Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 26

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 26

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 26: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 26. Sai binsu da ido Aseef yake yi yana murmushi,…

3,324 words

Sai binsu da ido Aseef yake yi yana murmushi, cikin harshen Hausa suka gaisa tare da fara hira, sai dariya take yi ta manta ma a ina take, almost 30 mins suna hira haka kafin Aseef ya ce "Uncle zan kira anjuma yanzu zata rakani wani waje ne". Da turanci ya yi maganar, okey Musharraf ya amsa da shi, diff ya katse kiran tare da cewa "To tashi muje ki rakani unguwa", ɗan zaro idanu ta yi, "Unguwa kuma yaya Aseef?". Gera ɗaya ya ɗaga mata alamar e, okey ta amsa mishi tare da miƙewa ta sauƙo kasa, har lokacin bai saki hannun nata ba, tamkar wasu mata da miji haka ya riƙe hannunta suka fita waje.

A palon sama ya cikaro da Areef yana ƙoƙarin shiga bedroom ɗin. "Kai, kai, kai, Aseef ina zaka je haka?" Ya yi maganar yana kare mishi kallo, ba karya ya yi kyau sosai. "To sarkin sa ido ina ruwanka da ni, ni dai yanzu bani saƙona ka gani". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce Okey, bai wani damu ba, dan yasan Aseef da Musharraf babu ɓoye ɓoye a tsakaninsu, wata kila Musharraf ne ya gaya mishi in da wasu ƴan uwansa suke zai je duba su.

Juyawa ya yi a tare suka sauƙa palon kasa, Lion yana garden zaune, Aseef da Rimsha suka wuce zuwa garden ɗin, shi kuma Areef ya wuce cikin bedroom nasa.

A ɓangaren Lion ɗin ma haka ne, da ya ce mishi zai je unguwa Rimsha zata raka shi, ya yi tunanin wajen wasu daga cikin ƴan uwan Musharraf zai je, tun da ɗan Kaduna ne Musharraf ɗin, sai bai hana shi fita ba.

Riƙo hannunta ya yi suka koma cikin gida Imran da jelly kuma basu nan sun tafi gidan Abbi, dama tare zasu fita da Rimshan, ganin tana barci a ɗakin Lion yasa ya tafi abinsa, dan shi bai ɗauka a sume take ba, ya yi zaton barci take yi.

Ɗakin dake kusa dana Areef a palon kasa ya wuce da ita, har lokaci bata ɗaura ɗankwalin nata ba, dan bata iya ba, lokacin da suka yi rayuwa da daddynta bata sanya atampha, sai blouse da sauransu, hakan yasa bata iya ba.

"Yaya Aseef ina zamu je?" Ta tambaya tana kallon uban akwatin da yake ƙoƙarin jawowa da hannu ɗaya. "Sarkin tambaya, ki bari idan muka je zaki gani, yanzu dai idan mun dawo wancan akwatin shi ne tsarabarki, sai ki zo ki ɗauka dan ni bani da karfi". Dariya ta yi, akwatin da yake hannunsa yake ja yanzu ma ai tafi tata da ya nuna girma, amma wai bashi da karfi, shima ya iya abin dariya.

Harabar gidan suka fito, da sauri wani soja ɗaya daga cikin shabiyu da Lion ya karon nan, ya nufosu ya karɓa mishi akwatin zuwa bayan motarsa, har lokacin kuma bai saki hannunta ba, yana rike da ita kamar an ce mishi zata gudun mishi ne. Yana isa wajen motar da zai fita da ita wadda Lion ya saya tun farkon zuwansa, sai ga Areef ya fito da wata kwali mai ɗan girma a hannunsa, a gidan baya na motar kusa da akwatin ya sanya mishi kwalin yana faɗin idan ya je ya gaishe mishi da ƴan uwan Musharraf, shima idan ya sami lafiya zaizo ya gansu har gida, okey kawai ya amsa mishi da shi, shi kaɗai ya barwa kansa sanin in da zai je, ya ɓoyewa ƴan uwan nasa, shi kaɗai yasan dalilin ɓoyewar tasa.

Gida gaba yasa Rimsha shi ma ya shiga mazaunin driver, Mark ya yi ƙoƙarin cewa zai raka shi, ya tuƙa su, amma yaki yarda, da su Areef suka tambaye shi yasan wajen ne, sai ya ce e ya sani shi dai su kyale shi, kada su sake tambayar shi ai shi ba yaro bane, haka suka kyale shi dan tun da Lion bai saka baki ba to sun san komai normal ne.

A hankali ya ja motar suka bar gidan, ita dai Rimsha ta zuba idanu tana ganin ikon Allah, sai tafiya yake yi yana kallon wayarsa kamar ya san hanya, da alama kuma ya kunna goggle map ne.

Sai da suka yi tafiya mai ɗan nisa lafin su kai kofar gidansu Akila, da mamaki ta juyo tana kallon shi, wai a ina kuma yasan gidan su Akila?. Shiru dai bata ce mishi komai ba, dan tana tunanin daddynta ne ya ce yazo ya gaishesu tun da Abban Imran yayan daddy ɗin ne. Shi ma bai yi magana ba sai ɗayar wayarsa da ya ɗauko ya kira number Akila ɗin, bugu ɗaya ta ɗauka.

"Hello My Heartbeat". Ya faɗa yana kallon anguwar ta cikin black glass ɗinsa. Shagwaɓe murya tayi tamkar zata yi kuka ta ce "Wai Heartbeat har yanzu baka iso bane? Nifa wlh na gaji". Ta kai karshen maganar idanunta sun ciko tap da kwallah, tana tsaye a kusa da gadonta, ta ci kwalliya sosai da sosai tamkar ba ita ba, atampha ta sanya ɗinkin riga da skit, abin kuma kamar haɗin baki, sak irin kayan jikin Rimsha, da yake tare Imran ya yi musu ɗinkin, ta yi kyau fiye da tunanin mai tunani, kun santa dama da iya tsara make up ba'a magana, sai dai bata yi make up irin na hauka da zai mai da ita kamar aljana ko bebin roba ba, mai kyau ta yi, tana ta tashin ni'imantaccen kamshi.

"Sarkin rigima, ni kada ki yi mini kuka, kada ki ɓata mani kwalliya, yanzu dai abin hawa nake nema, nan da 1 hour zan iso". Cikin sauri ta ce "No ni ka gaya mani a in da kake, zan sanya driver ya ɗauko ka kawai". "Ina bakin gate ɗin gidanku". Ya bata amsa a takaice. Wani irin tsalle ta yi ta dire a tsakiyar gadonta, yau zata ga zaɓin zuciyarta, wayyo Allah daɗi kasheta, zata gan shi ido da ido, tunani ta fara yi ya zasu yi ido huɗu da shi, anya kuwa zata iya? Amma dole ta je su ga juna ko dan taga ya zai yi da ya rinƙa nuna mata bai gane ta ba jiya har da cewa baya jin Hausa, abin da bata sani ba shi ne, yes Areef baya jin hausa kamar yadda ya gaya mata, maganar da ta yi a garden ko baka jin yare zaka fahimci me take nufi tun da a kan hakan suke maganar, bare kuma shi da yake babban jami'i, haka shi ma Aseef ɗin bana jin Hausar, akwai dai wani abu, amma basu jin Hausa, kuma abin ne ma ya haɗe mata ya birkita mata kwakwalwa ta yadda ta ɗauka yes Areef ɗin ne.

Mayafinta ta ɗauka ta nufo waje, a palo ta sami Ammie, ba ɓoye ɓoye ta gaya wa Ammie in da zata je wajen saurayinta, da farko Ammie ta hanata fita, daga karshe kuma da ta ga ƴar tata ta damu sai ta ce to ta je kada ta jima, sai murna take yi ta fito waje.

Tun da mai gadi ya ɓuɗe mata gate ta fito ya tsareta da idanu ta cikin glass, bata kai ga karisowa wajen motarsu ba, ya buɗe kofar motar ya fito, a zuciyarta ta ambaci tabbas shi ne, da yake ya sanya bakin glass bata ga kalar kwayar idanunsa daban dana Areef ba, bata saba ganinsu a tare ba, ba zata iya banbance su lokaci guda haka ba, kuma jini ba wasa ba, sannan kuma TRIPLETS ai ba karya ba, dole akwai wannan kama da idan ba a tare ka gansu ba, ba zaka iya banbanta su ba, amma fa ta ruɗewa kyau iya kyau, ta birkice, kuma tabbas a Areef ta ɗauke shi, shi kuma Aseef ne, cakwakiya kenan, ita dai Rimsha idanu kawai take binsu da shi, abin ya ɗaure mata kai, to wai shin wanene mason Akilar a cikinsu? Alamu dai sun nuna ba Areef bane, kamar yadda ya nuna mata da farko bai ganeta ba, bai da alaƙa da da ita, to hakan ne, yana da gaskiya.

TUN FARKO YA KAMATA KU ƊAUKI HASKEN WAYE MASOYIN AKILA A CIKINSU, WAYE TRIPLETS SUKE CEWA HEARTBEAT ƊIN SU❓ WAYE AUTANSU❓ IDAN BAKU MANTA BA YANA YAWAN CE MATA HEARTBEAT+HEARTBEAT, FATAN KUN GANE❓ SAURA KUMA ITA MA AKILAR TA GANE

Da fara'a ta kariso wajensa, da yake polo t-shirt ya sanya sai bata banbance yanayin jikinsu ba, cikin harshen Hausa ta ce mishi "Sannu da zuwa sarkin basaja, yanzu ma zaka ce mini baka gane ni ba ko?" Ta yi Maganar cikin zolaya.

Cikin harshen turanci ya ce mata "Kiyi magana da English ni bana jin Hausa". Babbar magana, to fa, ya tabbata basa jin hausa, amma ya akayi yake magana da ita a waya da Hausa,? To ko dai ba shi bane? Anya kuwa, kaina ya kulle sai Allah ya kaimu Monday da rai da lafiya dan jin ya wannan cakwakiya take, baya jin hausa kuma?🤔

Wayyo heartbeat+ Heartbeat, Auta+ Auta, Shagwaɓa+ Shagwaɓa, Kuka+ Kuka, Iya soyayya+ Iya soyayya, Tsarkakkan zuciya + Tsarkakkan zuciya. Ya kuke ganin Abin❓ Akwai cakwakiya a TRIPLETS sosai gaskiya. Masu cewa TRIPLETS ya zo ƙarshe to ku gyara zama, da sauran rina a gaba, wlh yanzu wasan zai fara, akwai tambayoyi da dama da idan na yi musu sai ku rantse da Allah yanzu ma zamu fara littafin nan, amma dai ba sai na yi muku ba, mu haɗu Monday kawai.

Ina barar addu'arku serious bani da lafiya, jikina yaki daɗi, kawai daurewa nake yi.

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

E21-22

Cikin harshen turanci ya ce mata "Kiyi magana da English ni bana jin Hausa".

Babbar magana, to fa, ya tabbata basa jin hausa, amma ya akayi yake magana da ita a waya da Hausa,? To ko dai ba shi bane? Anya kuwa, kaina ya kulle, baya jin hausa kuma?🤔

Da mamaki ta zaro idanu tana kallon shi, baya jin Hausa kuma? Ta maimaita a ranta.

"Why are you surprised after I told you I'm not understanding hausa?". Ya yi maganar yana tsareta sosai da idanunsa, da yake a cikin bakar glass ne, sai bata fahimci yana ganinta ɗin ba.

"How am I sure that you are not understanding after all we are chatting with hausa?". Wayarsa ya ciro ba tare da ya yi magana ba, numberta ya fara kira, ɗagowa tayi ta kalle shi, alama ya yi mata da hannu a kan ta ɗauki kiran.

Jim ta ɗan yi kafin ta ɗauki kiran, kara wayar a kunnensa ya yi, cikin harshen turanci ya ce mata "Hello my heartbeat good afternoon". Abin mamaki ita kuma sai ta ji maganar nasa da Hausa ya zo mata wayar tata, domin ta gasgata maganar abin da take ji, sai ta ce mishi cikin harshen Hausa "My heartbeat ina kewarka sosai". A cikin wayarsa ta ji muryarta na magana da English, babbar magana to me hakan yake nufi?.

A sukwane ta cire wayar daka kunnenta tana bin screen ɗin da kallo, shi kuma kallon rikitatciyar face nata kawai yake yi, da dai yaga bata da niyar magana ta shiga ruɗu sosai, sai ya ɗan matso kusa da ita, cikin shagwaɓa da harshen turanci ya fara magana "Sarkin shiga ruɗu ba, to ke yanzu a wannan ɗan abin me na shiga ruɗu fisabillilahi?". Ɗago idanuwanta ta yi tare da sauƙesu a kansa, "My heartbeat dole zan shiga ruɗu, taya hakan ta faru please,? How comes ni zanyi magana da Hausa kai kuma zaka ji da English, kuma ga shi murya ta ce da komai, sak yadda nayi magana, amma kuma ba da yaren da nayi ba yaje maka".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Na sha wahala sosai kafin na iya canzawa number ki language, sai da naje company musamman a ka buga mini wayar nan, lokacin da na je sayawa uncle Musharraf waya, a lokacin nasa aka buka mini ita, na kuma sanya a saka mata wannan tsari, ina sonki, kuma bana son ki san ni waye, ina sone in yi miki magana da yarenki dan hankalinki ya fi kwanciya da ni, dan ki karɓeni hannu bibbiyu, nasan idan na kiraki na fara magana da yarena, ba zaki wani ɗaukeni da muhimmanci ba, hasalima cemin zaki yi wrong number ne, saboda keɗin mai daraja yarenki ne, kuma hakan ya kamata kowani ɗan adam ya kasance, ya zama mai daraja yaren iyaye da kakanninsa, kada ya zama mai aron yare, sai dai a ari tasa yaren, kada ya yarda shi ya ari na wasu, wannan dalili yasa na sanya aka saka mini wannan tsari a wayata, dan koba komai idan kika ji nayi magana da Hausa, tabbas zaki saurareni, ko da kuwa ba zaki so ni ba, albarkacin wannan yare naki da nayi zaki bani dama, kuma nayi nasara, albarkacin magana da Hausar tasa kin bani dama, kin kula har na shiga zuciyarki, amma ina mai baki hakuri a kan hakan, nasan ban kyauta ba, yanzu dai kin ji, wayata ke canza maganar da na yi daga English ya baki da Hausa, shiyasa Hausar take fito miki a kema na fiki iyawa ai, dan ba mutun yake yi ba, computer yake yi". Ya kai karshen maganar cikin zolaya yana ɗaga mata gera ɗaya.

Ɗaure fuska ta yi tamkar ba ita ce mai murmushi yanzun nan ba, a kule ta ce "A ina ka san ni? Waye ya baka number ta?". Zuba mata idanu ya yi na ƴan mintoci kafin ya ɗan gyara tsayuwarsa cike da kulawa ya fara magana.

"Haba My heartbeat why sudden changed on your face, from smile to mood? Don't you know that i really like your smile? Please put smile on your face, so that I can get peace of mind". Kin kula shi ta yi, sai ma juyawa da ta yi da nufin ta koma cikin gida, ita a dole ta yi fushi da shi.

Cikin sauri ya riƙo hannunta, gabaɗayansu sai da suka ji wani shock, abin ku da zuciyoyin masoya, ya riƙe hannun Rimsha bai ji komai ba, dan ba ita ce ainahin wadda zuciyarsa ke marari ba, ita ma tana riƙe hannayen ƴan uwanta, bata jin komai sai na shi yau, har wani irin yarr suka ji a jikinsu lokaci guda.

"Please My heartbeat am so so sorry, okey don't change your face again, I will amsa you like this". Kasa kasa ta ce ya sakar mata hannu, kara marairace murya ya yi tamkar zai yi kuka, a shagwaɓa ya ce "Okey zan saki, amma please promise me that you can't go anywhere without my parmition?" Jinjina mishi kai ta yi alamar ta yi alkawarin ba zata tafi ba.

Sakin hannun nata ya yi tare da cigaba da magana "Before na fara kiranki a waya i have had some of your pictures that your brother sent to me last, ɗin kenan, so first time of seeing your pictures i fall in love with you, i bought this my phone second day of seeing your pictures, 3 day lokacin kuna gidan uncle naku, you are together with your sisters, uncles and your brothers, prof called me on video, wen I saw you, sai na ji i can't control my self or stop my self izuwa ga kiranki, already lokacin an haɗa mini wayar, Prof bai katse video call ɗin ba, ina kallonki na tura miki massage na farko a tsakanina dake, ina ganin action naki time ɗin, to kin ji yadda abin ya fara, please don't be angry with me, kin ji my heartbeat, my pleasure part 4".

"Part 4 kuma?" Ta maimaita, jinjina mata kai ya yi alamar yah part 4. "Why part 4? Who is the part 1, 2 and the 3?" Murmushi ya saki wadda ta kara bayyanar da tsantsar kyan da Allah ya ba shi, Allah ya yi halitta a kan TRIPLETS.

Ba ƙaramin rikitata murmushinsa ya yi ba, dama tun ɗazun sai faman satar kallon shi take yi, ya haɗu ta ko'ina, ai baza ma ta iya kwatanta shi da kowa a cikin zuciyarta ba, ba zata iya fushi da shi ba, yanzu tsantsar kaunarsa ma karuwa sosai ta yi a cikin zuciyarta, sai addu'ar Allah ya mallaka mata shi take yi.

"My TRIPLETS the are part 1 of my pleasures, and then your brother, prof part 2, my uncle Hossain part 3, then you part 4, then rest". Da mamaki cikin zola ta ce "Yanzu ko kunyata baka ji ba a gaba zaka ce nice part 4". Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "Yes My heartbeat, do you want me to lied to you ne? Ni bana yiwa wanda nake so karya, kai not only wanda nake so, everybody bana yi wa kowa karya, yanzu idan nace kece farincikina sama da Triplets na zaki yarda?". Girgiza Mishi kai ta yi alamar a'a. "To kingani, ba amfanin na gaya miki maganar da nasan ba zaki yarda da shi ba, wadda sai dai ki amsa mini dan jin daɗi na kawai, is better ka gayawa mutun gaskiya ko da zai ji ba daɗi, daga baya zai gane gaskiya na gaya Mishi".

Sosai ta karajin kaunarsa ya ninku a cikin zuciyarta. "Heartbeat what of Rimsha? Last time you told me tha she is your sister, and then you didn't mention her a cikin pleasures naka, why?". Ɗan juyawa ya yi ya kalli cikin motar tasa, da yake bakin glass ne, baka iya ganin mutumin da yake daga ta ciki, sai shi na ciki ne zai iya ganinka.

"My heartbeat idan nace my TRIPLETS i mean with her insert, Rimsha ita ce cikon TRIPLETS, In Sha Allah matar Saif ɗin mu ce, kinga kuma idan babu Saif to babu TRIPLETS, idan akwai Saif to akwai Rimsha kuma akwai Triplets, fatan kin gane?"

Jinjina mishi kai ta yi almar yes ta gane, kuma ba ƙaramin daɗin maganarsa ta ji ba, gaskiya Rimsha ta sami gurbi mai shegen tsada a zuciyar Areef da Aseef, wannan gurbi da ta samu kuma, zamu iya cewa tafi daddynsu samun matsayi, tashin sense.

Ita dai Rimsha ta zubawa satautar Allah idanu tana kallonsu, har barci ya fara ɗaukarta baiwar Allah.

"Heartbeat amma ya akayi kake iya controlling na wayata ko da yaushe, and then komai na yi kana gani". Shagwaɓe murya ya yi tamkar zai yi mata kuka. "Ke Heartbeat kin cika tambaya sosai, ni ba ɗaya daga cikin Triplets bane? Sakawa na yi a datsa mini camerar wayarki, a kayi yi mini connecting da laptop na, Tyrone babban yaron Lion ne ya yi wannan aiki, kuma na gaya mishi kada ya gayawa kowa, akwai sirri a tsakanin mu, shiyasa duk in da zaki je matikar kina tare da wayarki to sai na ga abin da kike yi, sai dai idan camerar wayar taki bata zauna saitin in da zan ganki ba, amma fa wani lokaci kawai ina cankar abin ne da kike yi ne da kai, dan wani lokaci a saman bedside drawer kike ajiye wayar taki, kuma ba kifa wayar kike yi ba, kina danne camerar a kasa, bana samin ganinki da kyau, sai na canka kawai, batun controlling na wayar ki ma Tyrone ne ya yi wannan aikin, so please stop asking me some questions kin ji?". Ya kai karshen maganar tamkar zai yi kuka.

"Amma fa Heartbeat ka yi wasa da kwakwalwata sosai, ba dan Rimsha ba serious fushi da kai zanyi, amma Rimsha ta ceceka". Ɗan langwaɓar da kansa ya yi a shagwaɓe ya ce "Heartbeat let's enter inside the car, ni na gaji da wannan ranar, serious tun ɗazun yake damuna, na daure ne saboda ke". Ɗan kallon motar ta yi kafin ta ce "No ni a ranar nake son ka tsaya".

Cool murmushi ya sakar mata "Okey i like everything you like, let's stay here ɗin kawai, kuma da kika yi magana ma ya fi daɗi". Murmushi ta saki ita ma, har cikin zuciyarta ta ji matuƙar daɗin zancensa, ya iya magana kamar ba gobe, dama ta ce su tsaya a nan ne dan ta gwada shi, dan taga shin zai iya yi mata gardama ko a'a, to ga shi dai duk abin da take so shi yake so, soyayya ruwan zuwa.

Readers Also Read