Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 70

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 70

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 70: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 70. Horn ɗaya ya yi Donald ya buɗe mishi gate…

3,327 words

Horn ɗaya ya yi Donald ya buɗe mishi gate ɗin, dan gateman kam yana gadon asibiti bai farfaɗo ba, ciki ya danno hancin motar, yana kasheta ya fito da sauri ya nufi cikin gida, ya kuwa yi sa'a ya sami Areef da daddyn Rimsha a palo suna hira, Rimsha kuma ta tafi school bata nan daddynta ya iso, sai dai ta dawo ta same shi kawai, Jehan tana ɗaki tana barci.

Cikin tsananin tashin hankali ya ce da Areef "Ina Lion?" Miƙewa Areef ɗin ya yi yana kallonsa da mamaki na lafiya?.

Lion baya nan ya fita neman Aseef ɗin ne, dan ya yi ta kiran numbersa bata shiga, suna zaune suka ji su coper suna ta daka haushi, hakan yasa Lion ɗin yasan Aseef baya lafiya, shi ne ya yi ƙoƙarin neman numbersa network babu kyau, bai same shi ba, wannan dalilin yasa ya fita nemansa.

Areef na kokarin tambayarsa ko lafiya ya shigo a birkice haka, sai suka ji tsayuwar motar Lion a harabar gidan, da sauri Imran ɗin ya juya, dan ba zai gayawa Areef me ake ciki ba, yasan ba zai iya ɗaukar Aseef ba saboda ciwonsa, dan haka sai ya nufi wajen kawai.

Da sauri suka rufa mishi baya, Lion na shigowa shi kuma yana fita, karo suka yi, baya yaɗan yi yana gaya mishi ya zo ya fito da Aseef daga cikin mota, ya yi sauri dan yana bukatar taimakon gaggawa, ɗan zaro idanu ya yi, ya ma kasa tambayar me ya sami ɗan uwan nasa, dan ba zai iya jin mummunar labari a kan TRIPLETS nasa ba, bai shiryawa hakan ba, kuma ba shi da wannan juriyar gaskiya.

Cikin sauri suka rankaya zuwa wajen motar, a zafafe Areef ya buɗe kofar ɓangaren da Aseef ɗin yake ciki, dan jikinsa har tsuma take yi yana son ya ga menene ya sami ɗan uwansa. Yana zaune kansa na jingine da jikin headboard na kujerar, tamkar babu rai a jikinsa, da alama ya suma ne, ga kuma mayafin Akilar a hannunsa bai saki ba, ya riƙe gam.

Areef zai taɓa shi Lion ya dakatar da shi tare da kai hannu dukka biyu ya tallaɓo shi, Imran kam baya ya yi yana jiran ya ga saukar aradu kawai, dan kuwa yasan akwai yaki yau ba kaɗan ba, wani abu ya sami Aseef dalilin AKila, tab aikuwa Akila zata mutu a tunaninsa.

Ciki Lion ya wuce da shi bayan ya saɓa shi a kafaɗarsa, har lokacin mayafin Akilar na hannunsa, saman bed nasa a bedroom nasa ya kwantar da shi, kallon juna Imran da Areef suka yi, yana ƙoƙarin tambayarsa menene ya sami ɗan uwan nasa, sexy voice ɗin Lion ya katse shi da cewa "Bani ruwa Areef". Da sauri ya nufi fridge.

Roba ɗaya mai sanyi ya ɗauko ya dawo ya miƙa mishi, karɓa ya yi tare da buɗewa ya tarfo a hannunsa, a fuska ya shafawa Aseef ɗin, shiru bai motsa ba, sake tarfowa ya yi ya shafa masa, nan ma shiru, sai a karo na uku ne ya ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali, sai kuma kuka ya biyo baya, dukkansu zuba mishi idanu suka yi suna kallon ikon Allah.

Kuka yake yi sosai, idanuwansa a datse gam ya fara sambatu. "Ki ce da Abba wlh zan iya mutuwa, ba zan iya jurewa ba, ki yafe mini dukkan abin da nayi miki a rayuwar da muka yi tare, ni nasan yau ba sai gobe ba zan rayu ba, mutuwa zan yi, zuciyata tana yi mini zafi sosai, mutuwa zan yi my heartbeat, ba zan rayu ba, idan na mutu ki rinƙa yi mini addu'a kin ji? Kuma kada ki manta dani, kin ga dai kin yi mini alkawarin ba zaki rabu da ni ba ko? Kuma ba zaki manta da ni ba, to dan Allah kada ki manta da ni, ki cika alkawari".

Juyowa Lion ya yi da kallonsa zuwa kan Areef while shi kuma Areef ɗin ya juya yana kallon Imran, shi kuma Imran daddyn Rimsha yake kallo. "Me ya sami my pleasure?!" Lion ya tambaya cikin tsawa. A tare dukkansu suka dawo da kallonsu kan shi.

Jin muryar Lion ɗin yasa Aseef ɗin dakatawa daga sambatun da yake yi, a hankali ya waro idanuwansa da suka riƙiɗe suka yi ja sosai na wuce misali, da kyar ya kai hannunsa ya riƙo hannun Lion ɗin, jin ya kama hannunsa yasa ya juyo da kallonsa kansa.

Zuba mishi idanu ya yi kafin ya kankame hannunsa cikin na shi, "My pleasure what is happening? What is wrong with you? Who break your heart?" Cewar Lion ɗin kenan.

Ba ɓoye ɓoye ya gaya mishi komai, tun farkon ganinsa da Akika har yau da suka yi sallamar bankwana, daga karshe ya rufe da cewa "Ba zan iya rabuwa da ita ba Lion, mutuwa zan yi yau na sani, aurenta za'a ɗaura da wani, ba zan iya juran hakan ba, burina a duniya bai wuce na aureta muyi rayuwa a tare ba, shi ne burina na karshe kuma zan mutu da shi ban cika ba, zafi zuciyata take yi mini sosai, ku yafe mini duk abin da na taɓa muku a rayuwarmu, ni na san ba zan tashi ba, ina ji a jikina mutuwa zan yi, zafi nake ji my TRIPLETS, ban san ya zan yi ba, jikina ciwo yake yi mini, amma dan Allah idan na mutu, in kun zo binne ni ku sakani da mayafin Heartbeat data bar mini, shi ne abinta ɗaya kawai da nake da shi, dan haka ku rufeni a rami da shi". Yana magana yana tari tare da fitar da wani irin numfashi mara daɗin ji na zafin zazzaɓi.

Duk taurin zuciya irin na daddyn Rimsha sai da ya yi hawaye, Imran kam tuni dama hawaye ya wanke mishi fuska sosai.

A ɓangaren Akila kuwa, bata kai ga shiga gida ba Abba ya ganta, ganin haka yasa ya ce da Abbi ya taro dukka mazan gidan yau za'a ɗaura auren nan, dan kuwa ya ga komai, ya ga motar Aseef, shiyasa dan gudun abin ya zama matsala ya san halin Turawa yanzu Aseef yana iya ɗaukarta su tafi kasarsu ma ko kuma ya biya bukatarsa da ita, shiyasa dan gujewa hakan ya ce a ɗaura auren yau kowa ya huta, bai san cewa Aseef kam soyayyar gaskiya yake yi mata ba, tsakani da Allah yake sonta babu wasa ko kaɗan, so ba zai taɓa kwanciya da ita ba tare da aure ba, lokacin da yake krista ma bai yi zina ba, baruwansa da mata, yanzu da ya musulta ya san girman Allah ba zai taɓa aikata hakan ba.

Lokacin da ta samu labarin Abba ya ce yau za'a ɗaura aurenta, a haukace ta nemo wayarta ta fara kiran number Aseef ɗin, sai kuka take yi.

Sau uku ta kira bai ɗauka ba dan wayar ya barta a mota, number Imran ta kira, bugu ɗaya ya ɗauka dan ya ji tana lafiya ne ko yaya, saboda shi ma bai cire rai akan dole sai ta cutu ba, hakan ma yasa ya ɗauki kira, sai kuma ya yi rashin sa'a wayar tasa volume tata a kure, harta Aseef ɗin dake kwance yana iya jiyo komai da ta faɗa.

A tsananin ruɗe ta ce "Yaya Imran zan mutu, yaya Imran ka taimake ni, Abba ya ce yau za'a ɗaura auren, ya ce yanzu ba sai anjuma ba, wlh mutuwa zan yi, ka haɗani da Heartbeat zan yi magana da shi wata kila shi ne zai zama magana ta da shi ta karshe kenan a duniya, dan nasan mutuwa sanyi, dan Allah....." Diff ya kashe wayar ba zai iya bari ta karisa maganar ba, zuciyarsa ba zata iya ɗauka ba.

Shi kuwa Aseef yana jin abin da ta ce hankalinsa ba karamin kara tashi ta yi ba, nan take ya fara murkusoso tamkar wanda ake zarewa rai, ya kankame hannun Lion a cikin nasa, ganin hakan yasa Lion ɗin ya ɗan danne shi ya fara karanto mishi kalmar shahada dan yasan duk idan rai ta zo fita haka bawa yake yi, so ba zai so ɗan uwansa ya tafi ba tare da kalmar shahada a bakinsa ba, gara kome yake ji ya danne ya bashi kalmar shahadar zai fi dan hakan ne cikakkiyar soyayya kenan.

Areef kam ganin abin yake tamkar mafarki ne, dan haka ya kasa motsawa daga in da yake tsaye, a hankali Aseef ɗin ya fara karɓar kalmar shahadar, da kyar ya kai na farko ya sake farowa, sai karanto mishi Lion ɗin yake yi ya ɗan dannesa kaɗan.

Bai kai karshen kalmar shahadar ta biyu ɗin da yake karanto mashi ba, ya yi shiru diff tamkar an ɗauke wutar nepa, rai ya yi halinsa.

Wani irin kururuwa Areef ya kurma tare da yin kan gadon a zafafe yana faɗin "No Aseef no, kada ka mutu, ka tashi, na yi maka alkawarin ko raina zan bada domin cika maka burinka na auren Heartbeat naka, ka tashi, ba zan iya jure rashinka ba". Yana magana yana jijjiga gawar Aseef ɗin da iya karfinsa na karshe.

Mikewa Lion ya yi ya fice daga cikin ɗakin da sauri, domin zuciyarsa ta kasa jure ganin abin da yake faruwa, motarsa ya je ya shiga, da kansa ya tuƙa ya fita a gidan da wani mahaukacin gudu, da alama ya fita a hayyacinsa sosai, Mark ya yi ƙokarin karɓa mishi tukun dan ya dawo da Rimsha yanzu, amma ina bai bi ta kan kowa ba ya figi motar ya yi waje.

Da sauri Imran da daddy suka yi kan gadon suna ƙoƙarin jan Areef ɗin baya dan ya dai'na jijjga gawar Aseef ɗin kada ya yi mishi illah. Idonsa ya rufe, baya ji kuma baya gani, shi dai kawai ɗan uwansa ya tashi, bai san suwaye ne suka riƙe shi ba kawai ya yi watsi da su tare da kurma wani irin mahaukacin ihu tamkar kururuwar maƴinwacin zaki, da karfi karfi ya cigaba da danne kirjin Aseef ɗin yana ambato sunansa tare da faɗi kada ya mutu ya tashi. Tamkar zautatce haka Areef ya zama a wannan rana.

Duk abin da yake faruwa Tyrone ya sani, dan haka sai ya kira Tga a waya ya sanar da shi Michael ya mutu, cikin ƙanƙanin lokaci labarin ya fara bazuwa, duk sojijin dake gidan sun samu labarin.

A yau family'n William jacop sun ga matsanancin tashin hankali na kin karawa. John ya yi suma sau ba adadi da suka samu labari ta bakin Tyrone, dan ya san me yake faruwa, shi ne ya sanar da Tga, shi kuma ya sanar musu, Jay kam tun da ya zube akan gwiwowinsa a tsakiyar palon kasa bai kara motsawa daga wajen ba, shin ko yana raye ko shima ya mutu, Allah masani, TGA kuwa duk taurin zuciya irin tasa yau sai da ya yi kwallar da ta kasa tsayawa, sun ki faɗawa daddy abin da yake faru, domin sun san idan ya ji labari, to fa tabbas za'ayi gawa biyu, Josephine kuwa lokacin da ta samu labari karamin hauka ta yi masu wadda sai da Areef ya sanya aka rufeta a ɗaki, lokacin da Rimsha ta dawo daga school ta sami labari da yake shabiyu suke dawowa yanzu, ta yi suma ya kai sau uku saboda tsananin tashin hankali, wannan bala'i da me ta yi kama?, Imran ma kuka ya sha tamkar ƙaramin yaro.

A ɓangaren daddyn Rimsha kuwa, ai kusan ya fi kowa hauka, domin idan ba ku manta ba, kusan za'ace ya fi su Areef shaƙuwa da Aseef ɗin a yanzu, idan baku mance ba komai a tare suke yi, hakan tasa sau biyu yana suma, ya yi kuka har idanunsa suka kumbura suka yi luhu luhu, ga shi sun yi jawur tamkar wuta, Jehan da bata san shi ba ma ta zubar da kwallah ganin halin da jama'ar gidan suka shiga.

Lion kuwa tun da ya sa kafa ya fita daga gidan bai kara dawowa ba, sai jiransa suke yi ya dawo ayiwa Aseef sutura a kai shi makwancinsa, amma shiru, sun kira wayarsa har sun gaji a kashe, sosai hankalin Areef ya tashi na rashin samun Lion ɗin a waya, tunani ya fara yi kada ace wani abin ne ya same shi fa, domin kuwa da kansa ya tuka mota ya fita daga gidan, kuma da alama baya cikin hayyacinsa time da ya fita.

Mukoma baya kaɗan dan jin ya akayi jenan ta dawo gidan, mu koma jiya kenan da za'a yanke mata hukunci.

Lokacin da Lion ya tashi daga barcin wannan allura da Areef ya yi mishi, ya ɗan ji komai ya ragu, zuciyar ta sauka, amma fa abin yana ransa, sai dai dama idan aka yi maka laifi, in baka yi hukunci a lokacin ba, to kana iya yafe lafin dan abin ya ɗan sauka, shi ma hakan ce ta faru da shi, toilet ya nufa ya yi wanka kafin ya fito ya shirya cikin kayan barcinsa ya zo ya kwanta, ba jikawa ya yi barci na gaskiya ba na allura ba.

Washegari da safe Rimsha ta shirya zuwa school, kamar kullum Mark ne ya kaita, kwata kwata bata haɗu da Lion ba, shi ma kuma bai zauna ba, tun asuba ya fita zuwa Abuja, sai karfe 11 ya dawo, Areef kuma ya tafi court dan hukuncin da za'a yankewa Jehan.

Da misalin karfe 12:30, Rimsha tana tsaye a bedroom ɗin Lion tana gyara mishi bed nasa, ba jimawa ta dawo daga school, ko abinci bata ci ba ta hau wannan gyara, tana ta aikintaTv dake manne a bango yana magana, labarai ake yi, ta kasa kunne tana jin abin da suke faɗe duk da bata ganinsu aikin da take yi kawai take kalla, tamkar saukar aradu yaka ta ji ana faɗin hukuncin da aka yankewa Jehan a labaran, wato hukuncin kisa ta hanyar rataya, hakan yasa ta yanke jiki ta faɗa saman bed ɗin da take gyarawa, saboda tsantsar tashin hankali, a lokacin Lion ɗin yana zaune saman sofa yana latsa laptop, shi abin ma mamaki ya bashi, ta ya ya za'ayi irin wannan shari'ar haka? Abu sai kace wasu marasa ilimi, amma bai wani damu ba, shi bincike ma yake yi akan wanda Jehan ɗin ta kashe, a nan ne kuma ya gano gaskiyar cewa ABUBAKAR SALAHUDDEEN shi ne mai gidan wanda ya kamo daga clubs ɗin nan, wato wanda Mark yake horarwa yanzu, ABUBAKAR SALAHUDDEEN shi ne ya basu contract na kashe daddyn Rimsha, wanda ya kamo babban yaron Abubakar jaja ɗin ne, babbar magana, Jehan ya kashe wanda ya yi yunkurin tarwatsa musu family koma a ce ya tarwatsa, ta kashe shi bata san waye shi ba, lallai idan Allah ya tashi kama bawa baya gaya mishi ga ta in da zai bi ya kama shi, yanzu shi Abubakar kafin ya rasu, lokacin da yake cin duniyarsa, idan aka ce mishi ƴar cikin Nawazudden ce zata kashe shi, wlh ba zai yarda ba, dan yana ganin ya fi karfin Nawazudden ma bare ƴarsa, amma da Allah ya tashi kama shi, sai ya haɗa shi da ƴar makiyinshi, shi ya santa, amma ita bata san shi ne ya tarwatsa musu gida ba, ta dai san abokin takarar mahaifinta ne, bayan haka batasan wani abu ba, bata san yana da alaƙa da mahaifinta ta wata fuska bayan siyasa ba, Allah mai iko, ga shi ta ɗauka musu fansa cikin rashin sani.

Ganin wanda ta kashe shi ne ya tarwatsa musu gida yasa Lion ya ciro wayarsa ya kira His excellency, cikin natsuwa ya sanar da shi, ya sanar da president na Nigeria yana bukatar court ta wanke Jehan duniya kowa ya gani, bayan haka ƴan'sandan da suka ɗauketa su dawo mishi da ita har cikin gidan nan kamar yadda suka ɗauketa.

Haka kuwa aka yi, duk abin da ya bukata an yi mishi, dan kakan nasa yasan jikan nasa baya yanke hukunci da kai haka kawai, duk abin da yake yi yana tsawaita tunani da bincike, kuma a kan gaskiya yake aiwatar da komai, hakan yasa a ka wanke Jehan daga idon duniya kamar yadda suka yi mata sharri, sai Allah yasan waye mai tsara musu magana, nan take suka juya maganar da cewa ai ba Jehan ba ce ta yi kisan, kuskure a ka samu, Jehan ta je wucewa ne a lokacin ta taka sahun ɓarawo, dan haka wanda ta yi kisa daban, ana nan ana bincike za'a nemota, ita kuma Jehan court ta wanketa tare da bata hakuri na abin da ya faru, daga karshe court tana kara jinjinawa Nawazudden tare da yi mishi fatan samun aljanna, nan take duniya ta ɗauki zancen gaskiya ne, kowa ya dai'na ganin laifin Jehan, ƴan'sanda mota uku ne suka ɗaukota zuwa gidan Lion ɗin, da mutunci suka sauketa suka juya.

Suna sauketa Areef ya iso wajen da matarsa shi da Donal, fita ya yi daga cikin motar bayan ya sa Donal ta taka birki, cikin sanyin murya ya ce mata su shiga cikin gidan Rimsha tana can tana jiranta, harara ta wurga mishi kafin ta wuce gaba abinta, ɗaya daga cikin sojojin ne ya buɗe musu gate, lokacin Rismha tana sume kwance saman bed ɗin Lion.

Bedroom ɗin Rimshar Areef ya rakata, ganin bata ciki ne yasa ya ce "ki zauna bari na duba miki ita a bedroom ɗin Lion", ko sannu bata ce mishi ba ta samu waje ta zauna abinta tana wani kwaɓe fuska.

Lokacin da ya shigo bedroom ɗin Lion ɗin, shi kuma ya miƙe daga saman sofa ya nufi toilet, ya yi mamakin ganin Rimsha a kwance a gado, shi a ɗaukarda barci take yi, sai da ya matso kusa da ita sannan ya san ba barci take yi ba suma ta yi, jin saukar ruwa a toilet ya sa ya gane Lion yana ciki, fridge ya nufa ya ɗauko ruwa mai sanyi da zuba mata ta fuska, duk a gajiye yake, jikinsa har ciwo yake yi mishi, ya sha fama ba kaɗan ba, kullun yana zarya tsakanin prison da gida, wani lokaci ma da daddare, Alhadulillah dai yanzu komai ya wuce ai.

Yana shafa mata ruwan ta farka a tsananin razane tana ambatar sunan Jehan, riƙota ya yi yana faɗin "Our Queen ki natsu, baby ta dawo tana ɗaki". Zuba mishi ido ta yi tana jin abin kamar a mafarki, jin motsin Lion yana fitowa ne yasa ya saketa dan baya son duk wani abin da zai kawo mishi matsala tsakaninsa da ɗan uwansa, tun da ya lura azababben kishi ɗan uwan nasa yake yi idan suka taɓata, sai ya fara ja baya da ita, kuma ko kaɗan bai ga laifin Lion ɗin ba dan ya yi kishj, domin kuwa haka suke dukkansu uku, shi ma yanzu misali idan Lion ya taɓa Jehan gaskiya zai ji babu daɗi, so dan haka shi ma gara ya kiyayewa ɗan uwan nasa matarsa dan shi ya rigada ya bashi ita.

Ta yi mamkin irin saketa da ya yi tare da ɗan matsawa baya kaɗan daga kusa da ita, ganin Lion ya fito ne yasa ta fahimci dalilin sakin nata da ya yi, kallo ɗaya ya wurga musu ya kawar da kansa kafin ya wuce zuwa dressing room abinsa, daga kallo ɗayan ba kari.

"Zo muje ki ga baby ita ma tana ɗaukin ganinki". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa ya yi gaba, da sauri ta diro kasa ta bi bayansa, bakinsa ɗauke da sallama ya shigo cikin bedroom ɗin. Da gudu Rimshar ta tafi ta rungume yar uwarta tana kuka, ita ma runguneta ta yi suna jin abin kamar a mafarki, shi kam tsayuwa ya yi ya zuba musu idanu yana kallonsu fuskarsa ɗauke da fara'a, yana jin daɗin ganin irin tsantsar farincikin da suke ciki, abin ba'a magana, mai saurin kuka ma sai ya zubar musu da kwallah. Rimsha an sha kuka kamar ba gobe, sai rarrashinta Jehan ɗin take yi tana goge mata hawaye.

Cikin zolaya ya ce "Au baby ashe kin iya rarrashin mutun? Wato ni ne kike yi wa wannan kallo na up and down ɗin ko?". Harara ta watsa mishi bata kula shi ba.

Readers Also Read