Kenza eBookz

Tarko complete novel - Chapter 97

Tarko complete novel - Chapter 97

Tarko complete novel Chapter 97: Tarko complete novel Chapter 97. ****** ********** ****** Kwance nake drip din ruwa tan shiga jikina daga kafan hannuwana…

3,274 words

****** ********** ****** Kwance nake drip din ruwa tan shiga jikina daga kafan hannuwana a hankali, Yaya Abubakar yana tsaye a gefe Maman Biu tana rike da hannuwan nawa, Likita ya shigo dakin da farar takarda da a hannun shi yana dan dubawa, Yace cikin gyara farar glass din dake idon shi, yana may mika wa Yaya Abubakar hannu, Yace, bata farka ba har yanzu suka amsa mai da cewa eh. Yace saboda alluran nan na amai da akai matane yasata wanan barcin , Amma shi lamarin ciki hakan yakan zowa wasu da wahala sai zuwa karshe a samu sauki, Jun ya ambaci ciki yasa Yaya Abubakar saurin kallon likita acikin mamaki,, Likitan yace, hakane maigida ciki ne na Sati shidda a jikin ta shike bata wahala haka, A sake ya juya yana mai kallona cikin tausayawa yana kallon yadda nake sauke numfashi a hankali, Maman Biu dake gefe rike da hannuna tace haba nima nayi tunanen wanan abin ko cikine, Shiru Yaya Abubakar yayi, na dan wani lokaci yana mai kura min ido kawai, batare da ya kifta ba, Wani irin so da kauna nane ya ke shigan shi a lokacin ga tausayi ga kuma murna da yakeyi min a lokaci guda, Har kwana biyu ina asibiti inda nake samun kulla daga maigyaya da kuma maman biu da Antyn Saloon, Daga bakin anty Saloon nake jin cewa ciki ne ga jikina inda hankalina yai mugun tashi sosai alokaci guda, Sai nake ganin cewa zan rasa Amir ke nan tunda yasha ciki a wanan stage din, haka, Sai addu,a nake raina cewa Allah yasa cikin ya bare kowa ma ya huta, da shi don ban san yadda zanyi daciki ba ga yaro karami haka wata takwas yake batun shiga Yau ma kamar kullun kowana barci niko ina kwace ina tunane barci ya ki zuwa min, A hankali kuka yadan fara zomin ina tunanen yadda zan zauna da matan gidan mu ga fitina ga goyo ga ciki, kuma, Muryan Mama Biu naji tana cewa haba Meenatu kina son kinunawa Allah cewa baki godewa Allah irin baiwa da kyautar da yai maki bane, Addu,a zakiyi kuma ki godewa Allah dayai maki wanan baiwar don baiwace daba kowace mace ke samun hakan ba a rayuwan ta, Abin alfahari saidai mata basu ganewa cewa wanan ai wani gatane Allah kewa mace, Tayi haihuwan ta alokaci guda ta kare yaranta su taso kan su guda gwanin sha,awa Yanayin maganan Maman Biu ya saka zuciyana yin sanyi inda nadan fara goge hawayen dake fito min a hankali da bayan hannuna, Muryan Anty Saloon wace nake zaton barci takeyi tace idan zaki zage kikula da dan ki da kuma cikin dake jikin ki dake kan ki har mijiki da ya fi maki alheri Don yanzu haka da zaran kishiyoyin ki sun samu labari zakiga sun tayar da hankalin su zasu ce ai kece kawai matar so, ga maigidan ku Tsawon wani lokaci suna kara bani hasken rayuwa ina sauraren su a hankali, Nace ni yaron nan ke bani tausayi wallahi sukace ba wani tausayi ki fara bashi multivitamin madu kyau masu gina jiki nikuma zan samo mak nq gargajiya masu kyau sai adinga bashi a hankali har zuwa in da za,a yaye shi, Ajiyan zuciya nayi don jin na samu mafita akan Amir addua kawai ya rage min yanzu akan al,amarin,

Washegari aka sallamay ni na koma gida da saidai har zuwa lokacin ba, da karfin jiki don haka muka zauna tare da maman Biu, A lokacin ba fita nake sosai ba amma duk da haka da girki ya zagayo a kaina dole nakarba don maigidan yace nayi, Badon komai ba nasan don ya samu kebawa danine muyi zancen, ni dashi, A hankalina shirya jiki ba kwari nasab Amur akadata muka hau sama zuwa turaka, Nasamay shi zaune abakin gado saye da bathrobe din shi a tunanen shi bazan shigo dakin ba, Yana ganin mu yamaida kallon shi a garmu, yana maidan jijiga kan shi, Na zagaya na shimfide yaron sanan nadawo kusa da yayana na zauna a hankali, Nan ya bude baki da nufin magana kenan aka kira layin wayan shi inda yai shiru yana kallon wayan nashi Ganin haka yasani dan kwantawa a hankali kafin yakare wayan nadhi,

ZEEE MAKAWA YELWA

🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 9⃣8⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH DHUL JALAL WAL lKRAM,,, ,,,,,,,,,,,,,

JUMMA,AT MUBARAK TO ALL MUSLIMS UMAH IN THE WORLD MAY ALLAH BE OUR NEEDS PROVIDES ALLAHUMA AMEEN YA ALLAH👏👏

Idona a rufe suke har zuwa lokacin da yafara karba, wayan ahankali kaman wanda baya son naji may yake fadi a wayan, Idon nawa a rufe tankar mai barci nake jin yana bada amsa da cewa Yanzu dare yayi amma tunda jiwane kawai maishi ta bari har zuwa safe sai su tafi asibiti,, Hakan yasani gabe cewa daya daga cikin matan shine yake waya da ita, mai shi tana bukatan ya kai ta asibiti ne a lokacin, Ban san may tace ba sai naji a cikin daga murya, yana cewa na fada maki dare yayi yanzu saboda juwa babu inda zan tafi yanzu, Wayan dai ba,a kareshi da dadin rai ba don, da fada aka karasa shi, don yace bazai fito ko ina ba, Ina dunkule guri guda saboda irin yanayin da nake jin jikina ba kwari, Hannuwan shi yamika daidai wuya na yadan shafa a hankali inda jikina yai dan dumi, alaman akwai zazzabi a tare dani, May ke damun ki yanzu kuma saida na dan gyara kwanciya na a hankali sanan, nacd bakomai. Ok kawai yace naga ya mike yaje gaban mirror, Yadauki dan lokaci tsaye a faban mirror hannu shi rungumay, a kirjin shi, da alaman tunanen wani abu yake a lokacin, A hankali ya dawo ya zauna a bank n gado tare da dan duban wayan shi dake gefe guda,, Dan rage muryana nayi ina cewa waye baida lafiya ne wai, A takaice yace min Fatima ce fita batun ta magana take nema zanyi maganin ta, Cikin murya ta mara lafiya nake cewa, ai da ka dubata kaga ko may ke damun ta cikin daren nan, Gyara kwanciyan shi yayi tare da fara karanto addu,an kwanciya a cikin yar murya, yashafa a jikin shi da namu, Ya juya ya rugumoni izuwa jikin shi yana sauke ajiyan zuciya kawai, Idanuwana na gyara lumshewa, tare da jin wani son mijina a raina, inda na kara makewa a cikin jikin shi daga haka barci ya dauke mu

****** ********** ****** Na dauki wani lokaci ban sauko ba daga sama saboda irin yadda nake jin jikina, Don nasan cewa ko na fito ba wani abinda zanyi hakane yasakani kwanciyana kawai, Ramatu ce mai min komai daga abincin da ake kaiwa su mama har wanda zan bawa maigida, Ramatu wace ke kasa itace ke ganin darama a gurin matan gidan don wanan tafito ta wuce fuuu, wanan ma tazo fuuu da ita, Sai da Amir ya fara kukan neman abinci na tashi na sauko a lokacin har yaya yai ma yaron wanka ya shirya mn shi tsab da kayan shi dake cikin baby bag din mu, A yayin da zan fito daga part din na Yaya Abubakar a falo na samu su Salawatu, kamar masu yin wani abu, Wanan ba wani bakon al,amari bane daga halaiyyan su domin inda sabo ai na saba ko, A daidai tsakiyan falon gida, naji muryan Salawatu tana cewa wai wani sabon salo kuma, Wanan ai zalunci ne ace wai kirikiri ake nuna wa mutane fifiko ko dan uwan ka baida lafiya ba a kula da mutum,, Tankar ban fahince ta ba nasakai zuwa dakina don banda lokacin ta ni, Ina shiga Ramatu ta samay tana min sannu ya jiki, Na bude baki da nufin magana, kenan aka turo kofan dakina, Gaba dayan mu muka maida duban mu ga kofan dakin don ganin ko waye mai shigowa Ya Abubakar ne dauke da Amir a kafadan shi yana cewa Ramatu a bashi madara yasha don Allah, Don kada ya damu Maman nashi da tsotso tana fama da kan ta ne ita, Dan guntun murmusawa nayi kawai ba tare da nace mai komai ba, Yacewa Ramatu don Allah itama a bata abinda zatayi break tasha maganin,ta, Har zai fita sai ya ja ya tsaya yana cewa au don Allah kibawa Big man maganin sa kamar yadda suke, a rubuce, Ta kara amsa da tau sabbaynil yanzunan insha Allahu zanbashi, Bin shi nayi da kallo cike da jin tausayi, shin ganin irin yadda duk ya shiga damu a kan mu,, Inda Amir yake zaune a gefena na kalla sai yaron kuma ya bani tausayi sosai, Nono yake bukata don haka daga kwance na bude mai yafara tsotsawa a hankali ya saida na tabbatar da cewa ya tsoho sosai nacewa Ramatu ta tafi dashi ta kara mai da madaran shi, Ina daga kwance nake mamakin yadda akayi babu wace ta iya yi min sannu, daga cikin su har izuwa yanzu dama Sadiya takan ce a,a ki mike fa kodai kina taya, mamanki ciwo ne, Murmushi kawai na keyi, idan tace min haka sai takan dan yi wa Amir wasa ta wuce,,

****** ********** ****** Zai fita daga gidan ne yaji muryan Fatima tana cewa, aini wanan mutumin ya bani mamaki sosai wallahi, Duk da na samu dubara mai karfi don na rama amma wai mutumin ga shine yai kemay may yafita batuna yace bazai fito ba wai dare yayi a lokacin, Salawatu tace ai na fada maki cewa, bazai fito ba kika dauka magana tace kawai, Kai kawai ya girgiza tare da ficewa gidan batare da sungan shi ba daga inda suke zaune suna hiran, Asibiti ya wuce direct gurin Mama don ya duba su da kwana duk da tana sa ran cewa, za,a sallamay ta kwanan nan insha Allah, Ya samu Mama a zaune bakin gadon asibitin tana dan shan lemon da aka wade mata a hankali, Yana shigowa dakin suka gausa inda yai dan mata tambayoyi akan jikin nata tace da sauki, Abin mamaki sai yaji muryan Mama tana cewa yajikin ita Amina kuma, Sai da yadago kai ya dubeta sanan yake cewa tasamu sauki sosai itama don tafara warwarewa yanzu, Anty Mariya daga gefe tace Allah dai yaba ku lafiya gaba daya, A hankali Mama da zata kai lemo abakin ta ta amsa da fadan amin, Hira suke yi na mutanen gida inda suke tuna wasu abubuwan da ya faru a baya, Baba Wadda wanda ke daga gefe guda yana dan fuskantar wayan shi yace amma idan Meenatu zata haihu wanan karon anan zamu tsaya ayi suna ko? Cikin wani irin murya Mama take tambaya ita Amina shin ciki na gareta kuma, A,a Mama ? Inji Anty Mariya tace wane irin tambayana haka shin,, Shiru tayi batare da tace uffan ba sai sai hira ake amma ita bata samu abinda ta furtaba again, Iyanzu ya fahinci cewa akwai wani shiri na makirci a tsakanin, Salawatu da Fatima wanda yasan bawai wani shiri bane na alheri su ke yi,, Tsakanin Sadiya da Meenatu kuma akwai dan alaka amma ba mai tsawoba don kowa a dakin ta take zama sabanin irin nasu Fatima da Salawatu, Amma yasan cewa ajuri zuwa wanan tafiyan ba mai dorewa bane, Ranan da suka tabbata da zancen cikina a ranan kamar zasu yi hauka, Salawatu tace wai kina nufin cewa wanan yarinyar cikine ta samu ma wahal da ita haka dama, A take idanun Salawa ya juye lokaci guda tankar mashayiya, Wai da gaske kike Fatima wanan labarin kodai wasa, ne wai don ni abin yq fara bani tsoro wallahi, Fatima wace ita,ma ranta a bace yake a lokacin, cikin hasala take cewa, ni ba yau ba nasan makircin yan uwan Bukar sam basu kaunan suga bare a tare da su, Salawatu dai barin gurin hiran tayi don yau duk a jagule take bata jin ta daidai ta rasa may ke mata dadi, a ranta, Gidan Lubuna ta nufa a cikin bacin rai can taje da tashin hankalin ta, duk ta dagawa kanta hankali, Ita ko Lubuna sai cewa tayi amma wanan Meenatun yar yawace yanzu ita kamar ta big chika zata tsaya tana wani yin ciki har kurkusa ma haka, Wani irin harara ta watsa ma kawar ta tana cewa wallahi ke wani lokaci banza ce ana zancen gaskiya sai ki tsaya ki na shirma, Haba Salawat ki duba fa ki gani dubi irin, yadda yarinyar nan t hadu ta koni Ganin yadda hankalin aminiyar ta ya daga yasata yin serious cewa, yanzu sai mun shirya mutafi can cikin Masaka akwai wani sabon shigowan malami, Wanda zamu shiga gurin shi don mutabbatar da cewa cikin yafita ko kuma ya sanyadda zai yi da ita, Salawatu taji dadin wanan shawaran na aminiyar ta sosai don haka suka aje ranan da zasu tafi Masaka gurin malami, A guje ta jawo mota zuwa gida ranta a bace duk ta rasa may ke mata dadi a ranta, Ita ko Lubna wani irin haushin Meenatu taji duk wani plan da tanadi da take a kan jan ra,ayin Meenatu sai taji kawai tayi watsi da shi yaushe wanan Yarinya karama zata zauna taita haihuwa time to time irin haka, It means bata da lokacin kan ta again sai na family kuma, don haka taja dogon tsuki tana cewa banza kawai, Yarinya may zaki gane a gurin maza banda haihuwa dama may suka sani suka iya da zaki tsaya bata kan ki agare su balle wanan busurun mijin naku wanda ya tara mata a gida kaman zai kaisu kurmi ya yasayar, Haka tai ta fadan haukan ta ita kadai a gida kaman wani ya sata ko ance tayi, sai kuma daga karshe haushin Salawatu ya zo mata duk tabi kanta ta susuce gana miji guda haka, Sai kudin ta take narkawa a kanshi wai kawai don ya so ta amma abu ya gagara da farko dai sunyi nasara samun kan shi har ya auri Salawa din amma yanzu duk ya birkice masu duk wani hari da suke kai mai kamar sun shuka dussa ne, Ita kuma Salawa din taki yarda ta hakkura da zancen shi ta manta da sha,anin shi duk da tace wai, sugar man ne shi,

****** ********** ****** Zaune yake a back yard din gidan yana shan iska don su Mama suna a falon zaune da mariya sai Maman Biu da tashigo gurin su, Fattu kuma muna daki zaune da ita muna hira, Waya Fatima ta gama da mahaifiyar ta duk da Mama ta yi bata hakkuri a cikin wayan bai sa ta bar zancen ba, A hargitse ta samay shi yana zaune yana shan iska sai dai aiki yake a system din shi yana kuma jin dadin yanayin garin na yau, Bai yi aune ba sai ganin ta yayi a gaban shi ta zauna saman kujeran dake fuskan tar shi, A hankali ya dago kai yai mata kallo guda ya mai da kan shi yaci gaba da abinda yakeyi, Yagane cewa da masifa tazo ma ahi yau ma don haka yasaka a ranshi cewa zai maganin ta, Muddin tarin rikicin da ya hango a tare da ita ba mai ma,ana bane kamar kullun tau zai ma tufkan magani, Babu alaman firgici ko wani sauyin yanayi a tare dashi yaci gaba da aikin shi kamar yadda ta samay shi, yana yi da farko, Zaune take a cikin huci batace kala ba sai cicika da take yi daga zaune hannayen ta suna a harde da junan su, Da karfi takira sunan shi cike da tari bala,i da masifa a cikin kiran, Abinda yasaka ahi dan dago kai kenan daga abinda yakeyi ya watsa mata harara acikin idanuwan shi da suka rine sukayi jajir, Ance Meenatu wai ciki gare ta again, ? Wani irin mamaki da kuma tsanan Fatima yadira mai a rai lokaci guda, Dan murmushin takaici ya sake tare da cewa baki tabbatar ba ma kenan don kwankwato kikeyi ke, Yaja system din nashi gefe guda yana fuskantar ta yace idan har kinji ne baki tabbatar ba sai ki kkoma gurin wanda ya fada maki ki kara tambaya ko yaya zancen yake, Fuskan ta ta tsuke tare da gyara zaman ta tana cewa watau ma da gaskene kenan, Cikin ne da ita, Shima kallon ta yayi acikin daga mata gira yace yes of course cikine da ita fa, Ashe labari ya iso gareki haka da sauri ban yi zaton har zakiji shi da wuri haka ba, Tashin hankali sai duban Abubakar take a cikin mamaki, don a lokaci guda sai ya juye mata, tankar ba dan Bukar din taba da suke shan minti a tare, Tashin hankali take shedan ya kara zuga ta inda idon ta ya rufe, tafara fada mai magana tana cewa, Tun da Meena tafi zaki da gardi ai dole kai ta dura mata ciki ita kadai acikin mu, don itace kawai kakake gani da idon mata, Wata fi iya haihuwa da za,ace mu na zaune itace matar haihuwa muko matan jindadine kawai, Tsab taga ya mike tsaye ya tsaya a gaban ta yana kallon ta a cikin firgitattun idanuwan shi da suka juye a lokaci guda,, Hannayen shi ya saka a aljihu yana cewa cikin girgiza kai , Idan ke jahilace kin mata Allah ne ke bayarwa a duk inda yaso yaga dama kuma toni ban mantaba, Don haka tunda dadi kike bani daga yau na daina shan dadin a gare ki kije na sake ki saki daya, Dif, taji wani wuta ya dauke mata tankar bata numfashi ido waje take kallon shi, Cikin taba kirjin ta da dan yatsa, tana cewa Bukar ni kace wa wanan kalman, Wani shu,umin murmushi ya sake, tare da dan ware hannayen shi biyu, yana ce yes of course, na fada maki bake bama duk wata mace da ke son kawo min fitina a cikin rayuwana haka zan mata ko wacece ita din, Na shiga uku ta fada da karfin tare da sulalewa kasa takai durkushe sai kawai ta saka kuka a lokaci guda, Yaya Abubakar yace wait Fatima kada ki tara min mutane da wanan kukan naki, don koma may ye kece kikajawa kanki, Daga haka ya juya a sukwane yabar gurin cikin bacin rai da tashin hankali, Gidan ya bari gaba daya a lokacin bai tsaya ciki ba don bai son sauraren irin kuka da, Fatima ke gumzawa , Ita ko Fatima ba kunya ta shiga gida da kukan ta tana share hawaye cikin tashin hankali, Wayar mahaifiyar ta takira acikin kuka takasa cewa komai sai kuka take sharbawa cikin tashin hankali, Wai may ke faruwane haka tunda safen nan kin kirani kin kasa magana sai kuka kikewa mutane, Da kyat ta iya bude bakin ta tace acikin wani irin murya mama ya sakeni ne ,,, Kalman Innalillahi uwar ta iya furtawa ciki, tashin hakali itama uwar kuka ta saka a lokaci guda, Cikin kukan take cewa shike nan Fati kin kaiga yadda kike so yanzu ai sai ki dawo ki share dakin ki na gado ki zauna, Kukan da uwar ke yi yakara tayar wa Fatima da hankalin ta sosai don tasan cewa da biyu take wanan kukan, Mahaifiyar nata bata iya cewa komaiba sai kashe wayan tayi acikin tashin hankali, Uwar na kashe wayan ta kira layin Aliyu acikin kuka take zayyana mai abinda ya faru, a cikin tashin hankali kuma,. Ya tambayi ko may ya kawo sakin amma sai maman tace itama bata tambayi dalili ba, Aliyu cikin bacin rai yace ai ta huta saita dawo ga gidan nan ai ta zauna, Dama ai bata san kowa ba ita kanta kawai ta sani sai yayan ta, Uwar tace yanzu duk wanan bashine abin yi ba kawai asan yadda za,a gyara kafin tadawo nan Yace yaji zai kira Abubakar ya farajin abinda ke faruwa tukun kafin ayi wani abu akai,

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull