Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 23

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 23

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 23: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 23. "Rimsha ko dan farincikinki zan yi yadda kika…

3,360 words

"Rimsha ko dan farincikinki zan yi yadda kika bani shawara, amma kuma ba zan gaya miki yadda zan yi wa Heartbeat ba, dan saboda nasan yana jina, zai ji komai da muka faɗa, dan haka kawai na barwa zuciyata sanin hakan, sai dai ki sani ba zan guje shi ba, ba kuma zan canza mishi ba, abu ɗaya zan yi mishi wadda sai nayi zaki gani". Sosai Rimsha ta ji daɗi, ita kaunar da take yi wa Akilar ce ma tasa take yi mata kwaɗayin samun ɗaya daga cikin TRIPLETS, saboda tasan zata sami kula fiye da tunanin mai tunani, zata sami farinciki sosai da sosai.

Shiru suka ɗan yi na ƴan mintoci kafin Akila ta ɗauki wayarta tare da miƙewa ta shiga toilet, fuskarta ta wanko tare da fitowa ta kara tsantsara make up, zuba mata idanu Rimsha tayi tana ganin ikon Allah.

Bayan ta kammaya ta ɗauki hoto kala biyu a wayar tata, tayi kyau sosai da sosai, ta fito a sak jinin Dr Salman da kuma barrister Naurat, feshe jikinta da perfume nata masu daɗin Kamshi ta yi kafin ta ce da Rimshan ta tashi su koma garden.

Ba musu ta tashi, sai dai kuma bata gaji da binta da idanu ba, sai mamaki take yi, irin wannan sauyi lokaci guda haka.

A yadda suka bar su Imran, haka suka dawo suka same su, sallama suka yi musu, har suna haɗa baki wajen amsawa, zuba mata idanu Areef ya yi har sai da ta zauna a saman sofa, cike da zolaya ya ce "Sarkin rigima, Prof this your sister fa ba'a magana, rigimammiya ce number ɗaya, Aseef part 2". Yana magana yana wannan murmushin nasa mai kayatarwa tare da ɗaukar hankali.

Cool murmushi ta sakar mishi kafin ta ce "Saboda ni auta ce ai yasa dole nayi rigima ko ba haka ba yaya Imran?". Cikin harshen turanci suke magana ba Hausa ba.

Gyaɗa mata kai Imran ya yi yana faɗin "Yes Our Heartbeat ke auta ce dole ki yi shagwaɓa, mu kuma mu kara shagwaɓa ki". Shima dai Imran da turanci ya yi maganar, sai murmushi suke yi dukkansu, Akila ta nuna kwata kwata ita ma bata gane shi ba, tun da haka ya nuna mata.

"Heartbeat ki shirya gobe da safe Akil zai mai dake gida kin ji ko?". Cewar Imran. Da sauri Rimsha ta ɗago kamar zata yi kuka, rarrashinta Imran ya fara yi tare da yi mata alkawarin bayan kwana biyu zai sake ɗauko mata ita, zai kawota su yi wata guda, ba dan ta so ba ta hakura.

Haka suka ci-gaba da yin hirarsu mai cike da nishaɗi tare da bawa juna kulawa cikakka, kayatattun murmushi ne ɗauke a kan fuskar ko wannansu, hakan zai tabbatar maka ba ƙaramin jin daɗin hirar suke yi ba, abin ba'a magana, shi kuma oga yana bedroom nasa yana bincike a kan wani sojansu da a ka kashe, a jikinsa an sami wani tambari na kungiyar ƴan ta'adda, to yana bincike yaga gano gaskiya, shin sojansun ɗan leƙen asirin ƴan'ta'adda ne ko yaya abin yake, ita kuma jelly tana can har yanzu tana barci, kuka ta sha iya son ranta kafin barci ɓarawo ya yi awon gaba da ita, ta gama period jiya, amma taki yarda da yaya Imran, da yazo zai shigeta sai ta yi ta yi mishi kuka, haka zai hakura ya kyaleta ba dan ya so ba, ɗazun ma abin da ya haɗasu kenan, ta sha kuka har barci ya ɗauketa, ta kafe akan ba zai taɓa mata tula tulanta ba dan suna yi mata zafi, shi kuma bawan Allah zafi sun haɗu sun yi mishi yawa, ya kasa jurewa, ɗan wasan da yake yi ma ya sami sauƙi, yanzu ta hana shi yi, abun sun haɗe mishi, baya son ya yi mata ta karfi dan kada ya sanya mata tsoron abin, shiyasa yake binta a hankali yake hakura, duk da ya hakura ya kyaketa dan baya son yi mata dole, amma sai da ta tasa shi a gaba ta rinƙa kuka yana rarrashinta, shi ne har barci ya ɗauketa, to daga barcin ne bata tashi ba har yanzu.

TO KUN JI YADDA GIDAN LION YAKE, BARI MU LEƘA GIDAN ABBI DAN MUGA ME SUKE CIKI, ZUWA ANJIMA SAI MU DAWO, SHIN YA SU ABBI SUKA DAWO DAGA KATSINA❓ BARI DAI MU LEƘA MU GANI.

GIDAN ABBI 💋

A ranar da suka je Katsina a ranar suka dawo, sun yi sa'a sosai da yake baban Sadiq mayen san kuɗi ne, sai ya basu Hanan dan ya ga ruwan kuɗi, har mamaki daddyn Jelly ya rinƙa yi na yadda bai san su bai san suwaye su ba ya ɗauke ƴa sukutum ɗungurumgum ya miƙa musu, Maman Sadiq ta yi ƙoƙarin hana shi, amma ina shi ya ga ruwan kuɗi, ta yi ƙoƙarin gaya mishi kila ƴan mafiya ne, kila kuma sayar da Hanan ɗin zasu je su yi, nan ma ya rufe idanu ya murje gaskiya ya ɗauki Hanan ya miƙa musu, Abbi kam daɗi ya rinƙa ji abinsa, shi kuma daddyn Jelly nasiha sosai ya yi wa baban Sadiq ɗin tare da tunatar da shi Hanan fa tana da babban hakki a kansa, a ranar alkiyama sai Allah ya yi mishi tambayoyi akan ta, yanzu da ya ɗauketa ɗungurumgum ya basu bai san suwaye su ba idan ya mutu Allah ya tambaye shi ina amanar da ya bashi ya ƴarinya Hanan me zai ce? Kenan cewa Allah zai yi ya kyautar da ita ko ya'ya? Dama an bashi ita ne dan ya kyautar da ita? Ya sani fa ba iya iyaye bane kawai ke da hakki a kan ƴaƴa, suma ƴaƴa suna da hakki sosai a kan iyayensu, tun daga ranar da aka haife yaro har izuwa ranar da zai koma ga mahaliccinsu sai Ubangiji ya tambayeka ya ka kula da su, cinsu, shansu, tarbiyarsu, iliminsu, sutura da sauransu, abin ku da jahilci, sai ya ce e shi dai ya ji ba dai sun ce sunan son Hanan ɗin ba? To gata ya basu, idan kuma wani munafurci da iskanci zasu kawo mishi ne to su ajiye mishi yarinya su wuce su bashi waje.

Jin hakan yasa suka kyale shi, ya yi nisa ba zai ji kira ba, jahilci babu daɗi, haka suka ɗauke ta, Abbi ya bashi 200k suka kamo hanyarsu ta dawowa gida, sai washe baki yake yi ya sami kuɗi, yau ba'a magana, sai ruwan Albarka yake sanyawa Hanan ɗin ta kawo mishi mai bashi kuɗi, bai wani damu da rasuwar maman Hanan ɗin ba ma, shi dai buƙata ta biya tunda ga kuɗi, duk wannan abin da ya faru Sadiq da Yusuf basu nan, Yusuf yana shagonsa, kasuwancin nasa Allah ya saka mata albarka, sai haɓaka take yi, shi kuma Sadiq yana gareji, har kwallah sai da Maman Sadiq ta yi, ta rinƙa haɗa su Abbi da Allah akan kada su cutar da Hanan, Irfan ne ya rinƙa bata hakuri tare da yi mata alkawarin babu abin da zai faru sai alkhari In Sha Allah, da hakan suka baro Katsina suka nufi KD

Suna shiga gida kowa ya wuce Part nasa, daddyn Jelly ya wuce part nasa shi da Irfan, da suka shiga ciki kuma Irfan ya wuce bedroom nasa, dama kun san shi sarkin ƙulewa a cikin ɗaki ne, kullum yana ƙule yana kwance abinsa, baya son hayaniya, shi kuma daddy jelly toilet ya nufa dan ya yi wanka, Ayla bata nan, tana can cikin gida wajensu Aunty.

Aunty da ta ga sun da wo da Hanan, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, baiwa Allah, ta tsala wankanta suna zaune a palo ita da Ayla, danƙareriyar lace ce pink color, ɗinkin riga da skit ne a jikinta, kayan sun zauna mata da kyau sosai, ba ƙaramin kyau ta yi ba, ta sha make up iya make up abinta, sai tashin ni'imantaccen kamshi take yi, ga wani kyakkyawar ɗaurin ture kaga tsiya data ɗaura, ganinsa ya sa ta miƙe da sauri tana yi mishi sannu da dawowa, ita ma Ayla ta sha kwalliya ba kaɗan ba, sai wani kara sihirtaccen kyau take yi, ta yi fresh sosai, ga kamshin da take zubawa, sai dai ita doguwar riga ce a jikinta, yaunin maroon color, da yake akwai duwatsu masu kyalli a jikin rigar, sai ta kara mata wani shegen kyau sosai.

Sai murmushi suke yi dukkansu, cikin sauri ita ma Aylar ta miƙe tare da yi wa Abbi sannu da zuwa suka gaisa ta gaisa da Hanan kafin ta zame cikin dabara ta gudu wajen mijinta, tun ɗazun take kewarsa, ta damu sosai, bai taɓa yin nisa da ita na awa ɗaya ba, sai ga shi yau wajen awa 8 basu tare, ta damu sosai, shiyasa bata ji kunyar su Abbi ba ta zame ta gudu abinta, sai dariya Abbi da Aunty suke yi mata domin sunga fitarta.

Ɗan zungurin Aunty Abbi ya yi kasa kasa ya ce "Kinga yadda ake yi wa miji ko? Ya zamana kullum marmarin shin zaki rinƙa yi, babu jin kunyar kowa kina ji ko?" Dariya ta yi tare da rungume shi tana faɗin "To bana yi maka ne?" Jan hancinta ya yi "Kina yi mini mana, amma ki kara, wancan ya yi mini kaɗan".

Ganin haka yasa Hanan ta zame sumui sumui ta basu waje, ta haura sama zuwa ɗakin da yake mallakinta a yanzu, lokacin ita ma Jelly tana nan, tana ɗakin kwance tana barci, kada ku manta mun ɗan koma baya ne kaɗan a gidan Abbin, dan kuji me suka faru a kwanakin da suka wuce, ita kuma Hjy Batula ta je kaiwa Aafia ziyara dan ta dubo wani hali take ciki, kamar kullum Ommu tana ɗakinta.

"Halima wai yanaga sai kara haske kike yi ne?" Ya tambaya yana kare mata kallo, zata yi magana kenan suka jiyo Ommu daga ta bayansu saman bene tana surfa uwar masifa da murya kamar babanin akuya.

"Yanzu cin amanar taku har ta kai ranar kwanana ku tsaya a palo kuna iskancinku ta yadda ma zan gani kenan ko? Wato na zo na gani da kyau kunci amanata ko? To Allah ya isa kuma sai Allah ya saka mini, ke kuma Halima ki jira ki gani, bakar munafuka, ai kinsan yau a ɗakina yake, shegiya kullun kina wani sunnar da kai kamar ta Allah ashe Musa ne baki fir'auna a zuci ko? Bakar azzaluma algunguma kullum cikin faɗar Allah ya ce Annabi ya ce kike, amma baki amfani da abin da kike faɗa, yanzu idan da ke malamar Allah da Annabi ce ai da ko kallon shi kin san haramun ne a wajenki yau kam tun da a ɗakina yake, mayya kin bi kin cinye mini kurwar miji, ya tattare ya tare a wajenki, to wlh ta Allah ba taki ba, ki gama tsafinki da asirinki duk haka zaki ganni ni Deeje ki barni, na fi karfin yarinya sai dai Uwar yarinya, wlh idan......" Bata kai karshen maganar ganin zata tara musu jama'a yasa Abbi ya daka mata wata uwar tsawa mai firgitarwa.

"Hadiza kina shan giyar wake ne? Kanki ɗaya ne ko akwai motsi a ciki? Kin san me kike faɗa kuwa? Kin san me kike yi kuwa? To idan ma kanki ba ɗaya ba ni zan dawo miki da shi ɗaya yanzun nan, ki sani ba zan iya wannan halin naki ba, kuma Halima ba zan iya raba makwanci da ita har na rinƙa raba muku kwana ba, kin manta shekaru nawa kika sa kafa kika yi fatali da aurenki kika bar gidan nan ne? To a wancan lokacin baki san da hakkin nawa ba kenan ko?, A wancan lokaci baki san da raba kwana zai zo ba kenan sai yanzu ko?, Ko dama kina tunanin zan yi ta zaman jiranki ne?, Idan haka kike tunani to kin tabbata mai ƙwaƙwalwar kifi, kinje kin yi ta yawace yawacenki na tsawon shekaru kin dawo, ban ce miki komai ba, na ɗaga miki kafa saboda albarkacin ƴaƴan dake a tsakaninmu, yanzu kin dawo kina son sake ɗaga mini hankali ki takurawa matata farincikina ko? To ina son ki sani ba zan iya rabuwa daidai da kwana ɗaya da matata mai sona domin Allah ba, Halima ita ce farincikina dan haka ki je na sake ki saki ɗaya". Ya yi maganar cikin faɗa da zafin zuciya, ya kai karshen maganar tare da riƙo hannun Aunty suka nufi saman benen.

Ta gefenta suka raɓa suka wuce, mamaki ne ko tsoro waya san mata, ta dai kasa magana, sai binsu da idanu take yi, jin abin take yi tamkar a mafarki, ita yau Abbi ya saka, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, ta furta a cikin ranta tare da juyawa jiki a mace ta koma cikin bedroom nata zuciyarta cike taf da tunanin mafita.

Shi kuwa Abbi yana shiga bedroom nasa toilet nufa dan ya yi wannan, duk zafin rai da ɓacin ran da Ommu ta sanya mishi a Palo, yana shigowa cikin ɗakinsa ya ji sanyi a zuciyarsa, Aunty ta gyara mishi ko'ina, sai tashin wani fitinannen daddaɗar kamshin air freshener ɗakin yake yi, ga wani daddaɗar sanyin Ac dake gudu a tsaka tsakiya, daddaɗar sanyin Ac da ni'imantaccen kamshi idan suka haɗu ya kuke tunanin abin zai kasance? Ai abin sai wanda ya ji.

Nan take ya nemi ɓacin ran nasa ya rasa, wani muguwar soyayyar Aunty ce ta karu mishi a cikin zuciyarsa, sai albarka ya ke zuba mata a cikin zuciya, da haka ya shiga cikin toilet, ita kuma ta hau fitar mishi da kayan sakawa, Baiwar Allah har ciwo kanta ya fara yi mata saboda hayaniyar da Ommu ta yi yanzu, da Ommu ta fara bala'in, ta yi ƙoƙarin guduwa ta haye sama, Abbin ne ya riƙeta ya dakatar da ita, dan yana son ta rinƙa rage tsoron nan nata, ta cika shiru shiru da bala'in tsoro, shiyasa duk wanda ya ɗebo rashin mutumcinsa sai ya sauƙe a kanta, to yana da kyau ta koyi faɗa ko kaɗan ne, dan ta rinƙa kwatarwa da kanta ƴanci, shiga ɗaki tana kuka ba shi ne mafita ba, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce idan aka yi maka abu ka ji ba zaka iya hakuri ba, ka rama daidai da abin da aka yi maka, kada ka kuskura ka kara koda kwayar zarrace a kan abin da aka yi maka ɗin, daidai zaka rama, wannan shi ne ka'ida ta musulci, amma idan zaka iya yafewa, to yafiyar dai tafi, zaka sami Rahmar Ubangiji, Allah kasa mu a cikinta.

A ɓangaren Ayla kuwa, tana fita wajen mijinta ta nufa, lokacin yana wanka, kai tsaye wajen drawer kayansa ta nufa, kananan kaya ta fitar mishi da su, da yake ba wani iya aikin kirki ta yi ba, sai gyaran ɗakin nata bai yi kyau sosai ba, amma ta yi ƙoƙari, ta shinfiɗa musu gado ta yi shara iya yadda ta iya, kada ku mance irin rayuwar da ta taso a ciki, bata zauna a gida ba bare ta koyi wani aiki, iya abin da ta koya a gidan su Kausar sai kuma wadda Aunty ke ɗan koya mata a yanzu shi kaɗai ta iya.

A saman gado ta ɗaura mishi kayan, ita ma ta zauna a gefen kayan tana jiran fitowarsa,. Yana fitowa da kyakkyawar fuskarta ya fara tozali, cool murmushi ya sakar mata kafin ya buɗe mata hannayensa akan ta zo, da sauri ta miƙe ta nufe shi, rungumeta ya yi sosai suna sakin Murmushi a tare. "Nayi kewarki sosai my baby". Ya faɗa kasa kasa.

"Daddy nima nayi kewarka, har ciwo sai da kaina fa ya yi dan baka dawo da wuri ba". Ta yi maganar a shagwaɓe. "Subhanallah ciwo kuma?" Ya tambaya yana ɗago haɓarta, gyaɗa mishi kai ta yi alamar e. "Ayya Sorry ba zan sake tafiya wani waje mai nisa na barki ba, idan zan tafi to kafata kafarki, idan ba haka ba, na fasa zuwa". Murmushi ta sakar mishi tare da kara lafewa a jikinsa, tana jin daɗin wannan damshin ruwan jikin nasa dake taɓata, ya lura da hakan, cikin sauri ya sake ɗago haɓarta suna kallon juna, tabbas idan ya canka daidai ciki gareta, dan ga alamominsa dukka sun bayyana a tattare da ita, wani irin mummunar faɗuwar gaba ya ji lokacin da ya tuna menene silar mutuwar mummyn jelly, Haihuwa, haihuwa ta zo yi Allah ya karɓi kayansa, kwata kwata ma ya mance da zancen kamanni dake tsakaninta da mummy'n Jelly ɗin, shi dai murna ya fara yi ya samu abin da yake so.

Sakinta ya yi tare da nufar gaban mirror, cikin sauri ya shirya tare da yi wa Allah sujudur shukur, sai bin shi da idanu take yi, bayan ya kammala ya zo ya runhumeta sosai a jikinsa yana zuba mata godiya da sambatun me take so ya yi mata, mamaki ne ya kamata, me yake faruwa ne kuma? Ta tambayi kanta.

Zaunar da ita a bakin gado ya yi tare da riƙo hannunta, cike da so da Kauna ya fara magana. "Babyn daddy kina jina ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi alamar e "Nine auta a wajen mamana, bayan ni babu wasu, mamana tana sona fiye da tunaninki, amma a haka ta barni tana kuka ta tafi, ba ma wannan ba nake son gaya miki, kinga ni bani da kani kuma Allah bai bani yara da yawa ba, jelly kawai gareni, zan so ki haifa mini yara dozen da zan rinƙa kallah ina jin daɗi, ina rage zafin kewar mamata". Ya yi maganar idanunsa cike tab da kwallah.

Da yake yarinya ce sai bata hango tsantsar ciwo dake cikin rayuwarsa ba, bata hango irin bakin cikin da yake ciki ba, ta ɗauka kawai irin kwallan da ya saba yi ne, bata san wannan kwallah mafi azaba bane a gare shi ba.

"Daddy dama gwaggo Batula ba kanwar ka bace?" Ta faɗa tana rufe mishi idanun dan hawayen dake ciki su zubo ta goge mishi. "Batula kanwata ce amma mamanmu ba ɗaya ba, baki ji nace miki nine auta a wajen mamanmu ba ne? Ba a wajen babanmu na ce ba, wajen mamata, ni ne auta". "Daddy to ina mamanka da babanka, dan Allah ka kaini ina son ganinsu". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Babana ya rasu, mamata kuma tana a in da bamu isa mun yi gigin tinkarar wajen ba, so kawai ki bar zancen, just kawai ki yi musu addu'a Allah ya jikan baba, mama kuma Allah ya fitar da ita zance ne ko kuma me oho dai, kawai ki yi musu addu'a da ta dace da su, amma itama mama fa bamu da tabbacin tana raye a yanzu ko ta mutu, kawai ki yi musu addu'ar Allah ya jikansu baki ɗaya". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya shiga toilet dan ya je ya yi kuka sosai ko zai sami saukin abin da yake ji a ransa. Allah sarki sunga rayuwa iya ganin idanunsu, musamman ma shi da yake Auta, an rabashi da mahaifiyarsa tun yana yaro ƙarami, tun bai wuci 2 to 3 years ba, Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, yafi su Abbi gabaɗaya shiga kuncin rayuwa, ga shi lokacin da ya fara girma ya dawo hannun Abbi, Ommu ta azabtar da rayuwarsa, ya zo ya yi aure da wuri ba dan ya shirya ba, sai dan samun mafita, a auren ma sai da ya fiskanci matsalar dangin matar tasa, shekara ɗaya da aurensa suna tsaka da son juna da matar Allah ya karɓi kayansa a lokacin haihuwa, ya yarda da kaddararsa bawan Allah, ya jure ya cigaba da addu'a, ya riƙi jelly hannu bibbiyu, baban Muneer ya zo ya sake jefa rayuwarsa a cikin kunci, bayan haka jelly ta ɓata, ya sha bakar wahalar da har jinya sai da ya yi, ya sake gane ta, a gabaɗaya rayuwarsa, waje uku ne ya ji daɗi, na farko rayuwar da ya yi ɗan kalilan da daddyn Rimsha, sai rayuwar shekara ɗaya na aurensa da mummyn jelly, sai kuma yanzu da ya sake aure ya auri Ayla, sune iya jin daɗi da ya samu a gabaɗaya rayuwarsa, amma duk da haka bai sare ba, ya dukufa ya koma ga Allah, bai ce wani ne ko wata suka yi mishi wani abin ba, ya yarda jarabawace daga Allah, kuma a wajen Allah kawai yake neman taimako.

Readers Also Read