Kenza eBookz

Triplets book 2 complete - Chapter 22

Triplets book 2 complete - Chapter 22

Triplets book 2 complete Chapter 22: Triplets book 2 complete Chapter 22. (Tof fa, lallai Rufee ai in dai gidan Abba ne, Bismillah zoki zauna, duk wanda ya…

4,455 words

(Tof fa, lallai Rufee ai in dai gidan Abba ne, Bismillah zoki zauna, duk wanda ya ci tuwo da gidan Abba wlh miya ya sha, bake yar son duniya ba Bismillah to)

Dun wani baki na Ammie yau sai da Rufee ta kashe mata shi, tatas ta mata, har sai da Aafia ta tsorata ta fara ce mata ta yi shiru, tana tsoron kada Ammie ta gaya wa su yayan Akil su ci ubanta. Amma ina Rufee ta ki yin shiru, tsab ta wanke Ammie, wankin babban bargo.

Idan kaga yadda yau Ammie ta yi shiru ta nitsu sai ta baka tausayi, gaba da gaban ta, yau ta haɗu da jiga-jigan yan bariki, wayanda suka fita gogewa a fannin iskanci da iya shege, wato Rufee da Anisa, dan Anisa ma ba baya ba wajen baki da iya faɗa, sai dai ita tsakani da Allah take tare da su Aafia, ba da wata manufa ba, kuma ita bata bin maza, cikakkiyar budurwa ce, amma ta iya faɗa.

Sai da suka tabbatar sun rufe bakin Ammie sannan suka wuce part ɗin Akil, Umaisha ta musu jagora.

Kwafa Ammie ta yi, a ranta tana faɗin "Kun jawo wa yar uwarku bala'in da sai ta gwammaci mutuwa"

Toh fa, su Aafia suna tunanin sun kashe wuta, basu san kara hura wutar suka yi ba.

(To mu dai koma Washington DC kafin mu dawo wata kila abubuwa sun ɗan gwaru a nan)

💖💖Washington DC💖💖

After some day's👌

A yanzu Tyrone ya samu sauki kuma ya dawo bakin aiki gadan-gadan.

Zaune suke a palon kasa, Michael ya tada kai da cinyar Uncle ɗin James wato Musharraf, yanzu Michael ya samu sauki sosai, sai dai ba gaba ɗaya ba, amma an samu cigaba sosai da sosai, yanzu yana iya tantance daidai da ba daidai ba, kuma ya fara koyan karatu da wasu abubuwan, sai dai shagwaɓar nan tasa tana nan.

Yanzu ma sai zubawa Uncle ɗin James shagwaɓa ya ke yi, Musharraf na biye masa, a yan kwanakin da suka yi, sun saba sosai, sun shakuda Michael fiye da yadda suka shaku da James, duk da cewa lokacin da James yake nan Musharraf baya iya tafiya, hakan yasa basa wasu wasannin tare, yanzu kuma yana iya tafiya, James baya nan, sai Michael ya maye masa gurbin James ɗin, idan kana son ku yi faɗa da Michael to ka taɓa masa uncle ɗin James ɗin sa, nan fa zai gwada maka shi Triplets ɗin The General of The Army ne, tuni zai ɗauko gun ya saita maka hanya, dan ma dai Lion ya tattare pistol dake cikin ɗakinsa dukka ya canza musu wajen zama saboda Michael, amma gaba ɗaya sojoji da bodyguards dake gidan, har wani girmama Musharraf suke yi, har sara masa suke yi idan zai wuce, kuma duk saboda Michael ɗan lalele.

Lion Tga Tyrone, tsaye suke gaban wani makeken desktop computer dake cikin ɗakin binciken su.

Tga da Tyrone sanye suke da Army trousers da kuma Army t-shirt, while shi kuma oga Lion yana sanye da irin wandunan nan masu aljihu dayawa a jikinsu, har ta gefen gwiwar su akwai aljihu, da kuma kyawawan ijiyoyi masu kama da igiyar boot, daga ta sama kuma yana sanye da farar t-shirt mara nauyi yar shara-shara, ya saki kyakkyawar gashin kansa, bai ɗaure ba, wannan guntu gashin na gaban goshin nasa yana nan, yar ramar da ya yi tasa idanuwansa sun kara girma.

Tsaye suke sun zubawa computer ido, Lion nata faman hargitsa dark black curly hair sa, alamar zuciyar sa na masa zafi, sai cizan red lips nasa yake yi.

Sun jima tsaye suna kallon yadda computer ke tariyo musu bayanan da suke bincike a kai.

Tga ne ya ce "Amma Lion wai wannan binciken na waye ne haka?" Shiru Lion ya yi na tsawo mintoci.

Har su Tga sun cire rai da zai yi magana, sai kuma suka ji sexy voice nasa yana faɗin "James ya yi kuskure, ya jefa kansa a in da mawuyacin abune ya fita, ko kuma ya rayu".

A sukwane Tga da Tyrone suka zaro ido suna kallon Lion, a tare kuma suka mai da kallon su kan desktop computer ɗin, dan su kara ganin abin da suke gani shin da gaske ne ko dai gizo idon su ke musu.

Sun jima sosai dukkansu a tsaye, sun yi mutuwar tsaye, dan sun kasa yarda da abin, sai wani gwalo idanuwan su suke kara yi ko zasu samu damar ganin akasin result da suke gani a system ɗin, amma ina wannan result da suka gani da farko shine dai a wajen.

Ganin haka yasa Tga ya ce "Amma Lion ba last month kasa su Tyrone sun tarwatsa kungiyar *I .D .A. E .S. A* ɗin nan ba?".

Dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, sannan ya fara magana a nutse.

"James ya sa na yi bincike a kan su, saboda na samu wasu abubuwa na tambarin kungiyar nasu a ɗakin sa, *I .D .A. E. S .A* sunan kasashen da suke da reshe a can ne, shine suka sanya a matsayin sunan kunguyar su".

Cikin sauri Tga ya ce "Wace kasa da wace kasa kenan?"

Ɗaukan wani ɗan karamin game Lion ya yi, irin wannan game ɗin da a ke haɗa shi da hannu, fara jujjuya game ɗin ya yi, yana kokarin haɗawa, zuba masa ido suka yi, sun ƙagu su ji amsar da zai bada, ga shi shi kuma idan ka masa magana sai ya ɗauki tsawon lokaci kafin ya amsa ka.

Haka suka yi ta dakon jiran amsar shi, har sun fara fidda rai, sai can suka ji zazzakar muryarsa ya fara magana, ya kuma lumshe dara daran idanuwansa.

"*I .D. A. E. S. A* Yana nufin I. India D. Dubai S. Spain, sune kasashen da na yi bincike na gano su jiya zuwa yau, so sauran ban san ina bane" cikin sauri Tga ya ce "Amma Lion why not nu duba kasashen da suka fara da wayan nan harufan A.E.A".

Nan ma Lion ya jima kafin ya ce mu su "Ba iya sunan kasashe bane a wajen, har da sunan garuruwa, ina kyautata zaton saura ukun nan sunan garuruwa ne, ko kuma sunan wajajen da suke haɗuwa".

Shiru Tga ya yi yana tunani ko zai gano wani abin, amma sai dai ba abin da ya iya gane wa, dan bai isa ya haɗa kwakwalwarsa da ta Lion ba, a shirmen sa wai zai gwada tunano sunan garuruwa dake cikin Spain India da kuma Dubai, sai ya ga fa aikin ba ƙaramin aiki ba ne, ba zai yiwu ya iya gane ko gari goma ba, aikin na manya ne, ya jinjina wa Lion da ya iya gane wayan nan ukun ma daga daren jiya zuwa yau, kuma ba'a faɗa masa sunan kasashe bane, kawai saboda ya saba aikinne, sai ya lura da yadda a ka rubuta sunan, bai yi kama da sunan jimillan abu guda ɗaya ba, kuma basu yi kamanceceniya da abu biyu zuwa uku ba, aikin akwai rikita ƙwaƙwalwa, ya za'a yi Lion ya iya gane garuruwan da suka fara da A.E.A a cikin duniyar nan tab, ai garuran da suka fara da haka suna dayawa, taya zai iya ganewa, har ya zaƙulo garin da ya kasance eh shine suke nema, aiki ja.

Dukkan su sun ɗauki tsawon lokaci a haka suna kallon computer, ba wanda ya iya yiwa Lion wata magana.

Sai can Tga ya ce "Amma Lion ya a kayi ba su saka sunan dabar su na nan ba?"

Shiru ya yi na tsawon minti 10 kafin gently ya ce "Already manyan cikinsu mazauna nan ne, kuma nan shine maɓoyarsu, ba zasu taɓa saka sunan maɓoyarsu ba, ina da tabbacin akwai su sosai a nan, ina buƙatar kama James da kai na, ina son isa gare shi tun kafin CIA su rigani".

Kara zaro ido waje Tyrone. Tga suka yi a tare, cikin sauri har yana haɗe words Tga ya ce "Lion kana nufin CIA na neman James ne? To me ya musu?"

Shiru Lion ya yi bai sake yin magana ba, dan shi ba mai buɗe sirrinsa ga kowa bane, ko da Tga yake uncle ɗin sa kuma na hannun damar sa, baya yarda ya buɗe masa sirrinsa, sai dai idan ya gama bincike ya basu umarnin a kan su tafi aiki kawai.

Har zaman nasu ya kare kowa ya watse Lion bai sake cewa komai ba, ba haka Tga ya so ba, yaso jin da wani kungiya da wanne James ya ke yi wa aiki, sai dai ba hali, dan bai isa ya tambayi Lion ba, kuma ko bincike zai yi, ba wani abin da zai gane, dan binciken Lion na daban ne, kwakwalwar ba ɗaya ba.

Sai dai fa Tga ya shiga matsanancin tashin hankali fiye da misali, domin zuciyar sa ba zata iya jurar rashin James ba, kuma yasan a wannan hali tabbas Lion ya kama shi, to da kansa zai harbe shi.

(BABBAR MAGANA, TOH FA YAU A KE YIN TA)

Shima Lion ɗakin sa ya koma ya shige toilet dan ya zubawa kansa ruwan sanyi, ko zai samu sauƙin raɗaɗin da zuciyar sa ke yi masa, har wani jiri yake gani, Bawan Allah tun jiya bai ci komai ba, ba abin da ya saka a cikinsa sai ruwa, ya dukufa bincike yana son gane in da James yake nan da lokacin kalilan.

Ni kuma tattara kayana na yi na tafi, sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu, much kauna my fans yan amana!!.🥰 [11/17, 12:27 PM] +234 906 579 6460: 💞💞TRIPLET'S💞💞

Sanya almakashin nan ya yi, ya fara yanka mata wandon jikinta, daga kafar wandon ya fara har zuwa ƙugunta, ta gefe kenan. Bayan ya yanke wannan gefen ya dawo ta ɗayar gefen ma.

Runtse idanuwanta ta yi a cikin zuciyarta take faɗin "Ya Allah, kai kace mu nemi taimako ka a lokacin da muke bukata, matikar munyi yakini da kai kuma mun yarda kai ne zaka iya biya mana bukatar mu, ya Allah ina tawassuli da sunayenka tsarkaka guda 99 ya Allah ka kawo mini ɗauki, kada ka bari wannan mugun ya lalata mini rayuwa, ya Allah alfarma girman zatinka da izzar ka, albarkacin girmanka ya Allah ka sauko mini da ni'imar ka a gareni, na kareni daga wannan azzalumi, kaine arrahmanu ya Allah, mai rahma a kan bayinsa, mun saida, kuma na miƙa wuya agareka, babu wanda ya isa ya yi wa bawa abin da baka tsara masa ba, ba kuma wanda ya isa ya hana bawa abin da ka tsara masa, babu abin da ya isa ya yi motsi a dukka faɗin sammai da kassa ba tare da izinin ka ba, ya Allah ka taimake ni, wasbunallahu waniimal wakil, daga karshe ta rufe addu'ar tata da salatin Annabi salatin ibrahimiyya

Shi kuma boda Jami'u almakashin yasa yana, ya fara yanka ɗayan gefen wandon nata. Yana tsaka da yanka wa kawai ya yanke jiki ya faɗi a gefen ta, ita kuma dama ta runtse ido tana hawaye.

Jin ya faɗi kusa da ita ya sanya ta waro idanuwanta da sauri, dan a tunaninta ya gama yanke mata kayan ne zai fara lalata mata rayuwa.

Rinannun idanuwanta ne suka mata arba da Ayla tsaye riƙe da katon katako a hannu ta, sai haki take yi, tana mai da numfashi.

Cikin sauri Rimsha ta yi kokarin yunkurawa ta tashi, ta mance a ɗaure take, ba zata iya tashi ba, kuka ta saka da wannan dashashiyar muryar tata, ga kuma rigar Kausar a bakinta, ita ma Ayla kukan ta saka tare da yin wurgi da katakon ta haye saman gadon ta rungumo Rimsha tare da cire mata tsummar rigar Kausar ɗin dake bakin ta, suka ci gaba da hawayen a tare.

Abin da ya faru shine, lokacin da Rimsha ke jan sakatar kofar ta kasa buɗe wa, to da ya zo ya fisgo hannunta, wannan jan ta da ya yi, dama hannun ta ɗayar na kan sakatan, yana jan ta, ta janyo sakatar ya fita, sai dai dukkansu basu lura da cewa sakatar ta fita ba.

Ayla kuma bayan sun je gidan, ta kasa samun nitsuwa, ta kasa zama waje guda, sai tunanin jikin Rimsha take yi, har kuka ta rinƙa yi a ɓuye.

Su iya suna can suna cin uwar sabada, an sake musu kiɗa, sai tikar rawa suke, shine ita ta lallaɓa ta saci hanya ta bar gidan bikin, ta kamo hanyar gida dan tazo ta duba jikin Rimsha ko zata samu nitsuwa, baiwar Allah ta kasa samun sukunin.

Kasan cewar bata san hanya ba, sau uku tana ɓata hanya sai ta sake komawa baya, da kyar ta Iya gane hanyar.

Lokacin da ta shigo gidan Allah yasa bata yi magana ba, kawai ta nufi ɗakin Kausar, tun da ga ɗan bakin-bakin kofar ɗakin take jiyo nishin Rimsha hakan yasa ta karisa da sauri.

Turus ta tsaya a bakin kofa ganin abin da ke faruwa, lokacin ya gama ɗaureta yana kokarin yanka mata wando, ga shi ya toshe mata baki. Ganin haka yasa Ayla ta ja da baya a hankali, zuciyar na tafasa kamar zai fashe ya fito waje, har ta fara hawaye, addu'a take yi Allah yasa bai lalatawa Rimsha rayuwarta ba.

Kitchen ta fara shiga, bata samu madaki ba, sai ta fito waje, da farko katon dutse ta ɗauke, sai ta ji bai yi ba, hakan yasa ta jefar, ta fara yan dube-dube, can ta hango katako, shine ta ɗauko cikin sauri ta koma cikin gida.

Ta shiga ɗakin a hankali-hankali take tafiya, Allah ma yasa Rimsha ta runtse idanunta a lokacin, shi kuma hankalin shi ya yi nisa yana tunanin yadda zai fara shigar Rimsha.

Tana isowa wajen ta ɗaga katakon da iya karfinta na karshen ta buga masa a kai, shine ya yanke jiki ya faɗi sumamme ne ko matatce ne wallahu a'alam, wannan shine abin da ya faru.

Sosai suke kuka. Sai da suka yi mai isar su, sannan Rimsha ta ce "Ayla kwanceni" Ayla bata iya jin me Rimsha ke faɗe saboda maganar nata baya fita sosai, sai da ta matso da kunnenta sai tin ɗan bakin Rimsha ɗin, sannan ta iya jiyo me take faɗa.

Cikin sauri ta sanya hannu tana kokarin kwancewa amma ina abin yaci tura, ba ɗaurin wasa ya yi mata ba.

Ganin ba zai kwancu ta daɗi bane ya sanya ta ɗauko wannan almakashi da ya fara yanka wa Rimsha wando, ta fara yanka kayan Kausar ɗin dukka tana zubarwa.

Bayan ta kammala, Rimsha ta miƙe ta rungumeta da kyau tana zuba mata godiya.

Itama Ayla godiya ta rinƙa yi mata, domin a cewar ta kome zata yi wa Rimsha ba zata iya biyan ta ba, domin Rimsha ita ce silar fitarsu Daular Mutuwa, shekara uku Ayla tana Daular Mutuwa, har ta cire ranta da fita sai ga shi Rimsha ta tazo ta zamo musu silar fita, hakan ya sa take kula da Rimsha sosai.

Da kyar Rimsha ta iya dirowa kasa daga saman gadon sannan ta miƙe tsaye, sai layi take yi kamar zata faɗi, wajen drawer kayan Kausar ta nufa, dogon riga ta ɗauka ta sanya, sannan ta ɗauki wani dogon wandon jeans ta cire na jikinta daya yanka ta jefar ta sanya wannan, sai binta da ido Ayla take yi.

bayan ta gama saka kayan nata, ta shirya tsab, ta fito da wannan paper da ta yi zanen Romeo a jiki, sannan ta ɗauki takardun girkin da ta saya jiya a kasuwa, ita dai Ayla sai binta da ido kawai take yi.

Sai da ta gama haɗa komai nata, bata bar ko abu guda ɗaya ba, sannan ta riko hannun Ayla tana faɗin muje Ayla.

"Rimsha ina kuma zamu je? Waye muka sani a nan?" Rimsha kamar zata yi kuka, sai layi take yi, ga zafin zazzaɓi, kanta kamar zai fashe mata saboda ciwon da yake yi mata.

Da kyar ta iya fara magana "Ayla kina son ne mu cigaba da zama a nan gidan? Kina son ne mu zauna su lalata mana rayuwa, ko ma su kashe mu baki ɗaya?".

Girgiza kai Ayla ta fara yi tana faɗin "A'a Rimsha bana so su lalata mana rayuwa, to amma abin da zaki duba a nan shine, waye muka sani a nan? Idan mun bar gidan nan ina muka nufa? Dawa muka san zamu haɗu? Gara wayan nan da already mun san halin su, mun san abin da suke nufi da mu, idan muka barnan bamu san da suwaye zamu sake haɗuwa ba, wata kila ma wayan da zamu haɗu da su sunfi wayan nan munin hali, dan haka Rimsha ina son ki tsaya ki yi tunani kin ji?".

Hawaye sosai Rimsha ta ke yi, "Ayla ya zama dole mu bar gidan nan, koma da su waye zamu sake haɗu, dole mu tafi, kada ki manta Ayla, muna Sallah sau biyar a rana, har ma mu kara da nafila, irin su walaha, shafa'i da witiri da sallar dare, sannan kada ki manta muna azumin litinin da Alhamis, muna askar da rokar Allah ya kare mu a ko yaushe, a kuma duk in da muke, In Sha Allah, Ubangijin ba zai taɓa barin rayuwar mu ta wulakanta ba, kada ki manta Allah da kansa ya yi alkawarin tallafawa duk wanda ya riƙe Sallah biyar a rana, yana yin su yadda ya dace kuma a kan lokacin su, ki sa a ranki Ayla Allah na tare da mu, kuma bayin Allah masu taimako basa karewa a duniyar nan, ki yarda dani mu bar gidan nan, kuma idan zamu fita, mu fita da yakinin Allah ya taimake mu ba wani ba, da izinin Allah zai kawo mana ɗauki"

Ta kai karshen maganar tare da fara tafiya tana tangal-tangal.

"Rimsha a hakan zamu tafi? Kina tafiya kamar zaki faɗi kasa" "Ayla kiyi wa Allah kizo mu tafi, idan kuma zaki zauna a nan ne to Bismillah, kada ki duba dan bana iya tafiya da kyau, niyar mu na tseratar da mutuncin mu shi zaki duba"

Tana magana tana tafiya, ganin hakan yasa Ayla ta yi saurin karisawa wajen ta, ta ɗan riƙota dan ta taimaka mata, shi kuma boda Jami'u ya ji bugun katako, ko motsi baya yi, haka zalika baya numfashi, da alama cikin kansa ne ya sha bugun da babu jini ko kaɗan, sai kumburi da kan nasa ya yi kamar anhura balo-balo.

Wajen gidan gaba ɗaya suka fito, sai da suka tsaya na yan mintocin da ba su fi biyar ba, sannan suka fara tafiya ta Eyankorin junction.

Sunyi Sa'a babu kowa, har kofar gidan su waliya ba mutane.

Da kyar Rimsha ta iya kai bakin junction ɗin, daga nan suka miki gabas suka ci-gaba da tafiya.

Sun yi tafiya mai nisa har suka sauƙa daga bakin titin suka fara ratsa lunguna.

Daidai wani kangon gida, Ayla ta zube kasa, saboda azababben ciwon mara da ya ziyarce ta lokaci guda.

Hankali tashe Rimsha ta yi kanta tana kiran sunan ta, sai murkusoso take ta riƙe cikinta, nan take ta fara hawaye, wani na bin wani.

"Ayla dan Allah ki yi mini magana, ki faɗa mini meke damun ki, na shiga uku na, Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, Ayla dan Allah ki ta shi".

Ina Ayla ko magana ta kasa yi, sai kuka kawai yake yi, Rismha na ƙoƙarin sake yin magana, idanunta suka mata arba da jini a jikin rigar Ayla, da yake doguwar rigar da ta sanya mai haske ne, sky blue ne. Ihu Rimsha ta saki, lokacin guda ta ji karfi yazo mata, dan a tunanin ta wani abinne ya sami Ayla, tabbas ta karanta mace na yin haila, sai dai bata san ya hailar take zuwa ma mace ba.

Da sauri ta miƙe ta bazama neman wanda zaizo ya duba mata meke damun Ayla, ko kaɗan Rimsha ba ta yi dana sanin barin gidan su Kausar ba, sai dai ita Ayla ta yi dana sanin yin hakan ɗin, domin a cewar ta, da tana gidan su Kausar ko ba komai za'a kawo mata ɗauki.

Ta hanyar da suka bi zuwa wajen, nan Rimsha ta bi, sai kuka take yi tana addu'a Allah ya dafa musu.

Tana kokarin fita lungun dan ta nemo mai duba mata Ayla, gaba ɗaya ta birkice, jiri take gani, saboda yinwa da kuma ciwo, bata gani sosai, saboda karfin hali da tausayi irin tata, hakan yasa ta rinƙa ɗaga kafa da iya karfinta kawai tana takawa, bata san inda take sauke kafar tata ba, domin bata iya ganin gaban ta.

Bata ankaraba ta ji ta yi karo da mutun, baya ta yi zata faɗi, cikin sauri ya riƙe hannun ta yana kallon kyakkyawar fuskar ta wanda ya birkice a yanzu.

"Lafiya baiwar Allah? Ina zaki je kike sauri hakan nan? Me ya same ki kike kuka?" Cikin harshen Hausa ya yi mata magana.

Jin an mata magana da Hausa yasa ta yi saurin waro idanuwanta waje.

Wani matashine, irin matasan fulanin nan, masu zuwa karatu ko dai wani abin, daga ganin sa, ɗan arewa ne, ba bayarabe bane, yana da tsabta jikinsa fes fes, ɗan gayu, ya ci gayunsa, daga gani kasan akwai naira a tattare da shi, hannusa ɗaya na riƙe da wani leda da a ka rubuta Item 7 a jiki, ledar tana da girma, sai tashin kamshin yake yi, kai daga gani kasan ba ɗan datti bane, a shekaru ba zai wuce 27 years ba, yana da kyau daidai gwargwado, kunsan jinin Hausa fulani da kyau ba'a magana.

Ganin shi yasa Rimsha ta kara fashewa da kuka, sakin hannunta ya yi yana faɗin "Lafiya ko dai baki jin Hausa ne? To bari na miki yarabanci ko fulatanci sai ki zaɓi yaren da kike ji ki bani amsa" haka ya maimaita tambayar da ya yi mata da farko, da yaren yarabanci da kuma fulatanci, ko zai samu ta amsa masa yare ɗaya.

Ciki ciki ta amsa masa da taimako take nema, sai dai bai iya jin taba saboda muryarta baya fita kuma ga shi tana kuka.

Ganin ta ki yi masa magane ya sa, ya sanya kansa zai wuce ta, cikin sauri ta riƙo rigarsa, tare da sanya hannu ta shake wuyarta tana kokarin kakalo magana da karfi.

Ganin haka yasa ya fahinci tana yi masa magana, amma baya ji ne, wata kila kurma ce ko bebiya, hakan yasa ya fara yi mata yar kurma-kurma, ita ma yar kurma-kurma kawai ta dawo yi masa, tun da magana yaki fitowa.

Da hannu ta nuna masa in da Ayla take, cikin sauri ya riƙo hannunta suka karisa wajen, gaba ɗaya jikin Ayla ya ɓaci da jini, saboda juyawa da ta rinƙa yi.

Shiru matashin nan ya tsaya, ya rasa ta ina zai fara taimaka musu, shi bai san komai game da period ba, ita Rimsha ta san yadda mai haila ya kamata ta kasan ce idan tana yi, ta karanta, sai dai kuma bata san ya mace ke fara yin hailar ba, ta san dai ance ya mace zata yi jini duk wata.

(Tofa yau ake yinta)

Miƙawa Rimsha ledar hannun sa ya yi, ya ce musu yana zuwa, karɓar ledar Rimsha ta yi tare da tsugunnawa kusa da Ayla tana hawaye.

Suna wajen har matashin nan ya dawo tare da wata bayarabiya, da kallo ɗaya ta yi wa Ayla ta gane matsalar, sai ta ce da saurayin ya saya mata always bari ta taimaka wa yarinyar suje gida ta wanke jiginta, ina ne gidan su?.

Kallon Rimsha ya yi, dan shima bai san gidan su ba, girgiza masa kai Rimsha ta yi, alamar ba su da gida.

Matsowa kusa da ita sosai ya yi ya ce "Kanwata kwata-kwata baki iya magana ne? Ko kaɗan ba zaki iya ba? Na zaci bebiyace ke ai ba kurma gaba ɗaya ba".

Cikin sauri ta ce masa "A'a ina iya magana" jin maganar ta na fita a hankali-hankali ne ya sanya ya matso da kunnensa kusa da ɗan bakinta dan ya ji me take faɗe, nan ta sanar masa tama magana.

Cikin sauri ya ɗago ido ya kalle fuskar ta, yadda ya ji zazzakar muryarta, ba karamin daɗi ya masa ba. "Wow beautiful girl and sexy voice" ya furta a zuciyarsa. Sake jefa mata tambayar ina gidan su yake ya yi, sannan ya mai da kunnansa kusa da bakinta. Nan ta gaya masa su yan Katsina ne, basu da gida a nan.

Ɗago ido ya yi yana kallonsu dukkan su biyu, lokacin guda ya ji yana son taimaka musu, dan haka sai ya ce da matar nan white house zata kai su, cikin sauri matar ta kalle shi.

Da yaren yarabanci ta ce "Haba Ahmad me yasa zaka lalata wa yarannan yaruwarsu? White House fa? Bai kamata ka ɗauki yara kanana kamar wayan nan ka kai su hotel ba".

Zaro idanuwansa waje ya yi, dan shi kwata-kwata bai kawo hakan a ransa ba, shi ba mazinaci bane, kawai sauƙa ya yi a white house ya kama ɗaki, dan ba shi da yan uwa a nan, amma bayan haka ba wani abin da yake yi a hotel, yana son taimaka musu sai dai ba shi da kowa, ya zamar masa dole ne ya kai su masaukinsa, in dai zai taimaka musu.

Da yarabanci shi ma ya ce mata "Iya kin san halina, yau shekara uku kenan ina zuwa garin nan, duk da baki san daga in da nake ba, amma ai ke da kanki kina yabon halina, bani da wani shagon da nake sayan kaya, sai shagonki, ke da bakin ki kike cewa Allah ya yi wa iyayena albarka, sun bani tarbiya, to ina son ki sani, ni ba mutumin banza bane, wayen nan da kike gani kanne nane, ba wai wasu bare bane".

Cikin sauri Iya ta fara bin fuskokin su Rimsha da kallo sannan ta kalli Ahmad ɗin, kasan cewar Hausa fulani duk in da suka shiga kamannin jini baya ɓata ɓuya, sai Iya ta ga kamanin Ayla da wannan matashin.

Yar murmushi ta yi sannan ta ce "Ahmad na yarda, ga wannan mara lafiyar kamannin ku ɗaya sosai da ita, mu je to ka yi mana jagora zuwa room ɗin naka, amma gaskiya wannan tafiku kyau sosai, ita ta yi kama da indiyawa, kila da babanku ta ke kama". Ta kai karshen maganar tana kallon Rismha.

Shi dai Ahmad burinsa kawai ta taimaka ta kai masa su ɗakin shi, dan yana son yaje wajen wani abokinsa ɗan school na su.

Haka matar nan ta saɓi Ayla a kafarɗar ta, kasan cewar kakkarfar mace ce, kun san yadda matan yarabawa suke ba sai an tsaya ɓata lokaci wajen zayyana muku yadda suke ba.

Allah sarki tana da kirki matar, bata ji kyamar jinin jikin Ayla ba, haka ta ɗauke ta suka tafi izuwa white house.

White House wani tampatsetsen hotel ne mai girma, wadda yake ɗan gaba da su kaɗan, dan haka ba su yi wani tafiya mai nisa ba suka isa wajen.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull