The sexxy boss book 4 by maman teddy - Chapter 5
The sexxy boss book 4 by maman teddy Chapter 5: The sexxy boss book 4 by maman teddy Chapter 5. Murmushi yayi yana cewa " Ohk ina zuwa . Juyawa yayi cike…
3,304 words
Murmushi yayi yana cewa " Ohk ina zuwa . Juyawa yayi cike da takon sa na tsayayyen namiji ya nufi can wani coridor , juyawa Umaima tayi tana kallon gyefen da gyefe tana bin ko ina da kallo , Kaman baƙauyiya . Tana anan a tsaye ne taji takowar sa a gaban ta ya tsaya yana fuskantar ta tare da miƙa mata lemu a glass cup , ki Sha kana mu wuce. Mika hannun ta tayi cikin zumma tana amsa , tare da kai lemun mai sanyi bakin ta . Tun da ta fara Sha bata waiwayo shi ba sai da ta shanye sannan ta miƙa masa tana cewa ' to mu tafi. Jin shirun nasa da take expecting Jin maganan sa amma sai shiru ya biyo baya yasata saurin kallon sa tana zuba idanun ta a saman nasa , Gani tayi yayi mata ƙurrr yana kallon ta ,haɗa ido sukayi yana sakin mata murmushi mai dadewa a zuciya , Murmushin tayi masa tare da motsa bakin ta tana cewa " Ya Umair . Hannun sa yasa yana haɗawa da nasa tare da cewa " Mu tafi ".
***
Hajiya Turai dake ta aikin kaiwa da komawa ta hana kan ta zaune tsaye , Bakin ta sai motsi yake kaman mai cewa wani Abu , sai kuma ta kai ta kawo jikin ta na rawar kyarma .
Tako taji na takalmi Mai tudu amma sam bata juyowa ba daga kai ƙawon da take yi . Momy lafiya me yake faruwa ne??. Umaima tayi mata maganan tana ƙarikowa zuwa inda take . Cikin sauri Hajiya Turai ta juyo tare da sakin ajiyar zuciya kaman wanda aka mata mummunar bishara. Hannun ta takai tana riƙe Umaima tare da cewa " Umaima daga ina kike?? Kin je wannan makarantar ?? Allah ya kiyaye baku haɗu da Umair ba , da sai dai ayi wanda ba'a so. Kin san shi da zafi kaman.... Momy wai shine duk hankalin ki ya tashi haka ? To ai shi ya dawo dani yanzu ya koma .
Saurin buɗe baki Hajiya Turai tayi tana kallon Umaima , Kamin tace " Shi dai Umair ɗin?? Lallai Soyayyar ta gaskiya ce ba wasa . Tayi maganan a ƙasan zuciyar ta ,bata san saurin ya fito ba . Umaima ne tace" Momy kika ce mene?? . A'a shiga ciki mayi maganan daga baya . Ohk Umaima tace tare da juyawa tana barin Hajiya Turai anan falon da ta koma ta tsaya ƙyammm kaman soja .
Juyawa tayi tana ɗaga wayar ta tare da karata a kunnen ta ,Ohk Daddyn Fareesa Amma ya kamata mu duba al'amarin yaran nan , kar mu shiga masu hakkarin juna , Umaima tun ba yau ba ,ta nuna mun tana Son mijin ta ,abar su kawai su....Shiru tayi tana sauraren sa tare da katse nata maganan. Ohk to babu damuwa sai ka taho ɗin , Allah ya kawoka lafiya ".
***
Yau kwanan Umaima uku da dawo gidan Hajiya Turai , kullum sai Umair yazo bashi safe bashi rana bashi yamma ,kullum a aikin zuruntu yake , Wannan ya Dada faranta ran Hajiya Turai . Don tuni ta samu Ammie da maganan A shirya tarewan Umaima a satin nan , Wanda Ammie Maryam ta tsaida maganan a ranan Juma'a za'a taru ƴan uwa ,a ranan za'a tare da Amarya .
Jin haka yasa Hajiya Turai sanar mawa Su Baba da Hajiya Balki , acewan Hajiya Turai dangi da yan uwa su taho gidan ta anan Abuja a zauna ayi taron bikin anan gidan ta sai akai amarya , ɗakin mijin ta daga nan kowa ya watse .
Hajiya Balki ne tasa Bala'in kan cewa " ita sam a'a Gida za'a dawo da Umaima , ayi taron bikin daga nan sai su ɗauko hanyar Abuja . Nan baba Shima yace hakan za'a yi . Ana saura kwana uku tarewa Umaima da Hajiya Turai suka ɗauko hanyar dawowa gidan Hajiya Balki don dole ba don Turai taso hakan ba .
A ranan da suka sauka ,a ranan aka fara saka Amarya a lalle da sauran Abubuwan mu ta al'ada . Tun da Umaima a ka lukume ta a uwar ɗakar Hajiya Balki ,babu fitowa acewan Hajiya Balki shirya amarya ake yi . Mai gyarar Amarya kuwa tun daga Ƙasar mu ,wato Mali , aka ɗauko bhuzuwa da ta iya haɗa amarya ciki da waje .
Zaune ake a falon Hajiya Balki har da Su yaya Hannatu , Fatima ce ta leƙo tana cewa " Hajiya Ina Umaiman take ne??. Ai shigowa zakiyi daga ciki kuyi gulman taku .... Alama Fatima tayi mata da hannu , wanda Hajiya Turai ne ta leƙo tana cewa " Hajiya Angon ne dea yazo ya kasa haƙuri , saura kwana biyu amma sai zaƙwaɗi yake yi . Jin ance Angon yar jikalle yasa Hajiya Balki wangale baki tana Faɗin " Wayyo ALLAH sarki , Don Allah jika na ka kula mun da Umaimatu yarinyar kirki ce... Dakin ne kowa yasa Dariya , Umair da Julyb dake waje suma dariyar suke . Umaima Fito maza sako hijabi gudun rana...Kamin Hajiya Kaka Ta ƙare maganan ne Suka ga Umaima da hijabi tana cewa " Ku bani hanya ,don dama ita a takure take an rufe ta a daki zafi duk ya isheta.
Da ido Hajiya Balki ta bita a sarari tana cewa " Amaryar zamani kenan . Dariya Su yaya Hannatu sukayi kana suce " ai ke Hajiya kin rufe ta a ɗaki ba dole ta gaji ba. To ai gata nake mata ,mazan yanzu sai sunji mace ko ina zam³ sannan sai kaji zaman lafiya shiru ya ɗore .
Kamin Umaima ne ta fito Hajiya Turai ta nufi dasu Julyb ɗakin Halima Matar Ƙanin Baba , Wato Ɗan juma. Biyo bayan su tayi tana fiƙi fiƙi da ido saboda ranan dake kashe mata ido ,na ta daɗe bata fito haske ba . A hankali tasa hannun ta tana buɗe labulen tare da sallama .
Fatima ne tace Yauwa gata nan ma , Umaima ƙariko . Wow' mashaallh . Julyb yayi mawa Umair magana ƙasa ƙasa ta yanda daga shi sai shi zai ji . Ƙai Boss kaji Wani irin ƙamshi ,anya ta shiga hannu zaka barta tasha ruwa ma kuwa?? Kar fa ka kashe masu yar mutane ,don kasan kayi mata girma... Bige sa Umair yayi yana bin UMAIMA da ta ƙara masa wata ƴar lukuta , fatan ta sai sheƙi yake ta wani irin masifar ƙyau . Gyefen Hajiya Turai ta zauna , wanda kamin ta ƙare zama Umair ne yace " No taso muje mota muyi maganan acan Ni dake . Kallon sa Hajiya Turai tayi , Kamin Tayi magana ne Julyb yace " Kaji malam da rainin wayo ,me zaka yi mata a motan?? . Wurga masa Harara Umair yayi don ya gane ya ramfo sa ,sai cewa yayi kai fa ɗan iskan mutum ne . Na dai ji ku zauna anan cewan Julyb yana sa mawa Umair dariyar shakiyanci .
Hajiya Turai ne tace " Umair zauna , zamu baku wuri kuyi maganan taku anan ,Amma Hajiya Dako Rana bata barin ta fita ,sam ba zata yarda da fita har waje ba . Miƙa Julyb yayi yana kallon Fatima kamin yace " Ƙawar Amaryar mu taho muje naji me kuke buƙata . Murmushi Fatima tayi tana bin bayan sa tare da cewa " Ai su Fa'iza ma na hanya , kila da wani abun da Ni ban fadi ba . Hajiya Turai ne itama ta mike tana mawa Umaima wani kallo , wanda Umaima cewa Tayi " Momy na sani ai .
Kallon ta Umair yayi ,yana fahimtar duk wani shu'umancin na Hajiya Turai , don kallon ki kula dai tayi ma Umaima . Fichewa Hajiya Turai tayi a zuciyar ta tana furta " Shashasha . Bin bayan Hajiya Turai Umaima tayi da kallo , wanda kamin tayi Aune bata farga ba taji Umair ne yasa Mata fuskar shi tare da shigar da hancin sa yana shaƙar ƙamshin ji kin ta ,yasa kan sa baki ɗaya tsakankanin ƙirjin ta da suka ƙara cika na tsaban shan garirika , saurin matswa tayi tana yin baya tare da cewa " Yah Umair meye wannan kuma??. Amaryan kin yi kyau sosai , anya ma idan an kawo mun ke a washe gari zan iya matswa daga jikin ki??.
Banza ta masa tana cuno bakin ta a shagwaɓe tace " Nidai bana So.! Lumshe idanun sa yayi na jin wani yarmmmm komai nata tada masa da feelings take . Ohk Na bari Kinji .
Kallon sa tayi ganin yanda idanun sa har sun sauya , kauda maganan nata tayi tare da cewa " Yah Umair baka ga Yanda nayi ba , Wallahi Hajiya Kaka babu abun da take mun sai gasa Ni da zafin Uwar ɗakar ta , da ƙyar nake numfashi don Wahala . Kecewa yayi da dariya yana faɗin " duk ana gatan ta mu ne . Kaman ya kenan ? Tayi maganan tana kallon sa...!
VOTER'S #THE VIRGIN MAID #MR ROMANTIC ZAƁI NAKY NE💃🕊️
*AUNTY MMN TEDDY* *Littafin THE SEXXY BOSS na kuɗi ne Regular group₦300 VIP group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed Aisha keystone bank ko MTN card zaku tura ta wannan Numbobi 08081202932*
A maimakon taji ya bata amsan maganan nata ji tayi yasa Hannun sa yana shafa gyefen Haɓar hannun ta . Saurin kallon sa tayi tana watso da idanun ta waje tare da kallon sa ,gani tayi ya fito mata da harshen sa yana mata wani Abu tamkar zai lashe zumar jikin ta . Tsoron sa ne ya kamata da sauri ta fin cike hannun ta daga gare shi , Tana Ficewa da gudu daga Ɗakin . Baiyi yinƙurin kirar ta sunan ta ,ko dakatar da ita ba , don ta san ba zata dakatu masa ba , ƙaɗan daga Cikin zalaman da yake akan ta ya nuna mata , wanda ya gagare hakan , Hannun sa yasa yana shafa kewayayen Sajen fuskar shi , Sauke Ajiyar zuciya yayi yana ɗaukar Wayar sa , text message ya tura mata kamin ya miƙe yana ficewa daga Ɗakin Halima .
Ke Umaima Mijin naki sun tafi kenan?. Umaima da ta laƙume a can cikin ƙuryar Ɗakin Hajiya Balki ne tace " Eh mana Hajiya kin fa fiye saka ido . Na saka ɗin , Bari ayi Auren a Tare kayana kaf zan ɗauko na dawo gidan naku sai naga ƙaryar ta tsiya.! Buɗe baki Umaima tayi cike da tsiwa zata yi magana kawai sai taji sako ya shigo ta wayar ta , jan bakin ta tayi shiru da sauri ganin Mai sunan me turo da saƙon. Shiru Umaima tayi tana dubawa , This is the begging of all ,I luv you forever my Wife. Begging Shine Umaima ta furta Ni ban fahimta ba , anya Ya Umair bai fara zaucewa akan Mace ba kuwa??? , Umaima magana kike yi ne??.
Taji Muryar Hajiya Balki , jan baki tayi shiru bata tanka ta ba ,a Zuciyar ta tana faɗin Hajiya Balki kenan Shegen Son Gulma .
***
A ranan Friday gidan Hajiya Balki ya cika yayi Al'umma ƙwarai ,Umaima mai jama'a mutanen ta tun na ƙuruciya duk sun shigo mata shagalun biiki yayin da kowa ke fatan Alheri tare da fatan itace matar har abada. Kowa ya shigo ya fita gidan Hajiya Balki da mamaki da jin daɗin irin dangin Ahalin da kuma Mijin da Umaima ta aura suke yi . Kayan Solveniance kuwa ,haka zaki ga Mutane na tahowa dashi hannu ciccike a wasu irin jakunkuna wanda da dama basu taɓa ganin irin sa ba .don Ordering nasu akayi daga Dubai . Wasu zaka ga A ciki turmomi biyu na Atampha da Turare . Wasu kuma track Suit ne da Abaya , Yan mata kenan . Wasu kuma zallar Turaruka ne na jiki dana Kaya . Abun gunin burgewa kowa da sambarka yake fita gidan .
Tun misalin Ƙarfe uku na yammaci Girgin yawo ya dire a farfajiyar layin Su Umaima ,abin da ba'a taɓa gani ba kenan , manya da yara kowa fitowa suka yi kallon jirgin da Umaima za'a yi ɗagawa ta ciki , don bazawarin iskancin da Umair ya kusa tamkawa shine " Cewa yayi Amarya kaɗai za'a ɗauko masa abun sa ,baya buƙatar kowa bayan ita ɗin ga ita kaɗai. Ihu Umaima tasa tana kirar Hajiya Turai tare da sanar da ita tana kuka , Wannan yasa Cike da Ɓacin Rai Hajiya Turai ta kira Umair take sanar masa hakan ba mai yiwuwa bane ba . Don dole tasa Aka taho da motoci don Ƙwasar Sauran dangi da ƴan uwa . A wannan lokacin kuma Umaima da Yaya Hannatu Sai Baban Kafancan suka shiga jirgin su suka kai ta gidan Sir Umair Ahmad moddibo dake Abuja ,kusa dana iyayen nashi ,wanda hakan sosai ya daɗaɗa Zukatan iyayen nashi musamman na Hajiya Turai . Tun kamin su Shiga Umaima ke Ware waren ganin Babu Fatima rabon ta da ita tun ƙarfe ɗaya . Amma kuma sam bata ganta ba . A haka dai tayi hakuri ta shiga har suka isa . A farfajiyar harabar gidan Jirgin ta sauka , Wanda tana isa ne Taga An bi hanyar wucewar su tun daga farkon da jirgin ta sauka aka shimfiɗa wani irin royals carpet red Mai masifar ƙyau da fuxgar hankali.
Tsayawa Umaima tayi har su Yaya Hannatu suka zagoyo da Baban Kafancan ta riƙeta ,kaman wanda bata taɓa shiga gidan ba haka tayi masu. Wata Personal VIRGIN MAID ce ta ƙariko garesu cikin sauri tana welcoming ɗin su tare da nuna masu hanyar da zai kaisu har zuwa falon Umaima . Buɗe Baki Umaima tayi don mmkin wannan kuma wacece ? A sarari da bata san ta furta ba tace THE VIRGIN MAID In my House?? Girgiza kai tayi na saurin cewa " Abun da ba zai yiwu ba kenan .! Ba za'ayi min sakiyar da babu ruwa ba A THE VIRGIN MAID , littafin Maman teddy , labarin da zaku na karanta tashi kiji shi a jinin jikin ki ,tamkar yanzu nan take ta faruwa . To abun ka ga Ƙwararran Alƙalami 😄 .
Juyawa Umaima tayi tana bin bayan ta Wannan ma'aikaciya kaman yanda Su Yaya Hannatu suka yi , THE VIRGIN MAID MY VIRGIN SISTER ,tuno da furucin sa akan Matar nasa... Gaban ta ne ya yanke ya faɗi ganin yanda Yarinyar take juyi ta ko ina a cike take dam , hips da mazaunan , gata jajir kaman balarabiya . Saurin shan gaban ta Umaima tayi tare da Dafa Ta tana cewa " Baiwar ALLAH nace ba.! Juyowa Tayi tana wangale mata baki alamu ya nuna budurwan mai fara'a ce kana tace " Na'am Madam . Ke ce wace a cikin gidan nan?. Ni kawai mai saukar amarya ce daga Ɓangaren Iyayen Sir Umair na Oustralia a daren yau zana koma .
Sakin mata murmushi tayi tare da cewa " Wlcm Sister. Thknyou Madam . Juyawa tayi tana jirar isowar su Yaya Hannatu da suka ce da Ita " Me kika ce mata ? Ko kin san ta ne??. Saurin girgiza masu kai tayi kamin tace " A'a tayi mun kama da wata ce ,a cikin book Ɗin THE VIRGIN MAID . Wow Gaskiya wannan labari zaiyi daɗi ba'a magana , cewan Baban Kafancan ... Murmushi Umaima tayi kamin tace " Hajiya Har daku kuma kun ce hakan, yo Ƙwarai ma kuwa , Ko daga ji kin san antaɓo ɓarayuyuka da dama , wanda haka ake Son Labari. Wacce marubuciyar ?? Ni ku bani contact nata?? Vip Zamu yi magana da ita . Dariya suka saka Sai yaya Hannatu ta buɗe Baki tana cewa " Maman teddy kenan . Marubuciya mai kirki da sanin ya kamata ,sam bata da wulaƙanci .... Kai yaya Hannatu ke kuwa ya akayi kika san da hakan?.
Cewan Umaima tana kallon Hannatu da ta ce" Munyi interview da ita Ta Special. Ehh to ƙwarai na gamsu da maganan ki . Nidai yanzu Umaima ki bamu number ta , Kar a fara babu mu sai dai muji labari ba...Zama kuji Hajiya Macace mai karamci idan kuma ta fara ,tana da dubban masoya da zasu watsa mawa masoya dama da hauni . Allah yakai mu yasa A fara lafiya Amin .
Tun daga wajen falon Hajiya Baban Kafancan ke ya ra kyawu da tsaruwan ko ina na falon . Komai an yi shi an kuma tsara shi yanda ya dace. Suna kuji ba kuji ban shiga da Umaima ƙayataccen Bedroom ɗin ta ne suka ji motsi daga bayan su . Juyawa suka yi Ganin Fatima da Julyb ashe su tuni suka ƙariko . Saurin nufowa inda take Fatima tayi tana murmushi Umaima na bin ta da kallon Ai kin ƙyauta.
Hannun ta Umaima ta riƙe tana cewa "Kun riga mu kenan dama , ina ta bulayin neman ki . Ai bar bulayi gata ita ta fara shigowa . Julyb yayi maganan yana Murmushi . Magana yayi mawa Fati da ido sai gashi ta kama hannun Umaima tana cewa " Hajiya bari mu taho. Kamin Suyi magana ne tuni ta ja hannun Umaima tana nufa da ita wani Room ,Wanda Umaima Bata San Ina bane ba. Ganin Makeup Artist tayi zaune a gaban wani mirror tana jirar isowan ta.
Cikin sauri ta tashi tana cewa " Please muyi komai cikin sauri mu suke jira .
Ita dai Umaima bata kuma cewa komai ba , nan take wannan matan ta fara kimtsa ta cikin wani Gown Golden Wanda ya amshi fatan jikin ta . Juyawa tayi tana bin Fati da kallo sai yanzu ta fahimta itama Gown ne jikin ta dark blue ,to Ina zamuje haka.? Tambayar da take mawa Kan ta kenan . Wani hill shoe tasa mai ƙyau tare da maɗauri sirara shima Golden ,sai ɗan mini poss ɗin da ta riƙe. Make up ne simple amma mai ƙyaun gaske , sosai ta yi kyau tafito amaryan ta ainun .
Surayya ne ta shigo cikin sauri tana faɗin " Komai yayi ready kuwa??. Ganin irin azabtar kyau n da Umaima tayi yasa ta faɗin Wow ANTY kin Yi kyau fa . Murmushi Umaima tayi tana cewa " Allah ko? To na gode . Kallon Fatima tayi a hankali tace " Wai ina zamuje ne ko duk budan fuska ne ake mawa wannan Adon , Tayi maganan tana ƙare rufa kan ta da siririn shara sharan mayafin da aka rufa mata fuska . Mai Makeup Artist din ne ta juya tana kama kasan Gown din ta ,Kamin Fatima tace " A wancen Baban falon mai kaman hall abokanan Sir Umair ne harda Dangin Mahaifiyar sa , mutum ne fiye da 50 a ciki muje ,zasu ga amarya kowa yayi presenting Gifts ɗin sa ga Ango da Amarya . Saurin kallon ta Umaima tayi ,a zuciyar ta tana cewa " Yanzu cikin can har da Turawa kenan ? , Hannun ta Surayya ta riƙe tana tsayawa a gyefen ta . A tsanake suka fara shigar hall ɗin .
Gani tayi ana ɗagawa wani abu tun daga shugiwan su kaman shine shine yana sauka akan su a hankali . Tafi Wurin aka ɗauka ,yayin da Fareesat dake cikin mutanen in zaka Uwar surutu tayi saurin nufar Inda Su Umaima ke takowa da sauran Mutane , don matan Wurin duka nufan su suka yi aka rufa ma Amarya baya . Saurin nufan Mr Mc Tayi tana amsan mk tare da fara ku zanta Amaryar su , Da a ƙarshe take cewa " This the best couple ever Dana taɓa gani a rayuwata ,ya sadaukar da koman sa domin ta ,haka itama ta tsaya dakon soyayyar sa na tsawon shekaru .....ihu Wurin ya ɗauka ana tafi . Nan tayi saurin nufar Amarya da suke gab da ƙarikowa wurin tsayuwar su . Hannun Umaima ta riƙe ,tana dakatar da Fatima tare da mata wani Kallo tana cewa " Kece wace??.