Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 34

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 34

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 34: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 34. Wayarsa ya ɗauka, ya sha ruwan mamaki lokacin…

3,338 words

Wayarsa ya ɗauka, ya sha ruwan mamaki lokacin da ya kalli miss call ɗin daddy almost 10, shiru ya ɗan yi kafin ya cire password ɗin wayar, ɗan waro idanunsa waje ya yi lokacin da ya kalli an yi picking na first call da daddy ya yi, bai kawo komai a ransa ba, ya yi tunanin ma Aseef ne ya yi picking, cikin kwanciyar hankali ya fara kiran daddyn video call, tamkar jiransa dad yake yi, bugu ɗaya ya ɗauka, fuskar nan nasa a ɗaure tamau, yau ya fito a ainahin dangerous Boss ɗinsa, zuba mishi idanu Lion ya yi yana kallon shi, bai ce ko uppan ba. "Who is she Romeo?" Shi ne tambayar da ya fara yi mishi, shiru ya yi bai amsa ba. "Me haɗinta da kai? Meyasa wayarka zai kasance a hannunta?" Nan ma shiru ya yi bai yi magana ba, sai bin daddyn nasa da ido kawai yake yi.

Tsawa daddyn ya daka mishi "Am i not talking to you?!" Ɗan zaro idanu kaɗan ya yi yana mamakin, wai yau shi daddy yake yi wa tsawa har haka lallai. "Romeo am i your mate?!" Nisawa ya yi kafin gently ya fara magana "Daddy i don't know what to say, because i don't know what you are talking about ".

"Romeo how comes za'a ce mace ta ɗauki wayar ka kuma ka ce you don't know her, how this can be possible?". Shiru ya yi dan shi ba zai iya wannan surutu na daddy ba. "Romeo a ina kuke yanzu haka?" Kai tsaye ya amsa mishi da "Nigeria". "Nigeria kuma?" Jinjina mishi kai ya yi alamar tabbatarwa. "Okey yanzun nan ku haɗa kayanku ku dawo, yau ba sai gobe ba, kuma i really hate this girl that a saw koma wace ce".

"Ba zai yiwu ba daddy, sai na kammala abin da nake yi zamu dawo". Ya yi magana a nitse cikin kwanciyar hankali.

A fusace dad ya miƙe tsaye, cikin fushi da kausashiyar murya ya fara magana, "Romeo I'm your father who born you not your friend or your Triplets!! So is better for you ka san irin maganar da zaka rinƙa gaya mini".

Shi ma a wannan karon ranshi ya ɓaci, baya son hayaniya ko kaɗan, daddy ya zo yana ta wani daga mishi tsawa, a fusace ya miƙe tsaye, cikin tsawa da ɗaga murya ya mayarwa da dad amsa kamar haka "I'm so what dad, am so what if it is you had born me? Take me back to your womb!" Tashin hankali da ba'a sama mata date.

"Romeo are you hard what you said? Are you forget who you're talking with?!!".

"Am talking with father of TRIPLETS so what,?". Babbar magana!!.

Dafe saitin zuciyarsa daddyn ya yi, cikin kunan rai ya buɗe baki da kyar ya furta "Romeo umarni nake baka yau ba sai gobe ba ku dawo Usa". "Daddy ba zan dawo ko'ina ba har sai na kammala abin da nake yi, so ya rage naka ka hakura ko ka ɗauki mataki, ni dai na gama maganata, ba kai zaka rinƙa gaya mini abin da zan yi ba, a matsayina na soja aiki yana iya kaini ko ina, so ba umarninka zan bi a kan aikina ba that's all!!". Shaiɗan da zuciya sun ɗebesa sosai yau

"Romeo so kake yi ka kashe ni ko?". Shiru ya yi dan idan ya ce zai buɗe baki zasu yi kaca kaca da dad ne, saboda babu wanda ya isa ya ce mishi ga abin da zai yi, sai wanda ya yi niyar yi, a cewarsa, daga karshe ma katse kiran ya yi tare da yin wurgi da wayar a saman gado, cikin zafin nama ya nufi waje, kyawawan gashin dake kwance a hannunsa har wani miƙewa suke yi saboda ɓacin rai, Rimsha ta raina shi da har zata ɗauka mishi waya, ga shi tasa dad ya zo yana yi mishi hayaniya a kai, kuma kowa yasan shi mutun ne da baya son magana ma bare hayani ya, ta ja ransa ya ɓaci ya mayarwa da daddynsa magana, duk da cewa su yin hakan ma a wajensu ba wani laifi bane, wai dan yara su mayarwa da iyaye magana, ba su ɗauke shi a matsayin wani laifi ba, domin tun farko a kan hakan iyayen ke renan ƴaƴan, su sunma yi ƙoƙarin da har suke iya dannewa suna yiwa dad ɗin su biyayya, amma ba dan haka ba kowa yasan yadda ainahin rayuwar turawa yake, yara suna da dama da ƴancin yin komai da suke so, doka ce a dokonin kasarsu, ciki kuwa har da rufe iyaye a prison yara suna yi, a takaice dai da yara da iyaye su duk ɗaya ne a wajensu. ALHADULILLAH DA ALLAH YA YI MU A WAJEN DA MUKE YIN KASA DA MURYA A GABAN IYAYENMU, WANNAN MA KAƊAI BABBAR NI'IMA CE A GARE MU.

Yana fita bai zame ko'ina ba sai bedroom nata, lokacin da ya sako kansa ya shigo ɗakin, ita kuma ta fito daga toilet ɗaure da towel a kirjinta, da alama wanka ta yi, ganinsa yasa ta watsa a guje ta koma cikin toilet ɗin, da karfi ta banko kofar har da murza key, rai a matuƙar ɓace ya karisa wajen kofar, da karfi ya sanya kafa ya take kofar, wani irin jijjiga ta yi bata buɗe ba, sake ɗan komawa baya ya yi, a zafafe ya take ta da karfi, sai ga kofar ta ɓalle, ihu ta kurma ganin hakan, takawa ya yi cikin zafin nama ya damko gashin kanta, dama ga shi babu ɗankwali a kan nata, ta saki gashin har baya, jawota ya yi da gashi har zuwa tsakiyar ɗakin, wurgi da ita a kasa ya yi, rai a matukar ɓace ya daka mata tsawar ta yi mishi shiru kokuma ya take ta a wajen har sai ta mutu.

Jin hakan yasa ta miƙe a guje dan ta bar ɗaki, tasan a wannan yanayi da yake ciki tsab zai iya aikata duk abin da ya faɗa.

Wani irin mahaukacin damƙa ya yi wa wuyarta, sosai ya shaƙeta tare da zaro mata dara daran blue eyes ɗin nan nasa, gently ya yi magana. "Waye ya ce ki taɓa mini waya?". Ba bakin magana, sai ma ƙoƙarin jawo numfashinta da take yi domin ta rayu, ita ko da iya idanunsa da ya zaro mata ma ya barta, to zata iya mutuwa, ba sai ya kara mata wani azaban ba, a yau ne ta fara nadamar saninsa a rayuwarta, zata mutu ba tare da ta sake haɗuwa da su mummy ba, da kaɗan da kaɗan ta fara dai na kallo, wani irin duhune ya turnuke idanunta, har lokacin kuma bai saki wuyar tata ba, yau ta kure shi, ya jima yana danne zuciyarsa dan kada ya yi kisan kai, dama ya san duk ranar da ya sauƙe hannunsa a jikinta da nufin hukunci, tofa tabbas sai dai gawarta, tana yi mishi Laifuka da dama yana dannewa saboda Triplets, Imran da kuma daddynta.

"Ba dake nake magana bane?!". Ya mance ba ta yadda za'ayi ta yi magana, ya shaƙeta sosai, sai fafutuka take numfashinta yana gaf da ɗaukewa, idanunta har sun yi jawur da su kamar wuta, ga hawaye wani na bin wani, abin gwanin ban tausayi, sai dai shi ko ɗingon tausayin babu a zuciyarsa, sau da dama yana ɗaukar kowa kamar soja, hakan kuma ba ƙaramin cutar da mutane yake yi ba.

A hankali towel dake jikinta ya warware ya gangaro kasa, yana ƙoƙarin faɗuwa, a zafafe ya sanya ɗayar hannunsa ya tare mata a daidai cikinta, runtse idanunsa ya yi, yarinyar nan tana neman kure zuciyarsa, idan ya biyewa zuciyarsa tabbas zai halakata, gently ya hauro mata da towel ɗin sama ba tare da ya buɗe idanunsa ba, bai kuma saki wuyar nata ba, ya kawo towel ɗin daidai saitin kirjinta, a zafafe ya kuma saki towel ɗin ta zame ta faɗi kasa.

Ba komai bane yasa ya saki face hannunsa da ya sauƙa a saman tula tulanta, ita kanta sai da ta waro dara daran idanunta waje, tamkar zasu faɗi kasa, nan take ta ji ta watsake, a karo na farko ya kallah, yanzu kuma ya taɓa, wayyo Allah wani irin kululun bankinciki ne ya ziyarci zuciyarta, ji ta yi gabaɗaya ta tsane shi, shi kuma wannan taɓasu da ya yi, sun sanya ya ji wani irin mahaukacin shock a jikinsa, daga tafin kafarsa har izuwa tsakiyar kansa sai da ya amsa, ko kusa ko alama bai taɓa taɓa kirjin wata mace ba a rayuwarsa, jinsu ya yi wani iri, sun buga mishi kwakwalwar kansa ba kaɗan ba, wani irin yanayi mara misaltuwa ya ji a jikinsa, gently ya zame hannunsa daga wuyar nata tare da juya mata baya ba tare da ya buɗe idanun nasa ba, cike da ɓacin rai ya sanya hannu ya fara watsa gashin kansa yana ciza lallausan laɓɓansa na kasa.

Yana sakinta ta zube kasa tana tari tamkar maƙoshinta zai fashe, yasan kallon tsiraicin mutun a musulci haramun ne, hakan yasa ya juya mata bayan, kuma saboda hakan yasa ya sake ta, ba dan haka ba yau sai dai a ɗauki gawarta, ita kuma tari take yi tamkar ba zata rayu ba, duk da halin da take ciki bai hanata lallaɓawa ta ɗauki towel nata ta ɗaura ba, gabaɗaya ilahirin jikinta kerma yake yi, ta gama tsorata da lamarinsa, ta sadaddaƙar mutuwa zata yi yau, bawan Allah yana da ƙoƙari wajen ganin ya kula da addininsa, sai idan abu yafi karfinsa ne yake take wa, amma gaskiya yana ƙoƙarin sosai, duk da yake Bature kuma krista a baya, yanzu ya riƙi addinin musulunci sosai, hannu bibbiyu ba wasa.

A wannan hali Areef ya shigo ya same su, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke dan yasan dama za'ayi hakan, shiyasa ma da ya je ɗakin Lion bai same shi ba, ya nufo ɗakinta dan ya dubata shin tana lafiya.

Karisowa cikin ɗakin ya yi, wajen ta kai tsaye ya nufa, har lokacin tari take yi tamkar ranta zai fita, ta dafe kirjinta da hannayenta dukka biyu, da sauri ya juya ya koma Palo, ruwa mai sanyi ya ɗauko mata tare da dawowa ya zo ya miƙa mata, shi kuma Lion a zafafe ya juya ya fice daga ɗakin, bai sake kallon in da take ba, yau Allah ya ceceta, tsiraicinta ya ceceta, bin shi da kallo Areef ya yi har sai da ya fita, dawo da kallonsa kanta ya yi, a hankali ya buɗe ruwan ya rinƙa bata, ta fita a hanyacinta sosai, idanuwanta tamkar ba ita ba, yau ta ji kamshin mutuwa.

Ta kasa tashi har sai da Areef ɗin ya taimaka mata ta miƙe, a gefen gado ya zaunar da ita tare da juyawa ya fice daga ɗakin yabi bayan ɗan uwan nasa.

Sai da ta ɗauki good 30 mins zaune a wajen tamkar an shuka dusa, da kyar ta iya dawowa daidai, bayan ta dawo daidai ɗin ma, sai da ta kara 30 mins zauna a wajen kafin ta iya lallaɓawa ta miƙe zuwa wajen trolleynta, wandon jeans baki ta ɗauko da riga pink color mai dogon hannu, har lokacin jikinta na kerma, da kyar ta iya sanya kayan, bayan ta kammala komai da komai, hawa saman gado ta yi ta kwanta tana tunanin yadda taji sauƙan hannunsa a saman kirjin nata, runtse idanunta gam ta yi tana hawaye, abin ya yi mata ciwo, ita ai gara ya yi ta shaketa har ta mutu da taɓa mata su da ya yi, kwata kwata bata yi la'akari da cewa abin da ya tare mata ya fi tula tulan hatsarin a gani ba, ta ji uban shaƙa bata san cewa towel ɗin ya gangara zai faɗi ne ya tare mata ba, a wawtarta da shirmenta, da gangan da saninsa ya sa hannu ya taɓa mata su, tunanin hakan yasa ta ji bata son sake haɗa idanu da shi.

Haka ta kwanta tana hawaye har barci ya yi awon gaba da ita, a ɓangaren sa shi kuma oga yana fita bedroom nasa ya koma, toilet ya wuce, ruwan sanyi ya zuba a kansa, bayan ya fito, sai da ya sha robar ruwa mai bala'in sanyi har guda biyu, sannan ne ya ɗan samu zuciyarsa ta ɗan sauƙa, pajama ya sanya a jikinsa ya hau gado ya kwanta, a lokacin Areef baya ɗakin, dan ya shigo ya samu yana toilet sai ya fice zuwa wajen su Brady, sai kuka suke yi tun ɗazun, da alama wani abin suke so, ga shi Aseef yasa sarka ya ɗaure su, yana zuwa ya kwance su, kanshi suka haye suna haushi, barema Brady da yafi kowa kuka a cikinsu, kamar wasu mutane haka Areef ya zauna yana rarrashinsu.

Shi kuma Aseef yana riƙe da waya yana magana da daddy, da kyar ya samu ya kwantarwa da daddy hankali ya kuma bashi hakuri na abin da Lion ya yi mishi, shi kam Areef ko a jikinsa, dan ma laifi daddyn ya gani, saboda ya sani sarai Lion baya son shi, yana hakuri ne kawai yana yi mishi biyayya a matsayinsa na uba, amma ya zo ya tsaya yana yi mishi hayaniya a kai, ai dole ta kwaɓe musu dama, sai ka ce bai san halin ɗan nasa ba, ya san komai domin ai renonsa ne yaran, shi ya ɗaurasu a kan wannan turba, tun suna yara ya basu horon kada su yarda wani ya ɗaga musu murya, to dama ita rayuwa haka take, duk abin da ka koyawa yaro a kwana a tashi watarana sai ya yi maka, shiyasa ake so ka ɗaura yara a kan turba mai kyau, dan idan suka tashi yi maka ka ga mai kyau, Allah dai yasa mu dace.

After some hours.

Da yamma misalin karfe 4:30, sanye da wando jeans pink color da riga fari mai ƙaramin hannu ta fito Palo, ta ɗaure wannan kyakkyawar bakin gashin nata, sai kyalli face nata yake yi, hannunta na riƙe da wayarta, da alama ta ci kuka har ta ƙoshi, dan ga idanunta nan sun kumbura, sun yi jawur ta kasan.

Palon kasa ta nufa, babu kowa, gidan shiru, ko'ina a gyare yake tsab tamkar hannu bai taɓa taɓa komai dake wajen ba, kamar daga leda aka ciro komai, fitinannen kamshi air freshener ne ke tashi ta ko'ina, ga blue light da sanyin Ac, abin ba'a magana, ya ƙayatar ba kaɗan ba. Sai buga hammar yunwa take yi, dan bata ci abincin rana ba, ta sha barci kamar ba gobe, shi kuma Imran ya tafi shopping shi da Jelly, dan ta matsa mishi a kan lallai suje su sayi kaya, shi ne ya ɗauketa suka tafi.

Mark na kitchen yana aikinsa, kamar dai kullum fuskar nan tasa tamkar na ogansa, babu annuri ko kaɗan, basu san wani abu wai shi murmushi ba, bare dariya kwata kwata a rayuwarsu, ɗaure fuska da bada umarni kawai suka iya. Kallo ɗaya ta yi mishi ta kawar da kanta, dan haushin kowa na gidan take ji, tun da Lion ya taɓa mata tula tula shikenan ta tsani kowa, yanzu ma yunwa ne ya fito da ita, ba dan haka ba, ta ce ba zata sake fitowa waje ba, ba zata sake kula kowa ba, yarinta kenan, shi kuma Areef bawan Allah lokacin da take barci sau biyu yana zuwa ya dubata bata tashi ba, lokacin cin abicin rana ya je ya dubata, dama zai ce mata su je su sayi abinci ne, sai ya samu bata tashi ba, ita kuma ashe fushi take yi da kowa, har da su masu saya mata abincin ma gabaɗaya.

(Wayyo cikina wlh Rimsha zata kashe ni da dariya 🤣 ƴar kaniya idan ta yi fushi da su to waye zai saya mata abincin?🤣 Kuruci dangin hauka)

Tana fita harabar gidan suka yi ido huɗu da Brady dake tsaye a harabar gidan, tun safe da Areef ya kwancesu bai sake ɗaure su ba, akwai ta da bala'in tsoron kare, bare kuma Brady da ya kasance renon soja, ai sai a hankali, Lion ya rene shi a irin halin sojoji, akwai shi da faɗa na bala'i, baka kula shi ba ma zai kula ka, idan ba TRIPLETS ba, baya ragawa kowa ɗan banzan karen nan.

Ihu ta kurma tare da juyawa a guje ta koma cikin in da ta fito, ai kuwa shima da gudu ya bi bayanta yana daka haushi, dama kunsan ka'idan karnuka ne hakan, idan mutun ya gudu zasu bishi, bare shi Brady da dama ko bata gudu ba sai ya bita ɗin dan bala'in faɗa, a guje ta haura sama tana ihu, shi ma a guje ya haura yana haushi.

Daidai tsakiyar palon suka ci karo da Lion ya fito zai sauƙa kasa, yana shirye cikin wasu shegun tsadaddun kananan kaya, da alama fita zai yi, yau ma kamar jiya, sarkarsa na saman riga ba a ciki ba, black glass ne a idanunsa, sai tashin kamshi yake yi kamar anyi ɓarin turare a jikinsa, ya yi kyau over tamkar shi ya yi kansa.

Bata lokacin da ta ƙanƙame shi da iya karfinta tana ihu ba, a guje Brady ya yi kanta yana ƙoƙarin kai mata cizo, wani irin mahaukaciyar damka ta yi wa Lion ɗin a kirjinsa, da alama bata ma san waye ta rungume ba, hankali ya tashi sosai idanunta sun rufe, bata gani, ita dai a rabata da wannan bala'in, wato Brady.

Yana ƙoƙarin kai mata cizo Lion ya tare shi da hannu ɗaya, gently ya yi mishi magana da English a kan ya bari, tsalle ya yi ya taka kafaɗarta ya haye jikin Lion ɗin yana wani girgiza kamar wadda ya je farauta ya dawo, ɗan banzan balaƴaƴen kare, ko da yake a haka a hore shi.

"Sake ni". Ya faɗa a nutse, shiru bata amsa ba kuma bata sake shin ba, ɗan duƙo da kansa ya yi a kan face nata, sai yaga ta sume mishi a jiki, ashe lokacin da Brady ya zo zai cijeta, bala'in tsoro yasa numfashinta ya ɗauke, ɗan ciza laɓɓansa ya yi tare da cewa Brady ya sauƙa mishi a jiki, ba musu ya diro kasa sai wani girgiza na iya shege yake yi.

Ji ya yi tamkar ya yi wurgi da ita kawai ya yi tafiyarsa, amma kuma sai ya kasa yin hakan, ɗan rage tsawonsa ya yi tare da ɗaukarta cak ya nufi saman sofa, har zai kwantar da ita a wajenku ko me ya tuna sai ya fasa, ya nufi bedroom nata, saman gadonta ya kwantar da ita, zai miƙe kenan sarkarsa ya dawo da shi, dan kuwa sarkar nasa ya makale a cikin nata sarkar dake ta cikin rigarta, ɗaukarta da ya yi yasa sarkar wuyarsa ya shiga rigarta.

Guntun tsaki ya ja tare da ɗan jan wuyar rigar nata kasa ya fito da nata sarkar, gently ya warware su ya zame nasa, miƙewar da zai idanunsa suka sake sauƙa a saman sunansa dake rubuce a tudun tula tulanta, shiru ya ɗan tsaya yana karewa sunan kallo, daga bisani kuma ya dawo da kallonsa a kan face nata, har wani shock ya ji lokacin da ya kallin face ɗin nata, yau taso ma ta yi mishi kama da Josephine, ɗan shafa kansa ya yi yana mamakin wannan fuskar tata, fuskar ce abu ta farko da ta tsaya mishi a rai, ya gane cewa ita ce ta kira sunan shi a gidansu Imran, dan ranar da ta kira Anaya a waya zata gaya mata cewa ya kallan mata breast, a ranar ya gane ita ta kira sunansa, da ta kira Anaya ta ce Anaya GAR ya kalla mini.. sai kuma ta yi shiru, yana cikin bedroom nasa yana jinta, yaji GAR da ta faɗa, tamkar a bakinta a ha halicci sunan, ta iya kira kamar ba gobe.

Gently ya juya zai bar ɗaki, idanu ɗuhu suka yi da Areef dake tsaye a bakin kofar shigo, tun lokacin da Lion ɗin ya shigo da ita shi ma ya shigo, dan ihun da ta yi ta gudu Brady ya bi bayanta, lokacin yana garden, ya ji ihun nata ne ya biyo bayanta, yana haurowa Palon sama lokacin shi kuma Lion ya ɗaukota zai kai bedroom nata.

Readers Also Read