Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 68

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 68

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 68: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 68. Kwashe kayan abincin ta yi ta mayar kitchen…

3,345 words

Kwashe kayan abincin ta yi ta mayar kitchen kafin ta koma bedroom nata ta ɗan kwanta, da misalin karfe 10, Lion bai dawo ba haka shi ma Areef, Aseef kuma har lokacin yana ta barci alluran bata sake shi ba. Sam ta kasa barci, ban da tunanin Jehan ba wani abin da take yi, a haka har 11 gari ya yi shiru, kasa jurewa ta yi ta diro kasa daga saman bed ɗin nata, mayafin abayar tata ta ɗauka ta yafa a kanta tare da nufar waje, gabaɗaya sojojin sai kewaye suke yi a cikin harabar gidan dan tabbatar da tsaro, wucesu ta yi ta nufi gate, kwata kwata ta manta Lion ya ce kada ta kuskura ta fita, idanunta sun rufe, ban da tunanin Jehan babu wani abin da take yi.

Hanata fita gateman ya yi, karya ta zuba mishi a in da ta ce mishi Areef ne yake kiranta yana waje, da yake ta san Areef ɗin baya nan. Jin hakan yasa ya buɗe mata gate ɗin ta fita, tafiya ta fara yi bata san ina ta dosa ba, ita dai prison kawai take son zuwa abinta.

Har ta fita daga layin nasu ba tare da ta sani ba, sai a lokacin ne kuma ta tuna ashe bata san hanyar zuwa prison ɗin ba ma, ga shi babu abin hawa, bugu da kari babu kuɗi a hannunta. Daurewa ta yi ta cigaba da tafiya abinta, ta ɗan kara tafiya can ta ci karo da irin matasan nan ƴan shaye shaye, wuka suka zare mata a kan ta basu kuɗin jikinta, dan a tunaninsu irin karuwan nan ne ita.

Kuka ta fara yi jikinta na kerma, ga shi ba abin da ta fito da shi, ko wayarta bata ɗauko ba bare ta basu su rabu da ita, cikin kuka ta ce musu ita bata da kuɗi, ɗaya daga cikinsu ya ce ta yi shiru ta dai'na yi musu kuka ko su kasheta, a yadda take kyakkyawan nan ne zata ce musu bata da kuɗi? Kenan a banza mazan suke kwasanta ne? Duk wannan kyau ɗin nata su kwasa ba biya? Ina karya take yi, ta basu kuɗi ko kuma su kasheta,. Rantse musu da Allah ya rinƙa yi a kan wlh ita bata da kuɗi, jikinta sai kerma yake yi, tana kuka kamar ranta zai fita tare da danasanin fitowarta.

Wuƙa ɗaya daga cikinsu ya fitar dan ya caka mata a ciki tun da taki basu kuɗi, cikin sauri wani daga cikin ya dakatar da shi yana faɗin "Kai wawa ne fa, ba gara muma mu ɗan kwasa na banzan ba tun da ba kuɗi, ka ga karamar yarinya ne, wato wayo mazan suke yi mata su kwashi daɗi basu biyanta, daga ganin wannan yarinyar irin yaran nan ne da uwarsu ta mutu suke hannun matar uba haka, shi ne yasa take fitowa bin maza, idan ba haka ba, ba yadda za'ayi uwarta tana raye ka ganta a yawon ta zubar a cikin daren nan, ka ganta kyakkyawa dan haka muma mu kwashi rabonmu tun da ba kuɗi". Amsa mishi suka yi da e haka ne ya kawo shawara mai kyau gaskiya.

Jin hakan yasa ta yi ƙoƙarin guduwa ta kuma yi musu ihu, damko mayafin abayarta kanta suka yi, da sauri ta cire musu mayafin ta fara gudu dan ta tsira, ina ai tana mace ba zata iya guje musu ba, tuni suka damko gashin kanta, janta suka fara yi da gashin dan tsabar mugunta, ɗaya daga cikinsu ya toshe mata baki, cikin ma gudanar ruwa dake gefe da gefen titi wato lambatu suka yi ƙoƙarin shigar da ita, da yake babu ruwa a ciki, duk ruwan saman da aka yi ya ganganre ya tafi, wajen har ma ya bushe, ga shi ya yi fresh saboda ruwa ya wanke shi.

Yana riƙe da gashin kanta gam, da shi yake janta yana ƙoƙarin shigar da ita ciki, ya toshe mata baki, ita kuma ta yi yarda ta shiga, haushi hakan yasa wanda ya ciro wuka ɗazun ya sake cirowa dan ya yanke mata wani sashe na daga jikinta ko kuma ya caka mata a ciki ta yadda zata zube kasa su shugar da ita, koma ta mutu su za su iya biyan buƙatarsu, cike da mugunta ya yi yunkurin caka mata wukar a cinya, cap Lion ya damki hannunsa, wani irin baya ya yi da hannun ya murɗe da karfi ji kake kas ya karya kashi, ihun azaba ya saki.

Saketa wanda ya riƙeta ɗin ya yi suka yi ƙoƙarin guduwa, kap nasu Mark ya damkosu, da yake sun ɗan yi shaye shayensu babu wani kuzarin kirfi a tattare da su, kwallo da su sosai Mark ya yi kafin ya haɗesu ya cire wandon ɗaya daga cikinsu ya yage shi ya ɗauresu da kyau kamar wasu goro.

Abin da ya faru, lokacin da yaran suka tareta, a lokacin motar Lion ta wuce su, sai dai bai kawo cewa ita ɗin ba ce, ya dai ga mace da maza suna tsaye, a tunaninsa ma duk tare suke, hira suke yi da yake ta bawa hanyar baya, sai dai fa da kallo ɗaya ya yi wa bayan nata ya ji cewa ita ce a zuciyarsa, sanin ita tana gida ba zata taɓa fitowa bane yasa ya kawar da tunanin a ransa suka wuce, bayan ya koma gida ya buƙaci shan fruits, ya kira Areef a waya dan ya sanyata ta kawo mishi tun da shi bashi da numberta, sau uku Areef yana kiran numberta bata ɗauka ba, shi ne ya sake kiran Lion ɗin ya ce dan Allah ya dubata a ɗakinta ko lafiya bata ɗaukar waya, da farko ya share ya kwanta, sai kuma ya tuna da yarinyar da ya gani tsaye cikin mazan nan tabbas bayanta ya yi maka da nata.

Tuna hakan yasa ya fito ya shiga bedroom ɗin nata, bata nan, palo ya fito zuwa waje ya tambayi gateman, a nan ne yake gaya mishi ai ta fita, wani mahaukacin mari ya sakarwa gateman ɗin wanda ya sanya shi sumewa, tsawa ya dakawa sojijin dake wajen a kan hauka suke yi ne da zasu bar wani ya fita daga cikin gidan nan ba tare da saninsa ba, kasa suka yi da kansu suna tsoron ce mishi yarinyar ta ce Areef ne ya kirata, in da ya harzukannan zai iya yanke musu mummunar hukunci, dan haka sai suka ja bakinsu suka yi shiru.

Tuna cewa tana tare da mazan can yasa bai bi ta kansu ba ya ce Mark ya fito da mota suje, to shi ne abin da ya faru a gida da har ya iya sanin in da take ha zo.

RIMSHA

Suna sakinta ta zube gwiwowinta a kasa a wajen, kuka ta saka dan tasan yau ta mutu a hannunsa, daga yanayin tsayuwar da ya yi ma tun bata kai kallonta ga face nasa ba tasan babu mai kwatarta yau, a zafafe rai a matukar ɓace sai huci yake yi ya damko wuyarta, jan ta ya yi har zuwa wajen mota, a gidan baya ya wurgata kafin ya shiga mazaunin driver, ya ja motar ya bar Mark ɗin a wajen, shi yasan ta yadda zai yi ya dawo gida tare da tantiran yaran da ya kama.

A guje ya figi motar tun bai karisa wajen gate ba yake danna musu uban horn, a zafafe sojojin nasa har suna rige rigen buɗe mishi gate ɗin gidan, da wani irin mahaukacin gudu ya danna hancin motar, sai huci yake kamar wani zaki, yau Rimsha ta kure shi, har zai ce kada ta fita kuma ta saka kafa ta fita, kenan tafi karfin shi ya yi mata magana, ta raina shi kenan, dole yau ya kashe yarinyar nan a cewarsa, dan babu wanda ya taɓa yi mishi abin da ta yi mishi.

Dani da ku duk mun san azababben bala'in kishi ne na waƴan can matasan sun taɓata, shi ne yake damunsa, ba wani dan ya ce kada ta fita ta fita, shi ne dai yake ganin ai raina shi ta yi, ya ce kada ta fita ta fita, mu kuma mun san kishin bala'i ne irin nasa.

Tun bai kashe motar ba ta fito a guje ta nufi cikin gida, dan tasan yau tashiga ɗari ba uku ba. Kai tsaye bedroom nata ta nufa, banko kofar ta yi tare da murza key ta je ta haye gado tana kuka tare da danasanin abin da ta yi, shi ma dai bai kashe motar ba ya fito a zafafe, cikin zafin nama yake taku ya bi bayanta, wani soja ne ya zo ya kashe mishi motar.

Kai tsaye bedroom ɗin nata ya nufa, jin kofar a rufe yasa ya yi baya ya take kofar da karfi, wani irin jijjiga ta yi bata buɗe ba, sake yin baya ya yi ya take ta da karfi sai ga kofar a kasa ta ruguzo, ihu ta kurma tare da miƙewa, ta rasa ina zata sanya ranta, ga kofar toilet nata already ya ɓalle mata shi ranar, wajen ɓuya dai ya kare, yau tashi ga ukunta.

Ihu take yi kamar mahaukaciya, a zafafe cikin takun jarumta ya shigo cikin ɗakin, gudu ta fara yi tana ƙokarin neman ina zata ɓuya, Aseef yana can yana barci ya sha allura bai san me yake faruwa ba, bawan Allah duk tsoronsa da allura yau da kansa ya ce ayi mishi, daga nan zaka san bala'in ta kai mishi bala'i.

Dai'dai lokacin motar Areef ya danno kai cikin gidan, damkota shi kuma Lion ɗin ya yi, ya jata har zuwa bedroom nasa, a tsakiyar ɗakin ya yi wurgi da ita, belt na wandonsa ya fara cirewa, dan wlh yau sai ya yi mata azababben dukar mutuwa, idan ta yi sa'a ta rayu to, idan kuma ta mutu ita ta ji yo a cewarsa, har lokacin ihu take yi ta kasa magana.

Jin ihunta yasa Areef ya karisa haurowa benen da sauri, dama yana haurowa zai zo wajen Lion ɗin ne. Yana shigo ya ga abin da yake faruwa, kai tsaye ɗan uwan nasa ya nufa yana tambayarsa me yake faruwa? Me ta yi mishi? Ko kallon in da yake bai yi ba ya zaro belt nasa tare da nufarta gadan gadan, da sauri Areef ɗin ya tare gabansa yana faɗin.

"Sister ki gudu, Lion dan girman Allah kada ka ce zata taɓa lafiyar Rimsha yanzu, wlh zaka iya kasheta har lahira, dan girman Allah ka yafe mata sai zuwa da safe ka yi mata hukunci duk da ma ban san me ta yi maka ba". Ko kallon in da Areef ɗin yake bai yi ba, yau idan bai ga Rimsha ta dai'na numfashi ba, wlh ba zai taɓa jin sanyi a ransa ba, da duka zai kasheta, tun da ita bata jin magana, dan kawai sun yi tafiya ya ɗan sake mata fuska shi ne har take ƙoƙarin kawo raini a tsakaninsu? Ya ce kada ta yi abu ta kama ta yi, wlh babu mai karɓarta yau, sai ta gane annabi ya faku, sau tari dama ɗaukar karamar yarinya yake yi mata shiyasa yake kawar da kansa a kan wasu abubuwa da take yi mishi, bai taɓa ɗaukarta a cikakkiyar babbar mace ba, idan ba ku manta ba a baya duk zaman da suka yi da ita a gidan bai taɓa ɗaga idanu ya kalleta ba sai a ƴan kwanakin nan sanadiyar tafiyar da suka yi ne daya kare mata kallo, a nan ne ya fahimci ta fara girma, kuma hakan yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sanya yake ƙoƙarin hanata kusantar su Areef kamar da, dan kun sani duk da yake Bature shi mutun ne mai kula da addininsa sosai, yana daraja addininsa, wannan dalili yasa yake taka musu birki ya kuma nuna mata ce yanzu ta girma dole ta dai'na zama a jikinsu Aseef kamar da tun da su ba dutse bane, ko yaya suna jin shauki, shi ne ma yasa ɗazun ya daka musu tsawa dan kada ta koma jikin Areef ɗin ta zauna, ita kuma bata ɗaukar hakan kamar wani abin, dan idan baku manta ba, da farko bata yarda ya rungumeta, amma a hankali ya saba mata da hakan, da ta fahimci ba cutar da ita zai yi ba sai ta saki jiki da shi, bugu da kari kuma taga daddynta ya yarda da shi sosai, shiyasa ta sake musu ta ɗaukesu tamkar yayyunta na jini, ga kuma karin yarinta a kanta.

Wani mahaukacin tsawa ya dakawa Areef ɗin a kan ya matsa mishi a gabansa ko ya yi mishi illah, kin matsawa ya yi yana faɗin "Rimsha ki gudu". Da gudu ta miƙe zata yi waje, ture Areef ɗin gefe ya yi da karfi tare da damko gashin kanta ya janyota baya da karfi, kafin ya hankaɗata ta faɗi kasa, ihun azaba ta sakar mishi, na gashi ta da ya ja, kokarin riƙesa Areef ya yi amma ina ya kasa, dan yau ran maza ya ɓaci over, baya ji kuma baya gani, almakashi ya ɗauko daga cikin drawer da chemical nasa suke, wurga mata ya yi yana faɗin "Ɗauka ki yanke gashin nan gabaki ɗaga ki zubar". Babbar magana, saboda waƴan can sun taɓa gashin sun kamata da gashin ne za ta yanke? Lallai Lion akwai bala'in kishi na wuce misali.

Ta kasa koda motsawa saboda tsananin tsoro da tashin hankali, yanzu gabaɗaya kukanta ma ya dai'na fita, yau taga tashin hankali, bata taɓa tunanin haka Lion yake da zuciya na bala'in fitar hankali ba, lallai ma, kuma a hakan ma saboda ita mace ce yasa bai wani hau ba, dan yasan duka ɗaya kwakkwara idan ya yi mata, ba zata tashi ba, da namiji ne ya yi mishi laifi ai data ga bala'in da ya sha gaban tunaninta.

Ganin haka yasa Areef ya juya ya fice daga cikin ɗakin dan yasa in dai Lion ya hau to duk duniya ba mai iya dannarsa, mafita ɗaya, shi ne su yi mishi allura, amma idan ya ce zai tare shi ma zasu yi faɗa ne, zai yi mishi illar a banza, ga shi dama ba lafiya gare shi ba, ko da yana da lafiya ma Lion ya fi karfinsa, idan suka sami ɓacin rana suka yi faɗa shi yake dakuwa dan karfin ba ɗaya ba, kuma yanzu a halin da Lion yake ciki ba zai ma tuna cewa Areef ɗin yana da wani ciwo ba ya tausaya mishi, idan ya tare mishi gaba tsab zai yi mishi dukan mutuwa, ko sun haɗu sun haɗa karfi da Tga basu iya riƙe shi idan ya fusata, alluran dai ita ce mafita.

Bedroom nasa ya koma, alluran ya haɗa na barci mai karfi na 30 mins, ɗaya daga cikin alluransa da ake masa time da yake jinya ne, lokacin da ya dawo bedroom ɗin Rimsha ta kasa motsawa har lokacin, shi kuma yana ƙoƙarin naɗa belt nasa zai zaneta. "Ki yanke gashin nan nace!!"

Tsawa ya daka mata wanda ya sanyata warwarewa, a sukwane ta ɗauki almakashin da nufin ta fara datse gashin nata, hawayenta har sun kafe dan azaba, hannunta ma da kyar ya iya riƙe almakashin saboda kerma da gabaɗaya ilahirin jikinta yake yi.

Shammatarsa Areef ɗin ya yi ya caka mishi alluran a hannu wajen damatsansa tare da zira mishi ruwanta a cikin jikinsa, da yake abune da suka saba yi, sun san yadda suke yi, alluran yana nan ɗan karami da shi, ba zama ka taɓa cewa allura bane, suna amfani da shi wajen kama manyan ƴan ta'addan idan sun shiga yakin sunkuru, da sun yi wa mutun ba zai fi second goma ba zai zube kasa.

A fusace Lion ɗin ya juyo ya damko wuyar Areef ɗin da karfi, sai kuma a hankali idanunsa suka rufe alamar barci, yana ƙoƙarin zubawa kasa, duk da ciwon da yake kirjin Areef ɗin bai hana shi tare ɗan uwan nasa ba ya faɗa saman kirjinsa, wash ya furta da ɗan karfi, dan ya ji zafin ciwon nasa, da kyar ya iya kai Lion ɗin saman bed nasa ya kwantar da shi kusa da Aseef kafin ya zauna a bakin gadon yana sauke nauyayyar ajiyar zuciya.

Miƙa mata hannu ya yi a kan ta bashi almakashin da yake hannunta, ba musu ta rarrafo zuwa gabansa ta miƙa mishi, karɓa ya yi yana sake sauke nauyayyar ajiyar zuciya. "Kawo mini ruwa". Ya faɗa yana ajiye almakashin a gefe, da kyar ta iya miƙewa ta nufi fridge dake cikin ɗakin, ruwa ta ɗauko mishi mai sanyi ta kawo, karɓa ya yi tare da buɗewa ya kafa kai, sai da ya shanye dukka kafin ya cire kansa.

"Me ya haɗaki da Lion?". Ba ɓoye ɓoye ta gaya mishi, bakin ciki tamkar ya tsinka mata mari, a fusace shi ma ya fara magana "Kina hauka ne zaki fita gidan nan da wannan dare haka? Kin san hanyar zuwa prison ɗin ne? Kin san da wa zaki haɗu a hanya? Da ace Lion bai ganki ba me kike tunanin zai faru? Gaskiya kin yi laifi sosai wlh, ya kamata nima na zane ki, idan ma ya hanaki zuwa ba sai ki kirani a waya ki gaya mini ba, idan kina son lallai sai kinga ƴar uwarta ki, ai akwai hanyoyi da dama da zan haɗa ki da ita wanda ba sai lallai ki take maganar da Lion ya gaya miki ba, to ki sani wlh Lion yana iya kin saka baki a case ɗin ƴar uwar taki dalilin laifin nan da kika yi mishi, me yasa kike son ɓata komai da kan ki ne? Meyasa ba zaki gaya mini ba? Kin taɓa gaya mini ga abin da kike so ban samo miki hanyar da zaki same shi bane?". Girgiza kai ta yi tana hawaye tana bashi hakuri, faɗa ya yi mata sosai a kan kada ta sake yin irin wannan gangancin, duniyar yanzu sai a hankali, tsab yarancan zasu lalata mata rayuwa, yanzu ta je ta yi wanka ta kwanta zuwa gobe ko ta wani hali zai haɗata da Jehan ɗin.

Kallon Lion dake kwance ta yi ta kasa motsawa, ya gane nufinta dan haka sai ya ce "Kije babu wani abu, idan ya tashi zai zama normal, zuciyar zata sauka, amma kada ki kara irin wannan kuskuren, sannan kada ki yarda nan kusa ya sake ganin gashin nan naki, dan wlh kika bari ya gani sai ya yanke shi dukka ya zubar, ki kyale shi sai ya huce na kwana biyu, ai wlh kin ma yi muguwar sa'a, na ma kara fahimtar wani abu a tsakaninku, ba dan haka ba Allah yau da sai dai wata ba ke ba, gateman kuma sai dai mu ce Allah ya jikansa, ki sani kuma idan ya mutu nauyin na kanki dan ke kika yi mishi karya kika sanya ya karya aikinsa, sai ki san yadda zaki yi ki shawo kan Lion ɗin kada ya yi mishi hukunci, dan yanzu Lion sai ya fi jin maganarki sama da tawa, je ki yi wanka ki kwanta sai da safe". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya nufi waje dan ya je ya yi wanka ya zo ya duba lafiyar Aseef kafin ya kwanta.

Da kyar ta iya miƙewa, zubawa Lion ɗin idanu ta yi yadda yake barci ga fuskarnan a ɗaure tamau tamkar hadari, rai a matukar ɓace, wani irin azababben so da kaunarsa ne yake kara shigarta kamar me, matsowa kusa da shi ta yi, kasa kasa ta fara magana tare da tsugunnawa a kusa da gadon "Kayi hakuri ba zan sake ba, na san nayi laifi sosai, ban ji daɗin ɓata maka rai da nayi ba, amma In Sha Allah ba zan sake ba, ka sani ni koma me ina sonka, kuma ba zan dai'na ba, wannan ita ce kaddarata ni kuma". Ta kai karshen maganar tare da riƙo hannunsa guda ɗaya a cikin nata, ga Aseef kwance a gefensa yana sharara barci.

Zubawa yatsun hannun nasa idanu ta yi tana kare musu kallo, kyau iya kyau, sai sheki farcensa suke yi ga su farare tas kamar madara, hannunsa laushi sosai kamar bai taɓa yin wani aiki ba. Ta ɗan jima tana kallon hannun nasa kafin ta sake shi ta miƙe ta nufi waje.

Readers Also Read