hade a falo ina son na dauko, abu a store din mu, Sai ji nayi tana cewa, idan dai mutum yace shi dan daukan alhaki ne sai ya matsa yai tacin hakin yan, uwa yagani, Duk da bata ambaci suna ba nasan cewa dani take wanan zancen amma tunda bata ambaci sunana ba sai kawai na share ta, Taci gaba da cewa don gadara har aiwa mutum sayayya shi kadai bada yan uwa ba, Salawatu tace haba maman Aina, ai kawai kiyi shiru kibar wanan zancen, don bai da amfani, fadi, A hankali na dubi Salawatu a cikin mamaki don na fahinci sun hada kai kenan a kan zancen, a kaina, Inda Sadiya take tsaye a bakin TV na kalla sai naga tai min alama da inyi shiru murmushi nayi kawai don nasan fitina suke so, Wanan cin amanan ai sai ke don kece mai son yin babakere da abin kowa, Muryan maigida ne daga bayan mu yake cewa hakan, Gaba dayan mu muka juya inda yake saukowa daga steps din a hankali, yana mai gyara hannuwan rigar shi da kyau, Idanuwan mu duk a kan shi kowa na bukatan son jin mai zaifada daga karshe, Fatima kina son ki sake min dokokin gidana da mugayen halaiyar ki da kika saba da su, Wanan abin da Yaya Abubakar yakw mata yana ci matarai sosai don ita bata bukatan ace, yana saka bakin shi ga zancen matan gida, Shiko a nashi bangaren baya kaunar wanan irin mugun halin kishin na Fatima , Tana son kawo mai rudani agida don babu wanda bata fada dashi a cikin abokan zaman ta, Kafin ya karaso ta sa kai zuwa cikin part din ta buguzun, buguzun tana magana a ciki ciki, Dakatawa yayi daga step din karashe ya rakat da harara tare da sake tsuki, A inda muke tsaye yadan juya yana kallo yace zan koma asibitin naga ko ta farka, yanzu, Sai a lokacin suka fahinci cewa mun dakata ne asibiti saboda jikin mama da yai tsami, Daga inda nake nake cewa bari na kara masu zannuwa koda za,a bukaci hakan ko, Yace, hakan na da kyau tunda batasu takeyi da zaran an canza mata shi, Daki na shiga ban wani dadeba nafito da ledan zannuwa harda, dan abin tabawa nace a kaiwa Anty Mariya, Ganin zai kara fita zuwa asibiti yasa Fatima bin shi da kallon mamaki don baya fitan dare haka, Sadiyace gab da zai fita take cewa yau jikin na Mama ya matsane ko, Daga inda nake tsaye nace a hankali yau jikin na mama gaskiya ba dadi, don maganin da ake mata allura yana bata reaction sosai wallahi, Fatima wace take daga kofan shiga part din ta tana sauraren mu sai jikin ta yai sanyi, Don sam tunanen ta bai kawo mata cewa asibiti muke ba tun dazun, To amma idan hakane, wancan ledan da ta shiga dashi daki na may ye shi, A hanya ke nan ya tsaya yai mata tsaraban shi ke nan, ko, koma nay ye a cikin shi dai ai, zai bulla,

****** ********** ****** Tuki yake yana waya da Aliyu wanda ke tambayan lafiyan jikin Mama Ladi, A hankali ya kira sunan Aliyu inda yake sheda mai cewa gaskiya halin Fatima ya canza a yadda ya san ta da farko, Subbahanallah tayi ma wani abin ke nan kumà ko ? Nan yake fada mai irin abubuwan da Fatima take mai wa yan da basu dace ba sam, a rayuwa harda rashin kula mahaifiyar shi da bata yi dama kowa nashi, Aliyu jikin shi yai sanyi don jin abinda ake fada akan yar uwar shi duk kunya ya rufe shi don baima san ko may zaice, ba, Hakkuri ya fara bawa Abubakar inda yake cewa zai yi magana da mahaifyar su don ta kara tsawata wa Fatima din, Ya isa asibitin ya samu Mama ta farka daga barci maganin ya dan saketa Inda take ya wuce direct har bakin gado yadan rankwafo yana mata yaya jikin tare da dan yi mata tambayoyi akan yadda, take ji,, Ledan hannun shi ta mikawa Mariya yace ga shinan wai a kawo maku inji Meenat ta karba tare da budewa da sauri, Peppe soup din kassan rago ne yaji hadin kayan gargakiya sai kamshi ke tashi daga cikin sa, Sai zannuwan da na aiko masu dashi daga cikin zannuwana, don su samu na canzawa, A hankali Mama Ladi ta dan lumshe idanuwan ta tare da sauke ajiyan zuciyan A cikin plate Anty Mariya ta zubo mata da yawa, tare da drinks Kafin wani lokaci Mama ta lashe shi tas tare da shan ruwan drinks din da aka zouba mata, Ya Abubakar yana daga gefe guda a zaune yana latse latsen wayan shi tankar baya kallon abinda ke faruwa a dakin, Ya dago kai a cikin sauke ajiyan zuciya yana tambayan Anty mariya cewa jikin na Mama bai kara yin zafi badai ko ? Mama da kanta tai yunkuri ta dan mike zaune tana cewa tun Aminatu ta goge min jiki da ruwan sanyi ban kara jin zafin jikin ya dawo ba, Hmmm kawai yace ba tare da ya furta wani abuba don abin dariya da mamaki yaba shi a ran shi wai yau Mama ce da kanta ke cewa wai Meenatu ta taimaka mata taji sauki, Amma a fili sai cewa yayi, yanzu tunda har kin sha wanan ai saiki kwanta ki barci ki huta ko zaki kara samun sauki, Babu bata lokaci Mama kamar karaman yarinya ta dan koma a hankali ta gyara kwanciyar ta, bai bar dakin ba saida ya tabbatar da cewa Mama ta samu barci mai nauyi yai ma Anty saida safe ya dawo gida, A lokacin shabiyun dare har yadan gwauta amna abun mamaki a falo ya samu Salawatu da Fatima zaune wai suna kallo, A ran shi ya ja tsuki ya haye sama abin shi Fatima wace dama a cikin shiri take ta mara mai baya, Salawtu ma yar ganin kwam bata wani dauki lokaci ba ta kashw wutan ko ina itama ta shige nata part din,

****** ********** ****** Washe gari ina idar da sallah na koma na kwanta saboda yadda na kwana da ciwon kai da zazzabi mai karfi, na damuna, Ga gabobbina duk ciwo suke min agajiye nake jin jikin nawa ba dadi, A cikin bacci na rika jin ana dan kiran suna na sama sama, nadan rika jin muryan Yaya Abubakar yana cewa Meenat, Meenat na farka adan firgice, A cikin karfin hali na bude idanuwa na nagan shi a tsaye saman kaina dauke da Amir a hannun shi, Lafiya kike yatambaya cikin kura min idanuwan shi lumsarsu, da ya kashe ni da su, Da kyat na iya bude bakina ina cewa ban jin dadi ne yau da zazzabi na kwana, Ido waje cikin nuna damuwa take cewa may je damun ki ne wai haka, saida na dan musguta kadan na gyara kwanciyana nake cewa zazzabine kawai ke damuna, Ina Ramatu ta shiga ne ga yaron nan ko wanka ba aimai ba ga hannun Aisha ma na karbe shi a falo, Cikin dan tausa murya nace Aisha Aisha tana ina ta kira min Ramatu a back yard, Baice komai ba naga ya fita da yaro sagale a kafadan shi yana mai wasa, Ramatu ce tashigo dakin cikin dan rudewa tana cewa Uwar daki bakya jin dadi kuma yanzu Alhaji ke fada min ina can muna gyaran gida, Nace Ramatu don Allah yiwa yaran nan wanka ki basu abin karyawa su karya, Tace to amma kema din aida kin tashi kin yi wankan ki samu abinda kikaci sai kisha magani ko ? Kai kawai na iya gyada mata tare da dan juyawa na gyara kwanciya na, Daga haka barci ya kara daukana bayan Ramatu tadawo dakin taga irin yanayin danake barci sai na bata tausayi, don duk wani yanayi na jin jiki ya baiyyana min, Na farka tare da jin yuwa bathroom na shiga, nai wanka tare da dauro alwala wanan dabi,a nane yin alwala bayan wanka, Na idar da sallah daga zaune nagyara jikina inda namike tsab zuwa gaban mirror ba wani kwalliya nayi ba mai kawai na shafa na zura wata doguwar rigata mai yar guntuwar hannuwa ta gaban shi da fadi, Gyalen kayan na tsuke kaina a cikin sa tare da, dan shafa mai a bakina, Yaya Abubakar ne dakin tabayana naji ya rungumay ni a hankali, Abinda ya haddasa min lumshe idanuwa na ke nan a hankali, A sake nace a hankali Yaya love ina kwana Saida ya dan rugumoni sosai zuwa jikin shi yace a hankali daidai saitin kunnuwana yace, Sweet sister jikin ki da zafi mana ko har yanzu zazzabin ne, Wani irin amaine yazo min a daidai lokacin da nake kokarin bude bakina na bashi amsa,, Kokarin jaye jikina nakeyi daga gare shi amma ya rikeni tamau, Jin ina kakarin amai yasa shi sakina da gudu na fada bathroom dina, Amai sosai na ke ji amma sai kumfa kawai nake zubuwa don babu komai a cikina, Yana zaune a saman gafon dakina har na fito ina cewa wassh Allah na, o,o wai, na fada gefen gadon a hankali tare da dan noke kaina a filo, Meenatu naji ya ambaci sunana yana cewa cikin dan bubuga kafan shi a hankali saman ties din dakin, Saka hijab dinki muje asibiti yanzun nan ga Lawal nan zai fita da mota, Sai a lokacin na dan dago kaina a wahalce nace basai naje asibiti ba ai zai bari insha Allah, Fuska a murtuke yace min ki tashi ki saka hijab din ki nace maki, Mikewa nayi daga kwancen da nake ina cewa, Yaya aman zai bari ai a cikin yar shagwaba, Yace kina son sai nayi fushi zaki tashi ko , Hannu nasa nadan dafashi namike daga zaune da kyau ina cewa zan sha tea yunwa nake ji, tukun, Mikewa yayi don kiran Ramatu a falo yasamu mutanen gidan kamar wasu masu jiran fitina, Sadiya ce kawai bata a cikin su amma su duk suna zaune dagani masifa suke ji, Bai ko kalli inda suke ba ya kecewa Lami ta kira mai Ramatu a waje,,, A lokacin ne Lawal ya shigo gidan yana masu ina kwana Yaya Abubakar ke ce mai, kabari ta yi breakfast don ba komai a cikin ta , Kallon, kallo suka fara yi a tsakanin su, suna mamaki da tuhuman ko may ke faruwa, Cikin son jin kwam Salawatu ke cewa lafiya dai ko dakin Maman Amir, Dan kallo ta yayi kamar zaiyi magana, sai kuma ya kawar da kai ba tare da tace uffan ba, Inda ya barni zaune da farko a nan ya samayni zaune Ramatu tana kada min tea, Yadda nasha tea din haka na amayar dashi atake kuma na fara dan fita hayacina a hankali, Da sauri, sauri yafara kiran sunana acikin dan firgici, Da sauri ya kamoni inda a daidai falon gidan yake cewa Lawal, tayar da mota mutafi, Cirko, cirko su kayi, suna kallon mu yadda duk Yaya Abubakar ya rude da yadda na koma, Saida su kaji cewa mun wuce, asibitin Fatima tafara cewa tau wani sabon kuma yanzu don kawai maigidan hankalinshi ya koma agareta shine takirkiro ciwon karya, Salawtu ta tafa hannayen tana, cewa ai, zakiga abu agun wanan yarinyar small girl da ita amma ta, iya abin manyan mata, Wuri ta samu inji Fatima, tana cewa, wallahi, sai nayi maganin shegiyar yarinyar nan yar iska kawai muna fuka, Jifa yadda tawani langabe kanta a kafadan shi ita a dole mai,wayyo munafukan yarinya kawai, A lokacin Sadiya ta shigo falon da alama abu zata dauka tana da daura gaba na zani da dogon rigar barci a jikin ta, Batare da tace masu uffan ba, , zata shige taji suna cewa towai ma may yasamayta hakane adaren jiya lafiya kalau fa suka shigo gidan nan a tare, Kitchen ta shiga tafito dauke da goran ruwa tana cewa har yau zancen fitan su Meenatu din ne, Ina a sibiti suke ance jikin Mama ne ba dadi jiyan ma duk ta bata jiki sauda ita Meenat tai mata wanka, Kin,gani ko, ai in tace iyeiyene gashi nan yau, tajawa kanta ciwo, Waye ba lafiya kuma Sadiyace ke tambaya a dakile, Salawatu tace Meenatu mana, Meenatu kuma may ya samay ta yau din ke dai fadi, Yanzu akafito da ita a kafada wai za,a asibiti ta kwana tana amai, Amai Sadiya ta tambaya a gagauce amai fa kedai wani irin dassss taji azuciyan ta kada dai ace wanan yarinyar wani ciki ne kuma ta kara samu, again, A take yanayin ta ya canza sai cewa tayi a fili watan danta nawa yanzu wai, Fatima tace what ke kada dai ace ciki yarinyar nan ta kara samu, Aiko da abin ya zama zalama Ciki da wanan dan karamin yaron haka, Daga haka Sadiya ta wuce tana cewa, Allah ya kyauta amna zuciyan ta tana mai tir da halin uwar ta koda yake idan tai imani da Allah kila dama ba zata haihun ba uwar ta Hajja dai ce ta saka nata ruwan a ciki, Ramatu tafito da Amir goye a bayan ta yana barci, da alama ya dan jima yana barcin, a bayan ta, Gaba dayan su suka watso mata idanuwan su akai, Salawatu ce cikin muryanta hausa gwarigwari take cewa, Ayya Ramatu yaron yana barci ne ko baida lafiyane, Ramatu ta fahinci may suke nufi wani gulma,ne suke son yi don haka tana cewa kalau yake kawai ta shige abinta, fuuu,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull