Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 29
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 29: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 29. Kiran Imran a waya Areef ya yi, ya tambaye…
3,315 words
Kiran Imran a waya Areef ya yi, ya tambaye shi a wani location restaurant ɗin da suke sayan abincin yake, ba musu ya gaya musu, bai kuma tambayesu me zasu je yi a can ba, dan yasan ba makawa Rimsha zasu je sayawa abinci. Kunna goggle map Aseef ya yi a wayarsa tun kafin su bar gidan, Rimsha ta so zama a gidan baya na motar, amma Areef ya ce lallai ta dawo gidan gaba su zauna a tare, shi kuma Aseef ya tukasu.
Bata yi musu da shi ba, ta dawo kusa da shi ta zauna, duk abin da suke yi a kan idanun Lion suke yi, a kan idanunsa suka bar gidan, sai tsokanar Rimsha Areef yake yi, suna ta murmushi.
Kai tsaye wajen wani katafaren restaurant suka shiga, suna parking suka fito kusan a tare, nan take kallo ya dawo kansu, kun san mutanenmu idan suka ga Turawa, sai kallonsu jama'a suke yi, su kuwa kwata kwata basu son wannan kallo da jama'a suke yi musu, dama kuma kunsan kallo bashi da daɗi ko kaɗan, idan mutun yana kallonka gabaɗaya sai ka tsargu, sai ka fara tunanin ko dai wani abin da bai kamata bane a jikinka yasa suke kallonka.
Saman tsadaddun kujerun dake wajen suka zauna, nan take masu karɓar oder suka nufo wajen nasu.
"Rimsha ki basu oder abin da kike buƙata". Cewar Areef, shi dai Aseef ya yi kasa da kai yana latsa wayarsa, da alama chatting yake yi da Heartbeat nasa.
Daidai lokacin aka fara kiraye kirayen sallar mangariba, umarni Areef ya yi musu a kan su yi mata takeaway ne kawai su wuce da shi gida, mangariba ya yi, sai dai abin dariya kuma abin haushin shi ne, babu mai ko biyar a jininsu, kuma ba ta yadda zasu yi su yi wa masu restaurant ɗin transfer, ko da aka kawo musu takeaway ɗin da bill ɗinsu, kallon Aseef Areef ya yi, shi ma a lokacin ya ɗago kansa dan ya kalli ɗan uwan nasa, da wani kuɗi zasu biya to? Suka tambayi kansu da kansu a cikin zuƙatansu, ita ma Rimsha sai kallonsu take yi tana kankame da laidar takeaway ɗin nata abinta.
Su kuwa masu karɓar kuɗi suna tsaye suna jira, dan kuwa ba zasu yafe ba, ice cream da suka sanyawa Rimsha ma kawai almost 10k bare azo kan saura abubuwa ga abinci.
Dariya ne ya subcewa Rimsha lokacin da ta gane me matsalar, zuba mata idanu Areef ya yi yana kallon yadda take dariyar, ba ƙaramin burge shi ta yi ba, shi ma dai Aseef dariya abin ya bashi, wai su a dole sun zo sayan abinci, sun manta ba'a Washington DC suke ba. Babbar magana yanzu ya zasu yi? Su mayar da abincin ne ko yaya za'ayi? Ga shi ita kuma Rimsha ta kankame ledar ta abinta, jira kawai take yi su biya su tafi, har ta kotsa ta fara shan ice cream dake cikin, ga shi har da pizza ta ce a sanya mata...........
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
E23-24
Suna a wannan hali sai ga Mark ya shigo cikin wajen, fusataccen fuskar nan tasa tamkar face ɗin shanu, yana sanye da wandon jeans black color da t-shirt maroon, faffaɗar kirjin nan nasa a buɗe irin na ogan nasa, tamkar wani zaki, ya sanya bakar glass a idanunsa, ba wasa a tattare da shi ka ɗigo, ganin shi ma kawai ya isa ya razanar da duk wata halitta mai rai.
Kai tsaye in da suke ya nufo, cikin girmamawa ya gaida su tare da miƙawa masu karɓar kuɗin rafar kuɗi ƴan dubu dubu, wadda a kallah zasu kai 100k, ko basu tambaya ba sun san Lion ya aiko shi, dan idan ba Lion ba, ba wanda ya isa ya sanya Mark fita daga gidan, ya bar bakin aikinsa, dama tun da suka fita Lion ya kira Mark ya bashi kuɗi a kan ya bi bayansu da shi, dan yasan basu da ko biyar a jikinsu, kuma yasan ba ta yadda za'ayi su yi transfer, su sun mance da hakan, amma shi tsabar kauna da kuma kula da su da yake yi bai manta ba, yana ankare dasu, shiyasa ya yi musu hakan, dan kada wata matsala ta biyo baya, Areef kawai yake jiyewa, ciwon nan nasa, tun da suka fita yake jin wani iri a ransa, yadda Areef ɗin ke jijjiga jikin nan nasa, ciwon nasa na jijjika, to shi ma haka Lion ɗin yake jin wannan jijjiga a jikinsa, tamkar ciwon a jikin nasa yake ba Areef ba, ya kyalesu su fita ne dan su yi farinciki, tun da sun nuna hakan suke so, bai taɓa hanasu abin da suke so ba, sai idan ya tabbatar da in suka yi abin zasu cutu matuƙa, shi ne zai taka musu birki, ba dan yaso ba, sai dan kada su cutu.
Tun da Mark ya miƙa kuɗin, Aseef ya riƙo hannunta suka nufi waje, shima Areef miƙewa ya yi ba tare da ya kalli in da Mark ɗin yake ba, ya bi bayansu.
Motarsu suka shiga, da gudu Aseef ya ja motar dan lokacin sallah ya yi, da mugun gudu shi ma Mark ya fito ya rufa musu baya, da motar da yazo da ita. Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa gida, saboda irin uban gudun da suke shararawa, dama idan baku mance ba, Aseef ya iya guduwa da mota kamar ba gobe.
Suna yin parking ta fito ta nufi bedroom nata dan ta yi sallah, a tsakar gida suka yi karo da Lion da Imran zasu tafi masallaci, bin su Aseef da Areef ɗin suka yi, zasu je su yi alwala a can ɗin kawai.
A palon sama taci karo da jelly, ko sannu bata ce mata ba, da alama ta rako Imran ne, ta kula da shi har ya fita dan kada ya kula Rimshar.
(Kai jama'a Jelly duniya, wato har waje take rako Imran ta tsare shi dan kada ya kula Rimsha 🤣)
Bedroom nata ta nufa, binta da kallon banza jelly'n ta yi bata ce da ita komai ba. Tana shiga bedroom ɗin nata, toilet ta nufa dan yin alwala, tare da ɗaura ledar takeaway ɗinta a saman bedside drawer. Bayan ta yi ta zo ta shinfiɗa dadduma ta tada sallah abinta.
A ɓangaren gidan Akil kuwa, wasa wasa har shabiyun dare shiru ba Akil babu labarinsa, Umaisha tayi kuka ne har ta godewa Allah, sai uban haɗa zufa take yi, duk da sanyin Ac dake gudu a cikin ɗakin, ta jigata sosai, ta kuma kasa yin barci, a ɓangaren shi ma Akil ɗin ya sha bakar wahala, dan bai saba kwana ba tare da ya taɓa tula tula ba, tun ranar da ya yi aure har zuwa yau, ya kasa runtsawa, sai juyi yake yi a saman gadonsa dake bedroom nasa a gidan Abba, ya jigata sosai, kuma yaga massage ɗin Akila, ya basar ne kawai, irin shi zai daure ya yi koda sati ɗayar nan ne haka, amma ina kwana ɗaya ma ya kasa jurewa, da ya gaji da kwanciya zai miƙe zaune yana haɗa zufa, gabaɗaya ya rasa ina zai sanya ransa ya ji daɗi, daga karshe dai miƙewa ya yi tare da zura jallabiya ya ɗauki makullin motarsa ya fito palo.
Babu kowa a Palon, kai tsaye waje ya nufa, su Ammie sun jima da yin barci abinsu, motarsa ya je ya shiga ya nufi gidansa. Lokacin da ya isa gida, tana zaune a palo sai kuka take yi, kwata kwata hawayenta ya dai'na zuba daga idanunta, sai shessheƙar ne kawai zaka ji, shi zai tabbatar maka da kuka take yi, amma hawaye kam ya dai'na zuba gabaɗaya.
Tana jin tsayuwar motarsa, amma ta kasa tashi saboda wani irin jiri da take ji yana ɗebanta, hakura ta yi ta cigaba da zama a in da take har ya shigo cikin palon, da farko bedroom nasu zai wuce, jin shessheƙar kuka a palo yasa ya tsaya tare da kunna wutar palon, ya tsorata sosai ganin yadda har idanunta suka kumbura, bai yi zaton kukan da Akila ta rubuta mishi a massage take yi ya kai har hakan ba, ya yi zaton irin kukan kullun ne da ta saba yi mishi. Da sauri ya kariso in da take yana ambatar sunanta, "Wife! Wife".
Kara rushe mishi da kuka ta yi, yana zuwa ya runhumeta yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi tare da zama a gefenta, ina ai sai da ta gan shi ne ma ta ji sabon kuka ya zo mata mai karfi, yi take yi yana rarrashinta, sai da ta bashi wahala kafin ta tsagaita da kukan, ɗaukarta ya yi suka nufi toilet, ko abinci bata ci ba, dan ta kasa ci ɗin, wanka ya fara yi mata kafin ya fito ya shiryata cikin kayan barci masu kyau, sosai ya yi nadamar abin da ya aikata, bai yi zaton zata wahala har haka ba, da yanzu cikin nasu ya zube waye gari ya wayanwa to? Ya tambayi kansa da kansa, dan yasan damuwa tana ɗaya daga cikin abin da take hana ciki zama a jikin mace.
Bayan sun shirya da kansa ya rinƙa bata abinci a baki yana rarrashinta, a wannan dare dai basu suka kwanta ba sai karfe 3 na dare, sai lokacin suka gama duk abin da zasu yi, sai sauke ajiyar zuciya take yi, har lokacin sai kara rarrashinta yake yi, ba shi ya sami kwanciyar hankali ba har sai da ya ga tayi barci cikin kwanciyar hankali kwance a kirjinsa tana faman sauke ajiyar zuciya, a sannan ne ya samu natsuwa tare da yin addu'ar barci ya shafa musu ita da shi baki ɗaya. ASUBA TA GARI.
GIDAN LION💋
Bayan ta yi sallar mangariba da issha, sai ta ɗauki abincinta ta fito palo dan taci tare da Aseef, shi ne abokin yin ta dama, kuma dama kafin su rabu ya tafi masallaci ta ce mishi idan ya dawo zasu ci abinci tare, okey ya amsa mata da shi, to shi ne yanzu zata je garden su ci abincin a tare idan zai iya.
Duk da tasan babu kowa a garden ɗin, sai da ta tsara sallamarta irin ta addinin musulunci, tana sa kai zata shiga ciki, ita kuma jelly tana fitowa, karo suka yi, baya kaɗan ta yi tana ce wa Jellyn sannu, dan ita ce ta bugeta, rai a ɓace jelly ta ɗaga hannun zata mareta, dan dama haushinta take ji, kamar daga sama ta ji an riƙe hannun nata, Rimshar ta gama rintse idanunta gam tana jiran saukar mari sai ta ji shiru.
A hankali ta waro dara daran fararen sleeping eyes nata a kan jelly, da mamaki take kallonta, cikin sauri kuma ta ɗan juya gefenta ganin jelly'n na kallon hannun nata, muryarta har rawa yake yi wajen furta "Yaya Areef". Yana tsaye ya rasa wani hukunci zai yi wa Jelly yau, ji yake tamkar ya murɗe hannun nata ya karye shi gida biyu, yau sai ta ɗanɗana kuɗarta, dawowansa daga masallaci kenan ya ce bari ya zo garden ɗin, dan yasan da wuya ba zai sami Gimbiyar tasu a wajen ba, yanzu a gabaɗaya gidan bata da wani wajen zama da ya wuci wannan wajen, shiyasa ya nufo wajen kai tsaye da fara'arsa, cike da kwarin gwiwar zai same zaune tana cikin farinciki, Aseef da Imran sun wuce ciki, shi Aseef ya je ya yi wanka ya sako kayan shan iska, dan ya ce zafi ta yi yawa, shi kuma Imran wajen Jellyn ya nufa, dan bai taɓa tunanin a wannan lokacin zai sameta a garden ba, ya fi zaton tana ɗaki, dan ita sarkin kallo ce, sai ta wuni a cikin ɗaki tana kallon film a Tv dake cikin ɗakin, bata wani cika fitowa waje ba.
Sun kai almost 2 mins tsaye a wajen, ba ƙaramin razana jelly ta yi da ganin face nasa ba, tun da take da su a gidan sai dai taga wucewarsu, bata taɓa yin ido huɗu da su ba, kuma shi ma Areef dama da Rimsha kawai yake wasa da dariya har haka bayan TRIPLETS nasa da Imran, bai cika yiwa mutanen da suka zo baki magana ba, idan suka yi mishi magana, yana amsawa saɓanin Lion da ko kallon in da suke ma bai ishe shi ba, a takaice dai bata taɓa yin gaba da gaba da ɗaya daga cikinsu ba, sai dai bayansu take gani.
Nan take ta sha jinin jikinta, tayi narai narai da ido, dan dama duk rashin kunyar mai rashin kunya sai dai idan bai yi ido huɗu da fusatattun fuskokin zakunan jikin William jacop ba, ga fuskokin nasu mai cike tap da bala'in kwarjini mai haukata mutane kamar me, ganin ya yi shiru bai saki hannun nata ba, bai kuma yi mata hukuncin da yake da burin ya yi mata ba, yana tunanin ya ɗaga mata kafa saboda auren dake kanta ne ko kuma ya karyeta kawai?.
A hankali cikin sanyin murya Rimsha ta sake ambatar sunansa "Yaya Areef". Dawo da dara daran ash eyes nasa kanta ya yi, tare da sakin hannun jelly'n ya wuce zuwa cikin garden ɗin, da gudu jelly ta watsa zuwa cikin gida, ita kuma Rimsha bayansa ta bi zuwa cikin garden ɗin.
A ɗan gefensa ta zauna tana mai ɗaga mishi gaisuwa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, bai amsa gaisuwar tata ba sai ya ce "Daga yau duk wanda ya yi kuskuren marinki, in ma a gidan nan ko a waje, ki rama, idan kika kuskura kika bari wata ta mare ki baki rama ba, to gaskiya zan yi miki hukunci, ko Mark ne ya mare ki, ki rama ki ce ya zo ya rama a kai'na, kina ji na ko?" Gyaɗa mishi kai ta yi, sai faman sauke numfashi yake yi tare da nisawa, tamkar shi aka yi niyar mara, gabaɗaya ya ji babu daɗi, yaso ɓalle hannun Jelly wlh, bai so ta yi wannan babban kuskure na yunkurin marin Rimsha ya barta ba, yau dai taci albarkacin igiyoyi ukun dake kanta, ba dan haka ba, da yanzu haka tana gadon asibiti.
Suna tsaka da hitarsu sai da Aseef, sanye yake da gajeren wando jeans baki zuwa gwiwarsa, sai riga mai ƙaramin hannu sky blue, kusa da ita ya zo ya zauna sai tashin kamshi yake yi, kamar ko da yaushe, sai aikin latsan waya yake yi, yana chatting da bugun zuciyarsa.
Shammatarsa Areef ya yi ya kwace wayar yana faɗin "Tun da kazo kafi bawa wayarnan mahimmanci sama da ni, wai me kake yi ne a cikinta ne?". Dawo da kallonsa kan Rimsha ya yi yana faɗin "To ka duba mana ka gani, ba wani abu bane hira nake da matata faricniki na, our Queen ina abincin mu?". Ya yi maganar yana ɗaga mata wannan kyakkyawar cikakken gerar tasa, gata baka kirin cike da gashi.
Zata yi magana kenan Areef ya katse ta da cewa "What? Me nake ganin nan, dan Allah da gaske ne abin da nake gani Aseef". Rimsha ce ta amsa mishi da "E mana yaya Areef da gaske ne, ai ni naga komai" tana magana tana dariya.
Ɗan leƙo face nata ya yi kafin ya ce "Wow our Queen kin ga ɗan bakin nan naki kamar baya magana ko? Ashe dai kin iya sa ido, wato kallona kike yi lokacin da nake hira da Heartbeat ko? Amma shi ne da na dawo cikin mota kika yi kamar mai barci ko? To Allah ya kamaki yanzu, har da wani cemin yaya Aseef ina son yin magana da Aunty Akila amma baka tashe ni ba, eyye wato barcin karya aka yi mini kenan? Ni ne ban gane ba, to ba zan bari ba, sai na zane ki".
Zata yi magana ya ɗaure kyakkyawar farin yatsansa a saman lips nata yana faɗin shiiiiiiiiii ta yi mishi shiru.
Buge hannunsa Areef ya yi yana faɗin "Ba wani shirun da zata yi maka, ka jimin mutun, ka dai'na taɓa mata baki, zo nan ma ka gaya mini tun yaushe wannan abin ya fara faruwa ban sani ba, ka barni a gantale ban san komai ba, shi ne dan iya shege zaka wani cemin kana mafarkin mace ko? To dama kana zuba irin wannan kalaman soyayya ya za'ayi ba zaka yi mafarki ba, lallai ma ka sha da rabona".
Cikin sauri ta ce "Yaya Areef nasan komai, duk abin da ya faɗa wa Aunty Akila ina jinsa, ni zan gaya maka". Aseef zai sake yin magana Lion ya shigo wajen bakinsa ɗauke da sallama kasa kasa, yana sanye da pajama launin fari tas, tamkar yanzu ya fitar dasu daga ledarsu, yau shima sarkar wuyarsa tana a waje saman rigar kamar yadda Aseef yake yi, bai barta a ta ciki ba, ya yi kyau over, kujera daban ɗan gefe dasu ya je ya zauna, hannunsa na riƙe da laptop da kuma wayarsa.
Ganinsa yasa suka watsar da zancen shirmen da suke yi dan sanya Rimsha dariya, Areef baya son Lion ya rinƙa kallonta kullum a cikin shirme da yarinta, gwara su rinƙa yin abu serious a gaban shi, dan ya dai'na yi mata kallon small baby. Abinci Areef ya ce ta kawo musu suci, miƙewa ta yi ta nufi cikin gida, jim kaɗan ta dawo hannunta ɗauke da plates and spoons.
A in da ta tashi, nan ta koma ta zauna tana Murmushi tare da satar kallon Lion ɗin, da yake wajen gabaɗaya wasu shegun fitillune masu ɗan karen haske, sai ya yi tamkar rana, ko'ina gauraye yake da haskensu, ta yadda ko allurarka ce ta faɗi zaka iya ganin kayanka, hakan yasa suke ganin komai tankar.
Abincin ta fara zuba musu, fried rice ce and pepper chicken, abin ba'a magana, sai tashin daddaɗar kamshi yake yi, shi dai Aseef ji yake kamar ba zai iya ci ba, amma ya daure dan ta yi farinciki, kuma dan Lion yana wajen yasa ya ɗauki spoon, suka matso da ɗaya daga cikin tables dake wajen, suka ɗaura plate ɗin, sun sanyata a tsakiya kamar ƴar karamar kanwarsu da suke uwa ɗaya uba ɗaya.
Ɗibar spoon na farko Areef ya yi ya kai mata saitin ɗan bakinta yana faɗin "Have my first spoon our Queen". Da sauri Aseef ya matso da bakinsa ya cinye abincin yana faɗin "Ba wanda ya isa ya yi having na first spoon naka sai ni, dan wulakanci shi ne zaka bata ko? To na cin ye in ga abin da za'ayi". Dariya sosai ta kwashe da shi, ganin yadda yake tsuke baki saboda abincin, kuma ga shi sai masifa yake yi yaki yin shiru.
Duk abin da suke yi Lion yana jinsu sarai, amma bai ɗago ya kallesu ba, sai dai ya sanya a ransa idan har suka iya cin wannan abincin Nigeria da Rimsha ta zuba musu to tabbas ya jinjina mata, dan kuwa yana kallon yadda Musharraf ke fama da Aseef a Washington DC a kan cin abincin Naija, kullum Aseef ya ɗanɗana sai ya yi amai, shi kuma Areef sau ɗaya ya ɗanɗana a wajen Imran, daga nan bai sake kwatantawa ba, yanzu idan ya tabbata sunci na hannun Rimsha, to ba makawa yarinyar nan ta kai matakin da shi ma ya kamata ya ɗauketa da mahimmanci, dan kuwa bayan shi babu mai saka TRIPLETS nasa murmushi kamar ita, har mamakinsu yake yi. Allah mai iko, ya sanya maka soyayyar wanda baka sani ba, ya kuma sanya maka tausayin wadda baku haɗa komai ba, wani ma baka san shi ba rana ta farko da fara ganinsa da kai, sai gaji duk duniya idan ba shi ba, ba zaka taɓa samun kwanciyar hankali, baku haɗa komai da mutun ba, yana iya zama shi ne farincikinka, kamar dai su yanzu, basu son mata kwata kwata, harta maza basu so, basu son kowa ya raɓesu, lokaci gudu suka kamu da kunamarta, kauna irin ta ƴan uwan taka, ganinta da idanun ma kawai tana sanyasu matukar farinciki , rana tsaka suka santa, basu haɗa komai da ita ba, amma ta zama ita ce farincikinsu, suna kaunarta kauna irin ta addinin musulunci, Allah mai iko.