Tarko complete novel - Chapter 98
Tarko complete novel Chapter 98: Tarko complete novel Chapter 98. ****** ********** ****** Yana barin gidan Lawal ya dauka suka fita tare duk da bai…
3,302 words
****** ********** ****** Yana barin gidan Lawal ya dauka suka fita tare duk da bai iyacewa komai ba amna ahi Lawal ya fahinci cewa maigidan shi ba lafiya yau, Wayan shi da aka kira batare da ya amsa ba ya kashe wayan gaba dayan ta, Sai fama zaga gari su keyi batare da sunje wani wuri na takamaimai ba, Azuciyan shi yace ashe abinda yasaka Meenatu boye min zancen cikin Amir ke nan a lokacin can,, Yanzu ashe don jahilci da bakin kishi har mace zata iya rufe idon ta tace wai an wa yar uwar ta ciki ita anki yi mata cki, Don kawai tsaban kishi da hassada, tare da sawa kai wahala kawai, Yanzu ita fatima har tana ganin wai tana bashi Bashi dadi ke nan ashe, Ita bata san zaman hakkuri yake dasu ba itafa tausaya mata ya keyi don ya na tausayin mutuwan mijin ta sosai wallahi, Gashi kuma yayan ta shakikin aminin shine na kwara bana wasa ba, don har abin yazama masu zumunci, Amma ita sam duk batq duban wanan reason din akan ta, Tashigo mai gida da wasu akidodi marasa ma,ana marasa kyaun koyi, Hannuwan shi yakai a kanshi tare da furzo iska don fitar da relief azuciyaer shi, Yace a hankali a fili mace kamar jahila komai akan idon ta aikin jahilai, Yanzu inba hauka ba wai Fatima tace yaiwa wata ciki ita kuma yaki, yi mata don kawai tsaban kishi da hauka irin na mata, Shi may ya rage Fatima dashine wai irin yadda yake mata dawainiya aiko, Meenatu da ke yar uwar shi matan shi uwar dan shi batasamun hakana, agare shi, Gaskiya idan ba wani ikon Allah ba bazai kara zama da Fatima ba wai a matsayin matan auren shi, kuma again,
Ramatu ce tashigo daki take ce min a cikin kashe murya uwar dakina yau gidan ina ga ba lafiya don naga maman Aina tana kuka a bayan gida ita da maigida, Daga,ni har Fattu muka dago kai a cikin tashin hankali mu na hada baki gurin cewa harshi maigidan ke kuka, Tace cikin gyara tsayuwan ta a,a ba hakana nake nufi ba uwardaki na, Nakoma saman kujera ina maida numfashina tare da tambayan ta ko may tagani, Ta, gyara tsayuwar ta nan ta kwashe duk abinda tagani a lokacin ta fada muna, kaf Fattu tace kinji jahila ko kinji sherin kishiya ke nan yanzuma ashe shi cikin mutum ne mai ba kashi ba Allah ba, ashe,? Duk hankalina naji ya tashi sai nake kuma jin tsoron kada suce za suyi min wani mugun abu, nan gaba, a gidan Amna sai na tuna da zancen Maman Biu da Ànty Saloon da suke ce min baiwane Allah yai min don za,a yi mugun hassada a duk lokacin da cikin nan ya bayyana a jikina, Ashe ko da gaske,ne don gashi, ba,a kai ko ina ba Allah ya fara nunamin hassadan su, a fili,gareni, Tambayan Fattu nayi dacewa yanzu Fattu matan nan ashe basu ko tausayi irin halin da nake ciki na ciki, daje jikina Cikin dake kwararan wata biyu ke nan insha Allahu,,
****** ********** ****** Jinta shiru yau bata leko ba yasaka Salawatu bin bayanta don taga ko may ke faruwa a dakin ta Zaune take akasa duk ta ya kuce tafita hayacin ta Idanuwanta suyi hulu,hulu don kukan da tasha, Da mamaki Salawatu ke kare mata kallo tana kuma dan bin dakin da kallo, May ke faruwa, ne haka wai, Idanuwanta ta dago cikin qani irin yanayi na tashin hankali tana kallon salawatu dashi, Nazone dama nagan ki shiru yau baki fito ba, dan Allah kifita babu abinda zakice min yanzu, Don kin riga da kin hada min sheri ko badon kin ce mu tunkari Abubakar ba aida bazanyi wanan shawaran ba, Itama Salawati ganin yadda Fatima zata wullakantata, tace don Allah dakata malama don kin samu har nazo, gurin ki shine zaki kama fada min magana, Daga haka cacan baki yafara a tsakanin su biyu salawatu zata juya sai Fatima abiyu ta har zuwa kofan part din ta yadda kowa ke iya jin irin fallasan da sukeyi, Gaba daya gidan akafito waje ana sauraren su, cikin tashin hankali,
Dawowan maigidan kena tun a bakin get yake jiyo muryan su acikin tashin hankali, Ga mamakin shi baiyi zaton cewa zai dawo gida ya samu Fatima a gidan ba don sanin da yayi cewa tunda sanyi safiya yai mata saki, Azaton shi zata wuce zuwa gida tunda akwai time da zai kaita gida, a ranan har ma su huta, Sai gashi ya dawo ya samay ta a gidan suna ta tonon asirin a tsakanin su, A cikin takon kasaita ya kara so cikin gidan yana cewa cikin daka tsawa may kike jira ne gidan nan ne wai, Ke kuma Salawatu bazan so inganki anan tsaye ba inba hakaba yanzu zaki jonata ku tafi tare, Sadaf, sadaf ta juya ta nufi hanyan zuwa part din ta, ta, zauna tana huci, Ganin ta, tafi yasa shi kokarin juyawa zuwa hawa sama da dan gudu gudu, yana mai kyatawa, Su Mama dake daga falo suka yi cirko cirko suna kallon ikon Allah don abin ya basu mamamki so sai, Fatima takoma daki tana hade rai, da kuma kuftawa don bakowa yaja mata wanan sakin ba sai uwar anyi ance, Salawatu datajiyo zancen taxo ta zungurata akan suyiwa mai gidan tujara, Yanzu gashi ta wargaza mata farincikin ta da keep marta ga mji da mutanen gida
ZEEE. MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🕸 9⃣9⃣
ZAINAB IDRIS MAKAWA
ALLAH AL MUQSIT
A cikin dare su Aliyu suka shigo garin Abuja shi da Mama da kanin mahaifiyar su, malam Alphaga Musa, Sun samu gidan kowa na part din shi ba wani abinda ya nuna masu sign din cewa akwai wani abu, daya faru, Sai dai a irin yadda suka samu tarone a gurin matan gidan, bai masu dadi ba saboda ba wanda ya nuna masu murnan zuwan su,, Daga Anty Sadiya har Salawatu da su ka samu a folo ba wani karbuwan kirki, da su ka samu a gurin su,, Ganin bani falon ya saka mahaifiyar Fatima tambayan ina yar mulkin gidan naku suke, alokacin, Ina can part dina tare da su Mama Ladi da Anty Mariya, duk da dai har yanzu ba wai akwai wani shirin kwarai bane a tsakani da Mama Ladi din, sama sama muke da ita sai dai ina kokarin jure duk wani abinda zata gwada min don kawai mu gama lafiya da ita, Ramatu ta shigo muna da labarin zuwan su iyayyen Fatima acikin wanan daren, Haka na daure jiki ba kwari na fita zuwa yi masu sannu da zuwa, Aliyu yana falo da, dayan mutumin da suka zo, tare da Yaya Abubakar zaune nai masu sannu da zuwa, inda na wuce dakin Fatima wanda zan iya cewa tun dawowa na gidan wanan ne karo na biyu dana shiga part din nata, A hargitse na samay su ita da mahaifiyar ta da alaman kuka su keyi a lokacin, don duk sallaman da na keyi a kofan falon su saida na kara matsowa gap da kofan shigowa sanan suka ganni a tsaye Naiwa matar gaisuwan mutunci tare da tambayan ta mutanen gida suna lafiya, Ina fitowa nasa Ramatu takai masu ruwa da abinsha hade da abincin da muka girka a part dina nida bakina su Mama, Sosai Yaya Abubakar yaji dadin wanan taron da naiwa bakin shi, Tun Ramatu bata fita ba taji uwar nacewa yanzu gashi ai su masoyan naki ko gaisuwan kirki ban samu ba daga gurin su, Saida na fada maki cewa kada ki ba wa kishiya amana amma ki ka,yi biris da zance na, Yanzu wa gari ya waya su ba suna falo suna jin dadin suba Ke ko gaki a daki cikin bakin ciki da takaici tare da tashin hankali, Yanzu ki duba Kiga abincin nan fa ita yar gidan Manya ce fa aiko min dashi, ga yaranki kince tun safe basuci komai ba sai corn flakes, suke sha, Mama don Allah duk wanan zancen abarshi tunda ya faru ko yanzu may nene abin yi, Mahaifiyar tace kibari muyi salkah sai asan abin yi don mu gobe zamu koma insha Allahu saboda gurin aikin yayan ki, Bathroom takai uwar inda ta dawo ta dan gyara guri, don su samu fili, Saida Uwar taci abinci sosai ta koshi sanan take tambayan ba,asin zancen, Fatima bata boye mata komai ba tafada mata gaskiyan yadda sukayi da maigidan nata, Uwar ta sauke ajiyan zuciya tana cewa an maki ingiza mai kanto ruwa ke nan yanzu an barki a ciki , Aliyu da kan shi ya shigo part din Fatima inda yai mata kaca kaca akan abinda Abubakar ya fada mai cewa Fatima tanayi mashi, Shiru tayi don tasan cewa duk abinda aka fadi a gamay da ita akwai babu karya daga cikin zancen, A hankali take kuka yayin da Aliyu ya cewa mahaifiyar su Mama kizo kiyi mashi magana da kan ki don gaskiya ni ban san ya zan fitowa Bukar da wanan zancen ba, Yanzu kin ga ni ko a lokacin da nake maki huduban cewa kiyi a hankali kada kijawa kan ki matsala ai baki dauki magana ta da muhinmanci ba, Yanzu ga irin ta nan ai kin jawowa mutane wulakanci dubi irin yadda matan nan ke kallon mu,. Sai ma ita yar gidan Manya ce da bata maga shigowar mu ba tazo tai muna taron mutunci har da bamu abinci gashi har yaran ki sunci, Tace Mama wallahi duk sherin shedan ne amna ina kokarin kiyayyewa ai, Uwar taja tsaki tana cewa ai tuni ni na daina yarda da dadin bakin ki kuma don kin samu yaro mai hakkurine aida kin gane kuren ki ko, Bata karashe zancen taba Abubakar ya shigo dakin yana son ya gaida mahaifiyar nata cikin ladabi, suka fara gaisawa da ita, Mahaifiyar ce ta sauko daga inda take zaune rana cewa kaiwa Allah Abubakar kayi hakkuri da yar uwar, Nasan kana hakkuri amna don Allah ka kara a saman wanda kakeyi , No, No , No, Mama dan Allah kada ki duka man baikai can ba, Kuka take sosai, tana cewa don Alkah Abubakar yayi hakkuri ya mayar da Fatima dakin ta, Yace Ya Salam Mama don Allah kiyi hakkuri amma gaskiya ko zan maida Fatima sai ta tafi gida na kwana biyu tukun idan ta kara koyo hankali da wayyo sai tadawo, Haba Abubakar baja yarda da hakkurin dana baka, bane ke nan ko, Aliyu dake gefe sai cewa yayi ai Mama munyi bayani dashi tare da kawu Salisu, abari a tafi da ita na kwana biyu din, Badon uwar taso ba ra amince amma da ita da Fatima sai suna ganin cewa dabara ne kawai yai masu don su tafi da ita,
****** ********** ****** Salawatu wace ta tura Lami don ta sauraro mata abinda ke wakana a dakin Fatima duk ta matsu Lami yar aiken ta ta dawo don taji may ake cikine wai, Fatima ce ta turo kofan dakin Salatu din inda tai firgigi tana kallon ta, Tace ashe bakiyi barci ba tace eh yanzu zan hau sama in kwata ai, Baki Fatima ta tabe tare da dan fuskan tar ta cikin daure fuska tace, Dama nazo ne in fada maki cewa don Alkah zan bar yaran nan gurin ki har nadawo, Ina , a gurina inji Salawatu, gaskiya kin san banda kokari gurin kula da yaroni, musaman akan tashi da safe dafa masu breakfast din da zasu dashi, school, Mamaki maganan da Salawatu ke fada mata tayi duk yadda suke amma zata ce bazata rike mata yara ba, Ko may Salawatu ta tuna sai cewa tayi ba, matsala amma don Allah tajawa yaran kunne sosai,, Batai fushi ba don bata da zabi saboda haka dole ta yarda cewa, zata ja masu kunne din, Washegari suka tafi kamar yadda aka aje zancen dole badon Fatima ta so ba Zuwan mahaifan Fatima ya kara sa mata bakin jini a gurin Mama Ladi, inda Mama Ladi take cewa, ai don sukaga gurin cine shine suka zo bada hakkuri kada a fita a kasa samu wani makaman cin shi, Amma in bashi ba don kawai an saki yar ki sai ki kwaso jiki kice wai kinzo bada hakkuri,, Tun bayan tafiyan ta kullun sai tabugo mai waya kusan sau goma sha amma bai daukan wayan, Tana da sati biyu da zuwa aka fahinci cewa tana da shigan ciki a jikin ta Aliyu ne ya bugowa Abubakar waya cewa Fatima bata da lafiya sunje asibiti an auna ance tana da ciki na wata daya da kwanaki, Ga lissafi bamu da wani tsairaiya sosai da ita gurin samun cikin, Azaton Fatima Abubakar zai yi murna sisai tare da farin ciki amma sai taji sabanin hakan, Bakira taba don suyi zancen sai dai da Aliyu ne sukayi magana inda yake fada mai cewa lafiya take baa da wani matsala a tare da ita,,
Ita ko Salawtu ba ruwanta da zancen yara ko kadan don yaran da kan su suka dawo part dina da zama tun suna shigowa Mama ta ce su fita, sun cika ta da ihu har dai tasa masu ido a nan suke komai, Samun hutun yaran yayi dai dai da lokacin da su mama za su koma BK don haka suka wuce da yaran, Zuwan yaran gida ya tayar da hankalin Fatima da mahaifiyar ta ya daga saboda sun ji irin yadda Salawatu tai rikon su kuma, yadda sam baruwan Abubakar da al,amarin su , Hakan ya kara tabbatar mata cewa bata a cikin rayuwan shi yanzu sam, Hankali ta yakara dagawa inda ta fara dan shige, shigen malai wai a taimaka mata hankalin shi ya dawo gare ta, Har takai ga sayar da sarkan gold dinta da ya sayo me na da ya tafiya, Amma duk a banza ga shi ta ramay tayi baki duk ta lalace ba ta da kyau gani, sam,
****** ********** ****** Cikina yana girma ina dan samun saukin jikina sosai, amma ban yarda inyi wani dogon motsi kamar yadda likita ya umurce ni,da cewa na samu bed rest irin na cikin Amir, Wanan abin ne ya fara dan haddasa muna fitina a tsakani na dashi, don shi a lokacin ne ta ke wani man,mane min, Yana nuna yafi bukatana fiye da kowani lokaci, Duk yadda nake kokarin tsare dokan likita amma sai Yayana yaci galaba a kaina, Irin wanan ranan nakan wuni ina fama da matsaloli akarshe ma sai na kai ga kwanciya asibiti, Dole likita yace zai aje ni asibiti gurin shi har nayi lafiya, Ranan Yaya Abubakar yai fitina sosai yana cewa wai bai yarda ba dole likita ya kyaleni na dawo gida, Alhamdullahi don na samu lafiya sosai yanzu don muna taka tsan,tsan, dagani har shi, A gurin Fattu nadan samu labarin cikin Fatima amma sai naja bakina nai gum ban fadawa kowa zancen ba, Sai harkokin mu muke tayi abin mu batare da mun sa wani abu a rayukan mu ba,, Abokan arzikina sai, tatalina suke suna kara sakani a hanyan alheri akoda yau she, Hakan yasani kara bude idanuwa da harkoki irin na matan manya sai dai a cikin natsuwa nake komai, bada garaje ba, Karfe tara na dare yashigo dakina a lokacin ina waya da Mama Saratu inda take min zancen Yayana Ibrahim, Daga idon da zanyi karaf muka hado ido dashi yana a tsaye daga kofa ya kura min ido, Murmushi na sake mai daga inda nake zaune ina kokarin yin sallama da Mama na, Yar hara ya sakar min tare da kara takowa zuwa inda nake zaune, Har,Yanzu wai dokan likitan tana aikine ko yane wai, Nace, cikin dan marairaicewa Yaya aika san bawai yabani time bane. Ya daga min gira yana cewa yau dai a daure a taimaka wa dan bawan Allah mana, Yakarashe zancen a cikin dan mararaicewa zabban tausayi, Nace, sai ka bugawa likita kaji idan babu matsala ai you, are welcome ko, Guntun murmushi naga ya saki yana cewa ina ruwana da likita ni kawai zan kare kaina ne daga fadawa a halaka, Kallon shi nake a cikin mamaki mutum mai mata har uku a gida zai tsaya yana fadan irin haka harda kiran halaka acikin zance, Wane ne ya karyar min da zuciya har na manta da zance dokan da likita yasamin, Bai wani sha wuyaba wurin yin galaba a zuciya ta, har na sakar mai ragamar komai ya kwashi garan shi a wanan daren, Duk da ba wai a gareje yazo min ba a natse ya aiwatar da komai nashi, Hakan bai hanani shan wahala ba bayan yakammala yafita, daga dakin nawa, A falo yasamu Salawatu tana sanar ta wai kallon program nan ko zaman gulma ne takeyi don kada a bata labari Bai tsaya falon ba ya haura zuwa sama don ya tsarkake jikin shi, Bayan shi Salawtu tabi da hara tana kira mai muna fuki tundazun da ya shiga yana can yana rarashin yar gwaldin shi, amma da watace ko ajikin shi, Ita da kanta bawa kanta ansa da cewa duk ya wani susuce yanzu tunda yarinyar nan bata da lafiya sai wani rawan kafa yake wai likita yace a bata kulawa na musan man, Amna ita shekaran jiya da kyat ya iya kaita Nasarawa suyo gaisuwan rasuwa a gurin dagin ta, Wata zuciya tace ke Salawatu kibi sannu kada ki wa kanki tugun sheri irin na Fatima duk fa yadda ake mutumin nan yana kokarin sa akan ki, Tawani tabe bakin ta tafada a fili cewa wallahi ni yarinyar ce ban kauna don komai da ake bukata a gurin mace akwashe a tare da ita, Nasan shi yasa My bai iya boye felling din shi a gaban kowa akanta,
****** ********* ****** Barci nake amma sai juyi nskeyi don murdan da marana yake a lokacin, A hankali ya fara sai gashi ya tsanan ta min lokaci karfe biyar na asubahi yayi don wani guri ana ma sallah ko, Bayi na shiga don narage marana inyi fitsari don sai nake ji kamar fitsari yadamay ni, Ina tsugunawa jini ne ya fara zubomin, zubur na mike tare da sauri dawowa bedroom dina na rarumi wayana, Kira daya biyu yadaga wayan inda nake ce mai don Allah yazo ya taimakamin Nai sa,a yana zaune yana lazimi da chasbaha a hannuwan shi Ba bata lokaci sai gashi dakin cikin tashin hankali da rudewa, yana tambayan lafiya Zani na da ya jike da jini na nunamai inda yafurta da karfi innalillahi, Lawal ya nemo a waya acikin daren nan Ramatu taimakamin muka tafi asibiti da maman biu, A gagauce suka karbeni inda suka fara bani taimakon gagawa kafin likita ya shigo,, Na dai san shigowan shi amma daga haka ban kara sani ina nake ba kuma,, Barci mai nauyi nayi don ban farkaba sai zuwa karfe dayan rana na farka, Yunwa da kuma juwa nake gani a ga kuma ruwa drip a hannuna na hagu don haka na kara lumshe idanuwana na koma barci, Ranan rayuwan likita ya baci sosai don yai ta fadan cewa sai da yace kada nai wani dogon wahala, Amma sai gashi ba,abi umurnin shi ba an bari ansamu matsala, Ya bada scanning yace aje ayi hoton cikin don a tantance lafiyan cikin, dake ajikina, Sai misalin biyar na marance aka kaini gurin yin scanning din ida Yaya Abubakar yana biye dam, Likitan da ke scanning din yace lafiya kalau abin cikin cikin sai dai yau da alaman bai dogon motsi don wahalan da yasha, na bleeding din da nayi Amman kuma kan shi, ya daure don ya rasa gane ida kan da yake ko kafan baby din, duk ina suke, Sai dai baiyi wani dogon bayanimai yawa ba in,banda rest da ya bani cewa na zauna asibiti har zuwa haihuwa,, Hankalin Yaya Abubakar ya daga sosai da wanan zancen, inda ya nemi likita da ya bari na koma gida nayi bed rest din, Amma likita yaki amin,cewa da wanan zancen