Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 67
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 67: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 67. Shi kuwa waje ya nufa dan ya je in da yake…
3,346 words
Shi kuwa waje ya nufa dan ya je in da yake bukatar zuwa, har ya kai tsakiyar palon kasa sai ya tuna bai karɓi birth certificate ɗin Jehan ba, juyuwa ya yi ya nufo saman, bedroom nata kai tsaye ya nufa.
Kasa kasa ya yi sallama kafin ya faɗa, bata ji sallamar tasa ba sai dai ta ji daddaɗar kamshin perfume nasa da ya ziyarci hancinta, cikin sauri ta ɗago da kallonta zuwa bakin kofar shigowa, a bakin kofa ta ciki ya tsaya yana ɗan latsa wayarsa, zubur ta miƙe zaune tana kallon shi, tamkar ba bedroom nata ya shigo ba, ta ruɗe ta rasa me zata ce mishi, muryarta na rawa ta ce "Yaya Saif sannu da zuwa ina wuni?".
(Wayyo cikina 🤣 wai yaya Saif sannu da zuwa ina wuni)
Tamkar babu shi a wajen, ko kallon in da take bai yi ba, duk ya rikitata, dirowa kasa ta yi daga saman bed ɗin nata ta nufo shi, kusa da shi ta tsaya tana son tambayarsa me ya zo yi, kwata kwata ta manta da cewa ya ce ta bashi birth certificate na jenan, sai wani ƴan kame kame take yi, shi kuma ya kware wajen gindayar da mutane, yanzu ma dai shirun gindayarwar ya yi mata.
Sai da ya ɗauki good 5 mins yana tsaye kafin ya ɗago da kallonsa a kanta, kasa ta yi da kai, zubawa kyakkyawar dark black curly hairnta idanu ya yi, ba ƙaramin kyau gashin suke yi mishi ba, sai wani murza yatsun hannunta take yi alamar duk a tsarge take.
"Ina birth certificate da na ce ki kawo mini?". Cikin sauri ta ɗago idanunta ta saukesu a saman faffaɗar kirjinsa, "Ban gani ba ne, yana Abuja". Ta yi maganar cikin natsuwa, mamakin natsuwarta wani lokaci yake yi, wata zubin kuma sai ka ganta kamar wanda aka sakawa battery, rawan kai kamar me.
Ganin bai tafi bane yasa ta ɗan ɗago ido dan ta saci kallonsa, caraf suka haɗa idanu, kasa ta sake yi da kanta tare da takure kanta ta ɗan turo baki, wannan turo bakin da ta yi nan take ta tuna mishi da abin da ya faru ɗazun na iska da ya hura mata, laushin da lips nata suke da shi ne kawai yake yi mishi yawo a cikin kwakwalwarsa.
Tuna hakan kuma yasa ya juya ya fice daga ɗakin, bin bayansa da kallo ta yi har ya isa tsakiyar palon saman, a nan ne kuma suka haɗu da Areef da ya fito daga bedroom nasa bayan ya yi wa Aseef allura kenan.
Tsayar da shi Areef ɗin ya yi yana faɗin "Gobe za'a yankewa baby hukunci fa, kuma ka san kai tsaye hukuncin kisa zasu yanke mata, yanzu me abin yi? Ka dai san tana da gaskiya ko? Kare kanta zata yi ta kashe shi bisa kuskure, kuma kasan wannan hukuncin da ta yi mishi dai'dai ne, dan ko kai ka kama irin shi, wannan hukuncin zaka yi mishi". A takaice ya ce "To ina ruwana da case ɗin?". Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya sauka kasa abinsa, bin bayansa Areef ɗin ya yi ba tare da wata damuwa ba dan yasan Lion ɗin ba zai taɓa bari a kasheta ba, dan kuwa yasan tana da gaskiya, kuma mugun iri ta kashe, shiyasa bai wani damu ba ya bi bayansa suka sauka kasa ya wuce bedroom nasa.
Ita kuwa Rimsha tun da ta ji abin da suka tattauna hankalinta ya yi kummunar tashi, nan take hawaye suka fara wanke mata fuska, shikenan za'a kashe Jehan kenan? Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, ba zata iya jurar wannan bala'in ba, saman bed nata ta koma ta kwanta, hawaye tamkar ruwan famfo haka yake gudu a face nata, ji take yi duniya na juya mata, har wani duhu duhu take gani yana gilma mata ta cikin idanunta, daga Lion ɗin har Areef ɗin ba wanda ya san ta ji abin da suka tattauna, da sun ji Areef ba zai tafi ba har sai ya tabbatar ya kwantar mata da hankali.
Haka ta kwanta har aka kira sallar la'asar, jiki duk a mace, da kyar ma ta iya mikewa ta yi sallar, bayan ta idar ta yi wanka ta shirya cikin Abaya sannan ta fito zuwa kitchen dan ta ɗauki abincinsa ta kai masa, tun karfe 3 ta ji dawowarsa, amma ta san ba zai ci abincin a lokacin ba, shi ne yasa ta yi kwanciyarta kawai.
Kitchen ta nufa, tsaye ta isko Mark yana latsa wayarsa, sannu ta yi mishi, bai amsa ba, bai kuma ɗago ya kalleta ba, tamkar dai babu shi a wajen kamar kullum, wanke hannunta ta yi ta ɗauki abincin ta fito ta nufi bedroom ɗin nasa.
Bakinta ɗauke da sallama ta shiga, yana zaune saman bed nasa ya jingina da jikin headboard na gadon tare da rufa bargo zuwa daidai saitin cikinsa yana latsa waya. In da ta saba ajiye mishi abincin ta nufa, ajiyewa ta yi tana ƙoƙarin zama kenan muryarsa ya daki dodan kunnenta. "Kawo mini fruits kawai is okey". Ya yi maganar ba tare da ya ɗago ya kalli in da take ba.
Okey ta amsa mishi da shi tare da ɗauko mishi ta nufo shi, saman bedside drawer ta ɗaura plate ɗin tare da zama a saman carpet ɗin dake wajen, cike da tsoro ta ce "Yaya Saif ina son zuwa prison in ga Jehan". Shiru ya yi bai kulata ba, almost 10 mins suna haka, sannan ne ya ce zata iya tafiya bedroom nata, kuma kada ta kuskura ta fita daga gidan nan, ba zata je prison ɗin ba.
Da sauri ta miƙe ta nufi waje, tana shiga bedroom nata ta faɗa a saman gado tare da sakin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, shikenan idan ma kashe Jehan ɗin za'ayi ita ba zata sake kallonta ba, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wannan bala'i da me tayi kama? Ji ta yi kamar ta rataye kanta dan bakin ciki, har wani irin shasshekar kuka take yi wadda daga ji kasan zuciyarta a kusa take, kiris take jira ta yi bindiga.
Shi kuwa ko a jikinsa ya sha fruits nasa kafin ya gyara kwanciyarsa da kyau tare da lumshe idanunsa kamar mai barci.
A ɓangaren Areef kuwa, wanka ya tsara ya nufi prison ɗin shi da Donald ɗaya daga cikin sojojin Lion, a lokacin Mark yana aiki shi ne yasa ba su tafi tare ba.
Sai da suka biya super market ya saya mata wasu abubuwa da yake ra'ayi, sannan ya fito suka nufi prison ɗin
Office ɗin shugaban gandurobobin ya zauna tare da bukatar ganinta, ba ɓata lokaci kamar dai kullum suka fito da ita, sun zuba mata sarkoki a hannu, dama idan za su fito da babban mai laifi haka suke yi.
A kasa saman carpet ɗin gandurobar ta zaunar da ita, hankalinta a kwance tamkar ba ita za'a yankewa hukunci gobe ba, Ameera da ba ita za'a yankewa hukunci ba ma, ta shiga tashin hankali sosai, duk bayan minti ɗaya sai ta ce "Yanzu Jehan ke sam baki damu ba? Kuma kin san hukuncin kisa zasu yanke miki fa ko?". Tsaki take ja tana faɗin "To idan su suka riƙe raina ba sai su kashe ni ɗin in gani ba, wai ma su suke da wuta ko aljanna ne? Ni fa Ameera ki daina damuna, duk wanda kika ga ya mutu to lokacinsa ne ya yi, idan lokaci kuma ya yi, ko a saman kadon kuɗi da mulki kike kwance sai kin mutu, to idan mutun ya san haka me zai wani takura wa kansa? Ke ni bari ki ji wlh ni bana ma ɗaukar alkalinma kamar mutun bare har na ɗaga idanu na kalle shi, ni dai nasan ga abin da na yi, so wannan tsakanina ne da ubangijina, idan sun cuceni a nan sun nuna mini fin karfi, suma suna nan zasu zo in da zasu turani ɗin, tun da babu wanda Allah ya ce zai tabbata a duniya, kowa sai ya mutu, dan haka za su mutu su zo su same ni suma, a nan ne kuma mai karfin iko, malikiyaumiddin mamallakin ranar sakamako zai karɓa mini hakkina, lokacin kuma babu wata rai da zata iya musawa ta ce bata yi kaza ba, ko kuskure aka samu, duk babu wannan korafin, ranar hukunci ne da ubangiji subhanahu wata'ala zai yanke ta dai'dai da abin da kowa ya yi, idan ta yi maka daɗi, ka yi da kyau kenan a duniya, kuma da haka zaka yi ta kallon mai kyau har abada, idan bata yi maka daɗi ba, to fa farkon kofar rashin jin daɗin rayuwarka ce ta buɗe har Illah Masha Allah, so dan haka ki dai'na takurawa kanki muddin kin san da mai wuta da aljanna kika dogara ba kato ba!!".
Baki Ameera take sakewa tana ganin ikon Allah ita dai, duk a tsorace take, amma ita da za'a yankewa hukunci ko a jikinta, hankalinta kwance tamkar wanda take gidan iyayenta tana shan Ac mai sanyi.
STORY💋
Zuba mata idanu sosai Areef ya yi yana kallon ramar da ta yi, sam baya son hakan, ba karya ta rame saboda zaɓar abinci da take yi, ji yake yi kamar ba zai iya hakuri ba, gara mishi kawai ya ɗauketa su tafi gida, amma yasan Lion ba zai yarda da hakan ba, dan ya saɓa doka, hakan yasa yake daurewa kawai yake kawar da kansa ya barta a prison ɗin.
Kallon shugaban gandurobobin ya yi, cikin natsuwa ya ce "Zaka iya bamu waje dan zan yi magana ta sirri ne da matata". Wani kallon sama da kasa ta wurga mishi, wai mata, ko waye ya bashi ita oho mishi.
Kashe mata ido ɗaya ya yi yana mata signal da gera ɗaya, guntun tsaki ta ja, dan duk lokacin da ya yi irin hakan, kama yake yi mata da tantiran maza irin ƴan duniyar nan, sai ya wani kashe ido ɗaya kamar wani tantirin ɗan iska, shi kuma ya saba abin ne sakamakon zaman da ya yi cikin ƴan ta'addan da ƴan iska, shi ne ya koyi abin, sai kuma ta zamo mishi jiki, har idan bai yi ba ma baya jin daɗi.
Miƙewa shugaban gandurobobin ya yi ya nufi waje, kallon Donald ya yi, tun bai yi magana ba shi ma ya fice da sauri abinsa.
Dawo da kallonsa kanta ya yi, cikin zolaya ya fara magana "Tun da ba zaki gaishe ni ba ni bari na gaishe ki? Ya jiki?". Kasa kasa ta amsa mishi da ta ji sauki.
"Wai da gaske baby har yanzu baki fara tunanina ba?". Ya yi maganar murya a sanyaye, kuma can kasa kasa ya yi maganar, harara ta watsa mishi ba tare da ta yi magana ba, dan a cewarta bata da lokacin ɓata bakinta na magana da shi, ga shi sai bala'in tsoronsa dake ji cike fal ranta, a fili kuma sai karfin halin bala'i.
Miƙa mata ledar hannunsa na shopping da ya yi mata ya yi yana faɗin "Okey tom shikenan yanzu dai bari na gama da case ɗin naki, dole zan koya miki tunanina, amma first yanzu dai karɓi wannan". Kin ɗagowa ma ta yi ta kalle shi bare ta yi ƙoƙarin karɓar ledar duk da hannunta ma dama da sarka a ɗaure, hakan yasa ya ɗaura mata ledar a saman cinyarta yana kara kare mata kallo, kyakkyawan gashin kan nan nata da ya sha gyara a gidan Hjyr daɗi kafin ta biyo Abubakar jaja, sai kyalli gashin yake yi in da ya leƙo ta cikin hijabin nata.
Hannu ya kai ya ɗan zame hijabin nata zuwa baya, ya sauke shi kenan daga kanta zuwa wuyarta, abin haushi shi ne hannunta ɗaure da sarka ba ta yadda zata yi ta buge hannunsa ko ta hana shi ya ta ɓata, ɗaure fuska sosai ta yi tana faɗin "Kada ka taɓa mini gashi". "Gashin ki ne ko nawa?" Harararsa ta gefen idanunta ta yi bata sake ce da shi komai ba, dan ko wani amsa ta bashi sai ya sake kawo mata wata maganar kuma, rufin asirinta kawai shi ne ta yi shiru.
Hannun ya sanya yana tara mata gashin nata yana faɗin "Uncle nawa yana zuwa gobe, dole na san abin yi, bana son uncle na ya zo ya same ki a nan, amma In Sha Allah nasan Lion ba zai taɓa bari a yanke miki hukuncin kisa ba, nima kuma ba zan bari ba, ki kula mini da kanki sosai, kada ki ji komai, gobe yiwar haka muna tare a gida, tare zamu ci abincin rana". Ko sannu bata ce mishi ba har ya tare mata gashin nata, pil ɗin da yake ɗaure gashin kansa da shi ya zaro ya sanya mata a kan nata yana faɗin "Bana son ki rinƙa sake gashin nan naki haka, nafi son ki rinƙa ɗaure mini shi kina ɓoye mini shi, kada ki bari kowa ya kalla mini abina, nawa ne ni kaɗai".
Mamaki ne ya kamata ganin yadda gashin nasa ya zubo mishi har kafaɗarsa kamar wata mace, dama bata san gashinsa yana da tsawo har haka ba, dan baya barinsa a sake, kullum a tare a bayan wuya ya sanya mata ɗan karamin pil ya ɗaure, ba zaka taɓa tunanin yana da tsawon gashi har haka ba, ya fi Lion tsawon gashi sosai, dan shi Lion yana rage tsawon nasa, baya bari ta wuce mishi bayan wuya, shi kuma Areef ɗin baya ragewa, ya bar kayansa ta kai har baya abinsa, yana kashe mata kuɗi over yana gyarata, kuɗin shampoos na gyaran gashinsa kawai ta isa ta sayawa mutum dankareren gida, ba karamin kuɗi suke kashewa gashin nasu ba, kowa da ra'ayinsa a cikinsu, shi Aseef ma ai dukka yake tankewa abinsa, baya son wahala, Lion rage tsawon, shi kuma har baya ya bar abinsa.
Zubawa gashin nasa idanu ta yi tana mamaki, ya fi nata tsawo. Bayan ya ɗaure mata nata ne ya tara nasan ya kulle a bayan wuyar nasa, duk da ya san zata warware, bai wani damu ba tun da ya ɗaure mata nata, gashin TRIPLETS akwai bala'in tsantsi ne sosai, hakan yasa dole idan zai ɗaure gashin nasa sai ya sanya pil, idan ba haka ba, warwarewa zata yi.
Hira ya ɗan yi mata na ƴan mintoci da basu wuce 10 ba, sannan ya yi mata sallama tare da rankwafowa ya manna mata sumbata a goshinta yana faɗin "Ki kula mana da kanki, ina son uncle ya zo ya sameki cikin ƙoshin lafiya, dan haka ki kula". Kallon uku goma ta watsa mishi, ko a jikinsa ya nufi waje abinsa yana yi mata bye bye.
Yana fita ba'afi da minti uku ba sai ga gandurobobin suka dawo ciki, macen da ta fito da ita, ita ta mayar da ita tare da ɗaukar ledar da ya bata, sai da suka je bakin kofar ɗakin nasu, sannan suka cire mata sarkar da suka ɗaure ta tare da karɓar ledar da Areef ɗin ya bata dan su zuba me a ciki, always ne da pants a ciki, sake baki ta yi tana kallon always ɗin da matar ta fitar, ko waye ya gaya mishi yau period nata ya zo da safe? Kai wato ma ya saka mata ido na wuce misali kenan? Ta tsaya sai tunane tunane take yi, sai magana gandurobar take yi mata a kan ta shiga ciki, amma ina ta lula duniyar tunani waye ya gaya mishi yau tana period kuma?.
Sai da gandurobar ta taɓata sannan ne ta dawo daga duniyar tunanin nata, Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta karɓi kedar ta wuce ciki, rufesu matar ta yi tare da juyawa ta bar wajen.
Shi kuma Areef yana barin prison ɗin gidansu Imran ya nufa dan ya riga da ya gaya wa Imran ɗin yana zuwa yau.
Gidan cike yake da ƴan biki, part ɗin Imran ɗin suka wuce, Akila tana ciki tana kwance bata da lafiya, zazzaɓi kamar zai kasheta, har Abbi ya ce ko za'a ɗaga bikin ne, Abba ya ce a'a ayi kawai ta je ta yi jinyar a gidanta, da yake shi ya san me matsalar, Ammie dai raba dare take yi tana rokan Allah da ya kawowa ƴar tata mafita, ya zaɓa mata abin da ya fi zama mata alkhari, bata wani nuna damuwa ba.
Lokacin da Areef ya shiga cikin palon, Imran, daddyn Jelly, AKil, Irfan, Dr Nawid, duk suna zaune saman sofa suna zuba hira, da yake yana sanye da black glass sai Akil bai iya rabe shi da Aseef ba, ya ɗauka ma Aseef ne, dan haka sai ya ɗan kawar da kansa, dan sam baya son haɗa idanu da Aseef, ya kasa manta zubewa a kasa a gabansa da Aseef ya yi kwana uku da suka wuce, lokacin su Abbi ba su dawo gidan ba, ya zo wajen Akila hira ne, har cikin palo ya shiga dan Abba baya nan, Akil ɗin ya fito zai fita zai je unguwa, shi ne ya zube gwiwowinsa a gabansa yana rokonsa da dan Allah ya rokan mishi Abba, wlh ba zai iya rabuwa da Akila ba, idan aka rabasu zai iya mutuwa, wannan abin ya tsayawa Akil sosai a rai, yadda ya kalli fuskar Aseef a wannan rana, ban da tsantsar soyayyar Akila babu wani abin da yake cikin idanunsa, bawan Allah.
Lallai rayuwa ba ta yadda bata zuwa wa bawa, yau a kan mace, a kan soyayya har ɗaya daga cikin TRIPLETS jinin William jacop, TRIPLETS ga The General Of Armys yake zube gwiwowinsa a kasa yana rokan kada a raba shi da ita? Ya ilahi ya lillahi, duk wata zuciya mai imani sai ta zubarwa da Aseef kwallah na halin da yake ciki, tabbas yana cikin halin mutuwa ko rayuwa, domin kuwa ya yi mummunar zurmawa over ne a soyayyar AKila.
Da yake shi Areef bai san komai ba, sai ya miƙa musu hannu dan su yi musabaha fuska ɗauke da murmushi, sosai Akil ya sha mamaki, sai kallonsa yake yi, ya kuma kasa gane cewa ba Aseef bane Areef ne, kila da ya cire glass ɗin face nasa ne ya iya gane shi ta kalar kwayar idanunsa.
Haka suka cigaba da hira Areef yana ta kallonsu dan baya jin Hausa, bai san me suke cewa ba. A nan ya yi sallar mangariba da issha sannan ya yi musu sallama ya nufi prison dan ya sake duba Jehan su yi sallama sai gobe, yana fita sai da Akil ya tambayi Imran ya akayi Aseef ya hakura ya wastsake? Nan yake gaya mishi wannan ba Aseef bane, Areef ne, ya sha mamaki irin tsantsar kamar da suka yi mishi har ya kasa raɓesu, shi kuma Dr Nawid ya sha mamakin dama wannan TRIPLETS na Lion ne, su Lion kawai suka sani, shi ma ba face nasa suka sani ba, bai taɓa ganinsu a zahiri ba sai yau, ga shi har musabaha suka yi ba tare da ya san shi ba ne.
A ɓangaren Lion kuwa, bayan ya yi sallar mangariba da issha bedroom nasa ya wuce dan yunwa yake ji sosai, zaune ya iskota ta kawo mishi abinci tana jiransa.
Wajen da ya saba zama ya je ya zauna tare da bata umarnin ta zuba mishi abinci, ba musu ta zuba mishi ta turo mishi a gabansa, ɗaukar spoon ya yi ya fara ci, shiru ta yi tana tunanin ƴar uwar tata, kamar saukar aradu haka ta ji zazzakar muryarsa ya daki dodan kunnenta. "What is wrong with you?". Shi ne abin da ya faɗa cikin sanyin murya.
Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin "Nothing". "Saboda na hanaki zuwa prison ko?" Nan ma girgiza mishi kai ta yi alamar a'a, ga idanunta kuma har sun kumbura saboda kuka, dole dama zai gane tana cikin damuwa ta kuma yi kuka sosai, saboda idanun nata, kuma kunsan yadda yake tsantsar kaunar ganin idanun nan nata, dole dama zai ɗago ya kallesu, idan ya gansu a kumbure kuma ai dole ya tambaya.
Shiru ya yi bai sake yin magana ba har ya kammala cin abincinsa ya tashi ya fita daga gidan, waje gabaɗaya ya nufa, a waje Mark ya fito da mota ya same shi, akwai in da za su je ne.