Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 13

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 13

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 13: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 13. Wata rana aka wayi gari Amarya ta yi yunkurin…

3,367 words

Wata rana aka wayi gari Amarya ta yi yunkurin dukar Na'ura, a lokacin kuma cikin ta ya kai wata biyar haka, ba imani Amarya ta yi yunkurin dukanta, aikuwa Abba ya yi mata ɗan iskan dukan mutuwa wadda har sai da aka kwantar da ita a gadon asibiti, daga nan ne fa wannan tsohuwar gaba ta faro tushe, dan kuwa da Dr Salman ya dawo ya ce ba zai taɓa yarda ba, da hannunsa ya miƙa Abba a police station aka rufe shi akan ya daki amarya, a wannan rana tamkar Naura zata yi hauka, babban ɗanta a police station, idan ba kaddara da soyayya ba akwai wanda ya isa ya rufe mata yaro ne, gida dukka ya birkice da kuka, Abbi ne kawai baya kuka yake rarrashinsu, Naura tana yi, Hassan da Hossain suna yi, yau sun ga ɗan karamin yaki bayin Allah.

Sai da Abba ya yi kwana biyu a rufe aka sako shi, Naura ta jigata sosai da kuka, ta yi nadamar musulta da ta yi, ta bar family'nta, ta bar dukka uban gatanta, ta yarda da Dr Salman, ta biyo shi, yanzu ya ci amanarta, yana azabtar da ita, ta yi danasanin cewa su dawo Nigeria. Abin da bata sani ba, shi ma ba laifinsa bane, iyayensa ne da basu kaunarta, su ne suka shirya dukka wannan abin.

Bayan kwana biyar da faruwar abin da ya faru na dukan Amarya da Abba ya yi, masifar Amarya dai ba abin da ya ragu, sai ma abin da ya karu, iskanci kala kala, a ranar da aka sallamota daga asibiti ta dawo gida, tun da ta ɗaura ido a kan daddyn Rimsha Allah ya jarrabeta da wani mummunar nufi a kan shi, ko da yake ba Allah bane ya jarrabeta, ita ce ta ɗaurawa kanta wannan wahala, wani irin azababben sha'awar daddyn Rimsha take yi, domin duk cikinsu ya fi su bala'in farin jini, ga shegen saurin shiga rai kamar me, yadda dai kuga Rimsharsa, shi ta gado, duk in da ya je sai an so shi, ga zahiri kuma kungani, yadda su Lion basu karɓar baki, amma shi sun karɓe shi hannu bibbiyu, to haka yake da shegen shiga rai tun yana yaro, ga bala'in kyau kamar shi ya yi kansa.

Amarya dai ta yi iya yinta akan ta yi wa daddyn Rimsha fyaɗe, amma ina abin ya ci tura, duk da yana matashi kuma ɗan tubabbiyar baturiya, ya sami kula ta uwa, ya yi dacen uwa da ta yi mashi tarbiya mai kyau, duk da Naura ainahinta ba musulma ba ce, amma da ta musulta ta riƙi addinin sosai, ta kuma koyi abubuwa da dama tun kafin ta haihu, haka ta koyawa yaranta addini, suka yi riƙo da shi sosai, har ma sun fi ainahin musulman da ba mix.

Idan suka je Bauchi kowa baya sonsu, sai su rinƙa ce masu ƴaƴan kafura, kyamatarsu kakanninsu suke yi, suna hantararsu, ita kuma Naura baiwar Allah duk da haka bata hana su zuwa ga dangin babansu, Abba yana da bala'in zuciya kamar babansu, sai ya ce shi wlh ba zai sake zuwa ga dangin babansu ba, ai suna zaginsu, suna ce masu ƴaƴan kafura, idan ya je wlh idan suka ce mashi haka, sai ya yi masu dukan mutuwa, a lokacin yana tashen faɗa kamar hauka, ai kuwa Naura tayi ta yi mashi nasiha a kan kada ya kuskura ya tanka, ba kakanninsa bane masu zagin nasa? To ya yi hakuri komai zai wuce watarana, fir yaki yarda, ya yi ta cika yana batsewa, ya ce shi dai ba zai yarda ba, wlh sai ya sumar da kakan nan nasu in dai bata dai na zaginsu ba, gudun kada ya je ya sumar da tsohuwa a banza ya kara ja mata bakin jini yasa Naura ta yarda ta bashi goyon baya akan ya daina zuwa, haka suma su Abbin suka daina zuwa Bauchi gabaɗaya, daga wannan lokacin suka rufe babin family'n babansu, suka cigaba da rayuwarsu.

A kwana a tashi lokaci ya ja, cikin Naurat na da wata 8, Amarya ta je gida Bauchi ta yi sati guda ta dawo, har lokacin kuma babansu yana manne da ita, ya guji Naura, abin ya yi Baiwar Allah yawa, ga shi bata isa ta ce zata koma kasarsu ba, domin kuwa ta watsawa iyayenta da ƴan uwanta kasa a ido, ta yarda da Dr Salman ta biyo shi, shi kuma ya ci amanar yarda, haka ta daure ta cigaba da zama cikin kunci tana kula da tarbiyar ƴaƴanta.

Ranar da Amarya ta dawo, tun da su Abban Imran suka yi ido biyu da ita, shikenan suka tare a gindinta suma, ta mallakesu, amma kuma Allah da ikonsa ta kasa mallake daddyn Rimsha da kuma daddy Anaya, ƴan biyun nan ƴan baiwa ne na gasken gaske kuwa, sam abin bai yiwa Amarya daɗi ba, domin ita burinta ne ta mallaki daddyn Rimsha dan ta sami abin da take buƙata, kuma duk mallake babansu da ta yi, baya hana shi kula su Daddy Rimsha, saboda su dai maganin bai kamasu ba, wani lokacin ma Amarya tana kiran shi ya zo su kwanta, zai ce a'a shi yau da yaran shi zai kwana, haka zai wuce ɗakinsu daddy Rimsha, su kaɗai yake kulawa a cikin ƴaƴansa. Sam amarya ta gaza samun sukuni, hakan yasa ta fara neman mafitar ta yadda zata salwantar da rayuwar yara biyun nan.

Dududu amaryar fa shekarunta 25 a duniya, iyayenta ke shirya mata duk wata manakisa, su burinsu cin dukiya, da ta je gidan ne ta gaya masu abin da su Abba suke yi mata, har da dukanta da Abba ya yi, shi ne mamanta ta kai sunan su Abba ga malaminsu aka mallakesu dan su samu su mulki gidan, su ƙori Naura su mamaye komai dukiya da kyawawan fararen turawan ƴaƴan.

A na tafiya a haka har cikin Naura ya kai wata 9, wata ranar Friday da ta kasance rana mafi bakin ciki a garesu, ranar da daddyn Rimsha ya gaza mancewa da shi, ranar data sanya Naura haihuwa ta shiri, ranar da ta kulla gaba tsakanin su Abba da daddy Rimsha, shi ne ranar da Amarya ta yi wa daddyn Rimsha wani mummunar sharrin wai yana nemanta da iskanci, kuma ta yi galaba akan shi ne ta haryar tabbatar masu da shaida, abin da ya faru shi ne.

Kiran shi ta yi ɗaki akan zata aikesa, a lokacin yana tare da mummynsa yana yi mata tausa, bawan Allah bai san komai ba sai Kaunar mummynsa da ƴan uwansa, ba in da ya sani a garin Kaduna sai school nasu, shopping da kuma gidansu, shi kuma Hassan yana ta faman shafa cikin mummyn nasu yana lissafa abin da zata haifa masu, kani ko kanwa, abin gwanin ban sha'awa da burgewa, duk wanda ya kalli yadda suke sai ya ji sun burge shi saboda yadda suke ta zubawa mummynsu hira, har lokacin kuma basu jin hausa sai turanci, suna bala'in kaunar juna tare da cikin mummynsu, sai murmushi suke yi abinsu, su Abbi kuma suna bedroom nasu.

Da farko da Amarya ta ce yazo, sai ya ce ba zai je kiran ba, sai da mummynsa ta sanya baki, shi ne ya je.

Yana zuwa ta rufe kofa, da karfi ta cire mashi kaya har sai da suka yi kokawa, jin ya fara ihu ne yasa ta fishi ɗaga murya wajen fara ihu ita ma, ta ɗauki kwalbar turaren humra ta buga mashi a goshi da karfin gaske, nan take wajen ta fashe, jini jajawur ya fara wanke mashi fuska, da haka ta gayawa Dr Salman ai shi ya shigo zai yi mata fyaɗe, a garin kare kanta ne ta buga mashi kwalbar turare, da yake ta mallake su Abba, sai suka amsa da haka ne da Dr Salman ya tambayesu, Abba har da cewa ai ranar ma ya ga daddyn Rimsha ɗin yana wasa da gabansa a cikin ɗakinta, ita kuma bata nan lokacin, shi kuma Abbi cewa ya yi ai ranar ma ya gan shi yana ta wasa da breziyarta yana kissing na bra ɗin........ Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun 😭 Allah ka tsinewa asiri albarka.

# Ai kuwa ran Dr Salman in ya yi dubu to a ranar ya yi mugun ɓaci, a nan ne kuma ya furta kalamai masu zafi a kan ɗan nasa, nan take ya ce ya yafe shi wa duniya, kuma sai an kai shi prison, sai ya yi zaman yari na shekaru goma, da yake su dokar turawa suka sani, ba na Nigeria ba, wani irin Mahaukaciyar razana da shiga tashin hankali Naura ta shiga, domin tasan dokan turawa ya fi namu a nan tsauri, su idan suka yanke hukunci fa, to sai an yi wannan shekarun, kuma ta ji har shekara goma ɗan nata zai yi a prison cewar babansa, bata san Nigeria kam ɗan ma zai iya gudu daga prison ɗin ba. In takaice maku labari, a wannan ranar dai Allah ne ya kaddara Naura kwananta na gaba, da sai dai a kwashi gawarta, saboda tsantsar bala'in tashin hankali da ta shiga, su Abba kuwa tsab suka bi bayan babansu da Amarya suka share Mummynsu, da alama ma sun mance ita ta haifesu, sai zaginta suke yi ita da daddyn Rimsha, yana jin suna zagin mumnynsa, shi sharrin da akayi mashi bai wani damesa sosai ba kamar yadda Abba da Abbi ke zagin mummynsu.

Suna ganin Naura na kuka, amma ko a jikinsu saboda basu a hayyacinsu, tashin hankali da damuwar kada a rufe mata yaro ne yasa ta ɗebo kuɗi masu yawa wadda ita ma bata san adadinsu ba, ta zuba kuɗin a cikin jaka, a lokacin Dr Salman ya kira ƴan'sanda, basu kai ga isowa ba, sai dukan daddyn Rimsha yake yi kamar zai kashe shi, da kyar Naura ta iya kwatarsa, ita kuma Amarya tana ɗaki abinta, yau ranta fes, Hassan kamar zai yi hauka, shi ne kuma ya taya mummyn nasu karɓar Hossain nasa, su Abba suna tsaye suna kallon me yake faru, ko a jikinsu.

Da kyar ta ja Daddyn Rimsha zuwa ɗakinta, ga ƙaton ciki wadda da alama ma ta fara naƙuda, tana kuka kamar ranta zai fita, haka shi ma Hassan, tamkar ransa zai fita yake kuka, shi kuma daddyn Rimsha ba'a magana, duk Dr Salman ya fashe mashi baki, ga gaskiya suna gani amma suka take. Ɗakin Amarya Dr Salman ya koma ya kwanta yana jiran dirowar ƴan'sanda dan su tafi da Hossain.

Suma su Abba kowa ya wuce ɗakinsa, lallaɓawa Naura ta yi tana naƙuda ta ɗauko jakar kuɗin nan ta bawa daddyn Rimsha ta ce ya gudu ya tafi, da yake shima a zuciye yake a lokacin, ya tsani kowa, sai ya karɓi kuɗin ya gudu, mai gadi ya so tare mashi hanya, ai kuwa ya sakarwa mai gadin kunamunsu na twins ya gudu ya fita daga gidan, bai san ko'ina ba, bai san kowa ba, dan ma dai Allah yasa yana da wayo sosai ga kuma ilimi, sai kuka Hassan yake yi yana cewa shi zai bi ɗan uwansa, amma Naura ta riƙe shi gam, da yake dama sun san yana kuka, sai basu kawo cewa Hossain ya fita ne yasa yake kara wannan mahaukacin ihun ba, sai suka bari a kan dukan da babansu ya yi wa Hossain ɗin ne yasa Hassan ke wannan ihu haka. A TAKAICE DAI WANNAN SHI NE SANDIYAR RABUWAR HASSAN DA HOSSAIN, WANNAN SHI NE ABIN DA YA FARU, SAURA LABARI KUMA ZAI ZO MAKU DAGA BAKIN ABBAN IMRAN, WANNAN MAGANA BA ZA SU MAIMAI TA SHI BANE YASA NA GAYA MAKU ABIN DA YA FARU, SHI KUMA DADDYN RIMSHA BAYAN FITAR SA GIDA INA YA JE? ZAI GAYA MAKU DA BAKINSA, INA NAURA TAKE? ME TA HAIFA A RANAR? YA AKAYI DADDYN JELLY YA YI RAYUWA DA DADDYN RIMSHA DA HAR YAKE IKIRARIN SUN FI KUSANCI DA HOSSAIN ƊIN? INA AMARYA? YA MAKOMARSU ABBA A WANNAN LOKACI? YA AKAYI WANNAN ASIRI DA AMARYA TA YI MASU ABBA YA WARWARE DA HAR A YANZU SUKA SAN KUMA SUKA GANE SUN YI WA DADDYN RIMSHA LAIFI? YA AKAYI DAGA BAYA SU ABBI SUKA RABU HAKA? SAURA LABARI YANA GABA, NA SAN A IYA WANNAN MA KAWAI KUN FAHIMCI IN DA ZANCEN YA DOSA, MU DAI JE ZUWA ZAMU HAƊU A GABA DAN WARWARE KOMAI A TARE.

STORY💋

💋GIDAN LION💋

Ajiye wayar Imran ya yi tare da kwanciya a saman gadonsa, tunani cike fal ransa, tabbas yana son sanin menene gaskiyar abin da ya raba iyayensu, meyasa daddyn Rimsha baya son haɗa inuwa ɗaya da su? Amma kuma meyasa yake taimaka masu sosai idan suka shiga damuwa? Imran bai san abin da suka yi mashi bane ta tsaya mashi a zuciya da yasa baya son haɗa inuwa da su, jini ba wasa ba, tabbas yana kaunarsu shiyasa ma yake taimaka masu kuma yake bibiyar lamuransu, amma kuma duk lokacin daya gansu, ba abin da yake tunawa fa ce irin sharrin da suka murje idanunsu a gaban kowa suka yi mashi, wai yana neman matar babansa, waiya zubillah, ya kasa mancewa da wannan abin, yana da Bala'in zuciya sosai.

A ɓangaren Rimsha kuwa, bata sami barci ba har wuraren karfe 1, tun da Imran ya dawo da ita ɗaki take kuka, kuma ta rasa dalilin kukan nata, ta rasa me yake yi mata daɗi, da kyar barci ya yi awon gaba da ita.

Washegari da misalin karfe 8 wanka ta yi, ta shirya tsab cikin wando da riga kamar dai kullum, sai dai yau, Pakistan ta sanya, rigar ma ta ɗan ɗara gwiwarta, wandon kuma yana da ɗan faɗi, sai mayafin mai ɗan girma, dukkansu launin sky blue ne, ba two colors bane.

Bayan ta gama shirin ta fes, sanya perfume nata ta yi, tare da ɗaukar wayarta ta nufi Palo, idanunta har yanzu suna kunbure, saboda ba karya ta sha kuka daren jiya.

Ko da ta fito Palo, babu kowa, dan haka sai ta wuce kawai ta nufi garden ɗin gidan. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga, Imran ne kawai yake zaune a wajen.

Kayatatcen murmushi ta saki mashi kafin ta ɗaga mashi gaisuwa, da fara ya amsa gaisuwar tata, kusa da shi ta je ta zauna, hira suka fara yi a tsakaninsu, cikin mutunta juna da girmamawa, sai murmushi suke sakarwa junansu gwanin burgewa.

Suna tsaka da hira suka ji diran motoncin a cikin gidan, nan take gabaɗaya gidan ya kauraye da jiniya tamkar yaki za'a tafi, jibga jibgan motoci masu numfashi kwara biyar ne cif, kuma dukka motocin sojiji ne masu rai, sabbi gal gal, haka zalika jibga jibgan fararen turawan sojoji ne a saman bayan waɗan nan motocin.

A razane ta miƙe tsaye tana ganin yadda waƴan nan jibga jibgan sojojin ke dirowa kasa daga saman bayan motoncinsu, dukkansu fuskar nan tasu babu alamar annuri, ga su da tsawo da kuma murɗaɗun jiki tamkar wasu warriors, su goma sha biyu ne cif cif kamar yadda ya faɗa, mamaki ne ya kamata dama da gaske yake yi da ya ce zai karo wa su sojoji goma sha biyu, innalillahi wa inna ilaihir rajiun wannan wace iriyar zuciya ce ke gare shi,? Muguntarsa ta wuce gaban misali.

Dafata Imran ya yi yana faɗin "Na san abin da kike tunani, bai wuce cewa da gaske ne daman Saif yake yi na karo wasu sojojin ba, to ki sani ni tun ranar da ya yi maganar na san cewa yes confirm sai ya kawo su kamar yadda ya faɗa domin duk abin da kika ji ya faɗa to wlh sai kin yi shi, ko mutuwa zaki yi sai kin yi shi, in ya so daga baya ki mutu, tun da ya ce sai kin yi wa waƴan nan kafuran aiki to fa ba makawa kuma babu mai canza hakan sai shi idan ya yi ra'ayi, ya sauƙo daga dokin zuciya da ya hau, ni yanzu damuwa ta ɗaya, tayaya zaki kasance a cikin waƴan nan kafurai masu fuskar shanun? Ba su da imani da tausayi, abin haushin ma, shi ne shiga ɗakinsu da zaki rinƙa yi, kafurai ne ba musulmai ba, bare na ce za su bi dokar Allah, gaskiya daddy bai kyauta ba maganar da ya gayawa Saif, ga shi yanzu ya ja maki bala'in da in danginmu dukka za su haɗu babu mai fiddaki, amma In Sha Allah komai zai wuce nan da ƴan kwanaki kaɗan, ina da tabbacin zai sauƙo, zuciyar zata yi sanyi".

Rushewa tayi da kuka tare da zube gwiwowinta a kasa ta toshe baki da hannayenta dukka biyu, ƙwaƙwalwarta yana tariyo mata irin muguntar da ya rinƙa yi mata, hannu yasa ya ɗagota yana mai rarrashinta.

A wannan halin Areef ya shigo garden ɗin ya same su, da fara'a ya shigo, amma ganinta a wannan hali yasa ya ɗaure fuska sosai. "Prof me ka yi mata take kuka?". "Me kuma zan yi mata Areef? Kawai dai taga sojojin nan da Lion ya ce zai kawo ne, to ta ga ya cika maganarsa ne, shi ne take kuka.

Murmushi kaɗan ya saki, cikin sigar rarrashi ya fara magana "Our princess ina raye ba zan taɓa barin hakan ta faru ba, ɗan uwana ne fa, na san ta yadda zan bi da shi, kada ki wani damu, In Sha Allah wannan aikin gabaɗaya kin kusa dainawa, daga yau zuwa gobe, zan san ta yadda zan dakatar da shi, ba dai na sami lafiya ba, kawai ki zuba ido ko sha kallo, yanzu dai share hawayenki gimbiyar TRIPLETS". Ba karamin daɗi ta ji ba, cikin sauri ta goge hawayenta tare da fara zuba mashi godiya.

Girgiza kai ya yi tare da sanya hannunsa ya ɗan rungumota a gefen jirjinsa, wani iri ta ji a jikinta, shi kuma ko a jikinsa bai damu ba, bai ji komai ba.

"Ku zauna mana, Prof ina da magana da kai". Ya faɗa tare da saketa ya zauna saman sofa, kusan a tare ita da Imran suka koma suka zauna.

"Prof what is goruba?". Ɗan zaro idanu waje Imran ya yi, tunani ya fara yi, wai a ina Areef kuma ya jiyo sunan goriba? Me kuma zai yi da ita? Dan dai tabbas shi dai ba iya cin gorobar zai yi ba, bai ma santa ba, amma ya zo yana tambaya.

"Prof i said what is goroba?". "Areef what are you going to do with the goruba?". Kai tsaye cikin wasa ya ce "My future wife mana zan kaiwa, wai kai Prof ina ruwanka ne? Just kawai tell me what is it, kai ni nama fasa son sani menene, just kawai a kawo mani goroba from now to tomorrow"........ To fa goruba kuma🤔

"To Shikenan za'a kawo maka, ba dai goroba ba? Ai gidanta kazo, Allah yasa ka iya ci". Imran bai yarda a kan wata zai kaiwa ba, domin shi dai yasan TRIPLETS ba ɗaya daga cikinsu da yake da girlfriend, kai idan ma ba Rimsha ba, ba su da wata mace da suke yi wa magana, hakan yasa bai yarda da zancen ya ce wata zai kaiwa ba, ya mayar mawai kila yana son ya gwada ci ne, tun da wani lokaci tana cewa zai ci abincin hausawa, to amma a ina yaga goriba? A ina yaji sunanta da har zai gwada ci ɗin? Shi da ko saninta bai yi ba? Akwai wata a kasa.

Areef zai yi magana Imran ya rigashi da cewa "Rimsha Saif na buƙatar abinci, ki je ki kai mashi, dan Allah Rimsha ki kula kin ji ko?" Gyaɗa mashi kai ta yi tare da amsawa da to, daga haka ta miƙe ta bar wajen, su kuma cigaba da hira suka yi.

Kamar kullun Mark ya kammala haɗa mata abincin, hannunta ta wanke kafin ta ɗauka ta wuce izuwa bedroom nasa.

Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga, yana balcony, ya miƙe a saman ɗaya daga cikin tsadaddun kujerun dake a wajen, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, sai wani Lumshe idanu yake yi kamar mai jin barci, pajama ne a jikinsa, launin army colar, ya saki wannan kyakkyawar dark black curly hairn nan nasa, sai wani kyalli gashin take yi, kwana biyu da suka ɗan yi a Nigeria har ya ɗan yi duhu saboda zafi, fatarsa ta rage haske, sai dai kuma ta kara kyau da kwanciya luf luf kamar matar jariri, ya kara fresh sosai.

Readers Also Read