Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 69
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 69: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 69. A gurguje ta yi wanka ta fito ta shirya cikin…
3,370 words
A gurguje ta yi wanka ta fito ta shirya cikin kayan barcinta masu kyau, dogon wando ne da riga mai dogon hannu, launin pink color, fesa perfume nata ta yi tare da hayewa gado ta kwanta, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita dan ta gaji, ta wahala ba karya.
After 1 day👌
Daddyn Rimsha bai samu damar tashi a jiya ba, sai yau ya taso shi da Tyrone, Tga dai har yanzu yana fama da jinya, ba karya ya wahala a wajen yakar wannan kungiya ta su Areef.
Shiri tsab Aseef ya yi cikin wandon jeans baki da polo t-shirt sky blue, ya yi kyau sosai, ya ɗan sami lafiya da kwarinjiki, kiran Akila ya yi a waya ya ce mata ga shi nan zuwa gidansu, dan ba zai iya hakuri yau kwana uku bai ganta ba, ba zai iya cika kwana na huɗu ba, ga shi gobe ɗaurin aurenta, tsabar kuka da zazzaɓin da take yi, sam muryarta baya fita, su Umaisha duk suna a tare da ita, amma ina ko sannu bata iya ce musu, sai aikin gyara Hjy Batula take yi mata, amma ba uhm bare uhm, yau za'ayi mata kunshi na amare, shi kuma Irfan bai wani damu sai ya rinƙa hira da ita ko ya kirata a waya ba, a cewarsa tun da bata da lafiya gara ya kyaleta kawai, hakan yasa baya damuwa da kiranta yake kyaleta.
Jin Aseef zai zo yasa ta tashi da kyar ta shiga bedroom ɗin Ammie dan ta sanar da ita, bata yin komai sai da yardan mahaifiyar tata, Aunty, Hjy Batula, Ammie ta samu a cikin ɗakin, sannu ta yi musu kafin ta ce "Ammie ina son yin magana dake". Okey ta amsa tare da miƙewa ta zo ta riƙo hannunta suka nufi waje, har wani jiri baiwar Allah take gani.
Bedroom ɗin Abba ta shiga da ita, da yake baya nan suna can shi da Abbi suna nasu shirye shiryen, kun san yadda bikin turawa, da uba da ƴaƴan duk haɗewa suke yi sai ka rasa gane ina iyayen suke ina yaran, to wannan ma haka ne, dan Abba da Abbi dai duk ɗabi'ar tana tare da da su, dan sune manya sun girma sosai a kasar Russia kafin su dawo Naija, so ɗabi'ar ta fi zama a jikinsu sosai.
"Akila lafiya?" Ammie ta tambaya, da kyar ta iya gaya mata Aseef ne ya kirata a kan yana zuwa, shiru Ammie ta ɗan yi kafin ta ce "To Akila ba zan hanaki zuwa wajensa ba, amma dai ki san ta in da zaki bi ki fita kada a ganki, kin ga jama'a suna cike, kada ki ja mana magana, kuma ki ce da Aseef ɗin ya tsayar da motarsa a can nesa da gidan nan, wlh duk lokacin da na yi sallah ina rokan miki mafita, Aseef dai shi ne idan na tuna zaki aura hankali yake kwanciya ba Irfan ba, shiyasa bana hanaki kula shi, dan ina ji a jikina kamar da shi za'a ɗaura auren nan gobe ba Irfan ba, amma Allah shi ne masanin gaibu, ba zan taɓa son a baki abin da baki so ba, ki je ki gan shi, amma kada ki jima, ki kuma kwantar mishi da hankali sosai, dan yadda na ganshi kwana huɗu da suka wuce sai da nayi mishi kwallah". Allah sarki babu mai fahimtarka sama da Mahaifiyarka a duniyar nan, uwa ta wuce wasa, babu mai son abin da zaka so sama da mahaifiya, ita ke sadaukar da farincikinta dan ƴaƴanta, uwa baban jigoce ga rayuwar ɗan adam, Allah ka jikan iyayenmu da suka rigamu gidan gaskiya, waƴan da suke raye Allah ka kara musu lafiya, ka kuma bamu ikon yi musu biyayya mu bisu sau da kafa.
Rungume Ammie nata ta yi tana ruwan hawaye, ita kaɗai tasan me take ji a ziciyarta, wlh tasan idan aka ce yau an ɗaura aurenta da wanin Aseef shikenan tata tazo karshe.
Ɗan raba jikinsu Ammie ta yi tana faɗin "Kije kada su Halima su yi tunanin wani abin muke faɗa da bamu yi magana a idanunsu ba, ki kula dai kada ki bari Abbanki or wani ya ganki, idan kika bari hakan ta faru kin san sauran, komai sai ya lalace miki, zaki haɗu da fushin mahaifinki sosai". Okey ta amsa da shi tare da juyawa ta fice da sauri, bedroom na Akil ta nufa, kayan Umaisha ta sanya, dama na gaya muku a baya idan baku manta ba, da Umaisha da Akila da Rimsha yanayin jikinsu kusan ɗaya, shape nasu ɗaya, dan haka kayan Umaisha sai ya zauna ɗam a jikinta tamkar nata ne dama bana Umaisha ɗin ba, ɗinkin riga da skit ne, kayan sun fita sosai.
Bedroom nata ta koma ta ɗauko bayafinta, dan Umaisha bata da mayafi, sai zumbula zumbulan hijabai har kasa, ita kuma ba zata iya saka hijabi ba gaskiya a cewarta, cikin dabara ta ɗauki mayafin bata bari su Umaisha ɗin sun ga me ta ɗauka ba, sai murna suke yi yau ta ji sauki har ta sanya kaya masu kyau, sai fara'a Umaisha take yi, Jelly kam tana kwance shiru kamar wata malamar islamiya, da alama dai malaikun natsuwa ne suka yi mata addu'a.
Bata wani kula su ba ta nufi waje tana faɗa musu tana zuwa, bedroom ɗin Akil ɗin ta sake komawa ta ɗauko face mask ta sanya a face nata tare da fesa perfume nasa, akwai mutane sosai a palo, haka ta zo ta wucesu, wasu sun gane ita ce wasu kuma basu gane ba.
A harabar gidan ma akwai jama'a amma haka ta ketasu ta wuce zuwa waje, da yake a harabar gidan sai hidima da aikace aikace suke yi, sai basu lura da ita ba, su kuma su Irfan su part ɗin Imran, waje ta nufa, ta yi tafi mai ɗan nisa kaɗan, amma tana iya hango gidan nasu, sannan ta tsaya tare da kiran shi a waya a kan ga in da zai sameta kada ya je kofar gida, okey ya amsa mata.
Bata fi minti 10 da tsayuwa ba sai ga shi nan ya danno hancin motarsa, a hankali yake tuka motar, hakan zai sa ka gane yana cikin tsantsar mawuyacin yanayi. Cikin sauri ta buɗe kofar motar ta shiga gidan gaba dan kada wani ma ya ganta, ko yaya Akil ya ganta, Alhamdulila glass ɗin motar ma baka ce, ta kuma yi sa'a ba wanda ya ganta ɗin, ruwa ya ɗauko a roba ya miƙa mata dan ya ga tana haki kamar wadda ta yi gudu, karɓa ta yi tare da cire face mask ɗin face nata, ta kafa ruwan a bakinta, ta sha mai ɗan yawa kafin ta cire ta mayar ta rufe tare da miƙa mishi, karɓa ya yi ya ajiye.
Zuba mata idanu ya yi na ƴan mintoci kafin nan ya ce "Heartbeat kin ga yadda kika rame kuwa? Ba zan iya juran hakan ba gaskiya". Ɗago dara daran idanunta na gadon nan ta yi, da ta rame ma sai idanun nata suka kara fitowa dara dara da su over, zuba mishi ido sosai ta yi, shi ma ya rame sosai, na shi ramar ma ya fi nata, duk yana harkitse.
"My shagwaɓati hakuri zamu yi, mu fawwalawa Allah komai, In Sha Allah idan mu rabon juna ne Allah zai kawo mana mafita, matar mutun ai kabarinsa ne". Nisawa ya yi kafin nan ya riƙo hannayenta tare da matsowa kusa da ita, zuba mata ido sosai ya yi while ita kuma tana kallon kasa.
A nutse cikin sanyin murya ya fara magana "Yanzu da gaske Heartbeat Abba ba zai canza magana ba? Da gaske Abba ba zai bani ke ba? Please ki ce mashi zan yi duk abin da yake so, dan Allah kada ya rabani dake, wlh zan iya mutuwa idan hakan ta faru, please my heartbeat ki ji tausayina, ni ban san menene soyayya ba sai a kanki, ban taɓa yin soyayya ba sai a kanki, tun rana ta farko da prof ya tura mini hotonki nayi bala'in kamuwa da kuanarki, wlh zuciyata ba zata iya jure rashinki ba, ba zan iya ba, ki tausayawa rayuwata, wlh nafi kowa sonki, na fi shi ma Irfan ɗin sonki, please my heartbeat ki rarrashi Abba, kome yake so nayi mashi in dai bai saɓawa Allah ba, to zan yi mashi dan ya bani ke, kin ji ko?". Ya kai karshen maganar yana zubar da kwallah.
Hawaye ne suka fara gangaromata daga eyes nata zuwa face nata, ta kasa ɗago kai ta kalle shi, tabbas bata san me yake cikin zuciyarsa ba, amma dai tana da yakinin idan bai same ta ɗin ba, kamar yadda ya faɗa, mutuwa zai yi, ta tabbatar da yana yi mata wani irin mahaukacin so, kuma ita ma a nata ɓangaren tabbas idan ba shi ɗin ta aura ba, zuciyarta zata ita bugawa, shi ne zuciyarta ta aminta da shi, shi ne zaɓinta, bazata iya rayuwa da wani namijin bayan shi ba.
Ganin tana hawaye ba ƙaramin ɗaga mashi hankali ta yi ba, cikin sauri ya sake hannayenta tare da ɗago haɓarta suna fuskantar juna, muryarsa har sarkewa yake yi wajen cewa "My Heartbeat please and please ki yi shiru, ki yi hakuri kada ki kara mini zafi a kan zafi, zan iya jure komai amma ban da kukanki heartbeat nawa, wlh hawayenki na bakin ciki, daidai yake da ana caka mini wuƙa a kahon zuciyata, zafi nake ji my heartbeat idan kina kuka, ni zan iya ɗaukar komai ban da kukanki, ki daina please". Yana magana yana hawaye shi ma.
Cikin kuka ta ce "My shagwaɓati kukan ka yafi nawa zama tashin hankali da bala'i a gare ni, ka daina dan Allah, wlh idan kana hawaye zuciyata zata iya bugawa ka ji?".
Bai san time da ya jawota jikinsa ba, wani irin shock suka ji su dukkansu biyu, dannewa ya yi tare da fara rarrashinta cikin salo da dabara tare da natsuwa, tamkar kara ingiza ta yake yi, sai kara kukan take yi, ta lafe a kirjinsa tana jan hanci tare da shaƙar daddaɗar kamshin perfume nasa mai kwantar mata da hankali.
Hannu yasa ya ɗago haɓarta daga saman faffaɗar kirjin nasa, ya zama suna fuskantar juna, goge mata hawaye ya shiga yi yana mai cigaba da rarrashinta, kukanta babbar bala'i ce a gare shi, zuciyarsa ba zata ɗauka ba.
Ganin taki daina ruwan hawayen ne yasa ya ranƙwafo kanta sosai tare da fito da harshensa ya fara lashe hawayen nata, cak ta tsaya da kukan nata sakamakon wani irin baƙon yanayi da ta ji na sanya harshensa a kan fuskarta da ya yi.
Shi kuwa tas ya lashe hawayen nata kafin ya ɗago da brawn eyes nasa ya sauƙesu cikin tata fararen idanun. Da kyar ya ƙaƙalo murmushin dole dan ya sanya ta farinciki, zuba mishi ido ta yi, ba ko kyaftawa, shi ma dai zuba mata dara daran idanuwansa ya yi yana mai kare mata kallo.
Sun ɗan ɗauki lokaci a haka kafin ya matso da fuskarsa daf da tata sosai ta yadda suna iya jiyo numfashin juna, can kasan maƙoshinsa da kyar ya iya furta "Can i kiss you one my heartbeat?". Wani irin faɗuwar gaba ta ji jin yadda ya yi maganar, ji take yi tamkar rabuwa da shi zata yi, ta kasa magana, ta dai zuba mashi ido kawai.
Ganin bata yi magana bane yasa ya matso da lausasan laɓɓansa zuwa saman tata, wani dogon numfashi ta ja tare da sauƙewa a hankali, yayin da shi kuma ya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, a hankali cikin natsuwa ya haɗe bakinsu ya shiga kissing nata.
Sumar zaune ta yi mishi, ko da sunan wasa ba wanda ya taɓa kissing nata, bata ma san ya ake ji ba idan aka yi kiss sai yau, tana dai karance karance novel nata, da kalle kallen film, amma bata taɓa ji a zahiri ba.
Shi kuwa kara jawota jikinsa ya yi tare da rungumota da kyau da kyau, kissing nata yake yi babu kama hannun yaro, cikin dabara ya zame mata mayafin kanta tare da ɗankwalinta baki ɗaya, shi ma bai taɓa yin kiss ba, bai san ya ake ji ba sai yau, kuma yau ɗin ma ya haɗu da ya yi wa macen da ya fi kauna a duniya, wow abin ba'a magana.
Shafa kyakkywar gashin kanta da ya sha gyaran biki ya shiga yi yana mai kara matseta a jikinsa bakinsu na a cikin na juna.
Sosai ya yi kissing nata, ita kuma ta yi mashi sumar zaune, duk jikinta ya mutu, ko motsin kirki ta kasa yi, bata ankaraba sai jin sauƙar hannunsa ta yi a saman breast nata, cikin sauri ta kwace bakinta tare da ja baya daga jikin nasa tana mai laluɓar ɗankwalinta.
Idanunwansa sun yi jawur, murya na rawa ya ce "My heartbeat lafiya kuwa? Me yasa zaki hanani?". Shiru ta kasa yi mishi magana, sai faman ɗaura ɗankwalinta take yi, tanayi tana hawaye, ji take yi kamar shikenan zata rabu da shi.
Tana ƙoƙarin mayar da mayafin nata ya yi saurin riƙewa yana faɗin "My heartbeat talk to me now".
Sai a lokacin ta ɗago idanuwanta wadda suke cike tap da ruwan hawaye, ga shi wasu kuma suna zuba mata a saman face nata, wani na bin wani.
"Ya subhanallah, Heartbeat me ya faru kuma kike sake yin kuka haka? Saboda na yi kissing naki ne? To idan saboda haka ne ki yi hakuri, na tuba, bazan kara ba, kin ji ko? Please ki daina kuka".
Kin yi mishi magana ta yi, da sauri ta sakin mishi mayafin tare da fita daga cikin motar, da gudu ta nuf gida tana sakin kuka mai sauti, tasan ko zata mutu Abba ba zai canza magana ba, dole gobe a ɗaura aurenta da Irfan, ga shi kuma ta zo ta yarda Heartbeat nata ya yi mata kiss, yanzu me makoman hakan kenan? Taci amanar yaya Irfan ko dai yaya?. Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun.
Cikin sauri da zafin nama shi ma ya fito daga cikin motar, hannunsa na riƙe da mayafinta da ta bar mishi. Kafin ya fito har ta shige ciki gida, kifa kansa ya yi a jikin motar yana kuka tare da dana sanin kissed ɗin nata da ya yi, a tunaninsa hakan ce tasa ta gudu, kuma hakan ce ta sakata kuka sosai.
Ya jima a wajen ya kasa motsawa, banda ruwan hawaye babu abin da yake yi, lokaci guda duk ilahirin jikinsa ya yi zafi jau alamar zazzaɓi, zuciyarsa tamkar zata fashe, sai da ya kwashi good 30 mins a haka, da kyar ya iya lallaɓawa ya shiga cikin motar.
Wayarsa ya ɗauko ya fara kiran number ta, dan ya rarrasheta ta yi shiru, yasan halinta sarai, yanzu tana can tana kuka, ba zai iya tafiya ba idan har bai rarrasheta ta yi shiru ba.
Sau uku yana kiranta bata ɗauka ba, sai a na huɗun ne ta ɗauka, ban da kuka babu wani sauti dake fitowa daga cikin wayar, dafe kansa dake barazanar tarwatsewa ya yi, zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri, da kyar yake fitar da numfashi mai zafin zazzaɓi, su dukkansu biyu sun kurɓi gubar soyayya, hawaye babbiyu yake zuba mishi daga idanunsa, ya kasa magana, ita ma ta kasa magana, dukkansu sai kuka suke yi wa juna,..... To fa, waye kenan zai rarrashi ɗan uwa? HEARTBEAT+ HEATHER ƴan auta kenan, kuma shagwaɓaɓɓu, bugun zuciyar family'ns guda biyu, sanyin idanunyar mutane da dama, BABBAR MAGANA akwai kallo da.
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*
💋Dedicated to My comments section groups people's🌹
E55-56💋
Jin irin sautin numfashinsa dake fita ta cikin wayar ne yasa ta tsagaita da dukan da take yi, a ruɗe cikin tashin hankali ta ambaci sunansa, shiru ya kasa amsawa, sake kiransa ta yi hawaye wani na bin wani a fuskarta, tana kwance a saman bed ɗin Akil, nan ma shiru, sau uku tana kira bai amsa ba, dan ba zai iya magana ba.
A tsananin razane ta miƙe zaune tare da dirowa kasa ta nufi waje, tamkar wata zararriya haka ta nufi waje babu ko mayafi a jikinta, ƴan biki suna ta hidimar gabansu, sai aikace aikacen girke girke da sauransu suke yi, haka ta keta mutane ta nufi waje.
A guje ta nufi motar tasa, ya kifa kai da jikin steering motar yana wani irin numfashi wanda da ka ji kasan da kyar yake fitar da ita, a tsananin tashin hankali ta buɗe motar ta shiga, sunansa ta rinƙa ambata Heartbeat! Heartbeat, amma ina ya kasa amsawa, jijjiga shi ta fara yi, jin irin azababben zafin da jikinsa ya yi yasa ta kara tsorata sosai tare da yin yunkurin ɗago kansa daga jikin steering dan ta kalli face nasa.
Tana ɗago shi ya sake mata jiki ya kwanta a saman kafaɗarta yana fitar da numfashi mai tsananin zafi, girgiza kumatunsa ta fara yi tana ambatar sunansa, ina ko motsin kirki baya yi, ban da wannan numfashin da yake fitarwa babu wani abin da zaka ji a tattare da shi, wayar dake hannunsa ta karɓa dan ta kira ɗaya daga cikin ƴan uwansa su zo kada ya mutu.
Kash wayar da akwai password a jikinta, tamkar zuciyarta zata fashe ta fito waje haka take ji, cikin fitar hayyaci ta fara lalauɓar number Imran a wayarta da ta fito da ita, har lokacin ko motsawa bai yi ba.
Bugu ɗaya ta yi wa Imran ya ɗauka, kuka ya hanata wani maganar kirki. "Yaya Imran ka zo, kazo Heartbeat zai mutu". "Akila ki natsu ki yi mini magana, na zo ina kuma?". Da kyar ta iya cewa "Kazo waje, yana waje". Daga haka ta katse kiran ta cigaba da ambatar sunansa.
Tana kashe wayar sai ga shi ya fito da sauri, nufo motar tasu ya yi, cikin sauri ya buɗe kofar ɓangaren da take, ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin abin da yake faruwa, ina ai idan wani abin ya sami Aseef a dalilin familynsu ya san sun shiga uku da Lion, dan ba zai taɓa ɗaukar wannan kaddara ba, shi da likitoci ma suka tabbatar mishi da Aseef ɗin ya mutu a baya, amma ya kafe ya ce sam ba za'a binne shi ba, ba wanda zai sanya mishi ɗan uwa a rami, bare kuma yanzu Aseef ya mutu sanadiyar AKila, ai wlh duk sai Lion ya kashe su har lahira, idan ma bai haɗa da mai gadi da kowa da kowa ba, ai duk wanda ma ya zo bikin nan sai ya mutu.
Fita ya ce ta yi bari ya duba Aseef ɗin, da kyar ta iya raba jikinta da na shi, ta kwantar da shi a jikin headboard na kujerar ta fito, sai kuka take gwanin ban tausayi, shi ga cikin motar ya yi yana ambatar sunansa, amma ina ba zai iya amsawa, ya rigada ya kurɓi gabar soyayya.
"Akila ki koma cikin gida bari na mayar da shi gida dan ayi gaggawar duba lafiyarsa kin ji?". Durkushewa a kasa a wajen ta yi tana kuka kamar ranta zai fita, cikin kuka ta ce "Yaya Imran dan Allah ka tafi da ni, wlh ba zan iya zama ban san halin da yake ciki ba". Tana magana tana dafe kirjinta da yake yi mata tsananin ciwo tamkar zata mutu.
"A'a Akila ki je gida, idan na tafi dake abin ba zai yi mana kyau ba dukkanmu, ke dai ki je gida, baki san waye kike tare da shi ba ne shiyasa kike cewa na tafi da ke, so ki koma kawai". A gudu ta miƙe ta nufi gida, binta da kallo ya yi yana matuƙar tausaya musu, ya rasa ya zai yi, tunani yake a kan wlh dukkansu biyu zasu iya mutuwa fa idan ba'a duba wannan lamari ba.
Fitowa ya yi daga cikin motar ya dawo ta ɓangaren da Aseef ɗin yake ciki, ya buɗe kofar, da kyar ya iya fito da shi ya mayar da shi gidan baya, sannan ya shiga mazaunin driver ya tada motar, da gudun gaske ya figita dan su isa gida da wuri, idan ba haka ba daga yanzu zuwa ko wani lokaci suna iya rasa Aseef ɗin bakiɗaya.