Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 36
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 36: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 36. Karisowa cikin ɗakin ya yi, wajen ta kai…
3,334 words
Karisowa cikin ɗakin ya yi, wajen ta kai tsaye ya nufa, har lokacin tari take yi tamkar ranta zai fita, ta dafe kirjinta da hannayenta dukka biyu, da sauri ya juya ya koma Palo, ruwa mai sanyi ya ɗauko mata tare da dawowa ya zo ya miƙa mata, shi kuma Lion a zafafe ya juya ya fice daga ɗakin, bai sake kallon in da take ba, yau Allah ya ceceta, tsiraicinta ya ceceta, bin shi da kallo Areef ya yi har sai da ya fita, dawo da kallonsa kanta ya yi, a hankali ya buɗe ruwan ya rinƙa bata, ta fita a hanyacinta sosai, idanuwanta tamkar ba ita ba, yau ta ji kamshin mutuwa.
Ta kasa tashi har sai da Areef ɗin ya taimaka mata ta miƙe, a gefen gado ya zaunar da ita tare da juyawa ya fice daga ɗakin yabi bayan ɗan uwan nasa.
Sai da ta ɗauki good 30 mins zaune a wajen tamkar an shuka dusa, da kyar ta iya dawowa daidai, bayan ta dawo daidai ɗin ma, sai da ta kara 30 mins zauna a wajen kafin ta iya lallaɓawa ta miƙe zuwa wajen trolleynta, wandon jeans baki ta ɗauko da riga pink color mai dogon hannu, har lokacin jikinta na kerma, da kyar ta iya sanya kayan, bayan ta kammala komai da komai, hawa saman gado ta yi ta kwanta tana tunanin yadda taji sauƙan hannunsa a saman kirjin nata, runtse idanunta gam ta yi tana hawaye, abin ya yi mata ciwo, ita ai gara ya yi ta shaketa har ta mutu da taɓa mata su da ya yi, kwata kwata bata yi la'akari da cewa abin da ya tare mata ya fi tula tulan hatsarin a gani ba, ta ji uban shaƙa bata san cewa towel ɗin ya gangara zai faɗi ne ya tare mata ba, a wawtarta da shirmenta, da gangan da saninsa ya sa hannu ya taɓa mata su, tunanin hakan yasa ta ji bata son sake haɗa idanu da shi.
Haka ta kwanta tana hawaye har barci ya yi awon gaba da ita, a ɓangaren sa shi kuma oga yana fita bedroom nasa ya koma, toilet ya wuce, ruwan sanyi ya zuba a kansa, bayan ya fito, sai da ya sha robar ruwa mai bala'in sanyi har guda biyu, sannan ne ya ɗan samu zuciyarsa ta ɗan sauƙa, pajama ya sanya a jikinsa ya hau gado ya kwanta, a lokacin Areef baya ɗakin, dan ya shigo ya samu yana toilet sai ya fice zuwa wajen su Brady, sai kuka suke yi tun ɗazun, da alama wani abin suke so, ga shi Aseef yasa sarka ya ɗaure su, yana zuwa ya kwance su, kanshi suka haye suna haushi, barema Brady da yafi kowa kuka a cikinsu, kamar wasu mutane haka Areef ya zauna yana rarrashinsu.
Shi kuma Aseef yana riƙe da waya yana magana da daddy, da kyar ya samu ya kwantarwa da daddy hankali ya kuma bashi hakuri na abin da Lion ya yi mishi, shi kam Areef ko a jikinsa, dan ma laifi daddyn ya gani, saboda ya sani sarai Lion baya son shi, yana hakuri ne kawai yana yi mishi biyayya a matsayinsa na uba, amma ya zo ya tsaya yana yi mishi hayaniya a kai, ai dole ta kwaɓe musu dama, sai ka ce bai san halin ɗan nasa ba, ya san komai domin ai renonsa ne yaran, shi ya ɗaurasu a kan wannan turba, tun suna yara ya basu horon kada su yarda wani ya ɗaga musu murya, to dama ita rayuwa haka take, duk abin da ka koyawa yaro a kwana a tashi watarana sai ya yi maka, shiyasa ake so ka ɗaura yara a kan turba mai kyau, dan idan suka tashi yi maka ka ga mai kyau, Allah dai yasa mu dace.
After some hours.
Da yamma misalin karfe 4:30, sanye da wando jeans pink color da riga fari mai ƙaramin hannu ta fito Palo, ta ɗaure wannan kyakkyawar bakin gashin nata, sai kyalli face nata yake yi, hannunta na riƙe da wayarta, da alama ta ci kuka har ta ƙoshi, dan ga idanunta nan sun kumbura, sun yi jawur ta kasan.
Palon kasa ta nufa, babu kowa, gidan shiru, ko'ina a gyare yake tsab tamkar hannu bai taɓa taɓa komai dake wajen ba, kamar daga leda aka ciro komai, fitinannen kamshi air freshener ne ke tashi ta ko'ina, ga blue light da sanyin Ac, abin ba'a magana, ya ƙayatar ba kaɗan ba. Sai buga hammar yunwa take yi, dan bata ci abincin rana ba, ta sha barci kamar ba gobe, shi kuma Imran ya tafi shopping shi da Jelly, dan ta matsa mishi a kan lallai suje su sayi kaya, shi ne ya ɗauketa suka tafi.
Mark na kitchen yana aikinsa, kamar dai kullum fuskar nan tasa tamkar na ogansa, babu annuri ko kaɗan, basu san wani abu wai shi murmushi ba, bare dariya kwata kwata a rayuwarsu, ɗaure fuska da bada umarni kawai suka iya. Kallo ɗaya ta yi mishi ta kawar da kanta, dan haushin kowa na gidan take ji, tun da Lion ya taɓa mata tula tula shikenan ta tsani kowa, yanzu ma yunwa ne ya fito da ita, ba dan haka ba, ta ce ba zata sake fitowa waje ba, ba zata sake kula kowa ba, yarinta kenan, shi kuma Areef bawan Allah lokacin da take barci sau biyu yana zuwa ya dubata bata tashi ba, lokacin cin abicin rana ya je ya dubata, dama zai ce mata su je su sayi abinci ne, sai ya samu bata tashi ba, ita kuma ashe fushi take yi da kowa, har da su masu saya mata abincin ma gabaɗaya.
(Wayyo cikina wlh Rimsha zata kashe ni da dariya 🤣 ƴar kaniya idan ta yi fushi da su to waye zai saya mata abincin?🤣 Kuruci dangin hauka)
Tana fita harabar gidan suka yi ido huɗu da Brady dake tsaye a harabar gidan, tun safe da Areef ya kwancesu bai sake ɗaure su ba, akwai ta da bala'in tsoron kare, bare kuma Brady da ya kasance renon soja, ai sai a hankali, Lion ya rene shi a irin halin sojoji, akwai shi da faɗa na bala'i, baka kula shi ba ma zai kula ka, idan ba TRIPLETS ba, baya ragawa kowa ɗan banzan karen nan.
Ihu ta kurma tare da juyawa a guje ta koma cikin in da ta fito, ai kuwa shima da gudu ya bi bayanta yana daka haushi, dama kunsan ka'idan karnuka ne hakan, idan mutun ya gudu zasu bishi, bare shi Brady da dama ko bata gudu ba sai ya bita ɗin dan bala'in faɗa, a guje ta haura sama tana ihu, shi ma a guje ya haura yana haushi.
Daidai tsakiyar palon suka ci karo da Lion ya fito zai sauƙa kasa, yana shirye cikin wasu shegun tsadaddun kananan kaya, da alama fita zai yi, yau ma kamar jiya, sarkarsa na saman riga ba a ciki ba, black glass ne a idanunsa, sai tashin kamshi yake yi kamar anyi ɓarin turare a jikinsa, ya yi kyau over tamkar shi ya yi kansa.
Bata lokacin da ta ƙanƙame shi da iya karfinta tana ihu ba, a guje Brady ya yi kanta yana ƙoƙarin kai mata cizo, wani irin mahaukaciyar damka ta yi wa Lion ɗin a kirjinsa, da alama bata ma san waye ta rungume ba, hankali ya tashi sosai idanunta sun rufe, bata gani, ita dai a rabata da wannan bala'in, wato Brady.
Yana ƙoƙarin kai mata cizo Lion ya tare shi da hannu ɗaya, gently ya yi mishi magana da English a kan ya bari, tsalle ya yi ya taka kafaɗarta ya haye jikin Lion ɗin yana wani girgiza kamar wadda ya je farauta ya dawo, ɗan banzan balaƴaƴen kare, ko da yake a haka a hore shi.
"Sake ni". Ya faɗa a nutse, shiru bata amsa ba kuma bata sake shin ba, ɗan duƙo da kansa ya yi a kan face nata, sai yaga ta sume mishi a jiki, ashe lokacin da Brady ya zo zai cijeta, bala'in tsoro yasa numfashinta ya ɗauke, ɗan ciza laɓɓansa ya yi tare da cewa Brady ya sauƙa mishi a jiki, ba musu ya diro kasa sai wani girgiza na iya shege yake yi.
Ji ya yi tamkar ya yi wurgi da ita kawai ya yi tafiyarsa, amma kuma sai ya kasa yin hakan, ɗan rage tsawonsa ya yi tare da ɗaukarta cak ya nufi saman sofa, har zai kwantar da ita a wajenku ko me ya tuna sai ya fasa, ya nufi bedroom nata, saman gadonta ya kwantar da ita, zai miƙe kenan sarkarsa ya dawo da shi, dan kuwa sarkar nasa ya makale a cikin nata sarkar dake ta cikin rigarta, ɗaukarta da ya yi yasa sarkar wuyarsa ya shiga rigarta.
Guntun tsaki ya ja tare da ɗan jan wuyar rigar nata kasa ya fito da nata sarkar, gently ya warware su ya zame nasa, miƙewar da zai idanunsa suka sake sauƙa a saman sunansa dake rubuce a tudun tula tulanta, shiru ya ɗan tsaya yana karewa sunan kallo, daga bisani kuma ya dawo da kallonsa a kan face nata, har wani shock ya ji lokacin da ya kallin face ɗin nata, yau taso ma ta yi mishi kama da Josephine, ɗan shafa kansa ya yi yana mamakin wannan fuskar tata, fuskar ce abu ta farko da ta tsaya mishi a rai, ya gane cewa ita ce ta kira sunan shi a gidansu Imran, dan ranar da ta kira Anaya a waya zata gaya mata cewa ya kallan mata breast, a ranar ya gane ita ta kira sunansa, da ta kira Anaya ta ce Anaya GAR ya kalla mini.. sai kuma ta yi shiru, yana cikin bedroom nasa yana jinta, yaji GAR da ta faɗa, tamkar a bakinta a ha halicci sunan, ta iya kira kamar ba gobe.
Gently ya juya zai bar ɗaki, idanu ɗuhu suka yi da Areef dake tsaye a bakin kofar shigo, tun lokacin da Lion ɗin ya shigo da ita shi ma ya shigo, dan ihun da ta yi ta gudu Brady ya bi bayanta, lokacin yana garden, ya ji ihun nata ne ya biyo bayanta, yana haurowa Palon sama lokacin shi kuma Lion ya ɗaukota zai kai bedroom nata.
Ko sannu bai ce da Areef ɗin ba ya wuce ya fice abinsa, mamaki Areef yake yi, wai me haɗin breast ɗin Rimsha da Lion ne, duk idan zasu yi karo to fa breast ɗin nan nata ne a gaba, sai ya kallesu, wannan wace iriyar kaddara ce? Ya tambayi kansa, suku nasu kaddarar a haka tazo kenan?. Juyawa shima ya yi ya fita, a harabar gidan ya isko Lion ɗin da Mark zasu fita, ga hadari na tasowa, alamar ruwan sama za'ayi, har walkiya ta fara wanzuwa a sararin samaniya, garden ya koma abinsa, shi kuma Lion ya wuce suka fita da Mark, Aseef kuma yana ta shararra barci bawan Allah.
A ɓangaren gidan Hajiyar daɗi kuwa.......
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
E29-30
A ɓangaren gidan Hajiyar daɗi kuwa, ranga ranga suka kwashi Zinariya suka fita da ita daga gidan, sai Allah ne kaɗai yasan in da zasu kai ta, ita kuwa Jehan, bayan sun kaita ɗaki sun fito, miƙewa ta yi zaune tare da cewa Adiva, "Adiva zo ki kwance ni kin ji?". Da farko Adiva taki, ta ce tana tsoro kada su Zinariya su zo su mata ɗan banzan duka, sai da Jehan ɗin ta yi ta kara mata karfin gwiwa sannan ta yarda ya zo ta kwaceta ɗin, "Bani ruwan sha Maryam". Da sauri ta ɗauko mata ruwan a fridge, tun da ta kafa kai bata ɗaga ba har sai da ta shanye ruwan nan tas, sai faman sauke nauyayyar ajiyar zuciyar take yi, ita kanta ta wahala, ina ga su Zinariya kuma? Abin ai ba'a magana, sun wahala ba kaɗan ba.
Jugum jugum suka yi, dukkansu idanu sun rena fata, bare ma Adiva da bata saba da shan wahala ba, renon madara da ice cream, jiki duk madara, yau ta kare a gidan karuwai, wannan shi ne ake kira da rashin sani yafi dare duhu, ga iyayensu a can suna haukar nemansu, ga su sukuma a nan, ana ƙoƙarin lalata musu rayuwa a sakasu a harkar bariki, gabaɗaƴansu ma sun ɗauka iyayen nasu sun mutu, ya Allah kasa mu fi karfin zukatanmu.
"Adiva ina wayar nan taki? Ɗauko ki saka mana ita a charji, bana son komai ya sameta, dan akwai abubuwan da na ajiye masu mahimmanci a cikinta". Cewar Jehan kenan, da sauri ta miƙe ta shiga cikin toilet ta ɗauko wayar, dan a can suka barota, da kyar ita kuma Jehan ɗin ta lallaɓa ta shiga toilet dan ta yi wanka ko jikinta ya sami kwari.
Kusa da A'isha da bata ko motsi Adiva ta zo ta zauna tare da zuba mata idanu, bayan ta yi wanka ta fito, kayan Adiva ta sake sakawa a jikinta kafin ta haye gadon Aisha ɗin, jugum jugum suka yi suna kallonta, fuskarta ya yi wani irin haske tamkar babu rai a jikinta, ga face ɗin natan ya kumbura kamar an hura balo balo, tunani Jehan take yi anya ba wani cutar wani alhajin ya sanyawa A'isha ba kuwa? Ji yadda take ta kumbura kamar ana hurata, anya ma akwai rai a jikinta kuwa? Anya akwai sauran numfashi a tattare da ita kuwa?. Sai tunane tunane take yi, abin ya ɗaure mata kai, ga shi ita ba iya gane matatciya da rayayyiya zata yi ba, basu da wata madafa, ba magani ba asibiti.
Sun jima zaune a wannan yanayi kafin a kira sallar mangariba, Jehan ce ta fara tashi ta ɗauro alwala ta fito, tana fita Adiva ta shiga, daga cikin su ƴar gwal kuwa, babu wacce ta sake shigowa cikin ɗakin nasu, basu sake jin ɗuriyar kowa a gidan ba, tamkar babu kowa.
Bayan sun idar da sallar mangariba sai suka zauna saman daddumar suna karatun Alqur'ani mai girma, har sai da aka kira sallar issha suka tashi suka gabatar da sallah, Maryam da Adiva suka je suka ɗauko musu abinci bayan sun idar da sallar kenan.
A tare suka ci abincin, Allah sarki yau ban da A'isha, abin gwanin ban tausayi, bayan sun gama ci, ko wace ta haye saman gadonta, ita kam Adiva gadon jenan ta haye dan tana tsoro, addu'ar barci suka yi, ba jimawa Adiva da Maryam suka yi barci, ita kuwa Jehan yadda taga rana, haka ta ga dare, ta kasa rintsawa, Allah ne kaɗai yasan me take tunani da bata yi barci ba, har wa yau A'isha bata motsa ba.
Washegari da safe kamar yadda suka saba, bayan sun yi sallar asuba suka gyara ɗakin nasu, suka yi wanka sannan suka zo suka zauna saman gadajensu, sai latsa waya Jehan take yi kamar mai tura wani saƙon.
Da misalin karfe tara na safe, suna zaune jugum jugum sun tasa A'isha a gaba, har lokacin bata motsa ba. A hankali aka turo kofar ɗakin nasu, wata hamshakiyar mace ce, mace wadda ta amsa sunanta mace, sanye take da wata shegiyar lace wadda ta amsa sunanta lace, ta haɗu lace ɗin nan, da alama zata yi bala'in tsada, wuya da hannayenta duk shaƙe suke da kayan ado na gwalagwalai, fara ce tas, amma farin mai ce, tana da faɗin fuska sosai, kafarta na sanye da wani tsadadden haɗadɗen plat shoe mai bala'i kyan gaske, ta ko'ina a jikin matan nan dukiya ce a narke a wajen, kanta ba ɗankwali, ta zuba uban attachment har baya, da kallo ɗaya zaka yi mata kasan ba bahaushiya bace, in ma bayarabiya or Ebo, egala, ɗaya daga ciki dai, ga wani uban make up da ta sha, eyelashes nan ba'a magana, kamar bindin kaza, hancin nan nata a haje a fuskar tata, irin matan nan ne masu cika ido, idan ka gansu sai sun cika maka idanu ta yadda zaka kasa yi musu gardama a kan abu, akwaita kuma da katon tunbi kamar mai ciki wata tara, tana da kiɓa ba cancan sosai ba, idanunta dara dara, irin waƴan nan idanun da suke tamkar a waje haka, gula gula da su, gasu jawur tamkar ƴar shaye shaye, sai tashin wani irin warin maganin gargajiya take yi, da alama wani turaren magani ta banka a jikin nata, dan ga kamshin perfume nata a gefe, shi kuma maganin warinsa na gefe.
Babu ko sallama ta kutso cikin ɗakin, zuba mata idanu suka yi har ta iso wajen bakin gadon nasu, tun da suka ɗaura idanunsu a kanta suka kasa ɗaukewa, da alama kuma gabaɗayansu sunyi la'asar, duk jikinsu ya mutu tamkar wani abin ta yi musu, da alama dai ba haka kawai ta shigo ba.
Gefen gadon ta zauna, cikin sanyin murya ta fara magana cikin harshen turanci, da alama babu Hausa a bakinta, "My daughters ya kuke ta kallon mummynku haka? Tamkar kunga wata bakuwa daga wata duniya? Ba zaku gaishe ni bane? Mummynku ce fa, ni ce mahaifiyar ku yanzu". Har suna haɗa baki wajen ɗaga mata gaisuwa, har lokacin kuma basu kawar da kallonsu daga kanta ba, wani irin shu'umin murmushi ta saki "Yauwa daughters ko ku fa? Ai yana da kyau ku rinƙa respect na mum ɗin ku, Jehan me ya same ki naga bakinki kamar ya ɗan kunbura?".
Hannu ta kai ta taɓa bakin nata tana faɗin "Mummy babu komai" "No daughter ki gaya mini idan wata ko wani ne suka taɓaki a gidan nan, yanzu zan sanya ayi musu hukunci!" Girgiza kai ta shiga yi tana faɗin "Da gaske mummy babu komai".
Dawo da kallonta kan A'isha dake kwance tamkar gawa ta yi, a ɗan ruɗe ta furta "Oh my god, me ya sami my daughter A'isha kuma?". Cikin sauri Adiva, Jehan suka haɗa baki wajen cewa "Muma bamu sani ba mummy". Miƙewa tsaye ta yi, da ganinta kasan anci duniya da tsinke, bariki ta zauna, goggiya ce, duk wani tantiranci ta iya shi, makirci, kirsa suma sara mata suke yi, nan take ta nuna musu ta birkice, ta shiga tsantsar tashin hankali da halin da A'ishar take a ciki, hankalin ya yi mummunar tashi, har da wani kyarkyatar karya, tare da ciro wayarta ta danna kira, cikin wani yare ta yi magana, bayan ta gama wayar ta koma ta zauna tare da fara shafa fuskar A'ishar tana faman ambatar "Oh my daughter, yau ina zan sa kai'na, dole a zo a kai mini ita Hospital, oloni". Bayin Allah sun ɗauka da gaske ne, ko da yake ba wani abin da za su iya yi, ta rufe musu baki ruf, yanzu sai abin da ta ce shi zasu yi, ba su isa su tsallake maganarta ba....... INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJIUN JUSTICE FOR JEHAN, ADIVA AND MARYAM, SUN SHIGA KOMA SUMA, DUK WANI MAI IMANI DOLE YA YI MUSU KWALLAH, SUN SHIGA HANNUN WANNAN MAKIRA.😭
Ba'afi minti 5 da yin wannan waya da ta yi ba, sai ga wasu mata sun shigo cikin ɗakin su biyu, mata ne amma masu kirar maza, duk layinsu ɗaya da hajiyar, cikin wannan yare nasu ta sake yi musu magana, tsawon minti uku suna maganar, daga bisani suka ɗauki A'isha suka fita da ita, Jehan, Adiva, Maryam, babu wacce ta iya tambayar ina za'a kai A'ishar, sun zuba ido kawai suna kallo, har aka fice da ita, juyowa garesu Hajiyar daɗin ta yi. "My daughter's kada ku damu magani za'a je a yi mata, Hospital zasu kai ta, dole nayi jinyar daughter ai, kada ku ji komai, nan ba da jimawa ba, zata dawo gareku, yanzu dai kunci abinci ne?" Har wa yau cikin harshen turanci ta yi maganar. E suka amsa mata da shi.
Girgiza kai ta yi tana faɗin "No daughters bari na sa a kawo muku wani abincin, ai ina gidan nan, kada ku damu dole zaku yi abin da kuka ga dama, tun da mummynku ta dawo shikenan ai, zaku ji daɗi, Jehan idan kun gama cin abinci ki shirya mu je super market a sayo miki kayayyaki masu shegen kyau da kuma sauran duk abin da kike buƙata". Da murnarta ta amsa da okey, Allah sarki kun shiga koma sai addu'a.