The sexxy boss book 4 by maman teddy - Chapter 4
The sexxy boss book 4 by maman teddy Chapter 4: The sexxy boss book 4 by maman teddy Chapter 4. Yanda yake take kukan ne yayi matuƙar karya masa zuciya…
3,219 words
Yanda yake take kukan ne yayi matuƙar karya masa zuciya ,duk da dama Soyayyar nata ta samu gurmi ta musamman a zuciyar ta ,hannun sa yasa yana ƙara haɗawa da nata a hankali ya furta " Ba haka bane Umaima? Ai haka yake , Ni nasani ko baki faɗa mun ba, nasan Momy Tana Son Aure na dake ne saboda ta cimma wani buri nata , sannan matsalar ma abun dake daɗa sa ma zuciya ta damuwa shine ke.! Yayi maganan yana lumshe lulun idanun sa tare da cijan laɓɓan sa na ƙasa . Cike da wauta Umaima ta riƙe hannun sa , Ya Umair kayi haƙuri , Momy zata sauya , amma wallahi a karon farkon nan dana taho gidan ka ba ita ta turo Ni ba , Kawai Ni ne nazo kaji Yah Umair...ware manyan idanun sa yayi yana zuba su akan fuskar ta kana yace " Kinji matsalar, Umaima kece.., Baki taɓa ce mun kina Sona ba , ko alama kin san ya zuciya ta take ji kuwa?? Sauƙin ta ɗaya idan na kalli cikin idanun ki anan kaɗai nake ganin Soyayayya ta , ga shi nan , anan ne kaɗai Bakya iya ɓoyemun . Sada kan ta ƙasa tayi tana yin shiru , jin Muryar sa tayi yana cewa " Faɗi mun duk abun dake kike so ,Zana baki Umaima , Kuɗi??? Kallon shi tayi saurin yi , a zuciyar ta tana cewa" oho a inda ya aje Ni kenan,so kuɗi tun da sanadin kudi komai ya faru tsakani na dashi . I love You ,ina Son naga na kasance dake har abadan abada . Faɗa mun ko nawa ne zan baki tun daga kan dala biliyan zuwa sama . Ƙurrr yaga tayi masa da ido , tana kallon shi ƙwallah na taruwa a saman ƙwarmin idon ta .
Girar sa ya gyara mata ,alamun ita yake sauraro . Shi dai Umair baiyi aune ba yaji Taji Dunkule hannun ta ne tana haɗa yatsun ta tare da bugun cikin sa . Ashhh. Ya saki ƙara don yaji zafin bugun nata . Dari ya ta sheƙe dashi tana yin baya , har da kama ƙwallah na mugun ta . I luv you.! Ya furta yana kallon ta , kallon idanun sa tayi kana ta saki murmushi tana cewa " Dama ashe Soja yana jin zafi idan an bige sa??. kamin yayi magana ne ta kuma cewa " Ina Son zama dakai Ya Umair, Ka san menene?? Shiru yayi mata bai ce mata komai ba sai dai idanun sa dake akan ta ,alamun yana sauraren ta . Ƙwallah ne ya fara gangaro mata , hannun ta tasa tana gogewa kamin ta motsa laɓɓan ta tana mai cewa "Aduk lokacin dana zauna Ni kaɗai bana tunawa da kai a zuciyata . Amma a duk lokacin da wani ɗa namiji yayi rabe Ni ,sai naji wutar Soyayyar ka a zuciyata. A da baya na ɗauka Wauta ce , kuma nayi kokarin hana zuciya ta faɗawa soyayyar ka ,amma ta gagara . Ina Son ka ya Umair...Ta ƙare maganan tana riƙo hannun sa . Hannun sa ya ware mata alamun taje garesa . Da sauri ta faɗa jikin sa tana jan shashsheƙa . Ina ji kaman Soyayya ta tafi taka?. Hannun sa yasa yana rufe bakin ta , kamin yace " Kar ki ƙara faɗin haka ba daidai bane , Ni dana zabi na bar komai na sa boda ke , na daina Kula kowacce mace ,amma ke Baga shi ba.
Shiru yayi da faɗin maganan don ji yayi zuciyar tasa na masa wani irin harbawa tuno da Fahad. Ɗago da kan ta tayi ba tare da ta tashi da jikin sa ba tace " Amma fa har yanzu Ban haƙura da kyeta mun mutunci na da kayi ba ,babu imani bare tausaya wa . I'm verry Sorry dear . Maƙale kafaɗa Tayi tana mai da kanta tare da lafewa jikin sa . A haka sam ta mance da wai a mota take , don mota ne suke cikin ta wanda ta amshi sunan ta , baka ko jin hayaniyar sauran abun hawa ,yanda kasan tana inner room din ta . Tafiya ce mai tsawo suke yi , wanda ganin ba zai iya komawa Abuja a mota ba yasa shi sawa a taho masa da jirgin yawo Helikwafta .
Ji tayi yana taɓa fuskar ta a hankali yana maida ita tare da ƙwantar da ita . Saurin buɗe ido tayi tana kallon gyefen da gyefen ta , wanda taga pilot Yana ƙoƙarin tada jirgin . Har ya dauke ta daga moton bata sani ba don barci ya ɗauke ta a jikin sa. Saurin kallon sa tayi cike da mamaki tace " Yah Umair Ina Zamu je?? . Ta ƙare maganan tana kuma juyawa tare da ganin Jirgin na sama dasu . Juyowan da zata yi da fuskar ta ne ya haɗe da nashi , haɗe bakin shi yayi da nata yana tsotsan harshen ta a sukune yana sa hannun sa tare da shafa gadon bayan ta , kasa motsi tayi don ji tayi gaba daya ya sakar mata da duk wani laka nata . Kusan mintuna biyar suka debe a haka kana ya zare bakin sa daga nata tana jan dogon ajiyar zuciya tare da sauke numfashi a hankali . Murmushi ya sakar mata wanda har hushiryar sa na bayyana kana cikin Muryar sa ta ingarman namji soja tsayayye , ya furta " Abuja nan da 1 hour Zamu sauka . Cox naga kinyi gaji da yawa. Bin sa tayi da kallo , cike da mmki kana ta komawa ta kwanta tana yin shiru , first a Rayuwar ta na duniya wai yau itace a jirgi . Ohh Umaimatuwa kenan😂 .
Kusan 50mins taji jirgin na ƙasa a hankali har ya ida sauka ,wannan ya alamta mata cewan sun fa iso . Hannun ta ya kama yana kallon ta cikin murya mai kama da rarrashi yace " Zaki iya sauka? Ko na...a'a zan iya ,ta katse shi cikin sauri tana miƙewa tashi daga jikin shi . A hankali ta sauko shima yana bin bayan ta . Hannun sa yasa yana rungumo ƙugunta tare da manna ta da jikin shi , kallon sa tayi tana Son raba jikin ta da nashi ,ganin ta a wani gida na daban ,ga kuma securities da sauran masu tsaron gidan da bata san ina ne ba . Ji tayi duk a takure rungume tan da yayi da jikin sa . Shi kam bai ganin yayi wani abu . Nufar wani apartment suka yi , wanda sai a sannan a hankali cikin sanyin Muryar ta tace " Ya Umair ina ne nan? Ai ba gidan Daddy bane nan . Hannun sa yasa yana kama subu subun kumatun ta ,yana murmushi tare da cewa " Calm down my Swt Ccbr . Wani kallo ta watsa masa na ita yake zolaya . Dariya yayi yana cewa" Our Swt House . Nan zamuyu rayuwa Ni dake , with ur kids , nasan they will come verry soon inshallah . Murmushi Tayi cike da jin kunya tayi kasa da kan ta ,don taga yana mata kallon kasa kasa. Wanda duk sai taji yarrrr. Nufan Wani falo Sukayi da babu komai sai glsses da suka kewaye ko ina . Gani tayi kamin su karasa basu danna ko ina ba wurin ya bude kaman hanyar kofa , suna shiga ya koma ya rufe , Ohhh wato da Ƙamshin jikin mutane yake aiki kenan.? Kallon ta Umair yayi kamin yace " Me kika ce??. Saurin dawara tayi don bata san maganan ciki ya fito sarari ba ,tace " A'a ban ce komai ba. Ohk taho mu shiga daga ciki yayi maganan yana kai hannun sa gareta . Saurin ja baya tayi tare da cewa " A'a Su Ammie fa basu san zaka kawo Ni ba. Huuuuu Sauke numfashi yayi tare da furxarwa yana kai hannun sa tare da shafa sumar kan sa.. tun da sun hana Ni mata na ,basai na kawo ki nan muyi amarcin kwana ɗaya ba ,idan kin koma sun gan ki da juna biyu sai Kice nawa ne sai su dawo mun dake dole ,daganan mu tafi honey moon da suka.....Ya Umair.!!! Ta kira sunan sa cikin tsoro da ɗaga murya na mamakin furucin sa gare ta ........
*MMN TEDDY* *Littafin THE SEXXY BOSS na kuɗi ne , Regular group₦300 VIP group ₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ,ko katin MTN ta wannan number 08081202932...idan kuma ki ka karanta baki biyani ba keda ALLAH*
Tare da ja baya kaman taga Abun tsoro , A hankali ta furta " Don Allah Ya Umair ka maidani gidan Daddy , Don Allah na roƙeka Pls ya Umair. Yanda tayi maganan ya kusa saka sa dariya amma sai ya mai da dariyar sa ciki yana mata kallon da ta rasa gane manufar sa . Kinji fa Wai Yaya...Ni kike kira Da Yaya a matsayi na na mijin ki , Kina ji Pls Mah wife ki bani dama just na kwana ɗaya , zan miki wani Abu mai daɗi da aƙwana ɗaya zaki sauya mun wannan sunan da kike kirana irin yanda su Fareesat ke kirana dashi kema a matsayin na Matana ace kina kira na dashi?? Kai kaiii ina ina ina??? Ya maimaita maganan kusan sau uku . Cikin sauri cike da tsoron sa kar yayi mata abun da take tsoro tayi saurin matsawa kusa dashi tana cewa " Zan sauya To , Wallahi zan sauya faɗa mun wani Sunan kake So ,Amma Ni dai don Allah ka maidani gida Ya Umair ". Shikenan ta maimaita ". Yayi maganan tare da kallon Gyefen Window Glass ɗin dake Kusa dashi. Kwana Biyu zamuyi ina koyar dake daga bisani sai na dauke ki na maida ki wurin Su Momy ya ƙare maganan tare da juyawa yana shirin tafiya , da gudu ta bi bayan sa tana sa hannun ta tare da maƙalewa a bayan sa tana sa hannayen ta duka biyun tana rungume sa ƙaammm , Cak ya ja ya tsaya ji yayi wani abu mai kamar shocking na kama tun daga ƙafafun sa yana circulating blood nashi har zuwa kan sa . Lumshe ido yayi yana jin tamkar suyi ta tsayuwa a haka kar ta cika shi , har sukai Wani yammacin a haka a tare . Cikin dadɗan Muryar ta wanda Fareesa ke cewa " Shine kaɗai mai daɗi a tare da Umaima bayan shi ita bata ga Abun da Yah Umair ya nace ya kuma maƙale mata ba . A Hankali yaji Muryar ta tana furta " I'm sorry My champ . Ba zan sake ba ,wannan yayi maka ko a sauya?. Lumshe lulun idanun sa yayi yana ware su . Wow'. Shine kalmar da ya furta , kamin yayi magana ne tayi saurin cika shi tana juyowa tare da fuskantar sa .
Hakan yayi ko? To mu tafi gida. Habawa my Bul bul , ki bari mana ki ci abinci ki shirya a gidan mijin ki ... Juyawa tayi tana bin kanta da kallo a tsakankanin glsses ɗin dake gaban su da bayan su . Haɗe girar sama da ƙasa tayi tana cuno baki , a sarari ta furta ,tabbas kuwa naci sunana Bul-bul gani nan can ƙasan ka , ga kuma kiba mai muni . Buɗe baki yayi dariyar da yayi ta danne ta ya kuɓce masa , haushi ne ya kamata , saurin juyawa tayi tana kallon sa kamin ta kai hannun ta tana riko nasa , meye na kauda kai kuma Yallaɓai.? Fuskance Ni kayi dariyar ka ,nima zan rama ai . Ayya Sorry My Swt Ccbr . Au ka ƙara ko?? Kace swt Tomato Mana kawai . Tayi maganan tana juya masa baya tare da sa hannayen ta tana naɗewa a ƙirjin ta . Ji tayi ya ɗaga ta cak yana sama da ita .wayyo Umma na sauke ni , Please Yah Umair Ka sauke ni ,juyi da ita yake yi bai tsaya ya saurare ta ba , sai dariya da yake mata ,wannan yasata saurin ƙanƙanesa itama tana Dariya . Yana ɗauke da ita suka nufi Ciki ,inda anan ne taga komai complete falo , kujerun ba royals bane ba , Amma sunyi masifar ƙyau tafi ganin su a season Film na ƙasashen Turai . Sauke ta yayi a hankali tana bin falon da kallo cikin burgewa take furta " Kai Falon nan yayi ƙyau sosai ,Wow my champ yayi ƙyau , Tamkar ba'a gida Nigeria muke ba . Waya faɗa maka Best colour ɗina dana ke So .! Tayi maganan tana kallon Yanda akayi Adon Falon da Pich and Ash colour .
A maimakon ya bata amsan da take saurare ji tayi ya riƙo ta yana hugging ɗin ta , kumatun ta yasa taffan hannun sa yana jan mata su . Dariya tayi masa tare da kallon sa , gani tayi ya juya yana riƙe da ita tare da nufan wani hanya . Step da stairs a hade uku suka haye sai dai ganin ta tayi a wani makeken ƙayataccen bedroom Wanda a ganin ta tsaruwan shi yafi na ko ina . Saurin kallon sa tayi , kamin ta juya tana zame hannun ta daga garesa . Cike da mmkin take bin dukiyar da yayi kuka a wurin da kallo , kamin ta motsa bakin ta tana shirin masa magana ne ,ya katse ta da cewa " Wane ya baka wannan arziki? A ina kake samun wannan kudade??. Nasan shine tambayar dake a Ranki da zuciyar ki ,shine tambayar da zaki mun ko Umaima?. Ji tayi ƙirjin ta ya buga ,don tabbas shine tambayar dake bakin ta . Wannan wani irin masifaffen brain yake dashi ? Abun da take fadi kenan a Zuciyar ta... Gani tayi ya matso dab da ita idanun sa ya zuba a fuskar ta , wanda ta kasa kirar hakan , sunkuyar da kan ta ƙasa tayi kana ya cigaba da cewa " Umaima Ni haka Allah yayi Ni , ina da brain Ni kaina na san da hakan , a lokaci guda na fahimci dalilin zuwan ki , amma kin san menene? Tun a lokacin na kamu da ƙaunar ki a zuciya ta . Kuma ban kokarin Azabtar da ita ba ,na yarda da na kamu da Soyayyar ki Umaima , ina Son ki har Abada bazan iya daina Son ki ba , Pls ki Soni Domun Soyayyar da nake maki , kiyi min Alƙawarin ba zaki bar Ni ba ,ba kuma zaki guje mun ba Har Abada .
A hankali Umaima taji hawaye na sauka daga idanun ta . Saurin kai hannun ta tayi tana ɗaurawa a Fuskar Umair tare da tallabo kuncin sa . Ganin ƙwallah tayi a cikin idanun sa . Kai To meye na wannan hakan ne?? Tayi maganan a ɗan shagwaɓe , sai kuma tace" Hawaye ne fa naga Ni a idanun ka miji na.! Ware idanun sa yayi yana kallon ƙwallahn da ya taru ma ƙwarmin idanun sa na gangarowa . Juyawa tayi tana ware ware cike da tsokana irin nata ta fara cewa " Ina kuke masu tsaro ,kuzo kuga Hawaye A idon Boss ɗin naku Ƙyauta . Duk hakan na meye wannan ? Yayi maganan yana ƙare haɗe ta da jikin shi . Ku taho ku gani kunji , babban Soja kuma Arrogant boss Wai yana kuka ku taho ku gani a kyaut...maganan nata ne ya maƙale sakamakon jin bakin sa da tayi ya haɗe da nata yana shan mata tamkar ya samu alawan yara . A wannan karon bata yi yunkurin hanasa ba ,sai da ya tsotsa Son ran sa kana ya zare bakin sa yana kallon ƙwayar idon ta tare da faɗin " I love You".
Juyawa tayi tana kallon sa tare da cewa " Wai kai baka gajiya da faɗin " I luv you ne?? Sai kace Bature ko jinin sss....jan bakin ta tayi cikin sauri tana kama harshen ta , tuno da katoɓaran da take shirin yi , don Hajiya Turai ta sanar mata da komai na Umair , da dangin Mahaifiyar sa da mahaifiyar tasa da suka kasance turawa . Kauda kan sa yayi yana kallon Gyefen ta , tare da cewa " Me kike kallo ?. Yi hakuri.! Tace dashi tare da kallon sa . To ba karya kika yi ba ai , Ina Son ki sai na ɓoye na bar ma zuciyata ?. Girgiza kan ta tayi tana murmushi tare sada kan ta ƙasa. Kema kina Sona ai Bakya faɗa mun ne kin ɗauki ɗabilar Kunya ta Hausa Fulani . Murmushi tayi tana cewa " Oho ka rama kenan ?. A'a ba ramawa nayi ba. Yah Umair Ina Son Ka, A da baya ban san ina Son Ka ba , duk idan na tuno ka sai nayi kuka kawai , ƙawata Fatima ce ta faɗa mun hakan wai zuciyata ta kamu da Soyayyar ka . To amma yanzu ya zanyi da Momy na??. Kallon ta yayi kaman zaiyi magana sai kuma ya sa kan sa tare da manna mata kiss a saman goshin ta . Juyawa yayi nan tayi saurin riƙe hannun sa . Pls Yah Umair Ka Mai dani gidan Momy ,nayi maka alƙawari a satin nan zan dawo gidan miji na da zama , zama kuma ta har abada. Wani irin sanyi ne yaji mai daɗi yana ratsa zuciyar sa . I lab you my dear wf. Ohhh Koda kince bana Gajiya. Dariya tayi tana riƙe hannun shi muje ka koma dani to.....
*AUNTY MMN TEDDY* *Littafin THE SEXXY BOSS na kuɗi ne Regular group ₦300 VIP group ₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ku tura katin MTN ta wannan number 08081202932*
_Kuyi voting Sabon littafin da zai fito nan ba da daɗewa ba , yawan ƙuri'un da muka samu a cikin wa'anan guda biyun #MR ROMANTIC ko kuma #THE VIRGIN MAID , wannan sune littafan da zan fitar mana in ALLAH ya yarda , kowa na da daman zaɓan wanda yayi masa a ciki , wanda ƙuri'iur sa yafi yawa sai mu ɗauke shi mu fara in Sha ALLAH . labarai ne ko wanne mai ɗauke da sabon salo ,daban dana saura , tamkar yanda nawa alƙalamin yake daban dana ki Hajiya ta ,haka wannan labaran suke daban a cikin jarangiya , masu voting afara kaftowa lahiya💃_
Murmushi yayi yana cewa " Ohk ina zuwa . Juyawa yayi cike da takon sa na tsayayyen namiji ya nufi can wani coridor , juyawa Umaima tayi tana kallon gyefen da gyefe tana bin ko ina da kallo , Kaman baƙauyiya . *Littafin THE SEXXY BOSS na kuɗi ne Regular group ₦300 VIP group ₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko ku tura katin MTN ta wannan number 08081202932*
_Kuyi voting Sabon littafin da zai fito nan ba da daɗewa ba , yawan ƙuri'un da muka samu a cikin wa'anan guda biyun #MR ROMANTIC ko kuma #THE VIRGIN MAID , wannan sune littafan da zan fitar mana in ALLAH ya yarda , kowa na da daman zaɓan wanda yayi masa a ciki , wanda ƙuri'iur sa yafi yawa sai mu ɗauke shi mu fara in Sha ALLAH . labarai ne ko wanne mai ɗauke da sabon salo ,daban dana saura , tamkar yanda nawa alƙalamin yake daban dana ki Hajiya ta ,haka wannan labaran suke daban a cikin jarangiya , masu voting afara kaftowa lahiya💃_