Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 103

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 103

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 103: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 103. Cool murmushi ta saki ga wasu guntun hawaye…

3,329 words

Cool murmushi ta saki ga wasu guntun hawaye na iya shege a kumatunta. Kaɗan ta karɓi abincin ta bar mishi sauran a spoon ɗin tana faɗin "To kai kuma ka ci wannan." Girgiza kai kawai ya yi tare da kai spoon ɗin bakinsa ya cinye. Lokaci na tafiya ita kuma ta zauna tana zuba mishi shagwaɓa tana kara cinye musu lokacin. Hakan yasa kawai ya fara bata abincin a baki dan su yi sauri, ya lura idan ba haka ya yi mata ba tabbas ba zasu bar cikin jirgin nan da wuri ba.

Sai da ya tabbatar ta ƙoshi tap sannan ya kyaleta tare da miƙewa ya ce su je. Kuka ta saka mishi a kan shi ya bai ci abincin ba, rarrashinta ya fara yi tare da ɗaukarta cak ya ɗauki Maltina ɗaya suka nufi waje. Sai zuba mishi shagwaɓa take yi a kan ita dai sai ya ci abinci gaskiya, shi kenan zai zauna da yunwa ko yaya?. Sam bai kulata ba, ya kyaleta tamkar bai san tana yi ba.

Sai da suka fito wajen ne ya sauketa tare da riko hannunta, dan yasanta da shegen tsoro, ko a wajen saukarsu ma zata iya bashi matsala. Haka kuwa aka yi, shegen tsoronta yasa ta kasa sauka daga jirgin, dan tana ganin kamar ruwan dake bakin tekun ma yana da zurfi. Girgiza kai ya yi tare da ɗaukarta ya saɓa a saman kafaɗa. Sai da suka sauka ya sauketa yana tunani wai shi kam anya ba horon sojoji zai fara bawa yarinyar nan ba kuwa? Yarinya sai hangen tsoro kamar farar kura.

Gaisawa da jami'an bakin ruwa su Mark suka yi. Tsayuwa Mark ya yi yana magana da su, shi kuwa Lion wucewarsa ya yi abinsa rike da hannunta suka nufi wata hanya. Tambayarsu Password da sauransu Jami'an suka fara yi. Sam Mark bai nuna musu kamar suma jami'ai ba ne, kawai ya fitar da password ɗin ya miƙa musu da sauran abubuwan da suka buƙata. Bin Lion da kallon suka yi suna mamakin yanayin jikinsa, ya yi musu kama da GAR na kasar America, basu san cewa shi ɗin ba ne. A takaice dai suka kammala komai da Mark ya zo ya sami su Lion suka wuce zuwa wani waje dake can gefe da tekun.

Tamkar gida wajen yake. Basu kai ga karisawa wajen ba ma jibga jibgan motoci har shidda suka nufosu. Mamaki Rimsha take yi na motocin waye kuma waƴan nan, gabaɗaya motocin bakake ne sai kyalli suke yi tamkar sabbi. Dakatawa suka yi da tafiya har sai da motocin suka iso garesu suka yi parking.

Buɗe mishi gidan baya na motar tsakiya Mark ya yi yana mai sara mishi. Hannunta ya saki kafin ya nuna mata cikin motar dan ta shiga. Cikin sauri ta shige ta zauna kafin shi ma ya shiga. Kara sara mishi Mark ɗin ya yi tare da rufe kofar motar sannan ya juyo ya nufi motar dake kusa da nasu amma ta baya.

Yana ƙoƙarin buɗe kofar motar ne wani kyakkyawan matashin Bature fari kal da shi mai kirar karfi ya fito daga cikin motar. Kyakkyawan gaske ne, Allah mai halitta kamanninsa ɗaya sak da Aseef, kamar an tsaga kara. Shi kansa Mark sai da ya ɗan yi jim yana ganin wannan matashi, ya yi kama da Aseef sosai da sosai. Shiru ya ɗan yi yana karewa matashin kallo. Sai daga baya ya fahimci wannan ya fi Aseef shekaru, kuma shi idanunsa Sapphire blue ne, while na Lion kuma Sky blue, sapphire blue ta fi shiga kala sosai. Duk da cewa Turawa kusan kamanninsu ɗaya dama, amma dai wannan ya yi kama over da Aseef, harta gashin kansu brown color iri ɗaya, idanun ne kawai banbanci sai shekaru da ya fisu.

Ɗan rungumo shi matashin ya yi yana faɗin "Michael Trump?." Jinjina mishi kai Mark ya yi alamar e haka ne shi ne Michael Trump. Cike da fara'a ya ce "My name is Alex Trump, nice to meet you my brother." Shiru Mark ya ɗan yi yana jujjuya sunan iyayen nasu, ya ji sunan iri ɗaya ne, dukkansu Trump, Trump kamar abin haɗin baki. Abin da bai sani ba shi ne sunan kakansu ne Trump ɗin hakan tasa aka yawai ta masu irin wannan sunan a family'n, dayawa daga cikin uncles nasa sun yi wa kakan nasu takwara, shi ne yasa shi ma Alex ɗin sunan babansa ya zama Trump.

Jin motar da Lion yake ciki sun danna musu horn ne yasa Mark ya ce su shiga ciki sa karisa magana a hanya, sake rungumo shi Alex ɗin ya yi kafin su shige ciki. A tare motocin suka tashi zuwa cikin gari. Sai tambayarsa Alex yake yi a kan ina zasu je ne? Me kuma suka zo yi a kasarsu?. Shiru ya yi bai bashi amsa ba, dan idan baku manta ba shi ma fa Mark kamar gunki yake wajen rashin magana, baya son surutu sam. Haka Alex ya gaji da magana ba amsa ya kyale shi kawai ya zubawa hanya idanu yana kallon in da zasu je ɗin kawai.

Ita kuwa Rimsha tun da suka sako kafarsu cikin kasar Russia wani azababben sanyi ya turnuketa. Shi dai Lion ko a jikinsa dama sun saba da sanyi, ita kam bata saba ba sai ta dunkule waje guda abinta.

A ɓangaren Jehan da Areef kuwa, wato Nigeria gidan Lion na Kaduna.

Tana zaune a bakin bed ɗin nasa har ya shigo cikin bedroom ɗin ya sameta, wajen Aseef ya je dama. Saman bed ɗin ya haye tare da jingina bayansa da jikin headboard na gadon, ɗan Juyowa ta yi tana kallon shi kafin daga bisa ta mayar da kallonta a saman plate ɗin fruits ɗin da ta kawo.

Ƙoƙarin kai hannu take yi dan ta ɗauko ruwan ta zuba mishi a cikin glass cup. Ɗan gyaran murya ya yi mata wanda ya sanyata mayar da kallonta kansa. Hannu ya miƙa mata a kan ta bashi nata hannun bari ya gani. Ba musu ta miƙa mishi hannun nata, rikewa ya yi da kyau kafin ya fisgota ta tafi luuu ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa.

Kusan a tare suka furta wash. Shi ya furta ne saboda ta buge mishi wajen ciwonsa sosai, ita kuma ta furta ne saboda yanda ya fisgota har wani jiri ta kallah, sai da ta ji hannunta da ya ja ɗin ya yi mata zafi sosai.

Ɗaure fuska sosai ta yi tamkar bata san menene murmushi ba. A kule ta ce "Me hakan kuma?." Shiru ya yi mata bai tanka ta ba, sai ma kara matseta da ya yi a jikin nasa yana sauke numfashi a hankali.

Ƙoƙarin kwace kanta ta yi dan ta bar ɗakin. Amma ina ta kasa saboda ya riketa da hannu ɗaya da kyau. "Please ka sakeni bana so, ni ba yar iska ba ce, dan haka ka sake ni wlh ko kuma nayi maka ihun kwarto." Leƙo face nata ya yi yana kallon yanda take magana with her full confidence kuma cikin masifa. "Zaki iya yi mini ihu ne?." Ya faɗa a sanyaye.

"Me zai hana in dai baka sake ni ba." "Tom shikenan ɗan yi ihun bari naji, kinga daga nan sai na danneki a ɗakin nan babu mai kwatarki, kin dai san ko kin yi ihu ma uncle ba zai ji ba, dan yana sama, su kuma sojojin da suke kasa ba ruwansu da ihunki, haka zalika su daddy da su John, dan haka kina yi zan danneki a cikin ɗakin nan sai nayi miki hot kiss son rai'na, dama kin san na gaya miki ina son nayi kissing naki ko? To ki yi ihu zaki ga abin da zan yi miki yau Allah kuwa, ina ga sai na baki baby a yau ɗin nan."

Zaro idanu waje ta yi, ta san halinsa sarai, tsab wlh zai aikata duk abin da ya faɗa, ƙaramin aikinsa ne ya danneta ɗin ya yi abin da yake so kamar yanda ya ce, rufin asirinta kawai ta bishi a hankali su rabu lafiya, ko ta yi ihu ta bakin nasa a banza ne, dan babu mai shigo mishi ɗaki ba tare da izininsa ba sai TRIPLETS nasa, to kuma Lion baya nan, shi kuma Aseef yana tare da matarsa suna aikin da suka saba, wato shagwaɓa wa junansu, dan haka bama zai bar matarsa ya zo dan ya ji ihunta ba.

Ganin ta yi shiru tana tunani ne yasa ya ɗan matso da bakinsa kusa da kunnenta, can kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "Ko dai idan nayi miki fyaɗen na baki baby zaki yanke mini bananata kamar yanda kika yi wa wancan kazamin mutun ne?."

Jinjina mishi kai ta yi tare da kara ɗaure fuska tana faɗin "Sosaima, me zai hana na yanke?." Cool murmushi ya saki tare da miƙewa ya kwanta da ita. Cikin salo ya juya da ita a in da ya yi mata runfa da faffaɗar kirjinsa. Kasa kasa ya ce "To bari na gwada yi miki fyaɗen sai kema ki gwada yanke mini mu gani, amma fa ni nawa ba irin na wancan kazamin mutumi da kika yanke bane, shi ai ya tsufa ni kuma ban tsufa ba, matashi ne ni mai jini a jika, kuma jarumin gaske, dan haka sai kin samo wuka mai kaifi sosai kafin ki iya yanke mini nawa."

Dama an ce duk iskancinka akwai ubanka a iyawa, to ita dai Jehan ga ubanta a iya shege ta gani, dan haka sai ta nemi sulhu kawai dan su gyarota ta samu ta bar ɗakinsa ba tare da wata hayaniya ba, ta san wlh tsab zai iya aikata duk abin da ya ce, ba ƙaramin aikinsa bane ya mai da ita cikakkiyar mace a yanzun nan.

Karo na farko a rayuwarta da ta fara bawa wani hakuri ta kuma yi magana cikin girmamawa da ladabi. "Dan Allah kayi hakuri, ba bazan iya ganin naka bama bare na yanke, ni dai please ka kyaleni na tafi ka ji my boyfriend?." "Are you sure am your boyfriend?." Ya yi maganar yana ɗaga mata gera ɗaya. Jinjina mishi kai ta yi alamar tabbatarwa. "Okey give me a hot kiss first."

Turo baki ta yi cikin natsuwa ta ce "No mu a nan yin hakan haramun ne, ka bari tukun nan sai gaba." "Gaba yaushe kenan?." Shiru ta yi tana tunanin wani irin wayo kuma zata yi mishi again...... Kai jama'a wai wayo Jenan zata yi wa Areef. Innalillahi gaskiya Jehan baki san waye Areef ba ne shiyasa zaki ce zaki yi mishi wayo, tab yo ai ko daddynki ba zai ce zai yi mishi wayo ba bare ke, duba ga irin yanayin rayuwar da ya yi, ya zauna da mutane daban daban, ba abin da bai sani ba sai dai ya nuna bai sani ɗin ba.

"Amsa me, gaba yaushe kenan?" Ya katse mata tunanin da take yi. Ɗago idanu ta yi tana kallon face nasa kafin ta ce "Gaba idan muka yi aure." Ɗan zaro idanu waje ya yi kafin ya ce "Aure? Are you sure zaki aureni?." Jinjina mishi kai ta yi alamar e, ita dai burinta kawai ya saketa ta samu ta gudu ta bar mishi ɗakin, a tunaninta idan ta ce zata aure shi ta yi mishi wayon da hakan zai sa ya kyaleta tun da dama ya jima yana cewa ta yarda ta aure shi. Rashin sani yafi dare duhu, bata ma san already ai ita mallakinsa ba ne.

Shi kuma yanayi mata irin hakan ne dan ta koyi girmama na gaba da ita, ta kuma koyi bawa wanda ta yi wa laifi hakuri, ga shi dai yau a dalilinsa ta bada hakuri, abin da bata taɓa yi ba, kuma ta yi magana cikin girmamawa, dama hakan yake so, komai cikin dabara yake koya mata, ba hayaniya ba ɓacin rai.

Kara matso da face nasa ya yi daf da tata sosai yana sakin cool murmushi kafin ya fara magana, duk abin da take yi da abin da take gaya mishi ya san ina ta dosa, ya san da cewa idan an barta wai wayo take son yi mishi, amma sai ya nuna mata bai san komai ba, da yake shi ma ɗan duniya ne. "Amma kina so na ne da kika yarda zaki aure ni? Or you wanted to play with my heart?." Yana magana yana kara matso da face nasa kusa da face nata sosai.

Tsabar tsorata na ganin yanda ya matso kusa da ita sosai har suna iya jiyo numfashin juna, yasa har wani in'ina ta fara yi, maganarta na rarrabewa. Kun san dai babu wani namijin da ya taɓa gigin kwatanta yi mata abin da ya yi mata yanzu, dole ma Maganar tata taki fita straight. "E... A'a... Dama...........

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 09162620621*

80

Tsabar tsorata na ganin yanda ya matso kusa da ita sosai har suna iya jiyo numfashin juna, yasa har wani in'ina ta fara yi, maganarta na rarrabewa. Kun san dai babu wani namijin da ya taɓa gigin kwatanta yi mata abin da ya yi mata a yanzu, dole ma Maganar tata taki fita straight. "E... A'a... Dama... na ji ina sonka.... Sonka ɗin ne ji.......". Yatsa ɗaya ya ɗaura mata a saman lips nata jin yanda take ta zuba mishi magana wani a saman wani, sam bai ma gane me take faɗa ba.

"Calm down, ki natsu ki yi magana, ni ai yanzu ban fara yi miki komai ba tukun nan, ba kin ce zaki aure ni ba?". Da sauri ta jinjina mishi kai tana kara tsuke fuska alamar tsantsar tsoronsa ya bayyana a saman face ɗin tata. "Okey ai tun da zaki aure ni ba zan yi miki komai ba, yanzu dai saki jikin ki sai ki yi mini magana a nutse ko?."

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "To dan Allah ka bari na koma koda saman bedside drawer ne sai muyi magana kaji ko?." Sumbatar kumatunta ya yi yana mai kara jin tsantsar kaunarta har cikin karkashin zuciyarsa.

"Jehan you are so beautiful, i don't know the reason why duk time da na kalleki am feeling like in ɗaukeki cancak in sanya ki a cikin zuciyata, so that ki kalli irin tsantsar kaunarki da yake ciki, amma i don't why kike bani headache, i ask you several times a kan ki gaya mini season da ya sanya baki so na, amma you refuse to tell me, a koda yaushe kina kawo mini bad season wanda ke da kanki you know i can't accept it, saboda all season da kike kawowa, ba wan da hankali zai kama ba ne, yanzu ina son ki gaya mini menene matsalarki?."

Hakika kalamansa sun ratsa ziciyarta sosai, ya iya magana a nutse wanda ko baka so sai ta ratsa maka can cikin zuciyarka. A nutse ta fara magana. "Ni kawai bana son rabuwa da daddy na ne." "That is the only reason?." Jinjina mishi kai ta yi alamar e. "Okey tom shikenan i will do something about it, yanzu dai ba wannan ba, kinga yau saura kwana uku mu gama game ko?". Jinjina mishi kai tayi alamar e. "Okey to zaki rakani unguwa please?."

Ɗan turo baki ta yi tana girgiza kai alamar a'a bazata je ba. Why ya tambaya. "Nothing kawai ba zan je ba ne." "Even wajen duba mum zanje?." Zaro idanu waje ta yi tana faɗin "A'a zanje nan kam."

Cool murmushi ya saki kafin ya sake cewa "I really like your lips and your eyes, kai i like everything about you, because you are special." "Same here, i like your attitude, you are a very very good person, you have a gold heart, beautiful life, like the way my dad said." Ta kai karshen maganar cikin sanyayyar murya.

"Really?." Ya tambaya da mamaki a kan face nasa. Bai taɓa tunanin zata ce mishi mutumin kirki ba, akoda yaushe ya ɗauka kallon ɗan iska take yi mishi kamar yanda ta faro tun daga farko.

"Yeah you're a good person, most a time daddy bashi da wani magana idan ba naka ba, hakan ce tasa nima na yardanwa kaina you are a special, daddy baya zama da kowa, before shi ko friend bai da shi, mum da Gwaggo sune friend nasa, sai ni da Rimsha, uncle Shitu PA sa ne, kuma yayan mum, sam daddy baya da yawan surutu, haka kuma baya yarda da mutane, amma i was surprised lokacin da naji yana yawan maganarka."

Shiru ya zuba mata idanu har sai da ta kai karshen maganar tata. Nisawa ya yi yana ƙoƙarin yin magana suka ji hayaniya a palon kasan. Ɗan kai kallonsa bakin kofar shigowa ya yi tare da sake dawo da kallonsa kanta. Zaro idanu ita ma ta yi tana jin surutan da ake yi a palon, tamkar faɗa suke yi.

"Muje ko baby? Muje muga suwaye ne." Ya faɗa tare da manna mata sumbata a kumatu, sannan ya mike daga rumfar da ya yi mata. Cikin hanzari ita ma ta miƙe ta sauko kasa.

Ta riga shi fita wajen dan tsabar saurin ta je ta ga menene, shi kuma ya tsaya sai da ya sha ruwan da ta kawo mishi.

Tana fitowa suka yi 4 eyes da mai irin face ɗin Lion kuma irin idanun Areef ɗan diramarta. Wani irin mummunar faɗuwar gaba ta ji, da farko ma ta ɗauka Lion ɗin ne, sai da ta kalli idanuwansa sannan ta gane wannan fa ash eyes gare shi ba blue ba. Asbunallahu wani'imal wakil ta furta a ranta jin yanda gabanta ya yi mummunar faɗuwa da ganinsa.

Gabaɗaya family sun yi cirko cirko suna tsaye, Aseef na rungume da Akila dake ta faman kwallah, ita ma ta kankame shi gam. Yanzun nan dirowar TGA cikin gidan kenan, yana shigowa palo ya cikaro da Aseef da Akila suna cin abinci, shi ne fa ya ce lallai sai Akila ta bar gidan dan baya son ganin bakar fata, to diramar da ake yi kenan, kuma kun san TGA renon Lion ne, sam bashi da sauki, bashi da imani bare tausayi, bashi da mutunci. Yanzu da za'a barshi tsab zai kashe Akila har lahira a wajen nan. Shi kuma Aseef ya rungume matarsa ya ce wlh babu in da zata je, dan ita ce farincikinsa, in dai zata bar gidan, to fa tare zasu tafi da shi gabaɗaya, zasu bar musu gidan, dan duk wanda ya ce baya son Akila a cikinsu, to shi ma kawai suce basu son shi, domin shi da ita babu banbanci, matarsa ce kuma yana son kayansa!!. Babbar magana, yau ake yinta.

Jin motsin fitowar Jehan yasa gabaɗaya suka dawo da kallonsu a kanta. Zaro idanu waje TGA ɗin ya yi yana mai kare mata kallo. "Okey wato bama mutun ɗaya bane, akwai wata ma kenan? Wai su waye ne waƴan nan ƙazaman?!!." Cewar TGAn, kuma ya yi maganar cikin tsawa.

Readers Also Read