Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 27

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 27

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 27: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 27. "Amma wannan hoton da ka turomini kana cikin…

3,244 words

"Amma wannan hoton da ka turomini kana cikin Hausa mens ɗin fa?" Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Pic ɗin Triplets na ne, ba ni bane, ni before bana son black peoples ko kaɗan, a baya mutun ɗaya daga cikin mu ne yake kula kowa har da black peoples, to hoton sa ne ba nawa ba, ni da Lion bamu so, amma yanzu da muka musulta, muna son kowa, mun gane kowa ɗan adam ne mai ƴanci". Shiru ta yi tana tunani, tana son gane banbancinsa da hoton, ta dage dole dole sai ta gano banbancin dake tsakanin TRIPLETS, ga shi kuma iya kalar kwayar idanun Areef kawai ta sani, bata san na Lion ido da ido ba, bata san na shi Aseef ɗin ba.

"My heartbeat you look so gorgeous more than everyday". Ya yi maganar kasa kasa cikin sigar soyayya da kauna, yana ji tamkar idan bai mai da ita cikin zuciyarsa ba, ba zai taɓa samin kwanciyar hankali ba.

Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "My heartbeat am surprised lokacin da na ganka, ba zan ɓoye maka ba har yanzu na kasa yarda da cewa wai kamar kai ne kake so na, tun da na ganka, na tabbatar kai ne, daga nan na shiga ruɗu akan soyayyar da kake ikirarin kana yi mini". Tana magana tana wasa da yatsun hannunta.

Hannun nata ya riƙo cikin nasa, a hankali yake murza ƴan yatsun nata, har cikin tsakiyar kansa yake jin wani irin yanayi mara misaltuwa, a ɓangarenta itama hakan ne, wani irin baƙon yanayi take ji.

"Me yasa kika ce haka my heartbeat?" Yana magana yana kallon face nata sosai, nisawa ta yi kafin ta fara magana a nitse, "Naga ko rabin ka ban yi a kyau ba, kuma gaka kai Bature ne, wadda ya fito cikin kyawawan fararen turawan, wadda farinsu babu ko miss, idan muka tashi kwatance kyau a nan cewa muke yi kyakkyawa kamar baturiya, saboda kyanku yasa kuke bamu sha'awa, amma duk da haka ka tsallakesu kazo har Nigeria, Nigeria ma Kaduna, ka ce ni kake so, ni fa a haka fara ce a gidan mu, ko in ce a danginmu, amma yanzu kallah da na zo kusa da kai, na dawo baka, hasken ka ya dishashe nawa, wannan dalilin yasa naji zuciyata ta karaya, na ji anya kuwa ba mafarki nake yi ba? Ko kuma wasa kake yi mini ba, sannan bugu da kari, ga kuɗi mulki kai komai ma kun haɗa, dan Allah Heartbeat ka gaya mini gaskiyar me kake so a waje na? Ni nasan ba soyayya bace ta kawoka waje na, zuciyata ta tsorata wlh". Ta kai karshen maganar hawaye na zuba daga idanunta.

Shiru ya ɗan yi kafin ya jingina da jikin motar tare da lumshe dara daran brawn eyes nasa, hakan yasa dogayen eyelashes nasa suka kara bayyana, zuba mishi idanu ta yi tana hawaye tana jiran amsa daga gare shi, kun sani na sani har ga Allah tana bala'in kaunar shi kafin ta san waye shi, ganin shi ido da ido yasa ta ji zuciyarta ta karaya, a nata ganin ya fi karfinta, sai dai idan wani abin kawai yake so da ita, dama jira take ta tabbatar da shi ɗin ne, to yanzu ya kawo mata kansa, ta tabbatar da yes shi ne, a zahiri ma yafi kyau fiye da hoton, duk da hoton ma tun yana ɗan 20 years ne, ta ruɗe da kyansa sosai, kuɗi, kwarjini, shiyasa take ganin kamar ba son gaskiya yake yi mata ba.

Almost 10 mins suna a haka, a hankali ya duƙo da kansa yana kallonta, ita ma shi take kallo, ya rasa da wani baki zai yi mata magana, mai da kallonsa izuwa kasa ya yi, da yake unguwa ce ta manyan mutane, titi har cikin unguwa, ga titin fes babu datti, hakan yasa ya zube gwiwowinsa a kasa a gabanta, duk wanda ya san turawa yasan yin hakan ɗabi'arsu ce, su zube gwiwowinsu a kasa dan bayyanar da soyayyansu.

A razane ta koma baya ganin ya zube gwiwowinsa a kasa a gabanta, duk da tasan ɗabi'arsu ce yin hakan, ba wani abu bane, amma sam bata yi tsammanin haka daga gare shi ba, dan a nata tunanin bata kai wannan matsayin ba, bata kai ya zube mata gwiwowinsa a kasa ba, duba da irin tarin dukiya da suke da shi, ita kanta Rimsha da ta san halinsu ta girgiza ganin ya zube gwiwowinsa a kasa, ta razana ainun, bata taɓa tsammanin hakan daga gare shi ba, ko a mafarki, bata san lokacin da idanunta suka washe ba, gabaɗaya barcin cikinsu ya gudu, zaro idanun nata ta yi tare da matsowa jikin glass ɗin motar sosai tana kallon wanan abin al'ajabin, yau ga ɗaya daga cikin TRIPLETS na THE GENERAL OF THE ARMY ya zube a kasa a gaban mace, ina ma wannan abin a Washington DC ta faru, da gabaɗaya gari ta ɗauka izuwa yanzu.

"My Heartbeat trust me, from the button of my heart nake sonki, serious babu wasa, ni bana son turawa, ke Allah ya zaɓa mini, kin san cewa ko TRIPLETS na ban gaya musu ina sonki ba, dama nace sai nazo Naija zan gaya musu, amma zumuɗin in zo in ganki ido da ido ya hanani tsayawa na basu lokaci na, muyi hira har na gaya musu, uncle Hosain kaɗai na gayawa, kuma shi ne ya kara mini confidence a kanki, he told me that ke ƴarsa ce, ƴar yayansa, kina da farar zuciya, zaki iya tambayarsa, da gaske nake sonki, yasan komai, please stop doubting a kai'na, kiyi hakuri ki yarda dani, ni bana karya, duk abin da nayi miki a baya na gaya miki dalilin yinsa, kuma idan da bana sonki ba zan ɓata lokaci na wajen zuwa in da kike ba, saboda ke na haɗa Exams uku a lokacin guda nayi, kuma ba rana ɗaya za'ayi su ba, ni ne nace dole a bani nayi a rana ɗaya, dan nayi miki alkawarin zan kawo miki kai'na yau, bana son saɓa miki alkawarin dana ɗauka miki, Shiyasa nayi hakan, ko kaɗan banji daɗi ba da zuciyarki ta fara tunanin ko ba da gaske nake sonki ba, please ki gaya mini wasa kike yi kinji ko?".

Ina ta kasa magana, har lokacin ganin abin take yi tamkar a mafarki, ta kasa yarda da abin da take gani, ji take yi tamkar ta gudu ta koma cikin gida, dan ta tsorata sosai.

Ganin bata yi magana bane yasa ya ɗan rarrafo da gwiwowinsa a kasa, ya matso kusa da ita, hannayenta ya riƙo cikin nasa, a wannan karon a shagwaɓa ya yi magana, "Please My heartbeat talk to me now, zuciyata tana bugawa da sauri sauri, ji nake yi like zan mutu, i need your amsa now please".

A hankali ita ma ta zube gwiwowinta kasa a gabansa, cikin sanyin murya ta fara magana "Already you knew that i really love you, wadda zata soka ba tare da sanin waye kai ba, ita ce masoyiya ta gaskiya, sanin waye kai a yanzu ne ya girgiza ni, ya sa naji tamkar matsayina bai kai a soni ɗin ba, amma ka dai'na tunanin zan dai'na sonka, never wlh, because kai ne first love ɗina".

Rimsha dai ta mai da su Tv, sai kallonsu take yi gwanin burgewa, da yake anguwa manya ne, babu mutane, kowa yana harkan gabansa, sai ɗai ɗai kun motoci dake wucewa lokaci zuwa lokaci.

"Yanzu you trust me ko?" Jinjina mishi kai ta yi alamar e, saboda tsabar daɗi bai san time da ya matsa hannayenta dake cikin nashi ba, sai da ya ji ta ambaci wash ya farga tare da ɗan sassauta riƙon da ya yi musu. Kada ku manta fa, ita Akila a ɗaukarta da Areef take magana ba Aseef ba, bata ma san Aseef ɗin ba, ya kenan idan ta san ba wanda take tunani bane kuma? Mu dai je zuwa, Areef Rimsha ta yaba mata kyawawan halayensa ba Aseef ba.

Miƙewa tsaye ta yi tare da jan jannunsa dake cikin nata sama, alamar ya miƙe shi ma, ba musu ya miƙe tare da ɗan duƙawa yana kakkaɓe mata ɗan kuran da ya hau saman skit nata wajen da ta duƙa, ita dai har yanzu mamaki take yi, bata san cewa yes yadda take ganin turawa a Tv wajen kula da soyayyansu da abin da suke so hakan suke a zahiri ba, ta ɗauka a iya Tv ne, bata san a zahiri ma hakan suke ba, in dai suna son abu, to suna bashi tsantsan kula da iya iyawarsu.

Sai bayan ya kammala kakkaɓe mata ya miƙe ne ita ma ta ɗan duka ta goge mishi wajen gwiwowinsa daya zube su kasa, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, har da sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya ya yi lokacin da ta fara kakkaɓe mishi.

Bayan ta Kammala ta miƙe tsaye suna fuskantar juna, ganin ta kafe shi da dara daran nan nata na gado ne yasa ya ɗan kyasta mata yatsunsa guda biyu a saman face nata, ɗan runtse idanun nata ta yi tana murmushi.

"Kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa". Ya faɗa yana murmushi, ita dai har yanzu bata yarda ba, idan ya ce ita kyakkywace, dan tana ganin ai daga cikin ƴan uwansa Turawa ya fito, a wawtarta da shirmenta, tana ganin daga kan turawa kyau ya kare, bata san cewa a ko'ina akwai kyawawan gaske ba, kamar dai ita ɗin, sai a tara turawa 50 ba'a a sami mai kyanta a cikinsu ba, hasken fatar kawai zasu fita da shi, kyau kam iya kyau Allah ya zubawa jinin Dr Salman da barrister Naurat, Ba fulatani da Baturiya, ya kuke tunanin haɗin zai fita, ai kunga suma madaran kyau ne a wajen.

Turo ɗan bakin nan nata kamar biro ta yi, cikin shagwaɓa ta ce "Ni Heartbeat ka dai'na ce mini kyakkyawan nan, dan nasan kawai kana faɗa ne dan ka ji daɗin bakin ka". Shima turo mata ɗan bakin nasa ya yi, tare da shagwaɓe murya "No serious nake gaya miki, you are so very gorgeous more than your expectations wlh". Shiru kawai ta yi ba dan ta yarda ba.

Sake kyasta mata yatsun sa guda biyu ya yi a fuska "Ga fa goribar ki a mota, na sanya Areef ya nemo mini tun kafin nazo, shi kuma ya sanya Prof ya nemo, a takaice dai ga shi nan na kawo miki, amma me ake yi da shi?". Jim ta ɗan yi tana maimaita sunan Areef, idan bata manta ba, idan kuma ƙwaƙwalwarta ya bata daidai sunan Areef Rimsha ta kira wadda ta ambata a matsayin masoyin ɓoye, to amma me yasa yanzu kuma ya ce ya sanya Areef ya memo mishi goriba, to shi kuma waye? Ko dai su dukka sunansu Areef Areef ne? Abin ya ɗan ɗaure mata kai.

Shi kuwa bai lura da yanayin da ta shiga na tunani ba, sai hira yake yi mata. "My heartbeat dan Allah yanzu zaka iya gaya mini sunanka?" Ta tambaya tana mai da kallonta kasa. Kai tsaye ya ce mata Aseef, maimaita sunan ta yi, sai ta ji da Aseef da Areef ai ba banbanci, hakan yana nufin ita ce bata ji sunan da Rimsha ta kira da kyau bane koyaya ne? Ta sake shiga ruɗu, sunan sunzo kusan iri ɗaya, wai me yake faruwa ne? Ta kasa gane komai.

To fa Akila ta kasa gane komai, shawara kawai ki bisu a duk yadda suka zo miki, idan ma kin gansu dukkansu biyu, duk sunan da yazo bakinki, in ma Aseef or Areef duk maka musu kawai, ai dole su amsa tun da suka rikita mini ƙwaƙwalwa, Allah sarki Baiwar Allah sai ma kin gansu su biyun da black glass, a nan ne zaki yi ainahin rikicewa, a dai Nigeria idan ba Rimsha da Imran ba, ba mai iya banbanta su.......🤣 Ita ma Rimsha Allah ne kaɗai yasan baiwar dake gareta, yasa take iya banbantasu, shi kuma Imran ya sansu tun ba'a kai haka ba.

"Heartbeat Ammie ta ce kada na jima, zan koma gida ba dan ina son rabuwa da kai ba, sai dan kada na tsallake maganar mahaifiyata, ka kula mini da kanka, zamu yi waya ko? Yanzu ai zaka dai'na ɓoye mini number ko?". Jim ya ɗan yi kafin ya wuce ya buɗe bayan motarsa ya fito mata da kwalin goribarta da kuma kawatin da ya yi mata tsaraba, already Rimsha ta jima da yin barci abinta, kwata kwata Akila bata san cewa tare yazo da Rimsha ba, shi kuma hira ta yi daɗi ya manta ya gayawa Akila ɗin tare suke da Rimshar.

"Heartbeat ya kamata ka je ka gaida Ammie fa idan ka sake zuwa". Yana jawo akwatin zuwa gabanta ya ce "Okey zan je idan na sake zuwa, yanzu dai ga kayanki, zaki iya ɗauka ne ko dai na kai miki ciki?".

Kada ku manta duk maganar da suke yi cikin harshen turanci suke yinsa, sannan karin wani haske, kada ku manta da Naurat da Dr Salman da farko a kasar Russia suke zaune, a can a ka haifi su Abba, to suma basu jin hausa sai da suka dawo Nigeria, hakan yasa su Jehan babu hausa a bakinsu sosai, dan iyayen nasu ma basu cika yin hausar ba, to suma su Akila turanci ya fi zama a bakinsu sama da Hausa, amma kuma sunfi kaunar yaren Hausa sama da turancin, shiyasa suke magana da Hausar idan suka haɗu da su Aafia, dan sun ce Hausa tafi musu ko wace yare a duniya, a takaice dai family'n Dr Salman duk gayyan ƴan yin turanci ne, na yi muku bayani ne dan kada ku ce to a ina suke jin American English da suke magana da TRIPLETS, to suma tushensu dai English ɗin turawan ne, shi suka iya, fatan kun gane?.

Da sauri ta buɗe kwalin goribar dan ta tabbatar da gaskiya, tabbas kuwa goriba ce da aduwa very fresh a ciki, gwanin ban sha'awa, ɗagowa ta yi tana kallon shi, while shima ita yake kallo.

"Me ake yi da su My heartbeat?" Ya tambaya yana zura hannu a cikin aljihun wandonsa. "Ci ake yi". Waro dara daran brawn eyes nasa ya yi yana kallon goribar, maimaita kalmar ci ya yi a filli, jinjina mishi kai ta yi tana mai tabbatar mishi da ci kuwa.

Hannu ya miƙe mata, a kan ta bashi guda ɗaya, bari ya ci ya ji, shi da abincin Nigeria mai shegen daɗi da Musharraf yake girkawa a Washington DC ma, ya kasa ci bare kuma goriba. Da farko kin bashi ta yi, sai da ya fara zuba mata shagwaɓa kamar zai yi kuka, sannan ta ɗauko goriba ɗaya aduwa ɗaya ta miƙa mishi, karɓa ya yi tare da kaiwa bakinsa da nufin ya gutsiri goribar, dan a wanke take kuma tana cikin leda kafin a sanyata cikin kwalin, sannan a cikin fridge Areef ya sanyata, a tunaninsa fruits ne kamar irinsu Apple, shiyasa ya sanya Mark ya wanketa tas, aka zuba a leda sannan aka sanya a cikin fridge ɗin, wai dan karta ruɓe kafin Aseef ɗin yazo.

(Wayyo cikina, goruba yaga gata, har da fridge 🤣 Wayyo rashin sani yafi dare duhu🤣🥱)

A tunaninsa laushi take da shi kamar apple, sai da ya kai bakinsa sai ya ji abu kamar dutse, da sauri ya fitar yana furta subhanallah, ya tsuke ɗan bakin nan nasa, tare da haɗa geran sama da ta katsa, tsabar dariyar mugunta Akila bata san lokaci da ta yi baya tana ƙoƙarin faɗuwa ba.

Bata kai ga faɗuwa ba ya yi maza ya riƙo hannunta ɗaya, har lokacin yana tsuke da ɗan bakin nan, ya je ya gabtari dutse ta kusa cire mishi hakwara a cewarsa, gata da shegen bauri kamar me, bai yi Sa'a ba, ya sami mai bauri a maimaikon zaki, tufarwa ya fara yi yana goge bakinsa da hannunsa, har lokacin sai dariya take yi mishi.

A shagwaɓe ya ce "Heartbeat stop laughing for me now". Yadda ya yi maganar ma, dariya ya kara bata, har da sanya hannu ta dafe cikinta saboda dariyar.

Turo ɗan bakin ya yi yana ƙoƙarin saka mata kukan shagwaɓa, cikin sauri ta tsayar da dariyar tana faɗin "Am so so sorryyyyyyyyyy my heartbeat". Turo ɗan bakin ya karayi sosai, bai ce da ita komai ba, sai aikin zubar da yawu yake yi, tana son ta yi dariya, tana tsoron rigimarsa kuma, haka ta danne ta yi shiru suka yi sallama, ba dan sun so rabuwa da juna ba, sai dan kada Ammie ta yi faɗa.

Har bakin gate ya ja mata trolley tsarabar da ya yi mata, ya kai mata, ita kuma ta ɗauki kwalin goribarta,. A bakin gate ɗin ma tsayuwa suka yi na ƴan mintoci da a kallah zasu kai 20 haka, kwata kwata basu son rabuwa da juna, umarni ya yi wa mai gadin a kan ya shigar mata da trolley da kuma kwalin goribar dukka cikin gida, hannayenta dukka biyu ya riƙo cikin nasa, abin ku da turawa, su yin hakan a wajensu ba wani abu bane, anyi sa'a ma da bai ce zai rungumeta ba, ita ma kuma bata hana shi riƙe hannayen nata da yake yi ba, ta biye mishi kawai, dan tana ganin ba zai wuce yin hakan ba, a iya hannu kawai zai tsaya.

Cike da kulawa da tsantsar kaunarta ya fara magana "My heartbeat zan yi kewarki, ji nake yi tamkar ba zan iya wannan rabuwa da zamu yi ba, ni gaskiya ba zan iya jimawa sosai ba, tun da nazo Kasarku kafin mu koma ayi mana aure kawai, ki gayawa daddynki, zanzo na ganshi, ya saka mini lokaci, amma kafin nan zan yi magana da Pleasures ɗina".

Kasa ta yi da kanta tana amsa mishi da okey, gabaɗaya ta koya mishi kunya, a wajenta ya koya, har yake jin kunyar TRIPLETS nasa. Daga haka ya saki hannayen nata tare da binta da idanu har ta shige cikin gida, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya juya zuwa wajen motarsa.

Lokacin da ya shigo cikin motar Rimsha sai zuba barcinta take yi kamar ba gobe, ƴar murmushi ya yi tare da shafa lallausan kyakkyawar gashin kannan nasa yana furta mata kalmar sorry kasa kasa. Cikin natsuwa ya tada motar ya nufi gida, lokacin yamma ta yi sosai, almost karfe 6.

Lokacin da suka koma gida, Imran da jelly sun dawo, Areef yana zaune a saman ɗaya daga cikin kujerun shan iska dake wajen pool na gidan, Lion yana cikin bedroom nasa, haka suma Imran da jelly ɗin, suna cikin bedroom nasu, sai iya shege kala kala jelly ke zuba mishi, bawan Allah shi kuma sai biye mata yake yi, dan ba yadda ya iya da ita.

Bayan ya yi parking na motar ne ya juyo da kallonsa a kanta, a hankali ta fara motsawa kafin ta buɗe dara daran sleeping eyes nata masu ɗauke da barci, ganin su a gida yasa ta juyo gefe dan ta ga a ina take, karaf suka yi idu huɗu, cool murmushi ya sakar mata yana furta kalmar sorry, murmushi ta mai da mishi ita ma kafin ta ce "Yaya Aseef am waiting for you ne fa, ina son ka gama magana da Aunty Akila, i wan to talk to her, amma shi ne ka dawo dani gida bamu yi magana ba ko?". Ɗan kama kunnansa ya yi yana mai kara maimaita mata kalmar sorry tare da ɗaurawa da gobe zai kaita ai kada ta damu, okey ta amsa mishi da shi kafin ta buɗe kofar motar ta fito waje.

Readers Also Read