Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 3
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 3: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 3. "Me yasa zaki yi tantama da abin da na gaya…
3,351 words
"Me yasa zaki yi tantama da abin da na gaya maki? Shin ina yi maki karya ne? Bana maki karya sai dai na yi maki wasa wadda kuma idan muka gama waya kafin mu yi sallama ina gaya maki wasa nake yi maki akan abu kaza domin kada ki ɗauke ni makaryaci, to dai a wannan ma wasa nake yi maki, sai dai ba zan gaya maki a cikin magana biyun man wanenen wasa ba, ni ɗan Nigeria ne or not, da kuma hotona na tura maki shi ma or not, ki gane da kan ki, ɗaya ne gaskiya ɗaya kuma wasa, na tafi karatu za mu yi waya anji ma, yana da kyau ki rinƙa wasa kwakwalwa kema, maza ki yi tunani a cikin maganganu biyun nan ɗaya gaskiya ce ɗaya kuma wasa, cox sai anjima my bugun zuciya".
Turo ɗan bakin nan ta yi kafin ta ce "To ai ni ban ga ji da jin muryar ka ba, dan haka ban sallame ka ba".
"Heartbeat karatu fa zan yi please mana?".
"No my heartbeat yau na soke karatun ba zaka yi ba, idan kuma ka tafi Allah ka sani ba zan ci abinci ba, kuma daga nan har ka gama karatu ka sake kirana ina kuka" .
Cikin sauri ya ce "Subhanallah, rufa mani asiri my bugun zuciya, ni na isa in yi abin da baki so ne? Ba dai karatun ne baki so ba? To an barshi, zan ce HAROON ya rubuta mani Exam ɗin, idan kuma na faɗi Shikenan, amma ba zan damu ba tun da gimbiya ta ce ta sanya ni faɗuwa, in dai zaki yi farinciki ai bana ma buƙatar karatun".
HAROON ta maimaita sunan da ya kira, ta yi ta yi da shi akan ya gaya mata sunansa, amma yaki, bata taɓa jin ko da sunan wasa ya kama wani suna na wani dake kusa da shi ba sai yau, ta sha ruwan mamaki sosai jin sunan HAROON kuma a bakinsa, to wai shin waye shi?.
Ta yi nisa cikin tunanin da take yi sai jin zazzakar muryarsa ta yi yana faɗin "My heartbeat sarkin tunani, to yanzu kuma tunanin me ake yi?".
Da alama bai san ya ambaci wani suna ba a cikin maganar tasa, domin kuwa baya son kwata kwata ta san wani abin da ya dangance shi, ina da ayar tambaya ma akan wannan hoto da ya tura mata, by mistake ya ambaci sunan nan na HAROON, ita kuma ta riƙe sunan tana ta juya shi a ƙwaƙwalwarta, kwata kwata bai kawo cewa ya faɗi wani suna da har ta riƙe take juya shi a ƙwaƙwalwarta haka ba.
"Heartbeat na magana nake yi maki fa, haba mana, ko so kike yi na yi maki kuka ne?" Ya kai karshen maganar tare da saka mata kukan shagwaɓa har da kumbura kumatu irin na ƴan shagwaɓar nan.
Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta ce "Sorry my husband to be In Sha Allah, tu ba nake yi, kada ka yi mani kuka ka ji Heartbeat ɗin Heartbeat nasa?".
"What? Me kika ce? Dan Allah my Heartbeat ki sake maimaita sunan da kika kirani da shi yanzu kin ji?".
"My husband to be In Sha Allah na ce". Ya ilahi ya lalliahi wani irin miƙewa tsaye ya yi, a rikece ya fara magana har yana haɗe words. "Heartbeat kina nufin da gaske zaki aureni? Kina nufin kin yarda kina sona duk da baki taɓa gani na ba? Kin yarda da ni kin bani zuciyarki? Dan Allah ki amsa mani ko zan samu natsuwa, zuciyata sai buga mani take yi da sauri sauri, My Heartbeat please say something to your husband ko zai ji sauki kaɗan".
Hannu tasa ta fure fuskarta tana murmushi, cikin tsantsar so da kuma kaunar shi ta ce "Yah, na yarda da kai, duk da ban san ka ba, ban taɓa ganin ka a fili ba, ban san a ina kake ba, shin mutun ne kai ko aljani, ban sani ba, amma na yarda da kai domin har cikin zuciyata ina jin baza ka cutar da ni ba, please ka riƙe mani amana, ka ji ko? Da gaske nake yi ba da wasa ba, wlh ina sonka fiye da tunaninka, bana jin zan iya rayuwa da wani namijin idan ba kai ba, ina sonka sosai wlh".
Shiru ya yi kamar an ɗauke wutar nepa, daɗi ya hanashi yin magana, ya rasa ta ina zai fara, wani irin daddaɗar yanayi ya tsinci kansa a ciki mara misaltuwa. Ya ɗauki tsawon minti ɗaya kafin ya ce "Heartbeat kin kasheni yau, anya ma zan iya yin barci yau kuwa? Kai daɗi ba zai barni ba, yau dole na yi sadakar da ba zan iya irga nawa ne na kashe ba, dole gobe na ɗauki azumi, dama na yi wa Allah alkawarin duk ranar da kika karɓi soyayyata, ki ka aminta zaki aureni, to tabbas zan yi azumi goma a jere, domin na nuna godiya ta ga Ubangiji na, idan kuma na zo gida Abba ya bani aurenki, to daga ranar zan ɗauki azumi sai na yi guda talatin cif dan nuna wa Ubangiji na tsantsan farin cikina da godiyata a gare shi na ni'imar da ya yi Mani, ya bani ke a matsayin mata, Heartbeat me kike so na yi maki yanzun nan, ki faɗa mani dan Allah, ni kuma na yi maki alkawarin zan yi maki shi matuƙar bai saɓawa Allah ba, kuma komai wuyarsa zan yi maki, please tell me kin ji bugun zuciya ta?".
Kai wayyo daɗi soyayya, to bari mu shaƙata da wagga waƙa na TRIPLETS MUSIC daga bakin ɓoyayyen masoyi.
"Nazo ki min kalamai my Heartbeat, ke ɗai a cikin mata Ni na riƙe, kuma ba bari ko canza maganaaaaaaa....... Da ke kaɗai na aminta, babu mai canza ni, ko wuya ko daɗi, zuciyata taki ce, sahiba kuma baby na........ Mmmmmm....... Mmmmmm, Ke ɗin ta dabance, in naji muryarki ko a ina zan wai waiya, kuma in tsaya har sai na ganki heartbeatttt, ke ɗai a cikin mata na zaɓa ne, in babuke to ni ɗin ma dai babu neeee, kuma dole ne in ce maki kizo, ni dake na amince, Heartbeat mai kyawun zance, kin iya zuba kalamai, ga iya shagwaɓa ba'a magana". Wayyo daɗi duniyar nan take Mani, duk in da ka ji ance Heartbeat + Heartbeat tofa mu ɗin ne kawai........ TRIPLETS MUSIC..✍️ PRINCESS TEEMA.
STORY💋
A shagwaɓe ta ce "Sai mun yi waya an jima zan gaya maka abin da nake so ka yi mani, amma yanzu ma ka fara mannawa Al Qur'ani mai girma kiss, ma'ana idan mun gama waya ka yi karatun Al Qur'ani mai girma koda shafi biyu ne a cikin suratul Maryam, sannan ka yi mana addu'a ka ji mijina?".
Wani irin dogon numfashi ya ja tare da sauƙewa a hankali, cike da so da kuma kaunar ta ya ce "Dole ma kuwa, yanzu ma ba sai anjima ba, kuma ina katse kiran alwala zan yi na yi Sallah raka'a biyu dan nuna tsantsar madarar godiya ga ubangijin mu, karatun Al Qur'ani ya zama dole, kuma full suratul Maryam ɗin ma zan karanta maki, ke kuma ki je ki yi tunani akan abin da na ce ki gane na wani magana ne na yi na wasa, wanne ne kuma na gaske, ni ɗan Nigeria ne ko a'a? Sannan kuma hotona ne ko ba nawa ba? Ki je ki yi tunani nima bari na je na aiwatar da Sallah da karatu, ki kula mani da kanki sosai da sosai". Yana kai karshen maganar diff ya katse kiran.
Har cikin zuciyarta ta yarda cewa yes hotonsa ne wannan, sai dai bata yarda shi ɗan Nigeria bane dan kalar fatarsa, abin da ta manta da shi kuma shi ne suma family'nsu haka kalar fatar haskensu take, sai dai sun ɗan rage haske saboda rana, kuma bata san daddynsu Rismha bane, da ba zata taɓa musa cewa masoyin ɓoye ba ɗan Nigeria bane, saboda kusan hasken daddyn Rimsha da wanda yake jikin wannan hoto wato masoyin ɓoye, duk kusan ɗaya ne, da kaɗan masoyin ɓoyen ya fi shi, haka zalika shima Hassan wato Azharuddeen daddy Anaya, shima kamar Bature haka yake, a A.B.U ma Bature suke kiransa ko kuma Yellow saboda haskensa.
Shiru ta kwanta a saman gadon tana tunanin me mafita, wannene ba gaskiya ba a cikin waɗan nan magana biyun nasa?.
A ɓangaren JELLY kuwa, bayan sun dawo bata fi da minti biyu ba ta dawo palo ta cigaba da kallonta da take yi ɗazun, kamar ba ita ba, su Hanan kam basa gajiya da mamakin halin jelly, ita ma Aunty sai lokacin ta dawo palon ta zauna, suka cigaba da hirarsu har zuwa lokacin da su Abbi suka fito dan aci abinci.
Bayan sun haɗu a saman table ne, Abbi ya ya ce su ba shi hankalinsu bari ya yi magana da su, dukkansu natsuwa suka yi tare da tattara mashi hankalinsu baki ɗaya a kansa.
Kowa na cikin gidan yana saman wannan table ɗin except Ommu da dama already kun san da cewa bata shiga cikinsu, domin ba shi ne ya kawo ta gidan ba, abin da ya kawota daban, shiyasa bata damu da kowa a gidan ba.
Gyaran Murya Abbi ya yi tare da fara magana "Batula da ke da Halima ina son gobe ku ɗauki Jalila zuwa gidan yaya babba domin ku gabatar wa da Umaiya ita, sannan ku barta a can dan ta zauna a gidan mijinta, bai kamata mu riƙeta a nan ba, ina kuma kunyar mu tasa Imran bai yi wata magana ba, to dan haka ba zamu zama iyaye masu son kai ba, da ni da Maik da Irfan za mu tafi Katsina idan Allah ya kai mu gobe wajen iyayen Hanan, dan yana da kyau su san abin da ake ciki, idan sun bamu Hanan za mu dawo da ita, idan kuma ba su ba mu ita ba, to a can ma zan ɗauki nauyin karatun ta da komai da komai nata har zuwa ta yi aure, amma dai zan so su ba mu ita ɗin, ban san ya halinsu yake bane, kun san wasu iyayen ba za su yarda da hakan ba, to fatan mu dai Allah yasa dai su aminta su baku ita".
Amin gaba ɗayansu suka amsa da shi, sannan daddyn Jelly ya ɗaura da cewa "Yaya Deen ai mun yi magana da Imran ɗin, shi ne ma ya ce mu bar jelly a nan zuwa nan da next week zai zo ya ɗauke ta su wuce gidansa".
Salati Abbi ya saka yana mamakin jin wannan magana, daddyn Jelly ya zama kamar wani ƙaramin yaro, yaushe aka taɓa yin haka? Dan suna ƴan uwa kawai shi Imran shi zai zo ya ɗauki jelly ya kaita ga iyayensa? Wannan abu sai ka ce wasan yara, aure fa aka ce!.
"Maik ya za'a yi muna da mata a gida kuma a ce Imran ne zai zo ya ɗauki Jalila da kansa ya kai ta ga iyayensa? Wannan ai ya zama wasan yara, kuma kai ma sai ka yarda da hakan? Iyaye fa ai ba abin wasa bane, dan haka Batula da Halima su shirya zuwa gobe su ɗauke ta su kai ta gidan da kansu, sannan su yi mata nasiha sosai dan ta natsu ta san yanzu ita matar aure ce, daga nan su barta su dawo, wannan shi ne umarnina!".
Jinjina kai daddy ya yi alamar to ba damuwa, shi kuma Irfan miƙewa ya yi ya nufi waje, gaba ɗaya baya jin daɗin abincin ma, ya rame ƴan kwana biyun nan kamar mara lafiya, baya wani cin abinci sosai, baya da kwanciyar hankali da natsuwa, jiya har kofar gidansu Akila ya je dan ya samu ya tambayeta ko lafiya number bata shi ga, amma da ya je mai gadi ya ce bata nan ta tafi school, ga shi numberta baya shiga tsawon kwana uku kenan, kuma ba sai na sake gaya maku ba kun san da cewa Ammie bata kaunarsu bare ya shiga ya tambayeta ko wani abin ne ya sami wayar Akila ɗin, haka ya juyo kan motarsa ya dawo gida, a wannan daren dai bawan Allah nan bai samu barci ba, kamar yadda ya ga rana haka ya ga wannan dare dai, ya ci bakar wuya na raɗaɗin da zuciyarsa take yi mashi.
Yanzu ma haka da ya fice daga palon ɗakinsa ya koma ya kwanta tare da runtse idanu kamar mai barci, dama kuma kun san shi ma'abocin kwanciya a ɗaki ne.
Yana fita kuma daddyn Jelly ya bisa da ido ba tare da ya ce da shi ko ubban ba. Sai bayan sun kammala cin abinci matan su tafi ne daddy ya dubi Abbi ya ce "Yaya Deen Irfan da Akila fa soyayya suke yi".
Da fara'a Abbi ya ce "Kai haba dai?" tabbatar mashi da hakan daddy ya yi, murna a wajen Abbi ba'a magana, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, sai murmushi yake yi ya ce "Zan je Banki ranar Monday da kai na in samu yaya In gaya Mashi, duk hukuncin da ya yanke shi zamu bi, ni nasan ba zai hana Irfan Akila ba, amma dai sai mun gaya mashi sannan asan abin yi".
Sosai suka sha hira tare da ɗan tsakuro hiran abin da ya faru a baya suka tattauna kafin daga bisani kowa ya nufi Part nasa, daddy wanka ya je ya yi sannan ya kira Aunty a waya akan ta turo mashi Ayla bari ya yi mata wanka za su fita ne, dan tun da suka bar saman table sai ta bi su Aunty ɗin zuwa ɗakinsu. Salati Aunty tasa tana mamaki wai bari ya yi wa Ayla wanka, kamar wata jaririya, ta faɗa cikin zolaya.
Shima cikin zolaya ya ce "To ai ni a wajena jaririya ce, dan haka dole kinga na rinƙa yi mata wanka ina goya kayana". Dariya Aunty ta yi kafin ta ce "Ko ba goyo ba? Wlh yaya Maik tun da ka yi aure ka sauya, wato ma.....".
Bai bari ta karisa ba ya ce "Zaki turo mani ita ne ko kuma na shigo da kaina na ɗauki kayata?". Da sauri ta ce "A'a ai yanzu ma gata nan zuwa".
Kashe wayar ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, ya cigaba da shirin da yake yi, a haka Ayla ta shigo ta same shi, wani irin sihirtaccen kyau ta kara yi yarinyar nan, fatar jikinta ya kwanta luwai luwai, ta samu hutu sai wani kara ƙiba take yi abinta, mazaunantan nan sai kara cikowa suke yi, da yake ta kasa take da ƙiba ba ta sama ba.
Tana sanye da wandon jeans palazo blue color, da kuma riga high neck t-shirt black color, ta yi kyau sosai, kanta na sanye da ɗan karamin hijabi please call me launin blue color, kalar wandonta kenan, jikin hijabin dukka akwai stones manya manyan masu kyalli sosai, hakan ya karawa hijabin da ita kanta kyau.
Yana sauke idanunsa akanta wani irin azababben sha'awarta ne ya kama shi, kashe mata ido ɗaya ya yi tare da yi mata alama akan ta zo, da sauri ta tafi ta faɗa jikinsa tana sauƙe ajiyar zuciya.
Shima wani irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin nan ya zame mata Hijabin jikinta, ya ɗaura hijabin a saman mirror yana wani irin sauke numfashi a hankali hankali.
Laluɓeta ya fara yi yana ƙoƙarin capko breast ɗinta, cikin dabara ya ɗauketa sai saman gado, ya manta da cewa shirin fita ya yi, tuni ya cire kayan nasa ya hau sabuwar aiki na wucewa sama jannati..........
Takaitacciyar Nasiha garemu mata, da farko zan fara da TSAFTA!! TSAFTA!! TSAFTA!! a addinance tsabta tana daga cikon addini, a zamanance ita ce garkuwan lafiya, duk macen da bata da tsabfa tabbas kusan da ita da dabba duk ɗaya ce, bambancin kawai tunani, bai kamata kina mace ki saki jiki duk datti ba, Hajiyata mace ƴar kwalliya ce, mace da gyara aka santa, mace ƴar gayu ce, ina kara gaya maku, ke ko nawa ne Hajiya ki kashewa jikinki, in dai a fagen gyara ne, sai kaga wata mace ta zauna fatar jiki duk ya bushe kamar wani bayan kada, haba mana ƴar uwa, me namiji zai taɓa ya ji daɗi haka? Jiki kamar bayan bushasshiyar kifi, kai ina kada ki yarda ki zama guzuma, kayan gyaran nan fa ba wani tsada ne da su ba, kuma ma yafi kyau ki zauna ki haɗa kayan gyaranki da kanki a gida, kama daga sabulun wanka, man shawa masu kyau da inganci, turaruka, dilka da sauransu, kada ki rinƙa sayan na haɗawa a waje, domin kuwa suna mixing nashi da chemicals, wadda idan kika saya kika yi amfani da shi, idan suka yi expire suna kashe matar mace, suna lalata mata jiki, wani daga nan fatarta zata daina karɓar kayan gyara, to yana da kyau duk wasu kayan gyara ki haɗawa kanki da kanki, zan baku kaɗan daga cikin sirrin kayan gyara na addini musulci domin lokaci ya tafi, page na ya kai dai dai munzalin da nake Dakatawa.
Abu na farko ki sami ganyen ɗanyar lalle ta Hausa, sannan ki sami dilka, nescafe, kwai (egg) da kuma madara ta ruwa, sai lemon tsami kaɗan, sannan sai zuma and ruwan tumatir kaɗan.
Wannan ganyen lallen zaki fara daketa sai ta yi laushi ta fitar da ruwa, sannan ki kwashe ki ajiyeta a gefe, kada fa ki daka a turmi mai yaji Hajiyata, to idan kika daga a cikin mai yaji matsalarki ce, ke zaki je kina ihu Princess Teema tana kwance a gado bata san me yake faruwa ba.
Bayan kin kwasheta kin ajiye, sai ki ɗauki kwai ki fasata a wata roba daban, dukka kwan zaki haɗa har da na cikin, wasu suna cire na cikin, amma ki zuba har da shi yafi kyau, idan iya yi ɗaya ne, kwai ɗaya ya isheki. Ki kaɗen kwannan sosai, sannan ki zuba wannan dakakkiyar ganyen lallen, ki sake kaɗesu sosai, ki yi tabbatar ganyen lallen nan ya yi laushi luƙui sosai ta yadda zai haɗe da kwai ɗin.
Idan kin kaɗesu sai ki zuba madara ta ruwa, idan ma ta gari ce ta samu, sai a jiƙata, sai ta narke, sannan a zubata a ciki, ruwa kaɗan za'a sanyawa madarar, sai ki sake kaɗewa kafin ki zuba zuma da ruwan tumatir kaɗan, sannan sai a zuba nescafe, na sanyawa a tea, shi wannan nescafe ɗin kala kala ne, akwai mai kyau, akwai mara kyau, to a nemi mai kyau dan a sami biyan buƙata, a haɗesu sosai ta yadda za su game jikinsu, daga karshe sai a matsa ruwan lemon kaɗan dan a kashe karnin kwan, sannan kuma yana kashe kananan dark sport na fata, tana kuma taimakawa fata sosai wajen ganin kananan kuraje sun dai'na fita.
Idan aka gamesu suka haɗe sosai, sannan za'a iya zuba kuka kaɗan, is and optional, bayan anyi haka, sai a shafe jiki gaba ɗaya, a barshi ya yi minti talatin, ya bushe, idan ya bushe, sai ki murje jikin naki, Hajiyata tun daga kan murjewa zakiga yadda jikinki ke murjuwa, yana fitar da wasu dattin da ke kanki sai kin yi mamakin ta ina wannan datti ya bayyana.
Idan kin murje, sai ki je ki yi wanka, wayyo Allah, zakiga yadda fatarki zata koma, wani irin fresh zaki yi, ki fito luwai luwai, kina glowing Hajiyata..
Lokaci ya tafi, sai mun haɗu a wani page ɗin, In Sha Allah duk sauran wasu kayan gyara suna nan tafe, daga gyaran fatar jiki, har kan gyaran can ciki, ma'ana kayan karin ni'ima na mata da sauransu, amma fa ba alkawari na yi maku ba, idan na sami time zan rinƙa jefo maku a cikin page's ne....... Ma'assalam...✍️ PRINCESS TEEMA💋
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
E3-4
Laluɓeta ya fara yi yana ƙoƙarin capko breast ɗinta, cikin dabara ya ɗauketa sai saman gado, ya manta da cewa shirin fita ya yi, tuni ya cire kayan nasa ya hau sabuwar aiki na wucewa sama jannati.
Can kasan maƙoshinsa ya ce "Babyn daddy ya naga kamar daddy ya yi ajiya ne?" Cikin nuna ko in kula domin bata ma san ma'anar maganar tasa ba, ta ce "Daddy ajiyar me kuma? A ina kuma kayi ajiyar?".