Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 14

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 14

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 14: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 14. A in da ta saba ajiye mashi abincin, a nan ta…

3,336 words

A in da ta saba ajiye mashi abincin, a nan ta ajiye, ita ma zaman ta yi tana jiran shi, shiru shiru ba shi babu labarinsa, sai ƴan waige waige take yi kamar mai neman wani abin, ji take yi tamkar ta tashi ta ɗan yi mashi taɓe taɓe tun da baya nan, amma sai ta tuna da abin da Imran ya gaya mata kafin ta zo, tuna hakan yasa ta daure ta cigaba da zama jiran shi kawai.

Sai da ta kwashi minti 30 a wajen a zaune kafin ya miƙe ya taho, wa iya zubillah, kallo ɗaya ta yi mashi, ta yi saurin kawar da kai, dan kada ya kamata, da yake yana nufota ne, amma ta kasa manta kyawun da ta kallah.

A in da ya saba zama ya zo ya zauna, abinci ta zuba ta tura Mashi, ba ɓata lokaci ya ɗauka tare da fara ci, sai satar kallon shi take yi.

Ɗan dai'dai ya ci abincin, ya ajiye spoon ɗin tare da yi mata alama da hannu akan ta zuba mashi ruwa, cikin sauri ta zuba ta mika mashi, ba ɓata lokaci ya karɓa ya sha, bayan ya ciro cup ɗin kuma, ya ajiye mata tare da miƙewa ya fice daga ɗakin, cikin sauri ta kwash kayan abincin ita ma ta fita.

Kitchen ta mayar da kayan abincin kafin ta dawo in da su Imran suke zaune, zama ta yi suka cigaba da hira.

Misalin karfe 10 daidai Imran ya je ya ɗauko AKILA, tun jiya dama Rimsha ta kirata a waya ta gaya mata cewa ta zo mata da kayan tea ɗin, yaya Imran ya ce zata zo su wuni, sai dai a gidan Akil ya je ya ɗaukota, yaki zuwa gida da kansa, domin ya ji labarin kiran da Ammie take mashi ta bakin Akil ɗin, to yaki zuwa, ya fi so sai ya haɗu da Abba sun tattauna kafin ya timkareta, sai Abbansa ya yanke hukuncin me zai ce mata kafin su haɗu kenan, shiyasa ya kira Akil akan ya ɗauko mashi Akilar daga gidan, ya ce wa Ammie za su je wani gari ne haka, domin yana so Akilar ta yi kwana biyu haka a gidan, ta ɗan ɗebewa Rimsha kewa, ai kuwa Akil da ya je, sai ya ce wa Ammie Abuja za su je, ita kuma in dai Akil ko Imran ne za su ɗauki Akilar, to bata damuwa, koma wata ne suje su yi, dan tasan suwa ye ta haifi........... OH WASA WASA AKIL DA IMRAN SUN ZAMA MAKARYATA SABODA SOYAYYA.🤔 SU DA BASU SAN MENENE KARYA BA, BASU YI, SUNA MA TSAWATARWA MASU YI, AMMA YANZU SABODA KAUNAR FAMILY'N ABBANSU SUN FARA KARYA SOSAI....🤔

Da Akil ya je gida ɗaukar Akila, Ammie ta tambaye shi ina Imran, sai ya ce mata ai baya kasar ne ma baki ɗaya, amma ya kusa dawowa, haushi kamar ta yi yaya, haka ta hakura ba dan ta so ba, ta yi kwafa tana jiran dawowar shi, dan dole ya saki jelly, bata san shi ma Akil ɗin yana tare da matarsa ba, in dare ya yi, sai ya dawo gida ya shiga ɗaki kamar mai barci, idan dare ta tsala kowa ya yi barci, sai ya fita ya gudu gidansa wajen Umaisharsa abinsa. (Ƴaƴan Ammie akwai ƴan air wlh🤣)

Yau murna a wajen Rimsha ba'a magana, ta rungumi Akila sosai kamar wani ya ce zai rabasu, ita tasan Akila ƴar uwarta ce ta jini, ita kuma Akila bata san hakan ba, kuma ga shi daddynta ya ce kada Imran ya faɗa, hakan tasa bai faɗa ba ya yi shiru, ita ma bata gayawa Akilar ba.

Ɗaki suka kule, sai zuba hira suke yi, a in da Akila take bata labarin masoyinta ya ce zai zo ranar Wednesday, tana cikin murna mara misaltuwa, sai murna Rimsha take taya ta, tun da Akila ta zo bata haɗu da Areef ba, haka ma Lion basu haɗu ba, hasalima daga Lion ɗin har Areef ɗin ba su san ma tazo ba, gara Lion ma Imran ya gaya mashi zai je ya ɗauko sister sa wa Rimsha, sai da ya bashi izini tukun nan ya ɗaukota.

Tun da tazo sun kasa motsawa ko nan da chan, sun baje a saman gado har sai da aka yi sallar azahar, a sannan ne suka yi wanka tare da sallah, yau Rimsha baki ya ki rufuwa, kuma ga shi yau gidan nasu a cike tab da bakin sojoji, idan ba ka kai zuciya nesa ba, to ba zaka iya zama a cikin waƴan nan jibga jibgan ba, wlh kallonsu ma kawai ya isa ya rinƙa razanaka har rai ya yi halinsa, gasu kamar wasu gumaka, basu magana ko kaɗan.

Shiryawa suka yi dukkansu cikin riga da wando, da yake Akila ta fi Rimsha cika sai kayan sam basu dace ta fita da su a haka ba, gara Rimsha, duk da ita ɗin ma bai dace ba cikin zaratan mazan nan ba, musamman yanzu da aka karo wasu, ita zuciya bata da kashi, da Allah yasa mazan ma dukka turawa ne, irin wannan shiga ba bako bane a wajensu, shi ne ma dama shigar matan kasarau, to amma ai yanayin jiki da halittar diri daban daban.

Palo suka fito, babu kowa a palon sama, dan haka sai suka nufi kasa, dukkansu suna sanye da ƙaramin hijabi please call me, sai murna suke yi, baki ma ba zai iya faɗen farincikin da bayin Allahn nan suke a ciki ba.

A palon kasa suka zauna suna hira, Mark na kitchen yana ta faman aikinsa, sai kallonsa Akila take yi, taga farin Bature tas babu mix.

A ɓangaren Gidan Abbo kuwa........

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

E11-12

A ɓangaren Gidan Abbo kuwa.

Bayan kwana biyu. A cikin wannan kwana biyun sun yi muguwar sabo a tsakaninsu, Aafia ta saki jiki sosai da shi, ya mantar da ita abin da yake damunta a ranta, har wa yau kuma Abbo dai shiru, ba shi ba labarinsa, kuma su dukka ba wanda ya sake tunawa da zancensa, abin kamar almara, ya rufe masu babinsa a bakunansu da kuma zuƙatansu.

Soyayya mai tsabta suke gudanarwa a tsakaninsu, sai dai fa tun daga wannan sumbata ɗaya da ta yi Mashi, ba wani abin da ya sake haɗa su, sai dai ya zauna ya yi ta zuba mata hira yana sanyata nishaɗi, Ummi na matikar kula da Aafia tamkar ita ta haifeta, ko ban faɗa ba kunsani, ta fi Hjy Hadiza sau dubu, dan ita dai Hjy Hadiza bata kula da ƴaƴan ba, kenan abin da nake nufi a nan shi ne, Ummi tana kula da Aafia fiye da uwar da ta haifeta.

Ba laifi Aafia na ƙoƙarin shiga kitchen ta taya Ummi aiki, suna yi suna hira, wani lokaci Nawid yana shigowa ya taya su, Ummi ta yi ta tsokanar shi wai yanzu kam ya san hanyar kitchen kenan, da sai dai ya zauna yana isar mutane da Ummi kaza zaki dafa mana yau, yanzu kuma har da shiga kitchen dan ya yi mata, kamar wani jikarta haka Ummi ke tsokanar shi, sai dai ya yi ta Murmushi dan bai san me zai gayawa Ummi ɗin ba.

Rayuwarsu abin burgewa da ban sha'awa, sun mai da Ummi kakansu, idan suna wani wasan ba zaka so su dai'na ba, saboda burgewa da ban sha'awa.

Kwance take a saman gado da misalin karfe huɗu na yamma, Nawid baya nan, ita kaɗai ce, Ummi na ɗakinta, gabaɗaya ko'ina a gyare tsab, sai kamshi yake tashi.

Sanye take da doguwar riga mai shegiyar kyau, launin pink color, duk kuma kayan jelly ce, Ummi ta ce sai sun huta, su shirya zuwa sayan mata kayan lefenta, shiyasa take amfani da na jelly tun da suna yi mata daidai.

Tayi simple make up a face nata, sai tashi wani irin fitinannen kamshi take yi, ta ɗaga kai sama da alama wani abin take tunani, karar ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa.

A nutse ta miƙa hannu saman bedside drawer ta ɗauko wayar. Umaisha itace mai kirar tata, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ɗauki kiran. "Hello Umaisha". Ta faɗa tana miƙewa zaune a tsakiyar gadon.

"Aunty Afi ina ta jiranki tun shekaran jiya baki kirani ba, Allah ma yasa bamu samu damar zuwa gida ba, amma kuma naji yaya Akil ya ce yau zamu je, shi ne na kiraki in ji hukuncin da kika yanke, in ɗaukawa Ommu kuɗin ne ko yaya? Wlh ina jin tsoro sosai". Tana magana tamkar zata yi kuka.

"Umaisha shi ne ko sallama babu bare gaisuwa? Ki natsu mana". Kamar zata saka ihu ta ce "Kiyi hakuri Aunty Afi, ina cikin matsananciyar damuwa ce, shiyasa ma na manta da wata gaisuwa, to ina wuni yasu yaya Nawid?".

"Lafiya lou ya yaya AKil?" "Yana nan lafiya". Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Kina ji Umaisha? Magana ta gaskiya dama ina son in kiraki, kasan cewar kwana biyun nan Yaya Nawid yana nan bai fita bane yasa ban kiraki ba, dama ina Allah Allah kada ki ɗauki kuɗin, to Alhadulillah da Allah yasa ma baku je gidan ba, yanzu dai abin da nake so da ke shi ne, idan kunje gida ki gayawa Ommu yaya Akil bashi da kuɗi, bai ajiye a gida ba, amma duk ranar da ya kawo kuɗin gida, zaki ɗebo mata ko nawa take so, kinga idan kika gaya mata haka ba zata ce kinki ɗauko mata bane, ba zata ɓata rai ko ta yi fushi dake ba, kinga bata isa ta ce a ciro mata a account nashi ba, dole ta hakura ta jira sai ranar da ya kawo kuɗin gida, kafin lokacin kuma zamu nemo wata shawara, amma ba Ommu ba kome zai faru kada ki kuskura ki saci kuɗin mijinki, kai bana mijinki kawai ba, na kowa da kowa ma, kada ki yarda ki ɗauki abin da ba naki ba, duk wanda ya roƙe ki abu, idan ya fi karfin aljihunki, sai ki bashi hakuri babu wani zancen ɓoye ɓoye, kuma duk wani abu idan ya taso kada ki kuskura ki yi gaban kanki, ki gaya mani ko ki gayawa yaya Irfan, idan ba zaki iya gayawa Abbi da yaya Akil ba, kina ji na ko?".

Dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali. "Aunty Afi na ji daɗi sosai, kuma ina godiya ga Allah daya bani ƴan uwa masu ƙaunata, nagode da shawararki a gareni, zanyi amfani da ita In Sha Allah".

"To shikenan mummyn Abbi in ji yaya Akil na ba, zan ji daɗi fa sosai idan yaya Akil ya cika alkawarinsa ya yi wa Abbi takwara". Dariya sosai Umaisha ta yi, tana matikar kaunar cikin nan nata, ko in ce suna matikar kaunar kayansu ita da mijin nata.

Da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin ɗakin, ganin shi yasa ta ce da Umaisha za su yi waya anjima, da haka suka yi sallama.

Ɗaura wayar saman bedside drawer ta yi tare da miƙewa da sauri ta nufe shi tana murmushi, sai wani lumshe idanu yake yi alamar a gajiye ya dawo, sanye yake da kayan aikinsa, daga ta ciki kuma suit baki ne kafin ya ɗaura rigar tasu ta likitocin, hannunsa na riƙe da bakar jaka mai shegen kyau, while kafarsa na sanye da cover baƙa, daga ciki kuma bakar safa ce a ciki, ya fito a cikakken likitansa.

Karisawa wajensa ta yi tana kara faɗaɗa murmushinta, shi ma murmushi yake sakar mata tare da buɗe mata hannu akan ta yi mashi oyoyo, kin yi mashi tayi, tana zuwa ta karɓi jakar hannunsa, zata juya ya yi maza ya riƙota.

"Ina zaki je ba tare da kin yi mani oyoyo da kuma sumbata na welcome back ba?". Kasa ta yi da kanta bata ce mashi komai ba.

"Haba matata, na fa gaji sosai, kuma nasha wahala, amma shi ne zaki zo ki karɓi jaka kawai, ba wani ɗan sumbata? Baki san cewa idan kika sumbace ni zan ji gajiyar ta gudu mani ba? please mana". Ya kai karshen maganar a ɗan shagwaɓe.

Bata san lokacin da ta juyo ta rungume shi ba, ya iya magana sosai, ta haka kuma yake bi da ita, har ya sanya ta ta yi abinda bata yi niya ba, ta haka yake kore mata duk wata damuwarta, ya mantar da ita komai.

Sosai ya sanya hannu biyu ya riƙota da kyau, tare da kara matseta a jikinsa yana mai jin tsantsar farinciki yau ta rungume shi.

Sun ɗan jima kaɗan a haka, kafin nan ya sanya hannu ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna, idanunta a lumshe.

"Kinyi kyau over my mata". Ya faɗa kasa kasa. Duk da idanunta a rufe, sai da ta saki haɗaɗɗen Murmushi, da yawan mata suna son ace sun yi kyau, shi kuma ya kware wajen iya yabon mace, shiyasa ma ta yi saurin kware mashi haka.

"Saura sumbata, ko dai yau za'a bani har da kiss ne?". Ya yi maganar cikin sigar zolaya.

"Ni fa yaya Nawid ban iya ba". Ita ma cikin sigar zolaya ta yi maganar. "In koya maki ne? Kin bani dama?". Kai ta gyaɗa mashi alamar e.

Wani irin daɗi ya ji sosai tare da sakin haɓar tata ya saketa yana faɗin "Bari na yi wanka to, ko dai zaki tayani yi ne?". Da sauri ta juya ta bar wajen tana faɗin "A'a zan dai fitar maka da kayan sakawa, daga nan kuma na ɗauko maka abincinka". Murmushi ya yi tare da karisawa ciki ya fara rage kayan jikinsa.

Ita kuma bayan ta ajiye jakar a mazauninsa, sai ta wuce ta fice daga ɗakin ta nufi Palo, binta da kallo ya yi yana mai jin kaunarta na ninkuwa a ransa.

Abinci ta ɗauko mashi, da yake yanzu a ɗaki take kawo mashi abinci su ci a tare, Ummi ce ta ce su rinka ci a ɗaki, dan ta lura da shi Nawid yana son suna cin abinci suna wasa da dariya tsakaninsu na masoya, ita kuma Aafia tana jin kunyar yin hakan a gaban Ummin, da yake Ummi mace ce mai adalci, ga lura, sai ta gane hakan, dan haka sai ta ce A'AFIA ta rinƙa kai masu abincin cikin ɗakinsu suci a tare.

Lokacin da ta ɗauko abincin ta dawo ɗakin, har ya cire kayansa ya shiga toilet, saman Chinese carpet dake tsakiyar ɗakin ta ajiye masu abincin tare da miƙewa ta nufi drawer kayansa dan fitar mashi da kayan sakawa.

Kananan kaya na shan iska ta fitar mashi, a saman bed nasu ta ɗaura kayan, ita ma ta kwanta a gefen kayan tana jiran fitowarsa.

After some minutes ya fito ɗaure da towel a kugunsa, tsayuwa ya yi a wajen drawer kayansa tare da zuba mata ido, ita kuwa tana jin fitowar shi, amma taki ɗagowa ta kalle shi.

"Mrs Nawid yanzu dai ba za'a taya ni sanya kaya ba?". Gyaɗa mashi kai ta yi tana daga kwance, har lokacin kuma taki ɗago kai.

Bai sake magana ba ya kariso wajen gadon, kayansa da ta ajiye mashi ya ɗauka yana mai bin kayan da kallo, har cikin ransa ya ji daɗin kayan da ta fitar mashi, hakan ya nuna lallai tana da kula sosai, a ɗan zamansu kwana biyun nan, har ta fahimci irin kayan da yake son sanyawa idan yana gida, abin ya sanya ya kara jin sonta a ransa.

Toilet ya koma dan baya son yin duk wani abin da bata so, yasan ba zata ji daɗi ya sanya kaya a cikin ɗakin tana ciki ba, tun da ba sabawa sosai suka yi ba, hakan yasa ya wuce toilet abinsa, kuma shima a yanzu dai ba zai iya sanya kaya a gabanta ba.

A yadda ya barta a haka ya sake fitowa shirye ya sameta, gaban mirror ya tsaya domin ya shafa mayukansa.

"Mrs Nawid ki zo ki taya ni shafa mai, idan ba haka ba, Allah zan yi maki alluran barci, dan tun da ba tayani aiki zaki nayi ba, gara kawai idan na dawo na rinƙa yi maki alluran barci sai nayi aikina ni kaɗai, kuma bayan haka zan ɓata dake tun da kina da son kai, ni in tayaki aiki, ke kuma baki son tayani ko?". Cikin zolaya ya yi maganar yana mai taje gemunsa.

Miƙewa ta yi tare da zuro kafafunta kasan gadon, kafin nan ta miƙe gabaɗaya, gabansa ta isa ta tsaya tana mai ɗauko Lotion da yake amfani da shi.

Da mamaki yake kallonta, bai yi zaton zata shafa mashi ɗin ba, ya zolayeta ne kawai, ashe dai zata yi mashi ɗin, a lallai yau rana ce ta Sa'a a gare shi.

"Zan iya rungume matata?" Ya faɗa kasa kasa, shiru ta yi Mashi, mamaki ma yake bata, wai komai zai yi mata sai ya tambayeta sai ka ce ita ta aure shi ba shi ya aureta ba.

Ɗan shafa gefen fuskarta ya yi yana mai kara faɗaɗa murmushin kan fuskarsa, ita ma sai murmushi take yi ta wani yi kasa da kai tana murza mai a hannunta.

Jawota jikin nasa ya yi, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ɗago haɓarta suna fuskantar juna. "Dama kin ce na koya maki kiss da sumbata ko?". Shiru ta yi mashi tana runtse idanunta. "To buɗe idanu mu kalli juna sai na koya maki daki daki ta yadda zaki fi iya ɗauka da kyau".

Ƙin buɗe idanun nata ta yi, har lokacin kuma tana Murmushi. A hankali ya rankwafo da kansa tare da haɗe fuskokinsu waje guda, jin tana iya shakar numfashinsa ne yasa ta razana sosai, nan take abin da ya faru a baya ya dawo mata sabo, a kiɗime ta fara ƙoƙarin kwace kanta daga gare shi, kara kankameta ya yi, dan shi bai kawo komai a ransa ba, ya yi zaton bata saba bane yasa take son guduwa.

Ba tare da ya yi magana ba ya ɗaura bakinsa a saman tata, a nutse ya fara kissing nata, tun tana mutsu mutsu tana neman kwace kanta, har ta hakura ta natsu tsit a jikin nasa, shi kuwa lafiyayyar kiss yake bata tare da kara matseta a jikinsa, sai faman sauƙe numfashi da sauri sauri yake yi, hankali ya kwanta, abin nema ya samu.

Sun ɗan jima a haka, ta natsu shiru, duk wasu ƙofofi da gaɓɓai na jikinta suna karɓar wannan daddaɗar saƙon da yake aika masu da shi, tuni ya sanya ta fara fita a hanyacinta. Can ta yi nisa bata jin shi sosai, kamar daga sama ta ji sauƙar hannunsa a kirjinta, wani irin bugu kirjinta ya bada, ƙoƙarin kwace kanta ta fara yi.

Can kasa kasa ta jiyo muryarsa bayan ya zame bakinsa daga nata. "Please kada ki hanani taɓawa, na yi maki alkawari ba zan kai hannuna ciki ba, a iya rigar kawai zan shafasu, bana son ɓacin ranki, idan har baki son na taɓa to na hakura". Allah sarki shi kuma yana ƙoƙarin saka ta farinciki ne dan yana tunanin tana cikin kunci anyi mata auren dole, auren da bata shirya ba, bata san shi ba rana ɗaya kawai aka haɗa auren, ranar da ta fara ganin shi, a ranar ta zama mallakinsa, hakan yasa yake binta a hankali dan ya koya mata son shi, a nasa tunanin fa kenan, abin da bai sani be shi ne, ta jima tana dakon soyayyarsa.

Jin abin da ya ce yasa tayi shiru ta natsu, dan kyautatawa iya kyautatawa yana yi mata, koda yaushe bashi da wata burin da ta wuce ya ganta tana murmushi tana farinciki, dole ita ma ta yi ƙoƙarin sanya shi farinciki.

Kamar yadda ya faɗa hakan ya yi, bai saɓa maganarsa ba, suna daga cikin rigar ya rinƙa matsasu yana wasa da su, ya kankameta sosai a jikinsa, Allah kaɗai yasan me yake ji, shekarunsa 28 to 29 a duniya yanzu.

Sun jima a haka kafin ya saketa ya juya ya nufi toilet ba tare da ya bari sun haɗa ido ba, da alama kunyarta yake ji. Ita kuma, da kyar ta koma saman gado ta kwanta tare da lumshe idanunta tamkar mai yin barci, ban da ajiyar zuciya babu wani abu da take sauƙewa.

After some minutes.

Readers Also Read