Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 24

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 24

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 24: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 24. Sai da ya yi kuka sosai kafin ya wanke…

3,310 words

Sai da ya yi kuka sosai kafin ya wanke fuskarsa ya fito ya dawo cikin ɗakin, kwance ya sameta a saman gadon har ta yi barci, abin ku da mai ƙaramin ciki, saurin barci.

Kusa da ita ya zo ya zauna tare da shafa kanta ya karanto mata addua'o'i sosai ya tofa mata, sosai yake jin tsantsar kaunarta a cikin zuciyarsa. Ya jima yana kallonta kafin ya haura saman gadon da kyau ya gyara mata kwanciya tare da rufa mata bargo dan garin akwai hadari da iskar ruwan sama.

Alwala ya wuce ya ɗauro a toilet tare da simfiɗa dadduma ya tada sallar la'asar da bai samu ya yi ba.

A ɓangaren gidan Lion kuwa.

Misalin Karfe 8 na dare, zaune suke ita da Akila a ɗakinta suna hira, tana sanye da Abaya mai shegen kyau launin pink color, ita kuma Akila atampha ce ɗin kin doguwar riga a jikinta, Akila ta zuba mata make up tamkar waƴan da zasu je party ko gidan bikin, bata ɗaure kyakkyawar dark black curly hair'nta ba, ta sake shi har gadon bayanta, sai ta yafa mayafin gyalen a kanta, sai tashin kamshi suke zubawa, Akila na ta bata labarin kyawu irin na kakanta Naurat, bata san cewa kakansu ɗaya ba, da yake ita Rimshan ta sani, sai kara tambayarta take yi da waye kakan nasu take kama, kuma dan Allah a ina ta san kakar tasu, nan Akila ta gaya mata a hoto ta santa, Abba yana da hotonta tun tana budurwa har aurensu da Dr Salman da bayan aure duk yana da hotunan, kamar zata yi kuka ta ce "Dan Allah Aunty Akila ki ɗauki hoton a waya ki turomin ko ta WhatsApp ne in ganta kin ji?" To ta amsa mata da shi, har mamaki Akilar take yi na yadda Rimsha ta damu sosai a kan maganar kakar tasu, tambayar kanta take yi sai ka ce Rimsha na da wani alaƙa da kakar tasu.

Suna tsaka da hira Imran ya shigo ya sanar da Rimsha ta je ta kaiwa Saif abinci, cikin sauri ta miƙe tana faɗin "Aunty Akila ina zuwa". Riƙo hannunta Akilar ta yi tana faɗin "A'a Rimsha ki jirani yau muje naga masoyin nan naki". Zata yi magana Imran ya rigata da cewa "A'a Heartbeat ki zauna ki jirata". Ba musu ta amsa da to, da sauri Rimsha ta wuce, sai da ta fita shi ma ya fice daga ɗakin suka bar Akilar ita kaɗai, wayarta ta jawo ta fara latsawa.

Kamar kullum Kitchen ta wuce ta ɗauko abincin, da sallama ta shiga ɗakin nasa, yana zaune saman bed nasa, jikinsa na sanye da wandon jeans baki da T-shirt fara tas, high neck t-shirt ne mai dogon hannu, ya ɗaure dark black curly hair'n nan nasa a bayan wuya, da alama yau yana cikin bakinciki, dan fusataccen fuskar nan tasa har wani kyalli take yi, saboda bala'in ɗaureta da ya yi, bata kalli in da yake ba, dan tana tsoron kada su haɗa ido ko ta kalli cikin idonsa ya tsorata ta.

In da ta saba ajiye mishi abincin ta je ta ajiye, tana zama bai fi da minti biyar ba sai ga shi ya miƙe ya iso in da take, a in da ya saba zama ya zauna tare da lanƙwashe kyawawan fararen kafafunsa.

Abincin ta fara zuba mishi, while shi kuma ya zubawa yatsun hannunsa idanu yana kallon,

A hankali ya juyo da kallonsa a kanta da nufin ya kalli abin da take zuba mashi a cikin plate ɗin, dan yau ba komai zai ci ba, akwai abin da baya sha'awar ci yau, yana ɗago dara daran blue eyes nasa kai tsaye suka sauƙa a saman kirjinta wadda kuma anyi sa'a wuyar abayar tata ta gangaro kasa kaɗan, hakan ya yi sanadiyar bayyanar sunansa dake a waje, sai dai sunan bai fito sosai ba, sakamakon ba sosai wuyar rigar tata ta yi kasa ba, iya sunan GRA ne kaɗai ya bayyana, saura ba su fito ba, dawo da kallonsa ya yi a kan fuskarta wadda shi ne kallonta na farko da ya fara yi a rayuwar zaman da suka yi, sun ɗan jima a tare amma bai taɓa ganin face nata ba sai yau, wannan kallon da ya yi mata kuma tayi daidai da ɗagowar kanta domin ta saci kallonsa ko me yake yi.

Ido cikin ido suka kalli juna yau, wani irin bugu da karfi kirjinta ya yi, yau ta kalli cikin tsakiyar kwayar idanunsa, a sukwane ta yi kasa da kanta yayin da shi kuma ya sanya hannunsa ya zame mayafin dake a kanta tare da riƙo rip ɗin gaban rigar tata domin ya zuge kasa ta yadda zai samu damar ganin abin da ta rubuta a kirjin nata da kyau.

A razane ta miƙe da nufin ta gudu ta bar ɗakin, cikin zafin nama ya riƙo hannunta tare da fisgota da karfi, ai kuwa yana fisgota sai saman kirjinsa ta faɗa, ko kaɗan bai ji komai ba tamkar wani dutse, ita kuwa suma ne kawai bata yi ba, amma har wani fitsari take ji ya zo mata da wani uban gudu tamkar zai zuba mata a pant nata, duk ta kiɗime ta fita hayyacinta, bata san time da ta saki wani marayan kuka ba wadda daga ji kasan cewa kukan tsoro ne ainun.

Shi bai wani damu dan tana jikinsa ba, abin da yake gabansa kawai yake yi, abin da ya yi niya kenan wato ganin me ta rubuta a wajen domin zuciyarsa na gaya mashi sunan sane da gaske kamar yadda ya gani.

Hannu ya kai ya damki zip ɗin rigar nata da nufin ya zuge, cikin sauri ta kai hannu bibbiyu ta kankame gaban rigar tata, ta hana shi zugewa, tana yi tana matsalar kwallah bibbiyu.

Gently ya ce "Remove your hands". Jin sexy voice nasa mai haukatar da tunani mai sauraro saboda daɗi, ba karamin haukata ta ya yi ba, bata ma san time da ta zame hannayen nata ba, sai dai ji ta yi ya zuge zip ɗin kasa har zuwa shafaffen cikinta, datse idanunta ta yi da kyau, wani irin azababben kunyarsa ne ya kamata, yau wani ya kallan mata tula-tulanta, kuma gata a kwance a jikinsa, abin haushi ma namiji ba mace ƴar uwarta ba, kuma namijin ma ba muharraminta ba, babu abin da ya haɗa su, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, shi ne kawai abin da ta iya furtawa a cikin zuciyarta.

Shi kuwa bai wani damu ba, hasalima bai kai idanunsa kan tula tulan nata ba, abin da yake bukatar gani shi kawai ya zubawa idanu yana karantawa tare da jan kyakkyawar farar vest ɗin jikinta kasa dan ya gani da kyau.

Tsab ya karance kafin ya dawo da kallonsa a kan kyakkyawar face nata da ya sha make up sosai yau, ta datse idanu gam tamkar zata fasa su, saboda matse su da ta yi, gabaɗaya ilahirin jikinta karma yake yi, kuma tabbas ya lura da hakan...............

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

E19-20

Tsab ya karance kafin ya dawo da kallonsa a kan kyakkyawar face nata da ya sha make up sosai yau, ta datse idanu gam tamkar zata fasa su, saboda matse su da ta yi, gabaɗaya ilahirin jikinta karma yake yi, kuma tabbas ya lura da hakan, daidai lokacin kuma Areef ya shigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama irin ta addinin Musulunci, bai lura da ita a jikin ɗan uwan nasa ba sakamakon sun bawa kofar shigowa baya.

Jin sallamar Areef yasa ya saki vest ɗin nata tare da sakinta, daidai lokacin shi kuma Areef ya kariso wajen, ya sha ruwan mamakin ganinta a jikin Lion ɗin, bai yi tunanin wani abin Lion ɗin ya duba a jikin nata ba, bai ma lura da zip ɗin rigarta a zuge kasa ba, da yake kunsan akwai vest, hakan yasa bai gane ba, amma dai kansa ya ƙulle, ya san dai dole akwai abin da ya kawo ta jikin Lion ɗin, to menene wannan?.

Zama ya yi kusa da ɗan uwan nasa har lokacin bai kau da idanunsa daga kansu ba, ita kuma idanunta a datse har lokacin, shi kuma Lion tun shigowar Areef yake kallon face nata yana nazarin wani abin, yes tabbas akwai abin da yake nazari dan gane da face ɗin nan nata, tabbas ya taɓa kallon mai irin wannan fuska sak a tare da Josephine, to wace ce? Ya tambayi kansa.

"Stand up from my body!" Shi ne abin da ya furta a nutse. Jikinta sai kerma yake yi ta miƙe daga jikin nasa ta sauƙa kasa, har ga Allah ganin sunansa yasa gabaɗaya ya ji wani iri, jikinsa ya yi sanyi, amma yana da bukatar ya tabbatar da tun yaushe aka yi wannan zane dan ya lura kamar ba na yanzu bane, idan zanen ya jima kenan hakan yana nufin dan Allah aka yi shi, idan kuma bai jima ba, akwai dalilin yin ta.

Cike da tsoro da fargaba idanunta a rufe bata lura da Areef ba, ta nufi hanyar fita daga ɗakin, har lokacin jikinta na karma, da kyar take iya taka kafafunta ta riƙe kanta dan kada ta zube kasa.

"Come here". Ya furta tare da dawo da kallonsa a kan Areef. Da kyar ta iya juyowa ta nufo shi tana mai kallon kasa, ta ki yarda ta ɗago kanta bare ma su yi ido huɗu.

In da ta saba zama, a nan ta koma ta zauna. "What is your Name?" Ya tambaya yana ɗauko wayarsa. Gabaɗaya ta nemi natsuwarta ta rasa, ta rasa ina zata sanya ranta ta ji daɗi, ta rasa me yake yi mata daɗi, da kyar murya na rawa ta bashi amsa da "My name is Rimsha". Shi dai Areef sai mamaki yake yi, wai me ya haɗa su ne? Ya kasa ganewa fa, a fitar da shi daga duhu.

"Yaushe kika yi wannan zanen? Kuma me yasa kika yi ta?". Yana maganar yana tura saƙo a watarsa zuwa ga Aseef. Cike da tsoro da fargaba, bata san lokacin da ta ce mishi last week ta yi ba, ta rikice ta manta ko yaushe nema ta yi zanen.

Jin ta ambaci last week yasa ya ce ta ɗauko mishi chemical da ya zubawa mata a lallen hannunta ranar bari ya zuba ya goge zanen, wani irin mahaukacin razana ta yi tare da sakin kuka mai sauti, ita kaɗai tasan azabar dake tattare da wannan shegiyar chemical ɗin, shi dai Areef ya zubawa sarautar Allah idanu kawai yana kare musu kallo, tun da an rasa me fidda shi daga duhu.

Ɗago dara daran blue eyes nasa ya yi tare da sauƙesu a kanta, nan take ta natsu sit tare da haɗiye kukan nata, ta nemi kukan ta rasa, tuni ya gudu, wargi ma ai waje ya samu, ba tare da ya yi magana ba ya mai da kallonsa izuwa saman drawer da chemical ɗin yake ciki, ta gane nufinsa, wato ba zai maimai ta maganarsa ba kenan.

Jiki ba kwari ta miƙe ta nufi wajen drawer, shi kuma Areef ya sanya hannu bibbiyu ya tallaɓo kumatunsa ta yadda zai ji daɗin mai dasu Tv'nsa kawai, tun da an rasa mai fidda shi duhu.

Ɗauko chemical ɗin ta yi tazo ta miƙa mishi tare da zube gwiwowinta a kasa, karɓa ya yi tare da buɗewa, gently ya ce ta cire rigar tata sannan ta sanya hannu ta tare chemical ɗin ta zuba a kirjin nata da kanta, shi kuma zai zuba mata a hannun, kuka take yi baiwar Allah, hawayen nan wani na bin wani, kara tsananta kermar jikinta ya yi, idanunta tamkar zasu firfito su faɗo kasa, hannayen nata sun kasa tsayawa wajen jan vest ɗin nata zuwa kasa, tsantsar kerma da jikinta yake yi ne, yasa komai nata ya kasa tsayawa waje guda, duk wata zuciya mai imani idan ta ga halin da take a ciki sai ta matsa mata kwallah, amma shi kuma Lion tamkar wani mai zuciyar dutse, ko kaɗan bai ji tausayinta ba.

"Lion wai me yake faruwa ne?". Cewar Areef ya yi maganar yana kamo hannunta dake ta faman kerma ta ɗaura a saman kirjinta ta kasa jan vest ɗin nata kasa, shiru Lion bai tanka mishi ba, riƙota da kyau Areef ɗin ya yi tare da jawota ta dawo kusa da shi, har lokacin kuma kallon ɗan uwan nasa yake yi, ya kasa kawar da kansa yana jiran amsa.

"Sister me yake faruwa? Me ya haɗaki da Lion?". Kasa magana ta yi, kuka yaci karfinta Baiwar Allah, hawayen nata ya fara goge mata yana mai kara jawota jikinsa.

Daga ita har shi sai da suka yi wani mahaukacin razana jin tsawar da Lion ɗin ya daka musu akan ta bashi hannunta ya zuba mata chemical ɗin nan ta zuba a kirjinta, tsabar razana bata san lokacin da ta kankame Areef da hannayenta dukkan biyu ba, ganin ta fita a hayyacinta sosai ne yasa Areef ɗin ya rungumota sosai a jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta.

"Saif me yake faruwa ne? Me ta yi maka?". A karo na biyu ma shiru ya yi bai tanka ba, miƙewa da ita a jikinsa Areef ɗin ya yi, bayan sun miƙe tsaye sai ya saɓata a kafaɗarsa dan ya lura ba zata iya tafiya ba, kuma ya lura muddin bai fitar da ita daga ɗakin nan ba tana iya mutuwa saboda tsabar razana.

Bai ce da su komai ba har suka fice daga ɗakin, ya yi hakan ne kuma dan saboda baya son ja in ja da Areef ɗin, duk abin da zai yi yana yin shi ne da lissafi, baya taɓa yi wa TRIPLETS nasa faɗa ko magana mara daɗi a gaban wani, dan baya son kowa yasan tsakaninsa da ƴan uwansa, ko ranar da ya ce Mark ya sanyata tsalle kwaɗo Areef ya hana, yana sane, abin da yasa bai yi magana a lokacin ba, baya son su Mark su raina TRIPLETS nasa, yana son tamkar yadda kowani securitynsa zasu ji maganarsa, to haka zasu ji maganar TRIPLETS nasa, yasan cewa idan ya yi magana a lokacin Mark zai raina Areef ɗin, zai zama idan Areef ya yi magana ba zai ɗauki maganar da muhimmanci ba, hakan yasa ya yi shiru sai da Areef ɗin ya shigo ɗaki ya same sa ne ya yi mishi faɗa tare da gaya mishi baya son ya rinƙa shiga irin wannan magana, idan ya bawa wani punishment to baya son su rinƙa saka baki, haka kuma ya saba yi musu, daga shi sai su yake yi musu faɗa, ko Imran baya bari yasan tsakaninsa da TRIPLETS nasa, yanzu ma yana jiran Areef ɗin ne ya dawo, kuma ma abin da yasa bai karfafa dole sai ya sanya mata chemical ɗin ba, saboda yasan zanen ba na yanzu bane, rikicewa da shiga ruɗu ne yasa ta ce na yanzu ne, amma a matsayinsa na babban soja ya san tabbas ba na yanzu bane, an jima da yin shi, to shiyasa bai karfafa dole sai ya zuba mata ba, ku kunsan da ya karfafa wane Areef ya karɓeta daga hannunsa, ba'ayi wadda zai iya karɓarta ba, bugu da kari fuskarta, wannan fuska tata ta sanya shi cikin tunani, akwai wani ɓoyayyen sirri a tarrare da face ɗin tata a cewarsa, bai kawo cewa son shi ne yasa ta yi zanen sunan ba, dan a yadda yake ganinta, kallon karamar yarinya yake yi mata, bata san menene ma soyayya ba, kuma kuma masu karatu kunsan a lokacin da ta yi wannan zanen ta yi ne ba dan tana son shi ba, ta yi ne kawai dan yana burgerta, a lokacin bata iya banbance soyayya da burgewa ba.

(Amma kuma da ta tara hannunta da gaske fa zai zuba mata chemical ɗin nan, gaskiya Lion halinsa sai shi, baka gane gabansa bare bayansa🤔)

Kai tsaye ɗakinta Areef ya wuce da ita, zaune ya isko Akila tana aikin latsa waya, ganinsa ɗauke da Rimshar yasa ta miƙe tsaye tana tambayarsa ko lafiya, bai ce da ita komai ba, ya wuce ya kwantar da ita a saman gado tare da zama a gefenta yana kallon yadda jikinta ke uban kerma tamkar mazari.

Gently ya fara magana "Rimsha ya isa haka nan, ki dai'na wannan kukan, yanzu ki tashi ki gaya mini gaskiya me ya faru tsakaninki da Lion? Me ya haɗa ku?". Ta ɗauki tsawon a kallah minti goma kafin ta iya dawo da natsuwarta, da kyar ta tattaro sauran muryar da ya rage mata, cikin shasshekar kuka ta fara magana "Yaya Areef ba zan ɓoye maka ba, dan ya kalli zanen dake a kan kirjina ne ya ce zai zuba mini chemical na goge shi". "Zan iya ganin wani zane ne?" Ya tambaya yana kallon kirjin nata, sai yanzu ya lura da zip ɗin rigarta a zuge kasa, abin ku da Turawa, kwata kwata basu san menene kunya ba a rayuwarsu, Akila kam ta zuba musu idanu kawai tana kare musu kallo.

Da kyar ta iya miƙewa zaune tare da sanya hannu cike da kunya ta ɗanyi kasa da vest ɗin jikinta kaɗan zuwa rabin tudun tula tulan nata, ta nuna mishi zanen, zuba wa zanen idanu ya yi yana karantawa.

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Lallai da kuwa Lion ya tabka babban kuskuren da ba zai iya gyarawa ba a rayuwarmu, yanzu idan ma ban da shi da neman magana, ko in ce da san gallazawa rai, ai yasan wannan zane daga ido ma ba ta yanzu bace, kowa ya ga wannan zane yasan ta jima, abinda har ta fara bin fatar jikinki, amma ba komai ina mai baki hakuri a madadinsa, kuma In Sha Allah daga yau kin dai'na zuwa in da yake, Aseef yana nan zuwa gobe, dama shi ne mai kai mishi abinci, zaki huta my sister, rabu da shi Allah yana ganin mu ai". Ya kai karshen maganar yana jawo mata zip ɗin rigar tata sama, sam bai ji daɗin abin da ɗan uwan nasa ya yi ba, yasan da cewa yana sane zanen ya jima, kawai bakar mugunta ce sai ya gallazawa ƴar mutane Baiwar Allah, amma ba komai zai gane kurensa, zai ɗanɗani ƙuɗarsa ne.

Bayan ya gama ja mata zip ɗin rigar ya goge mata hawaye tas kafin ya miƙe tsaye yana mai dawo da kallonsa a kan Akila da ta tsare shi da idanu. "Heartbeat sarkin rigima, yanzu kuma wani sabon rigima zaki yi mini?" Ya yi maganar cikin zolaya, kuma duk cikin harshen turanci suke magana.

Ɗan rufe fuska ta yi da hannunta tana murmushi bata ce komai ba, wucewa ya yi ya fice daga ɗakin ya koma wajen ɗan uwan nasa.

Yana fita ta koma ta kwanta ƙwaƙwalwarta na tariyo mata abin da ya faro, kwayar idanunsa kawai take gani cikin nata, matsowa kusa da ita Akila ta yi ta shiga rarrashinta tare da bata baki.

A ɓangaren Areef kuwa, abinci ya je ya zubawa ɗan uwan nasa, a tare suka ci suka ƙoshi, da kansa ya tattare kayan ya fitar tare da dawowa ya ɗauki chemical ɗin ya mai da shi mazauninsa, a lokacin shi kuma Lion already ya koma saman bed nasa ya kwanta, abu biyu suka tsaya mishi a zuciya tun zuwan shi NIGERIA, na farko Yarinyar da ta kira sunansa kai tsaye a ranar da ya sauƙa gidansu Imran, har cikin ransa yanzu da ya ga sunansa a kirjin Rimsha zuciyarsa ya bashi ita ce wannan yarinya, abu na biyu kuma fuskarta, tabbas ya taɓa kallon mai irin wannan fuska sak a tare da Josephine, to waye kenan? Wan can dai ba yarinya ba ce tare da Josephine, dattijuwa ce, kada ku mance kowa da yadda yake kallon mutum, wani zai ga kayi mishi kama da wani na shi, kai kuma ba zaka ga kamannin ba, to shi dai tabbas ya ga mai irin wannan fuska tata sak a tare da Josephine, sai dai ya rasa a ina ne ya taɓa ganin nasu tare, shiru ya yi yana faɗaɗa tunaninsa a ina ne ya ga hakan.

Readers Also Read