Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 66

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 66

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 66: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 66. Duk abin da ya faru a ɗakin a kan idanun…

3,339 words

Duk abin da ya faru a ɗakin a kan idanun Aseef ya faru, ya shigo duba Lion ɗin ne sai ya kalle shi yana ƙoƙarin hura mata iska, shi ne ya koma da baya, dan idan ya bari ya gan shi, to fa ba zai hura mata iskar nan ba sai dai ta mutu, shi ne yasa ya koma baya ya laɓe yana kallonsu tare da yi wa Allah godiya da Allah ya nuna mishi wannan rana da Lion yake damuwa da Rismha har haka, har zai hura mata iskan bakinsa a cikin nata dan ta tashi, kai ai dole su yi wa Allah godiya. Sai bayan ya ga Lion ɗin ya miƙe zai nufi toilet ne ya gudu ya koma ɗakinsa dan kada ya gan shi, yasan idan ya gan shi to fa ya jawa Rimsha ne, zai fara yin fushi da ita ya koreta a kusa da shi dan kada hakan ya sake faruwa ma bare wani ya gan shi. LION DUNIYA.

Hannu ta kai saman idanunta tana ɗan murjesu, da kyar ta warosu waje, a hankali ta miƙe zaune tana tunanin ina kuma ya nufa, lallaɓawa ta yi ta miƙe zuwa bedroom nata, toilet ta nufa ta yi wanka tare da ɗauro alwalar sallar azahar, abaya ta zura dan gabatar da sallah.

Sai bayan ta yi sallar ne ta zauna tsantsara kwalliya, wandon jeans ash color ta sanya mai bala'in kyau, ta sama kuma riga maroon ta sanya, ta yi kyau over, ta busar da gashinta da hand dryer, tare da shafa masa mayukanta masu bala'in kamshi, tana cikin ƙoƙarin ɗaure gashin ne ta tuna da shampoos da ta ɗauka mishi a shopping da suka yi a Abuja, da sauri ta saki gashin nata ta nufi trolleyn da ta daho da shi, buɗewa ta yi ta cirosu, cool murmushi ta saki kafin ta miƙe ta nufi gaban mirror dan ta karisa shirinta, saman drawer mirror ta ɗaura shampoos ɗin ta karisa komai, ta yi kyau over, sai tashin kamshi sosai take yi.

Bata ɗaure dark black curly hairnta ba, dan yaki ɗauruwa sam, yana da bala'in tsantsi, sai ta sake shi kamar wata Baturiya abinta, bata ɗaura ɗankwalin ba, dan tana sauri ta kai mishi shampoos ɗin.

Kwasansu ta yi har ta kai bakin kofa, sai ta tuna cewa ai ya ce ta kai mishi birth certificate ɗin Jehan, hakan yasa ta dawo da sauri ta sake bincika akwaitin dan ta duba, cash bata samu ba, babu a ciki, yana Abuja, ta ji babu daɗi, jikinta har ya mutu duk da bata san me zai yi da birth certificate ɗin ba, haka ta miƙe zuwa bedroom ɗin nasa.

Da sallama ɗauke a bakinta ta shigo, baya cikin ɗakin, ganin hakan yasa ta lallaɓa ta nufi toilet nasa, sauri sauri ta ajiye masa shampoos ɗin, dan tasan idan ta bashi hannu da hannu zai ce baya so, dan shi ba'a mishi goninta, komai ka yi mishi baka burge shi, ba'a yi mishi sai abin da ya ce ayi, shima abin da ya ce ayi ɗin baya taɓa yabawa koda shi ɗin ya ce ayi, haka yake a murɗe, shiyasa ta zaɓi ta kai mishi toilet ɗin ba tare da ya sani ba, sai dai kawai ya zo ya gani.

Sauri sauri ta ajiye mishi ta fito, yana cikin dressing room yana sanya kaya, saman sofa ta zauna, sai kuma ta kalli bed nasa ya ɗan hargitse alamar tun da ya tashi da safe ma bai sake komawa ya kwanta ba, kuma da alama Areef bai dawo gidan ba bare ya gyara mishi, shi kuma Aseef bawan Allah yana fama da kansa, bashi da kwanciyar hankalin da zai iya wannan aiki, ko da ma yana cikin kwanciyar hankali ba abin da ya iya, Areef ne bawan Allah dama mai yi, shi Aseef sai dai kwanciya da iya zuba shagwaɓa kamar ba gobe.

Miƙewa ta yi ta nufi bed ɗin dan ta gyara mishi, ta yi sa'a yau wannan gibgegen bargon nasa tana ninke, ba'a warwareta ba, gadon ta fara gyara mishi har lokacin ana ruwan sama sosai, garin ya yi sanyi sosai, tana jin sanyi amma bata sanya jacket ba, dan bata da shi tana kuma jin tsoron saka nasa da ta taɓa ɗauka a wajen Imran kada Brady ya biyo ta ya haukatata, shi ne ta shafawa kanta salama da zaman lafiya ta hakura bata saka ba, da sanyin haka ta jure.

Tsab ta gyara mishi gadon kafin ta zo ta ɗauko tsintsiya da mopper, ruwan da suka zubar a shigowarsu ɗasun da suna ɗigar ruwa, shi ta fara gogewa kafin ta fara share ɗakin, babu wani dattin komai kamar dai kullum.

A haka ya fito ya sameta, kallo ɗaya ya yi mata ya kawar da kansa, ya shirya cikin wandon jeans fari tas tamkar yanzu ya ciro ta a ledarta, ta sama kuma high neck t-shirt ne shi ma fari tas ya sanya, da yake rigar ta kama shi sosai, hakan yasa faffaɗar kirjin nan nasa ta bayyana kamar na zaki, ga breast nasa da suke ɓul ɓul, ya yi kyau sosai, shi ma ya busar da gashin kansa da hand dryer, sai kyalli gashin yake yi, ya ɗaure a bayan wuyarsa, ya ɗaura rigar ruwa a saman kayan nasa, kafarsa na sanye da bakaken takalma masu kama da slippers, sai dai waƴan nan suna da laushi sosai, sannan kuma an yi su ne kamar cover shoe ta samansu, jikinsu kuma kamar jikin mage, haka takalmar suke, suna da bala'in kyau ga tsada, sai zuba kamshi yake yi kamar ba gobe.

Bakin bed nasa ya zauna yana duba time a wayarsa, dressing room nasa ta nufi ita kuma, jim kaɗan ta fito riƙe da air freshener a hannunta, lungu da saƙo dake ɗakin bakiɗaya sai da ta bi ta fesa, har cikin ransa ya ji wannan daddaɗar kamshin air freshener data zaɓa mishi, sai dai a fuska kamar yadda kuka sani ne, ba zaka taɓa gane hakan ba.

Bayan ta gama ta mayar ne ta dawo kusa da shi ta tsaya, bai ce mata komai ba, kuma bai ɗago ya kalleta ba, shagwaɓe murya ta yi tana faɗin "Yaya Saif in ta fi ne?". Tamkar babu shi a cikin ɗakin, ita kuma ta manta abin da ma ta zo gaya mishi shi ne bata ga birth certificate na Jehan ba, sai ta tsaya shiru kawai, abin ya yi mata kamar shi ya kirata ne.

Ganin bashi da niyar kulata or ya ɗago ya kalleta ne yasa ta zauna a saman bedside drawer, kirjinta na dukan uku uku na tsoronsa, amma haka ta daure ta zauna abinta, ita dai tun da ance mata baya dukan mata, ya fi karfin ya ɗaura hannunsa a jikin mace dan duka, shikenan ta dai'na damuwa idan zata yi mishi wasu abubuwa, a shirmenta wai in dai iya punishment me to bata damu ba, bata san cewa punishment nasa ya fi dukan azaba ba.

A tare Aseef da Areef suka shigo suka same su, wani irin azababben kyau suka yi musu na yadda suka zauna shi a bakin bed ita a bedside drawer, cool murmushi Areef ya saki har cikin ransa ya ji wani irin daɗi, gefen Lion ɗin ya zo ya zauna yana faɗin "Our Queen kin ga irin azababben kyau ɗin da kika yi kuwa? Gaskiya kyau ɗin nan ya wuci a zauna a gida, muje ki rakani unguwa". A sukwane ta ɗago ta kalli Lion ɗin, dan ya hanata fita idan baku manta ba, tamkar babu shi a ɗakin yana ta aikin duba waya.

Hayewa saman bed ɗin Aseef ya yi, ta bayansu ya kwanta, bawan Allah ko zama ba zai iya wani yi ba, dan azaban jiri da yake ji, rabonsa da ya sanya abincin kirki a cikinsa yau kwana uku, kullum sai dai ya ɗan tsakura kaɗan dan kar ya mutu, ya sha ruwa ya kora da Maltina shikenan.

"Our Queen lafiya baki amsa ba?". Areef ya sake tambayarta, murmushin dole ta ƙaƙalo tana faɗin "Yaya Areef ina wuni?". Da yake shi ya fi kusa da ita sai ya sanya hannu ya ɗan buge bakintan yana faɗin "Tambayar da na yi miki shi zaki bani amsa". Kukan shagwaɓa ta saka mishi tana murje ɗan bakin nata, "Sarkin rigima zo na rarrasheki". Ya faɗa tare da jawota jikinsa yana cigaba da cewa "Zo muje zan saya miki chocolate kala kala na biya buge bakin da nayi".

"Yaya Areef ba chocolate ba, hoton Jehan zaka ɗauko ka nuna mini, wlh jiya har mafarkinta nayi, ina son sanin ya take". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai, shafa lallausan dark black curly hair'nta ya yi har zuwa bayanta yana faɗin "To zamu je dai tare ki ganta, daga nan muje yawo ki kaini gidansu Prof ina son naga ƴan uwan uncle". Yana magana yana ƙoƙarin tara mata lallausan gashin nan nata ya ɗaure mata, rabin jikinta na zaune saman cinyarsa rabi kuma saman bed, dan irin jawota da ya yi, sai ta ɗan kwantar da kanta a saman kirjinsa.

"Bari na tara wannan gashin na ɗaure miki dan ainahin kyanki ya kara fitowa Our Queen, ke fa da bikinki hmm ko da yake faɗe ɓatawa, Allah dai ya kai mu......". Bai kai karshen maganar ba Lion ya daka musu wani mahaukacin tsawa wanda ya sanyata miƙewa ba shiri, a kule ya yi tsawar, ransa a matukar ɓace, "Get out!!" Shi ne abin da ya faɗa, a cewarsa suna damunsa da surutu, sun toshe mishi kunne.

Ganin yadda ta miƙe a razane ne yasa Areef ya riƙo hannunta yana kallon ɗan uwan nasa da mamaki, ya riƙo hannunta ne kuma dan yasan halinta sarai da razana, yanzu tana iya sumewa a wajen ma bakiɗata, ba karamin ruwan mamakin jin tsawar Areef ɗin ya yi ba, tun da yake da ɗan uwan nasa yau shekara talatin da ɗaya, bai taɓa jin voice na ɗan uwan nasa mai sauti haka ba, kullun kasa kasa yake magana, ko sojojinsa baya yi musu tsawa, da idanu ma kawai idan ya kallesu sun san sauran, sun karanci ogan nasu tsab, wani shiru ma idan ya yi sun san me yake nufi, so shi tun ainahinsa ma haka yake baya ɗaga murna, baya magana da sauti, ga muryarsa da bala'in daɗin sauraro, amma sai rowarta ya iya.

Ita ma da yake ta saba da Areef fiye da kowa, bata wani damuwa da duk wani abin da zai yi mata, dan tasan ba zai taɓa cutar da ita ba, shiyasa ma take kwanciya a jikinsa da sauransu, ganin ya riƙo hannunta yasa ta tsaya ta natsu jikinta na kerma kamar me. Shi kansa Aseef dake kwance ta bayansu yana fama da kansa sai da ya miƙe zaune, jin tsawar ta ɗan uwansa yasa ya nemi damuwar tasa ma ya rasa ina ta nufa?, Ya ji abin da bai taɓa ji ba a tare da TRIPLETS nasa.

"Lion lafiya kuwa?". Cewar Areef. Ko sannu bai ce musu ba, ko ɗago kai ma bai yi ba bare su saka ran zai amsa, dawo da kallonsa kanta Areef ɗin ya yi sai kallon Lion ɗin take yi, shi dai sun kulle mishi kai, ɗan Juyowa ya yi ya kalli Aseef ko zai yi mishi cikakken bayani.

Tsabar tsiya irin na Aseef ɗin sai ya matso kusa da Lion ɗin sosai tare da sanya hannayensa dukka biyu ya tushewa ɗan uwan nasa kunne wai dan kada ya ji abin da zasu ce shi da Areef. "Ka toshewa sister ma kunne kada ta ji me zan ce mana". Cewar Aseef ɗin. Jawota jikinsa Areef ɗin ya yi don ya toshe mata kunne, dan shi dai yana son jin gulma ato, dole ya toshe mata kunne.

A zafafe Lion ya juyo ya damko wuyar Aseef ɗin, ransa a matukar ɓace ya shaƙesa sosai, da sauri Areef ya miƙe tsaye tare da sakinta, ko a mafarki bai taɓa mafarkin Lion zai shake Aseef ɗin ko ya ɗaura hannu a jikinsa da nufin duka ko wani abu makamancin haka ba, sai ga shi yau ya shakesa sosai, saketa ya yi tare da hayewa saman bed ɗin dan ya kwaci Aseef ɗin, ita kam yau ta ga bala'i, yadda nan take Lion ya canza musu daga Saif ya koma Lion na gaske.

Tamkar jira yake yi Areef ɗin ya zo, sai ya saki Aseef ɗin ya damko wuyar Areef ɗin, da alama fa ɓacin ran dama na Areef ne ba na Aseef ba.

Shiru Areef ɗin ya zuba mishi idanunsa da suka yi jawur kamar wuta yana jin shakar da ya yi mishi har cikin zuciyarsa, yana shan azaba amma bai motsa ba bare ya yi yunkurin kwatar kansa, sai ma tsare shi da idanu da ya yi yana karantar yanayinsa dan ya gane ɓacin ran na menene ne haka?.

Sai da ya tabbatar ɗan uwan nasa ya galabaita sosai kafin ya sake shi tare da miƙewa, da farko ya yi kamar zai nufi toilet, sai kuma ya juyo ya damko gashin kanta a in da take tsaye ta yi sumar tsaye, dan ta tsorata ganin ya shake Areef da Aseef yau, bata san a baya faɗa suke yi sosai ba, suna kaunar junansu, amma dama kunsan TRIPLETS or TWINS suna faɗa sosai dan suna ganin kansu ɗaya, to ɗaya ba zai yarda ɗaya ya nuna mishi fifiko ba, amma su da suka girma sosai sun dai'na gaskiya, sun jima basu yi ba na gaya muku a baya, ita dai Rimsha ita ce bata sani ba, shi ne abin ya yi mata wani iri hakan nan.

"Ban ce ki fita mini a ɗakin nan ba?" Ya faɗa murya can kasa kasa, ya yi maganar kuma har lokacin yana damke da dark black curly hairnta, dan gashin nata ya damko ba wuyarta ba, narai narai ta yi da idanu kamar zata yi kuka, zafi sosai gashin yake yi mata, ko kusa Areef bai yi yunkurin kwatar ta ba, dan yana zargin ɓacin ran ɗan uwan nasa yana da nasaba da rungumeta da ya yi or something like this, koma yaya yana dai da nasaba da ita, idan kuwa haka ne, Lion ɗin ba zai taɓa yi mata abin da zai cutar da ita ba, zai dai hukunta ta iya hukuncin irin nasa, amma ba zata cutu ba, shi ne yasa ya zuba musu idanu kawai, shi kam Aseef dama tun da aka sake shi ya koma ya kwanta ya basu baya abinsa, dan shi bala'in da yake ciki ma kawai ya ishe shi, ba zai iya ɗaukar wani ba kuma, kada ya mutu lokacin mutuwarsa bata yi ba.

Tsareta da idanu ya yi yana jiran amsa, a hankali ta motsa kyawawan laɓɓanta ta furta "Ka ce na fita, yanzu zan fita ɗin". Ganin yadda lips nata suke motsi dimples nata suke lotsawa ne yasa ya tuna abin da ya faru ɗazun na iska da ya hura mata cikin ɗan bakin nata, wani irin zirr ya ji a jikinsa tuna abin, sakinta ya yi ba tare da ya yi magana ba, da gudu ta juya ta fita, dama Malika ta faɗa, dole sai abin ya yi ta dawowa mishi cikin tunaninsa, dan abu ne da bai taɓa yi ba a rayuwarsa, so dole ya ji wani iri, dama mace da namiji kamar kararrawa suke, duk lokacin da suka haɗu dole sai zuciya ta bada sautin bugawar kararrawa, haka halittar take, musamman kuma yadda ya ji lips ɗin nata da bala'in laushi kamar me, ai dole ya tsaya mishi a rai.

(Gaskiya Malika bata kyauta mishi ba, Allah ya sakawa bawan Allah, yana zaman zamansa muguwa ta ɗarsa mishi abin da bai taɓa ji ba a zuciyarsa😭 justice for Lion, ta iya shirya kitimurmura Malikar nan wlh, duk wani tsiya ta san shi, yanzu sai Allah ma kaɗai yasan me ta yi ta shiryawa da har aka kawo wannan matakin😌)

Hanyar fita ya nufa, har ya yi gaba sai kuma ya juyo da kallonsa kan Aseef dake kwance ya basu baya, calmly ya ce "A karo na karshe zan tanbaye ka, me yake damunka?" Juyawa Areef ya yi ga Aseef ɗin, yayin da shi ma ya juyo ga ƴan uwan nasa, kasa kasa ya furta "Zazzaɓi and ciwon kai". Ɗan zaro idanu Areef ɗin ya yi tare da kai hannunsa saman lallausan kumatunsa dan ya ji akwai zazzaɓin ne ko babu, tabbas akwai ta a jikinsa, dan ga jikin nan ya yi zafi sosai, dawo da kallonsa kan Lion ɗin ya yi, gera ɗaya Lion ɗin ya ɗaga mishi alamar ya ake ciki? Jinjina mishi kai ya yi yana bashi tabbacin yes da akwai zazzaɓin a jikinsa, Juyowa ya yi ya dawo saman bed ɗin, hayewa ya yi tare da tallaɓo kan Aseef ɗin yana kallon cikin kwayar idanunsa.

Nan take dukkansu biyu suka shiga damuwa, A box Areef ya ɗauko dan su duba shi, shiru Lion ɗin ya yi yana tunanin cewa wannan zazzaɓi na Aseef ba zazzaɓin kwayar cuta ba ce, sai dai idan zazzaɓin tashin hankali ko makamancinsa, dan kuwa idan da zazzaɓin kwayar cuta ce dole za su ji a jikinsu na farko, na biyu kuma dole yanayin Aseef ɗin zai canza. Shi kuma Areef sai ƙoƙarin haɗa kayan aiki yake yi.

Kuka Aseef ɗin ya saka musu a kan shi dai ba za su yi mishi allura ba, ya warke dan haka su kyale shi, hannu Lion ya ɗagawa Areef a kan kada ya haɗa komai, da mamaki yake kallonsa, kwantar da kan Aseef ɗin ya yi a saman pillow tare da ɗan kwantowa kusa da shi yana faɗin "Menene ainahin abin da yake damunka?". Dama shi Aseef yariga da ya san tsab Lion zai iya gane zazzaɓin kwayar cuta da kuma ta firgici or tashin hankali, sai dai bai ɗauka da wuri haka zai gane ba, amma duk da haka sai ya kafe musu a kan shi babu wani abin da yake damunsa, hakan yasa Lion ɗin ya ce a kira mishi daddy Rimsha, dan yasan dole ne ma shi yasan menene yake damun ɗan uwan nasu, Areef na kokarin kiransa a waya, sai kuma ya ce no ya barshi kawai koma menene zai sani ne, shi kuma Aseef ya jira shi yana nan dawowa zai yi bayani ne tun da yaki gaya mishi gaskiya. Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya sauko kasa ya nufi waje dan aikin da yake yi bai karisa ba, ya dawo ɗaukar wasu abubuwa ne tare da birth certificate na Jehan.

Yana fita Areef ya dawo kusa da Aseef ɗin dan ya lallaɓa shi ko zai gaya mishi menene yake damunsa, nan ma dai kin faɗe ya yi, ya kafe a kan shi fa kansa ne yake ciwo da zazzaɓi, bayan haka kuma babu wani abu da ya sani, dole tasa Areef ɗin ya hakura ya kyale shi ba dan ya so, saukowa ya yi ya nufi waje, cikin sanyin murya Aseef ɗin ya ce "Areef please zo ka yi mini alluran barci". A sukwane ya juyo yana kallonsa da mamaki, wai me yake damun sa ne?.

Tunani cike fal ransa ya zo ya haɗa alluran ya yi mishi, bawan Allah yau tsawon kwana uku baya samun isasshen barci, yana son kuma ya yi barcin dan ya hutawa ransa, amma ina abin ya fi karfinsa, hakan yasa kawai ya ce ayi mishi alluran barci ko ya ɗan samu ya rintsa. Aikuwa ana yi mishi ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, Areef ya ɗauki tsawon lokacin yana kallonsa kafin ya miƙe ya fice daga ɗakin ya nufi nasa bedroom ɗin dan ya yi wanka ya je wajen Jehan a prison, gobe court zata yanke mata hukunci.

A ɓangaren Rimsha kuwa, tana fita bedroom nata ta koma..........

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*

E53-54💋

A ɓangaren Rimsha kuwa, tana fita bedroom nata ta koma, saman gado ta haye tana tunanin wai shi yaya Saif ɗin nan wani irin mutun ne? Sai ka rasa me yake damunsa sam.

Readers Also Read