Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 56

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 56

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 56: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 56. A wani irin mahaukacin razane A'A ya miƙe…

3,309 words

A wani irin mahaukacin razane A'A ya miƙe tsaye, dan ABUBAKAR SALAHUDDEEN ba kowa bane face mahaifinsa da ya haifesa, AHMAD ABUBAKAR SALAHUDDEEN shi ne suke ce mishi A'A, miƙewa su Abba ma suka yi dan su taushe shi, saboda duk sun san mahaifinsa ne, miƙewa ita ma maman Ayla ta yi tana faɗin "Alhadulillah, Alhadulillah, Alhadulillah, Allah na gode maka da ka muna mini mutuwar Abubakar kafin na bar duniya, azzalumin, mugu, macuci, banso ka mutu a haka ba, na so ne ka mutu a walaƙance, wanda ko kare sai ya fika daraja, bakin shaiɗani". Tana magana tamkar wadda ta zare, da alama farinciki ne ya yi mata yawa.

Kwantar da Ayla a hankali daddyn Jelly ya yi tare da miƙewa yana faɗin "Mama lafiya me yake faruwa,? Menene tsakaninki da Abubakar kuma?". Nisawa ta yi tana ta uban murmushi wadda tun da ta zo gidan bata taɓa yin shi ba "Abdul Malik wannan Abubakar ɗin da kake gani ba mutun bane, shaiɗan ne yazo a siffar mutun, ba kuna tambayata waye uban Aliya ba,? To shi ne, shi ne uban Aliya". Tashin sense da ba'a saka miki date. Nan take kallo ya dawo kanta, gabaɗaya palo suka zuba mata ido, Ayla baiwar Allah sai zuba barci take yi, bata san me yake faruwa ba.

"Shi ne mahaifin Ayla kuma?" Cewar Abbi, "Kwarai kuwa shi ne uban Aliya, babu wata tantanma, bakin azzalumin, ai naso Aliya ta girma ta kai mishi kanta da kanta ne, idan ya isa yanzu kuma ya ce ba yarsa bace, ai da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, da ya tashi bani ita sai ya bani ita kaman uban nata sak, babu in da ta baro shi, lokacin da take cikin cikina, ya ce ba cikinsa bane, ni kuma nasan ba mazinaciya bace, ban taɓa zina ba sai da shi, bayan shi ni ban taɓa kusantar wani ɗa na miji ba, nasan cikinsa ne, amma ya ce ba nashi bane, ya barni cikin bakin azaba da wahala, saboda son kai irin nasa, to ga shi yanzu babu wanda ya isa ya ɗaga idanu ya kalli Aliya ya kuma kalli Abubakar ya ce ba ubanta bane, kama harta idanunsa bata bari ba". Tana magana tana murmushi yau zuciyarta fari tas.

Cikin dakiya Abbi ya ce "Dan Allah ki yi mana bayani dallah dallah yadda zamu gane, ya akayi ya zama mahaifin Aliya? Kun taɓa yin aure da shi ne?". Dariya ta yi kamar zautatciya, da alama ta cutu sosai na abin da ya yi mata, da alama yau farincikin ya zautar da ita baiwar Allah, bata jin komai yau sai murna, dan haka bata damu ba zata iya wangale komai yau, dan tasan ko bata faɗa yau ba, to dole gobe ta faɗa, dan dole mijin Ayla ya buƙaci jin tarihinta.

Dan haka nan take ta buɗe musu aiki mai gabaɗaya "Ni ban taɓa yin aure ba, Aliya shegiya ce kuma ga ubanta nan a gabanku yanzu aka gama labarai a kansa, yanzu ni bana jin komai a raina, ko yanzu na mutu hankalina ya kwanta, ABUBAKAR SALAHUDDEEN bakin azzalumin, kune kuke kallonsa kamar mutumin kirki, saboda ya sanya fatar ɓauna ya lulluɓewa duniya laifukan da yake aikatawa, da Abubakar da Farooq wlh ko sun tuba sai sun ɗanɗani azaban Allah, dan kuwa akwai da yawan al'umma da suka mutu ta sanadiyarsu, waƴan nan azzaluman guda biyu, wlh sai Allah......" Bata kai karshen maganar ba A'A ya ɗaga hannu zai zabga mata mari, cak ta riƙe hannunsa tana kare mishi kallo.

"Saboda ina faɗar gaskiya a kan ubanka shi ne zaka mare ni? To kai kanka ka kalli kanka da kanka ka kalli Aliya dake kwance tana barci zaka iya banbanta fuskarka da tata ne? Bari ka ji idan kayi kuskuren marina, wlh, wlh, wlh, sai na kwantowa gabaɗaya juri'arku ruwan da ba zaku iya tsayar da shi ba, wlh sai na bankaɗo dukka laifukan ubanka da ɗan uwansa wa duniya, sai ya zama baku da idanun fita ku kalli jama'a saboda kunya, wasunku ma bakin cikine zai kashe su, idan kuma kace ba haka ba to Bismillah zaka gane shayi ruwa ne wlh, dama na rufe ne dan saboda kada ya kashe mini ƴa ta, na ɓuya ne dan kada ya kalli Aliya ya kasheta, shiyasa ban fito na nunawa duniya ɓarnar da suke yi ba, amma yanzu kabi a hankali!!". WANNAN SHI NE TASHIN HANKALI, BABBAR MAGANA.

Wani irin azababben kululun bakin cikine yasa A'A zubewa kasa tamkar gawa baya numfashi, kansa su Abbi suka yi suna ambatar sunansa, amma ina ko motsawa bai yi ba, ruwa Irfan ya ɗauko mai sanyi a fridge ya zo ya zuba mishi, amma ina ko motsi bai yi ba, daga karshe dai suka kwashe shi zuwa asibiti dan ceto rayuwarsa.

Ita kuma maman Ayla sama ta haura ta nufi ɗaki abinta, dan yau zuciyarta fes, Aunty kam taga tashin hankali yau, Hanan kuwa tun da aka fara hayaniyar ta bar palon, ta koma bedroom nata, dan bata son hayaniya ita ma,. Yanzu babbar abin tambayar a nan shi ne, a ina maman Ayla ta san mahaifin A'A? Menene yasa kuma ya ce ba cikinsa bane? Akwai lauje cikin naɗi, amma muje zuwa, zata warware mana komai ta bamu labarin yadda akayi komai, yanzu dai bari mu leƙa gidan Lion dan ganin wani hali suke ciki, wata kila kafin mu dawo wannan family sun ɗan sami kwanciyar hankali.

Misalin karfe 8 na safe, shirye suke cikin shiga iri ɗaya, sai dai wandon Areef ya fi shiga kalar brown sosai, na Aseef ya yi light, zaune suke a garden da alama dai shirin zuwa wani wajen suka yi, zubawa Aseef dara daran ash eyes nasa ya yi yana kallon yadda fuskarsa take wani kyalli, da alama yana cikin farinciki over, sai aikin latsa waya yake yi.

"Wai Aseef yana ga sai wani fresh kake yi ne? Seriously Naija ta karɓeka kai da Lion, sai wani kyalli face naka take yi, zo ka gaya mini me sirrin ne?". Bai ɗagoba, yana ta faman aikin latsa waya, sai murmushi yake yi Heartbeat ta yi kira. "Kana ji Areef, Heartbeat ce ta yi mini ciki, shiyasa kaga nake wannan kyan". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa dan Akila ta ce yazo yanzu. Areef ya gama fahimtar tun da Aseef ya fara soyayya ya dawo mara mutunci, da an yi mishi magana zai shere mutane, ko kuma ya mayar musu da amsar iya shege, yanzu me na wani cewa wai heartbeat ce ta yi mishi ciki daga tambaya? Gaskiya abin da ban haushi.

Yana can yana tunani sai ya ji tashin motar ɗan uwan nasa, alamar da gaske barin gidan zai yi, tafiya zai yi kenan, miƙewa ya yi da sauri ya nufe shi dan tare zasu je su gaida Ammie ya kalli heartbeat ɗin shi ma.

Lokacin da ya isa wajen, Aseef ɗin ya kashe motar ya fito zai nufi cikin gida, "Ina kuma zaka je mu tafi mana?" Ɗan juyowa ya yi yana faɗin "Yauwa Areef zo dan Allah, zo muje ka kallah wani abin". Ba musu ya bi bayansa, kai tsaye ɗakin da Jehan take suka nufa, ita kuma Rimsha, sai zuba barci take yi abinta, shi ma Lion haka, da alama dukkansu a tsananin gajiye suke.

Da sallama ya shigo cikin ɗakin, tana zaune a bakin gado ta farka, tun da Areef ya ɗaura idanunsa a kanta ya ce tabbas gaskiyar Aseef ne, duk yadda aka yi wannan jinin Uncle Hosain ce, akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakaninsu, dan kamar ta yi yawa, amma bari su je wajen heartbeat su dawo, tun da Rimsha tana nan zata warware musu komai ai.

Sannu suka yi mata, sai binsu da idanu kawai take yi, tana mamakin me kuma ya kawota gidan Turawa? Ko dai a kasar turai take ne? To yaushe a ka kaita can? Iya saninta a Nigeria take. Ganin taki yin magana ne yasa Areef ya ce "Kila bata magana ne, yanzu dai muje mu dawo, zan gayawa sister ta kula da ita kafin mu dawo sai mu san abin yi". Okey Aseef ya amsa, ya kuma ji matsananci daɗi da Areef ya yarda da cewa tabbas tana da alaƙa da uncle ɗin su, ya yi murna da hakan, juyawa suka yi suka fice daga ɗakin zuwa na Rimsha, ganin sai zuba barci take yi ne yasa Areef ya rubuta massage a wayarta a kan idan ta tashi akwai bakuwa dake ɗakin Imran, ta ɗan taimaka mata kafin su dawo, daga haka suka nufi waje dan su je wajen heartbeat, Lion kuwa tare suka yi sallar asuba da shi, dan haka sun san yana lafiya yana barci, sai ba su shiga ba bare su tashe shi suka wuce.

Sai misalin karfe 9 Rimsha ta farka daga barcin gajiya da take yi, da kyar ta sauko kasa ta nufi toilet dan yin wanka.

A gurguje ta yi wanka tare da shiryawa cikin kananan kaya ta fito da nufin ta duba su Areef dan su ci abinci yunwa take ji, ganin babu kowa a gidan ne yasa ta dawo cikin ɗaki ta ɗauki wayarta dan ta kira Areef ɗin, a nan ne ta ci karo da sakon da ya ajiye mata na bakuwar da suke da ita, fasa kiran nasa ta yi ta ce bari ta fara duba bakuwar tana zuwa, fitowa ta yi ta nufi bedroom ɗin.

Bakinta ɗauke da sallama ta shiga, a sukawane ta sanya hannu tana murje idanunta dan ta tabbatarwa da kanta abin da take kalla gaskiya ce ko ba gaskiya bace, ita ma Jehan ɗin a razane ta miƙe tsaye tana mai murza idanunta dan ta tabbatarwa da kanta ba mafarki take yi ba.

"Jehan". Rimshar ta ambaci sunanta, tare da tafiya da gudu ta rungumeta, ita ma rungumeta sosai ta yi suka shiga kewaye ɗakin suna ruwan hawaye. "Rimsha dama kina raye?" Ta faɗa tana kwallah. "Ina raye Jehan, ina raye, dama kema kina nan Kaduna? Shi ne Sadiq bai gaya mini ba".

"Rimsha bana Kaduna, dogon labarine zan baki daga baya, yanzu dai ina su mummy?" Ta yi maganar tana raba jikinsu. "Ban san in da suke ba, daddy kawai na san in da yake". "What daddy kuma?!!" Ta faɗa tana zaro idanu kamar zasu faɗi kasa, "E Jehan daddy, yana nan, yana raye bai mutu ba". Zata yi magana kenan suka ji jiniyar motocin ƴan'sanda ya karaɗe ko'ina a cikin anguwar, da alama jiga jigan ƴan'sanda ne, da alama kuma suna da yawa, dan motocin nasu manya ne, jiniya ya karaɗe ko'ina tamkar filin yaki suka nufa, kallon juna suka yi, "Zo mu je waje mu gani menene". Cewar Rimshar, da yake Jehan bata da tsoro ko kaɗan a fili, ga karfin hali da dakiya sai ta bita suka nufi waje dan suga menene.

Daga bakin kofar palon kasa suka tsaya suna hangen gate ɗin gidan, amma kafin su fito sai da Jehan ta sanya doguwar rigar Rimsha, dan idan baku manta ba, ba wani kayan arzikine a jikinta ba, daga three quarter sai ƴar vest, shiyasa ta ce ba zata fita a haka ba duk da bata san su waye ne a gidan ba, sai da Rimsha ta ɗauko mata doguwar rigarta ɗaya, ta sanya sannan suka nufo wajen.

Can suka hango gateman yana dirama da ƴan'sandan a kan lallai ba zasu shigo cikin gidan nan ba, su kuma sun kafe sai sun shigo, daga Rimsha har Jehan basu san menene yake gudana ba, garama Jehan bata yi mamakin ganin ƴan'sadan ba.

Waya gateman ɗin ya yi wa Lion da ƴan'sandan suka matsa, a lokacin shi ma ya tashi daga barci, ya fito daga wanka kenan, yana tsaye a gaban mirror ɗaure da towel a kugunsa, umarnin ya bawa gateman ɗin da ya bar ƴan'sandan su kama yarinyar tun da a kan aikinsu suke, shi yasan menene doka, dan sune doka, sune suke tsawatarwa da abi doka, tun da sunce kisan kai ta yi to su kamata, kuma sai ya ji dalilin da yasa su Aseef zasu kawo mishi mai laifi gida. To fa kada ku ga laifinsa, a kan dai'dai yake, doka ce dole a matsayinsu na masu doka su girmama dokan kafin na kasa da su subita, ba zai ce kada su kamata ba tun da shi bai san wacece ita ba, bai kuma san gaskiya a kan me ya faru ba, kuma kunga news ɗin da suka baza a gari a kan daɓa wa ABUBAKAR SALAHUDDEEN ɗin wuka ta yi a ciki, kuma ko su Aseef ne zasu yarda da yes ta daɓa mishi ɗin, dan kuwa a kan hanya suka ganta ana binta, basu san daga ina ta fito ba, sai dai idan sun yi bincike mai tsanani ne suna iya gane gaskiya, amma yanzu dai duk yarda zasu yi akan abin da ta yi kenan, babbar magana. WANNAN ABIN DA ƊAURE KAI YAKE AMMA MUKE ZUWA, DAN JIN DALILIN DA YASA AKA JUYA LABARIN YA KOMA KARYA, SUKA BINNE NA GASKIYAR.

Shigowa police biyu suka yi, mace ɗaya namiji ɗaya, in da su Jehan suke tsaye suka nufa, ko motsi Jehan ɗin bata yi ba, babu kuma alamar tsoro ko ɗigo a ranta, ita kuwa Rimsha ta tsorata sosai, sai ambatar sunan ta take yi tana tambayarta ko lafiya, su koma cikin ɗaki, amma ina ko motsawa Jehan ɗin bata yi ba, kamar wadda ta taki wata tsiya.

Kamata macen ta zo ta yi tana faɗin "Wuce mu tafi". Kankameta Rimsha ta yi tana kuka tana faɗin "Dan Allah kada ku tafimin da ita, wlh bata aikata laifin komai ba, dan girman Allah ku sake mini ita, wayyo Allah na, nashiga uku, daddy kazo ka hanasu tafiya da Jehan, zasu tafi da ita". Jehan ɗin kuwa, ko a jikinta tamkar ba ita ba, kamar bata san hukuma ne suka zo kamata ba, tsakaninta da Allah Rimsha take kuka kamar ranta zai fita, haka suka tafi da Jehan ɗin tana ji tana gani, da gudu ta koma cikin gida ta ɗauki wayarta dan ta kira su Areef ko daddynta, har wani jiri take gani, dama ga yunwa.

Number Areef ta kira, bugu ɗaya ya ɗauka, a haukace ta kasa natsuwa ta fara gaya mishi abin da yake faruwa, zaro idanuwansa ya yi yana tambayarta dama tana da sister ne? Kenan gaskiyar Aseef da ya ce Sister ta ce?. Muryarta na rawa ta gaya mishi e tana da sister, su biyu daddy ya haifa, cikin kwanciyar hankali ya ce "To ya isa haka kuka, ba dai ƴar uncle bace? To kada ki ji komai dole ma su dawo da ita, bari na dawo muyi magana da Lion, wai laifin me ma tayi musu ne?" Da kyar ta iya furta "Ban sani ba, ban sani ba yaya Areef, kawai sun tafi da ita ne, kuma nima basu gaya mini abin da ta yi musu ba". "To shikenan ya isa ki kwantar da hankalinki, ina nan juyowa yanzu, na ma fasa zuwa wajen Heartbeat ɗin, Aseef zai je shi kaɗai, bari na hau abin hawa na dawo". Okey ta amsa mishi da shi, katse kiran ya yi dan baya son jin kukanta, Allah sarki bawan Allah.

Ɗaura wayar saman bedside drawer ta yi tare da kifa kanta da jikin gado tana mai cigaba da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, duk da ta yarda da Areef, tasan idan ya ce abu to zai aikata, sai dai hankalinta ya kasa kwanciya ne dan tasan idan Lion bai bada goyon baya ba, shi ma Areef ɗin dole ya hakura, abin da bata sani ba shi ne, His excellency dukkansu kakansu ne, suna da damar su ce mushi ga abin da suke so ya yi musu, sai dai wani hanzari ba gudu ba, abin da ya shafi doka, shi kanshi his excellency sai ya nemi jin ta bakin Lion, sai abin da ya yanke zasu yi amfani da shi, babbar magana, akwai kura fa.......

A wannan hali Areef ya shigo ya sameta, ko kaɗan bai ji daɗin ganin tana kuka har haka ba, rarrashinta ya fara yi tare da yi mata alkawarin kada ta damu dole sisterta zata fito da izinin Allah, amma bari ya yi magana da Lion zai je police station ɗin yanzu da kansa dan ya ji laifin da ta aikata da har zasu kamata, idan ma laifin babba ne to ya yi mata alkawarin zai tsaya tsayin daka ya yi bincike a kan case ɗin sai in da karfinsa ya kare, ma'ana sai in da hujjojinsa suka kare, dan yasan Lion ba zai taɓa tallafawa rashin gaskiya ba, duk wuya duk daɗi yana bayan gaskiya.... TOFA GASKIYA A WANNAN LAMARI BINCIKO GASKIYA BA KARAMIN WAHALA BANE A WAJEN AREEF, DAN JEHAN BATA DA SHAIDAR BA'A KAN HANYA TA KASHE ABUBAKAR SALAHUDDEEN BA, KUMA SUN ƊAURETA TA YADDA FITA ZAI YI MATA WAHALA, DOLE TA KAWO SHAIDAR A GIDA TA KASHE SHI GA KUMA DALILINTA, SAI DAI KUNA GANIN JENAN ZATA IYA DA WANNAN SHARI'AR? ZATA IYA KAWO SHAIDAR KUWA?

Da kyar ya lallaɓata ta yi shiru, miƙewa ya yi ya nufi bedroom ɗin Lion,. Zaune saman sofa ya isko shi yana.......

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*

E45-46💋

Da kyar ya lallaɓata ta yi shiru, miƙewa ya yi ya nufi bedroom ɗin Lion,. Zaune saman sofa ya isko shi yana latsa waya, kusa da shi ya zauna, cike da kulawa ya ce "Good morning". Shiru bai amsa mishi ba, dama ya san ba amsawar zai yi ba, dan haka sai ya cigaba da cewa "Zanje police station na dawo". Jinjina mishi kai ya yi alamar okey ya ji, "Idan na dawo zamu yi magana da kai". Nan ma jinjina mishi kai ya yi, ya kuma barshi ya shiga case ɗin ne dan ya gano Jehan ƴar Nawazudden ce, sai dai ko da take ƴarsa idan har bata gaskiya, to shi babu ruwansa, ba zai shiga rigimar ba, yanzu kuma ba zai yi bincike a kan case ɗin nata ba, dan a kan na babanta yake har yanzu tukunnan, da saura bai kammala ba, wani sabon babi ma ya buɗe a kan binciken nasa, idan baku manta ba, baya haɗa abubuwa biyu, ko wanne da lokacin yinsa, idan ya fara sai ya kammala yake capko wani, shiyasa bai damu ba dan Areef ɗin zai shiga, saboda shi ba zai shi ga ba sai ya gama wadda yake kai, ya kuma lura ana son nunawa yarinyar fin karfi ne, shiyasa ya kyasu da Areef ɗin.

"Me yasa ka yin faɗa jiya? Kuma da waye kuka yi faɗar?" Ya yi maganar ba tare da ya ɗago da kallonsa ba, "Waƴan da suka biyo yarinyar ne suka nemi yi mini ba dai'dai ba, shi ne na taka musu birki". Shiru ya yi tamkar ba zai sake yin magana ba, can kuma sai ya ce "Yana da kyau ka dai'na wasa da ciwon nan naka, ka san me zai iya biyowa baya idan har baka bari wajen nan ya warke ba, wajen zai iya ci ya tafi kai tsaye ya huda zuciyarka, yana da kyau ka kula sosai".

Jinjina mishi kai ya yi, dan shi ma ya sani, tabbas idan ya yi wasa da wannan ciwo, to rayuwarsa tana cikin babbar haɗari, sai dai fa ko mutuwa zai yi sai da ya mutu amma babu wanda ya isa ya taɓa Aseef a duniyar nan ya kyale shi, da wani suka daka zai iya kawar da kai, amma Aseef ba zai taɓa yiwuwa ba, sun mari kyakkyawa kuma lallausan fuskar da bata taɓa shan mari ba, da yake shi Areef ɗin bai san da cewa Lion ya taɓa marin Aseef ɗin ba, so yana ganin ai babu wanda ya taɓa kusantar wannan kyakkyawar fuska ko da sunan wasa da sunan zai mara.

Readers Also Read