Triplets book 2 complete - Chapter 9
Triplets book 2 complete Chapter 9: Triplets book 2 complete Chapter 9. Da kyar suka samu Ayla ta yi shiru, tare da taimakawar Iya Ganiyu, bayan Ayla ta yi…
4,465 words
Da kyar suka samu Ayla ta yi shiru, tare da taimakawar Iya Ganiyu, bayan Ayla ta yi shiru ne Kausar ta tambayi Iya Ganiyu nawa ne kuɗinta na zane, don su biya ta su koma gida. Kin faɗa musu kuɗin ta yi, ta ce su je ta yafe musu, godiya sosai suka mata sannan suka wuce, Kausar ce ta ɗauka musu Coca Colarsu, don Ayla ta yasar da shi lokaci da take kuka.
Ko da suka koma gida a falo suka samu Iya Kausar tana zaune tana kallon Yoruba Film. Zama suka yi kusa da ita, da kyar su Rimsha suka iya shan Coca Colan da biscuit ɗin, sai shasshekar kuka tare da ajiyar zuciya Ayla take.
Matsowa kusa da su Iya ta yi ta ɗan shafa kan Ayla ta ce "Me ya same ki kayi kuka?" Kausar ce ta yi maza ta cafe zancen ta fara ba wa Iya labarin abin da ya faru, sosai Iya ta tausaya mata, sannan ta tambaye su yadda aka yi suka bar gidan iyayensu, Rimsha ce ta fara gaya mata cewar ta fito sayan ashana ne ƴan Daular Mutuwa suka ɗauke ta, sosai Iya ta tausaya mata tare da ba ta hakuri.
"Ke kuma Ayla ba ki faɗa mana ya aka yi kika bar wajen mamanki ba?" Cewar Iya, ɗaukar last biscuit da ya rage a cikin ledar Ayla ta yi, ta kai bakinta sannan ta ce "Tun da na taso na girma na yi wayo, mamana take cikin rashin lafiya, ba ta iya fita ko tsakar gida, ni nake zuwa na yi bara na samu mana abinci na kawo na bata ta ci a baki, idan za ta je banɗaki ni nake taimaka mata ta je, ba ta iya miƙewa da kanta, sai an taimaka mata, gidan da muke haya kuma, mu kaɗai ne a cikin gidan, babu kowa, ba zan taɓa manta wata ranar Laraba ba shekara uku cikin na huɗu da suka wuce, ranar jikin mamana ya tsananta, na dawo daga wajen bara na same ta tana wani irin numfashi kamar za ta mutu, sai kuka take, na ji tsoron kada ta mutu ta bar ni, sai na fito da gudu don na je na nemo wanda zai taimaka ya duba mini ita, a baya kafin na fara bara, duk inda na je neman taimako sai suce sai na basu kaina kafin su taimaka mini, mamana kuma ta tsawatar mini a kan hakan, ta ce ko mutuwa za ta yi kada na yarda na sayar da mutuncina, shi yasa na daina neman taimakon kowa a layinmu, sai dai na je wajen masu barar bakin kasuwa na zauna na yi bara. To wannan ranar Laraba na fito a gigice kamar mahaukaciya ina neman wanda zai taimaka wa mamana ya duba mini me ke damun ta, na je wajen mutane da dama amma ba su kula ni ba, don suna tunanin kuɗi nake so, na yi tafiya mai ɗan nisa ina neman taimako, har na bar layinmu. A gaba da layinmu na ci karo da wani mai ƙatuwar mota yana tsaye, ban yi wata-wata ba na karasa wajensa, har kasa na duƙa a gabansa ina haɗa shi da Allah da ya taimake ni ya zo ya duba mini me ke damun mamana, bai musa mini ba, ya ce na shiga mota mu je ya gan ta, na ruɗe na kiɗime ba na ganin komai sai mamana, hakan yasa na shiga motar, don mu je ya taimaka wa mamana, ashe ɗan Daular Mutuwa ne, shi ke nan tun da na shiga motar ban kara sanin inda nake ba, sai buɗe ido na yi na gan ni cikin Daular Mutuwa, na sha wahala fiye da tunanin mai tunani, shekarata kusan huɗu a can, babu kalar azabar da ban gani ba, ba irin tashin hankalin da ban gani ba, a gaban ido na ake kwakwalewa yara ido, a yanke wa mata nono da gaban su, baba da kuke ganin nan, shekaran sa zai kai talatin a Daular Mutuwa, su Mustapha kuma a gabana aka kawo su, ba zan iya misalta muku wahalar rayuwa da na sha ba, don ya wuce misali, sannan har yau da nake yi muku magana ban sake jin ɗuriyar wani da na sani ba, ban sani ba mamana tana raye ko ta mutu, duka ban sani ba!" Ta kai karshen maganar tare da kara sautin kukan da take.
Duk falon ba wanda bai yi wa Ayla kuka ba, musamman Rimsha ta fi kowa kuka a cikinsu, sai jan hanci Iya take.
Haɗuwa suka yi, suna hawaye suna rarrashin Ayla, da kyar suka samu ta yi shiru, hakuri iya ta ba ta tare da yi musu alkawarin baban Kausar na dawowa za ta karɓa musu kuɗi a wajensa, ta je da kanta ta sanya su a mota su koma wajen iyayensu, sosai suka ji daɗi tare da zuba mata ruwan godiya.
After some minutes👌
Falon ya yi shiru, miƙewa Iya ta yi ta nufi kitchen, da sauri Rimsha ta miƙe ta bi bayanta tana faɗin, "Ina son in koyi girki Iya." Miƙe kafafu Kausar ta yi ta gyara ta kwanta saman sofa tana faɗin, "Ba sai ki koya ba, ni me ruwana, abin da na sani dai shi ne a girka a ba ni na ci kawai na sani, ni ce ƴar auta a gidan nan, kuma ni kaɗai ce mace dole ba zan yi aikin komai ba, sai dai su boda Wasiu." Ita dai Ayla shiru ta yi tana son koyon girki ita ma, amma ba yau ba, don yau ta tuna da rayuwarta ta baya, duk jikinta a mace ba za ta iya ko motsa jikinta sosai ba.
Ita kam Rismha zagewa ta yi Iya na nuna mata yadda ake girki tana koya, don tun asalinta da ma tana da sha'awar koyon girki, shi yasa ko lokacin da suke gida tare da daddy tana yawan shiga kitchen wajen masu aiki ta tsaya tana ganin yadda suke aiki, saɓanin Jehan da ko hanyar kitchen ba ta bi bare ma ta shiga, ko abu take buƙata a Kitchen sai dai ta sanya masu aiki su ɗauko mata.
Kwanciya ita ma Ayla ta yi saman sofa ta rintse ido tana jin kanta na sara mata a hankali saboda kukan da ta sha, da haka har barci ya ɗauke ta. Ita kuma Kausar ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya daga kwance, ta kafe TV da idon tana kallo, Rimsha na Kitchen abinta tana koyon aiki tare da Iya.
Ni kuma na tattara kaya na, na wuce Kd don na je na ga wani hali Aunty take ciki?
💞💞KADUNA💞💞
Cike da tsananin tashin hankali Aafia ta figi mota zuwa asibiti, gudu take shararawa a kan titin nan kamar ba gobe, ga shi kuma dare ne, don lokaci karfe takwas da rabi za ta yi
Allah ya tsare, Allah ya kai su asibiti lafiya ba tare da wata matsala ba, tana shiga kuma ta yi sa'a likitoci suka karɓi Aunty hannu bibbiyu, suka shiga da ita A&E (Accident and Emergency) ke nan, sai kai komo Aafia take a bakin kofar, tana ta faman share zufar wahala da ke ta karyo mata ta gefe da gefen kunnenta, sai haki take kamar wadda ta ci uban gudu ta ƙoshi, gabaɗaya ta rasa sukuninta, ta yi da-na-sani har ta gaji.
A can gida kuma, Abbi da daddy su ma suna can cikin bedroom nasu, ransu na musu barazanar fita daga jikkunansu, sai fafutuka wajen neman ceton rayukan nasu suke, lokacin guda suka zazzage suka yi wata uwar rama kamar wadanda suka jima cikin ciwo, da ma shi Daddy Jelly akwai shi da dara-daran ido kamar na Jellynsa, ramar da suka yi ya sanya idanun nasa kara fitowa sosai abin gwanin ban tausayi.
A takaice dai daddy da Abbi zaune suka kwana, sun daina iya tafiya da kafafunsu, karfinsu duk ya kare, tun suna iya shiga bandaki da kafarsu, har suka dawo shiga da rarrafe, daga karshen a kasa wajen bakin gadajensu suka zube kan gwiwowinsu, suka kwantar da kansu a jikin gadon barcin wahala ya ɗauke su, ba su san abin da ke faruwa a cikin gida ba.
Ita ma Aafia kusan a tsaye ta kwana, don ba su ba ta damar ganin Aunty ba, ita kuma ba ta dawo gida ba, a kujerar da ke bakin kofar wajen ta zauna, idan ta jima ta jima sai ta tashi ta fara zarya a wajen tana tunanin ya su Abbi suke? Idan ta gaji da zaryar sai ta koma ta zauna, haka har dare ya tsala, a zaune saman kujerar wajen barcin wahala ya ɗauke ta.
A ɓangaren Umaisha kuma, kuka take sosai lokacin da Akil ya fita, bai kula ta ba yana jiyo kukan nata, amma yayi buris saboda ta raina shi sai wani cika yake yana batsewa, fuuu ya fice kamar wata guguwa.
Ya je ya shiga motarsa da niyyar ya tafi, sai kuma ya kasa kunna motar, a zahirin gaskiya har cikin dodon kunnensa, yake jiyo sautin kukan nata, ya kasa kunna motar tasa, har cikin ransa yake jin zafin kukan da take, sai dai kuma idan ya tuna cewa ta raina shi, sai ya ji ba zai iya komawa ya rarrashe ta ba, kuma ya kasa tafiya, don yana ji a jikinsa ba zai iya tafiya ya bar ta tana kukan nan ba, zuciyarsa ba zacta juri hakan ba. Shiru ya yi ya kasa gaba ya kasa baya, ya jingina kansa da jikin kofar motar yana tunanin ya zai yi?
Daga karshe dai ya yanke shawarar komawa don ya kasa tafiya, buɗe motar ya yi ya fito ya koma cikin gida.
Yadda ya bar ta tana zaune tana kuka, haka ya dawo ya same ta, kusa da ita ya zauna tare da ɗan rungumo ta a jikinsa yana faɗin "Is okey!" Kankame sa ta yi ta ci gaba da kukanta, hannu yasa ya ɗago haɓarta yana kallon cikin idonta, "Ya isa haka kukan nan kin ji?" Shigewa cikin kirjinsa da kyau ta yi ta lafe tana sauke ajiyar zuciya, ta daina kukan nata, shiru suka yi yana ɗan shafa bayanta a hankali, ya jingina kansa da jikin kayin gadon yana sauke numfashin a hankali, yana jin matukar son ta na kara ratsawa har cikin kwakwalwar kansa.
A ɓangaren Jelly kuwa, sosai Nawid ya ke tunanin yadda zai yi da ita, don a zahirin gaskiya ba zai iya auren Jelly ba, kwata-kwata babu son ta ko kaɗan a ran shi, Jehan yake so, ita kaɗai, bai taɓa jin son wata mace a ransa ba sai Jehan, yana ji a jikinsa cewa, ba zai iya rayuwa da ko wace mace ba bayan ita, har ƴar rama ya yi saboda tunanin mafita.
Gefen shi kuma Abbo tunanin yadda zai ɓullo wa lamarin Jelly yake, don a gaskiya ba zai iya haƙura da ita ba, yana bala'i son ta bai san ya zai yi da rayuwarsa ba.
Kamar kullun suna zaune saman table ɗin cin abinci, suna cin abinci dare, Nawid, Ummi, Jelly da kuma Abbo, Ummi sai faman cin abincinta take cikin kwanciyar hankali, tana farin ciki Nawid nata ɗa ɗaya tilo zai yi aure, kuma zai auri yarinyar da take bala'i so bayan shi, wato baby.
Ita kuma Jelly tana zaune tana ta yagar cinyar kaza hankalinta kwance, ba ta san me duniya take ciki ba, ba ta san abin da ake shirya mata ba, kun san dai Jelly da masifar kaunar nama, idan tana cin naman nan ba ta ji ba kuma ta gani, gabaɗaya barin duniyar mutane take, ko magana kake mata, ba ta amsawa matukar tana gaban nama. Hmm su Jelly manya.
"Abbon Nawid da ma ina son mu yi magana a kan auren baby da Nawid." Wani irin dum-dum gaban Nawid ya ba da duka, shi kansa Abbo dukan uku-uku jirginsa ya yi, har wani irin duhu ya gani ya gilma masa ta gaban idonsa, lokaci guda ya rasa nutsuwarsa, sai wani ƴan kame-kame ya fara yi kamar wani marar gaskiya
"Abbon Nawid lafiya na ga yanayinka ya canza cikin kankanin lokaci haka?" Cewar Ummi, ta yi maganar cikin kwanciyar hankali, shi ma Nawid ba karamin mamakin ganin Abbonsa ya shiga yanayi marar kyau ya yi ba. Da kyar Abbo ya iya sai ta nutsuwarsa ya ce, "Ina fa lafiya, ai ba lafiya, dole ki ga damuwa a tattare da ni." Zaro ido Ummi ta yi yayin da shi ma Nawid ya bude kunnuwansa yana jiran ya ji me Abbo zai ce? Sai addu'a yake Allah Ya sa Abbo ya ce, wannan haɗin da za a masa shi da jelly, ba ba ya so, bai yarda ba.
Cike da tashin hankali Ummi ta ce "Abbon Nawid ka mini bayani mene ne matsalar?" Ta yi maganar tana kara zaro ido cike da tashin hankali, dogon numfashi Abbo ya ja tare da sauƙewa a hankali kafin ya ce, "Ba na son wannan haɗi na Nawid da wannan yarinya baby?" Wani sanyi Nawid ya ji ya ratsa masa daga tafin kafar sa har izuwa tsakiyar kansa, wani murmushi siririn ne ya bayyana a fuskarsa.
A ɓangaren Ummi kuwa ƙara zaro ido waje ta yi ta ce, "Abbo mene ne ya sa ba ka son haɗin?" A takaice ya ce, "Saboda tsintaciyar mage ce, ba mu san asalinta ba."
_Ni ma na tattare kayana na yi nan wannan dirama ba a nan ba._
Sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai mu [11/11, 8:52 PM] +234 906 579 6460: 💞💞TRIPLET'S💞💞
🌹🌹Episode 15-16🌹🌹
After some day's, a yanzu Musharraf ya samu lafiya sosai, don yana iya taka kafarsa a hankali ya fito falon kasa, haka zalika shi ma Michael, ya samu sauƙin ciwukan da ya ji a sanadiyar accident ɗin da ya yi, sai dai matsalar kwakwalwarsa ce, har yanzu da saura ba ta warke ba.
Yau tun safe sosai helicopters ke shawagi a sararin samaniya, daga cikin Washington DC zuwa wajenta, kamar masu duba wani abin. Tun da daddy ya ji shawaginsu ya yi yawa ya san Romeo zai bar kasar ke nan, don da ma in dai ba fitar sirri zai yi ba kafin ya fita kasar sai an tashi helicopters sun yi ta kewaye cikin Washington DC, don tabbatar da tsaro, sai sun duba ko'ina. Idan sun tabbatar normal sannan private jet ɗin Romeo ya ɗaga, amma kafin ya ɗaga sai manya-manyan jiragen sojoji na kota-kwana biyu sun yi gaba, sannan nasa jet ɗin ya bi bayansu, sai wasu jiragen biyu su saka jet ɗinsa a tsakiya sai jirgin yaki ɗaya a bayan jet ɗin, don tabbatar da sun ba wa The General Of The Army kuma jika ga His excellency tsaro mai kyau, don ran Romeo daidai yake da ran zaratan sojoji 100 a cewarsu, don za a tara sojoji 100 ba za su iya aikin da shi kaɗai yake yi ba, kasancewar shi ba komai yake saka wa karfin dantse ba, akwai shi da aiki da kwakwalwa kamar agogo, manyan kasashe na duniya idan abin ya shige musu duhu sai sun nemi taimako daga wajensa, sannan kuma His Excellency yana bala'in kaunar sa fiye da tunanin mai tunani, duk cikin jikokinsa ya fi son lion, daga shi sai Michael yana matukar son su sosai. Ran Romeo babban abu ne mai matukar mahimmanci ba ga iya USA ba, har wajenta. Matukar Romeo zai fita Washington DC to fa sai an bincike ko'ina, har kasar da zai je, kafin ya dira cikin kasar sai helicopters sun tashi a cikin kasar ma, sun duba ko'ina da kyau.
Cikin taku irin na jaruman maza masu jini a jika, ya fito daga ɓangarensa, jikinsa na sanye da blue jeans mai bala'in kyau, sai Round neck T-shirt black color mai ratsin blue, a saman kayan nasa ya ɗora wannan jacket ɗin nasu, wato Puffer Jacket, ita ma black color, kalar rigarsa, kyawawan fararen kafafunsa na sanye da Hermes Birkenstock sandal, hannayensa na sanye cikin hand gloves baka, yayin da fuskarsa ke sanye da face mask baki, ya ɗaure dark black curly hair sa nan a baya, ya bar na gaban goshin kamar kullun. A yau fusatacciyar fuskar nan tasa ta fi ta koyaushe razana mai rai, domin yau fuskar tasa a ɗaure take tamau kamar wani hadari, har wani siraran jijiyo ne suka bayyana masa a goshinsa saboda ɗaure fuska sosai da ya yi, girarsa sun haɗe waje guda, saboda ɗaure fuska da ya yi, da ma gashin girar nasa ya kusa haɗewa saboda yawa, shi yasa da ya ɗaure fuska sai girar tasa ta haɗe, kwarjininsa ya kara bayyana sosai, tamkar wani zakin da ya yi shekara babu abinci, kallo ɗaya za ka masa ka san yau a fusace ya ke ainun.
Yana sako kafarsa ta saman benen zai sauƙo kasa, shi ma Musharraf yana sako tasa kafar zai hauro, bawan Allah bai san da cewa idan lion na saman staircase to ba wanda ya isa ya hau ba, har sai ya sauka, shi bai ma san waye lion ɗin ba, sunansa kawai yake ji.
Ga shi yau ran lion a matukar ɓace yake, don shi kaɗai ma sai wani huci yake, kamar ba lafiya ba, yana tafiya yana wani bubbuɗe kirjinsa, da ma kuma ga kirjin nasa a bubbuɗe.
A daidai tsakiyar staircase ɗin suka yi karo da Musharraf yana ɗan jan kafar sa a hankali yana ɗingisawa.
Wani mahaukacin mari lion ya sauƙe wa Musharraf a fuskarsa, wadda ya sanya shi yanke jiki ya zube kasa sumamme, kasancewar bene ne, hakan yasa ya gangara a sume ya sauka kasa, tsallakawa ta kansa lion ya yi, ya nufi hanyar fita daga cikin falon, don ma yana sauri ne shi yasa ya yi wa Musharraf mari ɗaya ya wuce.
"My lion where are you going?" Cewar daddy da ya fito daga ɗakin magungunansa da yake kasan benen, a hankali lion ya juyo da kallon sa kan daddy. Ganin fusatacciyar fuskarsa ba karamin razana daddy ya yi ba, ya sha jinin jikinsa don ya san halin ɗan nasa, kun san halin daddy da saurin birkicewa nan take ya ruɗe ya fara haɗa wa lion words yana in-ina. "My lion what is going on? What is happening? What is wrong with you?". Sai jero tambaya yake yi yana haɗe words, kuma ya yi maganar cike da tashin hankali.
Furzar da iska mai matikar zafi daga bakinsa lion ya yi, da kyar ya iya buɗe ɗan karamin bakinsa ya ce, "Zan je Spain ne dad, I need your prayer." Yana kai karshen maganar bai tsaya ya jira amsar da dad zai ba shi ba ya fice da sauri, don ba abin da zai hana shi dira cikin Spain yau, kuma bai son ganin tashin hankali da dad zai shiga, don ya san ba karamin tashin hankali zai shiga ba, ya san halinsa sarai, musamman ma Michael ba ya nan James ba ya nan, halin da zai shiga ba zai yi kyan gani ba, kuma ba tafiyar sirri zai yi ba ya zama dole daddy ya sani, ko bai faɗa masa ba, dole zai sani ko don jiragen dake shawagi a sama, shi yasa ma bai ɓoye masa ba, ya sanar da shi ga in da zai je kawai.
Yana fita daga falon ya nufi jerin gwanon motocinsa dake jere kamar kullun suna jiran tafiya kawai. Gidan nasu yau ya cika da zaratan sojoji sosai ta ko'ina, saboda sun san da tafiyar tasa, gabaɗaya sun jeru layi kamar wadanda za su tafi fareti, tun daga farkon kofar falon har zuwa, babban gate na gidan, Jibga-jibgan zaratan sojoji ne. Tun da ya fito suke ta faman ɗaga hannu suna sara masa tare da buga kafafunsu ɗaya a kasa.
Ko kallon in da suke bai yi ba, ya wuce ya nufi motoncin nasu, yau saɓanin kullun ne, don an kara yawan motoncin nasu, saboda kowa ya san da tafiyar tasa, don karin tsaro zuwa airport, shi yasa aka karo manya-manyan motocin sojoji masu numfashi.
Motarsa da ya saba shiga nan wannan Baturen ya buɗe masa kofar motar, ya shiga ya zauna. Yana zama Tga ya fito hannunsa riƙe da system da wayar lion, shi ma Tga yau sanye yake cikin kaki. Zuwa ya yi, ya miƙa wa lion system ɗin sannan ya ɗaga hannu ɗaya ya sara masa, karɓar system da wayar kawai lion ya yi ba tare da ya kalli Tga ɗin ba.
Runtse dara-daran idanunsa ya yi, har cikin ransa yake jiyo sautin kukan Brady, don yasa su Tga sun kulle Brady a ɗaki, saboda ba zai tafi da shi ba, kun san Turawa yadda suke da dabbobinsu, lion ya fi jin zafin rabuwa da Brady a kan su Tga, har ga Allah yana jin ciwon kukan da Brady ke yi, shi ma kuma Brady sai haushi yake dakawa da karfi, don Romeo ya ji shi ya dawo ya ɗauke shi, amma ina Romeo na jin shi, sai dai ba zai yiwu ya tafi da shi ba ne kawai.
Zuba masa ido sojan da zai tuka motarsa ya yi wato direbansa na yanzu tun da ya tura Tyrone gadon asibiti, da ma Tyrone shi ne asalin direbnsa, Tga kuma na hannun damarsa, kuma uncle nasa, ɗan autansu daddy. To har yanzu Tyrone na asibiti tun dukan da ya masa a kan watch.
Yau tun daga cikin gida suka saki jiniya mai tashin kai, tamkar fillin daga za su tafi, jiniyar yau ma ta daban suka saki, wadda da ka ji ka san manya-manyan jiga-jigan kasar ne za su fita.
Da gudun gaske motoncin suka tashi, don sun saka alamar danja a gaban motoncinsu, duk da cewa ko ba su saka alamar danja ba ma, babu wani abin hawa da ke hawa titin da suke kai har sai sun wuce, to amma yau da yake za su yi gudun wuce ka'ida sai suka sanya alamar danja don bin doka, kada su zama suna matsayin masu doka kuma suna karya doka da kansu.
Tun kafin su iso bakin gate security sun wangale musu katafaren gate ɗin gidan, a guje suka danna hancin motocinsu waje.
Ko'ina jiniya ta kareɗe cikin unguwar, da ma tuni jama'a sun san da tafiyar tasa don sun gani a labarai sai dai babu wanda ya san abin da zai kai shi Spain, sannan ba kowa ma ya san ina zai je ba, kawai dai sun san The General of The Army zai fita cikin Washington DC yau.
Tsabar gudun da suke shararawa a kan titin nan, gudu na wuce ka'ida, hakan yasa suka isa *Dulles International Airport* cikin ƙankanin lokaci. Ko'ina a cikin airport ɗin cike yake makil da manya-manyan sojoji da kuma jiga-jigan masu faɗa a ji a faɗin kasar, ga kuma manya-manyan gidajen TV wato ƴan jarida ta ko'ina, da ƴansanda ma ba a bar su a baya ba. Idan na ce zan tsaya zayyana muku jama'ar da suka halarci wannan airport ɗin to sai mu kwana mu wuni ba mu gama ba, kawai ku kwatanta a ranku, don fa waje airport ya cika iya cika, saboda lion bai yarda da su zo yi masa rakiya daga gida ba. Idan ba ku manta ba kun san family William Jacop gabaɗayansu ba sa yarda da mutane, ba wai kuma dan tsoro ko wani abu ba, haka suke ba sa son bako kuma ba sa yarda da mutun, kila suna da nasu dalilin na yin haka ba mu sani ba, shi yasa jama'a suka zo yi masa sallama a airport.
Suna danna hancin motocin su cikin airport ɗin, jerin gwanon motocin His Excellency Mr President ya danno hanci cikin airport ɗin, shi ma ya zo yi wa jikansa sallama.
Kusan a tare lion da His Excellency suka fito daga cikin motocinsu, dukansu manya-manyan jiga-jigan sojojin ne suka take musu baya. Rungume lion His Excellency ya zo ya yi, yayin da shi ma lion ya sanya hannayensa duka biyu ya rungumo kakan nasa sosai. Sai hotuna ƴan jarida ke ɗaukar su, don ba halin su matso kusa da su, ga shi kuma suna son jin me zai kai lion Spain, suna son tambayar shi amma ba dama, don ko lion shi kaɗai ya fito babu ɗan jarida mai karfin gwiwar iya tinkarar sa, ya ce zai masa tambayoyi, ballantana yau ga jiga-jigan dubban sojoji ta ko'ina, ai ko kusa ma ba su kawo a ransu za su samu damar ganin shi da ido ba ma, don ba tafiyar yara yake ba, taku yake irin na jaruman sadaukan yaki, da ya fito daga motarsa kafin su farga ya shige cikin jet ɗinsa. Amma Allah ya taimake su sun sa mu damar ganin shi albarkacin His Excellency, don ya tsaya su yi sallama.
Kiss His extcellency ya manna masa a kumatu tare da ɗan raba jikinsu yana masa fatan alkhari. Saboda face mask dake fuskarsa yasa bai sa mu damar yi wa His Excellency kiss ba, don ba zai cire face mask ɗin nan a gaban ƴan jarida ba, hakan yasa ya wuce ya nufi cikin jet nasa His Excellency na ɗaga masa hannu tare da fatan alheri.
Gabaɗaya sojojin dake wajen suka ɗaga manya-manyan bindigun su sama, suka saki harbi, ji kake ratatata ruwan wuta.
Wucewa yayi ya shiga cikin jet na sa, jibga-jibgan sojojin shida ne suka take masa baya zuwa cikin jet ɗin, su ka tsaitsaya a kansa, riƙe da manya-manyan jiga-jigan bindigogi masu numfashi, masu kai sako direct in da aka aika su. Zama yayi saman wani haɗaɗen sofa wadda da ka gan shi kasan na musamman ne, duk da cewa gaba ɗaya, luntsuma-luntsumar sofar dake cikin jet ɗin, sofa ne masu numfashi wanda idan ka gansu, kai kace a fadan shugaban ƙasa kake, saboda haɗuwar su, ga su da laushi sosai, ko wani sofa akoi wani kyakkyawan glass table a gaban shi, wanda za a ɗaura maka drinks ko wani abin. Kasan cewar mamallakin Jet ɗin sarkin son kamshi ne hakan yasa cikin Jet ɗin ke tashin wani fitinannen daddaɗar kamshi turare mai kwantar da hankalin mai shaƙa, ga kuma daddaɗar sanyin Ac dake tashi, abun gwanin burgewa, Jet ɗin nan ya haɗu iya haɗuwa, dan haɗuwar sa ma ba zai faɗu a baki ba, ɗauke yake da tambarin sunan Romeo kamar haka *The General of the Army Romeo, da manyan baki*.
Jingina kai ya yi da jikin sofar da yake zaune, ya lumshe dara-daran kyakkyawan idon sa, ya yin da jibga jibgan sojojin sa ke ta faman kallon gefe-gefen sa dan bashi tsaro, amma basu isa su kalle shi direct ba dan bai son yawan kallo, sai dai su kalli gefe-gefe da shi, dan su tabbatar ba wani motsi ko wani na'uran nesa dake ɗaukan shi, don yanzu daga nesa za'a iya dasa maka na'ura ta ɗauko ka duk halin da kake ciki, har makiya su iya farmakar ka, sai dai a na iya gane na'uran a jikin mutum idan a ka dasa maka, hakan yasa suke yawan kallon in da yake, don su tabbatar ogan su yana kalau yana cikin tsaro.