Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 25

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 25

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 25: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 25. Gefensa Areef ya zo ya zauna tare da ɗan taɓa…

3,362 words

Gefensa Areef ya zo ya zauna tare da ɗan taɓa shi, juyo da dara daran blue eyes nasa ya yi izuwa kan Areef ɗin, shiru bai ce komai ba, cikin natsuwa Areef ya fara magana. "My blood na san kana son farincikin mu fiye da naka, na san kana son abin da muke so, na san baka da wani burin da ta wuce ka ganmu a cikin farinciki, duk in da muka je muna alfahari da hakan, muna jin daɗin hakan, dan Allah yau ina neman Alfarma a wajenka, ba dan ni zaka yi ba, please and please dan girman Allah zaka yi, ina son ka rinƙa danne zuciyarka a kan sister, wlh tana da problem a kanta, ta shiga ta shin hankali, ko in ce taga tashin hankali da ya wuce shekarunta, ya wuci girman ƙwaƙwalwarta, hakan yasa take da yawan razana, to please tana tsoronka kamar ta mutu, tana tsoron ganin kwayar idanunka, idan har ka cigaba da kallonta ma kawai wlh kana iya ɗaukar gawarta, ni zaka yi wa, ina kaunarta, ina kaunarta fiye da tunaninka, idan tana farinciki nima ina yi, idan ta yi kuka, ko ban yi a zahiri ba, ina yi a cikin zuciyata, kasan dai bawa baya sanyawa kansa soyayya ko? To ba ni na sanyawa kaina sonta ita da mahaifinta ba, Allah ya jarrabeni da hakan, ka taimaka mini tun da Aseef zai zo gobe, ina son sister ta daina kawo maka abinci, ta daina zuwa kusa da kai, yanzu haka dole Prof ya ɗauketa zuwa asibiti, idan ba haka ba, akwai gagarumin matsala". Ya kai karshen maganar cikin wata iriyar murya mai ɗauke da damuwa ainun, tabbas duk abin da yake damun Rimsha ya sani, baiwar Allah bala'in da ta rinƙa gani na Daular Mutuwa ya birkita mata kwakwalwa, ko shi Dr Nawid bai gano ainahin damunwanta ba, wlh bala'in dake Daular Mutuwa ya fi karfin ƙwaƙwalwarta ya ɗauka, hakan ya haifar mata da razana, Areef ya gano hakan ne ta hanyar dubata da ya taɓa yi da bata da lafiya, hakan yasa take yawan suma, kuma Areef ya yi gaskiya idan ta cigaba da zama inuwa ɗaya da Lion to wata rana za'a iya ɗaukar gawarta a wajen.

Shiru ya yi bai tanka ɗan uwan nasa ba, shima Areef ɗin shiru ya yi, almost 30 mins suna haka kafin Lion ya ce "Haka kake so?" Gyaɗa mishi kai ya yi alamar e, jinjina kai ya yi alamar to ya yi accepted, wani irin farinciki ne ya dira mishi a cikin zuciyarsa, da sauri ya rungumi ɗan uwan nasa yana zuba mishi ruwan godiya tare da ruwan Albarka, shikenan yanzu Rimsha ta tashi daga ƴar aiki, ta yi free wow abin ya yi daɗi, yau saboda Areef Lion ya canza magana, saboda faricniki TRIPLETS kai abin ya kayatar.

Sun jima suna hira, ko da sunan wasa Lion bai sanar da Areef face ɗin Rimsha ya yi mishi kama da na wata da ya taɓa gani tare da Josephine ba, ya bar abin a ransa zan yi bincike a kan idan ya sami lokaci, yau dai kwanan faricniki Areef ya yi, shi kuma Saif mafarkin Josephine kamar kullum ya kwana yana yi.

A ɓangaren Rimsha da Akila kuwa, Rimsha dai barci ɓarawo ne ya yi awon gaba da ita, ita kuma Akila sai da suka yi waya da Umaisha kafin ta raba dare da sahibin nata suna hira, sai Misalin karfe 2 na dare suka hakura ba dan sun so ba, ko kaɗan a hirar tasu bata kawo mishi zancen cewa ta gane shi ko makamancin haka ba, shima bai kawo mata zancen ba, sun dai zuba soyayyarsu kamar yadda suka saba.

Wayar da suka yi da Umaisha ba komai bane face magana a kan yajin da Akil ya yi, mu koma baya kaɗan mu ji tattaunawar tasu kafin mu cigaba da tafiya.

Kiranta Umaisha ta yi, tamkar zata yi kuka ta fara magana "Hello Heartbeat". Cike da kulawa Akilar ta ce "Aunty Umaisha ta yaya Akil, to ya ake ciki ne? Ya naji muryarki haka? Ko dai babyna ne yake addaba miki? Kin san nina yi mishi huɗuba ai, na ce ya tabbatar yana takura miki sosai, ya yi ta naushinki a ciki har sai kin yabawa aya zakinta". Tana magana tana murmushi, turnuke fuska Umaisha ɗin ta yi, tamkar zata yi kuka ta ce "Ni Heartbeat ba wannan ba, dan girman Allah wata alfarma nake nema daga gare ki". Da sauri ta ce "Wace alfatma kuma?"

"Dan Allah heartbeat ki kira mani shi a waya, ki ce mashi wlh na tuba bazan kara ba, tun fa da safe ya yi fushi ya fita, kuma wlh kafin ya fita sai da ya ce mini ya yi yaji sai ya yi sati biyu ko wata ɗaya zai dawo, na ɗauka wasa yake yi kuma raina a ɓace na ce mashi kada ma ya dawo ma in yana so, ashe wlh da gaske yake yi, yanzu na kirashi yafi miss call hamsin ya ki ɗagawa, kuma wlh ni nasan yana ganin kirata, ɗauka ce kawai ba zai yi ba, na yi mashi massages har na gaji babu reply, dan girman Allah ki kirashi nasan zai ɗauki kiranki, ba zan taɓa iya yin barci ba har sai ya dawo". Kwashewa da dariya Akila ta yi har da riƙe ciki, iskanci Umaisha da Akil ya wuce misali.

"Heartbeat ki tausaya mini ko dan saboda babynki". Tana magana murya a dashe taci kuka ta ƙoshi, ita kuma Akila tsabar shakiyanci tana binta da to na iyashege, sai da Umaishar ta gama maganarta tas, sannan Akilar ta ce "Kai amma yaya Akil ya iya, wato ma shi ne ya yi yaji kenan? Wayyo cikina, ai kaɗan ma kika gani, ba ke duk abin da na gaya maki baki ɗauka ba, wlh yaya Akil ustadz ne, koyi da annabi yake yi, shiyasa shi ya yi yaji ya bar miki gidan, nasan yana masallaci a yanzu, ya tare a can, abin da zai faru kawai ki jira sai ya cika wa'adinsa da ya ɗebe". Ta kai karshen maganar tare da sake kwashewa da dariyar shakiyanci, katse kiran kawai Umaisha ta yi, dan ta lura Akila zata kara mata zafi a kan zafi ne.

Bayan ta katse kiran ne Akilar ta jawo bargo ta shiga kafin nan ta rubutawa Akil massage a kan halin da Matarsa ke ciki, bayan ya tura mishi ne bai fi da minti goma ba masoyin nata ya kira, shi ne suka fara hira har karfe biyu na dare, to kun ji yadda a ka yi.

Washegari karfe 8 na safe, Akil ya zo ya ɗauki Akila ya mai da ita gida, kamar yadda Imran ya faɗa, sun sha kukan rabuwa da Rimsha kamar ba gobe, sai da Areef ya ja Rimsha zuwa cikin gida, ita kuma Akila Imran ya turata cikin motar Akil suka nufi gida.

Ɗaki Areef ya mayar da Rimsha tare da yi mata albishir a kan daga yau ta bar aiki, school kawai zata rinƙa zuwa ta dawo, sai wanka da tsala kwalliya, sai kuma barci, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, dama kamar zata yi kuka, daurewa kawai take yi tana yin wannan aiki, amma badan haka ba, Allah ne kaɗai yasan yadda take ji a duk san da ta ɗauki abincin da nufin ta kai wa Lion.

Ganin sai murmushi take baki yaki rufuwa ne yasa shi ya miƙe tare da ficewa daga ɗakin yana mai jin tsantsar kaunarta a ransa.

Bin bayansa da kallo ta yi har ya kure wa ganin ta ya fice daga ɗakin, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare buga uban tagumi, ta rasa me yake damunta, daga jiya zuwa yau, a hankali hankali soyayyar da take yi wa Saif yana juyawa ya koma kan Areef ne ko Aseef ne ta rasa, ita kanta ta rasa me yake damunta, ko wace zuciya tana son mai kyautata mata, tabbas son da take yi wa Saif kaso 40 cikin ɗari ya dawo kan Aseef da Areef, sai dai a cikinsu ta rasa tantance waye ne take yi wa son aure, waye kuma take yi wa son kyautatawar da suke yi mata, shekarunta bai kai ta iya tantance hakan ba, ba karya suna bata kulawar da ko motsi ta yi sai sun tambayeta akwai wani abin ne idan suna kusa, shi kuma Aseef idan suna yin video call kenan, ba su taɓa barinta ta zauna shiru har ma ta yi wani tunanin da zai sanyata bakin ciki, tabbas tana son su ba kaɗan ba, ba zata iya yin wuni guda bata ga Aseef or Areef, idan bata yi Video call da Aseef ba, to zata kalli Areef, musamman ma shi Areef ɗin wanda suka yi mugun sabo na kin karawa, kuna ganin dai yadda suke da ita, kuma idan ba ku manta ba, shi Areef ɗin shi ya fara bata kulawa kafin Aseef ya biyo bayansa, shi ya kula mata da daddynta tamkar ɗan uwan shi, wannan matsala tata tana neman zama mata gagarumar matsala, domin ta rasa wa take so so na aure, waye kuma yake yi wa son kyautatawa a cikin TRIPLETS.

Yana fita abinci ya je ya ɗaukawa ɗan uwan nasa daga kitchen zuwa ɗakinsa, kamar dai kullum a tare suka ci abincin cikin nishaɗi da kaunar juna, bayan sun kammala suka koma saman bed dan su cigaba da hira, bayan Areef ya gyare wajen kenan, Allah sarki karfi da ya ji Areef ya koyi aikin da bai kamata ace shi ne yake yi ba, before bai iya ba sam, yanzu kuma Alhamdulila yana ƙoƙartawa ya yi.

Misalin karfe biyu na rana, taci kwalliya kamar ba gobe, ta sanya ɗaya daga cikin ɗinkunan da Imran ya ɗinka musu, wata shegiyar ɗinkin riga da skit a kayi mata, kayan sun zauna tsam a jikinta tamkar dan ita aka yi shi, ya bi shape ɗinta sosai da sosai, bata iya ɗaura ɗankwalin atampha ba, sai kawai ta yafa abinta a saman kanta, ta yi kyau iya kyau.

Palon sama ta fito ta zauna tana jiran Imran ya fito zai kai ta wajen gyaran gashi, yau tana ji tamkar ta yi kumshi idan suka je gyaran gashin tun da yanzu ta daina yi wa Saif aiki, farinciki a wajenta ba'a magana, tana zaune shiru ga wayarta na a gefenta, ko me ta tuna sai kuma idanunta suka cika tap da kwallah, wayar tata ta laluɓo.

Kunna hasken screen ɗin wayar ta yi, bayan ta cire password ɗin contact ta shiga, number Anaya ta fara kira, bugu ɗaya Anaya ta ɗaga dan lokacin ta dawo daga school, murya a gajiye ta ce "Rimsha ina wuni?". Tamkar zata fashe da kuka ta ce "Anaya, Anaya yau GAR ya kallah mini......." Sai kuma ta kasa karisawa ta yi shiru.

"Rimsha waye kuma GAR? Me kuma ya kallah miki ɗin". Girgiza kai ta fara yi tamkar Anaya ɗin na a gabanta "Babu komai Anaya zamu yi waya anjima". Ta kai karshen maganar ba tare da ta jira Amsar da Anaya ɗin zata bata ba, ta yi maza ta katse kiran.

Ajiye wayar a gefenta ta yi tare da buga uban tagumi tana tunani, abin da Lion ya yi matan nan, ya yi mata zafi ba ɗan kaɗan ba, kuma dai kunsan yadda take tattalin tula tulan nan nata, bata son ko iska su sha, idan zata sanya kaya sai ta rufesu da vest, bata bari ko alamarsu a gani, kawai ya zo ya wani buɗe mata su ya kalle kamar nashi ko an aike shi, yau da tana da dama sai ta kifa mishi maruka ko biyar ne haka, kila ta huce takaicin da take ciki, idan ta tuna shikenan ya kallesu, sai ta ji tamkar ta aza hannu a kai ta yi ta kurma ihu ko zata ji sauƙi a cikin rayuwarta.

Tana tsaka da tunani ta ji alamar gudu ana haurowa saman benen, kai kallonta izuwa wajen ta yi dan taga su wanene.

Coper, Lucky, Winston, da kuma Brady da wasu irin mahaukatan gudu suka hauro palon saman.

Tana yin ido huɗu da su bata san time da ta miƙe da wani mahaukacin gudu ba, ta ruɗe sosai, bata san time data faɗa ɗakinsa a maimakon na Imran ba, dan ba zata iya shiga ɗakinta ba, salon su bita su yi mata wani abin, gwara ɗakin Imran, duk wuya zai tare mata, ba zai bari su taɓata ba, ba zai bari su cije ta ba, sai aka samu akasi, ta fito daga ruwan zafi ta faɗa wuta, shi ne shiga ɗakin Lion da tayi kenan.

Yana tsaye a gaban mirror daga shi sai towel a kugunsa, kai tsaye wajensa ta nufa, su kuwa tana miƙewa suka rufa mata baya, dan su karnuka dama amfani suke yi da kamshin jikin mutun su nemo in da yake, Lion suke nema, ba ruwansu da ita, ita ce ta tsorata sosai, musamman ma Brady in da ya yi kewar Lion sosai, ai a guje ya nufi ɗakin Lion ɗin.

Ita kuma idanunta a rufe ta faɗa jikinsa ta baya tare da kankame shi sosai tana ihu, gently ya juyo tare da juyo da ita ta gabansa dan taga waye ta riƙe, ina ai idanunta a rufe, haushin su Brady yana kara haukata mata kwakwalwa, wani irin damka ta yi mishi tare da harɗe hannayenta a kugunsa ta kewayo da su ta bayansa, kanta a saman kirjinsa, ta kara ƙanƙame shi sosai ta yadda ba zai iya ɓanɓareta daga jikin nasa ba, ta manne kamar chewing gum, tare da datse idanunta gam

A fusace yake ƙoƙarin daka mata tsawa Brady ya yi kansu da gudun gaske, wani razanannen ihu ta saki tare da sake yin tsit tamkar an ɗauke wutar nepa, sarkin tsoro kenan number ɗaya.

Daka suwa Brady ya yi ya haye jikinsa yana kuka a hankali, ga Rimsha a ɓari guda ga Brady a ɓari guda, daidai lokacin Aseef ya shigo cikin ɗaki Areef na biye da shi a baya, su coper suna gefensu, shi Aseef ya ce ba zai iya tafiya mai nisa ya bar su coper ba, shiyasa ya tattarosu abinsa, tamkar sun dawo NIGERIA ne da zama.

Karisowa wajen ɗan uwan nasu suka yi, fuskokinsu ɗauke da tsantsan faricniki tare da kayatatcen murmushi,. Rimsha na ƙoƙarin sulalewa ta zube kasa dan bai riƙeta ba, kuma ta suma jikinta ya saki, yana jinta bai tare ta ba, a cewarsa me haɗin shi da ita, Aseef da Areef har suna rige rigen tareta, mamaki ne ya kama shi, kamata ya yi Aseef ya rungume shi ya yi mishi oyoyo amma suna rige rigen ɗaukar Rimsha, wai anya lafiyarsu kuwa? Ya tambayi kansa, yana tsaresu da ido.

Areef ne ya tareta, shi kuma Aseef ya dakawa Brady tsawa a kan ya sauƙa a jikin Lion ɗin bari shi ya rumgumi ɗan uwansa, da yake sabo tirken wawa, sun saba sai Brady ya sauka shi kuma ya rumgumi ɗan uwan nasa, rike shi sosai Lion ɗin ya yi yana shafa kansa, gently ya ce "Ya hanya?" Kiss ya yi wa ɗan uwan nasa a kumatu yana faɗin "Ai Exams dana haɗa nayi lokaci guda ya fi wannan tafiya wahala". Dariya Areef ya yi lokacin yana kwantar da ita a saman gadon Lion ɗin.

Da mamaki Lion ya bishi da kallo, wai me TRIPLETS suke nufi da shi ne? Ya tambayi kansa, kai kallonsa kan ta ya yi tare da dawo da kallon nasa a kan Areef ɗin. Cool murmushi Areef ya sakar mishi kafin ya ce "A filina ta kwanta ai ba'a fillinka ba".

Girgiza kai ya yi wato ma suna sane suke yi mishi abin da suka ga dama, bai damu sosai ba dan yana ɗauka cewa Areef yana sonta ne, soyayya irin ta aure suke yi, shiyasa sau da dama baya damuwa da irin hakan, kuma tabbas ya ga tsantsar kaunarta da sonta a idanun ɗan uwan nasa, to babban abin tambayar a nan shi ne, wannan suna da ta rubuta a kirjinta fa? Ya tambayi kansa da kansa, tabbas yana da tabbacin Areef yana sonta, kuma yaga yadda suke da ita da Areef ɗin gwanin ban sha'awa, baza'a ce bata son shi ba, to ya abin yake kenan? Ya sake tambayar kansa da kansa.

TO FA BABBAR MAGANA SHI LION SABODA SHAƘUWAR DAKE TSAKANIN TA DA AREEF YASA YANA TUNANIN SOYAYYA SUKE YI, KUMA IDAN BAKU MANTA BA TABBAS AREEF YANA SONTA, KAWAI DAN YASAN ƊAN UWANSA TAKE SO NE YASA YA HAKURA, SHI LION SABODA TSANTSAR KAUNAR TRIPLETS NASA YASA YAGA TSANTSAR SOYAYYAR RIMSHAR A CIKIN KWAYAR IDANUN AREEF ƊIN, HAKAN YASA YA GASGATA TUNANIN DA YAKE YI A KAN SHAƘUWAR TASU, YA KENAN WANNAN SHI NE CAKWAKIYA, ITA MA DAI KUNJI YANZU TA FARA SON AREEF ƊIN, MU DAI JE ZUWA.

"Je kayi wanka ka shirya sai ka zo ka ci abinci". Cewar Lion, ya yi maganar yana kallon Aseef. "Lion a kira masu gyara ɗaki, su zo su sanya mana bed guda uku a cikin bedroom ɗin nan ka ji?" Cewar Areef. Shiru ya yi musu tamkar bai ji su ba, zasu fara saka shi a gaba kenan, wai gado guda uku, ya bi uku da gudu, kowa ɗakinsa zai wuce iya shegensun nan.

Wucewa Aseef ya yi izuwa cikin toilet, shi kuma Areef ya tattara su Brady ya nufi waje da su, oga kuma, ya cigaba da abin da yake yi na shafa Lotion nasa.

Bayan ya kammala ya wuce dressing room nasa, ita kuma tana kwance a saman bed nasa, yau gata a bed ɗin Lion a matsayin budurwar Areef, lallai akwai cakwakiya ba ɗan karami ba wai.

After some hours💋

Shirye cikin wani shegiyar wandon jeans mai bala'in kyau da tsada Aseef ya fito, wandon launin blue, sai kuma riga launin ash color, ya yi matukar kyau sosai kamar ba shi ba, sai tashin kamshi perfume ɗin ɗan uwansa yake yi, yanzu saboda tsiya perfume ɗin Lion yake sakawa, tun da ya sami lafiya shikenan ya koyi takurawa Lion shima, ya bi kafar Areef, diamond watch nasu na TRIPLETS yau ya ɗauko ya sanya a hannunsa, dama idan baku mance ba Lion ya karɓe watch ɗin gabaɗaya ya ajiye, to ya je ɗaukar agogon Lion ɗin sai ya ga diamond watch nasu, hakan yasa ya ɗauke shi kawai, glass kuma, baki ya ɗauko wadda baka iya ganin kwayar idanunsa, kuma glass ɗin ba ƙaramin kyau ta yi mishi ba, sarkansu na nan a wuyarsa ko in ce a wuyoyinsu.

Bayan ya kammala shiri tsab ya fito daga dressing room ɗin zuwa cikin ɗakin, babu kowa a cikin ɗakin sai Rimsha dake sume, saman gadon ya hau tare da shafa fuskarta yana ambatar sunanta kasa kasa, shiru bata farka ba, sauƙowa kasa ya yi tare da buɗe fridge ya ɗauko ruwa mai sanyi, kaɗan ya tarfo a hannunsa tare da shafa mata a fuskarta, da yake a nitse ya yi mata, sai ta farka a nitse, ganin shi da black glass ya rufe kwayar idanunsa ba zata iya tantancewa ba sai ta yi zaton Lion ne, abin da mamaki yadda mutane ke kallon fuskokin mutane da dama a fuskar Aseef, dama akwai irin mutanen nan, sai dai basu da yawa a duniya, wadda idan ka kallesu dole sai sun yi maka kama da wani naka, haka halittar fuskarta ke.

Kokarin sauƙa kasa ta yi dan ta gudu kada ya yi mata hukunci, riƙo hannunta ya yi yana mai ambatar sunanta, jin muryarsa yasa ta tsaya tare da ambatar sunansa yaya Aseef, shi kuma mamaki take bashi yadda take banbanta voice nasa dana Areef, ta yi musu farin sani yarinyar nan, ko bata ga face nasu ba, tana iya banbanta voice nasu, akwai ta da kwakwalwa over.

"Waye ya ce miki ni ne? Areef ne fa". Ya faɗa cikin zolaya, dariya mara sauti ta yi ba tare da ta yi magana ba, yana riƙe da hannunta ɗaya cikin nasa ya ciro wayarsa da ɗayan hannu ya fara kiran number daddynta video call.

Bugu ɗaya daddyn nata ya ɗauka, yana zaune kusa da pool yana karatun husnul Muslim, ganinta yasa ya saki wani ƙayatattacen murmushi har sai da dimples nasa suka lotsa sosai, ita ma murmushi take yi sosai tamkar ta shiga ta jawo daddyn nata ra rungume haka take ji.

Readers Also Read