Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 102
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 102: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 102. "Where are you going?". Ya faɗa a sanyaye.…
3,372 words
"Where are you going?". Ya faɗa a sanyaye. "To ba kai ne ba?". Ta faɗa idanunta na cikowa da kwallah na zallar madarar shagwaɓa. "Me ni kuma nayi?". Hawayen ne suka fara zubo mata a saman kuncinta. A tsananin shagwaɓe ta ce "Ɗazun ina ta ce maka ka bari kaki, ka sakani kuka, amma yanzu sai ka ce me ya sami idanuna? Bayan kuma kai ne fa ka sakani kuka, kuma ga shi ina ta kiranka kaki ka amsa mini, uhm uhm ni Allah mun ɓata da kai."
Shi kam idanu kawai ya zuba mata yana kallon ikon Allah, sam baya ma jin abin da take faɗa, hankalinsa ya tafi wani tunani da ban, wannan irin magana tata shi ne yake kara tsananta azababben sha'awarta da yake ji.
Ganin bai tanka mata bane yasa ta yunkura zata miƙe daga jikin nasa ta sauka kasan gadon. Rikota ya yi yana mai cigaba da kallon ɗan guntun hawayen shagwaɓar dake face nata. "Look at me." Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa.
Make mishi kafaɗa ta yi tana ƙoƙarin kara shigewa jikinsa da kwantar da kanta da kyau a saman breast nasa. Sai a lokacin ta lura ashe babu riga a jikinta. A hanzarce ta rungume shi dan ta ɓuye breast nata, kuruci dangin hauka kenan.
Shi kansa ya ɗan yi mamakin yin hakan da ta yi, amma sam bai kawo cewa breast nata take ɓoyewa ba, rungumar shi ɗin da ta yin ne ya ɗan bashi mamaki.
Meesha, ya ambaci sunanta. "Na'am noori." Ta amsa kasa kasa. "Tashi ki yi wanka ki shirya kici abinci, kin ji jirginmu yana buga alamar mun iso madakata, so tashi ki ci abincin." "Zaka bani a baki?." Ta yi maganar tana ɗan ɗago kanta tare da runtse idanu.
Ya ɗan yi mamakin jin maganar tata, amma kuma shi ma zai so ya bata a bakin dan sam kwana biyun nan tana mugun wasa da cin abinci, wani lokaci ma sai ya yi mata magana take cin ɗan kaɗan ta bar saura.
"Noori zaka baki a baki?." Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "Idan har zaki iya kallon face na a lokacin da nake baki ɗin." Turo bakin sosai ta yi tana faɗin "Kawai dai ba zaka bani ba zaka ce mini." Shiru ya yi bai amsa mata ba. A duniya wannan kunya tata tana matuƙar burge shi, yanda take kin yarda su haɗa ido, da kuma idan abu ya bata kunya sai da rufe fuska da hannu tana murmushi, ba ƙaramin jin daɗin hakan yake yi ba.
Shiru tayi tana tunanin yanda zata yi mishi yau ya bata abinci a baki, ta san dai ba zata iya ganin face nasa suna fuskantar juna ba, to me yakamata ta yi?. Miƙewa ya yi da ita a jikinsa suka sauko kasan bed ɗin. Ɗan zaro idanu ta yi tana kallon lallausan wuyarsa while shi kuma yana kallon hanyar da yake tafiya.
Ta shagala da kallonsa sai jinta ta yi a cikin ruwa tsulumdum, kankame wuyarsa ta yi tana ƙoƙarin saka mishi kukan shagwaɓa. Yatsa ɗaya ya ɗaura a saman lips ɗin nata yana girgiza mata kai. Yanzu ba lokacin wasa bane, lokacin ya kure musu har sun isa madakatarsu a tafiya.
Matso da face nasa ya yi daf da tata a in da ya manna mata kyakkyawar sumbata a lips ɗin nata kafin ya juya ya fita zuwa ɗaya daga cikin bedrooms dake cikin jirgin dan shi ma ya yi wanka.
Bin bayansa da kallo ta yi har sai da ya kurewa ganinta. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani sabon azababben son mijin nata yana kara ratsata. Juyawa ta yi ta fara wanka, kafin nan sai da ta tsaya ta zubawa breast nata idanu tana tariyo duk abubuwan da suka faru ɗazun. Lokaci guda ta saki cool murmushi tuna irin abin da ya yi ta faɗa ɗazun, har da cewa ta yi mishi wasa da breast nasa, yanzu idan ka ce shi ne ya ce hakan zai ce wlh ba shi bane, dan ba'a cikin hayyacinsa ya faɗa ba, ya manta komai yanzu.
Wanka ta yi tare da fitowa ta nufo cikin bedroom ɗin. Mamaki ne ya kamata ganin ya fitar mata da kaya ya ɗaura a saman bed kafin ya fice daga cikin ɗakin. Karisowa wajen bed ɗin ta yi tare da ɗaukar kayan tana dubawa. Shiru ta yi a in da ta faɗa duniyar tunanin a ina kuma ya samo abaya? Ko dai a cikin kayan da Josephine ta saya mata ne?. Wani ɓangare na zuciyarta ne ya ce ina ai a kayan da Josephine ta saya mata babu abaya, gabaɗaya kananan kaya ne irin nasu na turawa, to shi a ina ya samo wannan abaya har da karamin hijabi fari tas? Sai zuba uban murmushi kayan suke yi sosai.
Ganin tunani ba wani mafita da zai bata ne yasa ta wuce zuwa wajen trolleys ɗin hannunta rike da kayan nata. A hanzarce ta shirya, abayar ya yi matukar yi mata kyau, ga ta dai'dai da jikinta tamkar dan ita aka yi shi. Da yake gashin kanta ya jike sai ta yi ƙoƙarin jona hand dryer ɗakin dan ta busar, amma ina yaki yi, hakan yasa ta hakura a in da ta yafo mayafin abayar kawai ta fito waje dan ta duba a wani ɗaki yake ta je ta ce ya zo ya jona mata hand dryer.
Tana sako kafarta wajen bedroom ɗin gabaki ɗaya sojojin nasa suka juya, lokaci guda suka bata baya. Ta sha ruwan mamaki na ganin hakan, barema yanda suka yi a tare, abin sai ya kayatar over. Bedroom dake kusa da nasu ta nufa.
Har zata yi sallama sai ta hango shi saman mirror chair yana busar da gashin kansa da hand dryer. A cikin zuciyarta ta yi sallamar dan kada ya ji. A hankali ta lallaɓo zuwa ciki kamar wata ɓarauniya. Jikinsa na sanye da wani irin haɗaɗɗen jeans fari tas da kuma high neck t-shirt sky blue, ya yi matuƙar kyau over, sai tashin wani azababben kamshi yake yi.
Lallaɓawa ta yi har ta ƙariso in da yake, da yake yana zaune ne sai tsawonta ya kai tana iya kallon kan nasa. Hannu ɗaya ta cusa cikin gashin nasa tare da saka ɗayan hannun ta karɓi hand dryer daga hannunsa. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗago idanunsa ta cikin mirror yana kallonta. Ta yi kyau over, sai satar kallon shi take yi bata san yana kallon ta ba.
Wani irin lumshe idanunta tayi tare da sake warosu a saman kan nasa. Gashin nasa ya yi mugun yi mata kyau. Shi kuma da yake kallonta ta cikin mirror har wani irin tsuma jikinsa ya yi na ganin yanda ta yi da sleeping eyes ɗin nan nata, dama idan baku manta ba, sune abu na farko da suka fara jan shi izuwa gareta, yana bala'in sonsu musamman idan tana jujjuyasu, haba ai har wani irin duniya yake lulawa a lokacin.
Busar mishi da gashin ta fara yi, tana yi tana cakuɗa hannunta cikin kan nasa. A hankali ya lumshe idanunsa saboda wani irin daɗi da yake ji yana ratse dukkanin ilahirin jikinsa. Ita kanta daɗin taɓa mishi gashin take ji saboda yanda yake da tsananin laushi ga tsantsi kamar me. A hankali ta kai ɗan bakinta ta sumbaci gashi tana sauke ajiyar zuciya. Yana jin duk abin da take yi mishi, jin saukar sumbatar ne yasa ya ɗan waro shanyayyun idanunsa waje. Zuba mata idanu ya yi yana kallon yanda take murmushin tana shafa gashin nasa.
Ƴan mintuna ta ɗauka tana busar mishi dan ya fara yi dama, ita karisawa kawai ta yi. Bayan ta kammala ta shafa mishi mayukansa dake saman mirror a wajen, lokacin da ta je ɗaukar mayukan ne ta fahimci ashe yana kallonta ta cikin mirror. Wani irin kunya ne ya kamata, kenan ya kalli sumbatar gashinsa da ta yi? Ta tambayi kanta. Lokaci guda ta sanya hannu ta rufe face nata tana murmushi. Shi dai har lokacin bai kawar da kallonsa daga kanta ba.
Sai da ta yi kora da kunyarta ya isheta sannan ta shafa mishi mayukan tare da tara gashin nasa waje guda. Da kyar ta iya ɗaurewa saboda bala'in tsantsi, sai da ya sanya hannu ya taimaka mata. Tun da yake a rayuwarsa bai taɓa ganin gashin kansa ta yi mishi tsantsar kyau irin na yau da ta gyara mishi ba. Bai san cewa matar aure tana da baiwa na wuce misali, kome ta taɓa in dai wa mijinta zata yi wa, to fa kyansa na daban ne, zaka ga namiji zai fita waje ya sayi abinci naira dubu ɗaya, amma zai cinye shi kaɗai wani lokaci ma bai koshi ba, amma da zai bawa matarsa wannan dubu ɗayan ya ce ta dafa musu abinci, da izinin Allah sai ta yi wannan abin da wannan dubu ɗayar su ci su koshi har ya yi saura, kaɗan kenan daga cikin ni'imomin da Allah ya yi wa matar aure wanda ba kowa ne ya san da su ba, sunanan bila adadi, idan nace zan tsaya zayyano muku baiwarsu, to sai mu cike littafin TRIPLETS fam bamu kammala ba, zai cinye mana ɗan sauran filinmu, dan haka a takaice matan aure dai Allah ya yi musu baiwa na daban, sai dai dayawa daga cikinsu basu san ta yaya za su yi amfani da baiwar ba, to Allah ya buɗawa kowacce ƙwaƙwalwarta ta iya sarrafa mijinta da kyau ta yanda zasu mori juna, mu dai muna iyaka bakin ƙoƙarin mu wajen ganin mun buɗe muku wasu abubuwa da baku sani ba dan ku gyara gidajenku!!.
Zazzakar muryarta ne ya katse shi da cewa "Noori na iya gyarawa? Ya yi maka kyau?." Ta kai karshen maganar tare da zuro hannayenta ta saman wuyarsa izuwa kirjinsa tana kwanto da kanta a saman kafaɗarsa. Lumshe idanu ya yi tare da sake buɗesu a kanta, ta kwantar da kanta shiru tana jiran amsa.
Hannun nata dake saman kirjinsa ya riko a in da ya jawota ta dawo ta gabansa. Saman cinyarsa ya nuna mata a kan ta zauna ba tare da ya yi magana ba. Ba musu ta zauna tana mai cigaba da murmushi.
Zame mayafin abayar dake kanta ya yi a in da ya ajiye shi a gefe guda saman mirror, da yake ya fita tsawo sosai sai ya zamana da ta zauna a cinyar nasa yana iya kallon tsakiyar kanta sosai. Hand dryer ya ɗauko tare da sake kunnata ya fara busar mata da gashi. Wani irin haɗaɗɗen murmushi ta saki lokacin da ta ji abin da yake yi mata. Duniya kenan, yau GAR ne yake busar mata da gashin kanta? Allah mai iko mai yin yanda ya so da bayinsa, yau dai gata a saman cikyar mutumin da take mahaukacin kauna tun tana yarinya, bugu da kari yanzu ya zama mallakinta, mijinta ne shi ɗin, ga tsantsar kulawa da yake bata, sam bata damuwa da tsantsar kishinta da yake yi, domin Areef ya gaya mata sai ana son abu ne ake kishinsa, to ta kwantar da hankalinta, idan Lion baya sonta ko kallon hanyar da take ma ba zai yi ba, so ne yaja yake kishin, kuma ta godewa Allah ma da ya bata namiji mai kishinta har haka, hakan na nufin shi ɗin mai tsantsar kula ne, zai bata kulawa fiye da tunanin mai tunani, duk wani motsi idan ta yi sai ya so jin menene yake damunta, ko dan kada wani ya raɓeta zai zamana kullum yana son ta kasance kusa da shi, haka zalika zai bata soyayya mai tsayawa a rai ta yanda bazama ta ga wani soyayyar a Tv ko a wani waje bama har ya burgeta, duk wani abin da ya san zata kallah a waje ya burgeta, to fa zai yi ƙoƙarin ya ga ya yi mata shi fiye da yanda ake yi a wajen dan kishin kada na wajen ya burgeta, kaɗan kenan daga cikin baiwa da falalar samun namiji mai kishi, ko takalmar sakawanki ba zai bari wani ya gani ba dan kishi.
Meesha, ya ambaci sunanta a hankali, ya kuma yi maganar dai'dai lokacin da yake kashe hand dryer yana tara mata gashin nata dan ya ɗaure. "Na'am Noori." "Tashi muje kici abinci sai mu wuce an gama shirya komai mu ake jira."
"Noori na koshi mu tafi kawai." "No zaki ci, because ba zan bari kici abincin gidansu kakanki ba idan munje, the are not Muslim, so zai iya kasancewa suna cin something da ba dai'dai ba a musulce." Zaro idanu waje ta yi tare da juyowa gare shi tana faɗin "Noori dama wajen kakana muka zo?".
Jinjina mata kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, sake juyawa ta yi tana fuskantar mirror tare da sakin wani ƙayatatcen murmushi. "Noori yanzu zan ga kakana wanda ta haifi daddyna? Tana gidan nasu ne? Da.....". Bata kai karshen maganar ba idanunta suka sauka cikin nasa ta cikin mirror. Cikin sauri ta runtse nata tana murmushi, bata san cewa ya tsareta da kallo ba.
Ɗan kwanto da kansa a saman kafaɗarta ya yi tare da daidaita fuskokinsu waje guda. Calmly ya furta "Open your eyes." A hankali tamkar mai tsoron wani abin ta ɗan waro idanun nata waje. Kai tsaye sai saman fuskokinsu ta cikin mirror. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon yanda suka yi wani azababben kyau, haɗin ya yi matuƙar dacewa, chocolate color and white color, abin ba'a magana.
"Are you interested?." Ya faɗa a hankali kamar mai raɗa, kuma ya yi maganar yana ɗaga mata gera ɗaya. Jinjina mishi kai ta yi alamar e, ɗaura hannunsa a saman shafaffen cikinta ya yi yana ɗan shafawa a hankali. Cike da tsokana ta sanya hannu ta shafo kyakkyawan sajensa zuwa wuyansa suna kallon juna ta cikin mirror. Yau dai ta daure tana kallon face nasa, amma ba cikin kwayar idanunsa ba.
"Noori." Ta ambaci sunansa. Tsareta da idanu ya yi ba tare da ya amsa ba. "Noori ina ka samo abaya?." Shiru ya ɗan yi na ƴan mintoci kafin ya ɗan juyo da kansa hakan tasa ɗan bakinsa ya kasance a saitin kunnenta. Raɗa ya fara yi mata a kunnen nata a hankali. Kyakkyawan murmushi ta sakar mishi tare da juyowa ta rungume shi da kyau.
Yatsa ya sanya mata a cikin dimple nata yana jin tsananin farinciki a tattare da shi. Sumbata ta kai mishi a wuyarsa ita ma tana cikin tsananin farinciki. Maganar da ya gaya mata a kunne ya yi matuƙar sanyata farinciki fiye da tunanin mai tunani.
(Ko me ya gaya mata?🤔 Amma muje dai zuwa zata fito fili ne ma muji.)
Hannunsa ɗaya ya ɗaura a saman bayanta a in da ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. Sai sakin murmushi take yi. "Why kike son yin smiling har haka?." Ɗan turo baki ta yi, a wannan karon bata runtse idanunta ba, sai ma ɗaga su sama da ta yi tana jujjuya su. A shagwaɓe ta ce "To Noori murmushin nawa baya yi maka kyau ne na dai'na yi?."
Shiru ya ɗan zuba mata idanu kafin ya bata amsa da cewa "Yana yi mini kyau over to over." "To Noori kai ma dan Allah ka yi murmushin ko sau ɗaya ne mana, ban taɓa ganin ko da sunan wasa kayi murmushin ba, tun da nake karama ina kallonka a Tv, fuskarka a ɗaure tamau na santa, har kuma izuwa yau a ɗauren take, ina son in gani ko da sau ɗaya ne kayi murmushin."
Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallonta kafin ya amsa mata da "I don't know how to do it, that is the reason why ban taɓa yi ba, even my pleasure yana son nayi, amma i don't know how to do." Shiru ta yi tana ɗan tunani yanda ya furta my pleasure wato Aseef, ashe dama ya iya kiran sunan soyayya, wato shi TRIPLETS nasa kawai ya iya sakawa wannan suna kenan?. Bata san ita ma sunan da yake kiranta ɗin suna ne na musamma ba, shi kaɗai yasan dalilin da yasa ya sanya mata wannan suna haka.
"Noori in koya maka yanda ake yi zaka yi mini?." Girgiza mata kai ya yi yana faɗin no. "To why baka son na koya maka?." Ta tambaya kamar zata yi kuka. Shiru ya ɗan yi kafin ya amsa da "Because bazata yi mini kyau ba, smile is for women only, ba zan iya yi ba ko da kin koya mini." "To Noori idan ina son kayi fa?."
Ɗan jan kumatunta ya yi yana faɗin "Zaki haɗa har da nawa sai ki rinƙa yi, it's okey ko?." Turo baki tayi tana tunani, kila ita kuma haka ne kaddararta, kila har ta mutu ta koma ga Allah ba zata taɓa ganin murmushi mijin nan nata ba, wato ma ita ce zata yi nashi murmushin? To fuskarsu ɗaya ne? Allah yaya Saif ɗin nan ya iya abu shi ma. Duk wannan zantuka a cikin zuciyarta take yin su.
Miƙewa ya yi tare da ita a jikinsa. Hannu tasa ta saƙalo wuyarsa tana kara lafewa a kirjinsa. Yana fitowa sojojin nasa suka sake juya musu baya cikin girmamawa. Tsananin tsoron ganin Rimsha suke yi, dan Mark ya ja musu kunne a kan kallonta, ya gaya musu kanwar oga ce, shi dai bai san cewa matar oga ce ma bakiɗaya ba, dan bai san da batun auren ba, ya dai san ogansa fa ya kamu da sonta, gudun kada ya yi ɓaran ɓarama ne yasa ya ce wa sojojin kanwar oga ne kawai. Sun sha ruwan mamakin jin hakan, amma basu da zaɓin da ya wuce su yi shiru, dan basu isa su tambayi Mark ɗin a kan yaushe oga kuma ya samu kanwa ba? Tun da su dai sun san TRIPLETS su kaɗai Josephine ta haifa, kuma ya za'ayi kanwar ogar ma ta kasance bakar fata kuma ƴar Nigeria? Amma da yake su dai umarni kawai suke bi sai suka yarda a kan kanwar oga ne, shi ne yasa suke mugun bata girma. Kun dai san suma ba yara ba ne, tsab sun fahimci soyayya ce mai zafi tsakanin ogan nasu da ƴar yarinyar nan, hakan tasa suke kara respecting nata fiye da tunanin mai tunani.
Saman table chair a cikin bedroom nasu ya sauƙeta, zama ya yi a gefenta saman ɗayan kujerar. Abincin ta fara zuba musu cikin natsuwa. Mikewa ya yi ya ɗauko wayarsa a in da ya turawa driver jirgin nasu sako da su dakata tun da tun ɗazun jirgin yake yi musu alamar sun iso madakata. Dama sojojinsa a tsananin tsorace suke na ganin sun fara haura iyaka kuma Lion ɗin yana sane. Amma bai ce a dakatar da jirgin ba, ba su san yana can yana zuba soyayyarsa bane yasa ya mance ma da sun isa madakatarsu, ga shi ƙasar da suka zo dama sai a hankali, to ace kuma tun daga farkon shiga kasa sun fara karya musu doka? Ai abin ba zai yi musu kyau ba, amma saboda isa irin na Lion sai da ya gama shan love nasa tas sannan na ce su dakata. Bayin Allan suna ganin rayuwa, basu isa su yi komai ba sai da izininsa Allah sarki.
In da ya tashi ya dawo ya zauna, ta gama zuba abinci, spoon ya ɗauka ya ɗebo da nufin ya kai bakinsa. Kuka ta saka mishi tana kumbura kumatu irin na shagwaɓa. Fasa kai abincin bakinsa ya yi a in da ya juyo ya tsareta da ido. Gabaɗaya ta zama ƴar rigima yarinyar nan, ya faɗa a ransa.
Ganin bai yi magana ba ne yasa ta tsananta kukan nata tana mai turo baki. "Meesha what happened? Why are crying?."
"To Noori ba kai ne ba, a gida fa idan kuna cin abinci da su yaya Aseef, sai ka bawa yaya Aseef first spoon naka cikin soyayya da kaunar juna, yanzu kuma ba yaya Aseef shi ne ni ba zaka bani first spoon ɗin naka ba ko? Yanzu fa ni ce yaya Aseef naka tun da baya nan?." Tana magana tana hawaye kamar da gaske.
Ɗago hannunsa ya yi a in da ya duba time a jikin diamond watch nasu na TRIPLETS. Jawota jikinsa ya yi yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi, bai yi magana ba sai dai ya ɗan matso mata da spoon ɗin alamar to ta karɓi first spoon ɗin nasa.