Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 58

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 58

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 58: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 58. Cikin sauri ya riƙo hannun nata yana faɗin…

3,238 words

Cikin sauri ya riƙo hannun nata yana faɗin "To yanzu kuma me nayi da za'ayi mini rigima? Kin san fa jiya kin saka ni ciwon kai, Allah kin iya rigima sosai Heartbeat, idan Areef yasan kina sakani ciwon kai ba zai kyale ki ba, sai ya baki punishment, sai dai ni kuma ba zan yarda ba, da a hukunta mini ke ai gara a zaneni". Wani irin shock ta ji lokacin da ya matse hannun nata a cikin nasa yana magana, buɗe tafin hannunta ya yi yana shafawa a hankali kamar mai murza mata mai, yana yi yana magana cikin kwanciyar hankali abinsa.

"Kazo muje ka gaishe da Ammie tukun nan". Tsareta ya yi da idanu yana kallon lallausan lips ɗin nan nata, har ga Allah suna burge shi, kuma yana son yi mata kiss, amma saboda ya girmama al'adun Hausawa yasa ya daure, ya jure dan farincikinta. "To ni Heartbeat ki bari mana na kalle ki sosai kafin mu shiga ciki". Ya yi maganar a shagwaɓe sosai.

"Kai ko". Ta faɗa tana kama yatsun hannunsa da yake murza mata fatar cikin tafin hannunta da shi, "Wai kai ina ruwanka da hannuna ne?" Ɗan matsowa ya yi yana faɗin "Laushinsu daɗi yake yi mini idan ina taɓawa, shiyasa nake son in yi ta shafasu". Kallon so ta wurga mishi tana mai buɗe tafin nasa hannun ta ji nasa laushin ya yake da zai takura wa nata hannun.

Bawan Allah baya wani aikin wahala, kullum yana cikin hutu, soft skin nasa ma har wani sheki yake yi bare fatar cikin hannunsa, ai ba'a magana, akwai laushi sosai da sosai, ɗan murza fatar ta yi har sai da ya furta wash, sake shi ta yi tana faɗin "Naka hannun ma ae yafi nawa laushi, amma saboda neman rigima sai ka rinƙa taɓa mini nawa ko?" "Naki ne ko nawa?". Ya faɗa yana ɗan juyar da tsayuwarsa da kyau ya dawo suna fuskantar juna da kyau da kyau.

"Innalillahi My shagwaɓati me ya sameka a kumatu? Ya naga shatin yatsun wani kuma a face naka? Marinka aka yi?". A ruɗe take jero mishi tambayoyin, ba karya marin da ɗan'sandan nan ya yi mishi ya maru, wajen ta yi jawur kamar ka taɓa jini ya zuba, da yake tun da ya shigo bai juya da kyau bane yasa bata gani ba, yanzu kuma ya juya suna fuskantar juna da kyau, hakan yasa ta gani. Bai ɓoye mata komai ba ya gaya mata abin da ya faru da kuma wanda ya mare shi, tambaya ɗaya ta yi mishi shi ne Lion ya sani, girgiza mata kai ya yi alamar a'a tare da sake riƙo hannunta yana faɗin "Ni ki dai'na maganar, ai Areef ya hukunta su, bana ma son Lion ya ji, dan nasan ba zai taɓa kyalesu ba, yanzu dai ki rufe idanunki bari na baki surprise".

Ba musu ta rufe idanun nata, komawa cikin mota ya yi, jim kaɗan ya fito tare da dawowa gabanta, mai gadi dai ya mayar da su kamar wasu Tv, yana kallon ikon Allah, sai kallon Aseef yake yi, yau yaga Bature, fari tas kamar madara. Zube gwiwowinsa ya yi a kasa a gabanta tare da buɗe wani ɗan akwai mai ɗauke da dankareren diamond ring, sai kyalli yake yi yana ɗaukar idanu, baki mai gadi ya sake yau yana kallon American film a zahiri.

Umarni ya bata a kan ta buɗe idanunta, ba musu ta warosu a hankali, kai tsaye dai kan zobben ta sauke idanun nata, da sauri ta mayar da kallonta kan face nasa, cool murmushi ya sakar mata tare da ciro ring ɗin ya kama hannunta ya sanya mata a yatsanta na kusa da babba na tsakiya, wani irin sihirtaccen kyau hannun nata ya kara yi, kai hannun nata saitin ɗan bakinsa ya yi tare da sumbatarta, wani irin shock suka ji dukkansu biyu, miƙewa ya yi tare da jingina da jikin motar yana lumshe idanu.

"My shagwaɓati ka kawo naka ring ɗin na saka maka mana?". Ta faɗa tana kai hannun nata kusan bakinta ta sumbaci zobben, "No ni bana sanya ring ai, amma zan saka na auren mu, a kasarmu idan ka saka ring yana nufin kai mai aure ne, abin da ya sanya kema na saka miki, dan naga ku a nan kuma sawa ne, naga akwai a hannun our Rimsha, to shiyasa kema na saka miki, amma ni a'a bana ma sanyawa, baya burgeni, chain kawai nake sakawa, shi ma da ne yanzu bana sakawa sai na mummynmu ne kawai a wuyana". Ya kai karshen maganar tare da fito mata da sarkar mum ɗin nasu dan ta gani, zubawa sarkar idanu ta yi tana kallon shi, tabbas ta taɓa ganin irin wannan sarka sak, babu banbanci ko kaɗan, to a ina? Shiru ta yi tana tunani, shi kuma mayar da sarkar ya yi yana faɗin "Ina su Prof?" Suna ciki ta bashi amsa yayin da take ƙoƙarin tunani wai daga ina ta taɓa ganin wannan sarka, sai ya yi mata kamar a hoton kakansu Naurat ta taɓa gani, yes tabbas a wuyar Naurat ta taɓa ganin wannan sarkar, akwai wani hoton Naurat ita da kanwarta autarsu, so dukkansu ita da kanwar nata suna sanye da irin sarkar nan.

"Okey muje bari na gaishe da Ammie sai nazo na koma ko?" "Koma wa kuma?" Ta tambaya tana turo baki, hannu yasa ya shafa lips nata na kasa yana faɗin "Wai ke bana ce ki dai'na turo mini ɗan bakin nan ba? Very soon zan sha kayana ki cihaba", Kama hannun nasa ta yi tana kallon kyawawan fararen yatsunsa, ga farcensa sai kyalli suke yi farare tas, ga wani kayatatcen brawn ɗin gashi kwance a saman yatsun nasa, haka zalika hannunsa, gabaɗaya kyawawan kwantatcen gashi ne sosai a wajen, "My shagwaɓati wlh yatsun hannunka suna yi mini kyau over". "To meyasa zaki wahalar da kanki wajen cewa suna yi miki kyau bayan mallakinki ne?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da sumbatar yatsun nasa tana murmushi, wannan sumbata har cikin ransa ya jita, lumshe idanu ya yi yana mai sauke nauyayyar ajiyar zuciya.

"Muje ko?" Ta faɗa tare da sakin hannun nasa ta yi gaba, zura hannayen nasa ya yi a cikin aljihunsa ya bi bayanta yana kallon yadda take tafiya a nitse kamar bata son taka kasa, ta kara tafiya da imaninsa ba kaɗan ba.

Bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin palon, zaune ta isko Ammie, Imran, Akil suna hira, iso ta yi mishi tare da wucewa kusa da Imran ta zauna, karisowa ciki ya yi, Imran ya fara miƙawa hannu kafin Akil, da yake shi bai san al'adar Hausawa ba sai nasu ya sani, sai ya miƙawa Ammie ma hanu dansu gaisa, bata yi mamaki ba, suma su Imran basu yi mamaki ba, sunma ga kokarin sa da bai ce zai rungumi Ammien bama, dan su runguma a wajensu kamar nuna murna da ganin mutun ne ba wani abin ba, Akila dai ta sha mamaki, kuma ta yi nadama da bata gaya mishi yadda zai yi wa Ammie ba idan ya shigo.

Ba musu Ammie ta miƙa mishi hannu suka gaisa dan ita ma mijin nata Baturen ne, duk kanwar ja ce, Bismillah ta yi mishi da ya zauna saman sofa, zama ya yi kafin su fara ƴan tattaunawa, a haka Abba ya sauko kasa ya same su, ya yi shirin zuwa office, Umaisha tana kitchen Jelly tana barci, Umaishar ta ce lallai sai ta taya Ammie aiki, shi ne ta shiga tana ɗan goge goge.

Ganin Abba yasa ya miƙe ya bashi hannu, ba musu Abba ya miƙa mishi hannu suka gaisa, ɗan rungume Abban kaɗan ya yi kamar yadda suka saba yi a kasarsu, shi ma Abban mayar mishi da martanin hakan ya yi dan duk ɗaya ne, da gani ba tambaya, komawa ya yi ya zauna abinsa yana kallon heartbeat nasa, sai murmushi take yi.

Abba ne ya tambayi Imran a ina suka samo Bature ruwansu mummynsu wato Na'urat kuma? Dan duk ɗaya ne, kai tsaye Imra ya ce mishi saurayin Akila ne, shiru Abba ya ɗan yi kafin ya ce " Saurayin Akila kuma?" Jinjina mishi kai Imran ɗin ya yi ba tare da ya wani damu ba. "Akila kam ai na riga da nayi mata miji". "What?!!" Imran ya faɗa tare da miƙewa, ita kan ta Ammie sai da ta miƙe, Akil ma dai tambaya ya yi akan miji kuma,? Shi ma Aseef miƙewa ya yi da yake da turanci suka yi maganar.

"Abba ban gane ka yi wa Akila miji ba? Waye ka bata to? Ka yi mana bayani". Cewar Imran, yana magana yana kallon Aseef da ya tsaresu da idanu, yasan idan hakan ta tabbata lallai akwai yaki kenan, babbar magana.

"E Imran kamar yadda ka ji dai haka ne, kwana uku da suka wuce Deen da Maik sun same ni a office akan maganar Irfan da Akila suna son junansu, na yi murna sosai, na kuma bawa Irfan aurenta, Friday mai zuwa za'a ɗaura aure, ranar Wednesday gabaɗaya iyalan gidan Deen zasu tattaro su dawo nan dan ayi komai waje guda, sai bayan biki zasu koma, Batula tana zuwa jibi, mantawa nayi ban gaya muku ba, amma an gama shirya komai ai". Tashin sense da ba'a saka mishi date, zube gwiwowinsa a kasa Aseef ya yi, nan take hawaye suka fara wanke mishi fuska cikin sanyin murya ya ce "Please Abba kada ka yi hakan, am very sure heartbeat bata son Irfan, ni ba zan iya rayuwa ba idan ka hana ni ita, please and please ka taimake mu, na san ita ma heartbeat ba zata iya rayuwa da kowa ba sai ni, wlh muna son junanmu over, ni kayi mini duk abin da zaka yi mini amma kada ka hanani auren Heartbeat, ba zan iya jurewa ba, ba kuma zan iya ɗauka ba". Yana magana hawaye wani na bin wani, Ammie bata san lokacin da hawaye ya fara bin kuncinta ba ita ma, dan dole Aseef ya bawa mutun tausayi a yanayin yadda yake magana.

Zubewa kasa ita ma Akilar ta yi, tana kuka tamkar ba gobe, hawaye wani na bin wani "Abba wlh ni bana soyayya da yaya Irfan, ni Heartbeat nake so, dan Allah kada ka aura mini yaya Irfan, Allah bana son shi". Imran sarkin saurin kuka tuni ya fara yi musu hawaye, dan shi yasan menene soyayya, yasan wahalarta, ya kuma ɗanɗana, Akil kuwa tunani yake yi tun da Akila ta buɗe baki ta ce bata son Irfan to gaskiya bai ga dalilin da zaisa a aure mata shi ba, aure ba abin wasa bane, ba abu ne da ake yin shi shekara ɗaya ko biyu ya kare ba, rayuwa ce ta har abada, zama da wadda baka so yafi komai wahala da azaba a duniyar nan, dan haka iyaye ku ji tsoron Allah ku dai'na yiwa yara dole, zama da wanda zuciya bata so babbar barazace ga rayuwar yarinya, ya kan sakata ta yi abubun da kowa zai zo ya yi dana sani daga baya, to maganin bari kada asoma, ku sani dai Allah zai tambayeku.

"Abba dan Allah ka duba wannan magana da kyau". Cewar Imran. "Imran ya kake so na yi to? Deen fa nace maka, bappanku Deen fa!, Shi da kansa ya zo ya nemanwa Irfan aurenta, yana da damar da zai aurawa Irfan ɗin ita ko ban sani ba, ba shi ya ɗaura muku aure ba? Nasan time da ya ɗaura muku ne? Ai ban sani ba, to haka ita ma Akilar zai iya aurar da ita ba tare da sanina ba, kuma bani da abin cewa, amma duk da haka ya wanke kafa ya zo ya nemi auren ta, na kuma ɗauka na bashi, yau saura kwana takwas kenan a ɗaura auren, kenan so kuke nace mishi na fasa bashi wani na waje zan bawa ne ko yaya?". Shiru palon ya yi, ban da shasshekar kuka Heartbeat and Heartbeat babu wani abin da yake tashi, su Imran dai sun rasa bakin magana, sun san ba ta yadda za'ayi Abba ya ce wa Abbi ya fasa bawa Irfan wani daga waje zai bamawa, hakan sam ba abune mai yiwuwa ba.

Suna tsaka da tunani basu ankara ba sai ganin Aseef suka yi ya sulale kasa sumamme, ihu Akila ta kurma ta yi kansa tana ambatar sunansa Heartbeat!! Heartbeat, kamata Akil ya yi ya rungumeta a jikinsa tare da bubbuga bayanta dan ta samu ta natsu.

Da gudu Umaisha ta fito daga cikin kitchen dan ta zo taga me yake faruwa ake ihu haka, Abba, Imran a zafafe suka yi kansa, sai kiran sunansa Aseef, Aseef Imran yake yi, amma ina shiru, ruwa Ammie ta ɗauko a fridge Abba ya karɓa ya tarbo a hannu ya shafa mishi a fuska, shi kuma Akil sama ya wuce da Akila dan kada ta karawa Aseef ɗin zafi a kan zafi, ga ciwo ga kuma kukanta, wucewa Abba ya yi yana faɗin "Ana jiransa a office tun ɗazun, bari ya je". Okey suka amsa mishi da shi, sauri yake yi sosai, kuma baya son tsayawa ne, dan baya son ganin halin da Aseef da Akila suke ciki, saboda yasan duk wuya duk daɗi ba zai canza magana ba, ba zai iya hana Irfan ya ɗauki Akila ya bawa wani bare ba, amma fa har can kasar zuciyarsa shi ma yana son bawa ƴar tasa zaɓinta, amma ba dama ne kawai, bashi da yadda zai yi, jini ba karya ba.

Sai rarrashinsa Imran yake yi, amma ina yaki yin shiru, sai ruwan hawaye yake yi bawan Allah, ba zai iya jure rashin Akila ba, ita ɗin ta zame masa wani ɓari na rayuwarsa, ita ce first love ɗinsa,. Sai da Imran ya ce ya yi mishi alkawarin zai shawo mishi kan Abba, duk wuya In Sha Allah Akila matarsa ce, sannan ne ya ɗan hakura ya dai'na ruwan hawaye, ita ma Ammie karfafa mishi gwiwa ta yi a kan kada ya damu, da izinin Allah Akila tasa ce, tun da har ta furta bata son Irfan to kada ya damu zasu shawo kan Abba idan ya dawo, da haka dai suka samu suka lallaɓa shi ya daure ya hakura ɗin.

Imran ya ce su je ya tuka shi zuwa gida, okey ya amsa tare da cewa Imran ɗin dan Allah kada ya gayawa su Areef, idan ya gaya musu yasan Lion zai ce sai dai ya rabu da Heartbeat ɗin tun da haka ne abin, to dan haka kada ya gaya musu, okey ya amsa mishi da shi, da haka ya yi wa Ammie sallama sai hakuri take bashi suka nufi gida.

Yana komawa bedroom nasa ya wuce ya haye gado saboda tsananin ciwo da kansa yake yi mishi, bai kula kowa ba yau a gidan, yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, sai sauke ajiyar zuciya yake yi cikin barci, shi kuma Areef yana can yana faman bincike a kan case ɗin Jehan.

Da misalin karfe 8:30 na dare, bayan sun gama cin abinci, da kyar Rimsha ta ci abinci, nan ma har sai da Areef ya ɓata rai sannan ta yarda ta ci, shi ma dai Aseef ba wani abincin kirki ya ci ba, dan ma dai Imran ya sake kiransa a waya ya kara kwantar mishi da hankali ne yasa ya yarda ya ci abincin, da kuma baya son su Lion su gane yana cikin damuwa, dan Lion ba zai goyi bayansa ba, zai ce akan mace har zai ɗaga hankalinsa, shi bai san so ba, ganin abin banza yake yi mata.

Wanka ta yi ta shirya cikin wani wando da bai karisa kai mata idon sahu na kafarta ba, sai riga mai karamar hannu mai shegen kyau, ɗaura handkerchief ta yi a kanta, ta yi kyau ba karya, sai dai fa kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana cikin matsananciyar damuwa, plat shoe ta sanya a kafarta tare da nufar waje, ban da tunanin jenan babu wani abu da take yi, garden ta nufa dan ta rage wa kanta raɗaɗin abin da take ji, gabaɗaya blue light ne kunne a garden ɗin, saman sofa ta kwanta tana tunane tunane har barci ya yi awon gaba da ita, sai misalin karfe 11 na dare da sanyin ya ratsata ne ta farka, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata, ganin a cikin garden take yasa ta miƙe a tsorace, bata lura da akwai mutun a cikin garden ɗin ba kawai ta nufi cikin gida, sai dai kash Mark ya rufe gabaɗaya kofofin gidan, ga shi bata fito da wayarta ba bare ta kira Areef, ga kofar ko ta yi knocking ba lallai su ji ba, kuma ma tana tsoron yin knocking ɗin dan kada Lion ya tashi daga barci.

Ta jima tsaye a wajen tana tunanin mafita, can ta ɗan ji motsin su Brady, dake ɗaure a kusa da ta wajen pool, a guje ta juya ta koma garden ɗin, saman sofar da ta tashi nan ta koma ta kwanta tare da takure jikinta waje guda, ga sanyi ga kuma tsoro, sai ta takure sosai, ta datse idanunta gam tamkar zata fasa su, jikinta har wani kerma yake yi, duk abin da take yi yana kallonta, dama idan baku manta ba, wajen zamansa kenan da daddare, wani lokaci sai ya kai karfe 2 na dare a wajen, so yanzu ma yana zaune yana aikin latsa waya, da ya gaji sai ya kishingiɗa a saman doguwar sofa dake kusa da shi, sai dai tsawonsa ta fi ta sofar, dan haka sai ya ɗan naɗe kafa, duk wani motsinta yana gani, amma ita bata san da shi a cikin garden ɗin ba, da haka barci ɓarawo ya sake ɗaukarta, ta takure jikinta over.

Can cikin dare misalin karfe 1 sanyi ya sauƙo sosai, sai dai ita kuma ɗumi take ji yana ratsata ba sanyi ba, wani irin daɗin barci take ji abinta, miƙa ta yi da nufin bari ta juya daga yanayin kwanciyar da take, sai ta ji wuyarta na ɗan yi mata zafi, waro idanunta waje ta yi, idanun nata ɗauke suke sosai da barci, still dai a cikin garden ɗin take, yunkurawa ta yi zata miƙe sai ta ji kamar ba jikin sofa ta dafa ba mutun ta dafa, da yake akwai hasken blue light a wajen sai ta kai kallonta in da ta dafa kafin ta ɗago kanta izuwa kansa, yana zaune ya jingina kansa da jikin headboard na sofar, da alama shi ma barci ne ta yi awon gaba da shi. Abin da ya faru, da misalin karfe 12 na dare, sai rawan sanyi take yi, hakwaranta na garuwa da na juna sosai, kasa jure jin sautin hakwaran nata ya yi, suna toshe mishi kunne, hakan yasa ya miƙe tare da dawowa saman sofar da take kwance, sofar ta yi musu kaɗan, dan haka sai ya ɗaga kanta ya ɗaura saman cinyarsa bayan ya zauna kenan, sannan ya cire jacket dake jikinsa ya rufa mata, da yake jacket ɗin nasa yana da girma sai ta rufe ta da kyau, ga kuma kauri jacket ɗin, cigaba da latsa wayarsa ya yi har barci ta yi awon gaba da shi shi ma, to shi ne abin da ya faru, ya yi mata hakan ne kuma a cewarsa yanzu tausayi take bashi saboda irin wahalar rayuwa da ta sha, idan baku manta ba a Abuja ya faɗa, ita ce mutun ta farko da ta fara mashi tausayi a rayuwarsa.

(To mudai je zuwa daga tausayi se me readers?)

Readers Also Read