Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 59

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 59

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 59: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 59. Ganin shi ne ba karamin ruwan mamaki ta sha…

3,339 words

Ganin shi ne ba karamin ruwan mamaki ta sha ba, tunani ta fara yi a kan yaushe ya zo garden ɗin kuma? Bata san tun karfe 9 yana wajen ba, kai kallonta saman jacket nasa dake rufe da jikinta ta yi, ba ƙaramin daɗi ta ji ba, da yake zuciya bata da kashi, sai ta ce yaya Saif yana da kirki, har ta manta abubuwan da suka faru a baya, zuba mishi idanu ta yi tana kallon yadda yake barci cikin kwanciyar hankali, Allah ya yi halitta, kyau iya kyau, tsabar rashin ji irin nata sai ta kai hannu ta shafi kumatunsa, kada ku manta bashi da nauyin barci, tun motsinta na farko da ta yi lokacin da ta yi miƙa tana son juyawa kafin ta farka kenan, to motsin nata ya farkar da shi, sai dai da yake barcin yana kan shi sosai ne sai bai buɗe idanu ba, ya cigaba da lumshe su dan kada barcin ya watse mishi.

Daga ita har shi sai da suka ji wani irin yarrrrr a jikinsu lokacin da ta shafa lallausa kuma kyakkyawar kumatunsa, sai dai ko motsawa bai yi ba, hannunta na kerma saboda rashin ji sai da ta sake kai hannu saman dark black curly hair, shafawa ta yi a hankali har zuwa sajensa, a hankali ta gangaro da hannunta zuwa saman lallausan laɓɓansa, tana ɗaura hannun nata a lips ɗin nasa caraf ya cafke hannun nata ba tare da ya buɗe idanu ba, ba ƙaramin razana ta yi ba, a zafafe ta yi yunkurin sauƙa daga saman sofar ta gudu.

(to ki gudu ki je ina? Ba kin iya neman bala'i ba? Baki jin magana ai sai ki tsaya ayi wace za'ayi)

Riƙe hannun nata da kyau ya yi tare da sauko da kansa sai tin face nata, a hankali ya waro dara daran blue eyes nasa masu ɗauke da barci a saman razananniyar face ɗin tata, datse idanunta ta yi tana addu'ar Allah yasa kada ya ce zai dake ta, Allah yasa ya yafe mata, wai mema ya kai ta ne? Wani ɓangare na zuciyarta ne ya ce mata kyau mana, kyansa ya kai ki taɓa shi,.

"Open your eyes". Ya faɗa a sanyaye, ya yi maganar can kasar maƙoshinsa, da ni da ku dukka mun san idanun nata yake son kallo, suna matukar burgesa, izza ta hana shi ya nuna sun burge shi, dama duk wanda ya kalli sleeping eyes nata dole su burge shi, ga su dara daran farare tas kamar audiga, dole su ɗauki hankali dan idanun duniya ne, bare ma idan ta tsorata ta zarosu ai ba'a magana, zata sanya samari da ƴan mata faɗawa cikin kwata, dole idan ta tsorata ta burge mutun, ko dan kara zarosu da take yi.

Tsuke ɗan bakin nan nata ta yi tare da waro idanun nata a hankali, kai tsaye sai cikin nasa idon, ita tana bala'in son na shi idon, shi ma yana son nata, ɗan kawar da kallonta ta yi daga cikin kwayar idanun nasa zuwa saman lips nasa da suke red color sosai.............

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*

E47-48💋

Tsuke ɗan bakin nan nata ta yi tare da waro idanun nata a hankali, kai tsaye sai cikin nasa idon, ita tana bala'in son na shi idon, shi ma yana son nata, ɗan kawar da kallonta ta yi daga cikin kwayar idanun nasa zuwa saman lips nasa da suke red color sosai, ita dai a duniya wannan lallausa kuma kyakkyawan lips ɗin nasa suna bala'in burgeta, ji take yi kamar ta sa hannu ta taɓa, shi kuma ya zubawa idanunta kallo babu ko kyaftawa, kamar mai nazarin wani abin a tattare da ita.

Slowly ya dawo da kallonsa saman beautiful lips nata sa suke pink color, ga shi ta tsuke ɗan bakin nata alamar a tsorace take, "Me haɗinki da face na?" Ya faɗa can kasan maƙoshinsa, girgiza mishi kai ta fara yi tana faɗin "Babu komai". Wani irin yanayi ya ji yadda ta motsa lips ɗin nata, shi bai san menene soyayya ba, bayan kaunar TRIPLETS nasa bai san wani so ko kauna or tausayin wani ba, ita ce ta farko da ya fara tausayawa bayan TRIPLETS nasa, wannan yanayin da yake ji a jikinsa idan tana kusa da shi, yana danganta hakan da tausayin da take bashi, idan baku manta ba shi a budurwar Areef ma yake ɗaukarta, dan ba karya ya san ɗan uwan nasa yana sonta, sai dai fa ganin abin ma a hauka yake yi, yana ganin Areef bai san me yake yi ba da zai ce yana son ƴar yarinyar nan da bata wuce a goya ba, to me abin so a wajen?.

(A lallau Lion ya yi mugun raina Rimsha, wai bai san cewa Rimsha tsab za'a iya yi mata aure kuma ta zauna bane? Ya je Gombe ya ga ikon Allah, gombawa ayi hakuri gaskiya ce🤪)

Sake hannun nata da ya riƙe ya yi tare da mayar da kansa jikin headboard na sofar ya lumshe idanunsa, barci yake ji sosai, jikinsa duk a mace, ya kasa miƙewa ya shige ciki, idan kuma bai shiga ba, ita ma ba ta haryar da zata shiga. Saboda tsiya irin tata da kuma tsoron wajen da take ji, sai ta mayar da kanta a hankali saman cinyar tasa ta kwanta tare da kara jawo jacket ɗin nasa ta rufe jikinta da kyau tana shakar daddaɗar kamshin perfume nasa, wani irin farinciki na wuce misali ta tsinci kanta a ciki, sai sakin murmushi take yi abinta, yau gata a cinyar abin kaunarta, kai abin ba'a magana, idan baku manta ba, ranar da ta kwana a saman kirjinsa a Abuja bata cikin hayyacinta, tana tsorace sosai, so bata sani ba, yau kuma tana cikin hayyacinta.

A can cikin gida kuwa, mu koma baya kaɗan, lokacin da suka gama cin abinci, Areef ya ɗauki laptop ɗin Aseef ya kule cikin bedroom nasa yana bincike da ƴan dube dubensa na wasu bayanai da ya kwaso a kan Family'n Nawazudden ɗin daga laptop na Lion, shi kuma Aseef bedroom nasa ya koma.

Bayan ya haye saman gado, gabaɗaya bawan Allah ya rasa me yake yi mishi daɗi, duniya har wani juya mishi take yi, wayarsa ya jawo tare da fara kiran number heartbeat, dan ita ce kaɗai zata sanya shi farinciki a rayuwarsa ta yanzu, bugu ɗaya ta ɗauka, baiwar Allah ta ci kuka har ta godewa Allah.

Tana ɗauka wani kukan ta saka mishi, dafe kansa dake yi masa barazanar tarwatsewa ya yi, murya a dashe can ƙasa ƙasa ya fara magana "My heartbeat please and please ki yi shiru, idan ba haka ba, kina iya jefani cikin damuwar da zata iya yin sanadiyar rayuwata, ni kukanki ya fi zama mini bala'i a kan hanani ke da akayi, please ki daina kin ji? Kada ki ɗauka daɗin baki ne nake yi miki, duk abin da zai fito daga cikin bakina ki sani tsantsar gaskiya ce wadda babu mix ko ɗigo, na san idan ban same ki ba, mutuwa zan yi, yanzu dai ki yi shiru kin ji ko?".

Tsabar kukar da ta sha, voice nata sam baya fita sosai, da kyar ta ce mishi, "Wlh Heartbeat kukan ne yaki tsayawa, idan har na ce zan tsayar da shi sai yaki, hawayena sun ki dai'na zuba, kai'na ciwo yake yi mini sosai, komai ya tsaya mini cak, duniya gabaɗaya juya mini take yi". Miƙewa zaune ya yi tare da nufar wajen da ya ajiye key ɗin motarsa yana faɗin "To shikenan, yanzu dai kinci abinci ne?" Girgiza mishi kai ta yi tamkar tana a gabansa, "Baki ci ba?". Ya yi maganar tare da ɗaukar key ɗin motar ya fice daga ɗakin "E ban ci ba, Heartbeat ni fa ba zan iya cin abincin bane, ko na saka a bakina ba zai wuce wuyana ba".

Kitchen ya shiga, da kansa ya ɗebi abinci daga cikin na Lion ya zuba mata a cikin wani dankareren kula mai bala'in kyau, dan yasan dama Lion baya cin ko rabin abincin da ake zubawa a kular tasa, shiyasa ya ɗeba mata, spoon ɗaya ya ɗauko tare da fitowa ya nufi motarsa, da gudun gaske ya tada motar ya fice, a lokacin ita ma Rismha tana ɗakinta kenan tun da baya muka koma.

Sai rarrashinta yake yi a wayar ba tare da ya gaya mata yana zuwa gidansu ba, duk magana idan ya yi sai ruwan hawaye ya kara tsananta a fuskarta, ita kaɗai tasan raɗaɗin azabar da take ji, ba zata iya rabu da shi ba gaskiya. "Heartbeat wai ba zaki dai'na wannan kuka ba har sai kin saka ni yi nima ko?". "Kayi hakuri zan dai'na, amma ko na goge hawayen sai wasu sun zubo ne". "Okey to fito gani a waje". Ya kai karshen maganar tare da yin parking na motarsa a ɗan nesa da gidan nasu.

Zubur ta miƙe daga kwanciyar da take, nan take hawayen nata suka kara tsananta, dirowa kasa ta yi daga saman gadon wayar tana manne a kunnanta, kayan barci ne a jikinta, riga da wando ne masu laushi launin brown color, suna da bala'in kyau ba kaɗan ba, hijabi ta ɗauko zuwa gwiwarta ta sanya a jikinta tare da fitowa ta nufi bedroom ɗin Ammie, har lokacin tana ruwan hawaye, ba ɓoye ɓoye ta sanar da Ammie ga Aseef ya zo zata je wajensa, Allah sarki uwa da ƴa, ita kanta dama ta shiga damuwa matuka a kan halin da ƴar tata ta shiga, dan haka sai ta yar je mata akan ta je suga juna, sai dai kada ta jima dan taga Abba ya kusa dawowa, dan ma ya biya wajen Abbi ne ai da ya jima da dawowa, idan ya dawo ya sameta a waje da Aseef kuma zai yi faɗa sosai, dan ya gaya musu ya yi mata miji, to ta amsa mata da shi, ta juya har lokacin sai ruwan hawaye take yi, binta da kallo Ammien ta yi tana mai matukar tausaya mata, dan tasan wannan aure nata da Irfan babu mai rusa shi, yanzu ma ta barta ta je wajen Aseef ɗin ne dan tana da yakinin idan ta je zata rage damuwa, zata samu ta yi barcin daren yau.

Tun da ya hango fitowarta daga gida shi ma ya fito daga cikin motarsa, jingina da jikin motar ya yi tare da zuba mata idanu yana kallon ta, wani azababben kaunarta ne yake kara ninku mishi a cikin farfajiyar zuciyarsa, har ta kariso gabansa ba tare da ya sani ba, yana can yana tunanin mafita, zazzakar muryarta dake dashe sabida kuka ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya faɗa. "Sannu da zuwa ina wuni?" Shi ne abin da ta faɗa.

Ganin har lokacin hawaye na a kan fuskarta ne yasa ya ce "Har yanzu baki dai'na yin kukan ba?" Kasa ta yi da kanta tana faɗin "Heartbeat na gaya maka kukan ne yaki tsayawa wlh, ko na goge hawayen sai ya dawo". Hannunta ya kama tare da jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, tun daga tsakiyar kansu har zuwa tafin kafarsu sai da suka ji wani irin shock, daurewa ya yi tare da ɗago haɓarta ya sanya kyakyawar farar hannunsa yana goge mata hawaye, tuni kukan nata ya tsaya cak, tun da ta faɗa saman kirjinsa ta nemi kukan ta rasa.

"To kinga na yanzu na goge miki hawayen dukka, kada ki bari wani ya fito kinji my rigimati?". Gyaɗa mishi kai ta yi alamar ta ji, nisawa ya yi yana tunani, a matsayinsa na namiji, dole shi ya ɓoye tashin hankalinsa da damuwarsa dan ya kwantar mata da hankali, idan ya nuna mata tsantsar bala'in da yake ciki abin zai yi mata yawa, to dole ya danne sosai.

"Me kike wani kallona haka?". Ya yi maganar a shagwaɓe dan ya mantar da ita damuwar da suke ciki, ɗan kwantar da kanta a saman kirjin nasa ta yi tana jan hanci bata ce komai ba, a hankali ya fara shafa bayanta kaɗan kaɗan, jin hakan yasa ta tashi daga jikin nasa cikin sauri tana koran shaiɗan ɗin da yake son ya shiga tsakaninsu, bai damu ba dan ta tashi daga jikin nasa, dama shi burinsa kawai ta yi shiru ta dai'na kuka, to kuma ya yi nasarar tsayar da hawayen nata.

"Zo mu shiga cikin mota kin ji ko?" Da farko taki yarda, sai da taga kamar bai ji daɗin hakan bane yasa ta ce to su je, gidan gaba ya buɗe mata ta shi, bayan ya rufe sai ya zagayo ta mazaunin driver ya shiga, wutar dake kan titin unguwar tana haska har cikin motar ta su, kular abincin ya ɗauko daga gidan baya tare da kawowa tsakaninsu, zuba mishi idanu ta yi tana kallon ikon Allah, buɗe abincin ya yi, wani irin daddaɗar kamshin ne ya daki hancinta, da yake ita kam tana cin ire iren abincin a manyan restaurant da suke sayan abinci, sai bata wani damu ba.

Ɗiba ya fara yi yana kai mata sai tin ɗan bakinta, tun tana nokewa har ta saki jiki tana karɓa, sai zuba mata hira masu daɗi yake yi har ta ci abincin sosai ba tare da ta sani ba, tissue paper ya ɗauko ya goge mata baki tare da rufe kular bayan ya tabbatar ta ƙoshi, ruwa ya sake ɗaukowa a kusa da su ya buɗe ya kai mata sai tin ɗan bakinta, kallon shi ta yi, kashe mata ido ɗaya ya yi kafin ya ce "Wai har yanzu duk da na tura miki hoton mu mu dukka uku kin kallemu, har yanzu ina yi miki kama da su sosai ta yadda baki banbantamu kamar yadda kika ce da farko?".

Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "E wlh ni kullum na kalli hoton sai in kalli kamar mutun ɗaya ne a wajen, ido ne kawai yake banbanta ku, na rasa wlh, sai dai Lion ya fiku cika, kuma kaman ya fiku tsawo ma". Kai mata ruwan bakinta ya yi ta karɓa ta fara sha. "Kin san menene?" Girgiza mishi kai ta yi tana kan shan ruwan. "Da ni da su ko a cikin duhu Rimsha tana iya banbanta mu, mafiya yawan lokuta daddy da ya haifemu idan yana magana a palo da Areef dake cikin bedroom, idan na amsa daga cikin bedroom ɗin a madadin Areef, to wlh baya gane ni na amsa, basu rabe muryata da ta Areef, duk duniya dama Lion ne kawai yake iya rabe muryoyinmu, na sha ruwan mamaki lokacin da Rimsha ta iya rabe muryoyinmu a rana ta farkonta da ganinmu, to haka take banbanta mu ko a cikin duhu, wani lokaci idan na rufe mata fuska ta baya zaki ji ta ambaci sunana, idan na ce waye ya gaya miki Areef ne fa ba Aseef ba, zata kafe lallai dole ni ne ba Areef bane, , shi kan shi Areef ya sha ruwan mamakin banbanta mu da Rimsha take yi a cikin duhu, bare ma masoyinta Lion, bata haɗa shi da kowa ba, karfi da ya ji ta rabamu, ko cikin zolaya idan na ce mata Saif ne bayan na rufe mata ido, zaki ji tana cewa, kai ina GAR ya fi haka, kai in takaice miki kome kika yi wa Rimsha dan ki rikitata a kanmu sai ta rabe miki mu tsab wlh, na rasa wani irin baiwa ke gareta, shi ma Areef ya gwadata har ya gaji ya hakura, su uncle T duk basu rabeni da Areef idan nayi magana, amma ita ina raba mu take yi tsab".

Dariya ta kwashe da shi tana faɗin "Kai ai dole Rimsha ta yi muku farin sani kafin ganinku, kasan yadda take kaunar Lion kuwa? Hmm banga laifinta ba dan ta ce muku bata haɗa shi da kowa ba, ai kai ma ban haɗa ka da kowa ba, gaskiya sosai Rimsha akwai kwakwalwa na wuce misali, gata da natsuwa sosai".

Hannayenta ya riƙo bayan ya ajiye robar ruwan, tsareta da idanu ya yi yana faɗin "Wace Rimshar ce mai natsuwa? Sai dai idan wata Rimsha a gidanku, amma mu na gidanmu kamar battery ake saka mata, tana da fitina ga neman rigima wajen Saif, watara Allah sai ya sumar da yarinyar nan ina da tabbaci". Murmushi ta yi tana wasa da ƴan yatsun hannunsa masu bala'in ɗaukar hankali, "Duk abin da kaga Rimsha tana yi wa Lion ni na gaya mata wlh, ni na san cewa yaro mai kiriniya yana da saurin shiga rai, na san idan tana yawan shiga harkarsa tana taɓa mishi abubuwa bai aiketa ba, dole watarana ya ɗago ido ya kalleta, a kwana a tashi dole ya fara sonta, Allah Rimsha ta sha bakar wahala akan soyayyarsa, idan ba shi ta aura ba, wlh aurenta ba zai taɓa zuwa ko'ina ba, tun tana da 9 years a duniya take haukar kallon shi a Tv, ni nasan a yadda yake ɗin nan, ba zai yi saurin ɗaura hannunsa a jikin mace da sunan duka ba, shiyasa na bata wannan shawarar ko kuma in ce maka kullum nake kara bata hakan idan mun yi waya, ta dai'na jin tsoronsa, ta rinƙa taɓa mishi wasu abubuwa nasa ba zai taɓa dukanta ba, amma a nawa ganin da nake masa fa kenan, bacin haka, wlh Rimsha nitsatsiya ce sosai, kuma idan ka lura ai Lion ɗin kawai take yi wa rashin ji ɗin, to ni nake zugata".

Nisawa ya yi yana faɗin "Yes da wuya Lion ya ɗaura hannunsa a jikinta da nufin duka gaskiya, ko ni ai ba zan daki mace ba, to wai me ma zaka daka a jikin mace? Ka je ka sumar ko ka kashe ƴar mutane a banza, mace ai bata da wajen duka a jikinta, shi Lion ma ya ce faɗuwa ce babba ga namiji ya sanya hannunsa a jikin mace da sunan duka, yo Allah na tuba Lion da yake mari manyan zaratan maza su faɗi su suma ina ga Rimsha kuma? Ai idan ya mareta sai mutuwa, gaskiya ma ba zai yiwu ba, duka kam a'a ba zai daketa ba, idan ta cika matsa mishi dai, sai dai ya bata punishment irin su frog jump da sauransu". Ya kai karshen maganar tare da kai hannunta dake cikin nasa saitin ɗan bakinsa ya sumbata.

Kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "I really love my heartbeat, kece bugun numfashina, idan bake to babu ni". Buɗe tafin hannunta ta yi tare da ɗaura nasa hannun a saman natan, yazama kamar sun tafa da juna kenan, cikin shagwaɓa ta ce "Promise me that ba zaka taɓa barina ba duk wuya duk daɗi". Matso da fuskarsa daf da tata ya yi "I promised you that ko me wuya ko me daɗi ni naki ne, a kanki zan tsaya ba ja baya". Cool murmushi ta saki har sai da gaf teeth nata suka bayyana

Heartbeat ya ambaci sunanta a tsananin sanyaye, ita ma a sanyaye ta amsa mishi, "Fito da harshenki dukka waje bari na gani". Ba musu ta fito da ita, tana da tsawo sosai harshen nata, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya ce tom ta mayar, mayarwa ta yi tana tambayarsa menene yasa ya ce ta fitar, jan dogon hancinta ya yi yana faɗin "Sai gaba zan gaya miki dalili". Make kafaɗa ta yi a kan lallai bata yarda ba sai ya gaya mata ita dai, kara matsowa kusa da ita sosai ya yi har suna iya jiyo sautin numfashin juna, "Ba kin ce na dai'na irin maganar sai mun yi aure ba?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e, "To kin gani ki bari sai mun yi aure sannan zan gaya miki dalili".

Turo baki ta yi taso jin meyasa ya kalle mata harshe, amma ba komai ai, yanzu ma da ya ce sai sun yi aure tun da ta ce ya dai'na irin wannan magana, ta fahimci ina ya dosa, sai dai bata san me na'amar hakan ba, ta dai fahimci duk zancene da ya shafi ma'aurata.

Readers Also Read