Kenza eBookz

Triplets book 2 complete - Chapter 21

Triplets book 2 complete - Chapter 21

Triplets book 2 complete Chapter 21: Triplets book 2 complete Chapter 21. Bayin Allah sai magana jama'a suke musu a kan suzo su zauna, idan ma wata suke…

4,493 words

Bayin Allah sai magana jama'a suke musu a kan suzo su zauna, idan ma wata suke jira, ga wajen zama a inuwa, amma saboda basa jin yaren sosai sun ki kula kowa, har jama'a suka ga ji suka kyale su, kuma Ayla daman ta san haka zata faru, dan tasan koda ma da English jama'a suka yi musu magana, mawuyacin abu ne Rimsha ta yarda ta shiga cikin shagon mutun, ko kuma runfarsa ta zauna, ba zata taba yarda ba kome zai faru, dan Rimsha tana kula da jikinta da mutuncinta fiye da tunanin mai tunani, kuma bata son shiga harkar kowa, haka zalika bata son rainin hankali da wulakanci, shi ya sa bata kula kowa.

Sai wajen awa ɗaya da rabi, sai da taga sun kusa zubewa kasa sannan ta fito, tana dariya, ba su ce mata komai ba, hakuri ta ba su, ta ce musu ai tana can wata kawar ta ce ta tsayar da ita, binta da ido kawai suka yi, ba su ce ko uppan ba.

Wucewa gaba ta yi tana faɗin "Muje wajen takardun koyar girki, Rimsha ke ki gani, dan nasan kece mai son iya girki.

Da farko Rimsha ta ce bazata sake zuwa ko ina ba, idan ba gida ba, amma da ta ji takardar koyar girki sai ta daure kamar zata faɗi ta bi bayan Kausar.

Wajen wani shagon sai da takardun koyar girki suka je, sosai Rimsha ta ji daɗi, ta kuma yi sa'a takardar ba tsada sosai 200 Naira ne ko wani guda ɗaya, wananna ragowar 500 ɗin wadda ya rage musu Shikenan, ta ɗauko ta miƙa masa ta ce Abata takardu guda biyu, kala daban-daban, karɓa ya yi, ya ce su zaba.

Masu kyau kala biyu Rimsha ta zaɓa sannan ya basu canjin Naira 100, suka wuce zuwa gida, sai neman su da magana Kausar take yi, idan sunki kulata, sai ta fara yi musu habaici, suna jin ta, kuma sun san da su take yi, amma basu nuna wani damuwa ba.

Bayan sun koma gida, bai fi da minti 40 ba Kausar ta sake sako su a gaba a kan lallai sai sun ta shi sun rakar wani gida.

Kamar za su yi kuka haka suka hakura suka tashi, dama ita Rimsha bata cire hijabin jikinta ba, suna dawowa ta zauna ta fara karanta takardar girki abinta.

Kausar ta riga su fita, sannan suka bi bayanta. Sai tafiya suke yi, Kausar na wani babbuɗe jiki kamar wata niga.

Wani gida mai ƙaramin gate ta shiga da su, su dai duk in da ta yi nan suke yi. Tun da suka shiga gidan Kausar ta fara baya baya, basu ankara ba suka ji ihun wasu mahaukatan karnuka, juyawar da za su yi dan su yi wa Kausar magana, sai su ka ga ba Kausar ta ware, kafin su yi wani yunkuri wayan nan mayun karnuka sun fito daga cikin wani lungu a cikin gidan.

A guje suma suka juya, Rismha ta fi Ayla iya gudu. Suna fita gidan karnukan suka dakata daga cikin gida, su kuma saboda sun tsorata sai gani suke yi kamar karnukan suna binsu, hakan yasa suka rinƙa tikar gudu, Ayla ta faɗi, ta buga bakin ta saman wani dutse, sai jini ya fara zuba, amma haka ta miƙe dan a tunaninta, karnukan suna binta.

Ko da suka koma gida Kausar bata Nan. A palo suka sami iya, tana ganin sun shigo a guje ta miƙe tsaye tana faɗin Lafiya Rimsha me yasa ku gudu haka.

Ka sa magana suka yi, suka zube gwiwowinsu a kasa, suna hawaye, ga Ayla baki ya kunbura sai jini yake zubarwa. Ganin Jinin yasa Iya ta kariso wajen su, a ruɗe ta rungumesu tana faɗin "Ina kuka je? Me ya same ki Ayla" har lokacin ba su iya buɗe baki sun yi magana ba, sai haki suke yi suna mai da numfashi.

Miƙewa iya ta yi taje ta ɗauko musu ruwa mai sanyi roba ɗaya, ta dawo ta miƙa musu, har suna rige-rigen wajen sanya hannu su karɓa.

Ganin Ayla tafi shan wahala ya sa Rimsha ta hakura Ayla ta fara shan ruwan, sai dai bata kai ga gama sha ba, gaba ɗaya ruwan ya ɓaci da jini, haka Rimsha ta hakura da ruwan sanyin ta sha na rijiya, dama ruwan guda ɗaya ya rage a fridge ɗin, Iya bata ji daɗin hakan ba, ita ma Ayla bata ji daɗi ba.

Sai da suka huta, sannan iya ta ɗan gasawa Ayla bakinta da ruwan zafi, ya kumbura suntum, Allah sarki sai fuskar tata ya koma kamar ruɓaɓen alale.

Bayan Iya ta gama gasa mata bakin ne teka tambayar ina suka je, Rismha ce ta bata labarin sun je wani gida ne, kare ya biyo su, ta ɓoye mata cewa a kan Kausar ce ta kai su ta gudo ta baro su.

Sosai Iya ta musu sannu, sannan ta gaya musu kada su sake zuwa gidan, domin gidan wani pastor ne, kuma kabilar Ebo ne, sannan ko da ya ɗaure karnukansa ma, kada su sake zuwa dan ɗan iska ne yana lalata mata.

Sosai suka ji tsoro tare da yiwa Iya alkawarin ba zasu sake zuwa ba.

"Ina Kausar?" Iya ce ta tambaye su tana ƙoƙarin miƙewa. Cikin sauri suka fara kallon juna, Ayla kam bata iya yin magana sosai saboda bakin nata ya kunbura sosai.

"Iya ba mu ganta ba" Rimsha ta bata amsa, Iya na ƙoƙarin shiga Kitchen ta ce "Wannan yarinya, wata kila tana gidan su Waliya ce, to shikenan ni bari na ɗaura mana girki" cikin sauri Rimsha ta miƙe ta bi bayan Iya zuwa kitchen dan taya ta Aiki.

Ayla na zaune a wajen har Kausar ta dawo, tana shigowa cikin palon ko sallama babu, idon ta ya sauƙa a kan Ayla, wani mahaukacin dariya ta kwanshe da shi tana faɗin "Ayla me a bakin ki haka kamar an hura balo-balo" ta kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariyar shakiyanci, har da rike ciki.

Binta da ido kawai Ayla ta yi tana tunanin yadda yan uwanta maza ke kokarin lalata musu rayuwa, ita shine ma babban abin da ya fi ɗaga mata hankali, shine ma abin da ya fi jefa ta cikin tashin hankali, duk abin da Kausar zata yi musu, mai sauƙi ne a kan wadda Jami'u ke kokarin yi musu.

Kausar sai da ta yi dariyar ta mai isar ta sannan ta wuce zuwa cikin dakinta, a ranta tana faɗin "Allah yasa ita kuma Rimsha karyewa ta yi" sai dai ta manta cewa, ita Rimsha duk rintsi duk wuya bata manta askar, haka duk rintsi duk yuwa bata fita gida ba tare da ta yi addu'a ba, dan haka duk in da zata je tana karkashin kulawar Mala'ikun Allah ta'ala.

After some hours💖

Iya da Rimsha sun kammala girki, yau sun girka, semo da miyar ɗanyen kuɓewa, yanzu Rimsha ta kware a iya tuka tuwon semo, kuma yanzu ta iya girki kusan kala bakwai kenan.

Da yarabanci Iya ta ce mata ta fito musu da abincin Palo, yanzu tana gane yaren duk da ba sosai ba, sama sama haka take ganewa, idan aka yi mai ɗan tsawo, kamar yadda ɗazun a kasuwa, jama'a suka rinƙa ce musu su fita a rana suzo su zauna a inuwa, ta dai ji suzo su zauna, amma bata gane su fita a rana ba domin bata san sunan rana da yaren ba, hakan yasa ta yi banza da su, kuma dama ko da ta ji me suka ce ma, ba zata taɓa shiga cikin shagon su ko rumfarsu ta zauna ba.

Bayan ta kawo abincin palo ne ta koma ɗaki ta cire kayan cikin ta, ta ɗaura towel ɗin Kausar ta wuce toilet dan yin wanka.

Lokacin da ta yi wanka ta fito Kausar na zaune a ɗakin, sannu ta ce mata sannan ta wuce wajen drawer kayan ta, kamar ba Kausar a cikin ɗakin haka ta yi banza da ita bata amsa sannun ba.

Dogon riga Rimsha ta ɗauko, tana kokarin sakawa a jikinta, Kausar ta yi saurin cewa "A'a Meesha kayan nan nake son sakawa yau" cikin sauri Rimsha ta juyo tana kallonta, kawar da kai Kausar ta yi kamar ba ita ba.

Mamaki Rimsha ta ke yi, domin farkon zuwansu ko da Kausar ta yi niyar saka kaya, idan Rimsha ta ɗauki kayan, hakura Kausar ta ke yi, amma yau shine zata ce kayan take son sakawa lallai.

Mayar mata da kayar Rimsha ta yi, ta ɗauko wani zata saka, nan ma Kausar ta ce "Kai Rimsha ki nayar da wannan saboda bana son a saka shi yau, kinga last week kin saka, kuma idan kika cika saka kaya mutuwa yake yi" wasu zafafan hawaye Rimsha ta ji sun cika mata ido.

Haka ta hakura ta mayar da kayan, sau huɗu tana ɗauko kaya Kausar tana cewa ba zata saka ba, daga karshe ma cewa ta yi "Ni fa Rimsha jikin ki na kashe min kaya, da alama ke renon miyar kuka da tuwon dawa ce, idan ba haka ba, da kin saka kaya sai ya koɗe kamar ba lafiya ba, to ni gaskiya na ga ji, ba zan iya ba"

Hawayen da Rimsha ke kokarin ɓoyewa ne suka zubo mata, wani na bin wani, dogon tsaki Kausar ta ja, tare da miƙe wa ta nufi waje tana habaici "An zo an zauna mana a gida, a ci a sha a saka sutura amma sai a laɓe a cikin ɗaki ana zagin yan gida, kai butulu kam bai yi ba, a canza hali ko za'a ji daɗin rayuwa". Ta kai karshen maganar tare da ficewa daga cikin ɗakin.

Zubewa kasa a wajen Rimsha ta yi tare da dafe kanta tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

Iya na falo tana ta jiran ta, ganin ta jima bata fito bane yasa ta ce "Kausar ki kira Rimsha tazo kuci abinci". Toro baki ta yi tare da miƙe wa ta koma cikin ɗakin.

Rimsha tana duke a kasa kan gwiwowinta tana shan kukan ta, a haka Kausar ta iskota, wani daɗi ta ji ta saka Rimsha kuka, ta fara kuntata musu.

Ta ɗauki yan mintoci tana kallon Rimsha kafin ta ce "Ki ta shi ki ɗauki wando da riga ki saka ba dan halinki ba, sai dan na lura kina son ɓoye abin, baki so a gani, amma daga yau ni zan rinƙa baki kayan da zaki saka" ta kai karshen maganar tare da bushewa da dariya, cikin sauri ta sanya hannu ta toshe bakinta, kada Iya ta jiyo dariyar tata.

Miƙewa Rismha ta yi, tazo ta raɓa gefenta ta wuce tana goge hawaye.

"Kizo ki saka kayan mana, ko haka zaki fita?" Banza da ita Rimsha ta yi, bata kula ta ba

(Ni ko nace baki san jinin Nawazudden da bala'i zuciya bane, zuciya da izza a cikin jinin su yake kawai dan dai Rimsha tun tana karama mum ɗin ta ta koya mata hakuri ne, da Jehan ne ai baki isa ba, ke da gidan ku Jehan zata mai daki baiwa, jinjina Jehan Nawazudden yau ga ranarki)

Tsohon kayanta da ta cire suka mai da tsumma shi ta ɗauka ta sanya a jikinta, ta fito palo.

"Subhanallah Rimsha yau kuma wannan dattin kika saka a jikin ki, ke da kike da tsabta baki son datti ko kaɗan?". Cewar Iya, kakalo murmushi Rimsha ta yi tare da zama kusa da Ayla tana faɗin "E iya yau ina son tuna gida ne shiyasa" "To na ji, amma me ya saki kuka?" Cikin sauri ta ce "Ba komai Iya ni ban yi kuka ba" da yake iya bata son matsa musu sosai, ta san halin su yanzu kila akan gida ta yi kuka, sai ta kyaleta, tare da miƙa musu abincin su.

Karɓa suka yi suka faraci kenan Kausar ta fito tana wakar habaice habaicen ta.

Cike da ɓacin rai Rimsha ta cire hannunta daga cikin abincin, ta miƙe ta nufi Kitchen ta wanko hannun tata, sannan ta dawo ta zauna.

"Rimsha lafiya? Me yake damun kine?" Cewar Iya, ita dai Ayla ta san matsalar dan haka sai ta yi shiru, kuma da yake ita bata kai Rimsha zuciya ba, sai ta ci gaba da cin abincin ta.

"Iya ba wani abin da ke damuna, kawai dai na ƙoshi da abincin ne"

Wani sanyi Kausar ta ji a ranta, ta jawo abincin Rimsha tana faɗin "To tun da ta ƙoshi ni bari na haɗa". Tsawa Iya ta daka mata a kan ta ajiye abincin, ba musu ta ajiye tana turo baki, a zuciyarta tana tunanin ta yadda zata cusawa iya tsanar su Rimsha.

Ita kuma Iya miƙewa ta yi, ta dawo kusa da Rimsha ta zauna ta hau lallashin ta, dan ta lura Rimsha tana da bala'i zuciya, ga zurfin ciki, ko zaka kwana kana tambayarta meke damunta, idan ba ta yi niyya ba bazata faɗa ba, sai dai ka gaji ka yi shiru.

Da kyar ta iya shawo kan Rismha ta hakura, hakan ma sai da ta haɗa ta da Allah da annabi, sanan ta yarda. Sai godiya Ayla take yi ga Allah daya sanya Rimsha ta hakura, dan tasan halin ta, idan ta yi fushi da abinci, to ko kashe ta yinwa zai yi, ba zata ci wannan abincin ba, a hakan ma tana duba abin da annabi ya ce na latatba kada ku yi fushi, ba dan haka ba, Rimsha da ta jima da hallaka kanta da zuciya.

Iya tana zaune tana kallonsu har sai da Rismha ta ci abincin nan tas, sannan ta ce da Kausar ta ɗaukowa Rismha kaya, Rimsha na kokarin cewa bata so, Iya ta yi sauri ɗaga mata hannu tana faɗin "In dai kika ce baki so, to baki ɗauke ni a matsayin uwa ba kenan" shiru Rimsha ta yi bata sake yin magana ba.

Ita kuma Kausar ta miƙe ta nufi ɗakin nata tana turo baki tana faɗin "Ke ma Iya da son kalen dangi, yaushe kika taɓa ganin wani daban ya ɗauki wata a matsayin uwa, tab to idan ba ki sani ba ma, har zagin ki ake yi" "Ni dai kaya na ce ki ɗauko mini ba surutu ba".

Wucewa ta yi sai cika take tana batsewa, ita a dole an bata mata rai.

Kasan cewar tasan Rimsha bata son kananan kaya dan mugunta sai ta ɗauko mata, Rimsha kamar zata yi kuka ganin kayan da a ka ɗauko mata, ga shi kuma bata son yiwa Iya gardama ko dan saboda alkhari da ta musu. Jinin Nawazudden basa manta Alkhari komai kankantarsa, haka suke, haka iyayen su suka koya musu.

Iya da kan ta ta sanya mata wandon. Sai bayan ta sanya mata wandon ne tazo zata zuke zip ɗin rigar, a zafafe Rimsha ta damki wuyar rigar, kada Iya ta cire mata kaya a gaban su Kausar, ga shi ba wani vest ne ta sanya a ciki ba.

Abinma dariya ya bawa Ayla da Iya, sai murmushi suke yi.

"Rimsha dukkan mu fa mata ne kuma yan uwanki ne, me abin ɓoye ɓoye?". Cewar iya, girgiza kai Rimsha ta yi tana faɗin "A'a Iya mum ɗina ta faɗa mini idan yara suna kanana kana cire musu kayansu a gaban juna, hakan yana sanyawa yarana sha'awar lesbian, idan kuma mazane luɗu, haka zalika idan yan matan suna cire kaya a gaban juna shima yana sanya musu sha'awar lesbian, kuskure ne ka cire kayan ka a gaban koma waye, ko mahaifiyar ka, idan ba wata lalura ba kada ka cire kaya a gabanta, kuma ko a addinance ma yin hakan haramun ne, ganin tsiraicin ɗan uwan ka Allah ya haramta, ai ba'a banza Ubangiji ya haramta ba, saboda tsiraici yana sanya sha'awa in ma mace ko namiji, to yanzu an mai da abin kamar wasa, sai kaga yan mata da girmansu suna wanka tare su biyu a toilet ɗaya, sheɗan kuma yana daga gefe yana kallonsu, kuma hakan ya samo asaline daga laifin uwa, ita take cire musu kaya a idon juna tun suna yara, kuma idan zata yi musu wanka tana kai su cikin banɗa ki tare ta yiwa ɗaya wanka ɗayar na tsaye tana kallonta, bata damuwa saboda za ta yi tunanin ai dukkan su mata ne, ko kuma dukkansu maza ne, bata san babban kuskure take yi ba, a kwai wani hadisi da na karanta, in da annabi (SAW) yake tsawatar wa da nana Faɗima a kan yiwa Al Hassan da Al Hussaini wanka a tare, so cire tsiraici koma a gaban waye kuskure ne, dan yana sanya sha'awa ko ba ka yi niyar yin abu ba, shaiɗan zai buga maka ganga ka yi ba tare da ka sani ba, kuma Mum ta ce wani karin kuskuren ma da iyaye suke yi, sai su bar ƴara mata da maza suna kallon irin Indian Film ɗin nan, ana kiss ana runguma dukka a gaban su, kuma suna ganin mace da namiji keyin hakan, ai dole suma su ɗauki hanya".

Zuba mata ido kawai suka yi har ta kammala sannan Iya ta ce "Kina da gaskiya Rimsha, mu iyaye bamu damuwa ba, muna yin hakan, mu na ɗaukan kamar yara ne shiyasa muke haɗa su a toilet mu yi musu wanka, kuma idan misali a ce yara uku ne, sai ki ga mun yi wa biyu wanka mun baro su a ɗaki muna yiwa ɗayan wanka, kawai dan son jiki, muna bin sauki muna ɓata yaranmu da kanmu, wani lokaci kuma zaki gani idan kika gama yiwa ɗayar na karshen wanka kika fito zaki samu su biyun nan ɗaya na wasa da gaban ɗaya, idan maza kenan, a tunanin mu yara ne, so kawai ya ɗauki abin kamar abin wasa ne, shiyasa bamu wani mai da hankali a kan hakan, amma tabbas yanzu da kuka faɗa na gane yin hakan babban kuskure ne, shike ruguza al'umma, sai kaga ka dage ka bawa yar ka tarbiya, sai ka rasa ta ina ka samu tangarɗa idan ta lalace, ashe baka sani ba tun farko kake lalata farkon ginin, wani lokaci ma ƴaƴan namu mace ce da na miji ne, amma haka muke haɗe su muna musu wanka a tare, saboda shegen son jiki, ba zamu hakura mu fara yi wa daya, mu gama mu shirya shi tsab sai mu zo nu yiwa ɗayar ba, wani sain kuma sai ki ga uwa tana cire kayanta a gaban yaro, a tunaninta yaro ne bai san komai ba, duk wayan nan kuskure ne, ko kasa ɗan ka matashi ya yi wa kanwarsa mace wanka, Allah dai yasa mu ji mu gyara, amma Rimsha kin bani mamaki waye ya koya miki wannan dukka abin"

Yar murmushi ta yi har sai da dimple nata ya lotsa, "Mum ɗina ne ta koya mini, kuma ai na karanta su Fiqhu da sauransu, na san abubuwa da dama, kuma mum tana karamin haske har shima dad, sannan ni ina da yawan tambaya idan na ga abu, kalmar lesbian ma ni a wani kittafi na karanta shine naji kalmar ta mini wani irin, sai na je na tambayi mum, shine tamin bayani dalla dalla, har na gane nima nake yi wa mutane"

Leƙo fuskar ta Iya ta yi tana faɗin "Eyee da mum tana gaya miki ya kika ji sarkin kunya" rufe ido tayi da hannunta tana dariya kasa kasa.

"Kai gaskiya ba zan yarda ba, Rimsha dole mu yi sauri mu miki aure dan ke ai kin gama sanin komai". Cewar Iya, cikin sauri Rimsha ta ce "Kai Aure kuma Iya?"

Gyaɗa mata kai iya ta yi tana faɗin "Sosai aure kuwa, ai kin gama sanin komai ne, dole mu kai ki daga ciki" wucewa Rimsha ta yi ta shiga cikin ɗakin Kausar hannun ta riƙe da rigar tata.

Bata son tsayawa magana da Iya, dan kada Iya ta bawa zancen auren karfi, dan ita bata da wani buri da ya wuce ta je ta ga mum ɗin ta da Jehan ɗin ta, kuma ita bata son aure.

(Tofa Rimshan mu ma bata son aure, a'a lallai banga laifin Jehan ba)

Tana shiga ɗaki ta sanya rigar sannan ta yi zaman ta saman gadon Kausar tana tunanin GAR, ba abin da yake mata yawo a ƙwaƙwalwar ta fa ce yadda ya matso zai yi kissing nata, a hankali ta kai hannunta saman lallausan laɓaɓɓan ta, mai kama da fure, ta shafo lips ɗin nata tana murmushi ita kaɗai, daga bisani kuma sai ta maida hannun tata saman kirjinta tana shafa sunan Lion, lokaci guda wani tunani ya faɗo mata, idan ta koma gida Mum taga wannan zane fa, ya zata yi, ta sani ko Jehan ce ta ga wannan zane ba zata taɓa barinta ta zauna lafita ba bare kuma mum.

Miƙewa tsaye ta yi a zabure, tana tunani tare da danasanin me ya kaita ta zana sunan wanda ba Musulmi ba a girjinta, bayan ba musulmi bama bai san da zaman ta a duniya ba, sunan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya kamata ta rubuta ko sunan dad da mum ɗin ta, wai shin me ya shiga kanta ne, har ta aikata hakan. Sai tunani take yi, tunanin da ba shi da amfani, domin suna dai ya riga da ya zanu ba gogewa, ba ta tashi sanin kuskure ta aikata ba, sai yau da ta tuna da littattafan musulunci.

(Lalai Rimsha kin shahara, to ni dai na kwashe kaya na, na wuce gidan Abba)

💖💖GIDAN ABBA💖💖

Yau tun safe su Akil suka wuce kano shi da Imran da Irfan, kamar yadda suka yi sammakon safe zuwa garin Kano, haka ita ma Hajiya Umaiya ta dakawa Umaisha sammako da uban kayan wanki. Umaisha ta sha mamaki, ta ce ga engine wanki za ta yi amfani da shi, amma Ammie ta hana ta, ta ce ai tasan da washing machine ɗin, ta ce ta mata wanki da hannunta, har ga Allah Umaisha bata iya wanki ba, bata taɓa yin wanki ba, ko kananan kayan ta irin su pant breziya ba ita take wanke wa ba, mai aiki ke wanke mata, haka suka taso, ba abin da suka iya, kayan sawan su akwai mai wanke musu namiji ne.

Tun karfe shida na safe take wankin uban kayan Ammie, tana yi tana kuka har karfe 1 na rana, abin haushin ma shine jijjiƙa kayan kawai ta yi, ta kara musu datti, ba abin da ya fita, hakan kuma ba ƙaramin haushi ya bawa Ammie ba, cikin zafin nama ta hauta da faɗa da masifa, ta ko'ina ɗura mata zagi ta ke yi ba sassauci, sai da tayi zagin mai isarta, sannan ta sa ta a kan ta sake faro wankin daga farko, sai ta wanke kayan sun fita fes idan tana son zaman lafiya, ga shi bala'i yinwa take ji, kuma Akila ta kai mata takeaway ɗaya ɗakinsu kafin ta wuce school, amma Ammie ta ki barinta ta je ta ci abinci, ga kukan yinwa ga na wahala, ta yi har ta ga ji.

A wannan hali su Aafia suka tarar da ita, Aafia tare da Rufee da Anisa ne suka zo, Irfan ne ya sa driver ya kawo su, tun kafin su wuce kano, dan Akil ya gaya masa yana son Aafia ta je ta taya Umaisha kwana tun da kwana za su yi a Kano, kuma daman Umaisha ta matsa masa a kan ya ɗauko mata Aafia. Sai dai da driver ya ɗauko ta ne, sai ta ce ya biya su je su ɗauki Rufee da Anisa, idan yamma ya yi sai ya mayar da Rufee da Anisa gida, Irfan ya hana Aafia tuki yanzu duk in da zata je kai ta a ke yi a ɗauko ta.

Ganin Umaisha na wanki a tsakar gida, da ruwan famfo duk ta rame, hakan yasa Aafia banko wani uban ashar wadda baki ba zai iya faɗin shi ba.

"Kutumar uban can, ke Umaisha wani dakikin bagidajen ya saki wannan ɗan iskan aikin?!!"

Kasa magana Umaisha ta yi, ta kuma kasa miƙewa ta je wajen su, sai kara sautin kukan ta da ta yi. Aafia da Anisa har suna rige-rigen karisowa wajen ta, ita kuma Rufee sai bin gidan take da kallo, taga tamɓatsetsen gidan da ya ci uban nasu Aafia a komai da komai, ta saki baki galala kawai tana kallo.

(Kai Rufee akwai son duniya)

A tare Aafia da Anisa suka ɗago Umaisha, duk ta rame ta ba kyan gani. "Ba kuka zaki yi ba Umaisha, ki faɗa mana waye yake baki wahala haka?" Cewar Anisa.

Cikin kuka da kyar ta iya buɗe baki ta ce "Ammie yaya Akil ne, ita ce wlh kullun take azabtar da ni, Aunty Afi dan Allah ki mai dani gida, idan ba haka ba, zan iya mutuwa a nan".

Wani sabon ashar ɗin Aafia ta sake wulwulowa, tare da jawo hannun Umaisha suka nufi cikin gida, tana faɗin "Ke mara mutuncin mata ina kike?".

Ummi na zaune saman sofa, palonta sai kamshi yake zubawa Umaisha ta gyare ko ina tsab, ta ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya tana kallon Tv ta bar baiwar ta Umaisha a waje tana tikar aiki.

Jin hayaniyar su Aafia ya sa ta juyo tana kallon kofar shigowa, ganin su yasa ta ja tsaki tare da mai da kallonta kan Tv.

Gabanta Aafia tazo ta tsaya rike da hannun Umaisha tana faɗin "Ke dai wlh anyi azzaluma muguwa, annamimiya, yanzu uban me Umaisha ta miki ki ke azabtar da ita haka?" Anisa ce ta karɓi zancen da cewa "Baiwa ce ita da zaki saka ta wancan uwar aikin? To wlh muna baki last warning idan kika sake saka ta aiki sai kin yabawa aya zakin ta, ai ba baiwa aka kawo miki ba".

Miƙewa Ammie ta yi tare da riƙo wuyar rigar Aafia ta dalla mara maruka masu kyau guda biyu, sannan ta ce "Ke wlh da alama sai na koya miki tarbiya, to shi bappan naku ma me a ido na bare uban ku bare kuma ku? To wlh tun wuri ku fita mini a gida tun ban muku dukan mutuwa ba, banza ye marasa tarbiyya".

Sanin su Akil basa nan ya sanya Aafia ta yi kokarin ja da Ammie, sake riƙota Ammie ta yi zata dake ta, daidai lokacin Rufee ta shigo, cikin sauri ta tarewa Aafia tare da riƙo wuyar rigar Ammie tana faɗin "Ke tsohuwar kilaki, ashawo, ki kama kanki wlh, idan ba haka ba zamu nuna miki mun fiki zama tantiran ƴan bariki, yanzu sai mu miki dukan kawo wuƙa a cikin gidan nan, muga uban da zai karɓe ki, muguwa azzaluma, kin tasa karamar yarinya a gaba sai zaluntar ta kike yi, idan kin kai shegiya, ai manyan yan duniya zaki samu irin mu sai mu buga game ɗin, ba karamar yarinya kamar Umaisha ba, wadda kin kusa jika da ita, dan da ga gani ke old woman ce sosai".

Idan kaga Rufee yadda take tarewa Aafia faɗa sai ka yi zaton da gaske tsakani da Allah take yi, amma azahirin gaskiya ba haka bane, kawai dan taga Ammie ta mata kama da matar gidan ne hakan yasa ta zage take cin mutuncin Ammie sosai, dan a cewarta gidan ya mata, ta samu wajen zama.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull